Daada
kawai ya kamata su ga raunin juna, ita kadai ta
rage masa kamar yanda a halin yanzun shi kadai
ya rage mata. Kafin azahar an fara fitowa da
wake da shinkafa faranti faranti kamar ana biki
ba zaman mutuwa ba.
Lokacin hira ta barke, ana kwasa ana labarai iriiri, yana gefe yana jin kamar ya tarwatsa taron
kowa ya kama gabanshi. Kasa-kasa ya fara jin
zancen Yelwa, basuyi tunanin yanda suke
maganar zai karasa kunnen shi ba, sai dai Allah
ya hore masa ji, irin yanda yake zaton ya zarta
na mutane da yawa, kamar iska na kara taimaka
masa wajen kwaso masa maganganu zuwa
kunnen shi
"Da gaske da ciki ta dawo?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 420
Ya jefi Daada da tambayar, saita dan juya masa
goyon dake bayanta. Don kukan da yarinyar
take tayine ma yasa wata a cikin yar uwarsu ta
bada madarar shanu a bulunbotin tace a bata
tunda taki kama maman duk wata mai shayarwa
a cikin, don ita bata da wadatar ruwan mama,
sai dashi take hadawa yaron da take goyo da
basuyi sati biyu da rufe arba'in ba. Sai gashi ta
sha kuwa.
"Daada..."
Julde ya kira da wani yanayi a muryar shi
"Daada a waje naji ana maganar Yelwa ta dawo
da ciki"
Wani abu ya hautsina a cikin Daada, zufa na
karyo mata
"Ki hada kayanki da safe mu tafi tare"
Yanda take kallon shi yasa shi fadin
"Baki da wani dalilin zama... Baki ga Yelwa ba
idan ta sake tafiya fa?"
Kallon nashi takeyi tana juya kalaman shi,
ma'anarsu da girmansu a wajenta. Bata amsa
Lubna sufyan
Hausabook.com 421
duk abinda yake fada ba ta juya ta koma daki,
lokacin ne kuma 'yan uwanta da suka rage a
cikin gidan suka zagayeta da tambayoyin inda ta
samo jaririya da kuma abinda sukaji mutane na
fada
"Da gaske Yelwa cikin shege tayo tazo ta haife
shi anan ta sake shiga duniya? Wanne irin bala'i
ne wannan Dije?"
Kallon su takeyi
"Shege a zuri'ar Baba? Kamar abin kunyar da
Julde yayi bai ishemu magana a garin nan ba? Ya
zakiyi da wannan Dije?"
Maganganu sukeyi tana jinsu, tana kuma
fahimtar su, su da suka hada uba kenan, a
kalamansu take tsinkayo yanda duk da basu
fada kai tsaye ba suke dana sanin jinin da suka
hada da ita, saboda ita da 'ya'yanta sun zame
musu abin kunya, har a tsakanin maganganun
taji kamar suna bada shawarar a shake jaririyar
da babu wanda ya bata zabi ta inda zata fito,
saboda komai zai fi zuwa da sauki idan bata
numfashi. Wannan kalaman ne yasa Dije kallon
Lubna sufyan
Hausabook.com 422
su, zuciyarta tayi wani irin shiru a kirjinta
lokacin da tace
"Ku fitar mun daga gida"
Ta sake maimaitawa, tana karawa a tsakanin
zagin da suke mata, ta kafe akan basu amsa daya
har saida sukai zuciya suka dauki mayafansu.
Kamar fitarsu take jira ta dauki jaka tana fara
harhada duk wani abu da hannunta zai iya
kaiwa sama. Ta kuma shiga dakin Datti, nan ne
ta ga ledar da ta gani a hannun Yelwa, ta dauko
ta ta fito, sai ga Julde ya shigo
"Ka tayani mu hada kayanmu Julde, da gaskene
babu abinda ya ragemun a garin Marake"
Da sabuwar jaririya, da iya abinda zata iya
hadawa wanda motar Julde zata dauka, bayan
kuma yayi mata alkawarin zai dawo ya kwaso
mata sauran kayayyakinta, zai biya yabar sako a
gidan Baabuga ko da Bukar ya dawo, zai bar
sako inda zai riski Yelwa ko da ta dawo itama.
