akan batun mutuwar auren ta, babu kuma
wanda ya sake mata zancen yaushe zatayi wani
auren kamar yanda taji Baba na zargi a cikin
tambayoyin shi. Dalilin ta ya sha bamban da duk
wannan
"Auren kisan wuta zakiyi Dije..."
Baba ya jefeta da wani yanayi mai nauyi a
muryar shi da yasa wani abu da tasan ba
hanjinta bane amman yana da tsayi ya tsinke a
cikin cikinta
"Kinsan girman munin abinda zakiyi a addinin
ki kuwa? Baki san haramcin shi ba ko?"
Da sauri take girgiza ma Baba kai
Lubna sufyan
Hausabook.com 51
"Ba auren kisan wuta zanyi ba Baba..."
Karya ta farko da ta gifta a tsakanin su tunda ta
mallaki hankalin ta, ba'a sirri a gabanta ko laifi
lokacin yarinta da yan matanci, don da Baba
yace
"Dije fadamun gaskiya kinji, me ya faru?"
Take zayyane masa komai, ko da kuwa harda ita
a cikin laifin. Shisa idan ta fadi magana yake
yarda kai tsaye, amman yau yanayinta da
muryarta duk sun nuna rashin gaskiyar ta
"Karki sa yazo wajena in dai ba son auren shi
kikeyi don ki zauna ba Dije, na rokeki karkiyi
wannan kuskuren har ki raba zunubin shi
dani..."
Wani abune tsaye a makoshin ta da ta kasa
hadiyewa, abin da kuma bai hanata sake furta
wata karyar ba da ita ce matakin farko na canza
abinda suka tsara ita da Datti
"Zaman aure zanyi Baba"
Karyar da zata bibiyeta a gaba
Karyar da zatayi dana sanin ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 52
**
Juma'atu babbar rana, juma'a hasken mako.
Daren ta ma cike yake da albarka, abune da ko
tsofaffi da aka haifa a musulunci suke kuma yin
shi yanda suka taso suka ga anayi batare da
neman ilimi ba sun san haka, kusan sune ma
suka fara furta kalaman da basu san har a
addinin da suke ikirarin bi ba kalaman su
gaskiya ne, in da sun san darajar daren ranar da
kuma ranar da ake so bawa ya raya da ibadun
da zasu kara kusanta shi da Ubangiji, to da sun
dage don ganin damar da suka samu ta
kasancewa rayayyu kuma masu lafiya a darare
da kuma ranakun juma'a mabanbanta bai wuce
suna masu shagala ba.
Juma'a ce ta uku a wajen Dije, don hatta da
lissafin awannin da suke cikin ranaku basa bace
mata, yanda duk ta hango kuntata a gidan
Baabuga ta wuce hasashen ta, bata saba ba, suna
da yawa a nasu gidan, amman ba irin wannan
yawan ba, kuma bakai kadai ake bari da aiki ba,
taimakawa kawai zakayi, a zamanta gidan Datti
kuwa ba kullum take abinci sau uku ba, fiye da
rabin lokuttan ma a gidan Hammadi sukeyi tare
Lubna sufyan
Hausabook.com 53
da Abu, sai ta dibo nasu ta taho da shi, ko Abun
tace mata karta dora girkin rana, ta saka abinci
da ita. Abu da tayi kewa fiye da tunani.
Amman rashin son kazantar ta yasa sai ta share
filin tsakar gidan na Baabuga sau biyu a rana
duk da babu shafen sumunti, bandaki kuwa
runtse ido kawai takeyi tana wanke iya inda
zata tsugunna, tunda ta ina zaka fara wanke
bandakin kasa? Wata irin jar kasa ce da lokaci
yasa ta hade waje daya, ko kurar kirki bata tashi
idan tana shara, amman ta bandakin batayi irin
ta tsakar gidan ba. Bata kuma damuwa da
zundenta da matan shi sukeyi, don ta kula kishi
sukeyi da ita kamar babu gobe. Da sun san bata
shigo domin ta zauna ba da sun sahirta mata,
duka kwananta uku a gidan suka fara tashin
hankalin sai ta karbi girki. Bata son hayaniyar
shisa ta karba, kwana dai-dai sukeyi da take
ganin kamar awa dai-dai ce, tuka tuwon gidan
da kuma tarin wanke-wanke ba abu bane mai
sauki.
