suka wankewa
kwakwalwa haka yaji, kafin ya fahimci menene
dan karamin abinda ke hannun shi mai dauke
da sakon da yake da nauyin gaske
"Zamu samu yaro ko yarinya?"
Ya tambaya muryar shi na fitowa a shake, kai
take daga masa, ya kuwa sake riketa kamar zai
mayar da ita cikin shi, tun shekarar farko ta
aurensu da sukaje asibiti aka tabbatar musu da
lafiyarsu kalau, babu mai wata matsala suka
dawo suka barwa Allah komai. Yana danne tashi
damuwar ne saboda ya karfafa mata gwiwa,
amman yasan abin yana damunta duk da bata
cika yi masa zancen ba, amman indai suka tare,
a dararen alhamis da juma'a, koma basa tare
takan tuna masa daya tashi yayi sallar dare don
neman biyan bukata, gashi kuma yau Allah ya
amsa musu.
Lubna sufyan
Hausabook.com 665
Yaje Kano, a tsakanin samun cikin nata,
laulayinta, kananun ciwuka da kuma taraddadin
da ba'a raba mai ciki dashi, yaga Bukar, yaga
Kaltume, ya gaisa dasu da wani yanayi a tare
dashi da bai gama fahimta ba. Farin cikin da
yake fuskar Daada na sanyaya wajaje da dama
da baisan a zafafe suke ba tare dashi. Daga
Bukar din kuma har Kaltume babu wanda yayi
wani yunkurin karfafa alakar tasu, kamar sun
matsa gefe suna jiranshi yaje musu da kanshi.
Sai dai a daren da ciwon nakuda ya kama
Murjanatu, ya dauketa a rude zuwa asibitin da
take awo, ya kuma ki sakin hannunta duk yanda
likitocin suka so, sai suka hakura suka barshi ya
bisu dakin nakudar tunda ita kadaice a ciki,
kuma kudine suke aiki balle a nuna musu fin
karfi.
Ba zaice baisan wacece uwa dan bai taso tare da
ita ba, a ranar da ya kara fahimtar wacece ita, ya
kuma ga dalilan da yasa aka daga darajarta a
addini, a gabanshi kan da ya fito, ya kuma
tokare saida aka kara Murjanatu, wani abu da
ba zai manta ba har karshen rayuwar shi, dan
Lubna sufyan
Hausabook.com 666
baisan yana hawaye ba sai da wata cikin Nurses
din tace masa
"Haba dai oga, idan kana kuka ai zaka kashe
mata jiki..."
Lokacin da kukan yaron ya karade dakin, aka
goge shi aka mika masa, sai komai ya tsaya
masa, idan yace komai a lokacin, yana nufin
komai, harda zuciyar shi da bugunta yayi wani
irin kasa. Lokaci daya yaji baisan komai ba,
baisan kowa ba sai halittar da aka saka masa a
cikin hannun shi, abu na farko kuma daya fara
dawo masa shine iyayen shi, iyayen shi da a yau
ya fahimci duk wani dalili da zai nisanta yara da
mahaifansu fa ba karami bane ba, musamman
uwa da tasha wannan gwagwarmayar. Daya
dago yaron yana yi masa kiran sallah cikin
kunnen shi hadi dayi masa hudu ba da Khalid,
sai wasu siraran hawaye suka zubo masa.
Lokacin daya fito waje yayi waya ya fada ma
Daada cewar Murjanatu ta haihu, da yammacin
ranar baiyi tsammanin duka ahalin shi zasu
taho ba, su dukansu suka yo mota uku suka
Lubna sufyan
Hausabook.com 667
taho. Wajen Kaltume ya fara nufa yana riko
hannunta da fadin
"Ummi, Ummi Na"
Yana saka wasu hawaye kwace mata, saiya
kwantar da kanshi a jikin kafadarta yana
barinta ta rike shi, yaji duminta da zaluncin
wasu mutane ya hana masa shi tsayin shekaru.
