tana
kallon Dije da idanuwanta suke a lumshe da
dukan da kalaman Datti sukayi mata, saita kalli
Julde, Julde da wani abu ya canza mata a tare
dashi lokaci daya. Takawa tayi har inda yake ta
kama hannunshi tana kokarin dago shi, tashin
yayi, yanajin shi babu nauyi, kamar iskar da
take kadawa zata iya dibar shi, bai saka takalmi
ba, bin Yelwa da take janshi yakeyi
"Ki sake shi ya fitar mun daga gida Yelwa"
Muryar Datti ta tsaida takunta, sai dai bata juyo
ba
"Idan kuka tafi tare Allah ya isa"
Kafarta daya da tayi mata wani irin nauyi ta
daga tana sauketa gaba tare da hawayen da suka
sulalo mata. Ta sake jan Julde suna cigaba da
tafiya. Kallon su Datti yakeyi su duka suna barin
gidan, komai yaji yana kwance masa, yanajin
Lubna sufyan
Hausabook.com 288
Dije ta zauna a kusa dashi, yana kuma jin
muryarta dake furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Sai dai idanuwanshi akan su Yelwa da suka fice
daga gidan suke, suna fita tare da kaso mafi
girma daga zuciyarshi
Sai dai wata kaddarar bata ma soma ba!
Idan yace baya so ya daina abinda yakeyi zaiyi
karya, ba don kowa ba sai don Dije, sai dan
yanayin da yake gani shimfide a cikin
idanuwanta duk lokacin da Datti ya bude baki
ya bishi da kalaman da suka zame masa jiki
yanzun.
"Allah ya isa"
Wannan sune masu sauki a cikin kalaman Datti
da suke fitowa daya bayan daya kamar ya
jingine alakar da take tsakanin shi da Julde, yayi
katanga da duk wata soyayya da ta taba giftawa
a tsakaninsu. Idan Julde ya rufe idanuwan shi
yana tuna lokuttan da suke zaune karkashin
Lubna sufyan
Hausabook.com 289
inuwa daya da Datti, suke cikin farin ciki, suna
wasa da dariya, sai yaga kamar wasu shekaru ne
masu yawan gaske suka shude. Shi da kanshi
idan ya duba zuciyarshi babu komai a ciki a
yanzun sai wani nauyi da duhun da ba zai
misaltu ba.
"Idan baka duba kowa ba, bakayi tunanin halin
da kowa zai shiga ba, nima ban gifta a ranka ba
kenan Julde? Ko abinda zanji bashida
muhimmanci a wajenka kaima?"
Kowacce kalma ta Dije ta dira kunnuwan shi
tana samun wajen zama, inda har yau yake jin
nauyin su, musamman da ta dauki idanuwa ta
saka masa bayan wannan kalaman. Tabarshi da
abinda ya zaba. Saratu tun yana biyewa tashin
hankalinta idan taji ko da canjin kamshine a
jikin kayan shi, harya gaji, musamman yanzun
da yake mata uzuri da cikin da yake jikinta,
cikin da yazo mata da wani irin laulayi mai zafi,
amman hakan bai hana mata neman rigima
dashi ba ko da yaushe, inda take samun karfin
hali yana bashi mamaki. Yelwa ce kawai batayi
masa magana ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 290
"Ba ki tambayeni komai ba Yelwa, ba ki cemun
komai ba..."
Idanuwanta ta saka cikin nashi, kafin ta sauke
numfashi
"Me zan tambaya Hamma? Yaushe ka fara? Me
yasa ka fara?"
Ta karashe tambayar tana dauke idanuwanta
daga cikin nashi kafin da wani yanayi a
muryarta ta sake cewa
"Me zance? Abinda kakeyi bashi da kyau? Ba
mutuncinka kawai ka zubarba har da namu? Me
zan fada wanda tunaninka bai kawo maka ba ka
ture kayi zabin zuciyarka, me zance Hamma?"
