da rokon alfarma ya gifta a tsakaninta
dashi zai kafa tarihi, saboda zai juyo mata da
bukatarta ne ba zai karba ba, ta runtsa
idanuwanta ganin ya bude baki yana shirin
amsawa, kamar tana so tace masa yayi shiru,
tana so ta roke shi ya bata wasu yan mintina ta
shiryama amsar shi, ta shiryawa kin amincewar
shi, ta kuma tabbatar duk fatanta kaddara ta
rigata, yanda duk ta hango shi karkashin inuwa
daya da Madina, hakan ba abu bane da zai taba
yiwuwa ko a halin nan da suka tsinci kansu
"Idan wannan ya zama dalilin da zan auri
Madina, kamar ba ayi mata adalci ba..."
Maganar ta fito daga bakin shi tana dukanta,
numfashi taja ta baki tana kokarin fitar dashi ta
hancinta taji an kira sunanta can nesa
"Daada..."
Yanayin yanda aka kirata din kamar da rashin
tabbaci
"Daada"
Wannan karin Madina ta kira tana kai hannu ta
kama hannun Daadar don ta tabbatar ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 477
mafarki takeyi ba, zuciyarta nayo tsalle ta dawo
makoshinta saboda murna, a hankali Daada ta
bude nata idanuwan, tana fara karewa dakin
kallo, saita mayar da hankalinta kan Madina da
take kokarin tashi zaune. Tsakanin gidan Julde,
daga inda take tsaye tana kallon komai kamar
bata da wata alaka da abinda yake faruwa
saboda jikinta da yaki bata hadin kai wajen yin
wani yunkuri, ko da na motsawa ne taga abinda
yake faruwa, ta kafe a wajen kamar anan
tushenta yake. Kafafuwanta da takejin kamar
sunyi sanyi na sanar da ita dadewar da tayi a
tsaye.
Sai dai tashin hankalin da take ciki ya girmi
gajiya, ya girmi duk wani abu da kalmomi zasu
iya misaltawa, shisa ta cigaba da binsu da
idanuwa, tana nan likitan da Khalid ya fita ya
kira ya dawo, ta gabanta suka kamo Julde suna
wucewa dashi bangaren shi, bata motsa ba, duk
kuwa da alamun da suke nuna kamar Julden
baya numfashi. Sai dai akan yara wanne abune
ya rage da bata gani ba? Kaddarar ma da bata
taba hasashen faruwarta ba yau alamu suna
Lubna sufyan
Hausabook.com 478
nuna ta faru, idan mutuwa Julde yayi ba zatayi
mamaki ba.
Bayan yaran da ta haifa suna komawa, har
bayan ta samu Bukar, baisa ta daina kallon Julde
kamar zata iya rasa shi ba shima, Bukar da
Yelwar ma da ta kwallafa rai akansu suna ina
yanzun? Ji take ya kamata ace ma indai akan
'ya'ya ne ta jima da sallamawa, ta jima da mika
wuya saboda ita sune kaddararta. Sai dai ya
kaddarar zata juya mata haka? Ya zata zagayo ta
soma yiwa jikokinta dauki dai-dai? Anya tana da
zuciyar daukar wannan kuwa? Tana jin abinda
yayi mata saura a cikin kirjinta yayi rauni, bashi
da karfin daukar koma menene yake faruwa
"Daada"
Khalid ya fadi yana tabata, yanayin fuskar shi
kuma data kalla na tabbatar mata ya dade yana
kokarin rabota da inda tunani ya dauketa ya
watsa
"Daddy nata kiranki"
Lubna sufyan
Hausabook.com 479
Kallon shi tayi tana nuna masa alamar labbanshi
kadai taga sun motsa, amman abinda ya fada bai
karasa kunnuwanta ba
"Daddy ya farka yana kiranki"
Ya fada da fulatanci wannan karin, ganin dai
kallon shi takeyi yasa shi kama hannunta yana
juyawa, batayi musu ba, tayi mamakin yanda ta
iya motsawa tana bin bayan Khalid din har
dakin da Julde yake ta kokarin tashi zaune
likitan da kuma Saratu nata hanashi
"Naji muryar Daada, naji sallamarta, ku barni
inje in sameta"
Yanayin yanda yake maganar zai tabbatar maka
da ba'a cikin hayyacin shi yake ba. Yana kuwa
ganin Daada ta shigo dakin ya sake zabura yana
kiran sunanta, waje ta samu tayi tsaye tana
kallon shi
"Daada banyi mata komai ba, bansan meya
sameni ba, wallahi bansani ba, bansan meya
sameni ba"
Ya karasa maganar muryarshi na sauka kasa
tare da kanshi daya saddar kamar wanda ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 480
fada cikin zurfin tunani, dagowa yayi lokaci
daya kuma yana kallon Daadar
"Me yake damuna?"