Sannan ta kulle gidan ta bishi. Bata san me ta
gane a hanya daya nuna mata alamun sun fita
daga Marake ba, iska dai taji tayi mata kadan
har bata iya numfashi yanda ya kamata
Lubna sufyan
Hausabook.com 423
"Ka tsayar da motar nan Julde..."
Ta fadi a wahalce, bai musa ba ya gangara gefen
titin yana tsayawa. Saita bude murfin ta fita tana
tsugunnawa cikin neman iskar data rasa, tana
jin Julde ya dafa kafadunta yana kiran sunanta.
Komai ne yake danneta yana hanata numfashi,
dakyar taja wani tana fito dashi hadi da wani
gunjin kuka. Ta zauna a kasa a gefen titi, a gefen
dajin da batasan na wanne kauye bane tana
kukan abubuwan da ta rasa, kuka irin wanda
bata tabayi ba, kuka a jikin Julde da hawayenta
suka bude masa nashi.
Kuka sukeyi da dukkan zuciyoyin su
Kuka ne na kadaici
Kuka ne na firgicin rashin sanin mai gobe tayi
musu tanadi idan har yau ta kasance musu a
haka
Zuciyarta cike take da abubuwan da ta binne a
wannan ranar, abubuwan da suka hadu suka
kawo su inda suke yau, tabar Marake rike da
hannun Julde, rike da hannun tilon dan da take
jin shi kadai ya rage mata a wancen lokacin, yau
Lubna sufyan
Hausabook.com 424
kuma kasar ce gabaki daya zata bari, rike da
hannun Nawfal
Amanarta
Amanar da Bukar yabar mata.
***
ALHAMDULILLAH!
Finally...
Yau munga karshen dogon waiwayen da Daada
tayi
Any guesses? Me zai faru?
Da idanuwa Khalid yake bin Salim da yana
shigowa falon wajen tv ya nufa ya rage sautin
gabaki daya tukunna ya wuce kitchen ya zubo
abinci ya fito
"Tashi ka koma waccen kujerar"
Ya fadi yana sake hade girarshi da take a sama
tun da ya shigo. In dai sunyi kallo a bangaren su
to baya nan ne, ko a laptop dinsu ne sai dai su
Lubna sufyan
Hausabook.com 425
saka earpiece. Nawfal baya zama bangaren
Nanna, sai da wani kwakkwaran dalili zaka
ganshi a ciki. Shisa Khalid dinma ya hakura,
tafiyar Nawfal karatu, a ranaku irin yau idan
yazo cin abinci sai yai zaman shi ya danyi kallo,
idan film dinma yaja hankalin shi sai yaje yayi
sallah ya dawo ya cigaba da kallon abin shi. Ya
nemi dalilin da zai sa Salim yawan zama
bangaren Nanna a satikan nan ya rasa.
"Ba magana nake maka ba"
Salim din ya karasa yana kai masa duka a
kafada
"Ouchhh... Hamma"
Cewar Khalid yana murza wajen hadi da mikewa
dan yaji zafi sosai. Salim baya ganin girman shi
dana sauran mutane ba daya bane ba, baya
ganin laifin Lukman da yake kauce ma duk wani
abu da zai hada shi da Salim din tun rannan
daya mare shi. Ranar ne shi kanshi Khalid din ya
ajiye shan kamshin da yake yiwa Salim din a
gefe, bai san sanda ya tsinto muryar shi yana
gaishe dashi a ladabce ba, gaisuwar da Salim din
bai amsa ba, kallon shi kawai yayi yana wucewa.
Lubna sufyan
Hausabook.com 426
Kafin ma ya fito yabar falon, Salim ba zai taba
duba shekarun shi ba balle kuma dan gemun
daya fara tarawa.
"Ka dauko mun ruwa"
Salim ya fadi, kanshi ciwo yakeyi, ga zuciyar shi
bata masa dadi ya kuma rasa dalilin hakan. Tun
a hanyar dawowa daga wajen aiki yakejin son
ganin Madina, ta zama abu na farko da zaici
karo dashi daya shiga gidan. Amman tun
dawowarta gidan sai yaga kamar yafi sakata a
idanuwan shi lokacin da take gidan Daada.