Harta tashi bai sake magana ba, yanayin dake
tattare da muryarta ya kashe masa jiki. Bayan
maganganun nan bata sake masa wasu dasu
dangancin abinda yakeyi ba. Duk da itace ta
farko a wajen rikicin shi da mutane duk idan
nema ya hadasu, tsinuwar Datti da ya koyi
hadawa yayi musu tare bata taba hanata ba. Sai
yakejin kamar ita kadai ta rage masa a duniyar
shi da bata bari laifukan shi sun shafi kaunar da
Lubna sufyan
Hausabook.com 291
take masa ba, sai Salim da zai fara mika
hannuwan shi daya hango Julden, Salim da bai
damu da tarin daudar da take lullube dashi ba
zai rungume shi, zaiyi masa dariya, zai kuma yi
kokarin yi masa yarensu na yara cike da son
bashi labarin da shi kadai yasan ma'anarsa, sai
kuma Saratu da baisan ya akeyi take gane me
yake nufi ba.
Kamar akwai wata fahimta a tsakaninsu da ta
tsaya iya su biyun. Ranakun da taga daman
takan sake maimaita masa abinda Salim din
yake kokarin fada. Idan kuma rikici take dashi,
yaron na hannun shi zata zo ta fincike shi ta
saba a baya, komin tirjiya da kukan da zaiyi
kuwa. Da ido Julde yakan bita a irin wannan
lokuttan, tunda kafin ma ya bar gidan ta fara
dirka nishin da baya barinta da wani zabi daya
wuce ta sauke Salim din. Takan bashi dariya,
wani zubin mamaki, harda tausayi a wasu
ranakun.
Abinda basu hango ba su duka shine zuwan
Bukar a dai-dai lokacin daya zo. Bayan yazo din
abinda Julde bai taba hangowa ba ko a mafarki
Lubna sufyan
Hausabook.com 292
shine ranar da wani abu zai faru da zaisa Bukar
ya nuna fushin shi, har ya daga murya
"Hamma..."
Ya kira bacin rai kwance kan fuskar shi, mamaki
yasa sauran kalaman idan suka karasa
kunnuwan Julde basa kaiwa cikin kanshi balle
ya fahimce su, ga fulatancin da Bukar yake
sirkawa da wani yare da alamu suka nuna na
inda yake karatu ne, yaren Borno
"Tafiya kayi Bukar... Ka zauna ne? Tafiya kayi
kabarmu"
Julde ya fadi bayan Bukar din ya rufe bakin shi,
sai dai kamar ya sake harzuka shine
"Tafiyata ce uzurinka? Hamma tafiyata ce
uzurinka?"
Shirun da yayi yasa Bukar din jinjina kai yana sa
kai ya fice daga gidan Julden ranshi a matukar
bace. Sai dai Julde yayi nisan da bacin ran da
kowa zai nuna akanshi ba zai juyo dashi ba, a
wannan bigiren bashida dalili guda daya da
yake jin zai saka shi barin abinda yake bari
Lubna sufyan
Hausabook.com 293
"Nabarwa duniya kai Julde, wallahi na
sallamawa duniya kai tunda ita ka zaba akan
mutuncina da naka dana ahalinmu duka"
Datti ya fada masa kamar daga ranar ya daina
bata rai da duk wani abu da zaiyi. Shida aka
sallamawa duniya? Me kuma ya rage? Karshen
abinda zai faru a gani da hangen Julde ya rigada
ya faru, ya gama lalacewa, babu kuma wani abu
da yake jin zai faru dashi bayan wannan. Shisa
ya mike shima, da nufin barin gidan bayan wasu
dakika da fitat Bukar. Kullum Saratu kallon shi
takeyi, kallo irin na wanda ya yanke maka buri
da samun dai-dai to, kallo daya rigada ya saba
dashi zuwa yanzu tunda ba ita kadai takeyi
masa wannan kallon ba. Shisa bai dauka fushin
Bukar zai dame shi ba, sai da aka kwana, aka
yini Bukar na cikin Marake amman bai neme shi
ba. Sai gashi ya shiga gida yana tambayar Dije ko
taga Bukar, ta kuma tabbatar masa ko da safiyar
ranar yazo ya gaisheta.
