yanayi, har yanajin kamar
idanuwan shi na neman tara hawaye, doyace da
kwai. Sai ruwan zafi, karba yayi ya tafi, har
ranshi baiyi niyyar cin komai ba, ko yunwa ma
bayaji, amman da ya kai musu saiya tsinci
kanshi da zuba shayin ya saka sugar, suna da
kayan tea dinsu. Ganin ya kurba ya ajiye da
sauri yasa Khalid dagowa sosai yana kallon shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 504
"Ruwan zafi ne Bajjo"
Ya fadi kamar yana son tunawa Nawfal din
"Nanna ce ta bamu"
Cewar Nawfal yana dago kofin hadi da hura iska
a ciki, kallon shi Khalid yakeyi, ya sha ya kai
rabin kofi kafin ya ajiye ya bude kular yaci doya
yanka hudu, ya karasa shanye ruwan shayin ya
mike saboda kiran daya shigo wayarshi, a bakin
kofa ya daga da fadin
"Jaan yanzun zan fito daga gida, na tsayawa
karyawa ne, Nanna ce ta bamu doya da shayi"
Yanda ya karasa maganar zaka rantse babu
wanda ya taba bashi doya da kwai da shayi a
rayuwar shi. Ya samu cunkoson abun hawa
sosai a hanya kafin ya karasa filin jirgin, shisa
tana ganin shi ta shagwabe fuska, ya mika mata
hannun shi da ta kama cikin nata, ya dan
dumtsa cikin ban hakuri, mutanen da suke
wajen na hanashi hade jikinshi da nata,
karasawa yayi yana karbar dan akwatin da take
rike dashi a dayan hannunta ya jata dan su
Lubna sufyan
Hausabook.com 505
karasa inda ya ajiye motar Khalid din daya fito
da ita
"Cunkoso yayi yawa a hanya shisa..."
Dan tana daya daga cikin mutanen daya sani da
basa son jira, ko kadan batason jira, da bashi
bane da yasha mitarta da bata karewa, batace
masa komai ba, shiya bude mata mota ta shiga,
ya saka akwatinta sannan ya zagaya ya shiga
shima
"Me yake damunka?"
Ta tambaye shi a sanyaye, numfashi yaja yana
tayar da motar, ya manta yanda take iya
karantarshi kamar littafi
"I can't talk about it"
Ya fadi da dukkan gaskiyar shi, kai ta jinjina
tana mika hannu ta shafi fuskar shi, lokutta irin
haka yana godewa Allah da girman da tayi a
cikin turawa, da kuma dabi'unsu irin wannan
data dauka, in dai gaskiyar shi zai fada mata ta
wadace ta, yanzun zata tabbatar da ta nuna
masa in har yana son maganar ta hadasu to a
shirye take da ta saurara, amman ba zata sake
Lubna sufyan
Hausabook.com 506
tambayar shi ba. Juya motar yayi yana nufar
gidan Daada kai tsaye, suna shiga da sallama
Murjanatu ta karasa tana rungume Daada da
take zaune
"Nayi kewarki"
Ta fadi da fulatanci, dariya Daada tayi, babu
yanda za'ayi ba zakaso Murjanatu ba
"Ina Madina?"
Ta tambaya saboda ita kawai take son gani, ko
hotonta bata dashi, data tambayi Nawfal shima
da mamaki a fuskarshi yace
"Kinsan sai yanzun nake tunanin anya na taba
ganin hoton Madina kuwa?"
Dariya sukayi sosai, yanda take jin Madinar,
yanda komai nata yasha bamban dana sauran
mutane yasa take son ganinta fiye da kowa a
danginshi, daga ita sai kuma Salim, Khalid
abinda ya rage kadan ne, tunda suna video call
sosai da Nawfal din, kuma zasi gaisa, har ayi
hirar da ita wasu ranakun. Amman Madina dan
video call din da zasuyi da Nawfal lokacin da
suke india duk ta fita, sai ta dawo ya gaya mata
Lubna sufyan
Hausabook.com 507
"Kaman Madina bataso in ganta"
Ta fadi rannan tana saka shi dariya
"Madina!"
Nawfal ya kira yana samun waje ya zauna
"Daada ina kwana... Ya jikinki?"