Satin ta biyu akayi dace Abu ta zo ranar girkinta,
ta sameta da dora wannan tukunyar tuwon
gayyar, tana kallo har hawaye Abu ta dinga
Lubna sufyan
Hausabook.com 54
daukewa don karta gani, itama sai ta nuna mata
bata gani din ba. Tayata tayi suka tuka suka
kwasawa kowacce mace kason ta ita da
bataliyar yaranta. Abun nata kallon ta, har kudi
ta kwanto a habar zaninta tana ba Dijen da ta
karba kawai tana ma Abu godiya. In ma ta tsaya
gardama Abu baji zatayi ba, tunda bata san
abinda suka shirya ba, haka bata san tana da
kudin ta da Datti ya bata ba, masu yawan gaske
kuwa.
"Abinda duk kike so ki bayar a siyo miki Dije, ba
iya cin abincin gidan nan zakiyi ba"
Bata kuwa iya ci din, idan ranar girkinta ne da
safe ta dama koko, takan fito da kofi ta diba ta
shiga dakin ta inda take da tulin sikari da farar
alawa, wata ran ta dauke ta tana gutsura tana
kurbar kokon, yan kananan yaran kan bata
tausayi, nasu kokon saita diba a wani bokiti ta
zuba musu sukari, ko ba ranar girkin ta ba da
yake ance kuruci dangin hauka, yaro kuma babu
ruwan shi da mahaifiyar shi bata san ka in dai
kana kyautata mishi, da sun faki idon iyayen
nasu sai taga sun fado dakin ta wai ta saka musu
sikari ko ta basu farar alawar ta, bata taba hana
Lubna sufyan
Hausabook.com 55
su ba, har kudi tana dauka ta basu su siyo yar
alawa.
Badon kowa takeyi ba sai dan kuruciyar yaran,
da kuma yanda take jin ko kishi ya hadata da
wata ba zata iyama yaranta mugunta ba, don shi
da na kowane, watakila ma a cikin yaran
kishiyar ne wani Allah zai nufa da samun arzikin
da zatayi fatan ya ture yan ubanci gefe ya tallafi
'yan uwan shi. A wajen matan Baabuga ba haka
abin yake ba, gani sukeyi kamar yaudara ce da
kissa irin ta mata, don ta fisu samun fada a
wajen miji. A dan zamanta matan duk sun canza,
yan sutturun su da sukan siya da kudaden
sana'o'in hannun da suke yi, can na kasan
akwati suke fiddowa kowacce na caske gayun da
basu sabayi ba.
Matan Baabuga da halayen sune nishadin da
takan samu a kuntataccen gidan shi duk idan
wani uzuri ya fito da ita tsakar gida. Shikuwa
duk daren duniya sai yayo mata kunshin tsire
da rogo mai yawan gaske ya mika mata daki, shi
take ci da dare ta rage har safe ta kara ci, wani
lokaci da fura da tasha nono yake hado mata,
tana kuma jin dadi, har rana ba zata wuni da
Lubna sufyan
Hausabook.com 56
yunwa ba tana jiran dawowar shi. Yawan
hidimar yasa ta fahimci da kudaden Dattin ta
akeyin su, shisa da wani irin nishadi take cin
naman. A ranar kwananta kuwa in Baabuga ta
shigo, kasa take sauka tabar mishi gadon karfen
da aka kai mata.
