gefe a dame shi a kitse sai ya yi matuqar kyau in ke mai santsin gashi ce ma zakiga har sheqi yake da dare ake wannan kitson bayan kin gama wa oga kwalliya, ma'anar yin wannan kitson na farko dai zaki yi bacci ba tare da kanki ya yi irin buyaya ɗin nan ba ki yi muni,da safe zaki tashi kan ki tsaf da shi bai barbaje ba, sannan kuma in ma kun samu kusantar juna da me gida kin yi wanka kanki ba zai na lalacewa ba nan da nan ki ji mata suna cewa kai yasha ruwa gashi ya na zubewa, akwai fa'ida sosai akan yin hakan wanda sai kin fara zaki gano su da kan ki.
Da sauri take yin komai ba tare da son jiki ba,dan ba ta son sai ya dawo ne zata yi wadannan abubuwan, ya na dawo wa daga masjid ya tsaya wajen Innar mu su gaisa, kamar kullum riqe shi ta yi da surutai na ba gaira ba dalili, daga baya ne ta fara tura masa saqon dake ranta cikin dabara irin ta masu son qulla sharri,
" Allah sarki Juwairah yarinyar nan akwai hakuri, kaga fa yanzu wata na wajen shida kenan da auren ku amma ba wani labari,gashi duk qawayen ta sun haihu ma su,ita ko da b'atan wata bata taɓa yi ba ka ga sam bata damu ba, ko dake dama yaran zamani ai ku ba ruwan ku, mu ne dake son yan jikoki mu za mu damu, waya sani ma ko maganin hana haihuwa take sha"
Wani irin faduwar gaba ne ya samu Jabeer ido ya zaro waje yace,
" Haba Innar mu Juwairan nawa take d zata yi wannan tinanin? Kuma har ta aikata hakan ma? Inaaaa sam ba zata yi haka ba kima daina wannan tinanin dan Allah, kuma da kk zancen sa'o'in ta Innar mu Nafeesa ma fa sa'ar ta ce ita kinga ai har yanzu ma bata yi aure ba, in da zaki gane komai nufi ne na Allah kenan"
Da jin wadannan kalaman daga bakin Jabeer sai Innarmu ta ji kamar ya watsa mata wuta, bala'i ta fara yi kamar ta ari baki,cikin masifa ta ce,
" Inyeeeee lallai ne Jabeeru ka nuna min mata tafi 'yar uwar ka ko? Har qanwar ka zaka duba ka yi wa gorin aure? To bari na faɗa maka abin da nake boye maka, nifa na fara gajiya da wannan yarinyar, tin da ka aureta ka daina bamu lokacin ka, ka daina zama ai hira kamar ta da da kai, sannan gaba ɗaya soyayyar ka da kulawar ka ta koma wajen ta, akan me?"
" Akan shi ne mijin ta, kuma hakan da yake shine yake nuna ya haifu ɗan sunna daga iyayen shi,yanzu dan Allah ba ki ji kunya ba? Kike haɗa kan ki da surukar ki?sannan 'Yar ki ta wani bangaren? Habaaaa Hansai, wace irin rayuwa kk daukar wa kan ki yanzu, abinda ba halayyar ki ba kina neman shaid'an ya maki huɗuba ki fara yi, to bari na faɗa maki abinda mata kan ku yake toshewa akai, kowacce mace dangin miji ce, kuma uwar miji ce wataran in ranta ya kai, dan haka in ki kai wa matar dan ki adalci, kema sai wata ta yi wa taki 'yar adalci, in kk kyautata wa matar wanki ko matar qanin ki, kema naki qannen mijin da matan yayun sa zasu tausaya maki su miki adalci, in kuma duk kin kiyaye amma ana maki abinda bai dace ba, to ki sani kowanne dan Adam akwai jarabawar shi, wataqila taki anan take, sai ku hakuri ki yi qoqari kuma ki cinye jarabawar taki, dan haka in kk kula, tin da Jabeeru ya yi aure kulawar da na ke ba ki ta qaru, ba dan komai ba sai dan kula da na yi kin kai idon ki gidan matar dan ki, ki gyara hali ko kin samu rabauta a lahira, baki tafi da haqqin kowa ba, haihuwa ta Allah ce, ko bata haihuwa haka yaga zai zauna da ita ke baki isa ki ce dan me ba"