Hannun shi na cikin nata suka shiga cikin gidan,
suna bin bayan kowa saboda sun shige cikine
suna basu wajen da suke tunanin suna bukata
shi da Kaltume. Da Khalid yaji sunan yaron,
saiya kalli Nawfal
"Nagode Hamma, da komai, nagode"
Nawfal ya furta a hankali yanda Khalid din ne
kawai zaiji, bai iya cewa komai ba, shiru yayi
yana kara rike yaron a jikin shi, saboda bai
yarda da kanshi ba
"Wai Khalid kuka zakayi?"
Cewar Adee, ya harareta da idanuwanshi da
sukayi maikon hawayen da yake cike dasu, yana
sa kowa yin dariya
Lubna sufyan
Hausabook.com 668
"To girma ya kamaka Khalid, sai kazo ka tsaida
matar aure tunda ni dai nace banayi"
Daada ta fadi, murmushi yayi, daman yana da
niyya, tunda sun gama dai-daita kansu shi da
Maryam da watannin su shidda da haduwa a
lokacin, ya dai san akalla za'a saka musu wasu
wata shiddan, tunda yana bukatar ya shirya
sosai, in dai ya samu yanda yake so gidan nashi
yana fatan ya zuba duka kayan amfani ya
daukewa iyayenta tunda ya kula ba karfi gare su
ba, wadatar zuci ce da kuma kokari irin na
talatan da zuciyar shi bata mutu ba.
"Yanzun fa mu da mu kara taruwa haka sai Bikin
Khalid ko?"
Murjanatu tayi maganar tana fisgo Nawfal daga
duniyar tunanin daya fada
"Ai Hamma na da matsala, biki wata takwas, mu
an taba saka biki mai nisa haka a family
dinmu?"
Fadar Nawfal yana hararar Khalid dake zaune
da takwaranshi da suke kira Junior a hannu
Lubna sufyan
Hausabook.com 669
yana ta kara gyara masa kwanciya, yaron dake
ta sharar bacci
"To abinka da bikin talaka, dole ina bukatar
shiri, yanzun ba gashi saura wata shidda ba"
Salim ne yayi tsaki wannan karin
"Menene shirin a ciki?"
Kai Khalid ya girgiza
"Dan Allah idan ana maganar kudi, ka daina
saka baki Hamma, albashinka da namu ba iri
daya bane, ba zaka fahimta ba...kuma kai Hajiya
Adee ta saka maka hannu"
Da mamaki Salim yake kallon shi
"Adee banda akwatuna, duk abinda aka saka a
lefen nan ba kudina bane ba?"
Dariya Adee takeyi
"Na fa kara da takalmi da jaka Hamma"
Tsakin ya kara ja yana girgiza kanshi kawai,
yaga alama so suke su bata masa rai
Lubna sufyan
Hausabook.com 670
"Hamma kace duk abubuwan masu
muhimmanci yi maka akayi, ai in ba wani auren
zaka kara ba babu yanda za'ayi ka gane..."
Bai karasa ba saboda hararar da Madina ta dago
kai tana watsa masa batare da tasan ma tayi ba
"Bajjo..."
Khalid ya kira yana dariya, shima dariyar yakeyi
yana daga hannuwan shi cikin sigar dake nuna
saduda
"Afuwan uwargida ran gida...subutar bakine"
Ya karasa maganar da dariyar data fito daga
kasan zuciyar shi, duk da kara tsuke fuska
Madina tayi, yana kuma jin kaunarsu da bata da
misali na cika zuciyar shi, a gefe daya godiya
yake yiwa Allah yana karawa, godiyar da yake
da tabbacin ba zata taba yankewa daga bakin
shi ba har karshen numfashin shi.
Epilogue 2
Mutuwa sunanta iri daya ne, sanadinta da
sakonta ne yake bambanta, akwai mutuwar da
Lubna sufyan
Hausabook.com 671
zakaji labarinta kawai ta tabaka, akwai wadda
zakaji labarinta ta baka mamaki badan wanda
ta dauka yafi karfinta ba, akwai wadda zaka jita
ta tuna maka taka mutuwar da kake zaman jira,
akwai kuma wadda zata idan ka jita zata daga
kafafuwanka ta sulmuyo da kai ta ka, ta hargitsa
lissafi da duk wata natsuwa da kake tare da ita.
Wannan mutuwar itace ta Yelwa a wajen
Madina, mutuwar da ta basu notice tunda ta
nuna alama ta hanyar rashin lafiyar Yelwar, sun
kuma dauka a shirye suke da zuwanta sai da ta
ratso din a lokacin da hankulansu sukayi nisa da
tunaninta.
