fanke yayi dadi tunda kike tunanin yi"
Dayan daya rage ta dauka tana ajiye robar
"Fanken ne baya sona Daada duk son da nakeyi
masa, kin manta na karshe da nayi"
Dariya Daada takeyi, dan ba zata manta da
wannan fanken da ya koma fankaso ba
"Amman dai ba zan cika ruwa ba"
Cewar Madina, Daada ta kasa daina dariya
"Daada mana"
Dakyar ta iya cewa
"Ki dai kwaba kadan dan a takaita barna"
Tare sukayi dariyar wannan karin, labari suke
danyi, kusan ma Madina ce take bata labarin,
Lubna sufyan
Hausabook.com 559
wani littafi data karanta, itama Daadar rabin
hankalinta ne yake kan Madina, saboda wata
irin bugawa da zuciyarta takeyi a cikin kirjinta,
kamar tana son sanar da ita wani abu data kasa
fahimta, shisa ita kuma zuciyar taki natsuwa
waje daya, take ta kai kawo cikin neman hanyar
da zata isar da sakonta, tasan muryar Salim,
amman yau da yayi sallama sai bugun zuciyarta
ya kara tsananta
"Hamma ne, yace zaije ya dawo ne daman"
Madina ta furta, amman Daada jin maganar tayi
can nesa da ita, haka da Salim ya shigo dakin, ya
zabi ya fara sauke idanuwan shi akanta a
maimakon Madina, Salim da yakeyi kamar
bayason magana da kowa, Salim da zaiyi duk
wani kokari na kaucewa hada idanuwa da ita
bayan ya gaisheta dan karta samu halin sakeyi
masa magana, yau nashi idanuwan ne suka fara
laluben nata, labbanshi suka motsa ya furta
"Daada..."
Kafin ya matsa daga hanyar kofar kamar yana
son bawa wani damar shigowa, sai idanuwanta
suka bar na Salim suka koma kan kofar, inda
Lubna sufyan
Hausabook.com 560
duk wani mafarki, duk wani hasashe, duk wani
tsammani a tsayin shekarun nan bai shirya
zuciyarta tarbar abinda take gani yanzun ba.
Kamar hudowar hasken rana ta tsakanin gizagizai, haka shigowar Yelwa dakin ta kasance
mata, sai farin mayafin da yake yane saman
kanta ya shiga idanuwan Daada, tare da wani
hasken da bata da kalmomin misalta shi, batare
data sani ba ta kai hannu saman cikinta, inda
take jin wani abu yana yamutsa mata, a lokaci
daya kuma abubuwa da yawa suka soma
turereniya da juna wajen dawo mata
A cikinta, Yelwa ta kwanta
Watanni tara harda satika uku, lissafi ba zai
taba kwace mata ba ko akan yaran da suka leko
dan ta amsa sunan uwa, suka koma kafin ta taka
wata rawar gani a wannan matsayin da suka
bata
Nakudar ta a tsakanin kai kawon Abu da kuma
mahaifiyarta
Kyawunta
Lubna sufyan
Hausabook.com 561
Kyawun Yelwa da ya zama abin magana wajen
duk wanda yayi tozali da ita
'Yarta
Tilon 'yarta
Sai kauna irin wadda mahaifiya ce kawai zata
taba fahimta ta danneta hartana kasa fitar da
numfashi yanda ya kamata, wannan kaunar da
babu wani laifi da yake disashe haskenta a
zuciyar mahaifiya, kaunar yaranta, kaunar da ko
mahaifansu ba zasu taba fahimta ba, saboda
kashin bayansu bai karye ba, kugunsu bai amsa
ba, ba suyi rayuwa a tsakanin duniya da lahira
ba a cikin dakin nakuda, ba suja numfashi suna
tsammanin shine na karshe ba, da suka fita suka
nemo don su ciyar, a cikin shekaru biyu abincin
daga aljihunsu ya fito ba daga jikinsu ba, ba zasu
taba fahimtar wannan soyayyar ba. Hannu ta
mika, saboda shine iya motsin da zata iya
"Daada...Daada Am"
Muryar Yelwa da take rawa ta ratsa kunnuwan
Daada data lumshe idanuwanta tana jero duk
wata godiya da zata iya tunawa wajen Ubangiji,
Lubna sufyan
Hausabook.com 562
da ya kadarta fitowar Yelwa daga cikinta, ya
kadarta zatayi mata nisa, ya kuma kadarta
