Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da take baka tana dorawa a sama, fuskarta fayau inka cire ta gilashin da yake manne a jiki, tayi masa kyau har baisan ajiyar zuciya ta kubce masa ba. Da kasala ya mika hannu ya bude mata murfin motar ta shigo tana zama. Ta jingina jikinta da kujerar motar sosai bayan ta rufe kofar, sannan ta dan juyo da kanta tana kallon shi, farar rigar da take jikinshi ta kara haska fatarshi, wannan kyawun nashi da yafi na kowa a gidan yana fitowa. Kallon shi takeyi kamar tayi wata bakwai bata ganshi ba maimakon kwanaki, idanuwanshi sunyi zuruzuru kamar wanda yayi jinya, sai taga kamar yayi duhu bayan ramar da yayi mata, ga gajiya fal idanuwan shi. Ta raba idanuwanta daga fuskar Yelwa, ta kalli inda yake don ta samu saukin hargitsin da takeji sai taga baya dakin, hakan ya tilasta mata maida kallonta kan Kabir daya samarwa kanshi wajen zama kan daya daga cikin kujeru masu zaman mutum daya dake dakin. Lubna sufyan Hausabook.com 586 Sai take ganin fuskarta a cikin tashi, bambancin na gashin da yake a tashine da kuma gilashin da yake tata fuskar. Shima ita yake kallo, saita dauke idanuwanta tana tashi tabar falon gabaki daya zuwa dakinta, a karo na farko tana kullewa daga ciki dan batason kowa ya shigo mata, ta hau gado taja bargo tana rufe jikinta gabaki daya duk da ba sanyi akeyi ba. A litattafai ba haka haduwa da iyaye bayan wasu shekaru yake kasancewa ba, wasu za'ace suna sauke idanuwansu akan mahaifiyarsu ko da basu santa ba zasuji a jikinsu cewar sun hada jini da ita, zasu ji wannan hadin da yake tsakaninsu tun suna kwance a cikinta, kafin wata irin kauna da basu tabaji akan wani ba ta dirar musu. Sai rungume rungumen juna ya biyo baya, cike da hawaye, sannan tarin tambayoyi, ina kika shiga? Me ya faru dake? Bayan amsa wannan tambayoyin, uzuri, uzuri saboda kauna da murnar ganinta ta cika zuciyarka. Ita akasin hakane ya faru da ita, ta kalli Yelwa, babu komai a zuciyarta sai mamaki, duk wasu tambayoyi sai suka bace mata suna barin guda daya tal, tana da rai bata nemesu ba duk tsayin lokacin nan? Lubna sufyan Hausabook.com 587 Sai wani kunci ya ziyarceta yana danne mata komai. Data kalli Kabir sai taji babu abinda yayi mata bayan tambarin kasancewar shi mahaifinta da jininshi da yake da karfin fisgar da yawa daga cikin kamanninta, sai kuma tabon da take tunanin shi da Yelwa sun hadu wajen ganin ta kasance dashi har karshen rayuwarta. Da ta kwanta din a daki, tayi juyi sai muryar Salim ta dawo mata "Ina son ki" Ko da kaddara ta zabar masa ita a matsayin yar uwa yana da zabin sonta ko akasin haka. Saiya zabi ya sota a matsayin 'yar uwa. A hankali sai lokaci ya juye hakan ya kalleta a matsayin mace batare daya duba cewar nata iyayen ma sun nisanta kansu da ita ba ya sota. Kafin nan Salim na tabbatar da bataji kadaici ba, yana kula da duk wani abu daya danganceta, karami ko babba, mai muhimmanci da marar muhimmanci duka a wajen shi basu da wani bambamci. Shisa bai zauna ba sai da ya gano mata iyayen da yanzun take jin kamar bata shiryawa ganinsu ba. Lubna sufyan Hausabook.com 588 Duk wani abu da zai sama mata sauki shi Salim yakeyi, me take jira da ba zata amsa soyayyar da yake miko mata