Murmushi tayi masa
"Jikina ai yayi sauki sai abinda ba'a rasa ba"
Kai ya jinjina yana shirin sake kwalawa Madina
kira ta fito daga dakinta, bata ga Murjanatu ba
sai da ta zagayo, ta kuwa bude baki cike da
mamaki kafin tayi dariya
"Jaan, ga Madina, Madina ga Murjanatu"
Nawfal ya fadi, karasawa Madina tayi ta zauna a
kusa da ita tana rasa asalin abinda take ji, sai
dai kallonta Murjanatu takeyi, har suka gaisa, ta
tashi tana nufar kitchen tare da tsegumin
Nawfal bai fada mata zata zo yau ba, yau ta fara
ganin Madina, amman tasanta, koma a ina ne ta
santa, sai da tayi dariya take ganin tabbas akwai
inda ta santa. Duk hirar da suke wannan
Lubna sufyan
Hausabook.com 508
sanayyar take nema a zuciyarta, har suka karya
da dankali da kwan da tayi musu da shayi, ta
shiga ta kara gyara dayan dakin da Nawfal kan
kwana idan yazo gidan Daadar, ta dauki akwatin
Murjanatun ta kai mata can, ta mike da fadin
zata dan watsa ruwa ta kwanta dan ji takeyi sam
bata huta ba tunda suka baro India.
Nawfal ya bi bayanta, a tsakiyar dakin ya
kamata yana juyo da ita ta fuskance shi,
hannuwanshi ya dora kan kafadunta yana
kallon fuskarta
"Gidado ji nakeyi kamar nasan Madina, da tayi
dariya sai inga akwai inda nasan yanayin da
yake kan fuskarta da idanuwanta, inata tunani
na rasa..."
Murmushi yayi yana sumbatar goshinta
"Madina irinta ita kadaice, sai dai ko in a film
kika ga mai kama da ita"
Dakuna fuska tayi tana zame jikinta daga nashi,
don da gaske wanka take so tayi, idan ta biye
masa zancen ne zai sauya. Akwatinta ta bude ta
dauki kayan wankanta ta shiga bandaki, saida ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 509
murje jikinta da sabulu sannan kamar an kwada
mata guduma akai ta tuna ina taga mai kama da
Madina, a gidan kawunta ne, ba mace bace ba
namiji ne, ko gashin da yake fuskarshi bai hana
kamannin shi fitowa da Madina ba, da sauri ta
zubama jikinta ruwa ta dauro tawul ta fito
"Gidado a Abuja naga me kama da
Madina...wallahi kamarsu daya, da tayi dariya
irin fuskarshi nake gani"
Wani abu Nawfal yaji ya doka a zuciyar shi
"Namiji? Ba mace ba?"
Ya tambaya yana son tabbatarwa, kai ta daga
masa tana dorawa da
"Kuna da 'yan uwa a Abuja?"
Da kai zai girgiza mata, saiya fasa, saboda ba
zaice ga inda suke da 'yan uwa ko inda basu da
yan uwa ba, daga Daada sai Julde ya sani, ba
kuma zai yiwu ace basu da wasu dangin ba.
"Wallahi ban taba ganin kamanni irin haka ba
tunda nake, ana cewa ina kama da Umma,
Lubna sufyan
Hausabook.com 510
amman ba irin na Madina da mutumin nan ba,
kamar babanta"
Haka kawai Nawfal yake jin zuciyar shi na
dokawa, ana kamanni a duniya, ya sani, ga Salim
nan da Julde, daya gifta ko ba'a fada maka ba
kasan ya hada jini da Julde.
"Ina zuwa"
Yace yana ficewa daga dakin, baiga kowa a falon
ba saiya nufi dakin Daada, ya kuwa sameta a
zaune
"Daada..."
Ya kira, ta dago ta kalle shi amman ya rasa ta
inda zai fara tambayarta
"Kar wani abu ya rikeka Bajjo, lokaci yayi da
dole zan amsa duk tambayoyin da nake ganin a
idanuwan ku kaida Madina, amman kuna kasa
tambayata, menene?"
