An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Lubna sufyan
Hausabook.com 1
Lubna sufyan
Hausabook.com 2
RAI DA KADDARA
2
02
2002
RAI DA KADDARA 2
Abubuwan da zai tuna kafin rasuwar mahaifin
shi ba su da yawa. Ya dai san basu taba hada
shekara biyu cikakku a waje daya ba kafin
zuwan su Marake, kauyen da kaso tamanin cikin
dari na mazaunan shi fulani ne, sai dai su suna
cikin fulanin da ake ma lakabi da "fulanin tashi".
Bai samu ya tambayi mahaifiyar shi ko rasuwar
mahaifin shi ce ta sasu yanke hukuncin zama a
Marake da ke karkashin hukumar Dutsi ta jahar
Katsina ba, itama nata ajalin ya risketa bayan
ciwon cikin kwanaki biyu rak. Rasuwar ta dake
shi fiye da ta mahaifin shi, saboda dalilai biyu,
yafi shakuwa da ita, kuma yana da hankali fiye
da waccen rasuwar.
Lubna sufyan
Hausabook.com 3
Datti shine sunan da ya taso yaji kowa na kiran
shi, saboda ance ya gaji sunan baban mahaifin
shine Auwal. Su biyune kawai a wajen mahaifin
su da mahaifiyar su, daga shi sai Hammadi,
bayan rasuwar su dukan kulawar shi sai ta
koma wajen Hammadin da bai sha wahala ba
wajen samun matar aure, ko basu duba sanyin
halaye irin na Hammadi sun bashi mata ba, zasu
duba tarin dukiyar da aka bar musu. Dan ko
lokacin da suka zo kauyen Marake ance babu
masu yawan dabbobi irin su, tun daga shanu
zuwa tumakai da awaki.
Ya na kula da yanda dukiyar da aka bar musu
take kara habbaka saboda kulawa da tattali irin
na Hammadi, ga gonaki da yake ta siye a hankali
da ma'aikatan da yake tarawa a karkashin shi
don ya fara zuwa kudu cinikayyar dabbobi, da
yake mutum ne shi da baya son tafiye-tafiye,
tunda ya samu mutum biyu masu amana saiya
bar musu wannan ragamar shi ya zauna yana
kula da komai daga nan kauyen. Sai da ya
zamana da wahala kayi zaman awa daya a waje
batare da kaji wani ya ambaci Hammadi ba, ya
kawo ma matasan kauyen cigaba ta hanyar
Lubna sufyan
Hausabook.com 4
sama musu sana'ar da zasu dogara da kan su, ga
alkhairi da yake da shi da son kyauta. Banda
kamanni halayen Datti da Hammadi sunyi
hannun riga ta yanda zakayi mamaki idan akace
maka daga tsatso daya suka fito.
Hammadi na da sanyin hali, Datti na da fadan da
wata irin zuciya da Hammadi kan ce
"Ina tsoron wannan saurin fushin naka Datti, ka
dinga sanyaya zuciyar ka. Ba kowanne al'amari
bane yake bukatar tashin hankali..."
Sai dai ta kunnen da maganganun Hammadi
suka shiga ta dayan suke fita batare da sun
samu wajen zama ba. Bayan wannan yana ji da
tarin dukiyar da suke da ita, Datti najin duka
Marake da kewayenta babu kamar su, saboda
haka babu wani wanda ya isa a idanuwan shi,
yafi karfin kowa kamar yanda yafi karfin komai.
Sunayen 'yan uwan biyu ya zagaya kauyen
Marake da kewayen ta, kowa a cikin su ya
shahara da halaye mabanbanta
"Baka ganin ya kamata Datti yayi aure?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 5
Matar Hammadi, Abu ta shawarce shi wani dare
bayan ya gama cin abinci, murmushi yayi cikin
sanyi
"Ba auren ba Abu, kina tunanin Datti zai iya
hakurin zama da mace?"
Yar dariya tayi
"Waya sani, kila auren ma yasa ya rage zafin kai.