duk da bata cancanceta ba? Da ta sake juyawa kwanciya sai wasu hawaye masu dumi suka zubo mata. Suka cigaba da fitowa tun tana goge su harta daina. Taji dadi da babu wanda yazo ya kwankwasa mata saida ta tashi da kanta dan tasan ya kamata ace ta dora musu girki duk da batajin yunwa. Idan bata fita ba Daada zatace ta dora. Sai dai tana samu ta sauko daga gadon ta bude kofar ta fita falon sai taci karo da abinda batayi tsammani ba, ta kuma yi mamakin nisan da hankalinta yayi da jikinta har bata juyo hayaniyar dake faruwa ba haka. Julde ne ya kama Kabiru ya shake shi, yanda yake jjijjigashi zai sanar dakai Kabirun baya wani yunkuri na ganin ya kwace kanshi ko ya hana Julden abinda yakeyi, tana hango kyallin hawayen da yake cikin idanuwan Kabirun. Saratu ma tana nan ta tsaya a gefe tana saka mayafin jikinta tana share kwallar da take zubar mata, Yelwa ce ta riko Julde tana fada masa abinda baya karasawa kunnuwan Madinar saboda wani yanayi daya lullubeta, wani yanayi Lubna sufyan Hausabook.com 589 na son bama Kabiru kariyar da bata samu daga wajen shi ba. Ko da Julde ya sake shi yanda ya koma cikin kujerar batasan kafafuwanta suna takawa ba sai da ta ganta tsaye a gabanshi, sai dai bakinta yayi mata nauyi da tambayar da take mata yawo a cikin kai "Baka ji ciwo ba? Babu abinda ya sameka?" Sune abinda take son tambayar shi, sai hawaye ne suka taho mata a maimakon maganar "Hamma....Hamma dan Allah..." Ta tsinto muryar Yelwa data durkushe a kasa tare da Julde daya hade fuskar shi cikin hannayen shi yana kuka kamar karamin yaro, itama kukan takeyi, su duka kuka sukeyi banda Yelwa da take kokarin lallashin Julde babu wanda yake wani yunkuri wajen ganin ya ba wani hakuri, Julde ne ya bude fuskarshi yana kallon Yelwa "Sai kika bishi? Sai kika zabe shi akanmu? Farin cikin shi kika auna da tashin hankalin da zamu shiga kikaga farin cikin nashi yafi Lubna sufyan Hausabook.com 590 muhimmanci...idan kina tunanin su Daada ba zasu fahimce ki ba Yelwa nifa?" Kai take girgiza masa, soyayyar Kabir ce ta fada mata zata iya hakura dasu, zata iya nisa dasu, dashi, zata iya tsallake kowa a ciki hardashi, amman ko nisa motarsu batayi ba wani abu ya danne zuciyarta. Shine abu na karshe data yi duk wani kokari na ganin ta binne can kasan zuciyarta, ko kewar kowa na nukurkusarta bata bari tashi ta taso mata "Hamma..." Ta furta cikin kuka tana sake rikoshi, kwacewa yakeyi tana sake kai hannu ta rikoshi ya sake tureta, sunyi hakan fiye da a kirga kafin ta dago rinannun idanuwanshi ya kalleta, saiya kamo hannuwanta yanajin gazawar da yayi a cikin kulawa da ita da ganin wani abu makamancin hakan bai faru da ita ba, yana jin kuskuren daya kusa aikata mata da yanzun bai samu karfin gwiwar tsayawa a gabanta yana fadin ta barsu ba "Hamma dan Allah..." Lubna sufyan Hausabook.com 591 Yelwa ta sake fadi a wahalce, kai ya jinjina mata kamar ya amshi yafiyar da take rokonshi duk da bata furta ba, yana saka wani gunjin kuka kwace mata, kukan da Madina taji ya ratsa zuciyarta yana sakata son rike Yelwar ko zata sama mata sauki. Saita sake barin wajen tana komawa daki kawai, waye yake da nutsuwar jin yunwa harya iya cin wani abinci a halin nan da suke ciki? Sai dai