Wani abu Nawfal ya hadiye kafin ya iya cewa
"Murjanatu tace mun tasan Madina, ko a ina ne
ta santa, tun dazun take tunani, shine tace mai
kama da itane ta gani, a Abuja...tace idan tayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 511
dariya kamar fuskar mutumin, in wani zai gani
zai iya cewa Babanta ne, zuciyata na dokawa
Daada, jikina yana mun wani iri, bansan me
nazo in tambayeki ba, mutum nawa ne suke
kama da juna a duniya..."
Kallon da Daada tayi masa nasa sauran
maganganun makale mishi
"Ya sunan shi?"
Ta tambaya da wani yanayi a muryarta, juyawa
yayi yana komawa ya samu Murjanatu da take
shafa mai
"Ya sunan shi? Mutumin?"
Kallon Nawfal tayi tana tunani, sau biyu yazo
gidan tana nan, bata cika mantuwa ba, tana fada
masa kamar karamin yaro ya fita da sauri yana
shiga dakin Daada
"Kabiru tace sunan shi Kabiru..."
Kamar an saki kofin gilashi a kasa haka Daada
taji wani abu ya fashe a cikin kirjinta, kafin
burinta ya hau benen da take fatan karya ruso
dasu gabaki daya.
Lubna sufyan
Hausabook.com 512
"Hamma zan kirga daya zuwa goma, idan baka
bude kofar nan ba zan karya in shigo"
Yana jinshi, tunda ya karaso kofar dakin yaji
takun tafiyar shi, saboda Khalid baya iya tafiya
da takalmi baija kafa ba, har mamakin shi
yakeyi, bashida wani nauyi balle yace jikinshi na
yiwa kafafuwanshi nauyin da ba zai iya daga su
yanda ya kamata ba. Daya kwankwasa daga
farko ji yayi kanshi da yake ciwo yana neman
rabewa biyu, tun jiya yake damunshi da kira a
waya sai da ya kashe wayar gabaki daya. Yazo ya
kwankwasa ya gaji ya tafi, shine yau ya sake
dawowa. Baya son ganin kowa.
"Da gaske zan karya kofar"
Karamin tsaki Salim yaja cikin zuciyarshi, ko
tunani Khalid yakeyi ya mutu a cikin dakin
bashida karfin da zai karya kofar batare da
taimakon wani ba
"Dan Allah ka bude, ba sai kayi magana dani ba,
ka bude ko abinci in miko maka saika sake
kullewa..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 513
Murmushi ne yaso ya kwace masa amman ciwon
da yake tsakanin hakarkarin shi ya rike duk
wata walwalar shi
"Hamma! Dan Allah ka bude, ko ka kunna
wayarka kace mun kana lafiya, kuma kana
bukatar kaci wani abu"
Sake juya kwanciya Salim yayi, a kwanaki uku,
biscuit ne yake ci, shima dan yasan jikinshi na
bukatar abinci, yau da safe yana gama ci har
ruwan da yasha sai da yayi amansu, dakyar ya
watsa ruwa ya dawo ya kwanta. Zuciyar shi da
duk wani abu da take da iko dashi a jikinshi
ciwo yakeyi
"Kuka ma sauki ne"
Yaji mutane na cewa, sai dai bai taba sanin yana
da wahala haka ba, ba wai don yana aiki a asibiti
ba, yana zagaye da mutanen da suke da dalilin
yin kuka kusan ko yaushe, amman ya zauna da
Adee, film ma kuka yake sakata, meye ma baya
saka Adee kuka? Ita ta saka shi jin kamar kowa
na da iko da hawayen shi, sanda kake so su zubo
zasu zubo, sai a kwanakin nan daya tsugunna, ya
zauna, ya kwanta, ya tashi tsaye, amman
Lubna sufyan
Hausabook.com 514
hawayen shi suka nuna masa iyakar shi ta
hanyar kin zubowa balle ya samun saukin da
yake nema. Bacci ma yayi masa tawaye kamar
sauran abubuwa, saboda daya rufe idanuwan
shi abinda bayaso ne yake gani, idan bacci ya
fisge shi mafarkin ne zai tashe shi.
