na shekara biyar ne,
wanne uzuri zan bata na sauran shekarun?
Bansan inda kuke ba? Inajin kamar banyi kokari
da yawa wajen nemanku ba Daada, saina
kwanta a gida na bar Kabiru da wannan
aikin...kamar inda nayi kokari ta bangare na
dana gano ku da wuri, da na samu wasu shekaru
tare da ita..."
Ta karasa maganar da hawaye cike da
idanuwanta. Ita, Madinar da alamu duka suka
jima da nuna ita kadaice rabonsu a duniya.
Lubna sufyan
Hausabook.com 612
Saboda bayan ita ko batan wata bata sakeyi ba
balle su saka ran wasu yaran. A tsayin shekarun
nan kuma ko da wasa Kabiru bai taba yi mata
zancen Madina ba, kamar yana tsoron fama
mata ciwon daya san tafi shi ji. Kuka tayi sosai a
jikin Daada kafin ta iya mikewa ta nufi dakin
Madina bayan ta wanke fuskarta, a kwance ta
sameta da littafi a hannunta, saita sauke littafin
bayan taji ta zauna a gefen gadon, kafafuwanta
taja ta mike su akai, sannan ta kamo hannun
Madinar tana dumtsewa cikin nata.
"Duk idan naga littafi a hannun wani lokacin
muna Marake, ko a kasuwa sai inta kallo inajin
daman na iya karatu danace Baba ya siyomun"
Kallonta Madina tayi
"Ban iya karatu ba a lokacin, na iya na hausa
yanzun, na koya daga baya...naga litattafai da
yawa a dakin nan"
Kai Madina ta jinjina
"Ina son karatu, ina so in zama babbar yar
jarida..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 613
Kallonta Yelwa takeyi tanajin kamar ta maida
hannun agogo baya
"Amman ina karanta komai fa, ba sai abinda ya
shafi harkar aikin Jarida ba, labarai, kimiyya,
tarihi, abubuwa da yawa dai haka. Hamma Salim
inya tashi siyomun litattafai akan abubuwa
mabambanta yake siyowa..."
Hira sukeyi har wajen sha biyu, Madina na bata
labaran yanzun, ita kuma tana bata labarin
Marake, al'adunsu da duk wani abu da take so a
garin, harda kuruciyarsu ita da Saratu, fadan da
Saratu tayi da rikicin Julde, kadan daga
abubuwan da zata iya tunawa game da Bukar,
labaran da Yelwa ta adana a kirjinta zata bawa
yaranta wata rana, labaran da ta dauka damar
bayar dasu ta wuceta ce ta samu yau, a cikin
hirar ne Madina ta kalleta, kallo na sosai tace
"Me yasa kika barni? Da zaki tafi me yasa baki
daukeni ba? Sai kika barni, me yasa kika barni"
Ta karasa muryarta na karyewa, idanuwan
Yelwa suka ciko da hawayen da take kokarin
ganin basu zuba ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 614
"Tunda na dawo nake hada kalmomin da zasu
zame mun uzuri, kalmomin da idan nayi amfani
dasu zasu sa ki yafemun, zasu wankeni a
idanuwanki, amman bandasu Madina, banda
wasu kalmomi, zan sake son kaina, kiyi hakuri
dana barki, ki yafemun da nayi miki nisa a
lokacin da kike bukatata...kiyi hakuri banzo da
wuri ba, nasan na makara, amman kiyi hakuri"
Gilashinta Madina ta cire tana saka bayan
hannunta ta share hawayen da kamar ta ba
wasu kofar fitowa ne, rikota Yelwa tayi, wani
irin kuka takeyi kamar ba zata daina ba shisa
Yelwar bata sake cewa komai ba, a tsakanin
kukan da ajiyar zuciyar da Madina takeyi ne
tace mata
"Karki sake bari na, kinji, dan Allah karki sake
barina...kinga zanyi aurema, dan Allah ki zauna"
Sai lokacin ta bari nata hawayen suka zubo, ta
daga mata kai
"Aure? Wa zaki aura?"
