Hammadi da Julde ya fita. Sai juyi takeyi
zuciyar kamar an watsa mata ruwan kankara,
amman kuma zafi take mata maimakon sanyi. A
haka baccin wahala ya dauketa cike da mafarkin
Bukar da rayuwar da zai tsinci kanshi a ciki a
gidan Baabuga.
**
Fada idan ka hango rashin nasara a cikin shi
babu wani amfani, yanda ranta yake a bace haka
take so na Datti ya kasance, amman yaki bata
wannan damar, hanyar duk da zatabi don ganin
ta bata masa rai ya toshe, daya biye mata, ko sau
daya ne ya biye mata su fadama juna
maganganu, ta fada mishi tarin abinda yake
binne a cikin zuciyarta, ko sau daya ta fada masa
bashi da tausayi, bashida adalci, ba kuma ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 128
sonta tunda baya son nata, ko zata samu
sassauci. Ganin yanda take wuni da kuncin
zuciya, kuka ne abokin hirarta duk dare kafin
bacci ya dauketa, yasa ta tsahirta ma kanta, ta
dauki shawarar Abu na ta mayar da komai
bakomai ba, tunda tana da sauran lokaci kafin a
mayar da Bukar din.
Ita ta zabi raba shimfida da Datti, ita kuma ta
zabi komawa da kanta, baice mata komai ba.
Riketa yayi a jikin shi yana jin kukan daya
kwace mata, kukan da yasan akan Bukar ne
shisa zuciyar shi bata motsa ba, kamar yanda ya
fadama Hammadi ne, ba zai rike Bukar ba, kome
zai faru ba zai rike yaron da ko sunan shi baya
so ya hau harshen shi ba. Abinda duk Dije take
tunanin zatayi don ya sama mata saukin
fahimtar hakan zai barta tayi, tsayin lokacin duk
da zata dauka zai bata shi, zai koma gefe ya
jirata har ta gama ta dawo wajen shi kamar
yanda tayi yanzun.
Duk da har aka kwana biyu ya kasa sakin jikin
shi, gani yake kamar zata koma Dijen nan da bai
sani ba, Dijen nan da bata shakkar neman
rigima da shi, Dijen da bai taba gani ba sai
Lubna sufyan
Hausabook.com 129
wannan karin. Amman shiru, hidima taci gaba
dayi tana gudanar da rayuwarta kamar babu
wani abu a ranta, har saida ya saki jikin shi.
Rayuwa suka cigaba dayi yanda suka saba. A
satin daya kama na bikin Hammadi da Pendo ne
Dije ta tabbatar da cikine a jikinta, ciki me
saukin laulayi. Da ta fadama Datti yayi murna ba
kadan ba
"Karka fadama Hamma dan Allah, saboda
Adda...zatayi murna na sani, amman zai zama
kamar muna tuna mata abinda ba zata samu
bane, ga maganar bikin nan da dalilin shi"
Kallon ta Datti yayi
"Idan ban fada yanzun ba, zai fito kowa ya gani.
Meye amfanin kin fadin?"
Dan murmushi tayi
"Nasani, abari sai ya fito din sun gani ni dai"
Numfashi yaja, numfashin nan daya kanyi idan
magana bata gama zauna masa ba, a wajen shi
maganar cikinta abin farin cikine da yake son
fadama duk wani da zai saurara batare da kunya
ba, baisan me yasa take son boyewa ba. Idan ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 130
samu ai kamar Hammadi ne ya samu, haka
Hammadin ya fada da bakin shi
"Dan Allah"
Ta sake roko, ya dauki wasu dakika yana juya
maganar kafin ya daga mata kai a hankali. Ashe
kuwa gara ma da tace masa subar maganar a
tsakanin su, dan cikin ba mai zama bane ba, a
cikin watan shi na uku ta wayi gari da zazzabi
mai zafi, zazzabin da bata kwana da cikin jikinta
ba, amman ta sake kwana ta tashi da shi na
tsayin kwanaki hudu, saboda barin ya jigatata.
Batasan ko Abu ta gane ba, ta dai dafo mata
zuma da kayan kanshi a ciki, ta bata a dan
kwano tace tayi kokarin shanyewa da duminta.
