ne yanda zai rufeni
da fada..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 24
Wannan karin da kwalla cikin idanuwan ta da
alamar kukan dake son kwace mata a muryarta
ta karasa maganar. Abinda Dije bata sani ba
shine daga Abu har Hammadi sun kula da
kaunar da Datti yake yiwa Julde gurguwar
kauna ce, duk da ita Abu ta mishi uzuri da yanda
kaddara ta zo mishi akan haihuwa
"Dan ya samu basu zauna bane a baya shisa, ana
kara haifar masa wani zakaga ya rage..."
Ta ce ma Hammadi da yayi mata magana ranar
da Julde yayi bacci a gidan su, amman Datti yayi
sallama yana shiga har ciki ya sabi dan shi a
kafada yayi musu bankwana ya tafi. Ba shi bane
na farko, ranar ne dai Hammadi yayi magana, ita
kanta Abu ranar farko ranta ya sosu, har kuka
tayi duk da ta nuna ma Hammadi abin bai taba
zuciyar ta ba. Rashin da akwai ciwo, kaddara ce
kuma da sai mai juriya ne yake iya karbarta da
hannu biyu. Kome wani zaiyi maka akan yaro
sai kaji tamkar yana goranta maka rashin
samun naka rabon ne da bakayi ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 25
"Bamu samu ba har yanzun Abu, amman kina
hango zakiyi abinda Datti yakeyi akan Julde
idan Allah ya bamu rabo?"
Dariya tayi, tsakanin yan uwa sai Allah, ita
matar Hammadi ce, idan yau kaddarar rabuwa
ta gifta musu ko a lahira sai in suna da hakkin
juna ne zasu hada hanya tunda babu yaran da
zasu hada su, amman shi da Datti har abada
zasu kasance yan uwa, kuma tarin kaunar da
yake mata ba zata kama kafar wanda yakewa
dan uwan shi ba, tana kokarin kiyaye harshenta
daga furta wani abu marar kyau daya dangancin
Datti, ko da kuwa wannan abin halin shine, kai
ko da ma ace a hirane irin wannan da sukeyi,
idan Hammadi ya huce ya tauna zantukan nata
ran shi zai iya sosuwa, a kasan zuciyar shi zaiji
haushin ta
"Kar dai mu cika baki kan abin da bai faru ba
tukunna"
Murmushi Hammadi yayi
"Ai shikenan, ba dai kyason in fadi laifin Datti"
Lubna sufyan
Hausabook.com 26
Dariya ta sakeyi tana kawo mishi wata hirar da
zata kore wadda suka gama. Amman ba ranar
kadai bane ya furta damuwar shi akan
makauniyar kaunar da Datti yake nuna ma
Julde.
"Nasan kina hakuri, zance ki kara hakuri ne
Dije, watakila dan yana ganin Julden ne kawai a
gaban shi yanzun...idan Allah ya kara kawo
muku wani rabon zaki ga ya rage"
Murmushin da Dije tayi mai ciwo ne
"Idan kuma shi kadai ne rabon fa?"
Maganar ta taba Abu har zuciyar ta
"Sai kiyi addu'a, komai zai tafi dai-dai... Idan
baya nan yayi kuskure kiyi kokarin nuna
masa...shima Dattin ki fahimtar da shi illolin
dake cikin tasowar yaro babu kwaba..."
Murmushin dai Dije ta sake yi tana furta
"Hmmn..."
Saboda bata da kalaman da zata fara amfani da
su wajen fada ma Abu cewa Datti baya cikin
jerin mazan da zaku zauna kuyi magana ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 27
fahimta da shi, ba irin Hammadi bane ba, bashi
da lokacin da zai saurare ta, komin
muhimmancin shawarar da take da ita kuwa. Ta
jima da gane wannan, bai daina yi mata ciwo
bane ba duk idan ta tuna, shima ta san lokaci zai
koya mata sabawa da hakan. Safiyar ranar tun
da ta tashi take jin ta wani iri, komai baya mata
dadi, dakyar tayi wanke-wanke bayan fitar
Datti, ta share gidan. Julde ma wajen Abu ta tura
shi tasan zatayi mishi wanka acan. Ta koma ta
kwanta, bata tashi ba sai azahar, sai kuma
lokacin tayi wanka.
