kiran Innar ta cikin neman dauki ya
dirar mata. Duka gidan babu wanda ya zaci zata
kwana, Innar A'i kuka ta dinga yi don macece ita
mai tsananin tausayi da raunin zuciya, harta
Babba ya karaya da ciwon Dijen.
Bata samu kanta ba sai washegari da wajen
azahar, cikin daren sumanta biyu. Duk wani
jike-jike an bata, amman takai kwanaki hudu
bata warware gabaki daya ba. In ta faki
idanuwan mutane takan share kwallar da take
silalo mata, saboda alama ta digon jini ma bata
gani ba balle tasa ran cikin jikinta ya fita. A
watanni biyu magunguna babu kalar wanda
Datti bai kawo mata ta gwada ba, amman ciki
saima fitowa da yake yi. Sun hadu su duka sunyi
kukan yanda Allah ya nuna musu iyakar su akan
cikin jikinta, tashin hankalin ta yafi na Datti,
saboda na shi tashin hankalin yana kara mata
nata ne
Lubna sufyan
Hausabook.com 76
"Ina jin karshen duniya ta ne yazo Dije, shisa
zan ga cikin wani na girma a jikin ki, shisa zanga
kin haihu da wani..."
Ya fada wani dare kamar wanda ya samu tabin
hankali
"Kuskure ne nayi, Hammadi yace in roki Allah
ya yafe mun, watakila na makara wajen rokon,
amman wannan hukuncin zan iya daukar shi
kuwa? Cikin Baabuga ne a jikin ki, haihuwa
zakiyi, ba dani ba da Baabuga"
Idan yana irin wannan surutan sai dai taita kuka
saboda bata da abinda zata fada mishi ta samu
sauki. Ta tsani Baabuga da dukkan zuciyar ta, ta
kuma tsani cikin da yake jikinta wanda ya zame
mata karfen kafa, har tana jin tana haihuwar shi
zata saka a zani ta aikama da Baabuga yasan
yanda zaiyi da shi. Wannan ne kudirin da yake
ranta duk sanda zata daga idanuwa ta dubi cikin
jikinta.
Haka yaci gaba da faruwa har sanyin safiyar
Alhamis din da ta tashi da nakuda, wata irin
nakuda da tazo mata da saukin da bata taba
sanin akwai shi a tare da ciwon nakuda ba, cikin
Lubna sufyan
Hausabook.com 77
kankanin lokaci, kukan jaririn da Innar A'i ta
karbi haihuwar shi ya karade dakin tare da
kabbar da tayi da kuma hamdala. Dije na runtse
idanuwanta, wasu hawaye masu zafi na gangaro
mata, duk bidirin da sukeyi tana jin su, ta daiki
bude idanuwanta
"Ungo, rike shi kiga dan ki, rike shi yaji dumin
ki"
Cewar Innar A'i tana saka mata yaron a jikinta,
cikin yanayin da bata ko bata wani zabi da ya
wuce na dagowa ba, tana gyara rikon yaron a
hannunta, sannan ta sauke idanuwanta akan
shi, zuciyarta na wata irin dokawa, ta rike
yaranta da yawa, ta rike Julde fiye da sau daya,
amman bata san irin wannan yanayin ba, bako
ne a wajen ta, ta kuma ji labarai da yawa akan
soyayya wadda take tsakanin mahaifiya da
abinda duk zata haifa, shisa ta dauka ta gama
sanin wannan soyayyar, sai yanzun, sai yau da
take rike da wannan yaron da take jin zata iya
gifta rayuwarta ya tsallaka in har bukatar hakan
ta taso.
Lubna sufyan
Hausabook.com 78
Hawayen ta na sauka kan fuskar shi, ya dan
motsa, tana jin motsin ya faru tare da zuciyar ta.