Ciwon kanshi yafi alaka da rashin bacci fiye da
abinda yake zuciyar shi, ya rasa inda zai tsoma
kanshi yaji sanyi, ko wanka yayi bayajin dadi,
sai dai tun ranar yasan wani abu ya canza a tare
dashi, abu fiye da daya, wani daga cikin
abubuwan yayi canjin da har abada ba zai taba
komawa dai-dai ba, amman a cikin canjin nan
harda sallar da cikin kwanakin nan duk da bai
fita masallaci ba yayi kowacce akan lokaci,
harma ya daga hannuwan shi da nufin yin
addu'a, sai ya rasa abinda zai roka, sai wani irin
nauyin na zunuban da yanzun yake jinsu suka
danne shi, kunya ta kamashi, a gefe daya kuma
wani irin tsoro, tsoro da bai taba sanin akwai
irin shi a duniya ba.
Ko wannan ne maikon zinar da Khalid yake
gudar masa? Karshenta kenan? Jin kunya? Idan
har kunyar duniya ce wannan, dacin zunubin da
Lubna sufyan
Hausabook.com 515
yake tare da zina ne yake ciki yanzun, da wanne
ido zai amsa laifukan shi a lahira? A gaban
bainar jama'a? Faduwa Julde yayi, akan idon shi
ya fadi, kuma yasan ba abinda ya danne shi yayi
masa nauyin dauka sai tozartar da yayi a gaban
idanuwan su. Yasan akwai abinda ya kamata
yayi don neman samun sauki, amman kamar an
shafe wasu sashi na kwakwalwar shi haka yake
ji, sam ya kasa tuna komai.
"Hamma dan Allah..."
Muryar Khalid ta kutsa cikin tunanin da yakeyi,
sai dai bayason ko motsa yatsan shi balle ya
raba jikinshi da gadon, a kasan duk wannan
kuma bayason ganin kowa, bayason magana da
kowa, so yake ya zauna shi kadai, yayi jinyar
abinda baima san girman illar da yayi masa ba
har yanzun. Wajen aiki sako ya tura cewar bashi
da lafiya
"Har yanzun bai fito ba?"
Yaji muryar Nawfal, ya runtsa idanuwan shi ya
bude, kiranshi Khalid yayi, Nawfal ya kira, kuma
yasan yafi Khalid din naci. Nawfal zai iya wuni a
wajen idan har bai bude kofar ba, kuma ba zai
Lubna sufyan
Hausabook.com 516
daina kwankwasawa ba tunda yasan bayason
irin wannan hayaniyar, yanzun ma daga zuwan
shi harya fara jibgar kofar
"Hamma..."
Kunnen shi ya juyo masa muryata ta tsakanin
bugun kofar da Nawfal yakeyi, zuciyarshi da tayi
luf a kirjinshi kamar ta soma gajiya da dokawa
saboda jinyar da suke fama da ita tayo wani
tsalle kamar zata fito waje, kafin ta koma
mazauninta tana cigaba da wani irin dokawa sai
kace a lokacin ta fara aiki
"Hamma..."
Ta sake kira tana sakashi sauke ajiyar zuciya
mai nauyin gaske
"Hamma dan Allah ka bude"
Ta fadi cikin wata irin murya da tasa tsikar
jikinshi mikewa, sai yaji kamar ta fama masa
ciwukan da yakeji, a lokaci daya kuma ta fifita
masa su, baisan ya akayi ba, kafafuwan shi suka
fara saukowa daga gadon, saiya tsinci kanshi da
takawa har wajen kofar yana murza mukullin ya
bude kofar, ya kuma yi dai-dai da lokacin da
Lubna sufyan
Hausabook.com 517
Khalid yayi baya yana kawo duka karfinshi da
nufin karya kofar, kaucewa Salim yayi sai ga
Khalid din ya fada cikin dakin ya kuma yi
wanwar a kasa
"Hamma..."
Ya fadi saboda ya bugu sosai, yaji wani abu yayi
kara, bai dai tantance kashin kugunshi bane
kona hannun daya fadi a kai, koma daya daga
cikin hakarkarin shi
"Kasan ba zan tareka ka sokeni da kashi ba ko?"