Tana da tambayoyin da ko a kasan ranta take
tsoron furtasu saboda zasu iya saka ta fita daga
addinin da shine rufin asirinta a duniya da
lahira. Duk yanda ake mata gaisuwa, ake
kallonta cike da tausayawa da ido kawai take
binsu. Sai da Salim ya ratso taron matan dake
cikin gidan bayan ya kirata tana kallon wayar ta
kasa dagawa, ya kuma kama hannunta bayan ya
gaishe da kowa, bai nuna ko a fuska ya damu da
kallon da sukeyi masa ba, idanuwan shi na kan
Madina da batayi masa gardamar mikewa ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 672
bishi ba, akwai hijabin Daada a jikinta saboda
sanyin da take ji. Bai tsaya da ita ko'ina ba sai
bakin motar shi inda ya bude murfin yana
sakata ciki.
Ya zagaya ya zauna, jingina jikinta tayi a jikin
kujerar motar tana lumshe idanuwa, bata bude
su ba sai da taji ya tsayar da motar, ta daiyi
mamakin ganinta a gidansu, ya kuma zagayo ya
bude murfin motar yana mika mata hannun shi,
batajin karfi ko kadan a jikinta, batayi musu ba
ta kama ya taimaka mata ta fita daga motar, ko
takalma babu a kafarta sai socks, janta yake har
bangarensu, zuwa dakin shi, inda kamar hakan
yake jira ya kama hijabinta ya zare bayan ya
rufe kofar, ya cire gilashinta ya ajiye a gefen
gado, ya kuma zagaya hannuwan shi yana riketa
hadi dayi mata rumfa da jikin shi. Ba tasan
menene ba a lokacin, dumin shi? Kamshin shi?
Ko kuma kulawar shi ce, ko duka ne suka hadu
sukayi tasiri akanta.
Dan wani irin kuka da batayi ba a kwanakin nan
ta tsinci kanta da rushewa dashi. Ya sake riketa,
kuka takeyi tana karawa, kukan rashin
mahaifiyar da bata jima da shigowa rayuwarta
Lubna sufyan
Hausabook.com 673
ba, kuka take a jikin Salim, Hammanta, kuma
mijinta a yanzun. Kuka tayi har saida sauran
karfinta ya kare, dan badan rikon da yayi mata
bana wasa bane, kafafuwanta ba zasu iya
daukarta ba. Dakyar da taimakon shi ya kaita
bandakin shi ya rufo mata ya fita, fuskarta ta
wanke ta kurkure baki ta fito, da bata ganshi ba
sai ta kwanta akan gadon kawai, bata da karfin
zama, bacci ne ya fara daukarta taji yana
tashinta. Dakyar ta iya mikewa zaune
"Kisa wani abu a cikinki"
Ya furta yana mika mata robar yoghurt din da
batayi masa musu ba ta karba, ta sha rabi, ya
kuma sake bata dankalin turawa da wainar
kwai, ta danci kadan, kafin ta girgiza masa kai
"Ki kwanta ki huta, anjima sai in mayar dake"
Komawa tayi ta kwanta, tana jinshi yana ta shige
da fice kafin taji hawan shi gadon, haka kawai
taji zuciyarta ta natsu, irin natsuwar da ta rasa a
kwanakin bakwai, ya mika hannu ya jata zuwa
jikin shi yanayi mata makwanci akan kirjin shi
inda tayi luf da ita, zata iya rantsewa kamar an
halitta mata shi dai-dai ita, dai-dai kwanciyarta,
Lubna sufyan
Hausabook.com 674
dan inda kanta yake a kafadarshi yayi dai-dai,
tamkar an auna kafin a halitta masa. Yaune karo
na farko da ta kwanta a jikin namiji, ya kamata
taji daban, yakamata taji wannan rashin sabon
da fargabar, amman babu komai a zuciyarta
banda natsuwa, irin natsuwar da taji bayan
labarin daura musu aure ya risketa.