da daddare Daada ta kwankwasa mata daki ta miko mata abinci a robar da ta tabbatar mata da siyowa akayi, ganin tambarin restaurant din manne da robar tasan Julde ne, dan yana son abincin wajen, yana yawan yi musu siye-siye a gurin. Ta ci kadan da fatan Salim bai zauna da yunwa ba manne a zuciyarta. Taso ta kirashi amman jikinta kamar anyi mata duka haka take jinshi, da ta samu tayi isha'i saita kwanta. Wannan karin bata kulle kofa ba, kuma fitilar da take karatu da ita a kunne take, shisa taga shigowar Yelwa, ta kuma bita da idanuwa data ga tahau gadon, sai taja jikinta ta matsa can karshe, kwanciya Yelwar tayi batare da tace mata komai ba. Saita tashi zaune ta mika hannu ta kashe fitilar, duhu ya mamaye dakin, ta koma Lubna sufyan Hausabook.com 592 ta kwanta tana sauraren bugun zuciyarta da yayi kasa. Haka kawai taji hawaye na taruwa a idanuwanta, saita cire gilashin ta lankwashe shi tana ajiyewa can gefe. Hakan kuma yaba hawayenta damar saukowa, kuka takeyi batasan yayi karfin ba sai da taji hannuwan Yelwa sun rikota, sai wani abu ya sake saukar mata yana sa kukan kwace mata sosai, kuka tayi a jikin mahaifiyar da bata hango sakata a idanuwanta ba, kuka tayi irin wanda bata tabayi ba a yan shekarun da take dasu. Kuka tayi har bacci ta dauketa. Kuma a kwanakin nan duka basa wata magana da Yelwa, banda gaisuwa, batasan me zatace mata ba, Kabiru ma yazo sau biyu, duka zuwan sun gaisa, duk da Daada da Yelwa sun basu waje, zama kawai sukayi batare da sun cewa juna komai ba, da alama basu san ta inda ya kamata su fara ba, bai sake dawowa ba, inya dawo dinma har yanzun bata san me zatace masa ba. Wuni takeyi a dakinta, daga gidan Julde ake kawo musu abinci yanzun, abinda ko da sallah bata taba ganin anayi ba. Duk dare kuma Yelwa zata zo dakinta ta kwanta, ko da bataje jikinta a Lubna sufyan Hausabook.com 593 lokacin ba idan tayi bacci to inta farka tana manne da ita kamar mai son komawa cikinta dan karta sake tafiya ta barta. Yau kuma da ta tashi wasa take tayi da wayarta, kamar tana jiran kiran Salim da take da yakinin ya bata wajene dan ta samu lokaci dasu Yelwa. Amman kamar kwanakin sunyi yawa, tun bayan data sanshi basu taba daukar lokaci mai tsayi basu ga juna ba haka, kasa hakuri tayi da yamma shisa ta kirashi, yanzun kuma da ta ganshi a gabanta sai wata sabuwar kewarshi ta kara danneta, da taga ramar dake fuskarshi sai zuciyarta tayi mata nauyi "Me ya sameka" Ta tsinci kanta da tambayar shi, kafadu kawai ya dan daga mata, me zaice? Ita ta same shi? Tunaninta ne ya hana masa sukuni? Ko kewarta? Duk inda aka zagaya, duk wata kwaskwarima da zaiyiwa kalaman karshe dai ita dince damuwar shi "Karatuna fa?" Lubna sufyan Hausabook.com 594 Muryarta ta fito can kasan makoshi, da ba shi bane zai wahala aji me tace, kallonta yayi cike da rashin fahimtar inda tambayar ta dosa "Idan na aureka, Hamma karatu na fa?" Ta furta wannan karin tana saka idanuwanta cikin nashi kafin ta sauke kamar abinda take gani a cikin nashi ya girmi daukarta, kallonta yakeyi tambayarta nayi masa yawo "Mug..." Ya kira, bata dago ta kalle shi ba "Saboda abinda nayi ne zaki aureni?" Abinda yayi na gano mata su Yelwa, tasan shi yake nufi, kai ta girgiza a