Wajen ma yayi mata kada don gadon da sauran
tarkacen ta duk ya cike dan dakin da bashi da
girma. In kuwa taji ya maida kofa ya rufe tare da
bugun zuciyar ta yake yin haka, bai taba bi
takanta ba, sai minsharinta da zai tayata hira
har wayewar gari. Wannan juma'ar kuwa itace
ta karshe da zatayi a gidan shi, ita ce kuma
wadda tazo mata a baibai. Ita din bata da wani
jiki, duk da tana da madaidaicin tsayi, amman
siririya ce da in tayi wani aikin zaka iya mamaki
saboda yanayinta bai nuna alamar karfi ba.
Karfin da dagaske bata da shi lokacin da tun
shigowar Baabuga dakin ya mayar da kofa ya
rufe ya zauna akan gado madadin kwanciya kai
tsaye kamar yanda ya saba ya fara kashe mata
jiki.
"Kwana uku ya rage miki da zama a gidan nan
Dije, ina bukatar dukiyar da Datti yai mun
Lubna sufyan
Hausabook.com 57
alkawari dan ita kadai ce damar da nake da ita
na tsayuwa akan nawa kafafun, tun tasowa ta a
karkashin wasu nake..."
Yake fadi kamar mai bata labarin da bata ga
alakarta da shi ba, bata kuma son ji
"Ko ban ciyar dake ba, na baki makwanci, na
kuma taimake ku, ki taimaka mun nima, ki
taimaka mun Dije in dandana abinda nake ta
hasashe tun shigowar ki gidan nan"
Zuciyarta har cikin idanuwanta da suka ciko da
hawayen tashin hankali take jin bugunta,
musamman da Baabugan ya mike yana nufota.
Takasance cikin mutanen da tashin hankali
yake kwacewa sautin murya, hawaye ne dai ke
zubar mata tana kuma matsawa baya, yanda ya
riko damtsen hannun ta tasan bata da karfin da
zata gwada da nashi.
"Allah ya isa tsakani na da kai Baabuga, har
abada ba zan yafe maka ba, Allah ya isa tsakani
na da kai"
Sune kalaman da ta furta cikin kuka da safe da
zai bar dakin, amman ko bi takanta baiyi ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 58
Kuka tayi shi kamar ranta zai fita tun daren har
wayewar gari, bokatan ruwa biyu ta ja a rijiyar
da take can karshen gidan tana wanke
jikinta, amman bata daina jin Baabuga a
wajajen da bai kamata ba a jikinta, a wajajen da
ba hurumin shi bane ba. Wuni tayi kuka, ta sake
kwana tana yin shi, dan ledar daya shigo mata
da ita ko kallon ta batayi ba har wani daren. Ta
cine saboda tazo sallar ishayi ta dinga ganin
wani duhu-duhu da bashi da alaka da dare,
karta halaka kanta bayan wayewar garin zata zo
mata da wani haske na daban.
*
Ta san fara'ar da ta kasa boyuwa a kan fuskarta
ce abu na farko daya fara tona mata asiri a
wajen yan gidan su
"Bakiji maganata ba ko Dije? Allah ya kyauta,
Allah ya kuma yafe mana gabaki daya"
Baba ya fadi bayan ta zo mishi da takardar saki
har uku da Baabuga yayi mata. Baban kuma
yaga dalili kwanaki hudu bayan haka, yaga da sa
hannun Baabuga akayi komai, gonar da ya siya
ba Baba kadai ta sanarwa da Baabuga yayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 59
auren yarjejeniya da Dijen Datti. Cikin kankanin
lokaci zancen auren kisan wutar da Dije tayi ya
karade kauyen Marake. Har mamaki ta dingayi,
yanda mutane zasu dauki abinda bai shafe su ba
suyi ta cece kuce akan shi. Ita yaki take da
zuciyarta, kamar yanda suka tsara da Datti, sai
ta gama iddar ta ne zai zo. Kewar shi ke
nukurkusar ta, ko da ba suyi wata magana mai
yawa ba suga juna.
