ya karya wani
bangare na zuciyar shi, saboda ta saka shi
hasaso ace masa ya hakura da auren Mero, ko
kuma a musanya masa auren nata da wata duk
kyawunta da kyawun halayenta. Sai yaji ko
Marake zata hade abune da ba zai taba yarda
dashi ba
"Kiyi hakuri..."
Ya furta da sanyin murya wannan karin, sai tayi
dariya, dariyar da yake juyowa har yanzun,
saboda ta zama kamar itace dariyarta ta karshe
da yaji
"Kaunar da nake maka mai yawa ce Hamma, kai
dai ka yafe mun kawai...sai yaushe zanga Meron
ka?"
Ta karasa tana canza akalar zancen. Da yasan ba
za'a ganta kafin Mero ta shigo gidan shi ba, da
yaja hannunta ya kaita sun gaisa, sai dai da
yasan zasu nemeta su rasa din a washegari da
idan ya jata ya kaita taga Mero ba zai taba bari
Lubna sufyan
Hausabook.com 342
ta bacewa ganin shi ba balle har suzo inda suke
yanzun. Kanwar shi, tilon kanwar shi da yanzun
yake kara fahimtar tarin kaunar da yakeyi mata
"Ba'a ganta ba ko?"
Saratu ta tambaye shi, idanuwanta cike taf da
hawaye, kai ya girgiza mata, a karon farko tun
da aka fara nemanta yanajin idanuwan shi sun
ciko da hawaye, hakan Saratu ta gani ta riko
hannun shi, fisgewa yayi yana sake girgiza mata
kai, ta kara rikowa, wannan karin tana kamo
duka hannuwan nashi
"Ina Yelwa zataje Saratu? Ina zataje haka bata
fadamun ba? Auren Mero ya dauke hankalina
har haka ne? Ta nuna alamun da idona ya rufe
bangani ba?"
Kai Saratu take girgiza masa, ita kanta batan
Yelwa ya maye mata gurbin duk wani tashin
hankali da auren nashi ya haifar mata. Mutanen
da take so a rayuwarta basu da yawa, zata iya
kirgasu da yatsun hannunta, Yelwa na daya daga
cikin mutanen nan. Ko ranar da ta kwanta,
tunaninta bai kai na yanda Julde baya tare da ita
akan gadon nasu ba, bai kai ga yana wajen Mero
Lubna sufyan
Hausabook.com 343
ba, balle tayi tunanin yanda ranar ne karon
farko da zata rabashi a matsayin miji da wata.
Gajiyar ranar da taji ta saukar mata gabaki daya
bayan ta kwanta, laushin katifar na saka jikinta
amsawa da wani yanayi mai dadi duk kuwa da
zuciyarta da take a cunkushe. Sai tunanin Yelwa
ya sake danneta, ina take? A wanne hali? Ta
samu inda zata kwanta? A wanne irin yanayi?
Sai hawaye suka cigaba da saukar mata, wani na
bin wani. Me yasa ba tayi magana da Datti akan
auren Modibbo da Yelwar ba taga ko ita zata iya
sauya ra'ayin shi? Ko ita zai saurareta tunda
yaki sauraren Yelwa. Babu kalar tunanin da
baizo mata ba, kafin gajiyar dake nukurkusar
jiki da ruhinta suyi galaba akanta bacci ya
dauketa.
"Da na saka ido akanta..."
Muryar Julde ta sake kutsawa cikin tunaninta,
kai ta girgiza masa, tana hade tazarar dake
tsakanin su, duk da cikin jikinta ya sake saka
musu wata tazarar, yana hana mata riko shi
jikinta yanda zuciyarta take sonyi
Lubna sufyan
Hausabook.com 344
"Ka daina, dan Allah karka dora laifin nan
akanka..."
