bambaro
Talatu da take mata murmushi daga jikinshi da
wani irin karfi da bata san tana dashi ba, ta
wanke mata fuska da marin da ya gigitata.
Kiciniyar kwacewa takeyi amman rikon da Mero
tayi mata bana wasa bane ba, a girman jiki ta
fita, haka a shekaru, shisa wannan karfin nata
yake bata mamaki, sau nawa tana zaneta.
"Mijina? Duk abubuwan da kike so ki hada dani
tun tasowata bai isheki ba, saida kika biyoni
Lubna sufyan
Hausabook.com 367
kina son hada miji dani, ubanme na tsare miki?
Me nayi miki haka?"
Mero take fada cikin fitar hayyaci, ashe labarin
haukan kishin mata da takeji wasa ne, danyen
aikin da take tur dashi idan ance sun aikata
sanadin kishi, tsari ya kamata ta nema dashi
tunda gata yau idonta ya rufe, abinda zata illata
Talatu take nema, ta shaketa tana jijjigawa tana
kai mata duka duk inda zata samu a jikinta.
Dakyar Julde ya iya mikewa yana rike Mero ya
samu ya kwaci Talatu da ta fice daga dakin da
gudu, bakinta da hancinta duk sun tara jini, sai
dai dawa Allah ya hada Mero idan ba Julde ba.
"Me nayi maka? Ban so ka ba? Ban baka dukkan
zuciyata ba? Banyi hakuri da matan da kake bi a
waje ba? Sai ita? Kanwar mahaifyata?
Kanwarta? Wacce macece ba zaka bi ba Julde?
Ka fadamun idan akwai macen da ba zaka iya bi
ba idan kaganta!"
So yake ta nutsu, amman takiya, duka take kai
masa inda duk ta samu, ga wani irin kuka da
takeyi kamar zata shide, jikinshi babu inda baya
bari saboda bai taba ganin tashin hankali irin
Lubna sufyan
Hausabook.com 368
wanda yake gani ba yanzun, saiya daina kokarin
riketa da kare dukan da take masa, kamar
hakan take jira ta sake shi
"Ba zan iya ba, na hakura da kai, ko kai kadai ka
rage a duniya na hakura da kai Julde, ko sonka
zai kasheni na hakura da kai"
Tayi maganar tana juyawa ta nufi inda kayan shi
suke ta dauko wata jaka ta zazzageta, sai take
kara daukar kayan da ta zazzage tana mayarwa
cikin jakar, rabi sun shiga, rabi basu shiga ba ta
jata tana fitowa tsakar gidan da ita, Julde na
binta da kallo kamar wanda aka dasa a wajen,
ya kasa motsawa
"Ga mijinki nan Saratu, ba zan iya zama dashi
ba"
Take fadawa Saratu da ta shigo gidan, don ta
biyo, bata samu mai kitson ba, shisa ta yanke
shawarar dawowa gida, kallon Mero tayi, bata
taba ganinta a hargitse irin yau ba, duk kuwa da
kaya a jikinta harma da hijabi. Jakar da take
hannun Mero ta fara kallo, sai ta sake kallonta
"Kema da kin hada jakarki zaifi miki alkhairi..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 369
Cewar Mero, sai dai idanuwan Saratu yabar kan
Mero, ya koma kan babbar robar da Meron take
zuba ruwa a ciki, da abinda taga yana yawo akai,
kafin zuciyarta ta tsinko har tafukan
kafafuwanta da taji suna barazanar daukarta.
"Mero..."
Ta kira cikin wata irin murya, batasan ko dan
yau bane karo na farko da Saratu ta kira
sunanta ko kuma yanayin muryarta bane ba
yasa taji ta fisgota daga duniyar tashin hankalin
da Julde ya jefata, hankalinta ya dawo jikinta
lokaci daya
"Mero..."