Amman a kasan zuciyarta tana jin zata iya
daukar wannan dan takaitaccen lokacin, tayi
kewar shi, tayi kewar Julde, dan Abu ita kadai
tazo mata wannan karin
"Fada ya kamata inyi miki idan da gaske na
dauke ki yar uwa, amman banda wannan
zuciyar, in da baki kaso auren nan ba ina gab da
zuwa in kashe miki shi"
Abu ta karasa tana rungume Dijen kafin ta
saketa tana share hawayen, suna kuka yin
dariya gabaki daya. Ko kowa yaji haushin
abinda tayi Abu ta wanke mata komai tas, kafin
ma kwanaki su karasa cika ta koma gidan Dattin
ta. Ta koma kusa da mutanen da take ji fiye da
Lubna sufyan
Hausabook.com 60
wasu a cikin yan uwanta. Innar ta bamai yawan
magana bace bayan
"Allah ya kyauta"
Bata sake furta komai ba, itama Dijen batayi
wani yunkuri na kare kanta ba, sun sani, meye
abin boye-boye. Auren kisan wuta tayi, zabinta
ne, a cikin su babu wanda yasan soyayya balle
tayi kokarin fahimtar da su, dul yayyaenta mata
babu wadda ta auri kamar Datti. Takardar da
Baabuga ya bata sai ta wanke mata abinda yayi
saura na shi da take ji a jikinta, shisa ko
tunaninta bai kara giftawa ta daren ba. Kwana
take tana tashi da farin cikin yanda ranar take
kara kusantata da cikar burinta na komawa
gidan Datti. Hankalin ta ya dauke, bata bi takan
jikinta balle ta kula da sauyin da yayi.
Haka bata zaben abinci, wanda duk taci zama
yake, sai dai ko gyada wani ya ambata sai taji
kamar ranta zai fita yabi ya nemo gyada duk
inda take sannan ya dawo, bata samun nutsuwa,
kudi ta cire ta aika gidan Asibi yayarta da yake
tana siyarwa sai ta soyo mata kwano daya mai
gishi ta zo ta adana tana diba kadan kadan,
Lubna sufyan
Hausabook.com 61
kamar nama haka takan ji gyadar. Bata kuma
damu da rashin ganin al'adarta ba a watan
farko, domin ta canza mata watanni biyu da
suka gabata, ta kara kwanaki shidda kan lokacin
ta, ta kuma kara kwanaki goma ana gaba.
Wannan ma ta dauka hakan ne, kafin ya daidaita tunda batasan dalilin shi na hargitsewar
ba.
Har wani yammaci da Innar A'i kamar yanda
suke kiran abokiyar zaman mahaifiyar su, duk
da A'in ta rasu tana shekara uku. Kuma ba ita
bace yarta ta farko, lakabin sunan yaki barinta
ta kalli Dijen da take zaune tsakar gida tana
tsintar wake, sosai take duban hasken da tayi,
fatarta tayi wani luf ta jefeta da tambayar da ta
razana duka ruhinta
"Dije yaushe rabon ki da ganin al'adar ki?"
A razanen ta dago da bayanannen tsoro a
fuskarta, tana neman nutsuwar da zata rage
gudun da zuciyarta takeyi cike da kai kawo a
cikin kirjinta
"Wancen watan da wanda ya gabata kafin shi
duka nayi karin kwanaki, ta rikice mun"
Lubna sufyan
Hausabook.com 62
Dan murmushi Innar A'i tayi
"To wannan rikicin kam mai motsi ne Dije"
Ai batasan tasan ta mike ba sai da taji salatin
Innar A'i, da kuma karar faduwar kwaryar
waken da take kan jikinta tana fitar da me kyan
tana zubawa a wata, ba'a kai da kwashewa ba
aka sake yin ruwan sama irin na bazatar nan,
duk sai wani yayi duhu cikin waken.
"Ni jikar Takko da Allareeni..."
Cewar Innar A'i tana dorawa da
"Me yake damun ki Dije? Ciki ne fa, rabo mai
girma amman kamar wani mugun abu?"
Ganin hawayen da suka wanke fuskar Dije. A
wajen ta ba ciki bane, a wajenta ba rabo bane, a
wajenta mugun abune a jikinta da zai nisantata
da Datti na tsayin watanni tara da doriya a
maimakon uku rak kamar yanda suka tsara.