Hannuwan shi ya zame ya tsugunna, yanajin
duka gwiwoyin shi sunyi masa sanyi, dakyar ta
samu itama takai kasa tana zama. Tana kallon
yanda yake kokawa da numfashin shi kafin ya
mike. Batayi yunkurin masa magana ba balle ta
hana shi, shiya shigo dakin da kanshi. Yana fita
wajen dakin Mero ya nufa, ya sameta a kwance,
tana shirin mikewa ya bita kan gadon ya kwanta
a gefenta
"Nagaji sosai"
Ya furta cikin karamar murya, saita kai
hannunta tana dorawa akan fuskar shi, lallashin
shi take so tayi, wani nata bai taba bacewa ba,
ba zatayi karyar hasaso yanda yakeji ba. Kamar
jira yake ta tabashi, wasu siraran hawaye suka
zubo masa, kirjin shi yayi nauyi fiye da yanda ya
tabayi lokacin rasuwar Hammadi. Akwai
bambanci a wancen rashin da wannan, tunda
dashi aka zuba ma Hammadi kasa har aka rufe
shi ruf, yasan inda yake, ko yanzun yaso zaije
makabartar, har gaban kabarin yayi masa
Lubna sufyan
Hausabook.com 345
addu'a. Amman Yelwa fa? Ba zai ce ga halin da
take ciki ba ko inda take balle ya fara nemanta.
"Idan ba'a ganta ba fa?"
Ya tambaya
"Za'a ganta, zata dawo..."
Mero tace masa, bai yarda ba, amman
kalamanta sun dan nutsar dashi. Kamar yanda
ya nemi samun nutsuwa a tare da ita. Sai ya
waye garin, kamar sauran dararen da ya raya
tare da ita. Wata irin nutsuwa ce da bai taba
tunanin ana samu tare da mace ba. Da farko ya
dauka mantar dashi tashin hankalin da yake
cikine na kankanin lokaci da yayi. Sai dai kamar
komai, batan Yelwa ba ciwo ya daina musu ba,
sabawa sukayi da ciwon. Meron ce daban, ita din
da kanta ce yake jin ta bambanta da duka
sauran matan da ya taba mu'alama da su. Sai dai
me, ya dauka ta ishe shi, a zuciyar shi Mero ta
ishe shi, bashida wani waje da zai sake saka
wata mace kuma da sunan aure.
Inda ba'a hada shi da Saratu ba, Mero ta ishe shi
a matsayin mata, kawai wata murya ce a cikin
Lubna sufyan
Hausabook.com 346
kanshi take saka masa alamar tambayar ko
akwai mata kamar Mero? Ko akwai wanda suka
fita? Duk idan zaiga wata macen ta wuce sai
tambayoyin su cigaba da yi masa yawo. Kuma su
suka sake janshi ya koma bin mata watanni
shidda bayan auren su da Mero. Bai san tana da
kishi ba sai daren daya dawo taga sawun labba
da jambaki a bayan wuyan shi.
"Saika nuna mun abinda kowa yake gujemun da
aurenka Julde? Saika shigomun da tambarinta
cikin daki? Ba zaka iya wanke jikinka daga
daudar daka kwaso ba zaka hawomun gado
kana neman hada jikina da naka?!"
Ta karasa tana hankado shi daga kan gadon
cikin karfin da bai taba sanin tana dashi ba,
kokarin tambayarta yakeyi abinda tagani a jikin
shi tunda baisan da jambakin ba, kamar ya
tunzurata, ta cigaba da hauka kamar wadda
jinnu suka shafa, dakyar ya iya riketa ganin
kamar tana neman abinda zata illata shi dashi,
saida yasa karfi sosai tukunna ya iya riketa,
saita fara wani irin kuka daya rikita masa lissafi
Lubna sufyan
Hausabook.com 347
"Na daina, kiyi hakuri dan Allah, ba zan sake ba
Mero, ki kalle ni...ba za sake ba"
Yake fadi yana rike fuskarta da tasa
hannuwanta akan nashi tana kokarin kwacewa
"Ba zan sake ba..."