Mai hankali za'a duba a hada su"
Kai Hammadi ya jinjina, ba zancen bane bai
zauna mishi ba, tun kafin ta furta yake tunanin a
cikin ran shi. Sai dai halayen Datti suna damun
shi, matuka, kusan rashin samun rabon su shi da
Abu a shekara ta bakwai da auren su yanzun
kadai ne abinda yake damun shi fiye da halayen
Datti. Bashi da dangin da zasu tsangwame ta kan
rashin haihuwa ko su matsa mishi da ya karo
aure yagani ko Allah zai bashi rabo ba, sai
abokan arziki da suma kai tsaye basu fito mishi
sun ce ya kamata ya kara aure ba. Dangin Abu
dai suna yi, har yanzun basu gaji da ce mata ta
rabu da shi ba ko Allah zai sa itama taga kwanta
a duniya, a cewar su ita din ta fito gidan da ake
haihuwa, dan su talatin da biyu ne a wajen
Lubna sufyan
Hausabook.com 6
mahaifin su, su tara a gurin mahaifiyar su, biyu
sun rasu.
Tana son mijin ta kamar yanda shima yake son
ta, rabuwa da junan sune karshen abinda zasuyi,
musamman akan matsala ta haihuwa da suka
san Allah ne yake bayarwa, sannan duk tarin
mutanen da suke musu surutu a ciki babu
wanda zai taimaka da komai wajen kula da
abinda zasu haifan. Amman Hammadi baya son
ya tauye Abu ko na rana daya
"Abu idan nine bana haihuwa fa?"
Murmushi tayi
"Idan kuma nice fa?"
Numfashi mai nauyin gaske Hammadi ya sauke
"Bana so in tauye ki, idan nine bana haihuwa, na
san kina son ki rike yaro ko yarinyar ki"
Gyara kwanciya tayi yanda zata fuskance shi
sosai duk da babu wadataccen haske cikin dakin
kasancewar dare ne, kuma sunyi kasa da fitilar
kwan da take ci a hankali
Lubna sufyan
Hausabook.com 7
"Kai ma kana so ka rike naka yaron ko yarinyar,
idan kaine baka haihuwa zamu raba kaddarar a
tare, zan zauna da kai har randa mutuwa zata
raba mu, ba zan taba gudun ka akan rashin
haihuwa ba, kai nake so, yaran da zamu samu
kari ne cikin kyautar samun ka. Amman zan so
ka kara aure ko Allah zai baka rabon da zamu
dinga kallo, ba sai yaran sun fito daga cikina ba,
in dai nakane zan kaunace su Hammadi"
Rabon da yaji hawaye sun cika idanuwan shi tun
da ya kama gawar mahaifiyar shi aka zirata
makwancin ta, sai kuma yau da kalaman Abu
suka taba wani abu a kasan zuciyar shi,
numfashi yake ja yana fitarwa a hankali har sai
da ya tabbatar da idan yayi magana muryar shi
ba zata fito da raunin da yake jiba tukunna ya
iya cewa
"Abu..."
Yana jira ta amsa sannan ya dora da
"Ke kadai kin isheni, idan Allah ya bamu rabo
zamuyi murna, idan bai bamu ba har abada kin
isheni"
Lubna sufyan
Hausabook.com 8
Daga ranar ne kuma suka toshe kunnuwan su
daga dukkan wani surutu da akeyi akan rashin
haihuwar su, kamar yanda suka fadane, sun ishi
junan su, samun yara cikon farin cikine a wajen
Abu da Hammadi ba wai farin cikin gabaki
dayan shi ba. A gefe daya kuma idanuwa da
kunnuwa Hammadi ya bude yana neman
yarinyar da zata dace da dan uwan shi, yarinyar
da ta fito daga gidan mutunci da tarbiya. Cikin
wannan neman ne akayi mishi zancen Dije yar
gidan Malam Hamisu. Yaji nauyin samun Malam
Hamisu da zancen daga farko saboda rashin
tabbas din da yake da shi akan halayen Datti.