Kafin kwanaki bakwai su zagayo dakyar take iya
kauda kai idan yana hannun wasu, da an dauke
shi take jin kamar an dauke mata zuciyar ta har
sai sun dawo mata da shi, ranar suna Baabuga
ya kawo wani dan rago da yasa Baba sawa aka
janyo daya daga inda yake kiwon dabbobi aka
hada aka yanka. Yaro yaci sunan shi Abubakar,
sunan wani dan Baabuga din da ya rasu. Ana
kuma zuwa aka fadama Dije sunan da yaro yaci,
wata mata na rangada guda tana dorawa da
"Allah shi raya mana Bukar"
Ta kalle shi ya sha askin suna yana bacci a
hannun ta, wata irin kaunar shi ta soke ta,
kauna mai tsanani, kauna kamar bata dauki
watanni tana son zubar da cikin shi ba, kamar
bata dauki karan tsana ta dora mishi a watannin
da yake kwance a cikin ta ba, daga randa ta
sauke idanuwan ta akan shi ya shafe komai,
komai banda kaunar shi
Bukar
Bukar dan ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 79
Abinda bata sani ba shine wata kaddarar bata
ma soma ba.
In da wani yace kafafuwan shi zasu sake daukar
shi zuwa kofar gidan su Dije zai karyata. Ya
hakura da ita, shine abinda ya gayama zuciyar
shi daga lokacin da Allah ya nuna musu cewar
basu isa su cire cikin da yake jikinta ba. Tun
tana mishi aiken yara a boye har itama ta
hakura. A wajen Hammadi yaji maganar
haihuwar ta
"Dije ta sauka lafiya, ta samu da namiji"
Kalaman suka bi ta cikin kunnen shi suna sokar
wani abu a kirjin shi da yaji zafin shi ya gauraye
ko ina na jikin shi, yawun daya hadiya mai daci
ne, dacin da bashi da kalaman da zaiyi amfani da
su wajen misalta hakan. Bai furta komai ba,
Hammadi ma bai sake ce mishi wani abu ba.
Ranar daya koma gida, sanda ya shiga ya dauko
Julde a wajen Abu yayi bacci, kwantar da shi
yayi yana kwanciya a gefe, yanda yaga rana haka
yaga dare, tunani babu wanda baiyi ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 80
Alkawurra kala-kala na rabuwa da Dije babu
wanda baiyi ma kan shi ba.
Hanyar duk da yasan idan yabi zai ganta
dainawa yayi, sau daya Abu tace masa
"Da ka dawo da Dije dakin ta Datti..."
Numfasawa yayi
"Dan Allah Adda karki kara mun zancenta, na
rigada na hakura, Allah ya hada kowa da rabon
shi"
Kuma Abu har kwanan yau da yake tsaye kofar
gidan su Dije bata sake tayar masa da zancen ba.
Kowa ya dauki idanuwa ya saka mishi, tunda shi
yake azabtuwa da kadaici da kuma wata irin
kewar Dije kamar zaiyi ihu, amman a gefe
kishinta da yake ya danne komai, sanin ta hada
shimfida da wani harda rabo ya shafe mishi
komai, har safiyar yau daya dora idanuwan shi a
kanta, ita bata ganshi ba, ta fito daga gidan
Mamuda, amman shi ya ganta, ya kuma koma
baya da sauri ya shiga kwanar daya fara cin
karo da ita, zuciyar shi a cikin makoshin shi
saboda tsallen da tayo.
Lubna sufyan
Hausabook.com 81
Ta kara kyau, tayi kyau kamar bata jin rashin
shi a kusa da ita, ko da yaje gona bai iya wani
abin kirki ba yace ma Hammadi kan shi na ciwo
ya koma gida ya kwanta. Ana idar da sallar isha'i
yasan cewa koya ake ciki saiya ga Dije, in bai
ganta ba sam ba zai iya runtsawa ba, shisa yayo
kofar gidan su, ya kuma aika aka kirawo ta, ta
dauki wasu mintuna da yake jin su kamar
awanni kafin fa fito, da alama bata san kowaye
ba, yanayin da yake fuskarta ya nuna hakan
"Dije..."