Ta sake kira idanuwanta akan robar ruwan,
inda take kallo Mero ta juya ta kalla, zuciyarta ta
tsaya na wasu dakika, kafin ta cigaba da dokawa
da wani irin yanayi da bana lafiya bane ba, taku
biyu tayi, ta tsaya, ta sake takawa, ta tsaya, ba
zatace da rarrafe ko da kafafuwanta ta karasa
ba, ta ganta a tsugunne bakin robar ne, ta saka
hannuwanta cikin ruwan da sanyin shi ya
ratsata da wani irin yanayi, ta ciro Haidar, ba
don ta taba ganin gawa ba, ko ta riketa da
Lubna sufyan
Hausabook.com 370
hannunta, amman kallo daya tayiwa fuskar shi
tasan babu rai a jikin shi.
Da ta tako kafafuwanta a cikin gidan Julde a
matsayin mata, sai taji kamar an rusata ne an
sake ginata
Da suka raya darensu na farko tare da juna sai
taji rayuwar su ta hade waje daya
Da ta shafa cikinta bayan ta san akwai ajiyarshi
a ciki, sai zuciyarta ta sake hadewa da tashi
Da ta rike Haidar a ranar farko, sai taga yanda
jininta da nashi ya gauraya waje daya
Sai mafarkinta ya kara tsayi har tana hasaso har
abadan din da zata kasance a tsakanin su
Bata san ya ginata bane don ya kara rusata
A rana daya ta rasa shi
A rana daya ta rasa sauran abinda ya hada su
Sai ta kalle shi, ya fito daga dakin yana tsaye, ya
kasa karasawa inda take
"Yanda kayi mun rami a zuciya, in Allah ya
yarda duk lokacin da kake tunanin hankalin ka
Lubna sufyan
Hausabook.com 371
ya kwanta sai Allah ya aiko abinda zai birkita
maka komai Julde..."
Mikewa tayi da gawar Haidar a hannunta, tana
jin zuciyarta kamar ta daskare a kirjinta, ta
karasa har inda yake tsaye ta kamo hannuwan
shi ta saka masa shi a hannun shi, wasu hawaye
masu zafi na silalo mata
"Ka datsemun igiyar da take daure damu
Julde...idan na kara mintina a gidan nan mutuwa
zanyi"
Yanayin da yake gani a idanuwanta, kalamanta,
gawar dan da bai taba yiwa soyayyar da yayi
masa ba, duniyar duka da ta birkice mishi da
wani sauyi da bai hango ba, muryar shi a
nisance ta fito
"Na sakeki"
Numfashi taja, ta saki tana daga masa kai, komai
bai dirar masa ba sai da yaga ta nufi kofa, yaga
tana shirin ficewa daga gidan
"Mero"
Lubna sufyan
Hausabook.com 372
Ya kira, bata juyo ba, bata da alamar zata juyi
din don sauri ta kara, binta yayi da gawar
Haidar a hannun shi yana kiran sunanta har
waje. Ta tsaya tana juyowa tana kallon shi da
gawar da ya rike a kirjin shi
Babu wani abu da ya rage a tsakanin su
Ya rabata da kanshi
Ya ruguzata ta hanyar da batajin zata taba
komawa dai-dai
Ta rasa komai yau!
Tana can tana hauka akanshi har danta ya fita,
tasan Haidar, yana da kazarniya, tunda ya fara
rarrafe ko wanka takeyi masa saiya kama
bokitin ya mike, burin shi ya shiga ciki. Yana son
ruwa, doguwar maganar farko da Saratu tayi
mata randa ya fita daga daki tana sallah ne,
kuma shine karo na farko da Saratu ta taka har
kofar dakinta tana daga mata labule, ta ajiye
mata Haidar da yake a jike sharkaf da ruwa
"Idan sallah zakiyi ki goya shi, ki daina barin shi
ya illata kanshi babu kowa a tsakar gida"
Lubna sufyan
Hausabook.com 373
Ko godiyar da tayi nufin yi bata furta ba Saratu
ta juya tabarta a wajen, ashe ruwan da yake so,
ruwan da ko a kofi ya gani saiya dauka ya sheka
a jikinshi ne zai zamo ajalin shi.
"Don Allah ka kyaleni Julde, karka biyoni, karka
nemeni, Haidar din daya rage a tsakaninmu
gashi nan a hannunka"
Bai jita ba, binta yayi yana rikota, ta kuwa juyo
ta wanke shi da mari, bai damu ba
"Mero don Allah, ba zaki barni ba..."
