girma ce. Kuma Hammadin ba
irin mutanen da zasu dishe maka a zuciya bane
ba.
Kalaman shine suke dawo mata suna
nukurkusar ta
"Me yasa son zuciya yayiwa mutane yawa
Daada? Ashe dan uwa zai iya neman rayuwar
dan uwan shi akan dukiya?"
Dan murmushi tayi
"Dukiya kace Bukar, mai hada iyaye da 'ya'yan
su...balle kuma 'yan uwa"
Numfasawa yayi
"Da irin dukiyar nan gwanda ace baka samu ba,
in dai zata taba zumunci bata da wata rana"
Sai dai Bukar bamai yawan magana bane ta
wannan fannin, da wuya kaji cikakken labari a
bakin shi, zai tattauna ne kan abinda yake
tunanin ya shafe shi. Wanda bai shafe shi ba zai
barshi
Lubna sufyan
Hausabook.com 261
"Wasu labaran bayar dasu bashi da amfani... Kai
da ka bayar da wanda ya saurara inka duba
duka ba zai amfane ku ba balle ku amfani
madaukin labarin... To ina amfani bata lokacin
da akayi?"
Shine kalaman shi inka nemi jin wani abu da
akayi akan idon shi, ko aka fada yana zaune.
Shisa bata tambaye shi dalilin da yasa yayi mata
maganar ba. Watakila wani abinne daya ga ya
faru acan Borno da yake karatu. Amman sati
dayan da yayi maganganun shi duk akan cin
amana ne da yake faruwa tsakanin 'yan uwa. Sai
da ya tafi take ta juyayin maganganun, tana
neman tushen su. Hannunta da ya taba wuyan
Yelwa na fisgota daga nisan da tunaninta yayi
"Ba zazzabi ke son kamaki ba, zazzabin kikeyi
Yelwa...bari Julde ya shigo in fada masa. A dibo
magunguna in dafa miki"
Sake shigewa jikinta Yelwa tayi, yanda ta hade
fuska tana turo baki na nuna rashin son
maganinta. Shisa in ba lura akayi da bata cin
abinci ba, tana kuma ramewa, sosai take
kokarin ganin ba'a san bata da lafiya ba dan kar
Lubna sufyan
Hausabook.com 262
asa ta sha magani. Yau dinma dan rashin lafiyar
ta wuce wajen jikinta, har a tsakanin
hakarkarinta ciwo yakeyi, musamman kirjinta
da yayi wani irin nauyi, shisa bata sake cewa
komai ba. Wuni tayi a kwance, sallah ce kawai
take fito da ita har bayan la'asar. Julde saida ya
sake dawowa, amman tayi luf kamar bacci
takeyi, kallo daya zai mata ya gane akwai abinda
yake damunta daya girmi ciwon da ta fada.
"Wai bata tashi ba har yanzun?"
Ya tambayi Daada data girgiza masa kai
"Tayi sallah, zazzabin ma ya sauka fa... Baccin
dai ta sake komawa"
Duka tana jinsu, kan tabarmar da ta saka pillow
ta kwanta ya ajiye ledar kifin daya siyo mata
tunda yasan tana so
"Allah ya kara sauki, kifi na dawo in kawo mata
daman"
Wani dan lokaci ta bashi da fita sannan ta
mirgina ta tashi tana murza ido
"Ga kifi nan Hammanki ya kawo miki"
Lubna sufyan
Hausabook.com 263
Dije tace mata, saida taje ta wanke fuskarta
sannan ta dawo ta bude ledar kifin. Ta fara ci
kenan duk da yau tashin hankalin da take ciki
ko dandanon kifin bata ji. Ta zare kaya daga
jikin wata tsoka da tayi nufin kaiwa bakinta
Datti ya shigo babu ko sallama, ta daga ido ta
sauke akan shi, kallon da yake mata na tabbatar
mata da karshen duniyarta na gab da zuwa
"Waye Kabiru? Ke kika turamun shi?"
Dan kifin da taci ya hargitse a cikinta yana
barazanar dawowa
"Kabiru kuma?"