A daddafe yaci abincin dare. Yana zame Salim da
yayi bacci a jikin shi ya mike yana shirin ficewa
"Ina zakaje?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 294
Saratu ta tambaya rikici fal a idanuwanta,
rikicin da yakejin ya gaji dashi har cikin
kasusuwan jikinshi, musamman yau
"Ba dare bane kawai lokacin da namiji yake
dashi na fita yabi mata Saratu...ki daina kallon
duk fitar dare na haka, ki saka ma ranki duk
sanda zan fita zai iya yiwuwa abinda na fita yi
kenan, kuma bakya daya daga cikin dalilin da
zan bari, kina jina? Karki sake tambayata inda
zani tunda ba aikena kikayi ba"
Ya karasa maganar yana ficewa yabar mata
dakin, mamaki da zafin maganganun shi na rufe
mata baki. Takawa yakeyi zuwa hanyoyin da
zasu hadashi da gidan Baabuga, akwai
wadataccen hasken farin wata, sai dai ko a cikin
hayaniyar mutanen dayake wucewa da suka
kafa majalissa akwai wani shiru, da kuma
hayaniyar halittun da Ubangijin daya halicce
sune kadai yasan da wanzuwar su, irin yanayin
nan da dare kadai kan haifar. Tunda ya sha
kwana ya hangota tsaye a kofar gidan, jikinta
sanye da riga da zani na atamfa, sai dankwalin
da ba daura shi tayi ba, ta dora a saman kanta
ne, habar na sauka kowanne gefe na kafadarta.
Lubna sufyan
Hausabook.com 295
Batare da tunanin komai ba ya karasa har gab
da ita, ganin babu yaro ko daya da zai iya
aikawa ya kira masa Bukar yasa shi ce mata
"Dan Allah a gidan nan kike?"
Juyowa tayi da mamaki bayyane a fuskarta tana
sauke idanuwanta cikin na Julde da yake tsaye,
lokaci daya wani abu yayi sanyi a cikin
kafafuwanshi. Baisan ko hasken farin wata bane
yasa shi ganin kamar akwai maiko a cikin
idanuwanta, wani irin maiko da bai taba gani a
idanuwan kowa ba
"Eh..."
Ta amsa cikin wata siririyar murya mai cike da
rashin tabbas, tana sauke idanuwanta daga
cikin nashi
"Bukar fa?"
Ya tambaya yana rokon ta sake dagowa ta kalle
shi, kamar taji rokon nashi ta sake dagowa tana
sake saka idanuwanta cikin nashi a karo na biyu
"Ya fita tun dazun, sai dai nasan yana gab da
dawowa"
Lubna sufyan
Hausabook.com 296
Ta fadi muryarta na zarta kunnuwanshi wannan
karin tana samun wajen zama a cikin kirjin shi,
kafin ya yawata da idanuwanshi akan gabaki
daya fuskarta, abinda bai taba faruwa dashi ba
ya faru a karo na farko, ta wuce ta cikin
idanuwan shi, ta yawata wajaje da dama cikin
kanshi, yanajin saukowar hotonta daya dauka
lokaci daya yana neman inda muryarta take ya
zauna a gefenta cikin kirji na shi, zaman da
nauyin shi yasa murmushi subuce masa.
Murmushin da ta mayar masa, kyallin shi na
haskawa har cikin idanuwanta
"Zan jira shi..."
Maganar ta subuce masa, kai ta dan daga masa
kafin ta sauke idanuwanta cike da wani yanayi
daya saka jikinshi gabaki daya daukar dumi
"Me kikeyi a waje?"
Wannan karin yayi mata maganar cikin harshen
fulatanci, saboda sabo da yayi da magana dashi,
yana kara kallon shigar jikinta da yanayinta
gabaki daya da bai masa kama da matan cikin
Marake ba, watalila shisa yayi mata hausa da
farko, kuma ta amsa shi da hausarta da take fita
Lubna sufyan
Hausabook.com 297
tar a sabanin tashi da zakaji alamun cewa ba ita
harshen shi ya fara lakanta ba
"Nayi aike ne tun dazun...saina leko in gani"
Ta amsa a takaice bayan ta dan juyo, ganin yana
kallonta yasa ta dora da
"Ya dade"
Tana dan dakuna fuskarta, murmushi ya sake
subuce ma Julde, tare da wani bangare daga
zuciyarshi batare daya sani ba
"Zaki gaji da tsayuwa ai"
Yar siririyar dariya tayi da yaji sautinta yayi
masa dadi
"Ban dade da fitowa ba"
Kai ya girgiza mata
"Duk da haka.."