Yanzun tsakanin Magriba da Isha'i da yayi mata
magana me yasa bata fitowa falon sai tace masa
"Azkar nakeyi Hamma...zuciyata bata da
natsuwa saboda Daada, idan nayi addu'a ina
samun sauki"
Ba kalaman bane ba, yanayin yanda tayi
maganar ne ya taba tashi zuciyar, saiya kasa ce
mata komai, ya kasa fada mata abinda yake
tashi zuciyar, a maimakon
"Ni fa? Ni da bana ganin ki? Me yasa bana ganin
ki kaman da yanzun kuma muna cikin gida
Lubna sufyan
Hausabook.com 427
daya? Lokacina da yake hade da naki fa? Bakya
kewar mu?"
Da tarin maganganu masu ma'ana da akasin
haka da yake son yi mata, saiya gyada mata kai
alamar ya fahimta. Saboda ita yake yawan zama
bangaren Nanna yanzun, lokuttan daya kamata
ace yana bacci sai yayi su a zaune yana jiran yaji
fitowarta. Baya son yaje ya kwankwasa mata
kofa ko tana bacci, ga waya tana kashewa
"Wayarki a kashe Mug"
Kai ta dan daga masa
"Sai inta kallo ina jiran kiran Hamma Nawfal"
Zuciyar shi ta sosu, sai da yayi dana sanin mata
magana akan kashe wayar, zuciyar shi batayi
masa dadine idan yaso jin muryarta bai samu
hakan ba. Kalamanta sunsa zuciyar shi tayi wani
irin zafi, kiran Nawfal take jira? Me yasa zata
jira kiran Nawfal? Idan saboda Daada ne me
yasa ba zatace masa tana jiran kiran Nawfal dan
ya hadata da Daada bane ba? Me yasa ba zata
hada da Daada a cikin maganar ba? Nawfal fa?
Lubna sufyan
Hausabook.com 428
Tunda Daada ta fara rashin lafiyar nan Madina
take gwada shi akan Nawfal
"Ga ruwan"
Muryar Khalid ta kutsa cikin tunanin shi, kallon
da yayi masa yasa shi ajiye robar yana komawa
dan ya dauko kofi. Karar shigowar sakon waya
yaji, haka kawai ya mika hannun shi bayan shi
ya zaro wayar duk da yasan ba tashi bace ba, ya
kuma saka hannu yana kasa da sakon ganin
daga banki ne, idon shi ya kai zuwa kudin daya
rage a gabaki daya asusun bankin. Wayar ya
ajiye yana tsintar kanshi da kirga kwanakin
wata a ranar, ko rabi watan baiyi ba. Abincin shi
yake ci a nutse kamar taunawar na masa wahala
"Account nawa kake amfani dashi?"
Ya tambayi Khalid da ya kalle shi cikin rashin
fahimta, bai maimaita tambayar ba, barin shi
yayi ya sake juyata cikin kanshi har saida ya
gane yana amsawa da
"Guda daya..."
Kamar Salim din ba zai sake magana ba, don
saida ya karasa cinye abincin shi ya ajiye plate
Lubna sufyan
Hausabook.com 429
din, ya dauki robar ruwan ya kwance, ya kafa
bakin shi yasa yana saka Khalid dan kankance
idanuwa tunda baiga amfanin kofin da yasa shi
komawa ya dauko ba tunda yasan ba amfani
zaiyi dashi ba
"Me ya samu motar ka?"
Yana kula dashi baya daukar motar kwana biyu
"Na kunna taki tashine fa"
Khalid ya amsa a takaice, kai Salim ya jinjina, da
kudin da yake asusun Khalid din ko shine ba zai
kira bakanike ba tunda baisan nawa motar zata
ballo masa ba. Yasan tunda suka fara tsayawa da
kafafuwan su, Julde kuma ya zabi ya kyalesu don
su koyi rayuwa dai-dai da samun su, yanayin
kashe kudinsu da Khalid ya bambanta, tunda
samun su ba daya bane ba. Har ranshi, lokutta
da dama yakan so ya dauki kudi ya ba Khalid
saboda bayason ganin yanda sai yayi tunani fiye
da sau daya kafin ya siyi wasu abubuwan.
Amman bayason ya sa Khalid din yaji kamar ya
raina masa abinda yake samu ne.