rayuwa ba zata kare mata ba sai ta sake ganinta,
idanuwan ta bude lokacin da dumin hannun
Yelwa ya ratsa nata
Shekaru goma sha bakwai ana neman hada ta
sha takwas din, a cikin shekarun tayi numfashi
da sanin adadin shi sai wanda ya bata ikon yi,
sai dai a tsayin lokacin, a cikin kowanne shiga
da fitar numfashinta akwai kewar ahalinta, wata
irin kewa da zatace ta danne ruhinta dan idan
tace zuciyarta kamar yayi kadan. Kewace mai
cike da taraddadin ya lafiyar su take, duk da
wautar tunani bata kawo mata rasa wani a
cikinsu ba a tsayin shekarun nan. Ko a tunaninta
abune da ba zata iya dauka ba. Musamman da
idanuwanta suka sauka kan Daada, da taja
numfashi ta fito dashi tana jin wani nauyi da
yake danne da zuciyarta ya daga, ta runtsa
idanuwanta ta bude su yafi a kirga a kasa da
dakika, tana son maida hawayen da suka cika
mata idanuwa suna hana mata ganin hoton
Daada tar a cikinsu.
Lubna sufyan
Hausabook.com 563
Sai maganganu kala-kala suka dinga turereniya
a cikin kanta, har tana rasa wanda ya kamata ta
fara furtawa, shisa ta zabi
"Daada...Daada Am"
Suna fitowa daga wani lungu na zuciyarta,
tazarar shekarun da tayi batare da Daadar ba na
hadewa da ita waje daya. Da ta karasa cikin
dakin sosai, saita durkusa a gaban Daada,
kafafuwanta na gode mata saboda ko da bata
taimaka musu ba gab suke da kasa daukar
gangar jikinta duk kuwa da yanda take jinta
sakayau, kamar fallen takarda. Sai dai har zuwa
lokacin ta rasa abinda zata sake cewa,ta sauke
kanta, hawayenta suna diga akan kafet din dake
shimfide cikin dakin, data dago da kan ma
hawayen ne suke zubo mata, tanajin karar
hancinta da taja na komawa cikin kunnenta da
wani irin yanayi saboda shirun da yake cikin
dakin
"Nayi kuskure"
Ta furta cikin kanta
"Ki yafemun?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 564
Kalmomin suka biyo bayan wadancan duka a
cikin kanta, kuskure ta sani, ta kuma fada a
waccen haduwar da sukayi, daga lokacin da taji
hannun Kabiru a cikin nata bayan auren da aka
daura musu suna sauka garin Kano, ta kalli
mutumin da yayi mata wakilci, ta juya ta kalli
wanda yayiwa Kabiru wakilci sai Malamin daya
daura musu aure da shine cikon mutum na uku,
kuskuren da tayi ya danneta, amman ya zatayi
da soyayyar Kabiru? Duk da a lokacin bata
hango rabon da yake tsakaninsu ba, kuskuren
kawai ta gani. Ta kuma sake ganin a daren da
suka dorar da auren su zuwa wayewar gari, tayi
wani irin kuka, ta wuni tanayi batare da ta samu
saukin nauyin da zuciyarta tayi mata a rikon da
Kabiru yayi mata cikin jikin shi yanayi mata
rumfa ba
"Inajin kamar ya kamata in baki hakuri Yelwa,
kamar ya kamata inji ban kyauta ba dana raboki
da ahalinki, na so kaina da yawa nasani. Amman
zuciyata bata dana sani, haka girman soyayyarki
ya rufemun ido, na kasa damuwa da laifin da
nayiwa ahalinki na raboki dasu Yelwa, ina taso
inji rashin kyautawar nan amman na kasa"
Lubna sufyan
Hausabook.com 565
Kanta kawai ta sake binnewa a cikin kirjinshi,
hawayenta na cigaba da zuba, saboda in zata
fadawa kanta gaskiya, a tsakanin nauyin
zuciyarta da kuskuren da take jin tayi, akwai
soyayyar shi, akwai kaunar da takeyi masa da
bata san yawanta ba. Ko yanzun da take son
juyawa ta koma gida, zai wahala yafiya ce
abinda zata fara rokansu, idan ta saka
gwiwoyinta a kasa a gaban Datti tana da yakinin
abinda zai fara fitowa daga bakinta ba zai wuce
"Dan Allah Baba karka rabani da Kabiru..."