Salim ya fadi yana kallon Khalid da yake mayar
da numfashi
"Ina jin na karya hakarkari"
Cewar Khalid yana kokarin mikewa hadi da
yatsina fuska
"Koya karye ai ba wata matsala fa Hamma, an
rigada an zari na matarka"
Hararar Nawfal Khalid yayi
"Dan an zari na matata sai akace bakomai dan
sauran sun karye?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 518
Numfashi Salim ya fitar yana dafe kanshi da
yake sarawa, hannu ya mika ya kamo na Khalid
yana mikar dashi
"Ja numfashi"
Kallon rashin fahimta Khalid yake masa
"Bana son maimaita magana Khalid kasani, kaja
numfashi"
Numfashin yaja
"Fitar..."
Yanda Salim din ke nazarin shi na saka shi yin
duk abinda yace, kafin ya kai hannu yana danna
kowanne cikin kasusuwan hakarkarin Khalid
din yana kuma saka shi yaja numfashi ya fitar
"Fitar mun daga daki"
Wannan karin Khalid din Nawfal ya kalla, kafin
ya kalli Salim
"Daga fitar da iska sai kuma fita daga daki
Hamma"
Lubna sufyan
Hausabook.com 519
Yanda Salim ya daga ido ya kalle shi yasa shi
rabawa ya fita daga dakin, Nawfal ya kalla, saiya
kafe shi da ido
"Ba zan tambayeka ko kana lafiya ba Hamma,
amman karka sake boye mana haka, Hamma
Khalid yayi kokarin karya kofa ne kawai,
kasanni, idan ya kama a sauke bangon nan
zanyi"
Numfashi Salim ya sake fitarwa
"Baka da hankali"
Kai Nawfal ya jinjina
"Nasani, shisa nake rokonka karka sake"
Ganin yayi shiru yasa Nawfal cewa
"Hamma"
Kai Salim ya jinjina masa yana dorawa da
"Naji Bajjo... Na jika"
Saboda Nawfal din ya tsare shi da idanuwa,
Khalid ya kalla yana masa alama da su bar
wajen, saboda Madina tana tsaye a gefe tana
kallon su kawai. Tun da Murjanatu tazo bai
Lubna sufyan
Hausabook.com 520
kwana a gidan ba, duk da yazo jiya, yaune baiyi
niyyar zuwa ba, abinda zaiyi da yawa, haka
nauyin da yake ji a kirjin shi
"Zai iya yiwuwa, Bajjo zai iya yiwuwa Babanta
ne"
Kwanaki biyu kenan da Daada ta fada masa
maganar da yaji kamar ta kwada masa guduma
a kai, yanda ta kalle shi yasa shi sanin duk wani
abu da zata sake fadi yana da karfin da zai iya
girgiza shi, kafafuwan shi zasu iya yi masa
barazana, shisa ya samu waje ya zauna a gefen
gadonta. Hasashen shi ya zama gaskiya
"Lokaci yayi, da ya kamata ku san komai, ba kai
da Madina kawai ba, har su Khalid, nasan ko
kafin kuyi hankali, fita da kukeyi cikin sauran
mutane kun fahimci kowanne mutum yana da
ahali, ko da a gidan marayu ya taso kuwa, akwai
dangin da bai sani ba a wani wajen suna rayuwa,
kamar yanda nasan tunda kuka fara hankali
kuka san dole kuna da wasu yan uwan, dole
muna da tushen da ba'a garin Kano ya fara
ba...Bajjo Kano maboya ta zamar mana, Marake
ne asalin mu, Marake ne tushen mu..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 521
Sanda ya bar dakinta kamar an watsa masa
ruwan kankara yake ji, yasan akwai sirrikan da
suke binne a zuciyarta, akwai kuma ciwon da
take tare dashi da yafi karfin binciken likita,
amman bai hango kaddararta na da girma haka
ba, baima dauka mutum daya zai iya daukar
abubuwan da suke kan Daada ba, daban yake
kallonta yanzun. Ko magana takeyi, ko
murmushi tayi saiya dinga kallonta, saiya dinga
neman hawayen daya kamata ace tana zubarwa
ya rasa. Sai yaji yana so ya riketa a jikin shi,
yana so yayi mata rumfa, rumfar da zata zame
mata kariya yanda wani abu ba zai sake tabata
ba. Yana so kuma ya maye mata gurbin duk wani
data rasa take kewa, shima saiya tsallake yayi
mata nisa.