hankali, ba saboda shi bane ba, saboda kafin ta shigo motar babu wannan tunanin a tare da ita, batasan zatayi masa tambayar da tayi masa ba. Kamar yanda ya fado rayuwarta babu shiri, ta fito daga dakine ta ganshi tsaye a cikin kitchen din Daada a ranar, haka kuma ta fito daga makaranta ne ta hange shi a tsaye a jikin motar shi kamar ya saba jiranta. Kamar yanda duk wani abu daya shafe shi yake faruwa da ita babu wani shiri haka Lubna sufyan Hausabook.com 595 wannan ma, kamar yanda ya fada mata yana sonta a karo na farko bata fahimci kalar son da yake nufi ba, haka a karon karshe data fahimci inda ya dosa duk da batayi tsammani ba haka taji bata da wani daya kamata ta raba sauran kwanakin rayuwarta dashi da zai wuce mata shi. Da safen nan da ta tashi ta janyo durowar kusa da gadonta da nufin saka wasu cikin litattafanta, sai taga agogon da Nawfal ya bata ranar da zai tafi. Da ta kalli agogon sai ta hango shi da Murjanatu a ciki, zata rantse da Allah taji muryar shi ya kira "Jaan..." Ta kuma hangi idanuwan shi da baka ganin komai a cikinsu idan Murjanatu na gabanshi sai son da yakeyi mata, kamar yanda a cikin nata idanuwan zakaga yanda duniyarta take tsaye tare da Nawfal din. Ko abinci ta zubo musu, tana ajiyewa Nawfal din nashi Murjanatu take dauka, zata ajiye nata a gefe saita tabbatar na shi ya huce, ta fara ci, ko ruwa Nawfal zai sha idan tana kusa saita fara sha take mika masa, kamar tana son tabbatar da abinda zaici yayi dai-dai yanda Lubna sufyan Hausabook.com 596 ba zai cutar dashi ba. Da ta saka litattafan ta danne agogon dasu ta mayar ta rufe, a karon farko taji tana son samun wannan kusancin da yake tsakaninsu, tana son ta kwanta ta tashi da sanin akwai wani a kusa da ita da ba zai taba barinta ba duk rintsi. "Bayan Daada, kaine abu mafi tabbaci a rayuwata Hamma, duk idan na juya ina ganinka...sanda nake bukatar dama sanda bansan ina bukatar ka ba sai naganka, duka kana nan..." Wani irin numfashi yaja ya sauke "Aurena ba zai shiga tsakanin ki da karatu ba..." Kai ta jinjina tana sake gyara zamanta a cikin kujerar "Hakan na nufin zaki aure ni?" Kai ta sake daga masa "Idan nace bana so ya dauki lokaci fa?" Kallon shi tayi tana jin inda rayuwarta a hannunta take zata iya bashi ajiya saboda zai Lubna sufyan Hausabook.com 597 kula da ita fiye da yanda zatayi, kai ta sake jinjina masa "Mug..." Ya iya furtawa yana hango nesan da tazo masa kusa, murmushi na kwace masa, yana kallon murmushin da tayi itama, sai dai bai iya hango akwai tazara a tsakanin wannan murmushin nata da sake yin wani ba. Ashe akwai ranar da zata zo da zai kalli Madina zuciyar shi cike fal da kishinta, kishin ma akan abinda ba a karkashin ikonta yake ba. Sai yau, da yake zaune a falon Daada, sai yau da suke gaisa da Yelwa, yaga Madina zaune a kusa da ita, kishi bai kara cika masa zuciya ba sai da akazo cin abinci, Madina ta saka lomar farko a bakinta, ta kai hannu da sauri tana fifita abincin a cikin bakin nata da alamun batayi zaton yana da zafi haka ba. Yelwa taja filet din gabanta tana bude mata abincin yanda zai sha iska sosai, kamar wata karamar yarinya. Ta ma bar nata abincin tana kallon Madina idanuwanta dauke da wani yanayi mai wahalar fassarawa. Duk