Sai da tayi mata hakan na kwana uku, cikin ikon
Allah sai taji dadi, har karfin jikinta ta samu,
kamar hadin zumar ya wanko duk wani sauran
ciwo da take tare da shi.
Har kasan ranta tausayin Abu ne fal, yanda take
kokarin ganin ta saukakama kowa komai duk da
rayuwarta da take a hargitse, hargitsin da bata
zubar da digon hawaye ko daya a gaban Dije ba,
itace ma tayi kuka ranar da dangin Pendo suka
Lubna sufyan
Hausabook.com 131
tafi da ita saboda irin maganganun da suka
dinga yi da habaici saboda ta samu rabo da
Hammadi
"Allah daya bata bai manta dani ba Dije...idan
rashin haihuwar shine alkhairi na akan
haihuwar fa? Naji dadi da kasa bata rufe mun
ido ba sai da naga rabon Hammadi... Hakan ma
ya isheni"
Ta fadi da wani murmushi a fuskarta daya kara
karyama Dije zuciya. Sai dai wauta ta tunani irin
na dan Adam da kan shafe giftawar mutuwa a
cikin tsarin al'amura na yau da kullum, duk
kuwa da sanin cewa zata iya sada zumuncin ta
da takanyi batare da sanarwa ba. Ko gudun da
watannin sukayi baisa sun kawo komai a ransu
ba, samu da rashin da ya samu Abu, ya same su
dukkan su, saboda Dije tayi kuka fiye da Abun,
mutuwar saita tuna mata da zafin da ta dandana
itama, komai na dawo mata kamar ranar ne ya
faru. Wannan ma baisa sun hango mutuwar
Pendo ba.
Pendo da jinin Dije bai hadu da nata ba, Pendo
da ko da mutuwarta ta daki Dijen fiye da yanda
Lubna sufyan
Hausabook.com 132
ta zata baisa taji ta sota ba, ta kasa goge laifukan
dangin Pendo, kalar rashin darajar da suka
yima Abu wani abune da ko ita kadai ta tuna sai
wani daci ya mamaye zuciyarta. Da sun hango
rayuwar Pendo ba mai tsayi bace kamar yanda
suka dauka da sun sassauta burin su. Cikin da
suke ta hauka akan shi, rabon da suke gani zai
zama tsanin da zai mallakama Pendo duk wata
ragama ta rayuwar Hammadi ga shi nan, ga 'yar
nan, amman babu Pendo. Abun da suke ki dole
idan lokaci yayi Hammadi ya karbi 'yar shi
rikonta a hannun Abu zai dawo.
Tun kwana biyu da rasuwar Dije bata jin dadin
jikinta, dakyar ta iya zuwa sadakar uku, har
Datti na mata fada kan cewa kukan da tayi ne
yasa mata rashin lafiya. Sai daga baya suka gane
laulayi ne, wani irin laulayi da bata tabayin irin
shi ba, ko ruwa tasha saiya dawo. Datti na gama
shiryawa yake zuwa ya kira Abu, sai yaga ta
dagata, ta kamata sun tafi gidanta sannan zai
rufe gidan ya fita, anan take wuni kwance, saiya
dawo da dare zai biya ya dauketa, ranaku daidai ne Julde yake kwana a wajen su tunda ta
samu cikin, shima idan Datti ne ya dauko shi,
Lubna sufyan
Hausabook.com 133
saboda ita bata da karfin kula da kanta ma balle
kuma Julden.
Kulawar su kacokan hannun Abu ta koma da
takeyinta kamar bata san ciwon jikinta ba.
Tasan hakan gidansu suka gani shisa suka kasa
samun zuciyar cewa zasu dauketa a yanayin
wahalar da take sha. Wannan damar kuma Baba
ya samu ya dauki Bukar ya mayar gidan
Baabuga, a cewar shi lokaci yayi, idan ma ba'a
mayar da shi yanzun din ba gaba za'ayi.
Haukane kawai Dije batayi ba, saboda Baba ya
zabi lokacin daya dace, lokacin da ba zata iya
tabukama kanta komai ba balle harta iya yin
wani abu akan Bukar.