Dariyar ta sakeyi, haka kawai tana saka shi jin
kamar ya santa tuntuni, kamar hira da ita na
daya daga cikin abinda ya saba dashi na yau da
kullum
Lubna sufyan
Hausabook.com 298
"Sai in jingina da bango"
Ta amsa da alamar dariya a muryarta
"Mu jingina dai, dan ni bana jure tsayuwa... In
jira Bukar ki jira dan aiken ki"
Bangon gidan kuwa suka samu suna jingina,
hira sukeyi kadan-kadan
"Baki tambayi sunana ba"
Julde ya fadi
"Na san sunan ka, ba Hamman Bukar bane ba?
Julde?"
Ganin yana kallonta da mamaki yasa ta dorawa
da
"Yana maganarka..."
Kai ya jinjina
"Ni ne ban sanki ba"
Yace, dan juyowa tayi idanuwansu ya sarke
cikin na juna tare da kaddarar da ta hadesu tun
kafin samuwar su.
Lubna sufyan
Hausabook.com 299
"Mero..."
Sunanta ya fito daga bakinta yana shiga kunnen
shi kafin ya maimaita a hankali kamar yana so
ya dandana yanda kowanne harafi yake zama
akan harshen shi. So yake ya tambayeta ko a
gidan take ko zuwa tayi amma ya rasa ta inda
zai fara, kamar yanda itama ta tsinci kanta da
fada masa ba a gidan take ba. A kauyen Marake
aka haifeta amman a garin Kano ta girma,
mahaifinta kanin Baabuga ne uwa daya uba
daya, kuma ita kadaice a wajen shi saboda
mahaifiyarta ta rasu tana da shekaru biyu a
duniya, babu wanda ya musa da kanin
mahaifiyarta Musa da yake kasuwancin shi a
Kano ya nuna son daukarta ya rike. Shekara
daya tsakani Allah ya dauki ran mahaifinta da
yayi jinyar kwanaki hudu rak.
Tashinta a Kano bai hana Musa kawota Marake
ba, ko ba tushensu bane, ita nata ne, tsatson
mahaifinta ne. Ba kuma zaiyi sanadin yankewar
zumuncinta da dangin mahaifin nata ba. Har
wata daya tanayi a Marake. Kauyen yayi mata.
Karatun bokon da takeyi take kuma sone dalilin
da yake hana mata dawowa marake gabaki
Lubna sufyan
Hausabook.com 300
daya, babu wanda yake takura mata anan, duk
da abinci da wajen kwanciya ba daya bane ba.
Amman tafi jin dadin zaman nan fiye da gidan
Musa.
Shisa tasan Bukar, suka kuma shaku dashi a iya
ganin da takeyi masa yanzun da zamanshi a
Borno yafi zamanshi a Marake yawa. A dan
sanin da tayi masane kuma tasan Julde. Ba
kamaninsu ta gani da Bukar ba, duk da akwai
wani kwarjini a tare da Bukar da Julde bashi da,
yafi Bukar din kyau, nesa ba kusa ba yafi Bukar
kyau. Akwai kuma kitso guda biyu a kanshi,
daya a kowanne gefe na kanshi, inda babun
kuma sumace cunkushe. Sumar da ta kara masa
kyau tana kuma fito da karan hancin shi.
"Bukar bai dawo ba, dan aikena bai dawo ba, ga
dare yanayi"
Ta fadi a maimakon tarin zantukan da suke
cikin kanta, tana raba jikinta da bangon da take
jingine dashi alamar zata shiga gida
"Sai da safe"
Lubna sufyan
Hausabook.com 301
Ta furta cikin sanyin murya, yana amsata, lokaci
daya yana ciza lebenshi kar son rokonta da ta
tsaya ya kubce masa. Rabon daya samu
nutsuwar daya samu a tsayuwar nan tasu an
kwana biyu. Yana kallo ta shiga gida, nauyin
zuciyar da ya daga masa ya dawo yana danne
shi, ya taso masa da hoton Mero daya samu
wajen zama yana soma jan zaren kaddarar daya
hade su waje daya.