Yayi tambayar da nauyi cikin muryarshi, wani
irin nauyi da Daada taji ya taba zuciyarta.
Kallonshi takeyi ko zataji tsanarshi a ranta,
amman babu komai banda tsanar halayen shi,
shidin yana nan daram a zuciyarta, asalima
duka laifukan shi take so ta dauka ta dora akan
Datti, tayi amfani da kaunar da ya nuna musu, ta
kuma fake a bayan bakin daya dinga bin Julde
dashi, tayiwa danta uzuri, ta rage laifinshi a
idanuwan duniya, ta roka masa gafara a wajen
Allah kamar yanda takeyi a duk rana, dan nata
bangaren babu wani abu da zaiyi ta kasa yafe
masa, koya ranta ya baci dashi kuwa, ko da a
cikin wannan laifukan akwai layin nan da yake
tabbatar mata bai tsallaka ba yanzun.
Da gaske babban kuskuren da al'umma sukeyi
shine dora laifukan yara akan mahaifiyarsu,
saboda a duniya duka babu wata uwa data ke so
ace yau danta ba nagartacce bane, ko da kuwa
ita akwai ayar tambaya a tata nagartar. Kowacce
Lubna sufyan
Hausabook.com 481
uwa fatanta ace idan an jera yaranta cikin
sauran yara ya kasance shine yafi kowa, kyau,
kyan hali da komai da komai. Dan tayi kokarin
boye laifinshi baya nufin tana goyon bayan
wannan hanyar lalacewar daya dauka, tana
kokarin boyewar ne don zuciyarta ta rage mata
nauyin da takeyi, tana kuma yi masa uzuri kome
ya akaita saboda shine zabin karshe da take
dashi, tana ganin yanda kowa yake aibata shi,
kowa yake kyararshi, ya ake tsammanin itama
tabi sahu bayan batasan komai ba daya wuce
kare shi daga duk wani abinki?
Ko bayan kwanaki a cikin satika, satika a cikin
watanni, laulayi, kwanciya dakyar, tashi dakyar,
rayuwa a cikin wata rayuwar da mai ciki ce
kawai zata fahimta, awanni a dakin nakuda, duk
wannan wahalar ana dora mata shi a hannunta
abu na farko da yake zuwa ranta shine tabbatar
da yana cikin koshin lafiya koda ita batajin
wannan lafiyar a tare da ita, daga ranar komai
na rayuwarta zai biyo bayan nashine, duk wata
bukata da take da ita a kasan tashi take. Kuma
sai ace tana so ta ga ya lalace? Ko da ta sake shi,
ko da ta sangarta shi, ko da akwai nakasu a
Lubna sufyan
Hausabook.com 482
yanayin tarbiyar da ta bashi, a cikin zuciyarta
tafi kowa son ganin ya kasance nagartacce.
Wannan kaunar ta tsananin mahaifiya da
yaranta babu wanda zai fahimta sai wata
mahaifiyar.