Ya fadi yana dorawa da
"Kince mun ni da ke har karshe, shisa na saki
jikina Mero, kince halaye na ne karshen abin da
zaki duba, me yasa? Me yasa sai da na saki jiki
zaki bar ni da kai na?"
Hadi da sake rikota, ta shiga kokarin fisgewa
tana wani irin kuka da yake fitowa daga lungun
zuciyarta. Baya ganin komai sai ita, shisa baiga
mutanen da suke fara taruwa ba, baiga yanda
matan unguwar keta lekowa ba, ana kallon su.
Balle kuma hayaniyar da akeyi, bayaji baya gani,
hankalin shi kacokan yana kan Mero
Lubna sufyan
Hausabook.com 374
"Me kayi mata Julde?"
Muryar Datti ta dirar masa, kafin hannun shi
daya riko ma Julden kafada, juyowa yayi har
lokacin yana rike dam da hannun Mero
"Baba ka bata hakuri"
Kai take girgizawa, idan bai saketa ba, tabbas
numfashinta na gab da tsayawa, so take tabar
garin Marake a yau din nan, tayi nisa da Julde da
duk wani abu daya taba hadata dashi
"Ka sakeni... Baba kace ya sakarmun hannu don
Allah"
Mero ta karasa fadi tana samu dakyar ta fisge
hannunta, da hanzari tabar wajen, binta zaiyi
muryar Datti ta tsayar dashi
"Me kayi mata?"
Juyowa yayi yana kallon Dattin, zuciyarshi na
kara rarrabewa a cikin kirjin shi, komai na hade
masa waje daya
"Bansan kanwar mahaifiyarta bace Baba..
Bansan alakar su ba... Kaga Haidar, baiyi motsi
ba tun dazun..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 375
Yayi maganar da wani irin yanayi, kamar wanda
ya samu tabin hankali, kallon shi Datti yakeyi
"Yanda ka kunyata ni Julde... Allah ya kunyata
ka a idanuwan mutanen da suka fi komai
muhimmanci a wajenka... Nagode kaji"
Cewar Datti yana juyawa, kirjin shi kamar an
dora dutse yakeji, sai Julde ya bishi, yana ture
mutane batare daya damu mata bane ko maza,
har cikin gida inda ya samu Dije a tsaye
"Daada kinji me Baba yace? Haka yace Allah ya
kunyata ni a idanuwan mutanen da suka fi
komai muhimmanci a wajena... Ki bashi hakuri,
ba zan kara ba, kinga Haidar ma baya numfashi,
Mero ta tafi tabarni, ki basu hakuri Daada, na
daina, ki basu hakuri"
Karasowa tayi ta karbi Haidar din da yanayin
shi ya tabbatar mata da gawace, dankwalin
kanta ta kwance tana kwantar dashi ta dago,
wani irin numfashi Julde yake fitarwa kamar
mai shirin shidewa, saita kama shi ta zaunar
"Ba zan iya zama a garin nan ba Daada...tafiya
zanyi..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 376
Ya karasa yana kallonta, ba zai iya dora dan
yatsa akan abinda yake ji ba, wani irin hargitsi
ne da ba zai taba misaltuwa ba, kalaman Datti
da na Mero ne suka hade masa waje daya suna
shiga wasu wajaje a jikin shi da baisan dasu ba,
sosai Dije take kallon shi, sai taji wani fili a inda
yake a zuciyarta shima, kamar yanda Bukar da
Yelwa suka bari
Haihuwa jarabawa ce
Kamar yanda rashinta ma yake jarabawa
Sai dai bata hango yau ne mafarin sauran
hargitsin da itama zai rabata da tushenta ba...!
Gidan yayi mata fili, filin da ba'a iya waje take
jin shi ba harma da zuciyarta. Idan ta rufe
idanuwanta ta tuno lokuttan da take dariya
kamar a duniya bata da wata matsala, sai taga
kamar a wata rayuwar ce daban, wadda ta sha
bamban da wadda take ciki yanzun. Tazarar da
take tsakanin wancen lokacin da kuma yanzun
tayi nisan da take ganin kamar dorata akan
wasu yan shekaru yayi kadan. Saboda babu
Lubna sufyan
Hausabook.com 377
yanda za'ace farin ciki ya bace daga rayuwar
dan adam lokaci daya haka. A yanayin da
zuciyarta take ciki ko wani taji yayi dariya mai
sauti saita kalle shi, sai taji kamar ta girgiza shi
tace masa ya kara yin wata, yayi iya wadda zai
iya saboda lokaci na iya zuwa da sai dai ya
hasaso dariyar a tunanin shi.