Abu ce ta karfafe shi akan zuwan
"Kowa ka zo nemawa aure a wajena ba zan
hanaka ba Hammadi, in dai Dije ce kace ya zo ya
ganta, in ta mishi wallahi na baku"
Malam Hamisu ya fada bayan yaji bukatar
Hammadin, karamci ne da Hammadi yake jin
har abada ba zai manta da shi ba, kamar yanda
Malam Hamisu yake jin shima ba zai manta da
karamcin da Hammadin yayi mishi ba, yaran shi
hudune suke ci da sha a karkashin Hammadi,
Lubna sufyan
Hausabook.com 9
kuma hakan bai taba sa girmamawar da take
tsakanin su ta raunana ba, mahaifi Hammadi ya
dauki Malam Hamisu, yanzun kuma yana fatan
zumuncin su ya kara karfi sanadin auren nan.
Sai Datti ya sanyaya mishi gwiwa
"Ko aure zanyi bana son yar gidan Malam
Hamisu...ka sanni Hamma ni ba zan hada jiki da
bahaushiya ba"
Numfashi Hammadi ya sauke, ko a gonakibin
har tare da Datti suka je zagayen ma'aikatan su,
yafi tsangwamar hausawan, haka kawai ya
dauki tsana ya dora musu kamar wani yaiwa
rawa da yazo a bafullatani
"Mahaifiyar ta bafullatana ce Datti, kaje ka ganta
dan girman Allah karka sa inji kunya"
Kai Datti ya kada
"Ni dai da ka shawarce ni kafin kayi musu
magana"
Ya karasa yana kankance idanuwan shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 10
"Kayi hakuri, laifina ne da ban fara maka zancen
ba, na yarda. Ni dai ko sai daya kaje ka ganta,
idan batayi maka ba sai in basu hakuri"
Har cikin ran Datti bai nufi hanyar gidan su Dije
da niyyar auren ta ba, yaje ne saboda girman
Hammadi da yake gani da kuma kasancewar shi
mutum daya daya rage mishi a duniya da baya
iya jan magana da shi. Sai dai kaddara ta riga
fata, yana dora idanuwan shi akan Dije ya san
kaf kauyen Marake bashi da matar aure banda
ita, ba zaice ya yarda da wata soyayya ba kamar
yanda yake gani a tare da Hammadi da Abu,
amman a ranar ba zaman aure kawai ya hango a
tsakanin shi da Dije ba, har da yaran da
Hammadi bai samu ba. Yana ji a jikin shi sunan
gidan su da tsatson su ba zai kare daga kan shi
da Hammadi ba, zai samar musu dangin da suka
rasa.
Ba Marake bane asalin su, amman kauyen zai
zama asalin yaran da jikokin da zasu fito daga
su. Ranar ta zame musu fari shi da Dije, ranar
kuma ta share doguwar shimfidar da har ta
kaisu da auren da labarin shagalin shi ya zagaya
har kauyukan ketare, kudine Hammadi ya fitar
Lubna sufyan
Hausabook.com 11
kamar bai san ciwon su ba, haka dabbobin da ya
fitar aka yanka don shagalin biki zakayi mamaki
idan kaji cewa bafullatani ne na asali har hausar
shi bata fita sosai, saboda kowa yasan fulani,
yasan kaunar su ga dabbobin su.
*
Katanga ce kadai ta raba gidan Hammadi da na
Datti, daga farko zaman aure su Datti suka fara
kamar babu wanda zaiji kan su, zamane suka
fara irin wanda Hammadi da Abu sukeyi, sai
shakuwa mai karfi da ta shiga tsakanin Dije da
Abu, har tana saka Abu tunanin ashe a fadin
garin Marake za'a samu mai sanyin hali irin na
mijinta, mai hakuri da kawaici irin na shi. In dai
dabi'a ake dubawa Dije bata dace da Datti ba, ko
Abu ta dade bata jin maganar Dije saboda
kunyar da take da ita, sai a hankali da yake Abu
tana da shiga rai.