Ya furta yana kuwa sa ta dube shi, duba na
tsanaki, nan take hawaye suka cika mata ido.
Yanda yayi ma kanshi alkawurra daban-daban a
bangaren Dijen ma hakane, ko Autan maza ne
shi ta hakura da shi, haka ta fadama kanta, haka
kuma ta fadawa Abu randa tayi mata zancen shi,
wacce wahala ce bata sha akan Dattin ba?
Wanne aike ne batayi masa ba a tsayin watannin
nan, kafin ta haihu duk kuwa da fadan da tasan
zata iya sha idan Baba yaji ta tsaya da shi, bayan
ta haihun ma haka, yayi biris da ita, amsar kirki
ma bata samu ba daga wajen shi.
Lubna sufyan
Hausabook.com 82
Watanni goma sha daya kenan da haihuwar ta,
idan aka hada da watannin baya, kafin haihuwar
shekara daya da wasu watanni da lissafin su
yake hango shekaru biyu. Rabon da ta saka shi a
idanuwanta, rabon da taji muryar shi cikin
kunnuwanta. Da bata da Bukar a kusa da ita fa?
Bukar da murmushi kawai zaiyi sai taji duk
wata damuwa da take zuciyarta ta kau, Bukar da
tun da cikin shi ya kamata ace ta gane cewa ko
da tana da rabon wasu yaran a gaba zai kasance
daban a cikin su, zai zama wata fitila da zata
haska rayuwarta a duk wani duhu da zata shiga.
Hakorin nan da yara suke shan wahalar shi,
hakorin da ta kusan fidda rai akan Julde lokacin
da yayi shi, dariya Bukar yayi ta ganshi a bakin
shi
"Allah ya bashi sadaka"
Cewar Innar A'i, sai dai menene ma Allah bai
bawa Bukar dinta ba? A watanni goma sha daya,
idan kofin ruwa ne Bukar yakai hannun shi a kai
kokarin shi yaga ya bata ta fara sha, ko cikin
gidan wani ya bashi yar alawa sai dai taji yana
kokarin saka mata a bakinta
Lubna sufyan
Hausabook.com 83
"Allah ya aramun rayuwa mai tsayi tare da kai
Bukar"
Ta kan furta idan yayi wani abin daya girmi
watannin shi, saboda haka kawai take ji a jikinta
kamar ba zata samu wani lokaci mai tsayi tare
da shi ba
"Dije..."
Datti ya sake kira yana katse mata tunanin da
takeyi yana kuma ba hawayen ta damar zubowa,
juyawa tayi duk da tasan yaudarar kanta takeyi,
koya tsayar da ita, ko bai tsayar da ita ba ma ba
zata iya kara wani taku akan wanda tayi ba
"Dije dan Allah"
Ya furta muryar shi cike da wani irin rauni da ya
sake saka hawayenta zubowa
"Na sake wani kuskuren ko?"
Juyowa tayi, ta kasa magana, ko zata iya
maganar ma bata san me zatace ba
"Kishin ki yayi mun yawa, akwai dararen da
nake jin kamar numfashina zai tsaya idan na
tuna kina da wani yaron da ba nawa ba...ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 84
zanyi? Ya zanyi ne Dije? Ya zan kalle ki ba zanga
yaron da kika samu batare da ni ba"
Kuka takeyi sosai zuwa yanzun
"Idan zaki iya sake zama dani ina so in sami
Baba"
Ya karasa maganar zuciyar shi cike da tabbacin
har yanzun idan ya rufe idanuwan shi ya yawata
cikin tunanin shi ba ya hango shi tare da
kowacce mace da ba ita ba, ta ina zai fara? Ita
din dai, Dijen shi da duk wasu halayen shi ta
sani, ta saba da su kamar yanda ya saba da
hakurin ta
"Idan kika ce a'a ban san ya zanyi ba"
Kai ta daga mishi, ta kasa magana saboda kukan
da takeyi, duk abinda ta fada yaudarar kanta
takeyi, bata kara tabbatar wa ba sai yanzun da
yake gabanta, take jin kamshin turaren nan da
yakan siyo duk ranar kasuwa, turaren da bata
taba jin shi tare da kowa ba sai shi, kewar shi
take ji har cikin kasusuwan jikin ta. Tasan kowa
ma ba zai kiya ba, zazzabin kwana biyu Bukar
yayi yana da watanni goma cif, saiya yaye kan
Lubna sufyan
Hausabook.com 85
shi, juyin duniya yaki kama Mama, kowa sai
yace ta kyale shi kawai tunda babu abinda baya
ci, kamar ya hango mata dawowar Datti shisa ya
saukaka mata komai.