Yara uku, uku kacal da suka zame mata
jarabawa, masu guda biyar fa? Takwas, goma,
maza masu ashirin harda doriya fa? Addu'ar da
take yiwa iyayenta da kasa ta rufe ma idanuwa
saita ninku, wanne fama sukayi da ita kafin su
aurar da ita, haka samun yara yake da wahala
daman? Lokacin da ta kafe kan auren Baabuga,
abubuwan da Baba ya dinga hango mata ashe
shi kadai yasan me yake ji a zuciyar shi. Kokarin
da iyaye sukeyi akan 'ya'yan su nagartattu da
wanda suka baude hanya duka ba zai taba
misaltuwa ba. Su kuma yaran ba zasu taba gane
girman wannan kokarin ba sai ranar da suka
haifi nasu, idan sun haifa din ma an jaraba su ta
hanyar wannan yaran.
Duka yaushe ne take rike da hannuwan Yelwa,
yaushe ne Yelwar bata iya aiwatar da komai
Lubna sufyan
Hausabook.com 378
batare da taimakonta ba, yaushe ne Yelwar ta
kalli cikin idanuwanta kamar ta dauki
zantukanta, sai ace ta nemeta ta rasa, ba kuma
ta da wata dabara ko abu da zata aiwatar akan
hakan. Ta yaya zuciyarta zata warke daga
wannan ciwon? Ta ina zata fara? Rabonta da
baccin kirki harta manta, cike suke da mafarkai
mabanbanta akan Yelwa da halin da take ciki.
Idan ta farka ma itace a ranta, tilon 'yarta da
batasan inda take ba.
Kamar bata da wannan ciwon a zuciyarta,
kamar Julde bai sani ba ya zabi ya kara mata
wani tunanin akan wanda yake cunkushe da
ruhinta.
"Tsakanin Kano da Marake wasu awanni ne da
ba zasu hanani zuwa ganinki ba Daada..."
Ya fadi yana rike da hannayenta
"Idan nace karka tafi zaka fasa? Kai kadai ka
ragemun da nake gani, kai kadai nake gani
Julde"
Lubna sufyan
Hausabook.com 379
Shine abinda taso tace masa, shine abinda ta
fada a cikin kanta, amman harshenta yayi mata
nauyi
"Inajin Marake ne mafarin komai, Daada inajin
idan har ina cikin kauyen nan zuciyata ba zata
samu sararin sauyin da nake bukata ba... Ina so
in shaki iska a wani waje da baya zagaye da
tunin akan abubuwan dana rasa... Bana so in
cigaba da kallon kofa ina jiran mutanen da
banda tabbaci akan dawowar su"
Ya zata hanashi tafiya bayan ya fadi haka? Bayan
har a cikin idanuwanshi da suke cike taf da
hawaye tana iya hango zuciyarshi da take a
karye, a karye da abubuwan da suka fi karfin
shekarun shi. Kwananshi uku a cikin dakinta,
alwala ma sai dai ta kawo masa ruwa da roba
yayi a cikinta, inda ya idar da sallah nan yake
komawa ya kwanta, banda ruwa, abinci sai tayi
da gaske zata samu ya tashi yaci cokali biyu ko
uku ya sake komawa ya kwanta. Idan ta leka
fuskar shi, idanuwan shi a rufe suke, badon
hawayen dake bin gefen fuskarshi ba, zata
dauka bacci yakeyi.
Lubna sufyan
Hausabook.com 380
"Nagaji, nagaji sosai Daada, kibarni in kwanta"
Bata hanashi ba, amman a cikin kwanaki ukun
nan ko wanka baiyi ba. Ranar na hudun ma
Saratu ce ta shigo, itama duk tayi zuru-zuru
kamar wadda taga wani abu daya firgitata.