**
Akwai wani fili da Kabiru yabar mata, filine da
ko da wasa batayi kokarin cike shi ba. Bata
yaudari kanta cewar zata iya ba. Ta ina ma zata
fara? Kewarshi da takeyi? Kewar hirarrakinsu?
Fara'arshi? Don shi mutum ne da baka raba
fuskarshi da murmushi. Ko kuma sanyin halin
nan nashi da bata taba gani a tare da kowa ba?
Dame zata cike filin da rashin shi yabar mata?
Daga ranar da Datti ya yanke musu hukunci
batare daya duba halin da su duka zata shiga ba
komai ya rage armashi a wajenta, komai ya rage
kala, komai ya rage dandano.
Lubna sufyan
Hausabook.com 302
Abubuwan da take jin dadinsu yanzun tanayi ne
saboda Dije da Julde da suke duk wani
kokarinsu na ganin ta koma dai-dai. Sai dai
batajin wani dai-daito ko kadan, idan tayi dariya
sai taji yanda tayi kewar fitowarta daga
zuciyarta. Idan ta tashi da safe jira kawai takeyi
dare yayi ta koma ta kwanta, idan daren yayi
kuma sai baccin yazo mata cike da mafarkai
marassa kan gado, duka akan Kabiru.
"Baba ba zai hanani aurenki ba Yelwa, zan fada
masa ban fara rayuwa dake ba, amman inajin
yanda kowacce rana da nayi babu ke tana
shiryani ne zuwa lokacin da zan hadu dake,
lokacin da kaddarar mu zata fara... Ba zai rabani
dake ba. Ko kin taba ganin an raba mutum da
kaddarar shi?"
Ya bata dariya, wasu kalaman na Kabiru takanji
sune, sai sun rabu ta zauna taita tunanu tana
neman hada ma'anarsu, sai ta rasa, ba kullum
bane idan ya bude mata zuciyar shi take
fahimtar shi. Sai dai abinda Datti ba zai iya ba
bashi da yawa, ciki kuwa harda rabasu. Ba ita da
Kabiru ba, har ita dashi Dattin da kanshi, kallon
shi takeyi yanzun kamar bako, kullum idan ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 303
gaishe shi da safe sai ta dinga kallon shi tana
neman Babanta a tare dashi, Babanta da yake
son duk wani abu da take so, Babanta da zasu
zauna suyi hirar awanni cike da raha da son
juna, amman yanzun kamar jira yake tayi wani
abu dan karami, tsinuwa da bakin da yake bin
yaran waje dasu ya sauke a kanta.
Tun randa ta saka kafa suka fita tare da Julde
laifinshi yake shafarta. Ya rabata da Kabiru,
Julden ma so yake tabarshi? Saboda yayi masa
laifi sai itama tabarshi kamar yanda yabarshi?
Shisa ta toshe kunnuwanta daga dukkan fadan
Datti, tsinuwa da bakinshi, akan Julde zata
dauki komai, ciki harda wadannan abubuwan.
Idan ta gaishe shi wata rana ya amsa, wata rana
ya shareta. Bata taba damuwa ba, itama yanzun
maganarta idan ta yawaita to da Julde ne, ko
kuma ta shiga gidan ta dauko Salim, shima itace
zataita masa surutu, ko yana ganewa baya nuna
mata alama sai dai yaita kallonta. Saratu ma
akan Kabiru fada sukayi sosai, saboda irin
kabilancin da yake zuciyar Datti shine a tata
zuciyar. Saita rage shiga gidan kamar da.
Lubna sufyan
Hausabook.com 304
Yanda take rayuwarta a yanzun ta dauka duka
tashin hankali kuma babu wanda bata gani ba.
Babu kuma wani abu da zai sake taba zuciyarta.