Tun lokacin ta hada wuta tana dora tuwon dare
takan jima in ba taji marmarin wani abu ba bata
dora girkin rana ba, sai dai ta shiga gidan Abu su
dafa acan, tunda nan Hammadi yake aikowa a
karbar musu abincin rana shi da Dattin. Dakyar
kuwa ta karasa girkin, sai da tayi dana sanin
dora shi bayan tayi talge, taji daman ta cewa
Abu ta saka abincin dare da su. Ta so sake watsa
ruwa gab da Magriba sai ta gujewa camfin cewa
wankan yammaci likis na saka zazzabi, tunda
daman ba dadin jikinta take ji ba. Ta fito bayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 28
kenan tana daura alwala Julde ya shigo da gudu
yana fadawa bayanta
"Daada na ci nama, Nenne ta bani nama"
Yake fadi cikin yaren fulatanci, yana kiran Abu
da Nenne kamar yanda ta koya mishi. Itama ta
taso mahaifiyar ta na yara musu a gida, amman
basu cika mayarwa ba tunda hausa tafi karfi a
cikin gidan. Zama da Julde dole yasa fulatancin
nata kara gogewa saboda yakan yi kwanaki bai
furta kalma guda daya da hausa ba, yana da
kishin yaren shi na ban mamaki. Kuma yana
mata fada idan yaji tana ma Julden hausa, in
baya nan kuwa takan yi mishi saboda nata
dangin bakowa yake jin fulatanci ba, kuma
hausar itace yaren mahaifinta, idan akabi ta
silsila ita bahaushiya ce, bata ga dalilin da za'a
haramta mata koyawa danta yaren ta ba.
"Ta kyauta, kace mata ka gode? Daga mun
baya..."
Sake kwanciya yayi a bayanta don tana
tsugunne ne, da ta idar da alwalar ma da shi ta
mike saboda ya zagaya hannuwan shi ya makale
mata wuya, ta samu ta sauke shi yana neman
Lubna sufyan
Hausabook.com 29
saka mata kukan sangartar daya saba. In ka
shigo gidan su daga soro katon tsakar gida zaka
fara samu da aka shafe da sumuntin da sai
gidajen wanda yaci ya tayar da kaine zaka samu
da shafen sumunti a cikin kauyen. Dan Datti da
yake bata labari yace a cikin garin Katsina ya
aika aka siyo sumuntin da ana ginin gidan,
amman kamar sauran gine-ginen kauyen nasu
ma na kasa ne, sai dakuna guda hudu, cikon na
biyar din kayan abincine ake ajiyewa, bayi, sai
dan karamin daki da aka rufe daya zama wajen
girki da inda take ajiye kwanoni, idan bama ana
damuna ba, a bakin kofar take ajiye murhun,
nan take girkin ta.
Daki biyu ma zata ce suna amfani da shi, nata sai
kuma na Datti, sauran akwai ledar daki a ciki da
katifu da Datti ne ya siya ya saka, amman in ba
ta shiga ta share ba, ba zama takeyi a ciki ba.
Dakinta ta nufa da Julde da yake biye da ita,
ganin ta shimfida darduma ta dauki hijabi ta
tayar da sallah yasa shi hayewa kan gadon
karfenta da yake cikin dakin ya kwanta, lokacin
da ta idar har yayi bacci, ta dan jima a zaune
tana rasa abinda yake damun ta, ba zatace
Lubna sufyan
Hausabook.com 30
rashin lafiya takeyi ba, zuciyarta take ji a
cunkushe. Tana nan zaunen dai har akayi isha'i
ta tashi ta gabatar da tata. Ta mike ta ninke
dardumarta, ta cire hijabin tana ninkewa ta
hada ta rataye su jikin karfen gadon tana fita
tsakar gida.