Yake fadi yana maimaitawa, yana so ya yarda da
kalaman shi fiye da yanda yake so ta yarda
dashi. Tana son Julde, tana masa wani irin so da
kafin ta shigo gidan shi taga wanda Saratu
takeyi masa ta dauka ba zai misaltu ba. Sai
yanzun da take hadiyar abinda tasan Saratun ta
shanye a shekarun zamanta dashi takejin ba
zata iya ba, mutuwa zatayi, zuciyarta fashewa
zatayi ta mutu. Saratu bata shiga harkarta, idan
ita ta gaishe da ita zata amsa, amman idan
batayi mata magana ba, ko inda take bata taba
kallo. Idan kuma tace bata kishin Saratu zatayi
karya, ga yaranta masu kyau, tana gidan ta haifi
Fadila. Ranar farko tana tsakar gida a bakin
kofar dakinta, Saratu takai ruwan wanka,
amman Fadila ta ki barinta ta shiga wanka
saboda kukan da takeyi
"Ko ki kawo in rike miki ita?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 348
Ta fadi, yanda Saratu ta kalleta sai taji tsoro, sai
dai ga mamakinta, kwanto Fadila tayi daga
bayanta tana karasawa ta mika mata ita, ta juya
abinta. Ta dauka Salim da baya zuwa wajenta ko
ta masa magana, Saratu ce ta hana shi, abinda
bata sani ba shine, Saratu bata sonta don so,
inda za'a bata zabi zata zabi tabar mata gidanta
da mijinta. Amman bata da wannan zabin,
yarane kona rana daya bata saka a ranta Mero
zata cutar mata dasu ba. Abu ta wanke mata
wannan shakkun daga ranta. Labarai takeji
akan kishiyar uwa, inda za'a bawa wani labarin
yanda Abu ta riketa zai iya karyatawa, yace ba
gaskiya bane ba, shisa itama ta zabi ta shure duk
wani mugun labari.
Tun daga ranar kuma in dai zata bukaci daukar
Fadila, Saratu bata hanata, saita je har kitso
tabar mata Fadilan, ba dai ta shiga harkarta ko
kadan.
"Yar uwata ce Mero, ko ban auri Saratu ba 'yar
uwata ce...zan rokeki, ki zauna lafiya da ita
gwargwadon yanda zaki iya..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 349
Shine rokon da Julde yayi mata. Koshi yayi
mamakin da a cikinsu babu wanda ya taba kai
masa karar dan uwan shi, Saratu ta bashi
mamaki. Sai wata kimarta da bai taba tunanin
zai gani ba ta ginu a zuciyar shi duk da
soyayyarta har lokacin ta kasa samun waje.
"Na daina, ba zan sake ba"
Sune kalaman shi, ta haddace su, amman ta dade
da daina yarda dasu. Da ta auri Julde ta aure shi
da halin shi, amman a kasan zuciyarta ta aure
shi da nufin soyayyar da taga yana mata ta canza
shi, ita zata canza shi, zatayi abinda matar shi ta
gida ta kasa. Sai yanzun ta gane babu yanda zaka
canza wanda baya so ya canza, babu wata
soyayya da ta isa ta canza halayya in har babu
niyya, idan da niyya soyayyar ko yanayin saiya
zama tsani na canjin, taimako kawai zaiyi bashi
bane jigo. Jigon canji na kowanne irin hali shine
niyya, niyyar nan itace komai.
Idan ta kalle shi taji wani ciwo da yake taso
mata tun daga dan yatsan kafanta har kasan
zuciyarta sai ta dinga hasaso barin shi, ko ta
tafiyarta ta huta, tabarshi da matan da ya zaba
Lubna sufyan
Hausabook.com 350
akanta, akan su iyalin shi. Amman abubuwa da
yawa sai su riketa, kalaman shi, nadamar shi
kowanne lokaci ta sake kamashi kamar ba zai
kara ba, soyayyar da take masa da take sakata
jin kamar ta yafe mishi, kamar zata cigaba da
yafe mishi a kullum. Musamman da ta samu ciki,
sai kulawa da soyayyar da yake nuna mata suka
karu, kamar bashi da wasu yaran, kamar a tare
da ita zai fara samu.
Tana son abinda yake cikinta tun kafin tasan
jinsin shi, amman kalar soyayyar da Julde yake
nuna ma abinda ke cikin sai ya sake ninka mata
kaunar da takeyi masa. Gajeriyar nakuda tayi,
kuma mai sauki, cikin kasa da awa biyu har tayi
ta gama. Da taimakon Dije da kuma matan
Baabuga guda biyu da suka zo, da aka saka mata
yaronta a hannu sai da ta faki idon mutane ta
share kwallar farin cikin da ta silalo mata don
kar ace tayi rashin kunya. Amman murmushin
dake fuskarta yaki bacewa, ta kuma kasa daina
kallon shi.