Hanci Madina taja, muryarta harta dishe tayi
kasa saboda kukan da takeyi
Lubna sufyan
Hausabook.com 615
"Hamma Salim, amman Daada bataso bansan me
yasa ba"
Hannun Madina da yake cikin nata ta murza
wani abu na tsirga mata. Wasu hawayen na
neman kubce mata
"Dare yayi, kiyi bacci da safe sai muyi magana"
Kai Madina ta jinjina tana gyara kwanciyarta ta
sake shigewa jikin Yelwar, ta kuma dumtse
hannunta a cikin nata kamar hakan zai hana
wani abin ya sake kwace mata ita. Addu'ar bacci
ta karanta batare da ta bude idanuwanta ba ta
tofa a hankali tana fatan ganin wayewar gari
Ya kira a hankali, cikin muryar da ta ratsa
shirun studio din tana kuma isa kunnuwan
Madina duk da hankalinta yayi nisan kiwo,
juyowa tayi tana kallon shi, idanuwanta tsaye
akanshi, sai dai rashin gilashinta yasa bata
ganin shi sosai, ta kara kankance idanuwanta
kamar hakan zai wanke mata hoton shi. Yanayi
ne da babu wasu kalamai da zasu misalta yanda
Salim yaji, ya kamata ace ya dago hannun shi ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 616
dafe zuciyarshi da take barazanar fitowa daga
kirjinshi saboda tsallen da takeyi, amman
bayason komai ya katse mishi yanayin, komai
na nufin har numfashin shi da yake kokarin
daukewa, tayi kyau, badon batayi mishi kyau
kullum ba, bakuma dan bai taba hasaso ta da
kayan mata ba, asalima tun kafin yasan zuciyar
shi na doka mata, duk idan zaiga mace tasha
kwalliya sai yayi kokarin dora fuskar Madina a
cikin tata.
"Hamma...Hamma Am"
Ta kira shi, tana saka shi sake kallonta, a kasan
duka kwalliyar fuskarta yana hangowa kuncin
da baisan ta inda zai fara rage mata radadin shi
ba. Kwalliyar kuma na baje mishi har yana
hangota kwanaki biyu da suka wuce tsaye a
wajen jira na asibitin koyarwa na Aminu Kano,
kanta babu ko dankwali, gashinta da bai taba
sanin haka yake ba ya hargitse, santsin shi yasa
wani daga cikin sashen ya barbazu ta gefe da
gefen fuskarta, ribbon din data saka ta kama
gashin dashi yayi baya sosai ta yanda zaka iya
ganin yalwar gashin da Allah yayi mata duk
kuwa da tsayin jelar a nannade yake. Wando ne
Lubna sufyan
Hausabook.com 617
a jikinta mai roba daga karshen, sai rigar da ta
sauka har wajen cinyoyinta, kafafuwanta babu
ko takalmi sai safa.
A yanda ya kula, shine karshen zuwa wajen,
saboda har Adee tana nan, ta kuma yanayin
kumburin idanuwanta zaka gane kukan da taci,
saboda daya dauke idanuwanshi na yan dakika
daga kan Madina, kauda kanta tayi kamar tana
kokarin boye masa hawayenta. Daada na zaune
kamar kowa, Julde na kusa da ita ya kama
hannunta ya dumtsa cikin nashi, daga nesa wani
zai iya cewa lallashinta yakeyi, amman shi daya
kara matsawa yaga Julden ne yake neman
lallashi a wajenta. Daga Madina sai Kabir ne a
tsaye, dan shi yana bakin kofar dakin da alamu
suka nuna Yelwa na ciki, kamar kiris yake jira
ya bankada kofar ya shiga. Madina ta jingina
bayanta da bangon wajen, kafafuwan shi a
saitinta suka tsaya.
Kamar wadda taji karasowar shi sai ta dago tana
kallon shi ta cikin gilashinta, numfashi ta fara ja
da baiga sanda ta fitar ba, kamar shi take jira,
kamar shi kadaine zaifi kowa fahimtar hargitsin
da take ciki haka ta kalle shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 618
"Lafiya kalau muka kwanta Hamma, a karo na
farko munyi hira, sosai mukayi hira, me yasa
zamu tashi haka? Me yasa zan tasheta taki tashi?