"Baabuga ya cuceni"
Maganar zuci ta subuce mata, wasu hawaye
sababbi na zubo mata
Lubna sufyan
Hausabook.com 63
"Wallahi Dije zan kwade ki da mari idan baki
nutsu da wannan haukan ba, ko dan kinga an sa
miki ido? Babu wanda yai miki maganar wautar
da kika aikata?"
Nan tabar Innar A'in tana bambami da yake in
dai wajen tarbiya ne a gidan kowa na da damar
hukunta dan kowa kamar yanda zai ma nashi.
Daki ta shige tana samun waje ta zauna dabas,
yanayin ta zaisa kayi tunanin karshen duniyarta
ne ya zo. Kuka take da yake fitowa daga
zuciyarta, me zata ce ma Datti? Ta karya
alkawarin da ta daukar mishi? Ta so binne
daren su da Baabuga a matsayin tarihin da ba
za'a taba tonowa ba, ba'aje ko ina ba asirinta
yana son tonuwa kowa yagani. A yanda azabar
son Datti ke nukurkusar ta ba zata iya fuskantar
shi ba, kamar yanda ko ba tada niyyar komawa
gidan shi ba zata taba hada iri da Baabuga ba
Zabi daya take da shi
Zabin da shine kuskuren ta na biyu.
Kallon ta Abu takeyi, in da wani yace zata taba
kallon Dije da irin wannan idanuwan zata
karyata, saboda Dije ce, Dije da ko lokacin da
Lubna sufyan
Hausabook.com 64
Datti ya auro ta da kuruciya bata ga alamar
hauka a tattare da ita ba. Ashe dai hauka bashi
da alaka da shekaru? Ashe hauka na iya samun
ka ako wanne bigire na rayuwa
"Haukan da ya same ki kenan Dije?"
Abu tayi maganar tashin hankalin da take ji na
bayyana ta cikin muryar ta, hannu Dije ta kai
tana dauke kwallar da ta taru a gefen idanuwan
ta
"Ba hauka nake ba Adda Abu, ke kadai ce zan iya
tunkara da maganar nan..."
Numfashi Abu taja, wata dariya mai sauti da
bata da alaka da nishadi tana subuce mata
"Saboda ni kadai ce ban taba ko batan wata ba
balle in san zafin haihuwa...shisa ko?"
Kai Dije take girgizawa tunda Abu ta fara
magana, har ga Allah ba haka bane nufin ta,
kamar yanda tace ne, babu wanda zata fara
tunkara da maganar tana son zubar da cikin da
yake jikinta
Lubna sufyan
Hausabook.com 65
"Me yasa to? Me yasa zaki tunkare ni da wannan
maganar? Na dauka zaki fi kowa sanin nice
karshen wadda ya kamata ki tunkara da cewa
kin samu rabon da ya isheki a duniya har kike
neman zubar da wani"
Wannan karin barin hawayenta tayi suka zubo,
saboda idanuwan Abun ma cike yake taf da
hawaye da wani kwantaccen bakin ciki da Allah
kadai yasan shekarun da tayi tana dauke da shi
"Karki ce haka Adda...Julde kadai gare ni, kin
san shi kadai ne..."
Numfashi Abu ta shaka ta bakinta saboda
hancinta ya toshe da wani abu da ba zata iya
fada ba
"Da alama ya isheki, shi kadai din"
Da zata iya da ta ciro abinda yake cikin Dije ta
mayar a nata, a lokacin da wani yake nema ido
rufe, yake nema da dukkan zuciyar shi a gefe
daya, a dai-dai irin wannan lokacin wani yake
samu yana kuma neman maraba da shi. Idan ba
Allah ba waye zaiyi haka? Duka bangarorin biyu
Lubna sufyan
Hausabook.com 66
Yana sane da su, bai kuma manta da su ba,
saboda dukkan su a cikin jarabawar Shi suke.