Dije da take kwashin tuwo tayi tambayar cike da
rashin fahimta, amman Datti bai amsata ba,
Yelwa yake kallo da duka alamunta ya tabbatar
da zargin shi. Ya dauka ya fara dawowa dai-dai,
bayan mutuwar Hammadi nan kusa babu wani
abu da zai hargitsa shi. Yana zaune karkashin
bishiyar da sukan zauna da Hammadi lokutta da
dama, aka zo masa da maganar yayi bakin da
suke neman shi. Mu'amala ta kasuwanci ma sai
an tona za'a kirga sanda ta hada shi da wani
kabila, saboda yanda yaki jininsu, musamman
Lubna sufyan
Hausabook.com 264
hausawa da duk wanda yaci karo dasu basu san
ya kamata ba a idanuwan shi
"Daman dan wajena ne yaga yarka, muka zo
neman izini"
Mutumin ya fadi bayan sun gaisa ya zayyana
masa daga shiyyar Kano suke, kauyen Bebeji, ya
kira kanshi da Malam Lawalli
"Ban mata miji ba, amman bahaushe baya cikin
tsarin kalar wanda nake so"
Ya tuna amsar daya basu a zafafe duk kuwa
yanda yaso ya tausasa kalaman shi, yanda yake
ta kokarin danne zuciyarshi a lokuttan da yasan
Hammadi zaiso yayi hakan. Sai Malam Lawalli
ya tsaya neman yi masa bayani harda kawo
masa wasu zantuka da larabcin da bayaji yana
kokarin fassarawa da hada masa da fulatanci
cikin yanayin daya kara harzuka shi. Ba zai tuna
duka abinda ya faru ba, amman yana sane da
karshen, karshen daya ja kunnen Malam Lawalli
akan kar hanya ta sake hada Kabiru da 'yar shi
"Ina son shi Baba...Kabirun, ina son shi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 265
Yelwa ta fadi cikin wata murya da take jin ta fito
daga kowacce kusurwa ta zuciyarta, kafin ta
sadda kanta kasa hawayen ta na samun zubowa
"Wani a cikin ku yaimun bayanin da zan
fahimta, waye Kabiru?"
Dije ta fadi tanajin wani tashin hankali na dirar
mata, yaranta suna da tasu rayuwar da bata san
da ita ba, ta jima da yarda da haka, tun lokacin
da Julde da Yelwa suka fara tasawa suka koyi
shawara da junan su, suka koyi adana sirrikan
juna suna wareta a ciki. Hakan bawai yana mata
dadi bane, a matsayinta na uwa tana son sanin
duk wani abu daya shafe su, mai muhimmanci
ko akasin haka. Amman ya zatayi idan suna
ganin sun ishi juna a wasu lamurran? Suna
ganin kamar ba sai taji ba? Sai dai in ta fahimta
wannan ba karamin abu bane, ba lamari bane
da ya kamata ace ya tsallake saninta.
"Bahaushe ne"
Cewar Datti da duk wata tsana da zai iya. Kamar
yaren Kabiru ya isa ya zama dalilin da zata
fahimta
Lubna sufyan
Hausabook.com 266
"Na sani"
Ta amsa tana saka idanuwanta da suke cike da
hawaye ana Datti
"Ki fita idona Yelwa, ki kiyaye ni wallahi...ki zabi
ko dan waye kaf Marake da tsallakenta, daga
kabilarki, yarenki, ki zabi kowa indai
bafullatani ne zan bashi. Banda wannan"
Ya karasa maganar a tausashe, cike da son ta
fahimce shi, hawaye wani na koro wani haka
suke saukar mata. Ji takeyi rabuwa da Kabiru
dai-dai yake da fitar numfashinta
"Dan Allah Baba, shi din dai"
Takawa Datti yayi yana zama gefen tabarmar da
Yelwa take, su duka sunayin kamar basa jin me
Dije take cewa, shisa ta dauki ido ta saka musu
tana ganin Ikon Allah, zuciyarta na cigaba da
lugude a cikin kirjinta
"Yelwa bahaushe ne, bahaushene"
Datti ya sake fadi kamar zai kamata ya jijjigata
ko zata fahimce shi
"Yana da halaye masu kyau..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 267
Itama tace tana so ya fahimceta
"Yanajin fulatanci"
Kai yake girgizawa, ba zai iya ba, hada jini da
hausawa, ya tsane su, tsanar da ba kowa bane
zai fahimta
"Bana sonki dashi, umarni ne..."