Sai daren da Datti ya zabi ya kama kafafuwanta
ya juyata ta tsaya da kanta, ya karasa birkita
mata komai da kalaman shi
"Na samo miki mijin aure Yelwa"
Yana dorawa da
"Modibbo ne, zaizo gobe ku gaisa"
Aure? A wawan tunani irin nata, haduwar
kalmar da ita a waje daya ta kare daga ranar da
Datti ya rabata da Kabiru. Ta hakura, da ta
hakura da Kabiru ba wai tana nufin shi kadai ta
hakura dashi ba, har da auren gabaki daya. Kasa
magana tayi, kirjinta yayi mata wani nauyi na
ban mamaki, washegarin ma kamar mai yawo
akan gajimare haka ta yini har daren da ta dora
idanuwanta akan Modibbo tanajin yanda baiyi
mata ba, badon yana da wata makusa ba, kawai
zuciyarta ce takeji an halitta mata ita saboda
mutum dayane kawai kacal
"Baba bana son shi, wallahi bana son Modibbo"
Lubna sufyan
Hausabook.com 305
Ta fada masa numfashinta na mata barazana.
Kallonta Datti yayi
"Haka nace bana son Dije tun kafin in ganta...
Shekarar mu nawa tare yanzun?"
Kai Yelwa take girgiza masa idanuwanta cike taf
da hawaye
"Bana son shi ko kadan, kayi hakuri kabarni"
Ta karasa hawayen na zubar mata
"Ni shine zabina Yelwa, gaya miki nayi ban
tambayi ko kina son shi ko bakya son shi ba"
Sune kalaman Datti
Kalaman da suka canza mata komai.
Ya dauka alfarma a tsakanin shi da Datti ta kare
daga ranar da ya fara ja masa Allah ya isa, har
kasan zuciyar shi ya dauka babu wata rana da
zata sake zuwa da zaizo gaban Datti ya tsugunna
da nufin neman alfarma. Sai dai wacce zuciyar?
Zuciyar da take kirjinshi da ya dauka mallakin
shi ce, mallakin shi da yake da iko da ita, ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 306
santa, suka zauna na tsayin shekaru harma ya
tabbatar tsayawarta dai-dai yake da tsayawar
shi. Sai da zuciyar nan ta nuna masa iyakarsa
lokaci daya, ta mayar da duk wata yardarshi ta
koma yaudarar kai, zuciyar nan dai itace ta ruga
tayi tsaye a gaban Mero ta cigaba da dokawar da
a wata uku kacal har fitar numfashin shi yake
jin idan batare da Mero ba zaiyi wahala, balle
kuma ita zuciyar da ta zama tata.
Tsintar kafafuwan shi ya sakeyi a kofar gidan
Baabuga washegari, bai ko yaudari kanshi ba ya
aika aka kira masa Mero, Mero da tayi masa
wani murmushi bayan ta fito kamar ta tsammaci
zuwan shi, kamar hakan ba bakon abu bane a
wajen su biyun, kafin su fara hirar da take fito
musu cikin sauki, kamar sauran abubuwa a tare
da ita. Bai sake sanin shakuwar da sukayi a dan
tsakanin tayi karfin da tayi ba saida ta koma
Kano, sai daren da ta koma daya kwanta yaji
wasu wajaje suna masa ciwo da son ganinta.
Kirjin shi ya bude yanajin wani fili daya lalubi
Saratu ko zata rage masa wannan fadin, amman
na yan mintina ne, daya mirgina gefe Mero ce a
kowanne shige da ficen numfashin shi.
Lubna sufyan
Hausabook.com 307
Bai san ya soyayya take ba sai da ya tsinci
kanshi a ciki, shisa tana dawowa bai bata lokaci
ba, bai tsaya dogon shiri ba ya bude mata
zuciyar shi, kamar yanda soyayyarta bata bashi
damar shiryawa ba, ya fada mata yana sonta ya
kuma dora da
"Ni ba mutumin kirki bane Mero, idan bakiji ana
labari ba a gari, idan nazo da maganar aurenki
zaki ji, ni ba mutumin kirki bane ba"
Ya karasa yana saka idanuwanshi cikin nata,
yana rokonta da duk wani abu da yake motsi a
jikinshi karta guje shi, sai dai taji, daga bakin
Bukar ta fara ji kafin ya koma
"Hamma na ne Mero, ina kaunar shi fiye da
tunaninki, amman kiyi wani zabin, bashi ba. Ko
menene tun kafin yafi karfin ku biyun ki
dakatar da shi"
Sannan daga bakunan da duk suke tunanin suna
da mutuntakar fada mata ta saurare su, sai dai
ta ina zata fara? Da wanne yaren zata fahimtar
dasu cewa daga ranar da ta saka idanuwanta
cikin na Julde ta jita a wani waje tare dashi,
wajen da ko taso ba zata iya barowa ba?