Suna cikin watanni na hudu da aure Dije ta fara
wani irin zazzabi mai zafin gaske, kafin wani
lokaci duk wata alama da zata nuna cewa ciki
take dauke da shi ta nuna. Murna a wajen Datti
ba'a magana, dan ya kasa boyewa ko a fuskar
Lubna sufyan
Hausabook.com 12
shi, dama can shi ba mai kunya bane ba, shisa
inda duk ya zauna zancen cikin Dije da abinda
zata haifa yake. Gabaki daya sai kulawar Dijen
ta koma wajen Abu da har girki ta dauke mata,
nan gidan su Abun take wuni, Datti na fita take
shiga sai gabanin Magriba tukunna, abinda duk
ta nuna tana son ci sai Abu ta samar mata shi.
Karamci irin na Abu yafi karfin kwatance,
addu'a kawai Dije takeyi mata itama ta samu
nata rabon.
Kwanci tashi babu wahala, cikin Dije na shiga
wata na tara gidan su suka nemi da ta koma dan
ta haihu a kuma kula da ita tunda haihuwar fari
ce, Abu ta so ta musa, ta so abar Dijen a wajenta
don har zuciyarta tana jin babu abinda ba zata
iyayi mata ba. Amman bata taba haihuwa ba,
tana bukatar kulawa a karkashin wanda suka
tabayi suka san komai, shisa ta bisu da fatan
alkhairi. Sati daya bayan komawarta gida, da
safiyar wata alhamis ta tashi da ciwon nakuda.
Sanin shakuwar dake tsakanin Dije da Abu yasa
aka tashi dan aike yaje ya sanar da Abu da
mayafinta a hannu lokacin da ta karasa.
Lubna sufyan
Hausabook.com 13
Kuka ta dingayi ganin irin azabar da Dijen take
sha, wasa-wasa har azahar. Datti ma yana kofar
gida yaron duk da zai shiga koya fito sai yayi
zaton labarin haihuwar ne, amman shiru. Nan
Hammadi ya same shi suka tsaya suna jiran ikon
Allah, wajen la'asar ta haifo yaron da ya kwala
kuka yana karade duka gidan, sanda aka fito
aka sanar da su Hammadi, Datti baisan lokacin
da yayi wani tsalle yana rungume dan uwan shi
cike da wani farin ciki da bai taba sanin akwai
irin shi a duniya ba.
Ruwan wanka aka dora, fuskar kowa ka kalla a
cikin gidan zaka ga farin ciki shimfide, farin
cikin da ba'a sauke ruwan wankan da aka dora
ba ya sauya. Yaro ya koma, Allah ya karbi
kyautar shi, sai gawa aka fito ma da Datti, bai
rike dan shi da rai ba. Bai san hawaye sun kwace
mishi ba sai da yaji zubowar su, ya kasa daina
kallon yaron da babu rabon ya rike shi da rai.
Ashe karyane baisan ciwon mutuwa ba sanda ya
rasa Inna, yanzun ne yake jin zuciyar shi kamar
ta rabu gida biyu a cikin kirjin shi. A ranar
alhamis ya binne dan shi na farko a bisa tsari na
shari'ar musulunci.
Lubna sufyan
Hausabook.com 14
Sai dai ko kadan daga shi har Dije basu hango
cewar bashi bane yaro na karshe da zai haska
musu farin ciki ya koma da shi ba, ba shi bane
karshen dan da zasu binne. A cikin shekaru
biyar da auren su haihuwar ta hudu yaran suna
komawa. Zuwa yanzun abin ya fara damunta,
bata taba furtawa ba amman abin yana damunta
fiye da yanda yake damun Datti, bashi yake
kwana ya tashi na tsayin watanni tara ba,
bakuma shi yake mata nakudar da mace yar
uwarta ce kawai zata misalta tarin k'alubalen da
yake cikin ta, amman sai yake ganin kamar ya
fita damuwa.