Damuwar ce ta kara mata ciwo na daban, ga
rashin cin abinci, saiya zamana har cikin ya
shiga wata na biyar bata da karfin kirki, yawan
aman ya tsaya, amman kukanta bai tsaya ba,
damuwar da take ciki banda karuwa babu
abinda takeyi. Hankalinta da duk na wani
makusancita ba'a kwance yake ba
"Ka dubo mun yarona Datti, dan Allah ka
dubomun halin da yake ciki"
Lubna sufyan
Hausabook.com 134
Ta roka wani dare da take jin numfashinta yana
barazanar tsayawa, kukan da takeyi kamar zata
shide yasa Datti cewa
"Zan biya in dubashi da safe...zan duba shi Dije,
ki daina kukan nan kinga baki da lafiyar kirki"
Tunda yake bai taba ganin irin wannan lamarin
ba, wacce irin kaunace take yiwa Bukar din
haka? Wacce irin kaunace da ta danne wadda
takeyiwa kanta, ta danne wadda take yi musu,
akan Bukar shi kadai tana kokarin halaka kanta
da abinda yake cikinta, shi da Julde ta jefa su
cikin wani hali. Babu abinda hakan yayi banda
kara masa tsanar Bukar, tsanar duk wani abu
daya dangance shi. Ko kadan bai niyyar zuwa ya
duba mata Bukar ba, amman saiya tsinci kanshi
a kofar gidan Baabuga da safen daya fita, harma
da aikawa akayi masa sallama da Baabuga da
bayan sun gaisa ya rasa ta inda zai fara
tambayar shi Bukar.
"Dije tace in duba mata ya Bukar?"
Ya fadi yanajin wani daci a ranshi, murmushi
Baabuga yayi, har ga Allah in zai fadi gaskiya bai
san ya Bukar din yake ba, yara ne a gidan shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 135
sun fi ashirin, wasu ma rabon daya saka su a
idon shi anfi sati, sanda zai fita ba tsayawa yake
ya duba su daya bayan daya ba, haka idan ya
dawo. Da daddare Baban Dije ya same shi ya
mika masa Bukar, bawai ya manta sun sami
rabo da Dije bane ba, koba komai bai taba hada
shimfida da matar da ta kasa gogewa a tunanin
shi irinta ba. Bai dai kawo ma ranshi zasu mayar
masa da Bukar ba sanin cewa suna da halin da
zasu rike shi. Ya karba babu wani musu, yana
mamakin kyawun yaron da irin sutturar da aka
hado shi da ita, tun kuma da yaje ya mika ma
uwargidan shi, bai sake bi takan shi ba.
"Yana lafiya"
Ya amsa yana kallon Datti daya daga kai, harya
juya sai kuma ya dawo. Hannu yasa a aljihu yana
zaro kudi, ya diba ya mika ma Baabuga
"A sai masa dan wani abu shida sauran yan
uwan shi"
Hannu Baabuga yasa ya karbi kudin dan yana da
bukatar su. Yayi ma Datti godiya. Ko daya koma
gida da dare, akan tabarma ya samu Dije zaune
ta saka fitilar kwai a gaba tana kallo kamar ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 136
samu majigi, tana jin sallamar shi bata ma amsa
ba tace
"Ya Bukar din? Ka gan shi?"
Karasawa yayi ya zauna a gefenta, yana kallon
yanda kasusuwa suka fito a fuskarta saboda
ramar da tayi, da zai iya da yayi mata karya ko
dan ta samu saukin da yaga tana nema
"Bangan shi ba, amman Baabuga yace mun yana
lafiya. Na kuma bashi kudi..."
Kai ta daga tana kai hannu ta share hawayen da
ke shirin zubo mata.
"Yace yana lafiya"
Ya sake jaddadawa, kan dai ta kara daga masa,
zuciyarta na kuna, da bata zauna gidan Baabuga
taga rayuwar da akeyi ba da kila sai hankalinta
yafi kwanciya. Ko nama Datti ta siyo ta kai
bakinta sai Bukar ya fado mata, tasan tunda aka
kaishi gidan baiji dandanon nama a bakin shi
ba, gidan Baabuga yayi kama da gidajen da ba'a
ganin nama da wani abu mai galihu sai shekarashekara, a lokacin bukukuwa na sallah. Iya
abinci aka tsaya Bukar yana cikin garari, balle
Lubna sufyan
Hausabook.com 137
suttura da wajen kwanciya, ga rashin kulawar
da tasan yana ciki.