wani fata Lubna sufyan Hausabook.com 598 nata ya cika, ba mahaifiyarta kawai tagani ba harda mahaifinta, harda wanketa daga zargin kowa akan asalinta. Shine babu wani buri akan bayyanar nashi iyayen. Sunje Marake shi da Khalid, da tambaya suka gano gidan Baabuga, ko da Khalid ya tsayar da mota a kofar gidan, baisan hannun shi na rawa ba sai da Khalid ya kira sunan shi a hankali "You are shaking Bajjo, ka tabbata ka shirya fuskantar wannan babin?" Numfashi yaja ya fitar, ya sake ja yana fitarwa, yayi hakan na kusan minti biyu sannan ya jinjinawa Khalid din kai, robar ruwan dake cikin motar Khalid ya dauka ya bude yana mika masa, ya karba, baisan yaji kishi haka ba, kadaj ya rage a robar, ruwan na samar mishi da nutsuwar bude murfin motar ya fito. Da suke aika cikin gidan ayi musu sallama da Baabuga, kafin ya fito kafafuwan shi Nawfal yaji suna rawa, dole ya tsugunna yana wani irin maida numfashi. Wata muryace take ta masa ihu cikin kai tana karasawa zuciyar shi da wani irin amo Lubna sufyan Hausabook.com 599 "Kakan ka zaka hadu dashi yau, Baban Bukar" Da wani yaro ya fito daga cikin gidan sai Nawfal ya bishi da kallo yana tunanin ko dan gidan ne, idan dan gidan ne, jinin da yake jikin shi shine a jikinshi kenan? Ya zasu karbe shi? Bayan basu san dashi ba, in suka tsane shifa? In suka tambaye shi ina Bukar fa? Ina mahaifiyar shi? Me zaice musu? Wacce amsa yake da ita? Wacce hujja ma yake da ita daga farko da zata tabbatarwa da Baabuga cewar shi din jinin Bukar ne? Duka wannan shakkun da yake dashi sai yabi ruwa lokacin da Baabuga ya fito da sandar da alamu suka nuna tana taimaka masane wajen tafiya, ya kuma zabi ya fara sauke idanuwan shi akan Nawfal din, yana kallon shi, kallo na tsanaki, kafin mamaki, tantama, wani sabon mamakin ya mamaye fuskar shi. "Ko ba'a tona ba yaro kai jinin Dije ne..." Baabuga ya fadi yana maida idanuwan shi kan Khalid, sai lokacin kuma Nawfal din ya samu ya iya mikewa tsaye, wannan karin da Baabuga ya kalle shi sake matsowa yayi yana kama hannun shi, muryarshi na rawa yace Lubna sufyan Hausabook.com 600 "Jinin Bukar ne kai?" Kaine kawai abinda Nawfal ya iya dagawa, makoshin shi ya bushe kamar bai sha ruwa ba,murnar dake fuskar Baabuga na saka shi sauke numfashin da ya tafi da kaso mai girma na karfin shi, da Baabuga ya kamashi yana kokarin janshi cikin gidan saiya kalli Khalid, kallo da yake fassara "Ya zanyi Hamma? Anya na shirya? Ka taimakamun" Sai Khalid din yayi masa murmushi yana dan daga masa kai kawai. Haka ya bi Baabuga har cikin gidan yanajin shi kamar mai yawo akan iska, yanda duk akayi dashi haka yake binsu, murmushin dake fuskar shi yakeji kamar plaster aka manna masa, ya rasa asalin abinda yake ji, bawai dan sune yan uwan shi daya hada jini dasu daya fara gani ba, gasu Khalid, amman yanajin kamar nan din tushen Bukar ne, mahaifin shi, yan uwan shi da suka hada uba dasu. Sai tambayoyin da yake hanawa kanshi a tsayin shekarun nan suka taso suna lullube shi. Ina Bukar? Me yasa zai kawo shi ya ajiye shi bai Lubna sufyan Hausabook.com 601 sake waiwayen shi ba? Ina mahaifiyar shi? Me yasa ko idanuwanshi ya rufe, yanda duk zaiyi yawo a cikin tunanin shi baya iya lalubo ko da muryarta