Na kiraka baka dauka ba"
Ta karasa maganar da alamar tuhuma, yabar
wayarshi cikin mota ne da yazo asibiti, sai da
yayi tunanin ya kirata ne ya kula da hakan, da
yaje ya dauka ba kiranta kadai ya gani ba, harda
na, Khalid, Adee, Nawfal da ma Saratu. Yawan
kiran yana tabbatar mishi da cewar ba lafiya ba
"Kirjina zafi yakeyi..."
Madina ta fadi tana kai hannu ta murza kirjinta
inda zuciyarta ke mata wani irin ciwo, ta dauka
tun akan Daada ta gama sanin meye tashin
hankali sai asubar yau da ta tashi Yelwa taki
tashi, ta kunna fitilar dakin ta dagota taga farar
fuskarta tayi wani irin haske kamar babu jini a
jiki. Sai kuma da ta ga Julde ya dagata ya saba a
kafadarshi kamar babu rai a tare da ita sannan
wani abu ya rabe a cikin kirjinta da take jin
zafin shi har yanzun. Hannunta ya kama batayi
musu ba ta bishi, ya jata yana karasawa da ita
inda Khalid da Nawfal suke zaune ya zaunar da
Lubna sufyan
Hausabook.com 619
ita a gefen Nawfal daya kalle su. Tunda suka
shigo asibitin, babu yanda basuyi da ita ba shi
da Khalid, musamman shi, maganar duniya yayi
mata bata ko daga kanta ba, haka ya gaji ya
hakura ya samu waje ya zauna.
Amman hankalin shi duka yana kanta, Salim na
shigowa ta kalle shi kamar shi take jira, bai ko yi
mata magana ba ta fara fada masa matsalarta
kamar tana tsammanin maganinta a tare dashi.
Haka kawai sai yaji zuciyarshi tayi masa wani
iri, musamman yanda ta riko Salim din bayan
yayi kokarin zare hannunshi daga cikin nata
"Ruwa zan kawo miki Madina"
Ya fadi yana zare hannun shi daga cikin nata. Bai
kuma dade ba ya dawo da robar ruwan da
batayi musu ba ta karba. Ya ajiye mata silipas
din da yake amfani dasu a asibitin, sai da yaga
tashi ruwan tukunna ya mika mata rigar shi,
itama karba tayi, daga zaunen ta saka tana zage
zip din, shiya kamo hular da take hade da rigar
ya dora mata saman kanta
"Ki zauna nan, kina jina? Ki zauna, zanje in duba
inga me yake faruwa..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 620
Saida yaga ta daga masa kai a hankali sannan ya
tafi. Ya shiga dakin, sun fito tare da likitan suna
karasawa Office din shi, Julde na rufa musu
baya. Sai dai shi kadai ya iya fitowa saboda
Madina tana jiran shi, Julde ya kasa fitowa, ya
barshine ya kifa kanshi da teburin ofishin
likitan, sai dai daya fita ba idanuwan Madina
bane kadai akanshi, na dukan sune, ahalin shi,
suna jiran yayi musu bayanin da baisan ta inda
zai fara ba. Kasancewar bangaren ba nashi ba
baya nufin baida sani kadan akai, kuma tunda
likitan ya kira
"Stomach cancer, last stage..."
Sauran bayanin ko baiyi masa ba ya rigada ya
fahimta, ciwon yayi rassa a cikinta, yayi girman
da babu wani taimako da za'a iyayi mata a
likitance daya wuce dirka mata magungunan da
zasu rage mata radadin da take ciki kafin
kwanakin da suka rage mata su cika, abinda
kowa yake jira da ciwo ko babu ya tabbata
akanta. Sai dai bai ganowa Madina ita dan ta
rasata ta wannan hanyar ba, daya ganota bai
hango bata da isashen lokaci haka ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 621
"Hamma mutuwa zatayi ko?"
Madina da baisan ta karaso inda yake ba ra
furta cikin wata irin karamar murya
"Stomach cancer"
Ya tsinci kanshi da furtawa, tashi muryar na
fitowa kamar rada, sai da ta hadiye wani abu
kafin ta iya ce masa
"Wanne mataki?"
Numfashi yaja yana fitarwa a hankali
"Na karshe..."
Rawar da kafafuwanta sukayi da bai rikota ba
faduwa zatayi, sai da ta dai-daita kanta, ya kuma
tabbatar idan ya saketa ba zata fadi ba sannan
ya saketa din, batare data kalle shi ba tace
"Wata nawa sukace?"