Tasan inda duk Datti yake yana hanyar gida, da
yakan dade bai shigo ba, ko da ta juyo muryar
Hammadi shi saiya kara jimawa kafin ta gan shi,
zai zo mata da labaran da suke tabbatar mata da
ya tsaya hira ne. Amman tun da ta haifi Julde
rabon da yayi wannan dadewar, duk da lokutta
da yawa idan ya dawo Julden yayi bacci, haka zai
dauke shi ya kwantar kan cinya, tun tana
magana idan zaici abinci daya ajiye shi har ta
koyi saka masa ido in dai akan lamarin Julde ne.
Kofi ta dauko ta dauraye saboda ta rigada ta
saba dan gudun ko wani abu ya shiga ciki,
musamman kananun kwari da kifewar da tayi
ba zai hanasu samun hanyar shiga suyi bidiri a
cikin kofin ba.
Ta bude randar da take tsakar gidan ta saka
kofin a ciki ta dibo ruwan tana kaiwa bakinta,
dai-dai lokacin da taji kamar an jeho wani abu,
Lubna sufyan
Hausabook.com 31
kafin wani irin gigitaccen kuka da Julde ya saki
ya sata yadda kofin tana nufar daki ciki hanzari,
da yake akwai hasken fitilar kwai a cikin dakin,
batayi wahala ba wajen ganin fadowa Julden
yayi daga kan gado, cikin rawar jiki ta karasa
tana daga shi, tako yi karo da jinin da yake fita
daga bakin shi da ya sa hanjin cikinta
yamutsawa. Cike da zafin nama ta dauke shi
tana karasawa ta dauko fitilar kwan tayo waje,
gurin magudaji ta nufa da shi ta tsugunnar,
kukan da yake da jinin dayaki tsayawa na
haduwa suka kara gigitata.
Dakyar ta samu ta dauko buta ta fara wanke
mishi bakin, tana dubawa taga wani irin rami a
leben shi daga ciki kamar hakorin shi ya datsa a
jiki, har harshen shi yanka ne, leben kuwa ta
ciki da waje, jini gullama yake fita kamar ba
wankewa takeyi ba, bata taba ganin tashin
hankali irin wannan ba, haka tunanin ta yake
fada mata kafin Datti ya shigo gidan yana fadin
"Me ya faru Dije? Me ya same shi?"
Cikin fulatancin shi da yake fita daki-daki kamar
don harshen shi kawai aka kirkiri yaren, yana
Lubna sufyan
Hausabook.com 32
karasawo yaga kalar jinin da yake zuba fisge shi
yayi daga hannun ta yana daga shi zuwa jikin shi
hadi da duba shi sosai, kukan nashi ya fara
tsagaitawa, sai ajiyar zuciya da yake saukewa,
jikin shi harya dauki dumi saboda azaba.
"Me ya same shi wai?"
Ya sake tambaya yana saka idanuwan shi cikin
nata
"Fadowa yayi daga kan gado yana bacci"
Sai da Datti ya sake duba Julde da jini har
lokacin bai daina fitowa daga bakin shi ba
sannan ya sake kallon ta, wannan karin kallon
na sa wani abu ya tsirga a cikin ta
"Na dauka nace in dai ba zaki zauna ki tsare shi
ba karki sake dora mun yaro kan gado?"
Kai Dije ta jinjina mishi
"Yanzun ma fitowa kawai na danyi...ka..."
Bai bari ta karasa ba ya katse ta
"Ban isa ba kenan ko? Ban isa ba shisa kika bar
mun yaro shi kadai..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 33
Idanuwanta ta sauke daga cikin nashi tana
neman danne bacin ran daya taso mata, sai dai
kamar ta dora shine akan wanda tayi shekaru
tana hadiyewa, sam sai taji shi tsaye a makoshin
ta har tana jin dandanon shi kan harshen ta,
musamman daya cigaba da fada yana hargowa
kamar Julden ba daga jikin ta ya fito ba
"Watanni tara da kwana goma sha bakwai..."