Da kalamai kwatankwacin wannan, sannan ta
roke shi ya yafe mata ta kara daya taimaka ya
fahimci girman son da take yiwa Kabirun da
yasa ta tsallake su ta bishi. Ko yanzun ma da
take durkushe a gaban Daada, dana saninta
baya jingine da auren Kabiru, kewar su da tayi
tafi komai yawa. Hannu ta dago ta share kwallar
da ta riga ta gangaro mata, ta dan juyar da kanta
ta kalli Kabiru da yake tsaye, idanuwan shi
akanta, kamar zubar hawayenta yake jira yagani
su bashi izinin karasowa yayi irin zaman da tayi
a gefenta, cikin son nuna mata yanda ba zai taba
barinta ita kadai ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 566
A tsayin zamansu, tun tana jiran ranar da
Kabiru zai nuna mata halinsu na maza da akafi
yi musu tambari dashi harta daina, tun tana
jiran alhakin bijirewa iyaye ya kamata ta
wannan fanni saida ta daina, ba zatace basu taba
fada ba, za dai tace a kowanne lokaci laifin nata
ne, zata kuma ce na rana daya Kabiru bai taba
biye mata ba, karshen abinda zaiyi ya nuna mata
ranshi ya baci shine ya saka takalman shi ya bar
mata gidan, da zuciyar shi tayi sanyi idan ya
dawo bayan sallama, lokutta da dama yakan
dora da
"Kin huce in shigo? Ko in har yanzun bakya son
ganina?"
Wasu ranakun kuma
"Yunwa nakeji Yelwa, in shigo ki taimaka ki bani
abinci ko fushin bai bari kin girka mana ba?"
Mazan da ta sani a rayuwarta basu da yawa, a
tsakanin kawaici irin ma Hammadi da sanyin
hali na Bukar, zatace Kabiru ya hada duka ya
kara da wasu halayen nagartattu. Zai wahala
kaga fuskar shi babu wannan murmushin da
kyallin shi yake haskawa har cikin kananun
Lubna sufyan
Hausabook.com 567
idanuwan shi. Shisa a hankali ya koya mata
kwantar da hankalinta, natsuwar da yake tare
da ita kullum tayi mata inuwa harta mike
kafafuwanta, saboda ta dauka kalubalen su daga
bangarenta ne kawai kuma sunyo masa nisa.
Tunda da sana'arshi ta fitar da dabbobi suka
dogara, tafiye-tafiyen shi basu taba damunta ba.
Ta hadu da nagartattun makotan da ko a barin
da tayi na farko da Kabiru baya nan bataji
rashin yan uwa a kusa da ita ba, sunyi mata
taimakon da sai da yasa ta hawaye saboda
batayi tsammanin a zaman su tayi musu wani
abu da ta cancanci wannan karamcin ba. Sai dai
mutanen arziki ba sunayi maka kirki bane dan
kayi musu, karamcin ne cike da zuciyar su shisa
rarrabashi baya taba yi musu wahala. A kowacce
tafiya idan zaiyi tana ganin damuwar nisan da
zaiyi mata cike da idanuwan shi
"Ina ta duba garin da masu irin sana'ata basu
yawaita ba mu koma, bana son yanda nake
barinki ke kadai"
Ya fadi kamar a lokacin yasan wannan tafiyar
tashi zata zama sanadi na farko na jirkicewar
Lubna sufyan
Hausabook.com 568
lamurran su. Murmushin da tayi masa cike yake
da kokarinta na karfafar shi. Bata hango
tsakanin wannan murmushin nata da wani
akwai wata tazara mai nisa ba, sai dai satika
hudun da yakanyi duk idan yayi tafiya suka
shige babu amon shi balle kuma labari, sai ta
daina lissafi da kwanaki lokacin daya hada
watanni uku, cikin jikinta kuma ya shiga watan
da lissafi ya nuna cewa yana gab da fitowa
duniya.