Kananun halayen shi tun satin ta na farko a
gidan ta fara kula da su, yana daga cikin
mutanen da suke da wahalar burgewa, yana da
fada, fadan da ta kasa sabawa da shi, da wahala
a shafe ranaku biyu baiyi mata akan wani dan
abu da bai taka kara ya karya ba har sai
zuciyarta ta sosu ta kasa tsaida hawayenta. Sai
dai banda kukan ko musayar yawu bata tabayi
da shi ba. Fadan shi abune mai saukin dauka a
wajen ta, haka saurin fushin shi bashi bane
Lubna sufyan
Hausabook.com 15
halayyar shi da tafi damun ta, sharrin da yake
fita daga bakin shi yafi alkhairin shi yawa.
Labari in zai bata duk na wani mugun abune da
ya sami wani, har tana rasa yanda yake samo
irin wannan labaran, kamar inya fita baya
neman yaji kowanne irin labari sai na wani abu
marar dadi daya sami wani a kauyen. Ranakun
da zai zo mata da labarin wani ya sami cigaba,
ya siyi dabbobi ko ya siyi gona, ko dai wani abu
na alkhairi, a muryar shi zaka fara jin rashin jin
dadin shi, a idanuwan shi zakaga hassadar da
take shimfide. Datti baya so wani ya kai shi,
dukiyar da yake da ita bayaso yaji wani ya samu
cigaba da kar ya kamo shi, karya ture sunan shi
daga layin manyan attajiran kauyen marake.
Har yau basu raba gadon su shi da Hammadi ba,
sai dai yanzun kowa akwai sashin dukiyar da
yake kula da ita, tunda aka raba, bangaren Datti
yanzun babu rabin ma'aikatan da, saboda ko
riga kasa da tafi tashi haske zai kore ka, baya so,
ko kadan baya son yaga wanda yake kasan shi
yana neman fin shi. Har sun gane, kullum cikin
boye wani cigaba da suka samu ko da ba'a
karkashin Dattin ba suke. Wannan halin na shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 16
shine abinda yafi komai damun Dije, yau ma
kamar kullum, sun gama cin abincin dare suna
zaune suna cin soyayyar gyadar da aka kawo
mata daga gidan su ya kalle ta yana fadin
"Ance dan gidan Musaji yayi ma wata ciki, tir da
irin wannan mugun hali. Kinsan kakan shi ma fa
haka naji labari yana haura gidaje lokacin
kuruciya"
Kai Dije ta jinjina
"Babu wanda yafi karfin kaddara..."
Gyadar da yake ci ya kara barawa ya murza yana
afawa a bakin shi
"Babu kaddara a cikin wannan abin Dije, mugun
haline kawai, yanzun sai ace miki ina da
kaddarar haura gidaje? Dan Allah ki rabani da
wannan zancen, Allah dai ya tsine ma zuri'a irin
ta Musaji, sun zama bala'i a gari"
Shiru tayi, ita batayi wani ilimin addini mai zurfi
ba, akwai makarantun allo a kauyen marake,
duk da basu da yawa. Ta samu na sallah, ta dai
san kaddara da girmanta, ta kuma fahimci kowa
da irin tashi, ta su Hammadi da Abu rashin
Lubna sufyan
Hausabook.com 17
haihuwa ce, ta su ita da Dattin yaran ne basa
zama, shisa tasan ta Musaji itace yara marassa
jin magana, ta ma yan gidan farin sani tunda
unguwar su daya. Sai dai shi Musajin mutumin
kirki ne, haka iyalan shi, dan duk juma'a ya kan
bada sadakar farar alawa, itama ta sha zuwa ta
karba. Ko da taji ta girmi zuwan haka zai ba
cikin yaran gidan su da kanje karba su kawo
mata.
Idan kaji wani mugun abu ya samu wani nemar
mishi sauki kakeyi kai kuma ka nemi tsari, haka
taji mahaifiyar ta nayi. Amman Datti bai san
wannan ba, ya daifi gane ya bisu da tsinuwa
saboda shi yana jin har ran shi ya wuce irin
wannan ta same shi. Suma din sun so ne shisa
hakan ta faru da su. Karshe ma mikewa tayi
saboda gyadar da taci taji tana daga mata
hankali, ko bayan ta kwanta haka taita fama da
tashin zuciya sai da tayi amai ta samu lafiya. Ta
alakanta hakan da dattin ciki, ko kadan bata
kawo yiwuwar tana da juna biyu ba, tunda
wannan karin ta dade bata samu ba.