Shisa ta lumshe idanuwanta tana barin bacci ya
dauketa. A bangaren Salim ne yanayin ya sha
bambam, ba ita bace macen farko da ta hau jikin
shi, ita daice ta farko da yake jin ba a jikin shi
kawai take kwance ba har a zuciyar shi, yau
kuma sai yake jin control din da yake yiwa
kansa a lokuttan da yake tare da ita yana neman
kwace masa. Wata wutar sonta nayin rassa a
duk gabban jikin shi. Ya gyara mata kwanciya
yafi a kirga ko zai samawa kanshi sauki, amman
hakan ya gagara. Tayi bacci, amman shi ko
idanuwan shi bai rufe ba, har azahar, shiya
tasheta bayan ya zameta daga jikin shi ya shiga
bandaki ya dan watsa ruwa yayo alwala.
Bai mayar da ita gida ba sai la'asar, sai kuma
lokacin wata irin kunya tayi mata rumfa, tasan
kowa dake dakin zaisan cewa Salim mijinta ne,
Lubna sufyan
Hausabook.com 675
bama su ba, yanda zata shiga gidan ta hada ido
da Daada shine babbar damuwarta. Taji dadi da
bata ga Daada a falon ba, saita wuce dakinta kai
tsaye. Ta kwanta akan gadon tana jin saukin
nauyin da kirjinta yayi mata. Musamman data
cigaba da jero
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Tana kara maimaitawa. Kamar ko da yaushe, a
dan tsakanin Salim saiya sake zame mata
bangon da take jingina dashi ta samu saukin
tsayuwar da take neman gagararta. A gefe daya
kuma Kabir ne, mahaifinta da ta kira da
"Abba..."
Karo na farko bayan rasuwar Yelwa da suka
hadu, sai ya durkushe a wajen, kuka marar sauti
na kwace masa, itama kukan takeyi, kuka sukayi
a falon Daada batare da wani ya lallashi wani ba,
kuka Madina takeyi na mahaifiyar data rasa,
kuka take na mahaifin da yake gabanta, kuka
takeyi na godiyar Allah daya sa tana da rabon
ganinsu ta san su. Shi kuma kuka yakeyi na
matar shi daya rasa, matar data tsallake kowa
da komai nata ta zabe shi, matar da tayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 676
gararamba a titi tsayin shekaru ta sanadin shi,
matar da ciwon da basu taba tsammani ba ya
dirar mata, kafin mutuwa ta risketa tana yi
musu tsakani na har abada. Mutuwar da ta saka
shi kokarin neman sauran yan uwan shi saboda
yanda yake jin shima bashi da wani sauran
lokaci mai tsayi.
Yan uwan da suka karbe shi kamar basu taba
korar shi ba, suka yi nadama kamar sun jima da
gane kuskuren su. Ya kuma yi kokarin daukar
Madina ya hadata dasu da jagorar Salim daya
rakasu. Taga 'yan uwan mahaifinta, taga ahalin
da idan ta juya a garin Kano zata kira da nata.
Yanda duk in anyi wani motsi mai girma Kabiru
zaice musu
"Babu ni idan ba Yelwa, inaji a jikina tazarar mu
ba mai nisa bace ba"
Jinshi kawai sukeyi, suna kuma tausaya masa,
ko Daada sai da tayi maganar shi, tasan Yelwa
batayi zabi me kyau ba lokacin data tsallake su,
amman alamu sun nuna ko su suka laluba zai
wahala su zabo mata mijin da zai mata soyayyar
da take gani a idanuwan Kabiru. Sai suka fara
Lubna sufyan
Hausabook.com 677
saka shi a addu'o'insu, da fatan Allah ya saukaka
masa radadin rashinta ya takaita masa kewa. Sai
dai jikin shi bai masa karya ba, kalaman shi
duka akan gaskiya suke, a lokacin da ya bi Yelwa
kwanaki arba'in da shidda cif a tsakanin su
bayan zazzabin kwanaki biyu rak. Wata
mutuwar da ta sake taba su dukansu.
Saboda Kabiru ba irin mutanen da zasu rabeka
ka kasa kaunarsu bane ba, ko murmushin shi
kawai da kyallin shi yake kaiwa har cikin
idanuwanshi zai tsaya maka, balle kuma kirkin
shi, komai a tare da Kabiru mai tsayawa a zuciya
ne.