Shisa babu wani horo da namiji zai yima mace
daya wuce ya saketa ya kuma rabata da yaranta,
saboda gabaki daya nutsuwarta ya rabata da ita,
tunanin halin da suke ciki ba zai taba barinta
bacci me kyau ba. Dije ta daina kokarin ganin
wani ya fahimce ta akan maganar Bukar, tana
dai jin kamar karshen duniyarta ne ya zo.
Kamar tana samun karfin bude idonta ne da duk
safiya don ta haifi abinda yake cikinta kafin ta
rufe shi na har abada. Har Abu daina kokarin yi
mata maganar Bukar tayi saboda
"Hmmm..."
Kawai take iya cewa sai hawaye. A haka randa
cikinta ya shiga wata tara da kwana biyu ta fara
nakuda a tsai-tsaye, nakudar da bata taho mata
gadan-gadan ba saida ta kwana hudu tana
wahala. Ranar ma wuni tayi ta sake kwana, sai
da kowa ya fara karaya da lamarin, Hammadi da
yake da raunin zuciya sai da yayi kuka duk da
bai ganta ba, Abu ya gani da yanda tayi zuruzuru saboda tashin hankali, idanuwanta duk sun
Lubna sufyan
Hausabook.com 138
dashe alamar yawan kukan da ta sha, suna hada
ido ta girgiza masa kai alamar har lokacin babu
wani labari.
Kukan jinjiri ya fara sanar musu da ta sauka,
saida Datti ya tsugunna yana wani irin mayar da
numfashi, da gudun Abu ta fito take fada musu
mace ce aka samu, an kuma fito musu da ita
bayan an mata wanka, a karo na farko da Datti
yayima Hammadi kara yana nuna ma Abu
alamar da ta bashi ita ya fara dauka. Yaji dadi
sosai, murnar shi bata boyu akan fuskar shi ba,
daya mika ma Datti ita idanuwa ya kura mata
yana kallo, Julde yayi kyau, har aka dinga
maganar a cikin kauyen, amman baiyi kyau irin
na yarinyar da take rike a hannun shi ba. Har
saida Datti ya kalli Hammadi adan tsorace yana
fadin
"Kaganta Hamma"
Saboda ya tabbatar bashi kadai yake ganinta ba,
kai Hammadi ya daga masa
"Ance ba'a gane kammanin jinjiri. Amman tana
kama da Inna, fuskar Inna nake gani a tata"
Lubna sufyan
Hausabook.com 139
Saida ya fada Datti ya gani, yaga kamannin, yaga
kyawun Innar shi da ba zai manta ba, kyawunta
da yake zama abin magana akai duk inda zasu
shiga
"Shisa zata ci sunan Inna"
Datti ya fadi, yana kuma cikawa, yarinya taci
suna Karima.
"Muna da wani tsayayyen gari kuwa? To in dai
za'a tambayeni zan iya cewa Yelwa"
Inna ta taba bashi amsa, ba zai manta ba farkofarkon dawowar su Marake ne
"Ina ne Yelwa?"
Dariya Innar tayi
"Wani kauye ne a karkashin Shendam ta jihar
Plateau, Innata da Babana anan suka zauna suka
haifeni, shine gari na..."
Akwai sunaye da yawa da zasu iya yima Karima
alkunya da shi, saiya zabi Yelwa.