Sauran lissafin da take tare dashi ya karasa
kwacewa ne ranar da ta fito daga bayi tana
kokarin zama dan daura alwala wata mata ta
shigo mata gida babu ko sallama tana kallonta
da fadin
"Yelwa ko?"
Tana da yakinin mamakinta ya bayyana akan
fuskarta
"Baki sanni ba nasani, matar Kabiru ce"
Abinda yayi saura na zuciyarta da baya tare da
Kabiru taji yana barazanar fitowa daga kirjinta
Lubna sufyan
Hausabook.com 569
"Kin dauka kinyi nasarar rabamu zakiyi rayuwa
dashi ke kadai ne? Ke kin isa yayi mun saki uku
ke ki rayu dashi? Waye ubanki?"
Kafafuwanta Yelwa taji suna rawa wannan karin
"Ki nemarwa cikin jikinki uba idan rabon shine
ya hada hanyarku, amman in dai Kabiru ne, ni
kuma ina da sauran numfashi yanda nabar shi
ya barki kenan. Na so in barki ki cigaba da
duban hanya, amman ina son kallon idanuwanki
ne kamar yanda nake son kiga fuskata"
Ko da ta fita bayan
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Da ta furta wani zazzabine ya danneta, kafin
tashin hankali ya fara barazana da rayuwarta.
Ba kirga kwanaki takeyi ba ballantana a lokacin
tasan kwana nawa ta hada kafin tunanin
komawa Marake ya dirar mata, ta dai san in tayi
numfashi sai abinda yake cikinta ya motsa mata
kamar yana tuna mata da yanda take wata
rayuwa a tsakanin duniya da lahira. Sai wani
sabon firgici ya sake danneta akan wanda take
ciki. A wajen Kabiru ta koyi rubutu da karatun
Lubna sufyan
Hausabook.com 570
hausa tunda gatan da Datti ya nuna musu bai
barsu sunyi karatun ba duk kuwa yanda Dije
taso su dashi, haka kawai safiyar data tashi da
nufin tafiya Marake wani abu yake fada mata ba
zata rayu da abinda yake cikinta ba, wannan
abin na sake tabbatar mata da macece, a lokaci
daya kuma yana sakata rubuta wasikar da bata
da yakinin zata isa inda take son isar da ita.
Sai dai ganin Datti a kwance ya kara birkita
mata komai, daren nan da ta kasa mantawa har
yau na dawo mata, muryar shi bayan ta roke shi
daya yafe mata, raunin da yake cikin muryar
lokacin daya furta
"Soyayyar da nayi muku laifi ce Yelwa? Me yasa
kuka kasa gane kune gabaki daya duniyata? Ko
dan nima ban kara tabbatar da hakan ba sai da
kuka zabi kuyi mun nisa naga fadinta? Na jini ni
kadai? Komai ya tsayamun yana sakani tunanin
inda na kuskure a tawa soyayyar..."
Ya karasa muryarshi na karyewa tare da wani
abu a zuciyarta
"Na yafe miki..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 571
Hawayenta suka zubo
"Zuciyata na ciwo, sosai..."
Kai ta daga hawayenta na zubowa, tasan itace
silar komai, saita dauka tunda ta tafine ya
kwanta ciwo, ta bude bakinta da nufin sake
rokon shi ya yafe mata sai yaja wani irin
numfashi da bataji ya fitar dashi ba, kafin
zuciyarta ta buga tare da bayanta daya amsa
"Kin kashe shi"
Wata murya ta fada mata a cikin kanta. Kuma ko
da ta fadawa Daada ta kashe shi a lokacin batayi
kokarin musa mata ba. Ta san ta haihu, saboda
ko mahaukaciya ta san da, balle kuma ita da ta
haihu cikin hayyacinta. Zata tuna wankan da
Daada tayi mata, kayan da ta saka mata,
yarinyar da ta damka mata a hannunta don ta
shayar da ita. A cikin wannan firgicin ne wani
irin abu ya tsirga mata daya sakata ajiye
yarinyar tana mikewa tsaye. Wannan abin daya
tsirga mata shine yake tunkudar zuciyarta da
wani irin karfi daya shallake ikonta. Ko yarinyar
da kukanta ya isa kunnenta da wani yanayi
batayi tunani ba balle takalmi da mayafi, saboda
Lubna sufyan
Hausabook.com 572
abinda yake fisgarta yana gaya mata ta bi hanya
kawai.