"Ba haka bane ba, ba haka bane ba.. Ba zan iya
hada jini da Baabuga ba, ba zan iya ba... Ba zan
iya ba Adda..."
Ta karasa maganar muryarta na sarkewa
saboda dacin da take ji
"Jini ne ba zaki iya hadawa da Baabuga ba ko
kuma cikin da zai hanaki komawa gidan Datti ne
bakya so? Ki fadama kanki gaskiya...ki bude
zuciyarki ki duba gaskiya..."
Ba sai ta bude zuciyarta ba, amsarta a bayyane
take, dula dalilan biyu ne, mikewa Abu tayi tana
saka gefen mayafinta ta dauke kwallar da take
shirin zubo mata
"Dije kar wannan ya kara zama kuskuren ki...in
dai cikine zaki zubar to ba da hannu na ba, ba
kuma da goyon baya na ba"
Bata ma bata wata dama ba ta fice daga dakin,
da akace ga Abu nan, ta jiyo muryarta har wani
sauki-sauki taji, ya Abu zata juya mata baya a
wannan bigiren da tafi bukatar ta? Babu yanda
Lubna sufyan
Hausabook.com 67
za'ayi ta fita, ko meye ya faru tasan ba za'a taba
bari ta fita batare da ta cika kwanakin iddarta
ba, amman lokacin da zata cika kwanakin iddar
lokaci ne da komai zai iya sake cakude mata. Ga
idanuwa da Innar A'i ta saka ma duk wani motsi
da zatayi, ko abinci sai ya zamana sai Innar ta
duba ake bata shi, ko aike tayi sai tace a miko
mata ledar ta duba taga meye a ciki.
Kuka ne abokin hirarta duk dare kafin baccin
wahala yayi awon gaba da ita, tayi ciki ba daya
ba, ba biyu ba, amman wannan bata laulayi,
ciwo ko na girar ido, gyada ce da ta dauko tun
washegarin ranar da ta gane akwai cikin ta
rabarma yaran gidan ita tas, kilan wannan ta
zama sanadin da zai fita, sai dai me, kamar
mahaukaciya kwana biyu a tsakani dole ta sake
fitar da wasu kudin ta bada aka nemo mata
gyadar, shine ma tana gama ci tayi amai kamar
zata amayar da kayan cikinta. Tun daga lokacin
saiya zamana ko ambaton gyadar bata so ayi.
Zuwa kuma yanzun kowa da yake gidan yasan
tana dauke da juna biyu, babu dai wanda yayi
mata maganar.
Lubna sufyan
Hausabook.com 68
Kamar wasa haka kwanaki suka dinga wucewa
da ita batare da ta samu tsayayyar mafita ba har
ranakun iddarta suka cika. A ranar kuma Datti
ya aiko kiranta, daman jiran shi takeyi, Allah
kadai yasan jigatar da tayi da kewar shi a tsayin
watannin nan, bata damu da fadan da Baba zai
iya yi ba, batama jira wani yace komai ba, ko
mayafin da ta dauka sa da takai soron gidan ta
yafa shi, tana fita tagan shi tsaye, jikin shi sanye
da rigar saki da farin wando na hadi, hasken
farin wata na haske mata fuskar shi tar,
murmushi ne ya kwace mata, kafin hawaye su
cika mata idanuwa, shima murmushin yayi
mata.