ne, anya akwai abinda ya kai rashin sanin iyaye ciwo? Akwai kadaicin da yafi na ka taso ba a kusa dasu ba zafi? Ranar duk wani taro na iyaye da za'ayi a makaranta, idan yaga Julde sai yaita kallon shi, idan ya juya yaga wasu iyayensu duka biyun suka halarta sai wani abu ya motsa a cikin zuciyar shi, idan suka dawo da sakamakon su, yaga su Khalid sun nufi bangaren Saratu shi ya nufi nasu da sakamakon da bashi da mahaifiyar da zai nunawa ta gani ta tayashi murna sai wani irin kadaici yayi masa rumfa. Da suka fara hankali sai Khalid ya wuce bangarensu tare dashi. Duk wani abu da zai kara masa radadin rashin nashi iyayen a kusa Khalid na kauce masa. Bashi kadai bama har su Adee, saboda duk yanda ake bikin ranakun iyaye na duniya ko Julde bai taba ganin sun saka ba, ko da suna sakawar suna tabbatar da baigani ba balle ranshi ya sosu. Lubna sufyan Hausabook.com 602 Daga baya zai samu Salim a tsaye a bakin kofa, zai mika masa hannu alamar ya bashi sakamon yana dorawa da "Kayi abin kirki ko ka kunyatani?" Haka daya tafi kasar waje, schedule dinshi gabaki daya Salim ya saka ya tura masa ta email, yana ganin duk wani motsin shi, ranakun da yake da presentation, test, da kuma jarabawa. Sai daya zamana duk wata nasara da zai samu a harkar makaranta, yana da wanda zai raba hakan dashi. Sunyi duk wani kokari, suna kanyi wajen rage masa kadaicin da suke tunanin sunsan yanaji. Amman a cikinsu babu wanda zai taba fahimta, babu wanda zai gane, Madina ce kadai zaice tasan abinda yake ji, ta fahimta, ita kadaice yake kallo yanajin bashi kadai bane ba, akwai wanda ya fahimta. Shisa yau yakejin wani irin kishinta da bai taba tunani ba, a wani sashi na zuciyarshi sai yakejin kamar taci amanarshi ne da tabarshi ya tsaya shi kadai yanzun a wannan kadaicin na rashin majingini. Ya zataga nata iyayen ita kadai? Shi kuma fa? Ta ina zai fara yanzun? Wa zai kalla ya Lubna sufyan Hausabook.com 603 fahimce shi batare da yace komai ba. Ya dauka ganin su Baabuga, ganin yawan dangin da yake dasu ya rage masa wani kaso a cikin wannan kadaicin, ashe karya yayiwa kan shi. Ya daiji dadi, ko yanzun akayi masa maganar tsatson shi yana da inda zai nuna, yana da dangin da zai nuna yace tushen shine, asalin shi. Ko Baabuga bayan sun natsa ya kalle shi yace masa "Bukar fa?" Yanajin idanuwan Khalid da yake zaune a gefe suna bin shi, ya hadiye wani katon abu dayaji ya tokare masa makoshi kafin ya iya fadin "Bansani ba, bansan inda yake ba" Da dukkan gaskiyar shi, kai Baabuga ya jinjina masa kamar ya fahimta. Sunyi sallama cike da mutunci da alkawarin Nawfal din na cigaba da kawo musu ziyara lokaci zuwa lokaci, ya kuma yi musu alkhairi. Da suka fito daga gidan suka shiga mota saiya kalli Khalid yace "Hamma anya mun kyauta idan muka juya bamu nemi ahalin Daada ba?" Lubna sufyan Hausabook.com 604 Kafadu Khalid ya daga masa, shi ba mai hayaniya bane ba, asalima zai iya kirga abubuwan da suke bata masa rai da lokuttan da hakan ya faru da yatsun hannuwan shi. Sai dai a gabaki daya labarin Daada da yaji daga bakin Nawfal, ranshi yayi bacin da bai tabayi ba, zuciyarshi ta sosu da yanda dangin Daada suka juya mata baya a lokacin da tafi bukatarsu. "Su suka cireta daga cikinsu, su