Dakin Daada ta nuna mata, ita ta shiga, takai
awa biyu a ciki, sannan ta fito, kamar ta kara
ramewa fiye da lokacin da ta shiga dakin.
Abinda Daada bata sani ba shine da Saratu ta
shiga, ta dafa Julde da yake kwance yafi sau
goma yana ture hannunta
"Ka tashi, ba su kadai kake dasu ba Julde... Bashi
kadai bane yaronka, akwai Salim, akwai Fadila...
Ka tashi don Allah, basu kadai kake dasu ba,
basu kadai suke bukatarka ba..."
Ta karasa muryarta na karyewa, tana riko
hannun shi da yake son kwacewa, dakyar ta iya
kamo hannun shi, ta dora a cikinta da kamar
hakan yake jira abinda yake ciki ya motsa har
yaji motsin ta cikin tafin hannun shi
"Ya kake so muyi? Idan muka rasaka ya kake so
muyi?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 381
Mirginowa yayi ya juyo, saita dago shi, baiyi
kokarin kwacewa ba harta dora kanshi a
cinyarta
"Zuciyata na mun ciwo... Saratu zuciyata namun
ciwo"
Ya karasa dumin hawayen shi na gangarawa har
kan cinyarta
"Ina nan, kayi kuka idan zakaji sanyi, kayi duk
abinda zai kawo maka sauki, amman karka
barmu"
Kukan yayi, a jikinta. Kuka yayi kamar karamin
yaro, kuka yayi kamar ba namiji ba, namiji mai
mata da yara. Kuka yayi da tunda yake duniya
bai taba yin irin shi ba, har a kasusuwan jikinshi
kuma yake da yakinin daga ranar zai wahala ya
sake kuka mai yawan wannan. Har saida bacci
ya dauke shi sannan Saratu ta zame jikinta daga
nashi tana fitowa. Da Magriba shima sai gashi ya
fito, ya kalli Daada yana mata murmushi, kafin
ya fita daga gidan gabaki daya. A ranar ya fara
shirin barin Marake, ta dauka Datti zai hanashi,
sai dai harya zo ya tsugunna a gabanshi yayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 382
masa sallama bai daga ido ya kalle shi ba, baice
komai ba.
Kuma har yau da shekara uku kenan, ko Julde
yazo duk juma'a bayan mako biyu ko uku, daga
shi har abinda ya kawo Datti baya kallansu.
Balle kuma ya amsa gaisuwar da Julden zaiyi
masa, da Dije tayi masa magana cikin wata irin
gajiyawa yace
"Ban isa ba, akan Julde. Ya nuna mun hakan fiye
da sau daya. Alkawarine nayiwa kaina, bakina
ba zai kuma ba, in dai akan shine, yaje shi da
rayuwar daya zaba"
Ranar ne kuma ta juye masa abinda yake
cikinta, abinda ta dade tana rikewa
"Kaso mafi girma na abinda ya same su kaine,
zan dauki sauran daya rage saboda na zabi zuba
muku ido maimakon yin iya bakin kokarina
wajen nuna muku kuskuren da kukeyi. Ka so su,
nice shaida, sai dai soyayyarka ce ta fara ja
musu matsalar da suke ciki Datti, soyayyarka da
ta hana ka nuna musu wata rana zasu nemi
abinda zaka iya hana su, zaka nemi abinda zaka
Lubna sufyan
Hausabook.com 383
so suyi maka biyayya, duk basu son wannan
ba..."
Ta sa hannu ta share hawayen daya zubo mata
kafin ta cigaba
"Saika nuna musu indai kana raye babu wani
abu da zasu nema su kasa samu, sai kayi tunanin
tarbiyarsu a hannunka take, shi yasa ka ganin
aibun yaran mutane, saboda kaine, Datti, kafi
karfin abinda kake ganin yaran wasu nayi ya
sami naka. Ranar da suka fara nuna maka bakafi
karfin su ture maganarka ba, saika kara
kuskure akan wanda kayi, daka gwada lallashi,
ka gwada fada, saika ga lokaci ya kure maka,
sunyi bushewar da lankwasa su yake dai-dai da
karyewar su, saika daure su da bakinka, kayi
musu dauri na gaske da bakinka, su sukayi
motsin Datti, matsatsin daurin da kayi musu da
suka motsa sai suka karye da kansu... Gashi nan
mu duka muke tayasu jinyar"
Idanuwa Datti ya rufe, kalamanta na shigar shi,
yanajin kamar jininshi na kara gudu a cikin
jikinshi, kuskuren shi da yaketa dannewa ne
take fito masa dashi tana goga masa a ko ina na
Lubna sufyan
Hausabook.com 384
jikinshi, tana tursasa shi ya fuskanci abinda a
wannan bigiren bashida karfin fuskantar shi
"Kuskuren namu ne, kuskuren mune duka..."