Hanyar kuwa tabi, hanyoyin da ba zata iya gane
su ba, saboda ba'a cikin hankalinta take tafiyar
ba. Bata kuma san ko wani yayi nufin
taimakonta da abinci inta karba sai dai taci shi
tana tafiya saboda inta zauna sai taji wannan
abin yana fisgarta komin zugin da kafafuwanta
sukeyi mata na alamun gajiya. Kamar yanda
bata san ta shafe shekaru biyar a wata irin
duniya da ko makiyinta bata fatan ya shiga ciki.
Kafin wata safiyar juma'a data canza mata
komai, tana tafiya kawai ta tsinci kanta a gefen
titi kamar wadda take yawo a mafarki saboda
karshen abinda zata tuna shine ta haihu, shine
tana cikin dakin Datti, sai kuma rasuwar shi, sai
ta ganta a gefen titi a tsaye, kafafuwanta babu ko
takalmi cikin wani yanayi daya nuna
gararambar da ta sha.
Haka kuma bata san cewa a wannan juma'ar ake
taron suna a wani gida, a daya daga cikin
sababbin unguwanni masu tasowa a lokacin a
garin Kano, sanadin wannan sunan da za'ayi sun
kira me majalisi don shagali a kofar gida, katon
Lubna sufyan
Hausabook.com 573
dutsen da tunda suka siyi filin, har akayi gini
yana nan gefe, samari suka taru suka saka karfi
wajen mirgina shi don a kara samun wajen da
mutane zasu tsaya su kalli majalisin da za'ayi, a
kasan dutsen kuma suka ga katuwar layar da
basu tsaya dogon tunani ba suka warwareta,
daya a ciki ya bada shawarar a kone zaren da
layar duka, suna jinjina neman duniya irin na
mutane, da kuma tunanin wa akayiwa wannan
mugun abin aka danne da wannan dutsen da
Allah kadai yasan shekarun da yayi a wajen.
Da yake Allah ya yanke mata wahala, sai sanadin
samun saukinta ya biyo ta hannun mutanen da
ko a titi zai wahala kaddara ta hadasu balle tayi
tunanin gode musu. Da taimakon mutanen
kauyen da take gararamba aka dorata a motar
Kano, da tambaya da komai ta gabo Bachirawa,
unguwar da gidansu yake, unguwar da taga ta
canza mata gabaki daya saboda gine-ginen da
akayi, da wata tambayar da taimakon Malam
Malami mai almajirai da suke layi daya a
wancen lokacin ta gano gidanta, gidansu ita da
Kabiru. Harta karasa ta kwankwasa kofar gidan
Lubna sufyan
Hausabook.com 574
batayi tunanin za'a bude ba, har yau kuma ba
zata manta yanayin fuskar Kabiru ba.
Ba zata manta yanda bai iya ce mata komai ba
sai hannunta daya kama yana janta zuwa
jikinshi yayi mata wani riko tamkar an mishi
alkawari karuwar kwanakin shi a duniya idan
ya riketa. Haka ba zata manta dumin hawayen
shi da suka sauka akan kafadarta ba. Sun kwana
a gidan, shi yana da labarin bayarwa, ya fada
mata yana son dawowa gida amman saiya kasa,
da yayi yunkuri sai yaga wani duhu da tunanin
shi na dawowa gida yake bacewa a ciki, abokin
cinikayyar shine ya kula da hakan, ya kuma
tsaya kai da fata wajen karbo mishi taimako
wajen wani Malami har abin ya karye, sai dai
daya dawo ya nemeta bai ganta ba saiya koma,
ya nemi abokin shi inda cikin rashin sa'a suka
tarar Allah ya amshi rayuwar Malamin, zargin
abinda ya same shi shiya sameta yasa shi bin
duk wani Malami da zaici karo dashi wajen
neman ya taimaka masa da addu'a akanta,
amman karshen abin baizo ba.