Lubna sufyan
Hausabook.com 430
Idan wani ya kalle su sai yayi tunanin basu da
matsalar kudi, tunda basu da nauyin iyali,
amman motocin dake hannuwansu ma kadai
iyali ce, sau nawa yaji abokan aikin shi na cewa
idan mota ta ballo maka wani gyaran ko
matarka ba zataci kudin a wata daya ba. Kamar
kowa suna da kananun bukatu, suna da
hidindimu, kuma duk da Julde na da wadata, su
suna neman albarka, zakayi siyayya ka kawo
gida, lokaci zuwa lokaci zaka shigo da cefane,
shi ko takalman yaga sun masa kyau yakan
siyowa Saratu. Iya farin cikin da take nunawa a
fuskarta yakan rage masa duhun da yake ji a
kirjin shi.
Yana da kashe kudi ya sani, yakan alakanta
hakan da wadatarsu da yake da ita. Amman
yanda Khalid bashi da kashe kudi
"Ba'a biyanku da kyau a wajen aikinku ne
Khalid?"
Ya karasa tambayar yana daga kai ya kalli
fuskar Khalid din da yayi wani murmushi da
Salim yaji baya so, saboda hade yake da wani
Lubna sufyan
Hausabook.com 431
yanayi na kamar duk bayanin da Khalid din zai
masa ba zai fahimta ba
"Ana biya"
Ya amsa, bayason wannan takaitattun amsoshin
da Khalid yake bashi
"Nawa?"
Ya sake tambaya yana tsare shi da idanuwa.
"Dari da goma"
Sosai yake kallon Khalid din kamar yana son ya
gano amsoshin da suke masa yawo batare da ya
fito da tambayoyin su a fili ba. Albashine me
kyau, a hidimar shi kawai bai kamata ace sun
kare haka ba. Me yakeyi da kudi?
"Sako ya shigo wayarka, na duba. Magana mai
yawa ba dabi'ata bace Khalid, shisa zan
tambayeka kai tsaye...me kake da kudi?"
Gyara zaman shi Khalid ya sakeyi, kallon Salim
din yakeyi sosai shima
"Na sake ganinka"
Lubna sufyan
Hausabook.com 432
Ya furta muryar shi na fitowa a dishe, da zuciyar
Salim da abincin daya gama ci suna yo masa
wani irin tsalle, ko da yana da abin da za fada
shiru zai zaba, dan yanajin maganar shi dai-dai
take da dawowar abincin da yake cikin shi
"Na sani, nace ba sai kamun bayani ba, amman
ina son sanin dalili, me yasa?"
Ya karasa maganar yana kallon idanuwan Salim
din daya sauke daga cikin nashi. Ba'a taba masa
tambaya mai nauyin wannan da Khalid yayi
masa ba. Ba kuma amsa bace bata da ita, ta inda
zai fara furta amsar ne bai sani ba. Mutuncin
Daddy zai zubar a idanuwan Khalid? In ba haka
ba ta ina zai fara fada masa saboda Daddy ya
fara neman mata? Abinda yake tattare da matan
da yasa bai duba lahirar shi ba, bai duba Nanna
ba, balle kuma ya duba su ya so yaji shima, yaji
din, ya kuma rasa ta inda zai fara dainawa
yanzun. Saboda tun kafin a ajiye masa wasu
dalilai yake jin Khalid kadai ya isa ya zama
dalilin da zai daina in har yasan ta inda zai fara.
"Daddy?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 433
Khalid ya fadi cikin wata irin murya, yana
dorawa da
"Saboda Daddy ko?"
Yana ruguza wani abu a kirjin Salim da baisan
yana wajen ba. Numfashi Khalid yaja yana
fitarwa cike da kunar rai. Ya sani, ya dade da
sanin abinda Julde yakeyi, saboda shi mutum ne
mai kula da al'amuran mutanen da yake so. Har
Lukman kuwa da ake tunanin rayuwar shi ta
bambanta data kowa a gidan, Khalid zai iya
fadar karfe nawa yake zuwa makaranta ya
dawo, ranakun da yake zuwa islamiyya da
wanda baya zuwa yanzun, wanne abinci ya fiso
da wanda baya so, saboda yana kula. Fiye da
yanda suke tunani, idanuwan shi nakan duk
wani motsi nasu.