Ya karasa maganar yana mikewa, kanshi sarawa
yake saboda tashin hankali, tilon 'yar tashi zai
dauka ya mikawa bahaushe? Abinda ya guda
kenan shisa ya hada Julde da Saratu, sai Yelwa ta
kwaso masa? Duk samarin dake Marake sai
bahaushe? Saboda ta hargitsa masa lissafi? Ba
zata barshi yaji da kewar Hammadi ba, saita
kara masa da wannan maganar da tashin
hankali ce a wajen shi, ganin yanda take kuka na
kara saka kirjin shi daukar dumi, akan
bahaushe? Shisa ya zabi ya tsoratata
"Allah ya isa tsakanina dake idan kika kara kula
shi Yelwa..."
Kalaman suka fito masa suna tsayar da duk
wani sauti da ke cikin gidan, suka dirar ma
Yelwa da wani yanayi marar dadi
Lubna sufyan
Hausabook.com 268
Ya zatayi da kaddarar da ta kullu a tsakaninta
da Kabiru tun kafin samuwar su?
Ta ina zata fara da abinda baya karkashin ikon
ta?
Da akace komai na da lokacin shi, a cikin lissafin
mutuwa, aure, haihuwa da arziki sune sama.
Komai sai yabi bayansu har suna danne wasu
abubuwan, a shafuka na kwakwalwar Julde
yanda lokaci ya kasance a bangarenshi saiya sha
shi tunanin ba zai taba nuna masa karfin ikon da
Allah ya bashi ba. Ba zai cika akan shi ba, cikar
da ta fara da bankado sirrikan da yake boyewa a
wajen Saratu a wayewar safiyar da ta gaji da
tashin shi don yin sallar asuba har gari ya waye.
Ya fito tsakar gida ya sameta da tsohon cikin da
yake jikinta, ta daga ido tana kallon shi, yanajin
yanda take yawatawa da idanuwan a jikin shi
kafin ta tsayar dashi akan wuyan shi
"Jambakin waye a wuyanka Julde?"
Ta jefe shi da tambayar da ta sakashi saurin kai
hannu ya taba wuyan, rashin gaskiyar shi na
Lubna sufyan
Hausabook.com 269
nunawa har kan fuskar shi. Ranar na bude musu
wani babi na tashin hankalin da bai taba
hangowa ba. Saratu na sakashi raina zafin
zuciyar da yake tunanin yana da ita. Tana nuna
mishi daga jikin Datti ya fito, amman a halayen
shi bai dauki komai ba. A tsakiyar tashin
hankalin ne takai mishi wata damka da yaga ta
neman taimako ce a cikin idanuwanta
"Bayana, bayana ya karye Julde"
Ta fadi tana durkusawa, su duka abin sai ya
zame musu bako, sai da yaga numfashinta na
barazanar barinta tukunna ya samu ya kwace
daga rikon da tayi masa yana rugawa gidansu ya
kira Dije da ko mayafi bata nema ba tabi
bayanshi. Haka aka wuni, dare ya batar da
hasken rana, duhu na mamaye ko'ina, amman
nakuda Saratu takeyi babu alamar zata tsagaita
mata. Yanayin da ya daga hankalin kowa
musamman Julde da yake ganin kamar laifin
shine. Haka kawai sai Hammadi yake ta fado
masa a rai, da yajuyo wani nishi da Saratu tayi a
tsakiyar dare kamar ana zare mata rai sai da
zuciyarshi ta tsinke.
Lubna sufyan
Hausabook.com 270
"Daman watan haihuwarta ne?"
Wata mata da aka kira ta tambaya, yanajin Dije
ta amsa da
"Akwai sauran satika uku kafin watan ma ya
tsaya"
Yana tsaye a tsakar gidan da yake mamaye da
duhu, baka ganin komai sai taurari da sukayiwa
sama ado suna dishe hasken watan daya fara
nuna alamar bankwana don ya ba wani hanya,
ya tsinkayi muryar Yelwa da baiji shigowarta ba
"Hamma har yanzun shiru?"