Ta furta da nisantaccen yanayi a muryar ta tana
dagowa ta saka idanuwan ta cikin na shi
"Kwanakin da yaron nan yayi a cikina, ba zan
rantse ba amman babu wata shakuwa da zakaji
kayi da shi da zata kamo iya wannan lokacin..
Me yasa? Me yasa kullum kake nuna mun kamar
kafi ni son shi? Kamar ni ban iya kula da shi ba?"
Fuskar shi bata boye mamakin da ya cika
zuciyar shi ba, bai taba fada ta mayar mishi ba,
balle harta dankara mishi magana haka. Da
yawa zasu ce yau daya ya kamata ya kauda kai,
amman shi ba kamar sauran maza bane ba, tun
kafin ya san menene aure ya rigada ya hasaso
babu macen da zai aura da ta isa tana karkashin
shi yana fada tana mayarwa, duk a fadin duniyar
Lubna sufyan
Hausabook.com 34
shi a yanzun babu wannan macen. Shisa bacin
ran shi ya ninku har wani jan haske ya gani ya
gilma ta cikin idanuwan shi.
Daga Datti har Dije idan wani zai tsare su yace
su maimaita maganganun da suka fada ma juna
ba zasu iya ba, ita dai zata rantse a cikin fadan
akwai inda ya fadi
"Nayi dana sanin auren ki"
Shi kuma zai rantse tace mishi
"Idan ka haifu ka sawwake mun mana ka huta,
auren naka ka dauka jin dadin shi nakeyi?"
Sai dai kowa a cikin su hanyar da zaibi a goyi da
bayan shi yake nema, ko lokacin daya daga
hannu yana marin ta, ya manta ma Julde na rike
a hannun shi, haka lokacin da ya furta
"Kije na sakeki saki uku! Ki barmun gida da
yaro kiga idan ba zan iya kula da shi fiye dake
ba"
Kafin hawayen da suke cikin idanuwanta su
zubo wani irin yanayi da ya girmi dana sani ya
rufe shi kamar bargo, shirun daya biyo bayan
Lubna sufyan
Hausabook.com 35
kalmomin nashi na gauraye gabaki daya gidan
har yana jin takun Dije cikin kunnuwan shi
lokacin da ta juya tana nufar dakin ta. Kamar
wanda aka dasa haka ya tsinci kan shi da kasa
motsawa har ta fito da lullubi tana saka
takalman ta, baiyi yunkurin hanata ba, duk
kuwa da ihun da zuciyar shi take mishi, da
idanuwan ya bita harta fice daga cikin gidan. Sai
lokacin kafafuwan shi suka motsa yana bin
bayanta, hannun riga sukayi, tayi dama inda zai
sadata da gidan su, shikuma yayi haggu yana
shiga gidan Hammadi babu ko sallama
"Datti...lafiya dai ko?"
Hammadi ya tambaya don suna zaune a tsakar
gida ne kan tabarma, sun saka fitilar kwai a
gaba saboda abu da take kokarin saka zare a
cikin allura tana son dinke rigar Julden da bata
san yanda akayi ya warware dinkin ba daga
gefe, shikuma Hammadi yana mata dariyar tsufa
ya kamata ganin ya fara ja da baya, zata mayar
mishi da martani kenan Datti ya fado musu,
tama riga Hammadi mikewa tana karasawa ta
karbi Julde da yayi luf a kafadar Datti, baiyi
musu ba ya mika mata yaron, salatin ta na isa
Lubna sufyan
Hausabook.com 36
kunnen shi da wani irin nisa saboda yanda yake
ji
"Na saki Dije... Hamma na sake ta"
Ya fadi kamar wanda maganar take ba mamaki.
Saboda jin shi yake kamar yana yawo saman
iska
"Bangane ka saki Dije ba, me tayi maka? Me ya
faru?"
Hammadi ya jera mishi tambayoyin cikin tashin
hankali da mamaki, dan Abu ma maganar taji ta
dake ta, kan tabarma ta ajiye Julde tana kallon
Datti tana jiran karin bayani
"Fada muke yi, bansan ya akayi ba, kawai na
sake ta"
Numfashi Hammadi yaja yana sakin shi tare da
fadin
"Inalillahi wa ilaihi raji'un... Datti kaga irin illar
zafin ran da nake guje maka ko?"