Shisa ya dinga jin kamar ya dauke ido da yawa
daga kan Salim shisa bai gane halin da yake ciki
da wuri ba, amman Salim ne, yaushe ma ya bude
bakin shi yayi magana da matan balle har ya
bisu? A cikin halaye marassa kyau wannan ne
karshen abinda za'a jingina Salim dashi saboda
ya sha bamban da dabi'un shi. Sai dai kaddara
Lubna sufyan
Hausabook.com 434
bata zabe, babu kuma wanda yazo duniya da
rubutun yanda halayen shi zasu kasance a
goshin shi. Idan duniya ta tashi miko maka
farantin dabi'u sai ta cakude maka mai kyau da
marar kyau a waje daya, waresu hankalin ka da
karfin yaki da zuciyarka ne kawai zaiyi maka
hakan.
Shirun Salim din ya tabbatar masa da komai,
numfashi ya sake ja yana fitarwa
"Akwai Angry Ustaz a manhajar twitter, yanayin
wani aiki build a well, suna bin garuruwa su
duka kauyukan dake karkashin garin inda suke
wahalar ruwa sai mutane su tara kudi a gina
rijiya a garin...da dan tsada idan mutum daya zai
biya duka kudin, inayin biya uku ko hudu,
saboda Daddy, saboda bansan ya zanyi ba, duk
idan naga ya fita ya dawo ina kallon shi da
nauyin da yake kafadun shi, yanzun gaka..."
Har lokacin Salim bai dago kanshi ba, cikin wata
irin murya yace
"Rijiya kayi a madadina Khalid?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 435
Dan daga kafadu Khalid yayi, kirjin shi yayi
nauyi. Wanne zabi suka bar masa? Yana kaunar
su, wannan rayuwar ta duniya yana da yakinin
mutuwa ce kawai zata raba tsakanin su, yana
musu kaunar da yake fatan kasancewa tare dasu
a aljanna,hakan ba zai faru ba idan suna wasa da
lahirarsu haka.
"Ya zanyi Hamma?"
Mikewa Salim yayi, baice komai ba ya fice daga
dakin zuwa bangaren su. Ya rasa dalilin da yasa
baya ganin hanya sosai har saida ya shiga dakin
shi ya mayar da kofar ya kulle tukunna ya gane
hawaye ne cike da idanuwan shi, kirjin shi yayi
wani irin nauyi cikin yanayin da bai taba sanin
akwai shi ba tunda yake a duniya. Iska yake ja
yana fitarwa hadi da kokarin mayar da hawayen
dake ta yi masa barazana
"Pull yourself together Salim"
Ya furta cikin wata irin murya, amman ya rasa
ta inda zai fara tattara abinda Khalid ya wargaza
masa, babu wasu kalamai da zasu fassara asalin
abinda yake ji, bacin rai? Farin ciki? Karyewar
zuciya? Rauni? Mamaki? Kowanne a cikin
Lubna sufyan
Hausabook.com 436
abubuwan ne da wasu da baisan sunayensu ba
suka hade masa waje daya. Dakyar ya iya jan
kafafuwan shi zuwa bandaki, ya watso ruwa ya
fito, babu abinda ya bashi tsoro sai wata irin
bukatar mace data taso masa saboda yanajin
duminta ne kawai abinda zai kauda masa
wannan hargitsin da Khalid ya jefa shi ciki.
Rurin wayarshi yaji, yana mamakin lokacin daya
cireta daga silent, karasawa yayi kan gadon ya
dauka. Ganin Nawfal ne ya sakashi saurin
dagawa ya kara a kunne
"Bajjo..."
Ya kira, sai dai Nawfal din bai amsa ba
"Bajjo..."
Ya sake kira, banda numfashin Nawfal din da
yake juyowa ta cikin wayar da zai dauka ko
kiran ya yanke ne
"Meya faru? Kamun magana"
Cewar Salim yana zama gefen gadon
"Ina Hamma?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 437
Nawfal ya bukata ta dayan bangaren yana
dorawa da
"Na kira shi bai daga ba"
Dan dafe kai Salim yayi
"Dole sai Khalid? Ba zaka iya magana dani ba?"
Jin yayi shiru yasa Salim din sauke numfashi
"Ina Daada? Ya jikinta? Yau za'ayi mata aikin
ko?"