Yau akwai yanda ya tsara zata kasance masa, a
ciki banda zuwa nan, Khalid yayi masa text
cewar har yau Salim yaki bude kofar, wayarshi a
kashe, saiya kira Khalid din, wayarsu Madina
taji tace saita biyo shi, yaso yace mata ta zauna,
saboda babu komai a zuciyarshi sai son ya
nisantata da inda Julde yake, amman yanda ta
tsaya tana kallon shi idan yace ta zauna zata
Lubna sufyan
Hausabook.com 522
nemi sanin dalilin da zaice mata ta zauna, Daada
tace bata tambayi ya akayi ta dawo gida ba har
yanzun, bata san meya faru ba, gara mutuwa ta
dauke shi kafin ya fada mata dalili
"Muje"
Kawai ya iya ce mata, ta ruga daki ta sakko
karamin hijab ta dora saman riga da wandon da
yake jikinta, ko Nawfal yace kayan sanyi.
Murjanatu sun fita ita da Adee, yanajin suna
fama da Madina tace zatayi wa wasu kunshi,
yasan halinta, in da gaske kunshin zatayi ba
zatace zata bishi ba, kawai bata son fitar ne. Yaji
dadin zuwan nashi saboda zasuyi magana da
Khalid, ya bashi labarin nan ko zai rage nauyin
da yake ji, ya kuma fada masa abinda yake
tunanin aiwatarwa. Tare da Khalid sukayi dakin
shi, suna barin Salim da Madina, sai lokacin ya
daga ido ya kalleta, wandon jeans ne a jikinta,
rigarta ta kusan zuwa gwiwa, sai karamar hijab
blue, ya tabbatar ba wannan rigar kadai bace a
jikinta
"Mug"
Lubna sufyan
Hausabook.com 523
Ya kira, da duka hankalinta baya kanta ba zataji
shi ba, dagowa tayi, ta kalle shi, fuskarshi duk
tayi gashi a wajajen da bata taba gani ba, yayi
zuru-zuru, idanuwan shi sun sauya launi. Tun
data tashi ta ga Daada a kusa da ita take son
tambayarta yanda akayi tazo, kallon da Daada
takeyi mata kamar tana rokonta karta
tambayeta komai, zuciyarta rawa take yi mata
tun ranar har zuwa yanzun, ko meye ya faru
tasan mai girma ne, saiga Nawfal shima, yana
kallonta kamar yayi mata laifi, yana kallonta
kamar yana yi mata alkawarin ba zai sake bari
wani abu ya sameta ba, duka yanayinsu saiya
kara tsoratata. Ta kira Salim, ta kira shi harta
bace lissafin ko sau nawa, amman wayar shi a
kashe, ba don ta tambaye shi abinda ya faru ba,
sai don taji muryar shi, saboda a yar karamar
duniyarta, Salim ya zame mata wani waje da
zata raba taji sanyi duk idan tana cikin halin
kunci.
Yau tunda tayi sallar asuba wata irin kewarshi
take danneta, so takeyi ta ganshi, taji muryar
shi, ta fito ta dauki ruwa ta ga Murjanatu da
Nawfal a kitchen din, daga inda take tsaye ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 524
zatace ga abinda suke fada ba, amman yana
bayanta, ya rike hannunta da take rike da robar
ruwa ya fadi wani abu dayasa ta daga kai ta
kalle shi tana dariya, komawa tayi, har zuwa
yanzun ba zatace ga dalilin da yasa ta koma ba,
ta duba zuciyarta ta rasa me taji, koma menene
kewar Salim saita danneta, komawa tayi ta
kwanta tana daukar wayarta ta kirashi, a kashe
har lokacin. Ta sauke wayar, hawayen da ya cika
mata idanuwa na shirin zubowa, sallamar da
Daada tayi mata na mayar da hawayen.