Addu'arta ta amsu akan yaron da yaci suna
Aliyu, take kuma kiran shi da Haidar. Yayi kama
da Julde, yayi kama da sauran yan uwan shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 351
Salim da Fadila. Ta kuma ci albarkacin Haidar,
Salim na zuwa wajenta saboda yaron, duk da sai
tayi masa magana hamsin sai taci sa'a zai
amsata sau biyu, zai daga kai ya kalleta sai ya
dakuna fuska, a yan shekarun shi yana nuna
alamar kamar bayason hayaniya, kamar
sautinta yayi masa yawa a cikin kunne, tunda
wani lokacin zata ga idan baki tayi, yan uwanta
daga gidan Baabuga, yana zaune a dakin, zai
takai dan yatsa kunnen shi kamar mai son toshe
hayaniyar su, karshe zai riko gefen zaninta yana
nuna mata Haidar, in ta dauke shi zai tashi ya
fice daga dakin.
Tana son yaron, yanda yake komai nashi kamar
ya girmi shekarun shi, komai ma a tare dashi,
tsayin shi, nutsuwar da zaka gani a fuskar shi da
rashin son hayaniyar shi. Har ranta taji dadin
yanda Saratu batayi mata katanga da yaran nata
ba, bata kuma yi musu katanga da nata yaron
ba. Zata so zumuncin su ya dore
Sam bata hango inda lokaci ya saka ma alakar su
aya ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 352
Kamar yanda batayi tunanin zamanta da Julde
ba mai dorewa bane ba
Shisa ta kara mike kafafuwanta, ta sake bude
zuciyarta tana karbar sabuwar soyayyar da
Julde yake nuna mata sanadin Haidar, kulawar
shi kamar ba zai kara bata mata rai ba, kamar
sabani ba zai sake shiga tsakanin su ba. A dan
lokacin, idan ma ya koma halin shi, to yana iya
bakin kokarin shi wajen boye mata. Hakan yayi
mata, kar taji, karta gani kuma. Bata son duk
wani abu da zaizo ya birkita mata kwanciyar
hankali da ta samu. Larabarta a nutse tazo mata,
shisa bata hango juma'arta zata zo da wani abu
akasin abinda larabar ta wanzar mata ba. Tana
zaune a kofar dakinta tana kallon Haidar da
take jin kamar a cikin zuciyarta yake rarrafen
da yakeyi, kaunar shi na cika mata zuciya.
"Kiyi mun addu'a, akwai abinda nake shiryawa,
idan harya tabbata zamu bar Marake, Mero
zamu koma Kano ko don su Haidar, ina so su
samu ilimin da ban samu ba, ina jin kamar ba
zasu mori tarin dukiyar da nake da ita a kauyen
nan ba..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 353
Saita tsinci kanta da hasaso mafarkin shi, itama
ko basu bar Marake ba, tayi ma kanta alkawarin
Haidar saiya samu ilimin addini dana boko,
saiya cika mata burinta data watsar saboda
soyayyar Julde
"Assalamu alaikum..."
Taji muryar da ta roka mata aminci amman
babu amincin a tare da ita kwata-kwata.
Zuciyarta ta dunkule tana gangarawa ta tsaya a
dai-dai kafafuwan Talatu, kafin ta daga kai ta
kalleta, ta cogalo daurin dankwalinta gaban
goshi, mayafinta akan kafada, fuskarta tasha
kwalliyar da ko cikin dare ka farka saika ganta a
furkar Talatu. Da cingam abakinta da take
taunawa cike da duniyanci. Talatu, itace Autar
su Musa da rikonta ya koma hannun shi tun
farkon auren shi, shekaru takwas ta baiwa
Mero, lalacewar da Musa yaga zatayi yasa shi yi
mata auren da ta kaso a watanni hudu kacal da
yin shi, bayan nan aurenta hudu, harda na
farkon biyar. Na karshen ne Mero tana da cikin
Haidar taji labarin Talatu ta kaso shi shima.