A takaice Nawfal ya amsa da
"Alhamdulillah. Eh..."
Shiru ya sake gifta musu
"Sai anjima Hamma..."
Nawfal ya fadi, kafin Salim din yace wani abu ya
kashe wayar ta dayan bangaren. Karamin tsaki
Salim yaja, kamar su duka sun hada baki yau,
babu abinda suke so sai su dagula masa lissafi.
Kaya ya sake ya dauki turaruka ya feshe jikin
shi, saiya tuna baiyi ko sallar la'asar ba, da fitar
zaiyi inya dawo saiya hada duka yayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 438
"Ya zanyi Hamma?"
Maganar Khalid da yanayin muryar shi suka
dawo masa suna hana masa fita, tsaki ya kara ja
ya koma bandaki ya dauro alwala, sanda ya idar
har anyi isha'i, don haka ya gabatar da ita. Ya
sake mikewa ya fice daga dakin. Bayason
haduwa da Khalid, da ya sani yayi musanyar
aikin shi na yau dana dare, tunda da yawa bason
aikin daren sukeyi ba. Yana son ganin Madina,
da dukkan zuciyar shi yana so ya ganta. Wayar
shi da yasa aljihu ya ciro ya kirata, yayi sa'a
bugun farko ta daga
"Hamma..."
Muryarta ta daki kunnenshi, wata irin nutsuwa
daya manta rabon daya sameta ta ratsa
"Ki fito in ganki"
Ya fada yana kasa gane muryarshi saboda yanda
tayi kasa. Bata amsa ba, ta dai kashe wayar daga
dayan bangaren. Sai yaga kamar ya kusa awa
yana jira kafin ta fito, wandone na jeans a
jikinta, sai ta saka wani takalmi mai gashi da ita
kadai yake gani dashi, rigarta fara, ita dashi
Lubna sufyan
Hausabook.com 439
zasu shiga ciki saboda girmanta, ta saka farar
hula akanta, sai hannunta da take kaiwa tana
gyara zaman gilashinta kamar tana tsoron idan
batayin hakan lokaci lokaci zai iya fadowa. Tayi
masa kyau, Madina tana yi masa kyau ko me
zata saka. Murmushi take masa da yake haska
wajaje da dama a cikin kirjin shi. Sai da ta
karaso gab dashi yaga fuskarta ta kumbura,
idanuwanta sun sake kankancewa ta cikin
gilashinta.
"Kuka kikayi ko?"
Murmushin ta sake fadadawa
"Tun dazun ne fa... Kuma na wanke fuskata"
Murmushi ya tsinci kanshi dayi, in dai tana kusa,
fara'a bata masa wahala, zata fadi wani abu da
ko bai tanka ba zai saka shi murmushi. Yanayin
da yake ciki da yanda take tsaye a gabanshi, sai
ya daga hannu, nufin shi ya taba kuncinta, koya
ne yaji duminta a jikin hannun shi. Saiya kare da
sake tura mata gilashinta yanda takanyi
"Ba kayi bacci ba ko Hamma?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 440
Dan daga mata gira yayi yana sa tayi dariyarta
da yake so
"Ya nuna a fuskarka... Girarka ta karayin sama
fiye da kullum"
Kai ya girgiza da murmushi a fuskarshi
"Mu fita yawo"
Dan yatsina fuska tayi
"Mu zauna muyi hira, kaje ka kwanta... Kana da
aiki gobe da safe... Kayi bacci"
Yanda yake hade fuska yasa Madina dorawa da
"Dan Allah Hamma kayi bacci..."
Sosai yake hade mata fuska
"Bana ganinki yanzun"
Ya furta da wani yanayi a muryarshi
"Kayi bacci, zaka ganni gobe In shaa Allah... Ina
nan daka dawo aiki, sai muje yawon"
Kallonta yake tana ganin musun da yake son yi
shimfide cikin idanuwan shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 441
"Ba gobe kawai ba, kullum idan ka dawo zaka
ganni"
Hannun shi ya mika mata, batayi musu ba ta
saka nata a ciki, tana ganin kankantar nata
hannun. Numfashi ya sauke mai nauyin gaske,
ganinta, magana da ita, da hannunta daya rike
ya samar mishi nutsuwar da yake bukata, kallon
ta yake
Kallon da ba zai iya hango abinda gobe ta
tanadar musu ba a cikin so
Tun tasowarta, koya ta juya zata ga Daada a
kusa da ita. A wautar tunani irin nata ko a
mafarki bata taba hasaso nisa da Daada irin
haka ba. Ace ba unguwa bace a tsakaninsu, ba
gari bane ba, kasa ce kacokan a tsakaninsu.