Ko yanzun da take tsaye so take ta karasa ta rike
shi, gani takeyi kamar yayi zuru-zuru, duk ya
rame, amman wani abu ya rike mata kafafuwa,
kallon shi takeyi kamar yanda shima yake
kallonta, hakan ya ba likita damar yin allurar
baccin da Julde yaki tsayawa ayi a cikin karin
ruwan da akeyi masa, cikin wasu dakika ta fara
aiki, jikinshi ya fara yi masa nauyi, dole ya
kwanta, kafin wani lokaci bacci ya dauke shi
"Yana bukatar bacci don jininshi da ya hau ya
sauka"
Likitan ya fadi yana yi musu bayanin dalilinshi
nayin allurar baccin. Hannu Saratu da take
zaune a gefen gadon ta kai tana dauke kwallar
da take cikin idanuwanta. Juyawa Daada tayi,
Khalid ya rufa mata baya, ganin tanayin hanyar
waje ya sashi fadin
"Bari in dauko Madina sai inzo in kaiku gida"
Lubna sufyan
Hausabook.com 483
Hakan kuwa akayi, idonta kur akan Khalid daya
sabo Madina zuwa mota ya kwantar da ita a
baya, itama bayan ta shiga tana daga kan
Madina ta kwantar a jikinta, kamar bacci takeyi,
tayi wani irin luf da ita, jikinta nade da zanin
gado, kanta ne kawai a waje. Ko da tana yarinya
bata da yawan rashin lafiya, hakora ma kanta ne
kawai yake zafi, sai wasu ranakun idan ka taba
jikinta zakaji akwai alamun zazzabi, amman
wannan wahalar duka Madina batayi ba
"Baki taso da uwa a kusa dake ba Madina, sai
Allah ya dubaki komai yake zo miki cikin sauki"
Daada ta tuna kalamanta bayan Madinar tayi
wata kyanda da bata hada sati daya ba, ba kuma
ta wani kwantar da ita yanda take yiwa sauran
yara ba. Da ta fara girma, idan zatace kanta na
ciwo ko cikinta, zai wahala ta tashi da safe ta
sake maimaita wannan maganar, idan ta
tambayeta ma zatace
"Tun jiya ne Daada, da na sha magani nayi bacci
yau ban tashi dashi ba"
Shisa ganin yanda Khalid din ya sabota yakeyi
mata wani iri, haka da suka karasa gidama.
Lubna sufyan
Hausabook.com 484
Mukullan gidan kowa yana dashi ita da Madina,
nata kuma yana tare da ita, don dakyar ta bawa
Nawfal riko lokacin tafiyarsu, suna kuma sauka
Abuja ta tambaye shi
"Daada kamar wanda zai gudu da mukullin nan?
A asibiti ma fa wajen sau hudu kika tambaya"
Dariya tayi
"Mukulli na da tsautsayi, kai ka batar mana da
guda daya, daga baka ko da zaka zo bama nan"
Kai Nawfal ya dafe
"Akan batan mukullin daya faru wajen shekara
goma har yanzun banyi hankalin da za'a yarda
zan iya ajiye wani ba, ai shikenan..."
Ya karasa yana zuwa ya dauko mukullin ya
danka mata, ta saka a yar jakar da take makale
da ita. Wani irin takeji ganin yanda duk inda
akayi da Madina take bi saboda alamu sun nuna
batasan inda kanta yake ba, kan kujera ya
shimfidar mata da ita yana fadin
Lubna sufyan
Hausabook.com 485
"Likita ya dubata itama, yace babu abinda yake
damunta, bacci takeyi zata tashi zuwa wani
lokaci"
Kallon Khalid din tayi, sai taga kamar yana
kokawa da wani abune, yana kokarin danne
abinda yakeji don yaga kamar su duka suna
bukatar wanda zai tallafe su a wannan yanayin
da suka tsinci kawunansu
"Bakomai kaje kayi hidimarka Khalid...Allah
yayi maka albarka"
Kai ya jinjina
"Idan kuna bukatar wani abu sai ki kirani
Daada, zan dawo ma zuwa anjima In shaa Allah"
Wannan karin ita ta jinjina masa kai, saida ya
fita take karewa falon kallo, ya kamata ace
akwai kura tunda an kwana biyu bakowa,
abinda bata sani ba shine duk kwana biyu sai
Madina tace Salim ya kawota, ranar farkon ta
dade, data dawo yake ce mata
"Tun dazun, kin barni ni kadai tun dazun"
Lubna sufyan
Hausabook.com 486
Da ta sake dawowa kuwa tare suka shiga, daya
fara shara kaman abin kirki ya ajiye mata
tsintsiyar
"Ni bana son shara Allah"
Ya fada, dan dakin shima yana kokarin ganin
kome yaci bai zube yanda zaiyi shara ba, idan
abune ya shiga dashi, yana gamawa yake tattara
ledojin ya fito dasu. Daya yi barin shinkafa
kwanaki zama yayi ya mike kafa ya fara
tsincewa, haka Khalid ya shiga ya same shi
"Bari kayi?"
Bai magana ba, irin wannan tambaye-tambayen
ne na Khalid baya so, abu yana gabanshi, ya gani
amman saiya sake maka tambaya akai
"Shinkafar zaka bi ka tsince da dai-dai Hamma?