**
Dangin Dije, wanda suka dinga kwashe ma Datti
albarka ana zayyane duk wani mugun halin shi
da suka sakani bayan ya sake ta, saboda hango
yankewar alherin da yake giftawa a tsakanin su
da sukayi, yanzun kowa sai karyata kan shi yake
da labarin sake daura musu aure ya riskini
kunnuwan su, harma da tsaida mako guda
bayan auren akan lokacin tarewar ta. Ikon Allah
take kallo
"Kinsan dan Adam ajizi ni Dije, amman ai ke da
Datti auren ku har a aljanna..."
Inji wata Gwaggon ta, abokiyar wasan Baba, da
ita tafi kowa zakewa wajen kwashe ma Datti
albarka, dan kuwa in taje gidan su, Dije kan bata
dan hasafi, kuma Datti ya aika mata nashi ta siyi
goro idan yaji zuwan nata, ga soyen sallah da
ake aika mata nata kullin daban, kusan da
kadan Dijen ta fita jin zafin sakin da Dattin yayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 86
mata. Surutu kala-kala babu wanda bata ji ba,
musamman babin halayen kirkin Datti, wasu ma
bakine a wajen ta, ita da ta kwana ta tashi dashi
a karkashin inuwa daya na tsayin shekaru, sam
bata san yana da wannan nagartattun halayen
da danginta suke ta yabawa ba.
Harda yayyenta da ya ba kyautar zannuwa na
binni da ya bayar aka taho mishi dasu daga
birnin ikko, kudi yake kashewa kamar wanda
zai dauki budurwa. Har Inna da bata da yawan
magana sai da tace
"Ki yawaita addu'a Dije, Allah ya sa zaman ku
mai dorewa ne wannan karin, Allah kuma ya
kauda mugun baki akan ku"
Duk kunya irin tata sai da ta amsa da
"Amin"
Can kasan makoshi, sai take jin kamar
kwanakin sunki sauri, kamar sunki matsowa.
Kirgawa takeyi, amman tamkar sunfi karfin
yatsun hannun ta. Sai dai me, ana ce mata tabar
Bukar nan sai an kwana biyu an bita da shi taji
zuciyarta ta fada, wani hadari mai rugugi na
Lubna sufyan
Hausabook.com 87
haduwa a cikin kanta, don wauta irin tata
komawarta gidan Datti kadai ta hango, bata
hango barin Bukar ba, bata kuma hasaso wani
zaice ta ajiye shi ba. Tayi yaya to? Ta fara kwana
bata gan shi ba ta saka zuciyar ta a ina taji
sanyi? In an kwana biyu fa taji suna cewa, kwana
biyun bahaushe da bata da tsayayyun ranaku.
Kamar suna cewa taje ne zata wayi gari ta wuni
ta sake kwana bata rike Bukar a jikin ta ba, bai
kira sunata da har yanzun shi kadai ya iya
furtawa ba taji muryar shi mai sanyi, ina suke so
ta saka ranta? Bayanannen tsoron da yake kan
fuskarta yasa Innar A'i murmusawa
"Lallai Dije..."
Ta fadi saboda ta hango wauta shimfide cikin
idanuwan Dijen
"Da shi kike tunanin tafiya? Kin dai san da ya
kara wayau gidan uban shi zaki mayar da shi
ko?"