Awanni ne masu yawan gaske idan akace
lissafasu za'ayi. Komai ba tajin dadin shi.
Duniyarta tayi tsaye waje daya, tana zaune
kawai sai taji hawaye na cika mata idanuwa.
Duk da taji muryar Daada yafi a kirga yanzun, ta
ganta a video calls din da Nawfal ya kirata yana
hadasu. Ta tabbatar mata da cewar tana samun
Lubna sufyan
Hausabook.com 442
sauki, har anma kusan saka lokacin dawowar
su. Ta wani bangaren hankalinta ya kwanta,
amman kewar Daada fa?
Abinda duk take so a gidan shi takeyi, banda
Salim kowa na bata wajen da suke tunanin tana
bukata, tunda Saratu tayi duk wani kokari na
ganin ta saki jikinta da ita amman ta kasa. Tasan
babu jituwar kirki tsakanin Saratu da Daada, a
iya tunaninta da fahimtarta kuma akan Nawfal
ne hakan ya faru. Duk yanda Saratu take faran
faran da ita sai ta tsinci kanta da kasa sakewa da
matar. Tana shiga kitchen ta tayata aiki sosai,
haka su sharar gidan da mopping ma, wasu
ranakun ita take dafa musu abincin gidan
gabaki daya. Tunda Saratu ta kula ta iya girkin
sosai, idan tace tabar mata bata musawa.
Yau ma daya daga cikin irin ranakun ne, sai ta
zabi ta dafa wake da shinkafa tunda miyar kifi
ce tayi. Sabonta ne zama kitchen idan tana girki
duk fadan da Daada zatayi, musamman yanzun
da Khalid ya nuna mata wani waje da zata iya
sauke litattafai a cikin wayarta, da kuma
manhajar da ta dauko don bude litattafan, ta dai
fi son taji littafi a hannunta, wannan yanayi ne
Lubna sufyan
Hausabook.com 443
da ba zai misaltu ba, ko kamshin takarda daban
yake a wajenta. Nutsuwar da kamshin yake
samar mata abune da ba zata iya amfani da
kalamai wajen fassara shi ba. Sai dai ya saukaka
mata ba saita dauki littafi zuwa ko ina ba,
yanzun a kitchen da ta shiga a wayarta sai ta
cigaba da karatunta tana zaune a kujerar robar
da take cikin kitchen din.
Hankalinta gabaki daya yana kan littafin da take
karantawa mai suna Obsidian na Jennifer L.
Armentrout. Tun daga shafin farko jiya littafin
ya riketa, so takeyi kawai taji ya za'a kare. Shisa
bataji shigowar Salim ba saida yasa hannun shi
yana rufe mata screen din wayar da ta tattara
nutsuwa a kai
"Hamma..."
Ta kira cikin kasalalliyar muryar da yaji kaman
ya fito wanka an kunna masa fanka, yanda ta
sauke idanuwanta a fuskar shi tana sauke
numfashi a hankali yasa har gwiwoyin shi yaji
sunyi masa sanyi. Mata da yawa, mata kala-kala
da ya gani, ya taba, suka bishi. Babu wadda take
da tasirin nan da Madina take dashi a rayuwar
Lubna sufyan
Hausabook.com 444
shi, yarinyar da ko shekara ashirin bata hadaba
a duniya ce take sanyaya masa jiki har haka.
Dan yatsa yasa yana tura mata gilashinta yana
sa tayin dariyar nan tata da sautinta yake sa kaji
kana son kasancewa cikin irin nishadin da take
ciki.
"Yunwa nake ji, me kike dafawa?"
Ya furta yana jingina da kantar kitchen din ya
harde hannayen shi a kirjin shi. Sai taga duk ya
cika kitchen din
"Wake da shinkafa da miyar kifi. Nanna tace
za'ayi salad, amman wake da shinkafar bai dahu
ba tukunna, yanzun ma na zuba shinkafar"
Dan hade girar shi ya sakeyi yana sakata yin
dariya
"Ina miyar kifin?"