suka kyamaceta, me yasa zamuje wajen su?" Khalid ya fadi da zafin da yakeji a zuciyarshi "Babu abinda lokaci ya koya maka ne Hamma? Baka kallon Daada? Baka ganin kewar tsatsonta a tare da ita? Bakaji bane ba, bakaji muryarta sanda take bani labarinsu ba, bakaga zubar hawayenta ba da kaine mutum na farko da zai fara nemo mata su yayi kokarin gyara alakar da take tsakanin su" Kauda kai Khalid yayi, ranshi a bace yake shisa kalaman Nawfal din basu tabashi ba, ko da suka nemo gidansu Daada, dakyar Nawfal ya shawo kanshi ya fito daga mota, sai dai ba'aje ko ina ba, hawayen da yake zuba daga idanuwan yan Lubna sufyan Hausabook.com 605 uwanta mata guda biyu da suka samu a gidan ya fara karya masa zuciya. Da akaje aka kikkira sauran sukazo suka zagaye su sai komai yayi masa wani iri, sai rikesu sukeyi suna fadin "Jikokin Dije ne, Dije tana raye" Gabaki daya gidan ya hargitse da koke-koke, dakyar suka bari suka taho su kadai bayan sunyi musu alkawarin dauko Daada su kawota, dan mutum biyu cikin yayyenta maza sunso binsu, sai dai basu shirya ba, sunyi musu maganar su kwanane su kuma sukaqi, suka dai taho da alkawarin zasu koma. Da suka hau hanya sai da Khalid ya sauka gefen titi yana hade kanshi da sitiyarin motar na dan wani lokaci. Nawfal baice masa komai ba, ya barshi ya dauki lokacin da yake bukata wajen tattara nutsuwar shi kafin ya iya jan motar suka cigaba da tafiya. Yaji dadin yanda Murjanatu bata tambayeshi komai ba, ta dai kama hannuwan shi taja shi jikinta tanayi masa rungumar da yake bukata. Ranar ne kuma ya samu hotel inda ya kama musu na sati biyu, kamar yasan Yelwa zata Lubna sufyan Hausabook.com 606 dawo. Yau da yace mata ta shirya su taho gidan Daada tare, kallon shi tayi batare da tace komai ba "Kema sai ku gaisa" Kallon shin dai ta sakeyi "Jaan" Ya kira "Zanje mu gaisa, amman ba yau ba, yau kaje cikin ahalinka" Matsawa yayi yana rikota "Kema ahalina ce" Ta sauke numfashi "Nasani, amman yau ne zaku fara haduwa, kuma ku duka zakuje, baka tunanin zaiyi wani iri idan nayi muku zaune? Kowanne yanayi zaku shiga sai dai inyi kamar na fahimta, amman kasan bansan me kukeji ba, zanje idan duka kun samu natsuwar da zamana a cikinku ba zaiyi wani iri ba" Lubna sufyan Hausabook.com 607 Amman da tazo da yanzun tana zaune kusa dashi, da zai juya ya kalleta, zai rage wannan kadaicin da yakeji na ganin Madina ta samu duk wani abu da take mafarkin samu. Duk da yanzun daya nutsar da hankalin shi akanta yaga kamar akwai wani abu a tattare da ita, tayi wani irin sanyi da bai taba gani ba. Bai san sanyin jikinta na da alaka da Salim bane ba, ta dawo gida a jiyan. Ta samu Daada a daki, saita karasa jikinta ta kwanta tana sauke numfashi "Daada..." Ta kira da sanyin murya tana dorawa da "Yayi kusa idan nayi aure yanzun?" Kallonta Daada tayi "Shi aure baya kusa kuma baya nesa ai Madina, musamman a rayuwar mace. Aure kike so?" Numfashi taja ta sauke tana rufe idanuwanta, yanayinta take ji babu dadi haka kawai, bugun zuciyarta ma kamar yayi kasa "Hamma Salim" Lubna sufyan Hausabook.com 608 Ta furta kamar sunan kawai ya isa ya amsa tambayar da Daada tayi dama wadda zatayi a gaba. Wannan karin da wani yanayi a fuskar Daada take kallon