Lubna sufyan
Hausabook.com 354
Ko da tana gidan Musa, idan Talatu ta kaso
aurenta tafi kowa shan wahala, haka kawai ta
dauki karan tsana ta dora mata, kamar kishi
takeyi da ita, duk wani abu da zata gani a
wajenta in bata rabata dasho ba sai ta samo irin
shi sak, ko dinki Mero tayi sai Talatu tayi irin
shi. Sai daya suka hadu tunda Meron tayi aure,
tunda sau daya taje ganin gida da tayi arba'in
din Haidar
"Ke kuma duk bokon sai kikaci baya? Kika bar
binni kika tafi kauye aure?"
Yanda Talatu tayi maganar zaka rantse ba kauye
bane asalinta, Mero murmushi kawai tayi bata
tanka ba, ta dai kula da yanda Talatu take ta
kallon Haidar, tunda kayane masu kyau da
tsada, irin na binni Julde yake bayarwa a siyo
musu, daga ita har shi da suke a kauye sunfi
Talatun kyawun gani
"Yau dai gani a gidan ki"
Cewar Talatu, tana tsugunnawa ta dauki Haidar,
sai Mero ta kasa amsa mata sallamar da tayi
mata, ta kasa ko da yi mata murmushi, saboda
zuciyarta na gaya mata zuwan Talatu ba alkhairi
Lubna sufyan
Hausabook.com 355
bane a wajenta, saboda Talatu bata da wani
dalili da zata kawo mata ziyara tun daga Kano
har Marake.
Hasashenta gaskiya ne
Hasashenta baiyi mata karya ba
Zuwan Talatu dai-dai yake da hargitsewar gidan
aurenta...
Duk yanda ake fada mata rashin tabbaci na
rayuwa bata taba yarda ba, idan misali akayi
mata da mutuwa sai wasu tambayoyin su
cunkushe mata, ko idan mai lafiya ya shiga halin
rashinta, mai dukiya ya rasa dukiyarsa, sai a
dinga fadin rayuwa kenan, bata da tabbas. A
cikin wannan abubuwan bata ga dalilin da za'a
kira rashin tabbaci ba, rai ne dai kowa yasan
bakone a duniya, iya lokacin da aka dibar masa
na bakunta yake jira, haka dukiyar, itama aro ce
aka baiwa wasu zababbun mutane, lafiyar ma
haka. Babu abin mamaki don an rasa daya a ciki,
daman tun farko ansan da rashin tabbacin su.
Lubna sufyan
Hausabook.com 356
A cikin jerin abubuwan da Mero bata dorawa
rashin tabbaci ba shine auren Julde, duk yanda
kowa yake da shakku akai, duk irin
maganganun da aka dinga fada mata tana saka
kafafuwa tana turewa, duk irin yanda halayen
shi basu sauya ba kamar yanda tayi tsammani.
Da hannuwan shi akan fuskarta, idanuwan shi a
cikin nata yace
"Ina son ki Mero, halayena nawa ne, kar rashin
canza su ya sa ki dauka son ki bai kai bane ba,
ina son ki, ko na miki laifi karki manta ina son
ki, ko da ban fada miki kullum ba, ko da wasu
ranakun ban nuna miki a aikace ba, ina son ki, a
kowanne yanayi zamu tsinci kanmu Mero, sonki
na daga cikin abinda nake ji zai kasance tare
dani har karshen rayuwata ko da komai ya
barni"
Kalaman shi suka zauna mata, kamar yanda
bata manta da amsar da ta bashi ba
"Halayenka ne karshen abinda zan duba a
zamantakewar mu, zuciyata taka ce, kasani.
Kowa da ya isa dani ya sani, saboda akan
soyayyar ka na fara nuna musu basu isa dani ba,
Lubna sufyan
Hausabook.com 357
halayenka ba zasu sa in barka ba, yanda basu
sakani kin fara rayuwa da kai ba"
Ashe bashi kadai ta yaudara ba harda kanta,
harda zuciyarta da bata taba hango mata
halayen shi zasuyi muni ba, basu taba hango
mata bakar ranar da zata kafa mata tarihin da
bata fatan ya maimaita kanshi ko da a
mafarkinta ne
"Kanwar mahaifiyata Julde..."