Wannan karin zuciyar da tayi tunani saita nemo
ta daga inda ta fada ce ta bazamo tana dawowa
mazauninta kafin ta cigaba da dokawa da wani
Lubna sufyan
Hausabook.com 88
sabon tashin hankali, gidan uban shi? Gidan
Baabuga? Mutumin da ko sau daya bai taba
zuwa da nufin duba lafiyar yaron ko me yake ci
ba? Baabugan da take mantawa daga jikin shi
Bukar ya fito? Baabugan da yaran da suke da
iyaye ma a cikin gidan shi bai iya basu kulawar
da ta dace ba shine ake cewa ta dauki Bukar ta
kai, tabbas wasa suke mata, ko kuma rayuwar ce
basa kaunar ganin ta a ciki shisa suke son
rabata da Bukar da zaiyi barazana da hakan.
"Gara ki sama ranki salama akan yaron nan... Ki
kuma yi hakuri don bana tunanin Datti zai rike
miki shi"
Yayarta Kulu ta dora akan zancen Innar A'i, suna
karasa hade mata dan wajen shan iskar da ya
rage a cikin kirjinta, tana jin komai ya tsaya
mata. Bayan nan yanda duk sukayi da ita haka
take binsu dan bata da wani kuzarin kirki, doki
da murnar da takeyi na komawa dakinta duk ya
dishe, hasken fitulun daya gauraye gidan nata
lokacin da aka kaita bai taimaka wajen haska
duhun daya lullube mata zuciya ba. Wata nasiha
da fatan alkhairi da ake ta mata take jiyowa can
nesa, sai kace ba cikin daki daya suke da masu
Lubna sufyan
Hausabook.com 89
maganar ba, da wannan yanayin Datti ya same
ta, fuskar shi dauke da haske kamar sabuwar
auduga, bakin shi yaki rufuwa saboda farin cikin
da yake ciki.
"Sai nake jin yau din kamar mafarki"
Ya furta yana zama kusa da ita, shi yana jin shi
kamar a mafarki ita tana jinta kamar ta farka
daga mafarki, in tace ga inda ta tattaro karfin
halin biye masa suka raya daren ba zata iya fada
ba, surutan shi da alkawurran shi duka basuyi
tasiri akan ta ba. Har washegari bata wani jin
dadin jikin ta, shima ya kula da haka, dan kafin
ya fita saida yace mata
"Dan Allah ki saki jikin ki dani Dije, ba zan sake
maimaita wannan kuskuren ba"
Murmushin karfin hali tayi masa, duk da haka
dakyar ta samu ya fita don ya dan bata sararin
da zatayi tunani me kyau ko zata samu mafita.
Ta rasa, mafita dayace shine ta roki Datti daya
barta ta rike Bukar a wajenta, tunda yana da
halin da zai iya kula da su gabaki daya. Idan
kuma yaki zata roki Inna da ta rike shi a wajen
ta, amman ba zata taba mayar da shi gidan
Lubna sufyan
Hausabook.com 90
Baabuga ba, kome zai faru ba zata kai danta
wannan gidan ba, sai dai in bata numfashi. Da
wannan tunanin ta dan samu sassaucin kuncin
da take ji, duk da kewar Bukar din da take
nukurkusar ta.
Ta dan samu sauki da shigowar da Abu tayi,
saboda sunyi hira suna ta raha, taso ta bita
gidanta tace
"Ki rufa mun asiri, ke fa yanzun sabuwar
amarya ce, kafin wani ya ganni ace nayi girman
banza nazo na fito da yar kanwar tawa"
Dariya tayi tana sunne kanta
"Kai Adda..."