Baice komai ba, harta shiga daki baice mata
komai ba, kuka tayi marar sauti a cikin daki, yai
nashi a tsakar gida. Kowa da kalar ciwon da
yake ji. Datti najin yanda kamar bai taba wata
rayuwa babu yaranshi a cikinta ba, yanajin
yanda sauran shekarun duka yayi sune cikin
zaman jiran ranar da zai zama uba, da tazo sai
yake jin yana da kudi, yana da asali, yana da duk
wani abu da zai isheshi ya karesu daga dukkan
abin ki, yana kuma da girman zuciyar daya
kaunace su da dukkaninta, yanzun da komai ya
hargitse masa sai yake kara jin yanda duk wani
numfashi da zai ja ya fitar kamar gayyata ce
yake yiwa ajalin shi.
Dije najin karshen duniyarta ne yazo. Sai Bukar
shima ya fado mata. Borno yace mata, ammam
Borno a ina? Gabas? Yamma? Kudu? Arewa? Ko
a tsakanin duka hudun? Shima idan neman shi
ta fita yi bata san ta inda zata fara ba, yana
lafiya? Me yasa ya dade fiye da kowanne lokaci?
Lubna sufyan
Hausabook.com 385
Yaushe zai dawo? Kullum tunaninta akan shi
baya wuce wannan zagayen, wanne hali yake
ciki, yaushe zata sake saka idanuwanta akan shi.
Sai taga kamar tunanin nata ne ya fisgo mata shi
ranar yammacin wata Alhamis da zata cigaba da
tunowa, saboda itace Alhamis ta karshe da ta
saka shi a idanuwanta.
Sai dai ba wannan Alhamis din bace kadai zata
kafa tarihi a rayuwar Dije
"Daada Am"
Ya kirata a maimakon sallama, cikin muryar nan
tashi mai sanyin gaske. Cikin wani yanayi daya
sata bude idanuwanta ta kuma dago daga
kishingidar da tayi a tsakar gidan tana kallon
shi, murmushi yayi mata. Murmushin shi da
yake cike da sanyin halin shi da kuma wani abu
da na shine kawai, na Bukar da bakowa Allah
yake halitta da shi ba.
"Daada..."
Ya sake kira, numfashi taja, ta fitar, ta sake ja
tana fitarwa
"Bukar"
Lubna sufyan
Hausabook.com 386
Ta amsa tana sake kallon fiye da fuskarshi
wannan karin, yadine a jikinshi kalar bula,
amman yayi wata irin dauda kamar wanda yayi
birgima a kasa, saita kalli kafafuwanshi,
takalmane yake sanye dasu yan soso, sababbi
kamar ranar ya fara takasu, amman kafarshi
kurace tamkar yayi kwanaki baiga ruwa ba,
bana wanka ba kawai harda na alwala. Tun da
take dashi, ko a lokacin yarinta bai taba dauda
irin wannan ba. Bata taba ganin shi haka ba,
jakace a hannun shi daya, saiya sata duban
dayan hannun nashi, zuciyarta nayo tsalle ta
daki allon kirjinta tana komawa mazauninta da
wani irin yanayi.