"Hamma daman sun dawo ne dan mutuwa ta
lallabo ta dauke mun su daya bayan daya?
Wacce irin kaddara ce wannan? Anya ina da
zuciyar dauka?"
Madina ta tambaye shi hawaye na silalo mata, ya
riko hannunta
"Kowanne rai da tashi kaddarar Madina, amman
Allah baya dorawa bawa wadda ba zai iya dauka
ba, ki godewa Allah da kika samu lokaci tare
dasu, duk da bai tsawaita ba kin samu, akwai
Lubna sufyan
Hausabook.com 678
yara da yawa da har abada ba zasu san iyayen su
ba, tasu kaddarar kenan...wasu ma kafin
haihuwar su suke rasa iyaye mazan, a wajen
haihuwa kuma su rasa matan...kiyi hakuri, dan
Allah kiyi hakuri, Allah zai sanyaya zuciyar ki"
Kauda kai kawai tayi wasu hawayen na zubo
mata, saboda kowa sai dai yayi kokarin fahimtar
halin da take ciki, amman ba zasu taba ganewa
ba, wanda ya taba shiga cikin irin shine kawai
zai fahimta. Kwanaki bakwai bayan rasuwar aka
tsayar da ranar da zata tare gidanta, aka saka
sati biyu. Da na farko ya cika aka kawo mata
lefen da batayi tsammani ba, saitin akwati masu
shidda guda biyu. Haka ta dinga kallon
akwatinan tana hasaso kudin da Salim ya kashe
wajen cika su. An sanarwa yan uwansu, na
mahaifinta, dan tarewar har Marake sai da su
Khalid sukaje da motoci uku ran daren suka
kwaso dangin Daada, suka kuma bata mamaki
da suka hado harda Abu.
Abu data fito daga motar tana sharar kwalla,
sababbi na zubowa bayan tayi tozali da Daada
Lubna sufyan
Hausabook.com 679
"Dije wanne dalili na baki na watsar dani haka?
Kika sa naji zumunci dake tsakanin mu bai kai
inda nake tsammani ba"
Itama Daadar tana kuka take girgiza mata kai
"Na taho ne a halin kidima, ki yafe mun, kina
daya daga cikin mutanen da tunaninsu bai taba
barina ba...saboda kece kadai nasan kin soni,
zaki kuma soni batare da kin juyamun baya ba a
duk wani juyi da kaddara zatayi mun..."
Anyi koke-koke, anyi alhini, an kuma yi hirar
yaushe rabo, kaunar da jini kadai kan samar ta
nuna a fuskokin kowa. Kafin Madina tayi nata
kukan lokacin da aka rakata dakin miji, tayi
kuka kashi-kashi, amman fiye da rabin kukanta
na farin cikin da taji ya dirar mata ne, ganin
tarin mutanen da sukayi mata rakiya gidanta,
kuma kusan kowa a ciki ta duba alaka ta jini ta
hadasu, kowa kuma yana riketa kamar yana son
tabbatar mata rashin Kabiru da Yelwa ba zaisa
ta taba yin maraici ba. Kafin su tafi su barta da
Salim da tun bayan sallar godiya da sukayi suka
ci abinci dan yanata mata koken yunwar da yake
ji, suka kwanta ya riketa a jikin shi yana fadin
Lubna sufyan
Hausabook.com 680
"Nagode Madina, da kika zabeni, duk da ina da
dalilai da yawa da nasan cewa ban cancanta ba.
Daga ranar da aure ya hade mu waje daya, daga
yau, zanyi kokarin ganin na kare miki
mutuncinki, zanyi kokarin ganin nayi miki rikon
da ba zakiyi dana sanin zaben da kikayi mun
ba..."