Ya koma Marake kuma, labari ya samu na taje
can, harta haihu, sai dai babu wanda yasan inda
Lubna sufyan
Hausabook.com 575
take daga nan, haka ma su Daada, a 'yan uwanta
yaji labarin Yelwa data haihu ta gudu ne saboda
abin kunya, Daadar ma saita kasa zama, anman
anfi kyautata zaton Kano ta gudu inda Julde
yake da zama. Wani zance daya daki zuciyar shi,
bakinshi yayi masa nauyi wajen fada musu
abinda Yelwa ta haifa ba ta hanyar da suke
tunani bane ba, saboda idan ya fada wacce
shaida zaiyi amfani da ita wajen gamsar dasu
gaskiyar shi? Daya dawo Kano saiya rasa gabas
zaiyi ko arewa, garin Kano da girma, ta ina zai
fara neman su Daada? Idan ya gansu kuma bai
samu Yelwa a tare dasu ba ya zaice? Wanne
labari zai basu? Ya gudo musu da yarinya ta
kuma bace a karkashin kulawar shi?
A cikin labaran shi duka da ido Yelwa ta dinga
binshi, saboda ita bata da labarin bashi, yasan ta
haihu, yasan mace ta haifa, yasan mahaifinta ya
rasu. Ina taje? Me yasa ta tafi? Me takeyi a
wannan shekaru biyar din duka bata sani ba,
mahaukaci koya warke bashi da labarin
bayarwa tunda hankalin da zai rike faruwar
abubuwan ne gabaki daya ya kubce masa. Ta dai
fada masa tsohuwar matarshi tazo, ta kuma fada
Lubna sufyan
Hausabook.com 576
masa maganganun da tayi mata wanda har yau
suke mata yawo
"Sahura?"
Ya tambaya da mamaki shimfide a fuskar shi,
ranar taji sunanta, sunan da bata so ta sakeji ko
a mafarki. Sun sake kwana a garin Kano, sai dai
Kabiru ya tsorata, shisa suka bar Kano
"Fadan nan ya wuce ayi cacar baki, ko a ware aji
karfin juna Yelwa, fadan da Sahura ta dauka
damu fadane da in ba imaninmu zamuyi nisa
dashi ba Allah yana iya sake bata nasara
akanmu dan ya sake jaraba mu, gara muyiwa
Kano nisa, muyi nisan da sai dai a buga kasa a
bata labarin mu wanda zai iya zama gaibu za'a
gaya mata, idan wani abin ya sake samun ki ba
zan iya yafewa kaina ba"
Yanda ya karasa maganar, ramar da tagani a
tare dashi da yanayin da yake cikin idanuwan
shine abinda yayi galaba akanta ta bishi, bayan
tarin alkawurran da yayi mata na cigaba da
neman ahalinta da kuma alkawarin yanda ya
rabota dasu zai sake sadata dasu cikin hukuncin
Ubangiji. Sai gashi ya cika mata wannan
Lubna sufyan
Hausabook.com 577
alkawarin a lokacin data cire rai da samuwar
hakan. Dan har suka hawo mota jinta takeyi
kamar a cikin mafarki take yawo, mafarkin da
bata farka ba sai yanzun da ta ganta a gaban
Daada, sai yanzun da taji hannun Daada rike da
nata. Sai ta dan karkata kai tana kallon Madina
da ta zuba mata ido ta cikin gilashin da yake
makale da fuskarta.
Yarinyarta
Yarinyar da rabonta yasa ta tsallake komai a
karo na farko
Yarinyar da ta haifa kaddara ta sata tsallaketa
tare da komai a karo na biyu
Sai wani abu ya tsirga mata, ta sake kallon
Daada da tambayar da bata iya furtawa ba,
Daada ta daga mata kai kamar ta karanci
tambayar
"Madina..."