Muryarta ta koma cikin kunnenta da wani irin
yanayi, kamar ruhinta ya bar jikinta ya koma
gefe yana son gangar jikinta kadai ta tabbatar
da abinda ta gani. Tunda Talatu tazo gidan
kwanaki biyu da suka wuce bata da sukuni, ta
daina zama tsakar gida saboda haka kawai take
son takaita ganin da Talatu zatayiwa Julden. Sai
dai yau din girki ya zagayo kanta, bata da wani
zabi, tare da Talatu suka fito da safe duk kuwa
yanda tayi fama da ita akan zatayi aikinta ita
kadai, duk kwana biyun da tayi ai ita kadai take
musu girkin da zasu ci, bata ga dalilin da yau din
zata tsiri son tayata ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 358
Yanda ta sake kasa da murya da suka gaisa da
Julde ya mata wani iri, ta daga kai ta kalli Julde,
sai dai idanuwan shi akanta suke, ya hade
girarshi waje daya cikin wani yanayi da take
yawan gani a fuskar Salim idan tayi masa
magana, kamar a takure yake, kamar yana so ya
roketa da ta ganshi taki ganin shi, ta ganshi
karta kula shi. Abinda bata sani ba shine ba'a
gidanta Julde ya fara ganin Talatu ba, yana da
rike fuskokin mutane, shisa yana shigowa ya
ganta yasan bashi bane karon shi na farko. Duk
da akwai sauyi a tare da ita, wannan Talatun ta
kara wayewa.
Kwana yayi yana tunanin inda ya taba ganinta,
sai washegari da yazo fita ta tare shi tana dubedube kar Mero ta fito, cikin hanzari tace mishi
"Ba bafullatanin J-town bane? Ko bakai bane na
taba gani a dakinta?"
Rabata yayi ya wuce, kwakwalwar shi nayi masa
tariyar dararen shi a sabon gari, a tsakanin
dakunan matan da yayi mu'amala dasu, yana
tuna J-town, wata yarinya yar garin Jos da
akewa laqabi da sunan garin da ta fito din. Ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 359
tuna inda ya santa yanzun, don ta matsa daf da
inda yake zaune a dakin J-town ta dora kanta a
kafadarshi tana riko hannun shi, ta sauke murya
tana fada masa kalaman da yake tsammanin
dasu take amfani wajen karkatar da hankulan
maza akanta, su sake mata jikinsu da bakin
aljihunsu tayi yanda ta ga dama dasu.
Ba zaice batayi masa ba, itama macece, kuma
kamar ko da yaushe yana so yaji ta inda ta
bambanta da sauran, shisa ya biye mata. A ranar
ya sake sanin kishi irin na matan bariki, yanda
sukayi baram-baram da J-town har ana rirrike
su zasu gwabza su gwada karfi. Ya dauke mata
kaine saboda a karo na biyu da muryar nan da
take manne dashi ta rada masa son sake
kasancewa da Talatu, ya manta yanda take,
yanzun da yake neman mace irin Mero, kowama
bi yakeyi batare da dogon tunani ba. Amman
Talatu na da alaka da Mero, duk da har yanzun
bata fayyace masa ya alakar tasu take ba.
"Ina bakuwar ki?"
Ya gwada tambayarta, yanda ta amsa masa
kamar bataso bakinshi ya sake furta wata
Lubna sufyan
Hausabook.com 360
magana data danganci Talatu yasa shi fasa
tambayar yanda suke da ita. Tunda kusan kowa
da yake gidan Kawunta ya sansu a bakinta, ya
kuma ga wasu. Amman bai tabajin ta ambaci
Talatu ba, watakila halayen Talatun ne dalili. Ya
kudiri niyyar kaucewa duk wata hanya da zata
hadashi da Talatu har lokacin da zata bar gidan
tunda yasan bashida iko da halinshi, sanda zaiyi
wani abin da zai iya ja masa matsala ba zai sani
ba sai bayan ya aikata.