A zuciyarta sai da ta dinga jin tsoro ko iya
rabonta ne ta binne. Har kuka tayi da ta gane
Lubna sufyan
Hausabook.com 18
tabbas tana dauke da wani cikin ne, cikin da
kowa ya bude baki bayan anga fitowar shi zaice
mata
"Dije Allah ya rabaki da dakon gawa"
Takan amsa da amin a cikin ranta, amman
zuciyarta ta gama karaya, Abu ce take tausarta
da kalamai masu sanyi. Ranar idi nakuda ta
kamata, nakuda mai sauki ba kamar ta baya ba,
cikin kasa da awa biyu ta haifo yaron ta namiji.
Yaron da taki karbar shi saboda tana ganin
kamar shima ba zai rayu ba, har akayi mishi
wanka, itama Abu ta taimaka mata tayi ta fito
sannan ta mika mata shi
"Ki karbi danki Dije, ki rike danki a hannun ki
yaji dumin ki"
Karbar shi tayi zuciyarta cike da tsoro, tana
kallon dogon hancin da zakaci karo da jarirai
hamsin baka samu irin shi ba, gashi da wani irin
hasken fata na ban mamaki
"Anya wannan zai zauna kuwa?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 19
Zancen da taso yi a zuciyarta ya subuce mata,
muryarta na fitowa a raunane. Dariyar da taji
Abu tayi ta sata gane a fili tayi maganar
"Zai zauna da yardar Allah"
Kyawun shine ta ga har yayi yawa shisa take
tunanin kamar ba mai zama bane ba. Ta kuma
ga wannan tsoron a cikin idanuwan Datti kamar
ta kalli mudubi, yanda batayi baccin kirkin ba
haka Datti, gani yake sakon farko da zai riske
shi da safe shine cewar yaron ya koma. Yini ya
dinga wucewa yana hada dararen da suke
wayewa cikin safiya har sati ya zagayo yaro
yana nan. Shanuwa Datti yasa aka yanka saboda
murna. Yaro yaci suna Isiya wanda shine asalin
sunan Hammadi, har kuka sai da yayi saboda jin
dadin karamcin da dan uwan na shi yayi mishi,
suka kuma sakaya da kiran shi Julde
kasancewar an haife shi ranar idi.
Sun rike shi da tunanin zai zama cikon garin
cikin su
A cikin su babu wanda ya hango cewar Julde ne
kaddarar su.
Lubna sufyan
Hausabook.com 20
Yau da gobe abin tsoro, ba a yanda ranaku suke
karewa zuwa daren da yake wayewa da safiya
ba, ba kuma a yanda kowacce rana take kara
kusanta dan Adam da kabari ba, rashin tabbas
din da yake cikin yau da gobe yafi komai tsorata
Dije da dan ta ya makalawa Daada yana sa
sunan nata fara bacewa a bakunan mutane. Ko
Julde ta kalla sai ta kara sallamawa da lamarin
duniya. Sai taga kamar jiya ne Abu ta saka mata
shi a hannun ta, amman yanzun gashi nan da
shekaru uku cur a duniya. Ko wanka tayi mishi
ta shirya shi sai taita kallon shi.
Allah me kyauta da kari, ko a mafarki bata taba
hango zata haifi kyakkyawan yaro kamar shi ba,
bata da muni, amman babu wanda zai sakata a
layin kyawawa, hasken fatar dai zatace na Datti
ne da nata, amman na Julde kalar shi daban ne,
ga fatar shi a murje irin ta yan binni da take gani
idan sun kawo ziyara kauyen nasu. Ga wata irin
sumar fulani da take kan Julden, a nannade irin
ta Datti, kuma kan a cike yake har kusan gaban
goshin shi. Misalta kaunar da take ma tilon dan
nata duk da irin kunya ta dan fari ba zata
Lubna sufyan
Hausabook.com 21
misaltu ba. Dan takan kasa yin kawaici a lokutta
da dama a gaban mutane, ko idan taje gidan su.