Shiru yayi, daga cikin jikin shi yake jin wani abu
yana tsirgawa da baisan yanda zai fara misalta
shi ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 37
"Ina Dijen yanzun?"
Cewar Hammadi
"Ta tafi gidan su..."
Takalma Hammadi ya zira
"Sai ka wuce muje ayi ma tufkar hanci tun yau"
Kai Datti ya girgiza mishi, baiyi wani ilimin
addini ba, amman yasan hukuncin saki uku a
musulunci
"Duka ne... Saki uku nayi mata"
Saida Hammadi ya dafa bangon wajen tukunna
ya iya komawa ya zauna, kafafuwan shi rawa
sukeyi da danyen aikin da Dattin yayi, a gefe
guda kuma zuciyar shi na hasaso mishi tarin
kunyar mahaifin Dije da zai kwasa, saki uku,
sakin tozarci, ba Dije kadai ba, har su ya tozarta
tunda bai duba girman da yake tsakanin su ya
nemi shawarar su ko suna da ta bayarwa wajen
bullowa lamarin ba kafin ya yanke hukunci.
"Ka kyauta Datti..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 38
Hammadi ya fadi muryar shi na rawa ya juya ya
kalli Abu da itama ta zauna, hawaye kawai ke
zubar mata, Dije ba mai yawan magana bace ba,
amman a cikin idanuwanta zaka iya karanta
damuwar da take boyewa a cikin zuciyar ta,
kowa kuma yasan halin Datti zai jinjina ma
kokarin da takeyi na zama da shi, tunda aure ya
girmi bayar da ci da sha, da kuma suttura, kana
bukatar samun kwanciyar hankali daga wajen
mijin ka. Amman rana daya Datti ya nuna mata
wannan hakurin nata ba abakin komai yake ba,
ita dinma bata da wani muhimmanci a rayuwar
shi, zai iya datse igiyoyin daya hadu zama inuwa
daya cikin kankanin lokaci.
"Zan dawo da ita, sai tayi wani aure in dawo da
ita"
A karo na farko da Hammadi ya kalle shi bacin
rai shimfide a idanuwan shi
"Me ka dauki mutane? Me ka dauki auren gabaki
dayan shi? Datti ka fitar mun daga gida wallahi
kafin inyi abinda mu duka zamuyi dana sanin
shi daga baya..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 39
Ganin da gaske Hammadi yake da kuma
kasancewar rana ta farko daya tabajin ya daga
murya sai jikin shi ya karayin sanyi. Juyawa yayi
ya fita batare da ko Julde ya dauka ba. Yabar
Hammadi da Abu suna jajanta danyen aikin da
yayi, kafin Abu ta iya mikewa dakyar tana tona
sauran garwashin daya rage cikin murhun da
tayi abinci dare ta dora dan ruwan zafi a cikin
tukunya a kai don ta gasa ma Julde bakin shi da
yaji ciwo. Tana ta kallon yaron yana bacci batare
da yasan abinda mahaifin shi yayi wa
mahaifiyar shi ba. Ta kuma kasa daina sharar
kwallar da take ta taruwa cikin idanuwan ta.