Rayuwa a hannun Allah take, hasashen likitoci
arashine kawai da akan samu, amman wani ya
isa ya hasaso adadin daya rage maka a duniya?
Shine abinda ya tsara fadawa Madina sai wani
abin daban ya kubce masa
Lubna sufyan
Hausabook.com 622
"Kwanaki, sati daya idan an dade ko kasa da
haka"
Kafin yayi saurin dorawa da
"Sai dai mu da muke da lafiyar ma bamu da
tabbas idan muna da wannan lokacin Madina..."
Kalaman na koma masa da wani irin firgici,
koda ayyukan alkhairi ya shafe shekarun shi
yanayi bayajin zai iya shiryawa mutuwa a dan
kankanin lokaci haka, idan kuma ayyukan basu
karbu bafa? Kamar tuban shi da bai dade da
farawa ba, da wanne guziri zaiyi rayuwar
barzahun da ake kira? Rayuwar da tafi kowacce
firgici idan baka samu dacewa da Rahmar Allah
ba, shekaru ne da babu wanda yasan adadinsu,
dari biyar, dubu dari biyar, miliyan dari biyar
kafin a tashi duniyar azo filin alkiyama, firgicin
da yake ji yana da yakinin yafi wanda yake gani
shimfide a fuskar Madina. Ita mahaifiyarta take
ji, shi kanshi yake hangowa, zunuban shi da
baisan ko yana da lokacin da zai wanke daudar
su ba yake tunani.
Batace komai ba, rabashi tayi tana wucewa ta
tura dakin da Yelwa take ciki ta shiga. Baiyi
Lubna sufyan
Hausabook.com 623
kokarin binta ba, bai kuma cewa kowa komai ba
tunda yasan sunji su, barin wajen yayi zuwa
Office din shi. Wayar shi dai na tare dashi, duk
mai bukatar shi zai nemeshi, da azahar tayi dai
ya fita yayo musu takeaway sannan ya koma.
Daya ba Madina nata kallon shi tayi
"Kina bukatar abinci ko bakyajin yunwa"
Ya fadi, kai ta dan daga masa a hankali
"Kaci dani to"
Ganin kamar yana son yi mata musu yasata
dorawa da
"Hamma...dan Allah"
So yake yace mata ya ci nashi, bashida wajen
saka wani, amman saiya kasa, zama yayi,
cokalin dayar robar abincin yayi amfani dashi
yana hadiye batare daya tauna ba saboda da
gaske ya koshi. Kuma saboda ita ya zauna yaci
abincin, tun na safe ne da bai samu yaci ba.
Yanzun ma gashi yana kara wani saboda ita. Ya
kuma zauna tare da ita har akayi la'asar,
magariba, isha'i, bai bar gefenta ba sai karfe
Lubna sufyan
Hausabook.com 624
goma na dare da jaddada mata in tana bukatar
shi waya kawai zata daga ta kirashi
"Kaje aikinka Hamma"
Yanda ya kalleta kamar bayason barinta ne yasa
ta yi masa murmushin karfin hali, kamar tana
son fada masa Yelwa ta tsallaketa tun bata
kwana a duniyar ba, babu abinda ya sameta
kuma, ta rayu, bambancin da yake tsakanin
wancen lokacin da wannan bashi da wani yawa.
A wancen Yelwa bata da zabi, wannan dinma
bata da zabi, bambancin kawai idan ta tafi
yanzun babu taraddadi, babu duban hanya,
sunsan ta tafi kenan. Saida ya kara kallon
Madina yana son tabbatarwa kanshi da in ya
tafin tana da sauran karfin zuciyar rike masa
kanta. Kwana biyu tsakani ta kirashi tace yaje
tana son ganin shi, zuciyar shi a cikin bakin shi
ya karasa wajenta saboda basu fi awa daya da
rabuwa ba, kafin ya furta wani abu ta rigashi
"Ka aureni Hamma..."