Sai dai lokacin da kake kaucewa abu, lokacin
yake kokarin kusantoka. Wannan tsautsayin ne
yake bibiyar shi tun safe, da nauyin jiki ya tashi
kamar ba zai fita ba. Saratu ta tambaye shi
unguwa, ya dauki kudi ya bata, tun sanda zai fita
da safe yaga tana ta shiri abinta. Bata cika
shisshige mishi kamar da ba, auren shi da Mero
ya canza abubuwa da yawa a tsakaninsu, kamar
ta rage fada, ta rage magana, ta rage kula dashi,
ta rage abubuwa da yawa da bai san ya saba
dasu ba sai bayan ta janye masa haka. Idan ya
kalleta kamar yau sai yayi kewar wadannan
abubuwan.
Lubna sufyan
Hausabook.com 361
Sabo abune mai wahala, ko itace da girki tana
iya kawo masa abinci tace masa zata duba yara,
sai ya bita wasu ranakun sannan zata dawo
masa, yana iyajin tana kokarin tashi ta koma
dakinta, sai idan ya riketa ya hanata fitane
"Kamar bakyason kasancewa dani yanzun
Saratu..."
Ya taba fada a wani dare da ya kasa hakuri da
rashin kulawarta
"Mu biyu gareka Julde. Kuma yaushe ka fara
damuwa a abinda nake so ko bana so? Ba kayi
auren soyayya ba? Karka damu dani, mu cigaba
da zamanmu yanda muka saba"
Bayajin surutu daya fada mata ba haka suka
saba zamansu ba, bata saba share shi ba, komin
yawo ko fadan da sukayi, ko da ba'a jikinshi ba,
a gado daya suke kwana.
"Yaushe zaki dawo?"
Ya tambaya, kallon shi takeyi da mamaki a
fuskarta, kamar ba zata amsa ba tace
"Sai da yamma, zan biya inyi kitso"
Lubna sufyan
Hausabook.com 362
Kai ya jinjina yana mata sallama, da Talatu bata
nan, yanda yakejin jikinshi yayi masa nauyi
haka. Haidar zai dauka ya kaishi wajen Daada,
ya dawo ya wuni manne da Meron shi. To itama
tace masa zata danje gidan Baabuga, ba jimawa
zatayi ba, dubiya zatayi ta dawo. Shisa kanshi
tsaye yayo gida wajen sha biyu na rana da nufin
ya kwanta ya danyi bacci ko zaiji dadin jikin shi.
Da yaga gidan a bude ya dauka ta fita harta
dawo, da sallama ya shiga, yaga tsakar gidan
babu kowa, kuma ba'a amsa mishi ba, saiya
bude dakin shi ya shiga. Kayan jikin shi ya rage
ya karasa kan gado ya kwanta yana maida
numfashi hadi da lumshe idanuwan
Da yaji an tura dakin ma, bai bude idanuwan shi
ba, a tunanin shi Mero ce, wani numfashi ya
sauke yana mika hannun shi
"Yau banajin dadin jikina Mero"
Ya furta, yana bude idanuwan shi babu shiri
lokacin da ta saka hannunta cikin nashi, saboda
yaji ba Mero bace ba, ba yatsunta bane ba, zai
gane su a cikin dubban mata ko da idanuwan shi
a rufe suke. Yanda idan ta sakala su cikin nashi
Lubna sufyan
Hausabook.com 363
yakan jisu cif-cif, kamar an auna ne kafin a
halitta mata su, dai-dai rikon shi, tsayinsu yanda
zasu kwanta a cikin nashi ya rike yana wasa
dasu, yana kallon fararen kumbuarta da baka
rabawa da jan lalle. Kokarin fisge hannun shi
yake, saita zauna kan gadon, jikinta yana taba
nashi da yaji ya mutu murus
"Meye haka Talatu? Me yake damunki?"