Cikin sanyi yake maganar, a hankali, da wani
taushi da ita kadai take gani a tare dashi
"Nice da godiya Hamma, kai da ka zabeni tun da
ayar tambaya akan asalina, kai da ka zame mun
bangon jingina a lokutta mabanbanta, Hamma
nice zan gode maka daka zabeni, daka soni"
Wani abu yakeji yana tsirga masa, shekarunta
da yaketa nanatawa kanshi da karantarta na
bace masa, baisan komai ba a lokacin sai
soyayyarta, kwakwalwar shi ta hade waje daya
da zuciyar shi kamar yanda yake son hade duk
wata tazara da take tsakaninsu shi da Madinar
da batayi mamaki ba, a littafin hausa ne kawai
zai tsaya rainonta, za'ace ya jirata saboda tayi
kankanta, amman a irin litattafan da take
karantawa shekarun nata ne kadai abinda zai
Lubna sufyan
Hausabook.com 681
jira, a wasu kasashen ta kai sha bakwai, a wasu
ta kai sha takwas. Sai dai babu wani littafi, babu
kuma wani hasashe da ya shirya mata wannan
daren da ba zai gogu ba. Daren da tausaya,
kauna da kuma lallamin Salim basu hana
kwallarta zuba ba. Sai dai ta samu sauki da
tabbaci a rikon da yayi mata kamar zai mayar da
ita cikin shi.
A hankali Salim ya bi duk wani lungu da sako da
soyayyarsa ta samu zama a tare da ita batare
data sani ba ya taso da son nan, tun tana
mamakin yiwuwar kaso mutum da duk wani
abu da zaka iya, amman duk rana sai yayi wani
abu da zaisa kaji wannan son ya karu.
Alkawarin da yayi mata kan karatu yayi kokarin
cikawa duk kuwa da kishin da yanzun take
sanin Salim din yana dashi. Ya kaita ta rubuta
jamb da kanshi, ya jirata ta gama ta fito suka tafi
gida. Karfi da yaji ya koya mata saka dogayen
hijabi, ya kuma koya mata mota dan bayason ta
shiga ta haya, kafin ya gama tara kudin motar da
zai sai mata, tashi yake bar mata idan tace masa
zata fita lokacin da yaci karo dana aikin shi. Shi
ya hau ta haya.
Lubna sufyan
Hausabook.com 682
A haka ta samu gurbin karatu a jami'ar Bayero.
Bayan roko da tarin nasihar kula da kanta da
Salim yake fada yana kara jaddada mata, duk
idan zata fita haka zaiyi kici-kicin da fuska,
kamar inda yana da zabi, inda baiyi mata
alkawari ba, da ya hana karatun. In tana masa
dariya wasu lokuttan kai kawai yake jinjinawa.
Saboda ba zata gane ba, ba zata taba fahimtar
baiwar halittar da Allah yayi mata a kasan
kayan da take boye su ba, baiwar da yayi mata
da sirrine a zuciyar Salim din. Taya zai san duk
wannan ya kasa kishi da fargabar kar wani ya
ko hango masa duk wannan?
Sai dai a cikin abubuwan da Madina ta kasa
fahimta game da Salim, yanda baya bari taje
gidan iyayen shi ita kadai, ko me akeyi kuwa
zaice ta bari suje tare, idan sunje din kuma tare
suke komawa gida. Ko kowa yana nan, ko ta
roke shi ya barta zata ga ya hade fuska cikin
yanayin da yake nuna mata ba zai tankwaru ba,
dole ta tashi ta bishi su tafi. A ahalinsu kaf kuma
babu wanda ya fahimci hakan sai Julde da
Saratu, babu wanda abin yake damu a zuciya
irin Julde, da zuwa yanzun yasan aura masa
Lubna sufyan
Hausabook.com 683
Saratu da Datti yayi gatane da son da baya mata
ya hana shi gani. Har zuwa yanzun kuma mace
daya ya so, Mero, kuma tazo a daya daga cikin
kaddarorin da zasu horashi, ya sameta, halin shi
ya nisanta shi da ita, nisa na har abada tunda
tana gidan wani a matsayin matar shi.
Sai dai ko baiso Saratu ba, yanzun tilas ya
girmamata, saboda ko Meron, duk son da yayi
mata, duk ikirarin son da takeyi masa da tayi
bai hanata tsallakewa ta barshi ba, bai kuka
hanata fadawa kowa dalilinta ba. Wani tonon
asiri da Saratu bata tabayi masa ba a tsayin
zaman su, sirrin neman matan shi da duk wani
wulakanci da ya taba yi mata a tsakanin su yake
tsayawa. Abinda ya fahimta a kurarren lokaci,
abinda kuma yake jin ciwon rashin fahimtar shi
tare da ciwon yanda koya yaran nashi suke
zaune a gidan, in dai Salim na nan da Madina ya
shigo zaiga yanda nutsuwa ta kwacewa Salim,
zai kuma ga yanda yake gyara zama yana duk
wani kokarin kare Madina daga ganin shi,
kamar yana tsoro, zai sake kallonta da
idanuwan da suka wuce na mahaifi.