Ta furta tana maida numfashi kamar tayi gudu,
yana kuma hangen hawayen da yake cike tafi da
idanuwanta
Lubna sufyan
Hausabook.com 625
"Bata ga abubuwa da yawa a tare dani ba, ba
kuma zata ga wasu da yawa ba, bana so auren
mu ya zama cikin jerin abubuwan da ba zata
gani ba Hamma, ka aureni"
Abinda yake sonji ne, amman ba haka ba, yana
son aurenta, aurenta ne abu na karshe da
yakejin zai zama cikon rayuwar shi, sai dai baiyi
wani shiri ba, kudaden da yake dasu a account
dinshi bayajin zasu isheshi hidimar aure, yana
da gida da Julde ya sai masa kamar kowa a
gidan, amman yan haya ne a ciki, kuma baima
san yaushe kudin da suka biya zai kare ba
ballantana kuma watannin da za'a kara musu su
nemi wani wajen daban. Akwai hidima da yawa
a aure, kananu da manyan abubuwan da suke
bukatar shiri, shiri kuma yana son lokaci, a
yanda Madina take masa magana bayajin yana
da lokacin da zaiyi duk wannan shirin.
"Kaji..."
Ta sake fadi tana kallon shi
"Akwai shirye-shirye da yawa fa, banda inda
zamu zauna, ga su lefe"
Lubna sufyan
Hausabook.com 626
Da sauri tace
"Duka wannan sai ayi daga baya, a daura auren
dai ta gani...bata da lokacin jiran duk wannan,
watakila mu muna dashi..."
Ta karasa cike da wani yanayi na nuna rashin
tabbacin rayuwa, saiya tsinci kanshi da daga
mata kai, yana kuma samun Julde a daren a karo
na biyu tunda na farkon daya same shi saiya
rasa abinda zaice masa, daya kalle shima wani
zafi yaji kirjinshi na dauka, saboda tunda abin
ya faru basu hadu haka su biyu kawai ba, duk
haduwar da sukayi a cikinsu babu mai natsuwar
dawo da ranar balle har su fuskanci junansu, sai
da Salim ya hadiye wani abu da yaji tokare da
wuyanshi sannan muryar shi can kasa yace
"Ina son Madina...Daddy ina sonta. Zan aure ta,
tunda ga Babanta yanzun, ka nemar mun
aurenta a wajen shi"
Kamar Julde ba zai magana ba, ya nisa yace
"Ita tana son ka?"
Kai Salim ya daga masa
Lubna sufyan
Hausabook.com 627
"Shikenan, zanyi masa maganar..."
Numfashi Salim ya sauke a hankali yana mikewa
daga zaman da yayi a gefen gadon Julden, har
yakai kofa Julde ya kirashi
"Salim..."
Tsaye yayi, hannun shi rike da handle din kofar
kafin a hankali ya juya
"Kayi hakuri, kayi hakuri duk da yin hakurin ba
zai taba goge hoton dana dasa a zuciyarka ba,
kayi hakuri, dan Allah kayi hakuri..."
Baice komai ba ya bude kofar ya fice, saboda
baisan meya kamata yace din ba, ya hakura?
Bayan zuciyarshi zafi takeyi kamar zata kone,
bayan baisan ya zai kalle shi baiga hoton shi
tsaye yana kokarin haramta masa Madina ba.
Lokaci na tafiya da komai, haka mutane suke
cewa, yana dai da yakinin ko lokaci ba zai tafar
masa da wannan mummunan hoton ba. Sunyi
maganar ne shida Julde batare da hango zasu
tashi da ciwon Yelwa ba. Da kuma ya same shi a
karo na biyu sai ya natsu yana nazarin fuskar
shi, yana ganin ramar da take idanuwanshi
Lubna sufyan
Hausabook.com 628
kamar tare suke jinyar da Yelwa. Yanda ya amsa
gaisuwar shi da wani irin sanyi na saka zuciyar
shi matsewa a cikin kirjinshi
"Daddy ko jikin ne? Kana shan magungunanka
kuwa?"
Murmushin karfin hali yayi yana fadin
"Wannan magungunan ba zasu yiwa ciwon da
yake damuna ba Salim, ya akayi?"
Numfasawa Salim yayi kamar ba zai fada masa
ba saboda yanayin shi yayi masa wani iri
"Madina tayi mun magana, tana so a fara daura
auren, komai sai yazo daga baya, tana so
Mamanta ta gani kafin..."