Ta tambayeshi, juyawa yayi, hasken fitilar dake
hannunta na shigar masa ido, sai yaji kanshi ya
sara, bayan gajiya, zullumi da yunwa akwai
rashin bacci daya hade masa tare da komai. Da
Saratu ta fada masa tana tunanin akwai ciki a
jikinta
"Allah ya saukeki lafiya"
Ya furta batare da yasan me yaji ba, haka da
cikin ya fara nunawa a jikinta. Randa ya
motsa suna zaune ta kama hannunshi da sauri
Lubna sufyan
Hausabook.com 271
tana dorawa akan cikinta, wannan karin motsin
na faruwa kamar a cikin jikinshi. Yaji zuciyarshi
ta buga, ta sake bugawa tare da motsin abinda
yake cikinta. Yanayine da babu kalaman da zasu
misalta shi, idan akwai ta ina zai fara? Ta ina zai
fara cewa Saratu bata taba saka zuciyarshi ta
motsa ba, amman daga ranar dayaji motsin
abinda yake cikinta idan ya kalleta sai ya tsinci
idanuwanshi da saukowa dai-dai cikinta, waje
daya da ya saka zuciyarshi motsawa a tare da
ita.
Cikin kanshi kalaman basu da wata ma'ana ko a
wajenshi, ya zai fara furtasu har wani yaji? Waye
zai fahimta? A wajen iyayen shi ya fara ganin
aure, yaga menene aure, Hammadi saiya nuna
masa aure a wajen kowa da yanda kowa ya
dauke shi ya bambanta. Asalin ma'ana ta aure ta
wuce hasashe, ta kuma wuce a kwatanta maka.
Gashi a cikin aure, nashi kuma ya bambanta da
duka wanda ya gani. A tsakanin fadan Datti,
akwai fahimta ta Dije da kuma hakurinta da
yake rike da igiyoyin aurensu, idan ka ajiye
duka wannan a gefe suna hira da juna, bai taba
ganinsu a tare sun rasa abin cewa juna ba. Ko da
Lubna sufyan
Hausabook.com 272
fadane kuwa zasuyi, shirun da yake cikin
zamantakewar su bashi da yawa.
Amman yaune fada na farko da sukayi da Saratu
tunda sukayi aure. Shiru yafi komai yawa a
zamansu, duk da inya koma yaci abinci ya sake
ficewa sai tayi bacci yake komawa wasu
ranakun, wasu ranakun kuma baya dawowar ne
da wuri saita fara bacci, inda Allah ya soshi ma
bata da nauyin bacci, inda duk zai kwankwasa
gidan sau daya zuwa biyu zaiji takun tafiyarta
tazo ta bude masa. Bata taba masa magana akan
dadewar da yayi ba kamar yanda bata taba
tambayar shi inda zashi ba idan ya gama cin
abincin dare. Wani abu da yake masa dadi a tare
da ita.
Tana kokari, da yawan lokutta Saratu na
kokarin jan shi da hira, ko ta bashi labari,
amman idan ya gama amsa mata, saiya duba
cikin kanshi yaga babu wani labari daya da yake
dashi wanda zata so taji. Mutanen da zai kira da
abokai yanzun hirarrakinsu duka akan matan
da suke bine ko wanda idanuwansu yake kai.