Daada ta furta muryarta a sarke saboda kukan
da yake son kwace mata, sai Yelwa ta rigata,
saboda bayan hawaye sun zubo mata, da taja
Lubna sufyan
Hausabook.com 578
numfashi tazo saukewa saiya taho da wata irin
shessheka da ta kasa dannewa
Tunda yake bai taba tunanin shan wani abu ba
sai a sati dayan nan, idan yana cikin yanayi irin
wannan Madina ce kawai yake gani yaji komai
ya dan lafa masa, to yanzun abinda yake ji yana
da alaka da ita. Ashe da yayi tunanin ya san
girman son da yakeyi mata karya yayiwa kanshi,
ko da yaga ya kusan rasata bai shiga rudani irin
na kwanakin nan ba, idanuwanta ne abu na
karshe da yake gani cikin kanshi kafin ya samu
bacci, haka daya bude ido dasu yake fara
sallama, ba dan bai taba ganinsu cike da
abubuwa da yawa ba, tunda tana da idanuwan
da zasu iya baka labarai kala-kala akanta idan
ka natsu cikin kallon su, ba tare data bude
bakinta ba, amman ranar ta dago ta kalle shi,
tayi masa kallon da bata taba yi masa irin shi ba,
ta kalle shi da wani kyalli da shine karo na farko
daya fara ganinshi cikin idanuwan nata.
Ta kalle shi kamar duka fatanta yana karkashin
kafafuwan shi, sai yaji wani abu daya girmi ace
Lubna sufyan
Hausabook.com 579
tsikar jikinshi ce tana tashi, ko yayi musu
sallama ba zai tuna ba, ya dai bar dakin, ya saka
takalman shi yaja kafafuwanshi zuwa motar shi,
inda yana zama ruwane abinda ya fara nema ya
jika makoshin da yakejin ya bushe masa
"Yarinya ce Salim, ko shekaru sha takwas bata
karasa ba, yarinya ce, get a grip"
Yake fada yana sake maimaitawa kanshi, a
lokaci daya kuma yana so ya tuna ma kanshi bai
kamata ace yarinya kamarta bace take neman
susuta shi haka. Shisa ya dauke kafarshi, ya bata
tazara ta gama karbar dawowar itayenta, tayi
musu duk wata tambaya data jima tana
adanawa a cikin zuciyarta. Yanda ta kalle shi
kamar babu wani abu da zai tambayeta da zata
kasa yi masa ya bashi tsoro, ya girgiza wajajen
da baisan da zaman su ba a cikin zuciyar shi. Ko
zata karbi soyayyar shi daya mika mata bayaso
tazo ta haka, bayaso ta karbeshi saboda ya zama
sanadin dawowar iyayenta, idan zata karbeshi
yana so ta karbeshi saboda shine zabinta.
Amman sai tazarar take taba shi fiye da yanda
yayi zato. Sai ya zamana kamar komai na
Lubna sufyan
Hausabook.com 580
rayuwarshi ya yanke shawarar tuna masa ita, ko
a asibiti duk wasu marassa lafiya da suke
karkashin kulawar shi a satin, suna dauke ne da
cututttukan da suka tattauna akai shi da
Madina, yana duba su komai na hirarrakin na
dawo masa, kewarta da son ganinta na kara
nukurkusar shi. Kwanan shi na hudu kenan a
asibiti, anan yake wuni kuma. Abinci ma sai dai
yayi order a kawo masa har cikin asibitin,
turawa yakanyi saboda, abincin kanshi yana
kara tuna masa da cewar alkawarin da yayi
mata na ba zai dinga zama da yunwa ba, ko da
bayaji ma idan har yasan jikinshi na bukatar
abinci ko kadanne zaiyi kokarin ganin yaci.
Sai gashi ta fara kutsowa har cikin baccin shi
tana sakashi farkawa babu adadi a duk wani
bacci da zaiyi na dare ko na rana. Ranar kwana
na takwas dinne kiran Nawfal ya shigo wayarshi
ya daga batare da yace komai ba
"Zaka dawo gida da kanka ko in kwaso kowa
muzo asibitin su tayani dauko ka?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 581
Hannu yakai yana murza goshin shi, ta inda
yakejin alamun ciwon kan dake neman wajen
zama
"Bajjo"
Ya kira, muryarshi na fitowa da gajiyar da baiso
ba
"Mu taho din kenan"
Halayenshi basu taba hana duka kannen shi
tsokanar shi ba, amman a cikinsu babu wanda
yake iya sakashi yin abinda bai niyya ba kamar
Nawfal, saboda ko me zaiyi ma Nawfal din sai
dai yayi, amman abinda yace zaiyi ba zai fasa ba.