Maimakon ka share?"
Numfashi yaja yana fitarwa
"Bana son shara, ka kyaleni Khalid, me ma kake
nema ka shigo mun daki kayi tsaye kana
damuna da magana?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 487
Dariya Khalid din yayi, karshe shine ya share
masa, sai yayi sati bai share daki ba, kome ya
zuba zai tsince. Shisa Madina take bashi
mamaki, ta tattara duka natsuwarta sai shara
takeyi, waje ya samu ya dinga kallonta harta
gama. Haka duk zuwan da zasuyi, tayi shararta,
tayi goge-goge yana zaune, idan yaji kamar
bashi da wani amfani ne ma zaice mata
"Kawo in fasa miki omon"
Ya kuwa bata dariya ranar, ko kuma yace
"In kara dibo miki ruwa?"
Idan ta gaji ne zatace
"Hamma kayi zamanka, ai kayi babban aiki
tunda ka kawoni, kuma zaka mayar dani, gashi
kanata tayani da idanuwanka ma"
Daman dan kar taga kamar bai tayata bane shisa
yake magana. Ai kuwa gidan ko ina tas, dan da ta
shiga tayi sallar azahar kamar bataje ko ina ba,
sai dai sau daya Madina ta motsa. Khalid ya
dawo kamar yanda yace, da ledojin da inda ya
ajiyesu nan suke har zuwa yanzun. Anan falon
tayi la'asar da alwalarta ta azahar da take rike
Lubna sufyan
Hausabook.com 488
da ita. Da Madina bata motsa ba zata kira wani
ne yazo ya taimaka mata su kaita asibiti, ko a
kira likita ya sake dubata. Tunani babu irin
wanda Daada batayi ba, tasha babu wadda bata
kama ba, sai dai inta kama din subuce mata
takeyi.
Wannan ciwon da tayi ta dauka karshen
rayuwarta ne yazo, duk da Bukar da Yelwa suka
cika tunaninta a lokacin, Madina saita danne su,
saboda a wajen Madina itace komai, itace
matsayin mahaifi da mahaifiya, bata taba
tunanin zata roki Allah ya kara ara mata wasu
shekaru a duniyar da ba dadin zamanta takeji
ba sai saboda Madina, saboda tana son ganin
wanda zai mayewa Madina gurbinta kafin
tabarta. Tasha hango Nawfal ne zaiyi wannan
aikin, sai yazo da maganar aure, sai kuma ta
ganshi da Murjanatu a India, taga yanda yake
kallonta kamar bashida sauran wajen da
Madina zata zauna a rayuwar shi.
Sai kuma ta ga yanda Murjanatun take kallon shi
itama, yanda ko abinci ne saita fara ci kamar
tana son dandana zafin shi a harshenta kafin ta
mika masa, duk da haka idan akwai wani abu a
Lubna sufyan
Hausabook.com 489
kusa da ita da zaiyi fifita zaka ga ta dauka tana
sake fifita masa abincin sanin bayason shi da
zafi, tunda tazo ita take fita tayi abubuwa da
yawa shi yana tare da ita. Idan kifine zaici, zata
wanko hannunta ta zauna ta zare duk wata kaya
da idanuwanta zasu iya gani kafin ta mika masa.
Soyayya ba bakuwar Daada bace ba, bayan
Hammadi da Abu, itama ta taba kalar tata
soyayyar, yaranta kuma sun sake nuna mata
indai soyayya ce suna cikin wanda Allah ya zaba
ya kadartawa ita a filin duniya.
Tun a asibitin saita cire rai, saboda Nawfal ya
rigada ya gama samun abokiyar rayuwa, amman
yau, tana so ta roke shi, tana so tayi masa
magiya ya dan matsar da Murjanatu ya samarwa
Madina wajen zama, saboda yanda bata taso
kusa da iyaye ba, haka shima, sunfi kowa
cancanta da su kula da junansu. Wannan zaren
take ta sakawa tana warwarewa batasan bacci
ya dauketa ba, a cikin baccin harda mafarkin ta
roki Nawfal din kuma yaki amincewa, in ba
mafarkin ba, ita da take hasaso su karashe
rayuwarsu da juna, me yasa zata roke shi
shekaru biyu?