Labaraine da yasan ba zata so taji ba, haka shiru
zai sake samun wajen zama a tare dasu
Lubna sufyan
Hausabook.com 273
"Zuciyata sai bugawa takeyi Hamma"
Yelwa ta katse masa tunanin da yake, sosai ya
kalleta, tayi wata irin rama kamar abincin duk
da zai shiga cikinta baya samun nutsuwar da zai
yawata har ya samu wajen zama. Gabaki daya
kamar ba kanwarshi ba, idanuwanta kamar anyi
mata musanyarsu, akwai wani kyalli da yake
cikinsu ada da yanzun babu shi. Julde baisan ko
shi kadai yake ganin haka ba, idan tayi dariya
sai sautin ya dirar masa daban, tun jinyar da
tayi bayan rabata da Kabiru bata dawo dai-dai
ba, jinyar da kowa ya fitar da rai da tashinta,
dan lokacin ta tabbatar masa da idan kaji ana
cewa maza dauriya suke da ita to lallai abinda
zai fito da hawayensu ne bai faru ba
"Baba dan Allah kabarta ta auri Kabirun, idan
akan shi take jinyar nan kabarta ta aure shi"
Ya roki Datti a lokacin, sai dai ya kalle shi, wani
kallo daya ja layi a tsakanin su, kafin kalaman
shi su saka layin yin kasa yana bayyanar da
wani fili mai zurfin gaske da Julde baya tunanin
zai tsallaku a wajen shi harya samu Dattin su
sake zama bangare daya
Lubna sufyan
Hausabook.com 274
"Gara in binneta da in dauketa in ba yaron nan"
Baice komai ba, ya mike, ya tafi yana barin
Dattin inda ya same shi. Sai dai sanda duk zai
ganshi sai kalaman sun dawo masa da wani
yanayi da baisan ya zai fassara shi ba. Yelwa ta
tashi, amman ya kasa daina jin kalaman sun
dawo masa duk idan ya kalli Datti, da duk rana
kuma da yanda yake jin suna kara yiwa juna
nisa duk da kusancin da suke dashi na mahaifi
da kuma da. A yanda kalaman da zasu cewa
junansu bayan gaisuwa da maganar kasuwanci
suke musu karanci yake kara jin da gaske nisa
suke yiwa juna, nisan da baisan ya zai tsayar
dashi ba
"Me yasa kika boyemun Kabiru?"
Ya tambayi Yelwa, yana ganin murmushin da
tayi da yasa kirjinshi zafi
"Duka ya wuce ai Hamma, ya zama tarihi"
Numfashi yaja yana fitarwa
"Na so in sani"
Cikin ido ta kalle shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 275
"Zaka iya canza ra'ayin Baba?"
Sai da ya juya maganar yanajin tasirinta har
cikin jikinshi tukunna ya girgiza mata kai, ya
bude baki ta rigashi ta hanyar canza akalar
hirar. Bai sake daga mata zancen Kabiru ba har
yau, yana dai nuna mata cewar idan tana son
maganar kofar hakan a bude take a wajenshi. Ya
bata tazarar da take bukata tayi jinyar zuciyarta
harta warke kafin ya tambayeta ya soyayya take
saboda yana son sani. Daga bakin Yelwa da tayi
soyayyar da take da tasirin canzata har haka
"Nima tawa zuciyar..."
Ya bata amsa yanzun
"Ba abinda zamu iyayi sai dai muyita jira ko?"
Kai ya daga mata a hankali, da bangon wajen
suka jingina suna jiran, kowa da tunanin da
yakeyi. Bata haihu ba sai bayan asuba inda aka
fito masa da jaririn da aka saka a hannun shi, ya
kalle shi yana jin wata irin kauna da bai taba
sanin akwai irinta ba a cikin duniya ta cika
kirjin shi. Dan shi, dan shi na farko ya rike a
Lubna sufyan
Hausabook.com 276
hannun shi, dan da bai hango samun shi a kusa
haka ba
"Salim"
Sunan ya gifta cikin kanshi, sunane da yaji an
kira wani yaro a cikin Kano. Sai sunan yayi masa
dadi, kamar yanda bai hango samun yaro nan
kusa ba, haka bai hango sunan zai zame masa
mai muhimmanci har haka ba. Ranar ya kamata
ace ya saka rayuwar shi gabaki daya manhangar
tunani ya fara canzata
Amman ya zaiyi da kaddarar da take bibiyarshi?
Kaddarar da kowanne mai rai da kalar tashi
Tun Saratu na zaman jego ya san cewa rigimar
da nakuda ta yanke musu bata kare ba a
tsakaninsu. Salim yake sakashi kusantar inda
take saboda hararar da take binshi da ita duk
idan idanuwan kowa baya kansu. Baisan me ya
bashi yakini da kuma kwarin gwiwar cewa
sirrin shi a adane yake a wajen Saratu kamar
yanda yake adana abinshi. Ba zata taba daga
maganar ta wuce tsakaninsu ba. Shisa yake
baccin shi hankali a kwance, sai kuma ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 277
tabbatar masa da hakan. A cikin gidansu tayi
zaman jegonta duk kuwa yanda yan uwan
mahaifiyarta suka so ta koma wajensu.