Yarone, hannuwan shi duka biyun rike dana
Bukar, sai dai ya labe a bayan kafafuwan shi, sai
daya jawo shine ya fito fili, amman akwai tsoro a
cikin idanuwanshi, sai taga kamar Bukar, saiya
tuna mata lokacin da Bukar yake da shekarun
shi, zuciyarta na wata irin cika, taji hawaye
masu zafi na tarar mata a idanuwa, jan hannun
yaron Bukar yayi har suka karasa inda Daada
take zaune, jakar ya ajiye a gefe, yana zama akan
tabarmarta ya kama yaron ya zaunar a
Lubna sufyan
Hausabook.com 387
tsakaninsu. Sai yanzun da suka zo dab da ita ta
kula bashi kadai yayi daudar ba harda yaron,
kayane na yan binni a jikinshi, da alama zasuyi
tsada ko ba'a fada mata ba, don tana ganin irin
kayan a jikin su Salim idan Julde ya bayar an
siyo musu daga binni.
"Aure nayi Daada... Ga Nawfal"
Ya fadi yana mika mata hannun yaron da ta rike,
hawayenta na zubowa. Tanajin shekarun da ta
rasa na rayuwar Bukar suna ninka mata, yayi
aure, bata sani ba, yana da mata, ko sunanta
bata sani ba, ga Nawfal, da ko baikai shekaru
uku ba ya kusa. Bukar ta kalla, haka tata
jarabawar tazo, rasa abubuwa a tare da yaran
da suka fito daga jikinta
"Abubuwa da yawa sun faru Daada, abubuwan
da zanso ace ina da cikakken lokacin da zan
miki bayani yanzun, amman babu, sai dai idan
na dawo..."
Bata san me yasa a duk abinda ya fada ta zabi
tambayar shi
"Ina zaka tafi?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 388
A maimakon tarin tambayoyin da suketa
kaikawo a cikin kanta ba, amman ita tafi sauran.
Yanzun yazo, yanzun taganshi bayan wasu
shekaru, me yasa yake mata maganar sake
tafiya ko numfasawa baiyi ba balle ya huta.
"Na barta, zan koma mu taho tare ne...banda
lokacin da zan kara batawa Daada, rayuwarta na
cikin hatsari"
Cike da rudani da rashin gane inda zantukanshi
suka dosa take kallon shi, sai dai kalaman shi na
gaba ma rudata suka sakeyi suna jefa wani
firgici a zuciyarta
"Wani abu a zuciyata yana fada mun shi kadai ne
kwan da nake da rabo a duniya Daada, ga
amanar dana, gatan da na hasaso ma rayuwar
shi mai yawa ne, ga amanar shi nan kafin in
samu dawowa, dalilin da zaisa ni barin shi mai
karfine..."
Kafin kuma tace wani abu ya janyo jakar dake
gefen shi ya mika mata
"Ga wannan Daada, duka abinda yake ciki
mallakin shine, amanar ba taki bace wannan, ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 389
Hamma ce, zai damkata a hannun shi a lokacin
daya dace... Banda lokaci... Banda lokaci da zan
tsaya in bashi da kaina"
Sai fadi yake bashida lokaci kamar yana ganin
agogon da yake dauke da kwanakin rayuwar shi.
"Bukar kayi mun magana yanda zan fahimta...
Babu wani abu da nagane a cikin zantukan
ka...rayuwar wacece a hatsari? Meye a jakar
nan? Me kake nufi da ga amanar danka nan? Kai
kuma fa? Ina zaka je?"
Tambayoyine masu yawan gaske da suke
turereniya da junansu wajen fito mata, sai dai
mikewar da Bukar yayi ta katse mata su
"Bani da lokaci Daada... Idan na dawo zan fada
miki"
Ya amsa yana mikewa
"Ka zauna a wajen Daada in dawo Nawfal"
Hannun shi daya Nawfal ya mika, Bukar din ya
sumbaci nashi hannun kafin ya dora akan na
Nawfal yana kuma janyewa. Hannun Nawfal ya
daga ya manna a kuncin shi na dama, na haggu,
Lubna sufyan
Hausabook.com 390
da kuma kan goshin shi. Kamar wani abune da
suka sabayi, kallon su Dije takeyi, ta kasa ko da
kwakkwaran motsi, komai yayi mata tsaye,
musamman da Bukar ya juya, harshenta ya nade
a bakinta, ta kasa ko da kiranshi balle kuma tayi
yunkurin hanashi tafiya, ya juyo ya kalleta,
kamar shine kallon karshe, ya kalleta da fatan
rayuwa ta sake ara musu lokacin makamancin
yau din, kafin ya fice daga gidan, ya bace ma
ganinta.