Ya kasa karasawa saboda yanda yaga wani abu
ya gilma a cikin idanuwan Julden kafin ya
lumshe su a hankali yana sake budewa
"Zanyiwa Kabirun magana anjima idan na shiga
asibiti"
Cewar Julde, duk da ya kula Kabirun yana
zillewa haduwa dashi, kuma a wannan gabar
baiga laifin Kabirun ba, randa ya fito daga dakin
Lubna sufyan
Hausabook.com 629
likitan nan bayan ya tabbatar da ciwon Yelwa ba
mai warkewa bane ba, kanshi tsaye inda Kabiru
yake tsaye ya nufa yana shako shi da dukkan
karfin shi kafin ya soma jijjigashi
"Ka dawomun da kanwata yanda ka gudu da ita
Kabiru, ka dawomun da ita yanda ka bar Marake
da ita"
Su Nawfal kasa kwatar Kabiru sukayi, saida
Daada tazo ta kamashi saiya kasa yi mata musu,
ya saki Kabiru ya barta taja hannunshi ta zaunar
dashi, daya fashe da wani irin kuka ma batayi
kokarin yanashi ba, zama tayi kawai a kusa
dashi. Sai dai a yan kwanakin nan ya kasa hana
idanuwanshi bin Kabiru da harara duk haduwar
da zasuyi. Amman yanzun Daada ya fara samu
da zancen Salim da Madina kafin ya fara yiwa
Kabiru maganar
"Nasani, Madina ta fadamun, ba kuma kinta da
Salim nakeyi ba, abinda zaije ya dawo ne nake
gujewa, ina tsoron wata kaddarar Julde"
Kanshi a kasa, idanuwanshi cike da hawayen da
suka zame masa abokai a satikan yace
Lubna sufyan
Hausabook.com 630
"Wacce irin kaddara ce bamu gani ba Daada?
Akwai wata fuska ta kaddara kuma da bamu
gani ba?"
Numfashi ta sauke
"Allah yayi mana jagora yasa alkhairin juna ne"
Ta furta da wata irin sanyin murya, daya samu
Kabiru ma suka zauna yayi masa maganar
nisawa yayi yana amsawa da
"Yaran duka nakane Julde, duka yaushe na shigo
rayuwar Madinar da nake da bakin cewa a
cikinta?"
Kai Julde ya girgiza masa
"Bana sonka kasani, banajin akwai wani dalili
da zaisa zuciyata ta soka, amman dan kazo
rayuwarta a makare ba zai canza matsayinka ba,
shisa nake tambayarka, nake nemar wa dana
auren 'yarka Madina"
Muryar Kabiru a karye yace
"Na bashi, in dai bakina ake so aji na bashi
Madina"
Lubna sufyan
Hausabook.com 631
A ranar juma'ar, bayan sallar isha'i, a
masallacin, Julde, Kabiru, Salim, Nawfal, Khalid,
limamin daya jagoranci sallar da mutanen da
suke cikin masallacin suka zama shaida, aka
daura auren Salim da Madina akan Sadaki dubu
dari, Sadakin da Julde ne ya bayar daga aljihun
shi, za kuma kaga mamakin da yake shimfide a
fuskokin su Khalid, musamman Nawfal da yaji
kamar an sakko masa wani dutse a saman kai,
tunda basu san da zancen ba, daurin aure kawai
sukaji kamar a shirin fim, banda raba idanuwa
babu abinda sukeyi har Julde ya tasa su gaba
suka fito daga masallacin, daman kiran da yayi
musu kenan? Dan su kara zama shaida a auren
Salim da Madina? Sun kara tabbatar da iya kiran
kenan ganin bai musu bayanin komai ba ya nufi
hanyar gida, Kabiru kuma daya fito suka kara
gaisawa a waje shima sallamar yayi musu yana
wucewa ya koma asibitin da zaije
"Ni kadai ne bansan da maganar nan ba?"