Itama Abun dariya tayi tana mata sallama ta fita
dan ta dora girkin rana. Bata kuma ba Julde ya
shigo
"Daada kin dade baki dawo ba"
Hannun shi ta kama tana riko shi
"Yanzun ai gashi na dawo"
Lubna sufyan
Hausabook.com 91
Ta karasa maganar tana saka dayan hannunta ta
shafi sumar shi da take a nannade irin ta Baban
shi. Tana godema Datti da ya sake bata damar
kasancewa da gudan jininta a karkashin inuwa
daya, jikinta Julde yahau ta kuwa rungume shi,
tana jin shi yayi luf kamar yana son fada mata
yayi kewar ta amman bashi da wata hanya da ta
wuce wannan, a jikinta yayi bacci tana kallon
girman da yayi, tana kuma kallon yanda kyawun
shi yake kara fitowa kamar ba danta ba, jikin shi
a murje alamar hutu da cima mai kyau da kuma
kulawar da yake samu, kulawar da take ma
Bukar dinta mafarkin samun ta.
Ta katanga Abu tayi mata maganar abinci,
nufinta ta tura Julde, sai kiran ya bata sanadin
fitar da take son yi, ta kuwa saba Julde da ta kai
daki ta kwantar saboda baccin da yake yi sanda
zatayi sallar azahar, ta dauki mayafi ta ja kofar
gidan ta shiga
"Oh ni Abu...fitowar dai kikayi"
Dariya tayi
"Ai shima yasan zan shigo dole"
Lubna sufyan
Hausabook.com 92
Tsakar gida kan tabarma ta shimfidar da Julde,
tare Abu ta zubo musu abincin da suna ci suna ta
hira kamar sun shekara basu ga juna ba, hannu
da Abu ta cire daga cikin abinci na saka Dije
cewa
"Ba dai har kin koshi ba"
Kai Abu ta gyada mata
"Ina jin cikina ne fa yayi datti, kinga dana fara
cin abinci sai inji duk ya dagamun hankali, na
jika magungunan da Hammadi ya kawo kamar
ma ba sha nake ba, zan sake masa magana harna
shawara a samo mun..."
Kallon ta Dije take tana ganin yanda tayi yar
fuska duk da itama ba jikin ne da ita ba, abinka
da farar fata duk sai Dije taga ta dashe mata sai
kace mai karancin jini
"Kinsan yanzun idan na dora tukunya bana tashi
daga wajen, dan koya na kishingida sai bacci ya
kwashe ni, satin daya gabata sai da aka aiko
karbar abinci na farka, ruwan zafi kawai na
dora, wutar taci ta cinye..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 93
Dariya Dije tayi wannan karin tare da Abun, su
duka basu kawo komai a ran su ba har suka
rabu. Ko da wasa Abu bata saka ma ranta komai
ba, bata taba batan wata ba, wannan karin da
taga kwanaki nata wucewa batare da taga
al'adarta ba, saita danganta hakan da canjin
yanayin da wasu matan kanyi magana a kai,
amman ita bai taba faruwa da ita ba, tana
karawa da yawan rashin lafiyar da takeyi da ba
Hammadu ba, har ita da kanta yanzun ta fara
damuwa da shi
"Anya ba zamu shirya muje binni a duba mun ke
ba Abu? Duk kin fita hayyacin ka, bana son
wannan zazzabin da kike kwana da shi"
Murmushin karfin hali tayi mishi
"Daga dan zazzabi?"
Kuma ita a cikin jikinta tana jin ya wuce dan
zazzabi, yanayi ne da bata taba jin shi ba tunda
take a rayuwar ta, kai kawai Hammad ya jinjina,
raunin da ke zuciyar shi na nunawa har cikin
idanuwan shi da basa iya boye sirrin da ke cikin
zuciyar tashi
Lubna sufyan
Hausabook.com 94
Basu hango rabo ba
Basu hango samu da rashin da ya tunkaro su ba
"Hammadi Am"
Ta kira tana kara gyara kwanciyar ta a kusa da
shi, muryarta na fitowa daga can kasan
makoshi, kuma a raunane, da ba kusa da ita
yake ba, da ba dukkan hankalin shi yana kanta
ba, da baiji ta kira shi ba, da sunan shi da yake
jin kamar an rada masa shine don harshenta,
hannu ya kai yana sake taba jikinta a karo na
babu adadi tun kwanciyar su, akwai zazzabin
har lokacin
"Hammadi"
Ta sake kira muryarta na sauka fiye da kiran
farko, har tsikar jikin shi sai da ta mike. Duk
wani labari na soyayya da ya taba ji bai kai
matsayin a dora shi mizani daya da abinda
zuciyar shi take ji akan Abu ba.