Lubna sufyan
Hausabook.com 308
Zuciyarta na dokawa tana sanar da ita shekarun
da tayi a baya cikin jiran lokacin da zata hadu
dashi ne, shisa tasa auduga ta toshe
kunnuwanta daga duk wani aibun shi da ake
haska mata
"Bakowanne abu da zuciyarka ta haska maka
bane alkhairinka"
Mutane kan fadi, a bigiren da Mero take tsaye
wannan kalamaine da basu da wani tasiri,
zuciyarta ta haska mata shi, alkhairi ko akasin
haka wannan zabinta ne bana kowa ba
"Zaka canza"
Ta fadi kamar tana magana da kanta ne bashi
ba, saboda yanayin yanda sautin ya fito, a
hankali, a nisance. Kalmomi biyu, kalmomi
masu nauyin gaske, kalmomi masu tarin
ma'anoni.
"Banda abubuwa da yawa da zan baki Mero,
bayan zuciyata, banda wani abu da zan iya baki
sai gaskiyata"
Lubna sufyan
Hausabook.com 309
Wannan karin akwai wani abu a cikin kallon da
tayi masa da yasa wani gashi mikewa a bayan
wuyan shi
"Bansan ko ina so in canza ba, bansani ba. Idan
ina so dinma bansan ko ta ina zan fara ba...zan
iya cewa zan canza saboda ke, zan canza saboda
son da nake miki. Amman shi kanshin son
bangama fahimtar shi ba balle in dora
alkawurra akan shi"
Batace komai ba, ta jinjina kai, alamar taji shi,
sannan ta mike tana bar masa wajen. Da nauyin
shirunta ya koma gida, washegari da yaje baiyi
zaton zata fito ba, ya daiji a jikin shi ko da bata
fito ba zai sake dawowa, zai dawo ko sau nawa
ne har saita fito. Wannan karin idan tabar
Marake zai bita. Sai ta fito, tana sake tabbatar
masa da karfin kaddarar da take tsakaninsu
Kaddarar da inda sun hango kurar da take
cikinta da sun yanke alakar da take tsakanin su
Da sun hango shafin da zai fara dasa musu aya a
alakarsu da sun hakura da juna
Akwai samu
Lubna sufyan
Hausabook.com 310
Akwai rashi
Rashi na rai a tafiyar su
Rashin da zai zama farko ya zama karshen
komai
Sai dai wauta irinta tunani, da taja Julde, ta
kuma ja Mero da furta
"Halayenka ne karshen abinda zan duba a
yanzun Julde, ina sonka, ina son kasancewa da
kai. Halayenka, abinda kowa yake fada bayan
wannan suke"
Kalamanta suka nutsar da duk wani abu da yake
a tashe a tare dashi. Suka kuma zame masa
akala lokacin da yazo ya tsugunna a gaban Datti
yana rokonshi
"Dan Allah Baba...karkace mun a'a, kace kabarni
da duniyar dana zaba akanka. Wannan karin
kawai, ka sake bani dama"
Kallon shi Datti yayi, kallo ne mai cike da gajiya.
Shi kanshi Julden rabon daya kalli Datti irin yau
harya manta. Yanda shekaru suka nuna a fuskar
shi, akwai kuma wani yanayi da gajiya da
Lubna sufyan
Hausabook.com 311
lamurran duniya ne kadai yake bayyana shi
shimfide a fuskar Dattin
"Baba dan Allah, ka nema mun aurenta"
Numfashi Datti yaja ya sauke
"Waye zai baka aure Julde? Waye zai dauki
yarinya ya baka? Wa zan kalli idanuwan shi ince
ya baka auren 'ya?"
Kirjinshi Julde yakejin kamar wani ya zira
hannu a ciki ya kama zuciyarshi yana matsawa
yana hana musu numfashi su duka biyun.