*
Kamar wasa kwanaki suka dinga wucewa har
Dije ta gama iddar ta, zuwa lokacin Datti yayi
zuwa yafi goma wajen ta, amman tana kin fitowa
ta saurare shi, har Abu yabi kan taje mishi
wajen ta ko zai samu ta fito ta saurari me zaice
"Ta ina zan fara hada idanuwa da ita in kawo
mata zance ka? Idan kai baka jin kunya ni ina ji"
Duka kowa ya juya mishi baya akan abinda ya
karba a matsayin kuskuren shi, ya dauka zaman
Lubna sufyan
Hausabook.com 40
aure ne kawai a tsakanin su da Dije, sai yanzun
da yake farkawa tsakiyar dare ya nemi duminta
a gefen shi ya rasa, wata irin kewarta ce take
damun shi hade da wasu abubuwa da yake
tunanin sun girmi ya dora su kan kalmar so. Har
mahaifinta ya bi yana bashi hakuri kan abinda
ya faru ko zai samu sauki
"Ba maganar hakuri bace ba Datti, tun kafin
kazo Hammadi ya sameni, nasan kaddara, na
kuma san kowanne mutum baya wuce kaddarar
shi.. Kai da Dije dai Allah ya kadarta zaman ku
bamai dorewa bane ba... Sai ku yafi juna kuyi wa
juna fatan alkhairi kuma... Hakuri na ba zai sa ta
koma gidan ka ba tunda saki uku kayi mata"
Amman kalaman kara daga mishi hankali
sukayi, baya son yaji ana fadin kaddarar zama ta
kare a tsakanin shi da Dije. Bai kara shiga tashin
hankali ba sai wanda ya biya dan su dinga
bibiyar mishi motsin Dijen suka zo mishi da
labarin ta fara tsayawa da wasu. Kishi yaji,
kishin da bai taba sanin Allah ya halitta masa ba,
musamman daren da yaje kofar gidan su ya
shaida da idanuwan shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 41
"Baka san matata bace ba Iroji? Baka sani ba?"
Ya karasa wajen su yana fadi kamar zautacce
harda shako wuyan rigar Irojin
"Ka sake shi Datti, ka sake shi nace maka...
Wanne irin matar ka? Yaushe na zama matar ka
kuma?"
Kallon ta yayi, kyallin farin wata na haska mishi
farar fuskar ta, hasken shi na ratsa cikin
idanuwan ta ya sauke nashi a ciki yana jin tsikar
jikin shi na mikewa da wata irin soyayyar shi,
har lokacin yana rike da wuyan rigar Iroji da ya
samu ya kwace dakyar yana mayar da numfashi
"Karka kara zuwa wajen ta, hada hanya dani
bata da kyau, kar ka kara zuwa mun wajen
mata"
Ya karasa maganar batare daya kalli Iroji da ya
sakai yana barin wajen ba, ko babu komai a
karkashin Hammadi yake samun rufin asiri, ba
zai so yayi ma kanshi sanadin rasa wannan
hanyar ba. Amman tun kafin Datti ya auri Dije
yake jinta a ran shi, yayi nauyin bakine a
Lubna sufyan
Hausabook.com 42
wancen lokacin shisa yanzun yazo ya gwada
sa'ar shi
"Meye kake nufi da korar shi? Kasan ko ba shi
ba dole zanyi aure ko?"
Ta karasa muryarta na rawa
"Na sani, zakiyi aure ki fito mu sake yin aure"
Wani irin kallo take masa
"Kar kuskuren da nayi yasa ki guje ni Dije...
Karki guje mu....dan Allah ki dawomun mu rayu
da dan mu, mu duka munyi kewar ki"
Zuciyarta taji ta karye da kalaman shi da yanda
yau ya kwantar da murya yana mata magana
cikin yanayin da bai taba ba tun kafin auren su
da bayan shi, hawaye masu zafi suka zubo mata,
ita kanta bata san tana son shi ba sai bayan
rabuwar su, kewar komai na gidan daya rabata
dashi takeyi, kewar danta takeyi kamar babu
gobe. Danma duk kwana juma'a Abu na zuwa
mata da shi, sai ta bar mata shi har sai bayan
la'asar ta hada shi da yaro a mayar da shi
"Daada yaushe zaki dawo?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 43
Shima Julden yakan tambayeta sai tayi mishi
dabara tunda bata da amsar bashi. Tana kewar
har Abu ma da hirarrakin su, don sun shaku da
juna
"Ba da kan ka kawai ka rabani ba Datti, harda
abubuwa da yawa dana saba dasu"
Ta fadi cikin dacin rai
"Na sani, kiyi hakuri ki bani dama in gyara
kuskuren da nayi..."