Abu bata duba halinta ba, bata duba yanda
darajarta a idanuwan Saratun bata da wani
yawa ba, ita ta zauna mata, kwanakin nan tayi
tsaye akanta yanda uwa zata tsaya akan yarta.
Saboda a wajen Abu zatayi fiye da haka akan
duk wani da yake da kusanci da Hammadi balle
kuma yarshi. Julde da kanshi ya roketa da ta
zauna tare dasu, zama har iya lokacin da rayuwa
ta ara musu
"Kwanakin nan na jure sune a tare daku saboda
ina hango karewarsu duk safiya Julde. Kayi
hakuri, nisana ba zai taba dishe kaunarku a
raina ba balle ya yanke zumuncin mu"
Wannan yanayin, yanayin nan mai cike da
kwarjini da yake tare da Abu shiya hana masa yi
mata musu. Datti daman bai gwada ba, zai iya
kirga haduwarsu, ko da yasan zata tafi ma,
sallamarshi daga bakin Dije ta fito, daya ganta
sai ta tuna masa da yanda Hammadi ya barsu,
bari na har abada, saiya kasa tsaida hawayenshi.
Lubna sufyan
Hausabook.com 278
Kewar dan uwanshi tana nukurkusar shi fiye da
yanda zai fada. Musamman a watannin nan da
yake jin kamar bashi da kowa a filin duniya
banda Dije da Saratu. Ga yaranshi yana kallon su
amman ji yake sun masa wani irin nisa. Basa
hira dashi kamar da, daga Julden har Yelwa
babu mai doguwar hira dashi, yanda suke
mikewa bayan sun gaisa na saka kalaman da yai
niyyar fadi koma masa.
Gudun shi sukeyi, da babu Saratu, da baya
ganinta, da bata shiga duk daren duniya tana
masa hira da yaji kamar bashi da yara a cikin
watannin nan. Saboda zabin da yake ganin don
gobensu yayi shi, saboda yana kokarin saita
musu hanyar da zasubi a zamansu na duniya
batare da sunci karo da komai ba. Sun kasa
ganin yanda su biyun ne fiye da rabin
duniyarshi. Lokutta da dama yana so yayiwa
Dije maganar amman saiya rasa ta inda zai fara
tunda ita bata tabayi masa ba. Bai kula da nisan
da Yelwa tayi masa saita hada harda ita a ciki ba.
Yanda bayajin hirarta haka itama, har Julde ma,
yana gaisheta, yana zuwa ya zauna kusa da ita,
Lubna sufyan
Hausabook.com 279
amman Yelwa na fitowa zasu tashi tare, suna
rayuwa kamar basu da kowa sai junansu.
Sai suka kara mata kewar su akan ta Bukar da
take fama da ita. Tayi kokarin magana da
dukkan su taji matsalarsu, kamar sun hada baki
kowanne a cikinsu ya amsa mata da
"Bakomai Daada, me kika gani?"
Yanda duk tayi amsar su idan batazo daya ba to
tana shige da juna. Sun saka wata kofa a
tsakaninta da damuwarsu sunja sun rufe. Saita
koma gefe ta saka musu ido, Abu da take gani
tanajin dadi tayi mata nisa itama, wasu
abubuwan kuma ba tasan ta inda zata fara
maganarsu da Datti ba, waje kawai ta share a
zuciyarta ta zubasu tana jin yanda suke kara
taruwa. Komai dai shiru, irin shirun da zai saka
maka shakku akan abinda zai biyo bayanshi.
Hakan ta faru dasu kuwa, hayaniyar da ta biyo
bayan shirun ta bankado sirrikan Julde da aka
samu Datti har wajen dabbobi aka fada masa,
daga bakin mutumin da shine na karshe da Datti
yayi tsammanin zai samu kwarin gwiwar
tsayawa dashi ido cikin ido ya fada masa
Lubna sufyan
Hausabook.com 280
magana. Saboda daga mata har maza a gidan
Balarabe babu na kirki, daya a cikin matan ma
ta balle ta shiga duniya, labarin karshe da Dattin
yaji akanta ana fada shine kudu ta gudu, gari
mabanbanta a bakin mutane, wasu suce tana
Lafia, wasu suce tana Makodi. Har zancenta ya
shude saboda sababbin labarai da suka danne
nata. Kusan kowa a garin ya sallama indai akan
yan gidan Balarabe ne.