Jikin shi na bari da son riko ko da hannun tane,
tun kafin Hammadi ya fada mishi ya rame yaji
fuskar shi ta fada
"Nayi kewar ki, sosai nayi kewar ki"
Ya fadi muryar shi na fitowa a raunane, itama
tayi kewar shi, siraran hawayen da suka zubo
matane ta bari suka sanar da shi haka don ta
kasa magana, wasu yanayoyi ne take ji da bai
kamata ace sun hade mata a lokaci daya ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 69
"Gobe zan samu Baba da maganar auren mu, ya
mayar mun dake, ya dawo mun dake Dije ko zan
samu nutsuwa"
Wannan karin wani irin gunjin kuka ne ya
kwace mata da ya fito daga lungun zuciyar ta,
cikin tashin hankali Datti yake kallon ta,
musamman da yaga ta durkushe tana zama kan
dakalin da yake gefen gidan nasu saboda
kafafuwan ta da suke barazar kin daukarta,
shima zama yayi a gefe, sai dai maganar duniya
da yayi mata baisa ta dago ba, saima sautin
kukan ta da yake karuwa, wani irin kuka da bai
taba ganin tana yin irin shi ba duk zaman su, ko
da kuwa yayi mata fadan nan nashi da yake daga
mata hankali, yau nashi hankalin ne a tashe.
Babu kalar tunanin da baiyi ba, har mamakin
sauri irin na kwakwalwar shi yayi, saboda
gudun aikin da takeyi mishi a cikin dan
kankanin lokaci haka, kafin kalaman Dije su
tsayar mishi da komai, idan yace komai yana
nufin har da bugun zuciyar shi na dakika kafin
tayi wani tsalle tana neman hanyar fita daga
kirjin shi gabaki daya
Lubna sufyan
Hausabook.com 70
"Ina dauke da juna biyu..."
Kalaman suka sake dawo mishi kamar saukar
aradun da bai taba yarda yana faruwa ba tunda
bai taba cin karo da hakan ba, kafin wani duhun
kishi ya lullube shi, duhu fiye da na dararen da
kan samu saukin nasu da hasken farin wata ko
na taurari, baisan ya tashi daga kusa da ita ba,
sai da ta dago jajayen idanuwan ta tana saukewa
cikin nashi yana ganin nisan da sukayi ma juna
lokaci daya
"Me yasa? Abu daya na roke ki Dije...me yasa
zaki hadamun jikin ki da na shi?"
Mikewa tayi, saiya matsa taku biyu baya, yana sa
bugun zuciyar ta yana karuwa
"Dan Allah Datti"
Kai yake girgizawa, kwakwalwar shi na hasko
mishi hotunan Dije da Baabuga batare da ta
tausaya ma halin da zuciyar shi take ciki ba,
idanuwan shi ya runtsa yana bude su. Ya sake
runtsa su saboda wani hawayen bakin ciki da
yake jin yajin su cikin idanuwan shi, ashe akwai
sauran abinda zai iya bayyana hawayen shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 71
haka? Wannan karin shine ya tsugunna, yana jin
kamar ana zarar wani abu tare da shi, da farin
ciki ya wuni, zuciyar shi cike taf da shi, ya daren
shi zai juye haka? Ya zaiji zuciyar shi ta fada
wani waje da yake jin ganota zaiyi masa wahala.
Hawaye ne wani nabin wani yake zubo ma Dije,
ganin yanda Datti yake kokawa da numfashin
shi, sai ace zuciya bata da kashi, sai ace tsoka ce
zalla, abinda take ji yana karyewa cikin kirjinta
yanzun fa? Meye shi? Abinda take gani yana
karyewa yanzun a tare da Datti menene shi?
"Ina so in zubar... In zubar da cikin, tun da nasan
da shi nake so in cire shi... Bansan ya zanyi
ba...kuskure ne...wallahi ba yanda zanyi"
Sai da Datti ya dafa kasa sannan ya iya mikewa,
a sarari yake, fili ne gaban shi da bayan shi, sai
dai yana kallon Dije yaji kamar tayi masa
katanga da samun wadatacciyar iska. Juyawa
kawai yayi yana jin yanda take kiran shi amman
ko juyawa baiyi ba. Tafiya yake da Dije take jin
takun ta kamar a cikin kirjinta da yake kara
daukar dumi. Dakyar ta iya komawa cikin gida
tana wucewa daki kai tsaye, maganar da Innarta
Lubna sufyan
Hausabook.com 72
take mata ma bata tsaya ta saurara ba, tana
shiga ta samu wajen lungun gadon Innar ta
zauna tana jan kafafuwanta ta hade su da jikinta
hadi da sakin wani irin kuka mai cin rai.