Bata amsa ba, baya kuma bukata, a wajen shi
shirunta amincewa ne, kalamai ya cigaba da yi
mata da baisan daga ibda suke fitowa ba shi kan
shi har saida tace
"Wa kake ganin zai aureni ya sakeni bayan wata
daya?"
Murmushin nasara yayi
"Wanda zan ba shanu biyar idan ya amince"
Itama murmushin ne ya kwace mata, su duka
biyun suna rasa dalilin rabuwar su in har suna
jin haka akan juna.
Lubna sufyan
Hausabook.com 44
Basu sani ba
Basu san rabo ne ya fito da Dije ba
Rabo mai ciwo
***
"Kar in kara jin ance an ganki da Datti..."
Kashedin da Babanta yayi mata yana dawo mata
yana kuma saka zuciyar ta dokawa a cikin
kirjinta a lokacin da take tsaye tare da Dattin,
yana mata murmushin shi da zaka hango kyallin
shi har cikin idanuwan shi da wahala bata saka
su yin ja, ko ita ta samu kyawu da hasken
idanuwan shi tana so.
"Wahalar mu ta zo karshe Dije, na samo mana
wanda zai aure ki ya sakomun ke bayan wata
daya...anjima zai zo wajen ki, gobe sai yaje
wajen Baba..."
Ya karasa maganar fara'ar shi na dan dishewa
da wani tunani daya gifta mishi, lokaci daya
kirjin shi ya dauki dumi, duhun kishi na lullube
shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 45
"Karki hada shimfida dashi Dije, karki rabamun
kan ki da wani, zuciyata ba zata dauka ba"
Kai ta gyada mishi a kunyace tana ganin kamar
wannan bukatar tashi ce abu mafi sauki a
duniyar ta. Su duka basa hango yanda ba
kowanne iko bane yake a hannun su. Ko da ta
koma gida shaukin kaunar Datti ce ta dinga
dawainiya da ita har bayan isha'i, tana kirga
kwanakin da zata suka rage kafin ta kasancewa
karkashin shi a matsayin mata. Da aka aiko
kiranta hijabi ta dauka ta saka tana kaucewa
idanuwan Innar ta da ta kafe a kanta. Gaisawa
kawai sukayi suna rasa abinda zasu ce ma juna,
ita Dije ma yawo tunaninta yakeyi yana neman
inda ta san mutumin da yake tsaye a gaban ta,
duk da babu wadataccen haske a wajen
kasancewar wata yayi nisa, hasken shi ya dishe.
"Baabuga sunana, dan gidan Sajo"
Sai lokacin ta tuna, Baabuga ne, Baabugan da
suke kirga ma yawan yara tun lokacin tana
budurwa har ma bayan tayi aure in tazo gida,
ba'a rasa wani a cikin yan uwan ta da zai ce
"Matar Baabuga ta haihu..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 46
Dariya ta kanyi
"Nifa harna bace lissafi tunda ya karo mata ta
uku..."
Dan haihuwa a gidan Baabuga ta zama tamkar
gasa ce a tsakanin matan shi da suka sakama
kan su na ganin kowacce ta tsere ma 'yar uwar
ta a yawan yara. Wani idan yaji labarin su zai
dauka wani abin duniyar Baabuga ya tara shisa
suke gasar haihuwa don wata tafi wata samun
dukiya idan shi Baabuga din ya kwanta dama, to
babu wani kudin da yake da shi, asali ko gonar
shi ta kanshi baida ita, sai dai wannan shekarar
yayi aiki a karkashin wa'ansu su biya shi da
amfanin gonar da yake ciyar da zuri'ar shi da
ita. Yaran gidan Baabuga sun fi kowa dauda a
yaran kauyen nasu gabaki daya,ga su kyawawa
saboda Baabuga bashi da muni, an kuma ce baya
auren mummuna, cikin talakawa yan uwan shi
yake kurdawa ya zabo mai kyawun gaske.