Nawfal ya fadi yana kallon Khalid
"Fuskata tayi maka kama da nasan da auren nan
Bajjo?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 632
Kai Nawfal ya girgiza masa yanajin shi wani iri,
tare suka karasa cikin gidan, suka shiga motar
Khalid ya mayar dashi hotel din da suke zaune
shi da Murjanatu, Khalid kuma ya kamo hanya
ya dawo gida ya nufi bangarensu, inda ya samu
Salim zaune a falo da kofin shayi a hannun shi,
ya kai bakin shi yana hura iska a ciki a hankali
"Ka fadi abinda yake zuciyarka Khalid, tun a
masallaci nake jin idanuwanka suna bina da
kallo"
Kallon nashi Khalid yakeyi, kafin ya girgiza
kanshi a hankali yana rabawa ta gefen kujerar
da nufin karasawa dakin shi
"Khalid..."
Salim ya kira cike da kashedi, juyowa Khalid din
yayi
"Me zan fada maka da baka sani ba Hamma? Ta
yanda baka dace da Madina ba? Yanda in har
baka shirya gyara halayenka ba kayi sahihin
tuba ba zaka taba dacewa da ita ba? Ko tsorona
zan fada maka na gudun karka sake karya mana
zuciyoyin da suke a karye?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 633
Runtsa idanuwa Salim yayi yana budesu a
hankali, baisan ta inda zai fara fadawa Khalid ko
bai auri Madina ba yayi hannun riga da bin wasu
matan, yaga kunyar duniya a tare da Julde,
kuma iya idanuwansu kunyar ta tsaya, har
yanzun idan ya fita waje mutane suna gaishe
dashi, suna kallon shi da rigar mutuncin nan,
bashi da kwarin gwiwar tsayawa gaban Allah da
tarin daudar nan, kamar yanda bashi da
kalaman amfani dasu wajen yiwa Khalid bayani
"Maganganuna basu da yawa Khalid, kasani,
banda abin fada maka, zan dai ce maka na daina,
ina kokarin rage zunubaina, ba kuma saboda
Madina ba, da soyayyarta a raina nake laifuka
na, ba don ita na bari ba, na bari don kaina da
lahirata..."
Wani irin numfashi Khalid ya sauke
"Allah ya yafe mana ya cigaba da yi mana jagora.
Allah yasa alkhairi da albarka a aurenku..."
Kai Salim ya jinjina yana amsawa a cikin zuciyar
shi, Khalid yace auren su
Lubna sufyan
Hausabook.com 634
Hannunta ta saka cikin na Salim, bashi bane
karo na farko da hannuwansu ya shiga cikin na
juna, amman yanda ya dumtsa yatsunta yau sai
taji kamar an halitta musu wajen zama a cikin
nashi ne, daya dan juyo ya kalleta, sai ya dago
dayan hannun shi yana goge mata jambakin
daya haura gefen lebenta da yatsanshi yana
yawatawa da idanuwan shi kan fuskarta kamar
yana neman wani abin da baiyi mishi ba ya
gyara, kafin ya dan daga kai alamun komai yayi.
Yaja hannunta
"Hamma bana gani sosai"
Ta fadi saboda komai yayi mata dishi dishi, ya
saka gilashinta cikin aljihun shi, so take ta
ganshi sosai, yau da ya saka babbar riga, dinkin
farar shadda, sai hular shi da aikin shaddar da
suke ruwan kasa mai cizawa, itama farar rigace
a jikinta da ba zatace ga tsafin da Adee tayi a
cikin kwana daya aka dinka rigar ba, sai
dankwalin da aka daura mata shine ruwan toka,
aka yafa mata bridal net fari da yasha duwatsu
ruwan toka masu kyalli, fuskarta takeji tayi
mata nauyi da kwalliyar da akayi mata. Sai dai
bai kai nauyin da takeji a zuciyarta ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 635
"Ni ina ganar mana komai..."