Ko juma'ar da ta fita da taje, kiriniya irin ta yara
yana wasa yayi tuntube ya fadi, bata san ta mike
ba sai da taji babbar yayar su wato Hanne tana
salallami
"Dije...yau naga abin da yafi zare tsayi ni
Hanne... To je ki dauke shi, ni bari in zauna"
Tukunna ta koma ta zauna a kunyace, dan ma ta
fara sabawa da surutun da akeyi mata akan
yanda bata iya boye son da take masa, taya zata
fara boyewa bayan tayi bari bayan samun shi?
Idan kuma shine kwai daya da take da rabon
gani a duniya fa? Ba zata bata lokacin da ta samu
tare da shi wajen nuna kunyar dan fari taki jan
shi a jikinta ba. To na Datti ma ya zarta na kowa,
halayen shi babu wanda bata gama sani ba zuwa
yanzun, don yau da gobe tafi karfin komai. Abin
fada da bana fada ba a wajen Datti duka dayane,
baka kuma isa kace zaka fahimtar da shi kan
abinda ya rigada ya raya ma zuciyar shi ba.
Tun tana kuka harta fara dakewa kan wasu
lamurran na shi, tunda ci da suttura Datti fitar
Lubna sufyan
Hausabook.com 22
da kudi yake yana mata kamar bai san ciwon su
ba. Haka yan uwanta baya gajiya da hidimta
musu, kawai dai hakan bai taba tserar da su
daga tijarar shi idan sun shiga sabgogin shi ba.
Yanda ta fahimci halin shi kusan suma tana
tunanin sun fahimta, ko kuma alherin da yake
musu ne ya kashe bakunan su, tunda in dai zaka
kaskantar da kai ka nuna ma Datti girmamawar
da yake so to zaka more shi, kuskuren dai da
zaka yi shine kayi wani abu da zai nuna alamar
cewa kana so ka fishi, ko da kuwa takalmi ne ka
saka da yafi na shi haske a fuskar shi zaka fara
ganin yanda baiji dadi ba, kafin alkhairin da
yake giftawa a tsakanin ku ya dauke.
Duk wasu hanyoyin samun sabani a tsakanin ta
da Datti ta san su, tana kokarin kiyaye su,
hanyar da bata taba hangowa ba shine Julde.
Bata taba hasaso cewa zasu dinga samun sabani
akan tilon dan nasu ba. Tun yana jinjiri daya
bude baki yasa kuka zai rufeta da fada kamar
tasan dalilin kukan shi ko ma itace dalilin
gabaki daya. Haka cikin dare zai ce sai ta goya
shi ko zaiyi shiru. A gaban Datti idan har Julde
ya saka kuka ranta saiya baci, barna ta yara idan
Lubna sufyan
Hausabook.com 23
yayi bata da damar tsawatar mishi saboda Datti
zai rufeta da fada kamar zai daketa. Na rana
daya bata taba furtama wani yanda fadan Datti
yake tsaya mata a rai ba
"Adda Abu bana so Julde ya taso a sangarce,
bana so ya taso bai san meye kuskure ba"
Ta ce ma Abu cikin sanyi murya wani yammaci
ta shiga gidan
"Amman Baban shi baya so, kina ganin bai kai
shekarun da zan fara tsawatar mishi ba?"
Ta karasa maganar tana kallon Abu da ta bata
dukkan hankalin ta
"Shi icce tun yana danye ake lankwasa shi ai,
banajin akwai wani kayadadden lokaci da yaro
zai kai kafin a fara nuna mishi yayi kuskure..."
Kai Dije ta jinjina
"Tunani na dana Baban shi sunyi hannun riga a
wannan bigiren, kukan rashin dalili idan Julde
ya saka sai kin dauka lefina
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 27