Lubna sufyan
Hausabook.com 490
"Daada"
Madina ta sake kira, tana murza idanuwanta
wannan karin, gilashinta da yake gefe da Khalid
ya bawa Daadar ta dauka tana mika mata,
sakawa tayi ta kalli Daada, idanuwanta cike da
tarin tambayoyi wannan karin, tana kuma saka
bugun zuciyar Daada karuwa saboda bata san
me zatace mata ba
"Jikina yayi mun nauyi kamar nayi kwanaki ina
bacci..."
Ta karasa maganar tana zaro jikinta daga
bargon da take ciki, sai dai jikin nata ta kalla, ta
rage kayanta kafin ta kwanta, tana da wannan
yakinin, amman ba zata taba fitowa haka ba,
kanta yayi nauyi na gaske, girgiza shi tayi a
hankali tana dafa kujerar ta mike, duk wasu
tambayoyi zasu iya jira ta watso ruwa ko zata
dawo dai-dai. Harta taka saita dawo ta rankwafa
tana riko Daada jikinta
"Daada nayi kewarki sosai, kamar in biyoku
wallahi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 491
Yanda ta sauke wallahin muryarta na karyewa
da alamun kuka zatayi yasa Daada saurin fadin
"To ba gani na dawo ba, kije ki watso ruwan ki
fito, kinga abinci Khalid ya kawo mana tun
dazun nake jira ki tashi muci"
Raba jikinta tayi dana Daada dakyar, tana kai
hannu ta kasan gilashinta ta goge kwallar da taji
ta tarar mata
"Yanzun zan fito"
Cewar Madina tana nufar dakinta cikin hanzari,
Daada ta bita da kallo, wani abu na hadewa a
cikin kirjinta
Kamar lokaci yayi
Lokacin da zata amsa tambayoyin da Madina
bata taba bude baki ta furta mata su ba...
Ba zaice ga asalin abinda ya faru da Baban shi
ba, tun idan ya rufe idanuwanshi yana hada
kadan daga cikin alamomin fuskar Bukar har ta
bace masa, muryarshi da yake tunawa ma gani
Lubna sufyan
Hausabook.com 492
yake kamar hasashen zuciyarshi ne. Sauran
abubuwan a bakin Saratu yaji
"Babanka ma tsallakewa yayi ya barka, me yasa
ni za'a tilasta mun zama da kai?"
Ranaku babu adadi, ya sha numfasawa da nufin
tambayar Daada, saiya kasa, saboda yanda take
kallon shi, saboda abinda yake gani a cikin
idanuwanta, shine yake tsayar dashi kowanne
lokaci, saboda tasha furta
"Bukar..."
A kasan numfashinta idan yayi sallama, ko
kuma taga giccin shi, sai yaga ta runtsa
idanuwanta ta sake budewa ta girgiza kanta a
hankali, yanayin saiya taba zuciyar shi. Taya zai
tambayeta, me zaice mata?
"Daada me ya faru? Ina Babana? Me yasa ya tafi
bai sake waiwayen mu ba?"
Bayan yana ganin yanda take da tambayoyi iri
daya da nashi, yana kuma ganin yanda rashin
dawowar Bukar din yake nukurkusarta fiye
dashi. Duka sanin shekara nawa yayi masa?
Daada tasan shi tun yana cikin jikinta, ta so shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 493
tun kafin ta dora idanuwanta akan shi. Da wacce
zuciyar zai tambayi uwa labarin batan danta? Ya
taba tambayar Julde sau daya
"Kome zan fada maka zanyi karya Bajjo, Bukar
ya tafi neman karatu Maiduguri, da farko baya
hada shekara yake zuwa ganin gida, daga baya
saiya dade baizo ba, sai mu dade bamu saka shi
a idanuwanmu ba. Bansan dawowar shi ta
karshe ba, saboda ina nan Kano, na koma na
samu ya dawo ya barka..."