"Kamar Bukar nagani ya fita"
Datti daya shigo ya fadi yana dawo da ita cikin
hayyacinta
"Ya sake tafiya... Bukar ya sake tafiya"
Sosai Datti ya sake shiga cikin gidan yana kallon
su, ita da Nawfal. Badon Nawfal din da kuma
jakar da take gani ba, da zuwan Bukar zai mata
kamar mafarki, kamar daya daga cikin
mafarkan da ta saba nashi. Amman ga shaida
nan, yazo, ya sake tafiya tana kallon shi bata
tsayar dashi ba. Hannun shi Nawfal ya mikawa
Datti, ya kalli hannun, ya kalli fuskar Nawfal da
ko ba'a fada ba yasan jinin Bukar ne, ga
Lubna sufyan
Hausabook.com 391
mamakin shi saiya kama hannun yana mikar
dashi, saiya daga shi ya rike shi a jikinshi
"Ya sunan ka?"
Ya tambaya da fulatanci
"Nawfal... Kai ya sunanka?"
Ya amsa, murmushi Datti yayi, murmushin da
Dije ta dade bata gani ba a fuskar shi, ya sake
gyarama Nawfal zama a jikin shi suna magana
cikin yaren da yafi komai soyuwa a wajen Datti
Kamar Bukar bai zo ya sake tafiya kamar
walkiya ba
Kamar duniyar bata sake birkice mata ba
Sai ta kalli Nawfal da yayi dariya, yanayin fuskar
shi da sautin dariyar na mata iri daya data
Bukar
Datti take kallo da yake kwance, motsin kirki
ma baya son yi, yanzun saiya wuni cikin gida baj
fita ba. Kamar babu wani abu daya rage masa a
waje, duka duniyar shi na cikin gidan, na tare da
Lubna sufyan
Hausabook.com 392
ita yanzun da babu yaransu. Sauran gonakin su
na cikin Marake akwai masu kula dasu da suke
karkashin Julde, kome suke da bukata yana
kawo musu. Datti ma bai nuna hakan na damun
shi ba, tunda ya daina fita in ba da wani dalili
mai karfi ba. Akwai hasken fitilar da suka
kunna,amman tunda Julde ya dauke Nawfal
kamar duk wani haske da zata kunna iya
idanuwan Datti suke tsayawa. Kamar Nawfal din
wani haskene da suka kwana biyu basu gani ba.
Kuma Nawfal din wata alama ce da ta tabbatar
mata da kadaicin da Datti yake ciki, idan har zai
ture tsanar da yake yiwa Bukar ya rungumi
Datti haka, tabbas kewar ganin yaran shi a
gabanshi da yake ta wuce yanda zata iya
hasashe. A karo na farko yanayin shi na sakata
tunanin duk yaran da suka binne, da sun rayu
watakila da basuyi kadaici haka ba. Da ba zasu
rasa a cikinsu ko da kwara dayane da zai zauna
tare dasu ba, da basu ji kamar a filin duniya
basu da kowa sai junansu ba.
Akwai wani mataki na shekaru ko rayuwa da
yara suke kaiwa sai su dinga dauka babu wani
abu da iyayensu suka fi bukata sama da
Lubna sufyan
Hausabook.com 393
kyautatawa, rage musu ko ma dauke musu duk
wani nauyi da yake kawunansu, ci, suttura da
ma duk wani abu na jin dadin rayuwa. Albarkar
nan da ita sukan bi hadi da addu'o'i da suke
nuna jin dadin su na wannan kyautatawar.
Amman yawanci a kasan zukatansu akwai
muradi na daban, akwai kewar da gudun yanda
yaran nasu zasu dauki maganar in sun fito da ita
yasa suke kara danneta. A karo babu adadi, zasu
dauki kasancewa da yaransu na wuni daya akan
wannan tarin sutturar da suka kawo suka juya a
cikin wasu yan mintina, ko suka aiko da ita.
Amman yara sun kasa fahimtar wannan, rana
daya bayan makwanni biyu, uku, harma hudu
yayi mata
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 27