Shima kamar ya daina damuwa da zantukan
mutane, yanda duk ake cewa ya murzawa
idanuwan shi toka, Datti bai hango yakai har
haka ba, ya kai matakin da zai kalle shi yace
masa
"Ciki danka yayiwa 'yata"
Batare da ko yi masa sallama ba balle kuma su
gaisa. Zantukan nayi masa daban, kamar da
wani yare yayi masa magana ba da fulatanci ba,
a karo na farko da ya kalli Balarabe yana jira ya
fassara masa abinda yake nufi
"Yanzun haka tana can rai a hannun Allah
saboda kokarin zubar da cikin da tayi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 281
Ya sake dukan shi da wasu kalaman da yakejin
su baki a cikin yarenshi. Kallon Balarabe kawai
yakeyi, sauran maganganun shi na wucewa tare
da iskar da take kadawa a ciki. Can ya tsinkayi
tashi muryar cikin wani yanayi yana tambayar
Balarabe
"Wanne yaron nawa?"
Saboda kalmar yaro yasan tana nufin abubuwa
da yawa, ciki harda wanda suke aiki a karkashin
shi bawai iya Julde kadai ba
"Kana da wani yaron daya wuce Julde ne?"
Baiga tashin hannun shi ba sam, sai karar marin
daya wanke fuskar Balarabe dashi da yaji cikin
kunnuwan shi. Balarabe yayi kokarin ramawa
sai Datti ya rike hannun shi yana sake wanka
masa wani marin. Ba za'a kira abinda ya wakana
tsakanin su da dambe ba, tunda ko sau daya
Balarabe bai samu damar rama marukan da
Datti ya dinga jera masa kafin a rabasu ba
"Idona zaka kalla kace dana yawa yarka ciki?
Iskancin ka a kaina zai juyo yau? Ni sa'anka ne?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 282
Dakyar aka sha kan Datti bayan yaci alwashin
duka Marake babu wanda ya isa ya hanashi
nunawa Balarabe iyakarshi. Inda yasan zai sami
Julde ya nufa kanshi tsaye
"Yace bayajin dadi ya tafi gida"
Aka fada masa, sai yayi gidan. Inda ya sami Julde
zaune kusa da Daada, tunda ya tashi da safe
yake jinshi wani iri. Har Saratu saida ta tambaye
shi ko wani abu yana damunshi tunda taga bai
dauki Salim ba. Ko cikin dare ya tashi yana
kukan rashin dalili, kuma taga ba yunwa yakeji
ba, Julde zai karbeshi, tun tana dariya idan yace
ta goya masa shi har ta saba, haka zaita
jagalniya dashi yace ta koma baccinta.
"Kawai jikina ne yayi mun nauyi"
Ya amsa mata a takaice yana fita. Wajen la'asar
ya dawo, abinci ma kadan yaci ya sake fita. Sai
dai ba nisa yayi ba, gidan Daada ya shiga saboda
koya yakejin zuciyarshi babu dadi zama a kusa
da ita na rage masa wannan nauyin ko da ba
hira sukeyi ba. Balle yau hirar ma sukeyi da
suka kwana biyu basuyi ba, tana bashi labarin
irin al'adun na Marake da yanzun zamani ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 283
fara shudewa dasu, abubuwan da suka canza.
Yanata mamaki, yanajin kamar anya da rayuwa
akeyi ta jin dadi kuwa? Kamar sun tsaurara a
cikin lamarin su da yawa.
Yanda Datti ya shigo gidan, kallo daya Julde yayi
masa yaji zuciyar shi ta buga a cikin kirjinshi,
kafin ta koma mazauninta
"Balarabe yace kawa 'yar shi ciki... Me yasa
Balarabe zaice kawa 'yar shi ciki? Me yasa zai
hada sunanka a waje daya da wannan
kwamacalar?"
Datti ya fadi cikin wata irin murya da take nuna
yanda ranshi yayi kololuwa wajen baci. Yanayin
da yasa zuciyar Julde sulalowa ta fado kan
tandaryar kasa. Wani tashin hankali da bai taba
sanin akwai shi ba yana maye masa gurbinta.