Shirun da yayi bayan amsar Julde yasa Julden
kiran sunan shi a hankali
"Ba kai kadai yabari ba, mu duka ya bari"
Shisa ya kasa tambayar Daada, da gaskene su
duka ya bari, ko a kalaman Julde yana jin ciwon
da yake zuciyarshi na tafiyar Bukar din da
rashin sanin abinda ya faru dashi. Sai dai a
lokacin ya dauka tafiyar Bukar ta karya wani
abu a zuciyarshi, tana kuma karyawa duk ranar
da zai wayi gari tunanin ya fado masa. Yanda
Julde ya rike shi, yana da yakinin ko a hannun
Bukar ya tashi, soyayya ta mahaifi iya wadda zai
samu kenan. Duk da tunasarwar da Saratu take
Lubna sufyan
Hausabook.com 494
yawan yi masa, na cewa Julde ba mahaifinshi
bane ba, ya kuma sani, tunda ko a makaranta ba
da sunan yake amfani ba, Nawfal Bukar yake
sakawa. A zuciyar shi, Julde kawunshi ne daya
dauki matsayin mahaifin daya tsallake shi.
Baisan matsayin da yake dashi ya wuce duk
wani tunanin shi ba sai jiya, saida yaga abinda a
labaran duk da suka taba isa kunnuwanshi bai
taba cin karo da kwatankwacin su ba. Ba kamar
Khalid da Salim ba, halayen Julde masu kyan
kadai ya sani, shisa da yaga wannan bangaren
ya girgiza, abinda kuma ya karye a zuciyar shi
ba irin wanda ya karye da tafiyar Bukar bane ba,
da kuma rashin dawowar shi, ko tunanin Bukar
ya mutu bai jefashi kunci irin wanda yake ciki
ba. Ko ganin kirki bayayi sanda ya karasa cikin
dakinsu. A kasa ya zauna, sai yaji kamar bashi
da karfin zaman shisa ya kwanta, da takalma da
komai a kafarshi, yaja jikinshi ya dunkule waje
daya.
Zuciyarshi ciwo takeyi da yake amsawa a ko ina
na jikinshi, da zai iya daya cirota ya ajiyeta a
gefe ya dan sarara. Baisan kuka yakeyi ba saida
yaja numfashi yaji wata shesheka ta kwace masa
Lubna sufyan
Hausabook.com 495
kamar karamin yaro, kuka yakeyi da yaji dadi
babu kowa a kusa dashi balle ace za'a bashi
hakuri ko a lallashe shi. Kuka yakeyi da yake
neman zuciyarshi ta samu saukin ciwon da
takeyi ko kadanne. Anan kasan wani wahalallen
bacci ya dauke shi. Sanda ya tashi yanayin
duhun dakin ya sanar dashi Magriba tayi ko
kuma tana gab, tunda yake bai taba baccin rana
irin wannan ba. Mikewa yayi dakyar, ko ina na
jikinshi ciwo yake masa kamar mota ta taka shi.
Karasawa yayi wajen makunni ya kunna kwan
dakin, mamaki ya fara cika masa zuciya ganin
Khalid kwance akan gadon. Alamu sun nuna ya
dawo, ya ganshi kwance a kasa, ya zagaye shi ya
hau gado ya kwanta. Bai kuma tashe shi yayi
sallah ba, yanda yaga Khalid din kwance luf sai
yaji zuciyarshi ta doka, wani tunani da yasa
kafafuwan shi motsawa na gifta masa
"Hamma..."
Ya kira da sauri yana bubbuga shi, a hankali ya
motsa yana juyo da jikinshi
"Yamma tayi sosai, kayi sallah? Ni ko azahar
banyi ba"
Lubna sufyan
Hausabook.com 496
Kai Khalid ya daga masa, yayi azahar da la'asar
duka, baima dade da shigowa dakin ya kwanta
ba
"To ka tashi ko ba'a kira Magrib ba yanzun za'a
kira"
Ya karasa fadi yana wucewa bandakin, fuskarshi
ya fara wankewa sannan ya dauro alwala ya fito,
azahar da la'asar ya gabatar, yana idarwa yaji
ana kiran Magriba, saiya mike, a hanyarshi ta
zuwa masallacin yake neman gafarar Ubangiji ta
sallolin da baiyi akan lokaci ba, saboda hade
sallah ba sabonshi bane ba, wani iri yakeji. Da
aka idar saida ya duba Khalid bai ganshi ba, nan
ya zauna cikin masallacin saboda zuciyarshi ta
dan samu sarari, sanyin masallacin ya sanyaya
masa wajajen da suke masa zafi, yasan yana fita
daga ciki komai zai sake danne shi.