Lubna sufyan
Hausabook.com 684
Abinda ya kasa sabawa da ciwon shi, abinda
yake shiga daki ya zubar da hawaye duk idan ya
kadaice. Tabbas ko dashi kadai aka barshi ya
ishe shi horo, kuma ya ishe shi karin ganin
girman Allah, da zaka yiwa laifi, ka maimaita, ka
tuba ya yafe maka, ka sake maimaitawa, kaje da
kokon tuba kuma ya sake duba ka da Rahmar
Shi ya yafe maka. Shisa Julde a yanzun yake
kokarin ganin ya gyara tsakanin shi da Allah,
tunda ya gane, yana kuma da yakinin Allah ne
kadai zai gyara tsakanin shi da sauran mutane,
wata rana ya wanke shi a idanuwan Salim, ya
yarda da kaddara ce da take tare da kowanne
rai, ita ta fisge shi ya dubi Madina da wani ido na
daban, kaddarar da ya san ba zata sake faruwa
ba.
Salim din bawai nadamar Julde bace bai yarda
da ita ba, zuciyar shi ce baisan yanda zata wanke
masa shi ba, baisan ya zai goge hoton data adana
masa ba, watakila a gaba, watakila hoton na
daya daga cikin abinda lokaci zai tafi dashi, ko
kuma akasin hakan. A kowanne yanayi dai, shi
din mai godiya ne, musamman a ranakun daya
dawo daga aiki a gajiye, ko a ranakun daya
Lubna sufyan
Hausabook.com 685
ranshi yake a bace, saiya dawo gida, ya samu
Madina da murmushinta, Madina da sanyinta,
Madina da duk wani halaye daya hade ya samar
da ita tana jiran shi, hannuwanta a bude a
matsayin tashi, matar da Allah ya bashi duk da
yanajin bai cancanci samunta ba.
Sai ya godewa Allah, musamman da bincike ya
nuna akwai karamar ajiyar shi a tare da ita.
Saiya rikota a jikin shi
"Ina son ki"
Ya furta yana dora goshin shi akan nata, ta
lumshe idanuwanta kawai, bata gajiya da yanda
yake yawan fada mata yana sonta, sai dai ita son
da takeyi masa a yanzun tana jin kalmomin
ukku sunyi kadan su misalta shi, tare da cikin da
yake jikinta dai take fatan ya fahimci kadan
daga ciki, tunda ta shirya tara iyali dashi, ta
shiryama kaddarar data hada rayukan su
karkashin inuwa daya, ta shirya ma zama dashi
a kowanne yanayi zasu tsinci kansu. Tunda har
abada din da kowa yake musu fata ana karawa
da gaban abadan ma duka tafiya ce mai nisa. Sai
dai zatayi ta, zasu cigaba da yinta cikin godewa
Lubna sufyan
Hausabook.com 686
Allah da kuma fatan kowacce kaddara, mai
sauki da marar sauki idan ta riske su, ya basu
mafita, ya basu karfin zuciyar daukarta.
Ta sauke numfashi tana zagaya hannuwanta ta
rike Salim din, Hammanta, mijinta. Nima kuma
na sauke alkalamina anan, cike da godiya ga
Allah da naga farko da karshen tafiyar nan duk
nisan da tazo da ita.
Godiya ga daukacin mutanen da addu'o'in su
suka sama mun kwarin gwiwa a duk lokacin da
naso tsayar da tafiyar nan.
Nagode da goyon bayan da kuke bani a ko da
yaushe
Nagode da yanda kuke supporting dina da
kalaman ku, wasu a ciki da katin waya, data
harma da wanda sukayi mun kyautukan da suka
bani mamaki
Nagode
Nagode
Nagode
Lubna sufyan
Hausabook.com 687
Ku sani, batare da goyon bayanku ba, ni din a
matsayin marubuciya ba kowa bace ba.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 27