Madinar kamar tana neman tabbacin maganar da taji "Salim? Salim kike so ki aura?" Kai ta tsinci kanta da dagawa Daada a hankali tana sake shigewa jikinta. Kallonta Daada takeyi har lokacin, ta rasa mamaki ne take ji ko taraddadi, ba zatace mamaki ba, sai dai tace tayi kokarin nisanta kanta da wannan tunanin duk kuwa da alamun da Salim yake nunawa a yanayin ziyarar shi da siye-siyen da yakeyiwa Madina, dama kacokan yanda a tare da ita halayenshi suke canzawa. Tasha hangowa Madina aure, amman har ranta ba da Salim ba, da Nawfal take hango mata wannan rayuwar. Burinta ya dishene lokacin da Nawfal yayi aure, amman bawai ya bace bane gabaki daya. Kuma yanzun ta ina Madina zatace ta auri Salim bayan abinda Julde yayi kokarin yi? Idan ta sani zata yarda ta aure shi? Idan ta aure shi ta sani daga baya fa? Zata iya yafewa Julde harta cigaba da zama da Salim din a matsayin miji? Lubna sufyan Hausabook.com 609 Kaddarar su mai nauyi ce tasani, ta dauka zata tsayane kawai akan yaranta, amman alamu suna nuna har kan jikokin nata zata tsallako. Wani abu da zuciyarta take tabbatar mata ba zata iya dauka ba "Ke kina son Salim din?" Ta tambaya da wani yanayi a muryarta da yasa Madina bude idanuwanta tana nazarin fuskarta "Bakya son shi Daada?" Kai ta girgiza mata a hankali, saita dago daga jikinta tana kallon cikin idanuwanta "Bakya sona da Hamma Salim" Madina tayi maganar wannan karin da tabbaci tana dorawa da "Me yasa?" Kai Daada take girgiza mata, wani abu takeji yayi mata tsaye a kirjinta "Ina son shi" Ta furta a hankali tanajin kalaman sun zauna mata, kafin ta mike a hankali tana barin dakin. Lubna sufyan Hausabook.com 610 Haka kawai tun jiyan yanayin Daada yaki barinta, ta kuma rasa dalilinta nakin Salim tunda a iya hange da tunanin Madina bata ga wani abu da zaisa a guje mata aurenshi ba, idan za'ayi zancen gaskiya ma shi ya kamata a gujewa aurenta, bayyanar iyayenta yanzun, ko dama ace suna cikin rayuwarta tun daga farko, in ba kaddara ba Salim ba irin namijin da zai kalleta sau biyu bane dan hanya ta hadasu. Har yanzun data yarda zata aure shi tana jinjina abinda yagani a tare da ita yaji yana son aurenta. Duk da ta sha karanta yanda ake cewa so baisan kama ba, baya kuma bukatar dalili. Rabin abinci ta iyaci tana mikewa ta kai plate din kitchen, data fito ta bayan kujerun tabi ta wuce zuwa dakinta. Yanda duk Nawfal ya dinga kallon kofar dakin baisa ta sake fitowa ba har suka tafi. Haka kawai sanyinta sai yayi masa tsaye a rai. Sanyin da ba ita kadai tayi shi ba har Yelwa, dan bayan tayi sallar isha'i ta shiga dakin Daada ta sameta zaune tana jan carbinta. Yanda suka saba yi mata daga ita har Julde tayi wannan karin, tana daukar shekarunta ta ajiyesu a gefe, Lubna sufyan Hausabook.com 611 ta kwantar da kanta a kan cinyar Daada tana sauke numfashi "Daada bakice kin yafe mun ba" Kallonta Daada tayi "Na yafe miki tun kafin ki tambaya Yelwa, na yafe miki tun ranar da muka nemeki muka rasa, na yafe miki tun bansan inda kika shiga ba" Wani numfashin Yelwa taja tana fitarwa "Bansan me zan cewa Madina ba, har yanzun. Shima yace mun baisan me zaice mata ba...Daada me zance mata? Tayi hakuri banso barinta ba? Haukan da nayi

Chapter 23 of 27