Sai yai zamanshi har akayi isha'i sannan, shima
dakyar ya tafi, don ji yake kamar ya kwana cikin
masallacin, dole gidanshi ko bai gina masallaci
ba, zai ware wani waje da sallah kawai za'a
dingayi, watalila yayi sanyi da albarka irin
wadda masallacine kawai yake da ita, don ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 497
samu wajen kwanciya idan yana cikin damuwa.
Zuciyarshi matse a cikin kirjinshi da yaga Khalid
a zaune kan darduma, a gida yayi sallah kenan,
abinda zaisa shi sallah a gida ba karami bane ba.
Baiyi masa magana ba
"Ina mukullin motarka?"
Ya tambaya, hannu yasa a aljihu ya ciro ya mika
masa, nashi aljihun ya duba yaga yana da dubu
shidda. Sai ya fita, baiyi wani nisa ba yayo musu
takeaway badan yana jin yunwa ko yana cikin
yanayin son cin komai ba, jikinshi na bukatar
abinci ya sani, haka Khalid, yafi bukatar ganin
yaci wani abu ma. Yana komawa ya samu Khalid
harya kwanta, a kasa ya ajiye komai
"Hamma ka taso mu ci abinci"
Cikin sanyin murya Khalid ya amsa shi da
"Banajin yunwa Bajjo, ka kyaleni dan Allah"
Mikewa Nawfal yayi ya shiga bandaki ya watsa
ruwa ya fito ya sake kaya ya kwanta shima
"Ka tashi kaci wani abu, ka kashe mana kwan
dakin kuma"
Lubna sufyan
Hausabook.com 498
Khalid ya fadi, don yana kallon Nawfal din, ko
amsa bai bashi ba
"Da kai nake magana kana jina kuma"
Bargo Nawfal yaja ya rufe jikinshi har kai
"Ka girmi wannan yarintar, har mata kake da
Bajjo"
Baiyi magana ba, yanajin Khalid din sarai, idan
ba haka yayi masa ba, ba zaici abincin ba, bashi
bane yaro, Khalid ne yarinta bata saki ba, yi
masa dabara bashida wahala, yanajin shi yaja
tsaki a jere yafi sau hudu kafin ya sauka
"Saika sauko muci dan ubanka"
Duk yanayin da yakeji bai hana murmushi
kwace masa ba
"Magana fa nake maka"
Bude bargon yayi ya fito yana kokarin danne
dariyar da take neman subuce masa. Abincin
sukaci, shinkafa da dankali ne ya siyowa Khalid,
shikuma ya siyowa kanshi kifi da dankali, yayi
mamakin yanda sukaci abincin sosai, shiya
kwashe kwanonin ya dawo, suka zauna suna
Lubna sufyan
Hausabook.com 499
dan hirar da ba zasuce ga asalin abinda suke
fada ba, hirace da kowa abinda yake son magana
akai daban da abinda yake fitowa daga bakin
shi. Wani numfashi mai nauyi Khalid yaja yana
fitarwa, idanuwanshi kafe jikin bangon wajen
kamar mai son gano duka amsoshin tambayoyin
da yake dasu akan bangon yace
"Idan abin nan ya taba har yaranmu fa?"
Wani irin shiru ya ratsa dakin kafin Nawfal ya
iya bude bakin shi da yakejin yayi masa nauyi
"Babu abinda ya faru, kaji Daddy ai, yace babu
abinda ya faru"
Kai Khalid ya jinjina, Julde nada halaye da yawa,
amman karya bata cikinsu
"Bai faru ba yau..."
Khalid ya fada yana rasa ta inda zai fara gayawa
Nawfal halayen Julde daya sani, da kuma yanda
Salim yaga babu halin daya kamaci ya dauka irin
wannan, da gaskene kowa yana da labarin
bayarwa, kowanne mutum da zaka hadu dashi a
hanya yana da labarin da zai baka inda zaka
tambaye shi, amman wasu labaran duk da
Lubna sufyan
Hausabook.com 500
akwaisu ba zasu taba baduwa ba, wasu labarin
kokarin binne su akeyi yanda ko kurarsu wani
ba zai tarar ba balle kuma yaji su. A cikin
wannan labaran akwai wannan, saboda ba
labarinshi bane ba, masu labarin idan suna so ya
sani zasu bashi da kansu, idan yana da rabon ya
sani zai sani kamar yanda shima ya sani.