Lubna sufyan
Hausabook.com 140
"Ki rage fita da yarinyar nan saboda bakin
mutane da kuma miyagu, idan bikine ko suna ki
barta wajen Abu, idan tare zaku je ki biyo ki
kawota gida"
Shine abinda Innar A'i tace mata lokacin da taje
yawon arba'in ta kuma kwance goyon Yelwa
tana mika ma Innar A'i da ta karbeta tana kura
mata idanuwa. Ko ita haka take saka Yelwa a
gaba tana kallo, tana jinjina ma ikon Allah da ya
fitar da halitta kyakkyawa kamar Yelwa daga
jikinta. Julde na da haske, Yelwa ma haka,
amman farin yarinyar wani irin sirki gare shi da
zakayi zaton ta hada jini da buzayen kasar
Agadez
"Mahaifiyar babana buzuwa ce"
Datti yace mata randa tayi maganar, sai dai da
alamar wasa a muryar shi da kuma dariyar da
yayi bayan maganar, sai ta kasa tantance
tsokanarta yakeyi ko kuma hakikanin gaskiya
yake fada mata, ga kan Yelwa ya cika da gashi
zaka rantse basuyi askin sunan da Abu tace
Lubna sufyan
Hausabook.com 141
"Wanzamin nan bashida tausayi ko kadan, jibi
yanda ya sude kan yarinyar nan kamar sabuwar
kwarya dan Allah"
Har suka dinga mata dariya saboda tayita mitar
dake nuna alamun da an biye mata ba za'ayi
askin ba.
"Allah ya kare rayuwarki daga mugun baki"
Innar A'i ta fadi tana sake juya Yelwa, watakila
da a wani wajen Dije ta haihu ba gida ba, zatace
ko sunyo musaya ne sun dauko yar data hada iri
da larabawa, amman a gabansu Yelwa ta fado
bayan doguwar nakudar da mahaifiyarta tasha
"Kyauta, kyautar Allah ce kawai"
Ta gasgata zantukan Abu, Abu da bata iya boye
tsantsar soyayyar da take ma Dije da ahalinta a
gaban kowa. Dije kuwa dariya takanyi idan suna
irin maganganun nan, to saboda gudun bakin
mutane kuma sai ace ba zata fita da Yelwa ba,
miyagun da ake cewa har tsuntsaye suna zama
su dira gidan da suke so, su lashe kurwar wanda
tsautsayi ya giftawa, boyon Yelwa na me zatayi
musu? Tunda dai zasu iya rikida su shigo gidan,
Lubna sufyan
Hausabook.com 142
ko ma ba'a tsuntsaye ba, sun kawo talla har
cikin gida, kuma ba ganewa zatayi ba. Da
zuciyarta daya take fita, abinda zai faru tasan ba
zasu tsallake masa ba.
Tayi niyyar sai tayi isha'i zata wuce gida, shisa
ta kara mike kafa, bata hango Baba zai rushe
mata wannan shirin ba, sai da yammaci daya
shigo gidan ya ganta, yayi tsaye saida yaga ta
mike ta goya Yelwa, tayi ma su Innarta da Innar
A'i da yake ma fadan suna kallon yammaci yayi
har haka suka bar Dijen ta sake mike kafafuwa
maimakon su korata gida. Harta kai soron gidan
kafin ta karasa ficewa tana jiyo shi bai bar fadan
ba, murmushi ta danyi tana kama hanyar da
zata kaita gidanta. Kafin tunanin Bukar kamar
ko da yaushe ya diro mata yana danne komai.
Idan tace komai harda kafafuwanta da tunanin
ya jagoranta har kofar gidan Baabuga da bata
farga ba sai da tasa kai ciki da sallamarta.
Hararar da uwargidan shi Nana ta watsa mata
nasa wani abu ya tsirga mata, saboda har ranta
bata fito daga gida da tunanin kafafuwanta zasu
daukota su kawo gidan Baabuga ba, zuciyarta
ce, da kuma son ganin Bukar da takeyi
Lubna sufyan
Hausabook.com 143
"Ina wuni"
Ta gaishe da ita cikin harshen hausar da tasan
tana ji, amman sai ta tsaya da kullin gyadar da
takeyi tana kallonta kamar bata tabajin yaren
da tayi magana da shi ba
"Ya kuke? Ya yara? Daman nazo wucewa nace
bari in shigo mu gaisa in kuma duba Bukar"
Wannan karin Dije tayi maganar cikin harshen
fulatanci tana yawo da idonta cikin gidan da
yake kaca-kaca, kwantsin kayan wanke-wanke
ko ina, harda wata miyar kuka mai munin gani
da ta zube a kasa, bakuma a damu da ko kasa a
zuba mata ba, an bar wajen harya bushe kudaje
sunyi dandazo suna shagalinsu
"Lafiya... Baya gidan to"
Wani rugugi Dije taji cikin kirjinta
"Baya gidan? Yana ina? Ina yaje?"