Sai da ta kalli tukunyar, sannan ta kalle shi, ta
bude baki, kafin tayi magana ya raba jikinshi da
inda yake tsaye ya karasa ya bude, cokali ya
dauka ya tsamo kifi guda daya
"Hamma me kakeyi?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 445
Inda zai saka kifin yake nema, wani kwano ya
gani ya dauka ya saka kifin a ciki yana kara
tsamo guda biyu
"Inalillahi... Hamma kifin zaka tsame mana? Ka
tsaya a kirga aga kowa nawa zai samu"
Makale mata kafada yayi yana kara yanka daya
sannan ya rufe tukunyar
"Guda nawa ka dauka?"
Madina ta fadi tana mikewa tsaye itama, sama
yayi da kwanon hannun shi
"Ni ki kyaleni yunwa nakeji"
Dariya takeyi har lokacin
"Ka kawo to inga guda nawa ka dauka"
Yana sake sama da hannun shi Saratu ta shigo
kitchen din
"Me kake mun a kitchen Salim?"
Tayi masa tambayar cikin harshen fulatanci
"Yunwa nake ji"
Lubna sufyan
Hausabook.com 446
Ya amsa Madina na karbewa da
"Shine ya kwashe mana kifi Nanna"
Kallon shi Saratu tayi, sai ya sauko da kwanon
yana nuna mata tare da turo labbanshi
"Ba da yawa na diba ba Nanna... Yunwa nakeji"
Lukman ne karami a cikin yaranta, amman babu
mai nuna har yanzun shi yarone a wajenta
kamar Salim din, duk da maganarshi bata cika
tsawaita ba, dan ya shagwabe mata ko a gaban
waye baya masa wahala. Yanda zai kalleta ya
shagwabe fuska, ya juya ya canza fuska wa
kannen shi yana basu umarni har mamaki da
dariya yake bata. Sai dai ta kula da abu daya,
dariyarshi ta karu tun dawowar Madina gidan,
kamar akwai wata shakuwa a tsakaninsu da
yanzun ne take sanin akwaita. Sannan ko baiyi
magana ba idan yaga Madinar yanayin fuskar
shi saiya canza, girarshi da bayason saukewa ko
yaushe da kanta take sauka kafin karamin
murmushi ya bayyana kan fuskarshi da tazo
waje.
Lubna sufyan
Hausabook.com 447
Surutun kowa har da na Saratun kuwa yana
nuna ya dame shi, amman banda na Madina, da
kanshi zai fara janta da kananun hira. Kacokan
ya dawo da zama a falonta duk saboda Madina
din, shisa ita ta rage zaman falon dan suyi hirar
su cikin kwanciyar hankali tunda ta kula
Madinar bata sakewa yanda take so idan tana
waje. Da tasan matsayin Yelwa a wajenta da ta
sake da ita, da tasan yanda itace wadda taso a
kusa da ita ba Nawfal na da ta bata dama fiye da
wadda ta bata a filin rayuwarta. Ayar tambayar
da yake zagaye da asalinta bai damu Saratu ba.
Saboda tana jin abinda zata iya yiwa Yelwa
shine kulawa da Madinar, fatanta shine
hasashenta tsakanin Madina da Salim ya zama
gaskiya. Saboda sirrinsu zaifi lullubuwa idan
hakan ta faru, daga ita har Julde babu wanda zai
bukaci wani tone-tone, sune dangin Madina,
sune kuma iyayen Salim.
Sai dai wani fatan zai iya kasancewa a hasashe
kawai zai tsaya
Kamar yanda wasu sirrikan da kansu suke
bayyana kansu ba sai sun jira an tono su ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 448
"Baka karya ba?"
Wannan karin Madina ce ta amsa mata da
"Yau laraba, aikin kwana yake da duka satin
nan"
Kai Saratu ta jinjina
"Ka nemi wani abin kaci kafin a gama abinci"
Kwanon ya ajiye yana karasawa wajen fanfo ya
wanke hannun shi kamar ba dashi suke magana
ba. Murmushi Saratu
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 27