Karasa takowa Datti yayi yana zama gefen Julde
da ya sadda kanshi kasa, kwakwalwar shi tayi
nisan kiwo saboda babu komai a cikin kanshi,
wayam yake ji
"Akan me zai kira sunanka? Akan me zai kira
mun sunan yaro?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 284
Ya karasa maganar yana kallon Dije da takejin
bugun zuciyarta har cikin kunnuwanta. Julde ta
kalla, sai taji jijiyoyin dake rike da zuciyarta na
tsinkewa, saboda abubuwa da yawa a yanayin
shi ya nuna rashin gaskiyarshi, lumshe
idanuwanta tayi abubuwa da yawa na mata
yawo cikin kai, a cikinsu harda wani sabon
shafin tashin hankali da kaddara ta bude musu
"Zai iya yiwuwa ba karya yayi ba"
Julde yai maganar, muryarshi na korar duk wata
hayaniya da take cikin gidan, har iskar dake
kadawa sai da kararta ta dauke musu kamar taji
yanda kalaman Julde suka fito suke kuma canza
komai
"Me kace?"
Datti ya tambaya, dago kai Julde yayi suna hada
ido da Datti
"Zai iya yiwuwa ba karya yayi ba Baba..."
Marin shi Datti yayi, abinda bai taba yi ba tun
haihuwar shi, yanajin wani abu na tarwatse a
cikin kirjinshi da karar marin, sai dai a wajen
Julde marin ba zai sa ya canza kalamanshi
Lubna sufyan
Hausabook.com 285
ba. Gaskiya ya fada, idan cikine a jikin Jummai
yar Balarabe to tabbas akwai yiwuwar nashine.
Kome zai fada a wannan bigiren, a wajen Datti
da Dije dai asirin shi ya gama tonuwa, a duka
Marake ma harda kewayenta, labarin shi zai iya
tsallakawa. Saboda yayi ban ruwa a gidan da
fitowar shukar yake dai-dai da ganin idanuwan
kowa
"Kayi mun maganar da zan gane"
Da wani yanayi Julde ya sake kallon shi
"Me zan sake cewa Baba? Me kake so in sake
fada?"
Tari Datti yayi, kwarewa yayi, amman a cikin
kirjinshi yake jin wasu abubuwa sun sarke,
sosai yake tari ga wani irin juyawa da yaga
gidan yanayi masa. Sama-sama yake jin muryar
Dije tana masa maganar da bata karasawa cikin
kanshi balle ya fahimta. Harta rike masa kafada
ba zaice ga abinda yake faruwa ba. So yake ta
jijjigashi ta tashe shi daga wannan mugun
mafarkin da yakeyi. Ta tashe shi ya fara sake
rayuwa kafin Yelwa ta jajubo Kabiru daya fara
canza musu komai har zuwa yau, kanshi ya dan
Lubna sufyan
Hausabook.com 286
karkata yana kallon Julde da yake zaune kamar
an dasa shi. Sai yaga kamar baya numfashi,
kamar gawarshi ce a gabanshi binne shi kawai
yake jira yayi.
Saboda danshi mai rai, wanda ya fito daga
jikinshi ba zai masa abinda Julde yayi masa ba,
ba zai mayar dashi abin magana da kwatance a
cikin garin Marake yanda yaga ya'yan wasu sun
mayar dasu. Shi da yake zama ayi labari dashi? A
kwatanta lalacewar yaran wani gidan da wani, a
la'ance su tare da shi. Yaushe abin ya tsallako
kanshi? Numfashi yaja ya fitar yanajin wani irin
ciwo marar misaltuwa, tarin ya tsagaita masa,
amman gara tarin da abinda yakeji
"Allah ya isa tsakanina da kai Julde... Allah ya
tsine maka albarka"
Kalaman suka kwace masa suna binne masa
Julde da yake gabanshi. Yelwa da ta shigo itama
kalaman taji
"Baba..."
Ta kira muryarta dauke da tashin hankali
Lubna sufyan
Hausabook.com 287
"Kema rayuwar da ya zaba zaki zaba in hadaku
tare in sallamawa duniya?"
Datti ya tambaya yana kallonta, dauke
idanuwanta da suka cika da hawaye tayi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 27