Dan rikoshi ta sakeyi har saida ya tsaya yana
kallonta, ta turo bakinta da yasha jambaki tana
saka jikinshi daukar dumi
"Ina so in ganka"
Numfashi ya sauke yana janta har gaban motar
shi, ya saki hannunta yana zagayawa cikin
motar ya dauko sabon gilashin da tuntuni ya
zabi frame daya tambayeta awon, ya manta ne
saboda abubuwan da suka tarar masa, baije ya
karba ba. Bude dan akwatin yayi ya ciro shi
yana zagayawa ya sameta inda take tsaye, da
kanshi ya saka mata madaidaicin gilashin daya
zauna a fuskarta yanayi mata kyau, data kalle
shi da mamaki a idanuwanta
"Bana son wannan frame din naki, yana
karemun rabin fuskarki"
Dariya tayi mai sauti, tana kallon shi sosai, tasan
yana da kyau, yana cikin irin mazan da ko a titi
sai kayi sa'a zaka ga giccinsu, sai dai yanzun da
waya ta wadata a hannuwan mutane to zakaga
hotunan maza irin Salim na yawo a social media,
Lubna sufyan
Hausabook.com 636
musamman groups na mata ana musu lakabi da
mazajen novel. Bambancin kawai, yawancin
mazajen novel sun san suna da kyau, suna kuma
da jin kai, sai kudi, zunzurutun kudin da Salim
bashi dasu. Gasu miskilai na bugawa a jarida,
Salim kuma hayaniya ce bayaso, amman yana
magana, yana hira a zababbun wajaje da kuma
zababbun mutane. Sannan sam yanayi kamar
baisan yana da kyau haka ba.
"Kayi kyau..."
Ta tsinci kanta da furtawa a hankali, dariya yayi
yana bude mata motar batare da yace komai ba,
shiga tayi, ya rufe murfin, sannan ya zagaya
yana shiga. Sun so kama waje ne don yin
walimar da hotunan su, amman Yelwa tace in
dai ba zata takura musu ba ayi a gidan Julde,
suka amince, tunda kacokan walimar don ta
gani aka shiryata, idan a cikin gida take son ta
kasance zasuyi hakan. Daman dakyar likita ya
basu aronta na awanni uku, a cewar shi jikinta
yayi raunin da take bukatar taimakon likitoci
kowanne yan mintina. Da suka karasa harabar
gidan yayi parking, yana fitowa ya ga su Khalid a
tsaitsaye, sai Adee da waya a hannunta, bakinta
Lubna sufyan
Hausabook.com 637
yaki rufuwa, kusan zaice shi kadai ya fita farin
ciki da auren
"Hamma..."
Ta kira tana wani iri da fuska kamar mai son yin
kuka, murmushi kawai yayi yana budewa
Madina kofar ya mika mata hannu, ganin yanda
take kallon shi yasa shi kamo hannun nata
kawai yana dagota ya taimaka mata ta fito daga
motar
"Woo"
Cewar Khalid yana sa Salim hararar shi
"Ina mai hoton ne wai? Yazo nan ya fara
haskamun su ya baro tsofaffin can dan Allah"
Khalid ya fadi yana juyawa ya shiga cikin gidan
ya kira mai hoton, tare da Nawfal da Murjanatu
suka dawo, itama doguwar rigace a jikinta kalar
ruwan toka mai cizawa, tayi kyau har mamakin
kyan nata Madina ta kanyi, gata yar gayu, dinkin
rigar iri daya dana Adee, itace ta karaso tana
dan rungume Madinar da fadin
"Ina tayaki murna"
Lubna sufyan
Hausabook.com 638
Cikin harshen fulatanci, murmushi Madina tayi
a kunyace. Nawfal kuwa yana daga bayan
Khalid, kamar yana son boyewa komai. Sai
kallon yanda Salim yake kara riketa yakeyi,
haka kawai yake jin zuciyarshi tayi masa nauyi.
Ya san Madina zatayi aure wata rana, amman
bai taba kawo mata auren nan kusa ba, lokaci
daya haka, kuma da Salim. Ji yake bai shirya ba,
anyi masa bazata, kamar ya kamata ace an bashi
lokaci ya shiryawa ganinta tsaye a kusa da wani
a matsayin tashi, mallakinsa. Yanzun ta ina ake
so ya fara? Yana daga ido ya kuwa ga Salim ya
tallabi habar Madinar yana kallon cikin
idanuwanta, kafin ya girgiza mata kai a hankali
kamar yana lallashinta, nata kan ta gyada masa,
yanayi ne da shi da Murjanatu suka sha tsintar
kansu a ciki, yanayi ne kuma da ganin Madina a
cikin shi yanzun yasa shi jin kamar Salim dinne
ya mika hannu cikin kirjinshi, inda zuciyar shi
take ya rikota yana matsewa da dukkan karfin
shi.
Da Khalid yaja shi don ayi musu hotuna ma
binshi kawai yakeyi, duk abinda akeyi a wajen
jinshi yake wani
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 27