"Baka gwada ba, ka gwada... Dan Allah ka
gwada"
Ya sake roka, shi ba ma'abocin kuka bane ba,
amman yanda yake ji yanzun idan Datti yace
masa a'a tabbas fashewa zaiyi da kuka. Sai ya
dan daga masa kai, a zaune Julde yake, amman
sai yaji kamar ya sake zama, yaji shi sakayau,
kamar an dauke masa wani nauyi daya shigo
dakin Dattin dashi
"Meye a tare da Kabirun? Yana da kyau?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 312
Ya tambayi Yelwa data girgiza masa kai, tana
amsa tambayar da ba zaice wacce ce a cikin
biyun da yayi mata ba
"Me kika gani bayan kinsan Baba ba zai taba
yarda ba?"
Kafadu ta dan daga masa alamar itama bata sani
ba, ya numfasa da nufin sake tambayarta ta
rigashi da
"Kana son Adda Saratu?"
Yadan dakuna fuska saboda yanda tambayar
tayi masa bazata, yana zaune da Saratu, suna
hada shimfida, akwai yaro a tsakaninsu, gana
biyu na hanya. Amman idan ya kalleta har
yanzun yanajin yanda dolen da akayi masace
kawai abinda ya kulle su zama waje daya. Da
kanshi, ba zai taba zabenta a matsayin macen da
zai karasa sauran kwanakin shi da ita ba.
"Randa kaso wata, sai ka sake tambayata
Hamma, bansan ya zan maka bayani akan
abinda baka san ya yake ba"
Fada sukayi a lokacin, duk da Yelwar shiru tayi
ta kyaleshi, amman ya fahimta yanzun. Ko da ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 313
fada masa a baya ba zai taba ganewa ba. Yana
son mace da zai kalla yaga ta amsa sunanta
mace, duk da kowa ta tari gabanshi yana so yaji
yanda take, amman idanuwanshi basa iya sauka
daga kan irin wannan matan da suka amsa
sunansu na mata. Shisa ya dauka inda zabin
mata yayi da kanshi cikin irin wannan zai zabo,
macen da ba zai gaji da bin duk wani motsinta
da idanuwa ba. Sai gashi idanuwan Mero ya fara
gani a jikinta zuciyar shi ta rabu da kirjinshi
tana samun wajen zama a tare da ita.
Bata da muni, ba kuma zaka kirata me kyau
farat daya ba. Idanuwanta ne abinda yafi komai
kyau a jikinta. Idan Saratu ta tsaya a gabanshi,
idan ya rungumeta yanajin kanta a kafadarshi,
saboda doguwace. Bai rungumi Mero ba, amman
yana da yakinin da kadan zata wuce cikinshi.
Karamace, Mero bata da girman jikin da cikar
halittar da yake tunanin yana so a tare da mace.
Da gaskene, ba kowanne so yake da dalili ba.
Yau dai, baccin da zaiyi yau da sanin Datti ya
amince da nemar masa auren Mero dabanne.
Sai dai a gefe daya, a dai-dai wannan lokacin ne
Yelwa take bude ido duk safiya tana jin duniyar
Lubna sufyan
Hausabook.com 314
na kara hadewa da ita da yanda kwanaki sittin
suka rage a daureta a karkashin inuwar aure da
Modibbo. Modibbo da ko a tunaninta ya gifta sai
taji numfashinta yana mata barazana. Ji take ya
kamata ace littafin kaddararka yana hannunka
a rike, yanda zakayi masa zama daya ka karanta,
idan kaga yau kasan me gobe take rike dashi,
yanda komai ba zai zo maka da bazata ba, ciwon
zai dan rage idan kasan da zuwan shi. Ka
shiryama zuwan shi. Amman rayuwar ba haka
take tafiya ba.
Ji take kamar tana rike da wani sashi na
numfashinta ne tunda aka rabata da Kabiru,
shisa duk iskar da zata shaka bata kai mata inda
ya kamata, komai baya mata dadi. Yanzun
yanayin ne ya ninku, dutsen da yake danne da
kirjinta Datti ya dauko wani ya kara a kai. Ba
saiya hadata da Modibbo ba, tasan karfin ikon
shi akanta, tun akan Kabiru ta fahimta, ba iya
haihuwarta yayi ba, ya share wani titi da ya saka
ma ranshi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 27