Ta jero tambayoyin cikin taradaddi
"Ina zansan inda yake ko inda yaje? Sun fita
wasa da yara"
Lubna sufyan
Hausabook.com 144
Nana ta amsa a zafafe, Dije bata bi takanta ba ta
juya tana nufar inda ta fito, dogon tsaki da zagin
da Nana ta rakata dashi na isa kunnenta, amman
bai mata zafi ba, batajin akwai wani abu da za'a
fada ko ayi mata a lokacin da zataji zafin shi
kwatankwacin zafin da takeji a kirjinta a
lokacin. Bukar take hangowa a yawon gantali,
irin gantalin da yaran gidan Baabuga sukeyi, ta
tuna ranar da aka zabga da zafinta bai gushe ba
har yammacin da take gabannin faduwa, ta
kuma tabbatar zaiyi wahala idan da takalma a
kafar Bukar, ko yaci abincin rana ko baici ba,
wannan duk wani abune da bata da tabbas akai.
Hannu takai tana share zafafan hawayen da
suka zubo mata, idan tabi ta bayan gidan
Baabuga zaifi mata saukin zuwa gida, a
maimakon tabi ta hanyar da ta fito, kusan zai
zamana kamar tayi zagaye. Hawayenta sun kasa
daina zuba, zuciyarta ta cunkushe da tunani
kala-kala, gefen mayafinta tasa ta share
hawayenta da suke hana mata ganin hanya da
kyau, kiris ta fada kwatar dake bayan gidan
Baabuga, bayan da tayi tana kusan take wani
dan yaro da yake kwance jikin katangar gidan,
Lubna sufyan
Hausabook.com 145
yanayin kayan jikin shi da daudar su na nuna
alamun cewa almajiri ne. Kai ta girgiza kawai
tana tsanar iyayen da suka turo karamin yaro
kamar wannan almajiranci.
Har tayi gaba ta dawo, bambancin rayuwar
gidan Baabuga da wannan shine kawai akwai
tabbacin zasu ci abinci, ko basu koshi ba za'a
dafa sau ukkun nan, ko babu dadi rana bata taba
fitowa ta fadi ba'a dora tukunya ba. Dan
rankwafawa tayi tana kamo dantsen hannun
yaron, zafin zazzabin dake jikin shi na ratsa
kayan shi yana shiga tafin hannunta
"Kai baka da lafiya ne ha..."
Sauran maganar ta makale mata bayan ta dago
shi gabaki daya ta kalli fuskar shi, taga fuskar
Bukar ko abinda yayi saura a fuskar tashi
saboda bakin dauda da yayi, sumar shi da yake
da yalwarta ta cakude kamar sabon mahaukaci,
kafafuwanta taji sunyi sanyi har suna barazanar
kasa daukarta, bangon wajen ta dafa tana
kokawa da numfashin da take ja tana fitarwa a
wahale
"Bu.. Bukar"
Lubna sufyan
Hausabook.com 146
Ta furta tana rabo hannunta daga bangon ta
hada duka biyun ta tallafi fuskar shi tana
dubanshi, tana duban gudan jininta, tana jin
wata tsana ta taso mata tana zama a kirjinta,
amman bata da wanda zata jefa da wannan
tsanar, sai dai ta rarrabata a cikin jikinta,
saboda itace sanadi, ita tabar rayuwar Bukar
haka, itace bata tsaya tayi fada yanda ya kamata
da Datti akan rike Bukar din ba. Dagashi tayi
tana sabar shi a kafadarta, bata taba ganin nisan
gidanta irin yau ba, harta karasa kuka takeyi,
duk da maimakon ta shiga gidanta, gidan Abu ta
shiga
"Adda kinga Bukar.... Kalli Bukar dina Adda..."