Sai dai na wucin gadi ne, komawa sukayi don su
tattaro yan uwansu suyo rubdugu wajen fitowa
tare da kalaman bakin Daada, da labarin da yayi
mata tsaye, labarin kuma daya hade mata
tambayoyin da take dasu tun sanda taci karo da
wasikar Yelwa. Tayi kuka, Daada ta riketa a
jikinta ne batare da tayi yunkurin hanata kukan
ba, batasan bacci ya dauketa ba saida ta farka,
Daada bata dakin, tayi wanka ta fito ne taga
Nawfal, suka taho. Ta dauka hawayenta na yau
dai sun gama karewa, sai yanzun da taji sun cika
mata idanuwa
"Mug..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 525
Salim ya kira yana dakuna hadi da girgiza mata
kai, yau kwana uku da yayi alkawari a cikin
kanshi, macen duk da hannun shi zai sake
tabawa zai zamana akwa halarcin yin hakan,
amman ta tsaya a gabanshi, tana kallon shi
idanuwanta cike taf da hawaye kamar tana rike
da wata damuwa ne da ba zata iya bari kowa ya
gani ba sai shi
"Daada ta fadamun Hamma, komai..."
Komai din data fada na dukan zuciyar shi, sai
yaji kafafuwan shi na rawa, shisa ya koma cikin
dakin yana zama a kasa ya jingina bayanshi da
gadon dake dakin yana kallonta, a bakin kofar
ta zare takalmanta tana shiga dakin ta zauna a
gefen shi itama tana jingina bayanta, ko ina na
jikinshi rawa yakeyi, data bude bakinta sai yaji
kamar ya katse ta, kamar yace mata abinda zata
fada ya sani, abinda zata fada abune da ko lokaci
ba zai goge masa ba, sai tayi masa bazata, sai ta
fara bashi wani labari da ta kowacce fuska ya
shafe shi amman jinshi yakeyi kamar almara,
kamar wani abu da ya kamata ace a litattafi ko
fina finai ya faru, ba'a rayuwar mutane ba, ba'a
zahiri ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 526
Sai dai ita kanta Madina bata san Daada ta tace
wasu abubuwan daga cikin labarin ba, balle
kuma Salim da yake jinshi daga bakinta
"Ina so in gansu Hamma, su duka biyun, bansan
me zance musu ba, amman ina so in gansu"
Ta karasa tana kai hannu ta goge hawayen da
take jin sun zubo mata
"Daada tace Adda Murjanatu taga wani a Abuja,
tace sunan shi Kabir...tace muna kama..."
Kai yake girgiza mata, duka yau suka ji labarin
nan, idan ita ya gama zauna mata, shi kam zaiyi
karya idan yace ya gama zauna masa, sannan
bashi kadai bane abinda yake damunshi a yau,
abubuwan sunyi masa yawa shi kadai
"Karki je wajen nan yau, kar muje wajen nan
yau Madina, bari mu numfasa da duka
abubuwan nan tukunna...idan bashi bane bafa?"
Ya karasa yana kallonta, idanuwanta sun sake
cika da hawaye
"Idan shine kuma fa?"
Ta amsa tambayar shi da tata tambayar
Lubna sufyan
Hausabook.com 527
"Hamma ka dubamun, dan Allah ka dubamun...
Ba zan daga burina ba, nayi alkawari, amman
ina so in sani..."
Kai yake daga mata, ba Abuja ba, yanda tayi
masa maganar, ciwon da yake cikin idanuwanta,
idan a karkashin duniya akace anganshi, zaiyi
kokarin dagata ya duba mata shi, alkawarin da
yayiwa kanshi sai ya bace masa lokacin daya
kama hannunta ya rike a cikin nashi, hotonta
akan gadon a kwance, da Julde a tsaye ya dawo
masa, yana saka shi kokarin cire hannunshi
daga nata, sai yaji ta dumtsa, ta sakala yatsunta
sun zauna a ciki kamar an halicce sune kawai
don su sarke cikin juna, da idanuwan shi suka
sauka cikin nata sai kalaman Julde suka dawo
masa
"Ban mata komai ba..."
Sai son kareta daga faruwar komai din ya cika
zuciyar shi, sai son samunta kafin ta haramta a
wajen shi ya lullube shi kamar bargo, ya dago
hannunta da yake cikin nashi yana kallo, ya sake
kallonta
"Ina son ki"
Lubna sufyan
Hausabook.com 528
Kalaman suka subuce masa, a karo na biyu daya
fada mata, karon farko batayi mamaki ba,
saboda tasan ko bai fada ba yana sonta, ko bata
fada ba tana son shi, akwai wanda zaice baya
son dan uwan shi? Jinin shi, amman yau
idanuwan shi a cikin nata suke, kuma idanuwan
Salim, a gabanta basa boye abinda yake ji,
zuciyarta ta yunkuro tana komawa cikin
idanuwanta da take kallon shi, saboda itama
tana son fahimta sosai, asalin ma'anar kalaman
shi
"Nasan da yawa, son da nake miki, amman
bansan yana da girma haka ba sai da naga
kamar na rasaki..."