Ba zata gaji da aika ma Baabuga Allah ya isa na
yanda ya canza musu komai a dare daya ba. Ta
tashe ni, ta tsani abinda yake cikinta. Haka Inna
ta shigo ta sameta tana kuka kamar an labarta
mata mutuwar Innar ko ta Baba
"Kinga ki sahirta ma kanki wannan damuwar
Dije, lamari na duniya a hankali ake bin shi,
musamman abinda baka isa ka sauya ba...kiyi
hakuri kibi komai a sannu"
Maganar ta kunnen haggunta ta shiga tana bi ta
dama ta fice batare da ta samu wajen zama ba,
wacce duniya ce zata bi a hankali? Duniyar da
batayi mata adalci ba? Me zata bi a hankali, daga
sakin ta zuwa yau, babu wani abu guda daya da
yazo mata da sauki, sai ita ce zata bi komai a
hankali? Wannan magana ce da bata da
hankalin daukarta a yanzun. Runtse dai bata
runtsa ba, dan sai cikin dare ta samu tayi sallar
isha'i, da alwalar ta mayar da asuba tana
Lubna sufyan
Hausabook.com 73
kwanciya dakyar. Koko da kosan da aka kawo
mata haka akazo aka dauke da rana da aka
kawo mata wake da shinkafa da ya sha man
gyada, ko yunwar ma bata ji, dakyar ta iya
mikewa ta dauro alwala tazo tayi azahar.
Tashin hankalin da take ciki bai bari ta tuna da
wani wani wanka ba, da la'asar ta idar da Sallah
kenan Innar A'i ta shigo tana jingina bayanta da
bangon dakin
"Kinki cin komai duk yau Dije, in baki duba
kanki ba, ki tausaya ma abinda yake cikin ki kici
wani abu dan Allah"
Ta san Innar ta ce ta turo Innar A'in, wasu
hawaye masu zafi suka zubo mata, takai hannu
tana dauke su
"Kiyi hakuri, watannin zaki ga sun wuce kamar
kiftawar ido in dai Allah ya bamu aron rayuwar,
kiga kin koma dakin mijin ki kamar komai bai
faru ba, amman in kika rasa lafiyar ki fa?"
Haka Innar A'i ta dinga bata baki, a cikin
maganganun babu wanda suka fi mata tasiri irin
jin zancen komawarta gidan Datti, shisa ma
Lubna sufyan
Hausabook.com 74
harta dauki kwanon abincin, aikuwa tas ta cinye
shi, tana dorawa da furar da Innar A'in tasa aka
kai mata, sai taji wani karfi na daban yana
shigarta, da kuwa shafal take jinta. Bata sake
samun wani karfin ba sai da aka aiko kiranta
bayan isha'i, har tuntube tayi garin sauri, innar
ta zatayi magana Innar A'i ta girgiza mata kai
tana dorawa da
"Ki rabu da ita, in ta ganshi ta samu nutsuwa,
yaran yanzun na da bambanci da mu, in aka
matsa mata mu duka lamarin ba zai mana dadi
ba"
Bayan Dijen ta fita ta samu Datti tsaye kamar
jiya, sai dai fuskar shi ta kumbura kamar wanda
yaci kuka. Wata yar leda ce ya zaro daga cikin
aljihun shi yana bata.
"Kulli daya zaki juye duka a ruwa ki sha yau, ki
kara juye dayan ki sha gobe"
Karba tayi da sauri, sai dai bai jira amsarta ba ya
juya. Tsaye tayi bata koma gida ba saida ya bace
ma ganin ta. Jikinta bari yake sanda ta koma
cikin gida, sai take ganin kamar wani zai ganta,
kasa samun nutsuwa tayi har sai da dare ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 75
raba, tukunna ta iya shan maganin, washegari
ma bata samu wani sarari ba sai Magriba.
Aikuwa wajen karfe daya wani irin ciwon mara
da yasa ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 27