Dije ta karasa maganar wani irin kuka na kwace
mata, tasowa Abu tayi tana karbar Bukar daga
hannunta, zuciyarta na wani irin dokawa ganin
yanda yaron yabi jikinta kamar babu numfashi a
jikin shi, karasawa tayi ta kwantar dashi kan
tabarma, jikinta ko ina yana bari, ruwa ta dibo
ta dawo ta zuba a hannunta tana shafa ma Bukar
din, zuciyarta take ji a tafin hannunta saboda
tashin hankali, sai da tayi hakan kusan sau hudu
sannan yaja wani dogon numfashi yana bude
Lubna sufyan
Hausabook.com 147
idanuwan shi da sukayi fari qal kamar bashida
wadataccen jini. Ita kanta Abu saida ta sauke
numfashin sannan ta samu nutsuwar mikewa.
Dije ta kama ta zaunar a gefen shi, tana gama
tuwo ta cika wata tukunya ta dora kan
garwashin da sauran itacen tabarta, tasan
komin zafi Hammadi saiya kashe ruwa yake iya
yin wanka, duk tsokanar da zatayi masa ba zai
kulata ba
"Hammadi kana bada maza, dan ruwan sanyin
nan ba zaka iya watsa ma jikin ka ba, yanzun da
yaqi ne kuma fa?"
Idan yana jin biye mata zaiyi dariya yace
"Yaqi daban, batun wanka da ruwan sanyi
daban, azo yakin mana kigani, sai dai labari
yazo miki ana ga Hammadin Abu can yana zubar
da maza"
Kuma wankan nan biyu a rana sai yayi, kafin ya
fita, sai kuma kafin ya kwanta, idan ta cika
tukunya ta rufe, sauran garwashin yana rike
ruwan zafin har lokacin da zai tashi wankan,
saita kwalfe, idan yayi zafi da yawa ta sirka
Lubna sufyan
Hausabook.com 148
masa, idan baiyi ba tabar masa haka. Cikin
wannan ruwan ne ta dauko bokiti ta diba tana
sirkawa, ta dawo ta dauki Bukar, sai da tayi
masa sabi uku tana tunanin anya tunda aka
mayar da shi gidan Baabuga yaron nan kuwa
yaga ruwa? Ita kanta saida tayi kwalla ganin
daudar da take wankowa cikin kan yaron kawai,
daudar da yayi kanta cuta ce ta daban.
Cikin kayan Julde ta samu wasa ta saka masa, ta
shafa masa mai, sai ga yaro ya fara dawowa
hayyacin shi, sai dai duk yayi kasusuwa, ga
kuma zazzabin har lokacin bai sauka ba. Duk
abinda akeyi Dije na zaune tana sharar kwalla,
da ido kawai take bin Abu, harta sake hada wuta
ta dama masa kunun kanwa da yaji sikari, dan
tasan da wahala ya iya cin wani abinci mai
nauyi, da kanta ta dinga bashi, baifi ludayi biyar
ya sha ba ya girgiza mata kai yana komawa ya
kwanta. Bata matsa masa ba
"Ki tashi kiyi alwala..."
Ta ce ma Dije da bata musa ba ta mike, tana tuna
Yelwa na goye a bayanta, da yake bata da rigima,
Lubna sufyan
Hausabook.com 149
in kaji kukanta yunwa ce ko kuma an tsomata a
ruwa za'ayi mata wanka.
"Ba zan mayar dashi ba Adda, sai dai in hakura
da auren Datti, amman wallahi ba zan mayar
dashi gidan Baabuga ya mutu ba"
Ta karasa maganar tana goge fuskarta da bayan
hannunta, jin saita shiga bayi yasa ta kwance
Yelwa tazo ta kwantar da ita. Ko da tayi alwala
ta zo ta gabatar da sallah, ji tayi ita kanta bata
yadda da ingancin sallar da tayi ba, saboda
rabinta tunanin yanda zata fuskancin Datti ne,
shisa ta kara sakewa, zaune tayi a inda tayi
sallar har aka kira isha'i, ta mike ta gabatar da
ita. Ko da Abu tayi mata tayin abinci kai ta
girgiza mata, rikicin da take ji ya gama cika
mata ciki, bata da wajen saka wani abu. Balle da
taji sallamar su Dattin, muryar shi na danne ta
Hammadi, alamar yana cikin nishadi, sai taji ta
kara harzuka.