Wannan karin mazauninta zuciyar ta koma tana
bugawa, sautin bugun da take ji har cikin
kunnuwanta
"Bai faru ba, babu abinda ya faru, daga yau zan
tabbatar da babu abinda ya tabaki, kina jina?"
Tsintar kanta tayi da daga masa kai
"Ina son ki..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 529
Ya sake fada kamar yana so kalaman su zauna
mata fiye da yanda soyayyarta take zaune a
kowanne gurbi na zuciyar shi...!
Rawar da zuciyar shi takeyi ce tasa har duka
jikin shi na amsawa, ta waje da ta ciki, a zaune
yake, sai yakejin kamar ya kwanta, ko zai samu
sauki, ko zaiji wani abu ya zame mishi dai-dai ko
da na dan lokaci ne, takarda ce a hannun shi,
kwara daya da take lankwashe, bai kamata ace
tana da nauyin da yakeji har cikin zuciyar shi
ba. Karfin warware takardar yake nema,
yanayin bugun zuciyar shi na fada masa bashida
wannan karfin, bai shirya ba, in har takardar na
masa nauyi haka, ya nauyin kalaman da take
dauke dasu zai kasance? Bayaso ya bude abinda
ba durkusar dashi kawai zaiyi ba binne shi zaiyi
da ranshi.
"Ya kamata in baka takardar nan, tuntuni ya
kamata, tunda ka fara hankalin dana yarda
dashi amman na kasa Bajjo, saboda ina tsoron
kar ta zama sanadin da zakayi mana nisa irin
wanda Bukar yayi mana, ban taba kwatanta
Lubna sufyan
Hausabook.com 530
budewa ba, bansan menene a ciki ba...Daada
tace mun Bukar yace abinda duk yake a jakar
naka ne, mallakinka ne, sai na dauka harda
wannan takardar, zuciyata ce ta hanani baka,
idan ka tashi lissafin abubuwan da zaka yafe
mun harda boye maka wannan"
Haka Julde yace masa, shi baije wajen Julde don
ya dawo da wannan nauyin ba, ya shiga ne da
niyyar ya duba shi saboda kullum Saratu na
cewa bacci yakeyi, daya tambayi Khalid ma haka
yace tace masa, amman Khalid din yayi magana
da likita, yace masa jinin Julde daya hau ya
sauka, idan ya kiyaye ka'idojin duk da aka
shimfida zai cigaba da samun sauki cikin
hukuncin Allah. Haka kawai saiya kasa samun
natsuwa, dan ko da Saratun tace masa
"Bacci yakeyi"
Kai ya girgiza mata, saboda a kasan kwalliyar da
take fuskarta yana ganin damuwa shimfide,
yana kuma ganin idanuwanta da suka nuna
alamun yawan hawayen da suke zubarwa, da
kuma wanda suke kwance a ciki a lokacin
Lubna sufyan
Hausabook.com 531
"Ina so in ganshi, dan Allah Nanna... Zan ganshi
ne kawai"
Sai kuwa ta jinjina masa kai, sai daya
kwankwasa dakin Julden ya tura, yana zaune
akan gado, suna hada ido sai yaga yanda Julden
yake shirin saukowa, kamar yana neman wajen
da zai ruga don ya boye, yanayin shi na saka shi
gane cewa ba bacci yake ba duk sanda suka zo
da nufin duba shi, boye musu yake, suma
boyewar sukeyi shisa a cikinsu babu wanda ya
matsa saiya ganshi ko da daga kwancen ne, su
duka gujewa fuskantar juna sukeyi
"Idan ka cigaba da boyewa, Daddy idan muka
cigaba da boyewa ya zamu wuce abin nan? Ya
zaiyi mana saukin dauka?"
Kalaman suka subuce ma Nawfal suna dukan shi
kamar yanda suka daki Julden,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 27