"Na'am..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 95
Ya amsa sanin halin ta, duk da tasan ba bacci
yake ba, tana iya cigaba da kiran sunan shi
batare da ta fadi abinda take so ba har saiya
amsa ta, wasu lokuttan dan kawai ta ga ya daga
ido ya kalle ta
"Kinsan fa ina jinki Abu, ko ban amsa ba ina jin
ki"
Sai tayi dariya, dariyarta da yake so
"Bafa wani abin zan fada ba, kawai dai ina son in
kira sunan ka"
Girma na shekaru dai ba zai taba canza wasu
abubuwan a tare da ita ba, kuruciyar ta dashi
kadai yake gani tana nan daram
"Alfarma nake roko Hammadi, ba zan so takura
ba, amman a lokaci daya kuma ba zan so kace
a'a ba, dan Allah ba kunnuwan ka kadai nake so
ka bude kaji ni ba, harda zuciyar ka"
Numfashi ya sauke da taji hucin shi saman
fuskarta saboda kusancin da suke dashi da juna.
Tana son Hammadi, wani irin so da ba zai
misaltu ba, amman a kwanakin nan sai take jin
kamar zatayi mishi nisa, kamar jikinta na nuna
Lubna sufyan
Hausabook.com 96
mata alamar zata bar shi, zata barshi taje inda
zata jira zuwan shi, bata son yayi kadaici kafin
ya tarar da ita
"Ka kara aure..."
Maganar ta dake shi fiye da zaton ta, kafin ya
samu damar cewa wani abu ta dora da
"Dan Allah ka kara aure, nasan duk alkawurran
da muka daukar ma kan mu a baya... Ina so ka
kara aure, inajin kamar rabon inga jinin ka a
duniya na tare da hakan"
Shiru ne ya biyo bayan maganar ta, shirun da
kan zo da duhun dare, shiru irin wanda yakan
biyo bayan magana mai nauyi da bukatar nazari.
"Abu..."
Hammadi ya kira sunanta, kirjin shi yayi masa
nauyi, kalamanta sun danne shi, idan yace baya
son ganin jinin shi a duniya yayi karya. Ko giccin
Julde ya gani sai wani abu ya matse a cikin kirjin
shi
"Baffa..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 97
Haka Julde yake kiran shi, ko da na dakika daya
idan ya rike shi ya so ya manta cewa ba daga
jikin shi ya fito ba, ya so ya yaudari kan shi, na
dakika daya kawai, sai kalmar ta fizgo shi ta
dawo da shi, sai ta tuna mishi cewa Julde dan
Datti ne. Tun kafin ma azo kan shi Dattin ma da
baisan kara ba, Datti da baya gajiya da fada
masa cewar Julden dan shine, ya sani, amman
Datti baya gajiya da tunasar da shi. Bai fada ba,
amman abin yana masa zafi har kasan zuciyar
shi. Rashin da akwai ciwo, rashin haihuwa
jarabtace da wanda yake cikinta kawai ya san
zafin hakan.