Saboda Hammadi ne kawai tayi musu sannu da
zuwa, ko Julde da yazo ya fada jikinta daga shi
tayi, girman Hammadi a idanuwanta na hana ta
wanka ma Julde mari saboda ta fara batama
Lubna sufyan
Hausabook.com 150
Datti rai, sai yafi biye mata ko zata fada masa
maganganun da zaisa zuciyarta ta sauka.
"Dagani dalla...kai baka san ka girma ba"
Ta fadi tana sake ture Julde, da yake yana da
kulafaci baiyi zuciya ba ya sake binta.
"Waye wannan a kwance?"
Datti ya tambaya yana zama kan tabarmar da
Abu ta shimfida musu
"Kai dai kuci abincin tukunna"
Ta fadi da sauri tana katse Dije da ta numfasa ta
bashi amsa, bai musa ba, abincin ta zuba tana
kawo musu. Suna ci suna hirar da Datti yake
kokarin sako Dije ciki ganin yanda ta koma gefe
kamar bata gidan, hakan da yayi baisa ta kula
shi ba, zuwa yanzun sai dai yaba wani labarin
halayenta, ranta a bace yake ba sai ta fada masa
ba. Bai dai san dalilin bacin ran bane, yasan
bashi bane tunda lafiya lau sukai sallama da
safe. Har sai da ya wanko hannun shi ya dawo ya
zauna, ya dauki kwanon ruwa ya kafa a bakin
shi kenan ya tsinkayi muryarta
Lubna sufyan
Hausabook.com 151
"Bukar ne na dauko, bashi da lafiya, na dauko
dana, ba kuma zan mayar da shi ba..."
Tayi maganar tanajin wani daci a makoshinta,
saida yasha ruwan shi sannan ya sauke kwanon
yana kallonta, fitalar kwan dake ci a tsakar
gidan bata haska masa fuskarta yanda yake so,
amman yana fatan ita tana ganin fuskar shi,
saboda taga yanda maganarta ba mai yiwuwa
bace ba, ta karanci fuskar shi, ta kuma gani a
idanuwan shi ba zai zauna da Bukar ba
"Mayar da shi kuwa zakiyi, bashi da lafiya ba
matsalata bane ba, na rigada na gaya miki ba
zan rike shi ba, wallahi babu wanda ya isa
yasani rike dan Baabuga"
Ya karasa maganar yana mikewa ganin
Hammadi na shirin saka musu baki
"Idan ba zaka rike dan Baabuga ba, dana fa?
Datti dana fa? Ko ka manta ba dan Baabuga bane
kawai, nima dana ne, Bukar dana ne kamar
yanda yake dan Baabuga, idan ba zaka rike dan
Baabuga ba, ka rike nawa tunda nima ga naka
nan ina rike da su..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 152
Wata dariya Datti yayi, dariyar da bata da alaka
da nishadi, asalima kirjinshi ya dauki wani irin
zafi da maganganun da tayi
"Dije ni zaki gayawa Bukar danki ne ke da
Baabuga? Ni zaki kalla kina fadamun ke da
Baabuga dan ku ne? Ni?"
Rigar shi Hammadi ya dan kamo
"Ka zauna Datti, ka zauna muyi magana gabaki
daya..."
Mikewa Dije tayi itama, idonta ya rufe, ta dauki
kunyar Hammadi ta ajiye a gefe, idan Bukar din
ya mutu ta kula ita kadai take da asara ba Datti
ba
"Sai me dan na fada maka? Karya nayi? Gani
nayi kamar ka manta shisa nake tuna maka...
Yarone na dauko shi ba zan mayar da shi ba
kuma wallahi, sai dai ka sawwake mun ni da shi
duka sai mubar maka gidanka, in dire maka
naka yaran ka nemo wadda zata rike maka su..."
Sosai yake kallon Dije yana mamakin yanda ta
saka idanuwanta cikin nashi tana fada masa
maganganun nan,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 27