Kowa din ba zai wuce Khalid ba, in kuma za'a
hada Nawfal da irin Khalid biyar ba zasu iya
daukar shi ba. Sai dai bayason kure Nawfal din,
bayason yaga shi da Khalid dinne kawai zasu zo
ko kuwa harda wasu zai gayyato suyi masa
hayaniyar da bashida wajen daukarta.
"Ba zaka iya numfashi a hankali bane?"
Salim ya fadi yana janye wayar daga kunnen shi,
shisa yake amsa waya a speaker, saboda ya tsani
yanajin wannan numfarfashin cikin kunnen shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 582
"Ya zanyi numfashi a hankali Hamma?"
Kara hade girarshi Salim yayi kamar Nawfal din
yana ganin shi sannan yace
"Ban sani ba, karar numfashin yana shigarmun
kunne"
Ya karasa yana saka kiran a speaker ya ajiye
wayar kan teburin da yake gabanshi
"Karar numfashi? Kasan me? Ba kira nayi muyi
maganar nan ba, mu zo?"
Wannan karin numfashi Salim ya sauke
"Zan dawo gida anjima"
Ko da baya ganin Nawfal yasan kai yake
jinjinawa
"Idan baka dawo ba zamu zo"
Bai amsa ba ya kashe wayar. Bai fita daga
asibitin ba sai bayan la'asar, daya fito daga
masallacin saiya nufi motar shi, duk da hargitsin
da yake ciki akwai wata natsuwa ta daban da
koya taba saninta toya manta haka take, duk
lokacin da zai shiga masallaci ayi sallah dashi a
Lubna sufyan
Hausabook.com 583
jam'i akan lokacinta sai yaji kamar an diga masa
haske a duhun da bai taba sanin yana tare da
zuciyarshi ba. Ba kamar lokacin da inya hada
salloli ya idar zaiji wani irin nauyi ya danne
masa zuciyar ba, yanzun sakat yake jinta ta
wannan fannin, sai tarin zunuban da yake rokon
yafiyar Allah akansu cike da wata kunya marar
misaltuwa.
Kunya hadi da tsoro saboda yaga maikon da
zina take dashi, yaga yanda take da karfin
ruguza abubuwa da yawa, a duniya kenan, ko
anan din bashida kafafuwan tsayawa a gaban
makusantan shi idan daudar zunuban shi ta
bayyana, sai yanzun tsoro ko yace firgici yake
shigarshi, nauyin zunubanshi nayi masa rumfa
"Astagfirullah..."
Ya furta a kasan numfashin shi yana murza
mukullin motar ya tasheta, a kasan duk wannan
firgicin baya manta Allah Mai yawan Gafara ne,
Mai yawan Rahma. Yana fita titi wayarshi nayin
kara alamar shigowar kira, harya shirya zagin
da zai watsawa Nawfal idan ya daga sai
zuciyarshi tayo wani zullo kamar tana son
Lubna sufyan
Hausabook.com 584
fitowa ta daga kiran da kanta ganin Madina ce,
yana karawa a kunnen shi kafin yace wani abu
ta rigashi da fadin
"Hamma..."
Kuma baisan ko zuciyarshi bace take kitsa mishi
abinda su duka suke sonji, kamar akwai
kewarshi a muryarta, a yanayin yanda ta
kirashin
"Kina ina?"
Ya tambaya saboda ba zai iya sake kwana bai
sakata a idanuwan shi ba
"Ina gida"
Ta amsa a takaice, kai ya jinjina kamar tana
ganin shi ya sauke wayar daga kunnenshi yana
katse kiran daga bangarenshi, kafin ya mike
yana shan U-turn ya koma hanyar da zata
hadashi da gidan Daada. Yana parking din motar
shi yana jinta tana kwankwasa gilashin motar
kamar tana kofar gida tana jiranshi, daga inda
yake ya fara kallonta. Rigace mai hula a jikinta,
ta saka hannunta daya a cikin aljihun rigar,
dayan tana kwankwasa masa kofa, akwai wata
Lubna sufyan
Hausabook.com 585
hular ta sanyi fara kal a saman kanta, sai kuma
taja ta rigar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 27