Ba zaka taba sanin ka damu da haihuwa ba sai
kaga alamun ba zaka same ta ba, sai kaga hakan
yasa ka fita daban a cikin sauran ma'aurata, sai
ka gansu rike da nasu yaran zakaji kamar suna
nuna maka yanda ba zaka taba samun naka
bane
"Dana yayi kaza"
Sai kaji kamar sun goga maka gishiri akan ciwon
ka
"Yar waje na ce"
Lubna sufyan
Hausabook.com 98
Kamar suna maka habaici ne a fakaice, suna
nuna maka sun samu baka samu ba, suna da su
kai baka da su, zasu iya, kai ka gaza. Sosai akwai
ciwo, hakurin bana lokaci daya bane ba,
musamman idan addu'ar kowa bayan ka
kyautata mishi bata wuce
"Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kawo rabo
mai albarka kaima ka samu mai maka addu'a"
Da zai iya, da yace musu subar sauran addu'ar,
suyi masa ita iya zuciyar su ba sai sun furta yaji
ba, ba sai yaga wannan tausayin a cikin
idanuwan su ba, suna kallon shi kamar rashin
haihuwa wata bayananniyar nakasa ce da yake
tare da ita
"Bana sha'awar kara aure"
Hannun shi da yake jikinta ta kamo tana hade
yatsun su waje daya, tana jin alamun aikin karfi
na yau da kullum a duk lokacin da ta rike
hannun shi, inda da haske ma tasan in zata duba
ba zata rasa sabon ciwo a jiki ba.
"Na sani, shisa nace ka bude zuciyar ka"
Numfashi yaja yana saukewa a hankali
Lubna sufyan
Hausabook.com 99
"Ko na bude babu wanda zai bani 'yar shi bayan
a bayyane yake bana haihuwa"
Dumtsa hannun shi da yake cikin nata tayi
"Inji wa? Kaf garin marake ko 'yar wa ka nema
za'a baka... Dan Allah ka duba bukatata"
Baice komai ba, matsawa ya sakeyi yana hade
sauran wajen da yake tsakanin su, itama bata ce
komai ba, barin kusancin su tayi ya karasa musu
sauran zancen.
*
"Bangane kince ya karo aure ba? Adda idan ta zo
ta haihu fa?"
Murmushi tayi ganin tashin hankalin da yake
shimfide a fuskar Dije
"To ai abinda muke nema kenan daman"
Kai Dije take girgizawa, maganar ta kasa zauna
mata, bata kasance cikin mata masu zafin kishi
ba, ta duba, ta hango Datti da wata, akwai ciwo a
hasashen da tayi, amman ciwo ne da zata iya
rayuwa da shi batare daya cutar da ita ba. Sai
dai da ta saka kafafuwanta a takalman Abu, ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 100
haska, ta hango rashin haihuwa, ta hango Datti
da karo wata, ta hango rabo a tsakanin su sai taji
numfashinta ya fara neman tsayawa, kirjinta
yayi wani irin nauyi. Idan tayi mata gori fa? Idan
ta hanata daukar dan ko yar? Miji ne ta rigada ta
kwace shi daman, idan ta kore ta daga gidan
gabaki daya fa? Shikenan? Babu haihuwa kuma
mijin ma babu shi
"Kayya... Adda maganar nan abar ta, karki fara
abinda ba zai bulle damu ba gabaki daya"
Dariya kawai tayi, ba zata ce bata jin kishi ba,
soyayyar Hammadi duk kauyen sun shaida
kalarta daban ce, balle kuma ita da akalar
soyayyar ta karkata akan ta. Kishin raba shi da
wata, ba kishin ta shigo ta samu rabo da shi ba.
Tana ma Hammadu son da take addu'a da
dukkan zuciyar ta rashin haihuwar su ya fito
daga bangaren ta. Shi din ya zame mata komai a
lokuttan mabanbanta, a wajen haihuwarta ta
rasa mahaifiyar ta, kowa zai shaida wuya bata
kisa, da Abu bata rayu ba saboda wahalar da ta
sha a wajen kishiyar mahaifiyar ta.
Lubna sufyan
Hausabook.com 101
Tana dakin Hammadi ta sake rasa mahaifinta,
sai ya zame mata wani bango da take jingine da
shi, bangon da har yan uwan da suka nuna mata
tsangwama a baya sun rabota suna morar
wannan bangon. Da zuciya daya take son
Hammadi ya kara aure
"Zata iya shigowa ta samu rabo ke kuma ta
rabaki da gidan"
Daya daga cikin maganganun da tayi ta ji kenan
daga yan uwa da abokan arziki, kowa da kalar
tashi, basu sa ta tsorata ba balle
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 27