Amman rashin suttura da kulawar gaske tasa
yaran sunyi wani muni da talauci kadai kan
samar, in ta ga giccin su idan zataje unguwa sai
ta tsinci kanta da neman tsari daga talauci dan
Lubna sufyan
Hausabook.com 47
ba jarabta bace mai saukin dauka. A wani
bangaren na zuciyarta kuma sai ta dinga hasaso
kafafuwanta a cikin takalma Baabuga tana duba
zabinka da yayi ma rayuwar shi da kuma yanda
idan itace zata yisu, cikin zabukan harda zama
da mata kwara daya don yaran da zasu haifa su
sami wadatacciyar kulawa. Bata cika kyamatar
zabukan mutane ba, saboda duk yanda ita
basuyi mata ba, to tasan suna da nasu dalilin.
Baabuga na cikin sahun farko na mutanen da
take kasa yima uzuri. Amman tayiwa Datti da ya
kawo mata shi, zata jure zama da Baabuga na
kwanaki talatin, zata runtse idanuwanta daga
ganin duk wani abu da bata so a tare da shi ta
kalle shi a matsayin maslahar su kadai, ita da
Datti, a matsayin hanya daya da suke da ita da
zata sake hada su da juna
"Nagane, gobe zaka sami Baba ko?"
Ta bukata cikin harshen fulatanci dan shima da
shi yayi mata magana, kai ya jinjina mata
"Hakane..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 48
Numfashi ta sauke mai nauyi, ko Datti bai
bukaci karta hada shimfida da Baabuga ba, ita
da kanta tasan abune da ba zai yiwuwa ba.
"Allah ya nuna mana ya kuma sadamu da
alkhairi, sai da safe"
Ta karasa tana juyawa ta shige gida. Bata jima
ba taji shigowar Baba, tana da yakinin 'yan
rahon shi da suka daukar ma kan su nauyin kula
da duk wani motsin ta sun bishi sun labarta
masa ta sake tsayawa da Julde, tunda da sanyin
yamma ya zo, ko da Baba yasa aka kirata yana
rufeta da fada tasan kwanan zancen, batare da
tsoron komai ko wani dar a ranta ba ta kyale shi
ya kai karshe har yana dorawa da
"Idan ku baku da hankali mu muna da shi, saki
uku wasa ne? Me kuka dauki rayuwar ne wai?
Zan sami Dattin in masa kashedi shima..."
Nan ne ta dago da kai tana saukewa idanuwan
kan fuskar Baba
"Ba sai kaje ba Baba, za'a zo a gaishe da kai gobe
da yardar Allah..."
Har a fuskar shi ta ga mamaki
Lubna sufyan
Hausabook.com 49
"Waye?"
Ya bukata a a takaice
"Baabuga ne dan gidan..."
Bata ma karasa ba ya katse ta da fadin
"Baabuga? Baabuga dan gidan mai rasuwa
Sajo?"
Kai ta daga masa a hankali, duk da maganar
tashi tayi kama da yanayi da kanshi ne fiye da
yanda tayi kama da yana mata tambaya
"Baabuga kika ce Dije"
Baban ya sake fada cikin jinjina nauyin
maganar, saboda baiga dalilin da zaisa ta zabi
Baabuga ba, takowacce fuska basu dace da juna
ba, batafi karfin shi ba, amman gazawar shi a
kula da iyali ba boyayyen abu bane a wajen
mazauna kauyen nasu, zai masa adalci daya, iya
karfin shi yake tsaye akan iyalin shi, aikin duk
daya fado ma Baabuga yi yakeyi, iyalan shine
suna da yawa, sunfi karfin abinda yake samu
nesa ba kusa ba. Dije zata zama kamar karin
nauyi a wajen Baabuga, nauyin da Baba bai
Lubna sufyan
Hausabook.com 50
hango zai iya dauka ba. Yana kaunar yar tashi
kusan fiye da sauran yaran saboda nutsuwar ta.
"Me yasa Baabuga? Ko dan ina miki fadan
tsayawa da Datti? Ko wani a gidan yayi miki
maganar rashin dadi akan batun mutuwar
auren ki?"
Wannan karin muryar Baba a tausashe ta fito,
kai Dije take girgiza masa, banda tausayi babu
wani abu da yan gidan gabaki daya suka nuna
mata
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 27