Murmushi tayi, idan tace ba da nufin tazo taga
mijin da Mero ta aura ta shigo Marake ba zatayi
karya. Tun ranar da suka hadu ta gansu, taga
kyawun da suka kara kamar ba'a karkara suke
ba take son taga wanda ta aura haka. Mero bata
da muni, amman kuma bata da kyawun da
Haidar zai biyo haka, yaro bulbul dashi, ga
hanci, ga idanuwa, ga wani danbaki karami
kamar an shafa mishi jambaki. Kowa Mero ta
aura me kyaune, dansu ya nuna haka, kuma
yanayin sutturarsu da yanda take ta ciro kudi
tana bayarwa ana siyo musu abin bukata, ba wa
kanta da yaron ba kawai harda yan cikin gidan
ya tabbatar mata da ba mai rufin asiri bane ba,
maikudi ne.
Lubna sufyan
Hausabook.com 364
Sai dai bata hango Julde bane ba, wannan
danfulanin da taso kwacewa a hannun J-town
wasu yan shekaru baya. Ta hango ta rikitashi da
salonta, ta yaudare shi da kissosin da ta koya
har sai ya bar matar shi idan yana da ita ya nemi
aurenta, saboda yana da kyau, yana da wani irin
kyau da ta kwana biyu bata ci karo da mai irin
shi ba. Ta ga ya daina yin kitso da gashin shi
yanzun, amman lokacin da ta ganshi akwai kitso
akan shi, kitson daya kara masa kyau. Yanzun
da ta ganshi babu kitson kuma sai taga kamar
yafi kyau, ya kara girma, shekarun sunbi
jikinshi sunyi wata irin kwanciya data kara fito
da halittar shi ta cikakken namiji.
Sai bata sake ganin shi ba, har tayi aure bayan
haduwar su yakan kutsa cikin tunaninta lokaci
zuwa lokaci, zai wahala ka hadu dashi ka manta
shi da wuri, komai nashi mai tsayawa a raine,
ciki harda yanayin mu'amalar shi da ta jima
bata goge mata ba. Bata sa ran irin wannan
haduwar zasu sakeyi ba. Me yasa Mero zata
dinga samun komai ne haka? Me yasa komai zai
dinga tafiyar mata dai-dai? Shisa ta tsaneta
tuntuni, a makaranta ta kasance mai kokari,
Lubna sufyan
Hausabook.com 365
kuma duk yanda zata gallaza mata da wahala
kaga hawaye a idanuwanta, sai tayi da gaske
take ganin gazawar Mero. Ta biyo mahaifiyarta
da har yanzun kowa yake yabon halayenta, da
ko bayan rasuwarta basu daina kwatancen
halinta da duk wani abu da Talatun zatayi ba,
duk da ita batayi wayan saninta sosai ba.
Da gaske har ranta bata son Mero, so take taga
wani abu ya hargitse mata ko yaya ne. Ashe zata
samu dama haka
"Ganinka ya tunamun da abubuwa da yawa
Julde...kasan yanda na dade ban manta ka ba
kuwa? Yanda ka jima a tunani na, ashe zan sake
ganinka?"
Duka maganar nan tanayi ne cikin wani irin
sauke murya da ya kara kashe masa jiki. Mace,
in dai macece baisan yanda zaiyi da jikinshi
akanta ba, ya rasa abinda yake damun shi haka.
So yake ya tureta daga jikinshi da take ta sake
shigewa, kamshinta ya cika masa hanci, duk ta
lakaikaye shi, tana sake dumtsa hannunta da
yake cikin nashi har lokacin. Ba zaice ga abinda
ta cigaba da fada ba, ba zaice ga lokacin da jikin
Lubna sufyan
Hausabook.com 366
shi ya fara amsa mata ba. Ya manta komai, babu
komai cikin kanshi sai yanayin nan da yakan
shiga duk idan ya kebance da mace, yanayin da
yake danne komai da kowa, yanayin son sanin
yanda take, son gane bambancinta da sauran
mata.
Shisa baiji shigowar Mero ba, baiji tura dakin da
tayi ba
"Kanwar mahaifiyata Julde..."
Muryarta ta ratsa ilahirin dakin da jikin shi,
kafin komai ya tsaya cak, ya kasa motsi, har ta
kwance Haidar da yake goye a bayanta ta ajiye
shi, ta karasa cikin dakin sosai tana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 27