Numfashi ya sake ja, kirjinshi na tafasa, daya
runtsa idanuwa, fuskar Daada ta dawo masa
dazun, yanda tayi masa murmushi kamar babu
ciwo a kirjinta, kokarin yakice zuciyarshi yakeyi
dan karta hasaso masa abinda Daadar take ji
amman ya kasa. Ya Daddy zai musu haka? Jin
wani abu na toshe masa makoshi, tafukan
hannunshi yasa ya tallabi fuskarshi dasu yana
sauke numfashi hadi dajin dumin hawayen shi
na zubowa, wanne irin abin kunya ne wannan?
Ya zai iya sake hada idanuwa da Madina
yanzun? Ta sani? Idan bata sani ba ta sani din ya
zataji? Rayuwarta zatayi canzawar da ba zata
taba komawa dai-dai ba.
Saboda Julde ya tabasu ta fannin da
warkewarshi zaiyi wahala, tabon da zai bari
kuma zai dauke su har karshen rayuwarsu bai
Lubna sufyan
Hausabook.com 501
daina ciwo ba, ko motsin kirki Nawfal baiyi ba,
numfashin shima bayaso yayi karar da zata
katsewa Khalid yanayin da yake ciki. Kuka ne
yau anyi musu abinda dole zasuyi shi, zai karya
idan yace baiji sauki-sauki ba, hade kanshi da
gwiwa Khalid yayi, ya dauki lokaci a haka kafin
ya dago, sai Nawfal ya kauda kanshi kawai, ya
bashi tazarar da yasan yana bukata harya mike
ya shiga bandaki, saiya tashi ya hau gadon ya
kwanta. Daya fito shi ya kashe musu fitilar
dakin, sannan shima ya kwanta, ko saida safe ba
suyiwa juna ba, kowa ya juya kwanciya,
zuciyoyinsu cunkushe da tunanin da yayi
kamanceceniya a lokaci daya kuma yasha
bamban.
*
Da safe har wajen karfe goma suna daki, Nawfal
yaji Khalid yayi waya wajen aiki yace musu ba
zaije ba bashida lafiya. Shikuma yayi waya da
Murjanatu tace masa ta gama shiryawa, za'a
sauketa filin jirgi, yasan duk inda take tana gab
da sauka, shisa yayi wanka ya shirya ya koma ya
zauna. Khalid yake so yaga ya tashi sai su shiga
bangaren Saratu tare, amman saiya koma ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 502
kwanta, yana so yace masa ya tashi suje amman
bayason fama masa ciwon da duka suke ta
lallabawa. Dakyar ya tattaro karfin gwiwa ya
mike yana fita, ya kai wasu mintina a bakin
kofar dakin kafin ya shiga da sallama, a kitchen
ya samu Saratu
"Ina kwana Nanna"
Ya fadi muryarshi na rawa, juyowa tayi, sai yaga
fuskarta kamar a kumbure
"Bajjo...kun tashi lafiya"
Mamaki yasa shi ya bude bakin shi, amman sauti
ko daya yaki fitowa, ya rufe yayi gyaran murya
kadan kafin ya iya amsawa da
"Alhamdulillah, ya jikin Daddy?"
Dan juyawa tayi kafin ta amsa
"Da sauki, bacci yakeyi"
Kai ya jinjina yana kokarin juyawa saboda
baisan me zai sake fada ba
"Ka tsaya ka wuce muku da abin kari"
Lubna sufyan
Hausabook.com 503
Wani mamakin ya sake dukanshi tare da
maganganunta, tunani yakeyi, idan akwai ranar
da ta taba yi masa tayin abinci, koma ta damu da
yaci ko baici ba, asalima rashin cin nashi yafi
muhimmanci a wajenta tunda yanda duk zata
dafa saita tabbatar ya haramta a wajen shi.
"Sai dai in kaiwa Hamma, zan fita ne ni"
Juyowa Saratu tayi
"Haka zaka fita baka ci wani abu ba? Ka tsaya ka
tafar muku dashi ku duka, kaima karka fita
bakaci wani abu ba"
Ko yaso yayi magana ba zai iya ba, wani abu ya
tokare masa makoshi, iya wannan maganar, iya
wannan kulawar ya tuna masa dararen da ya
shafe cikin kewar kulawar uwa, tasa zuciyarshi
ta motsa da wani irin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 27