Baba Balarabe kenan ya ke yi wa Innarmu faɗa akan abinda take yi mara kyau, wanda ya dad'e a tsaye yana jin maganganun Innar mu, wata irin nadama da kunya ce ta kama ta nan take cikin jin nauyi ta furta,
" Malam ka yi hakuri, Jabeeru ka yafe min sharrin zuciya da shaid'an ne, baqin ciki na da tin da ta zo komai namu ya ja baya, ga shi kana nuna mata tsantsar so, idona ya rufe akan hakan na manta nima nawa mijin yana iya qoqarin shi akaina, ku yafen ba zan qara ba"
Nan ta zayyano yan sace2n da tai ta yi wa Juwairah dan ta haɗa su faɗa da Jabeer amma sai ta ji shiru, sakamakon iya zaman duniya da Juwairah ke da shi da ta kula hakan ta faru zata san dabarar da ta yi ta bashi hakuri, da jikin ta da kalaman ta,
" Babu komai Innarmu ya wuce ke uwa ce a wajen ta, da bata ɗauke ki a uwa ba uwar miji ta ɗauke ki da ita kanta zaman sai ya mata wuya amma tasan ko da uwa da uba ana sab'awa fiye da haka ma a kuma ci gaba da zama, dan haka na san ba ta qullace ki ba, jiya kwana ta yi ma ba lafiya, asibiti zamu je yanzu ma ni take jira na san"
" Subhanallahi"
Suka hada baki dika ukun har da Nafeesa suka fada,Innar mu ce ta furta,
"Meke damun ta?"
" Da ciwon jiki ta kwana ga zazzabi da ciwon kai, ciwon mara da yawan kasala, dan jiya wani irin bacci ma ta dinga yi"
Murmushi Innar mu ta yi sosai sannan ta ce,
" Ikon Allah ai ya kamata a kaita ta ga likita bokan turai a fada mana wata nawa ne, na fara tanadin kayan kwalliya dan da alama bana zan yi ango nima, in kishiya ce na samu na gyaran daki,kar ta zo ta fini a Wajen Malam"
"Innar mu me kk nufi da hakan?"
Nafeesah ta yi tambayar cikin mamaki, Jabeer kuma a ranshi cewa yake yi,
'Allahumma ameen Allah ka amsa ka sa hasashen Innarmu ya zama gaskiya'
A zahiri Kuma ya ce
" Innar mu bari na wuce naga ko ta shirya mu tafi kar mu makara"
" To Allah ya qara afuwa"
Tashi ya yi baki a washe kamar gonar audiga ya isa sashen nasu, qamshin da ya ji ne ya qara kwantar masa da hankali da nutsuwa tare da qaunar matar tashi da yake matuqar so, sallama ya yi ta amsa cikin muryar da ke tafiya da hankalin shi,durqusawa ta yi ta gaida shi, ya amsa tare da jawo ta jikin shi, d'aga kanta ya yi yana kallo, wata riga ta saka shara2 ko ina ana hangowa a jikin ta, sai wando guntu rigar bata gama rufe mata cibiya ba , ta yi parking gashin ta a tsakiyar kan ta, fuskar ta ta yi fayau kyaunta ya qara fitowa, the more yana kallon ta the more yana qara ganin kyaunta, bata cikawa fuskar ta makeup ba, iyakar ta powder da lipstick, sai tirare da ta fesa ta shafa mai, zame rigar ya yi daga kafad'ar ta yana shinshina wuyan ta, maida ita ya yi baya ya tsaida ita ya na kallon ta,cikin shagwab'a Juwairiyyah ta ce,
" Babe ni dai bana son wannan kallon da kk man ya yi yawa, tin da ka shigo kk ta kallona"
Ta wani sake narkewa a jikin shi tana wani dan zame wa shi kuma da sauri ya janyo ta, gaba daya ta gama rikita shi, daukar ta ya yi cak suka yi daki, ban qara sanin me ake ba sai da naje na wajen Innarmu na sha kokon safe na dawo a gadon na hango su suna manne da juna, Jabeer ne ya ce,
" My princess , jiya kin manta yau munyi zan kai ki asibiti ne? Gaba daya naga yanda jikin ki yake jiya da yamma yau kin tashi garau da ke" Eh My dear, kaga in banda da asuba dana tashi na ji kaina na ɗan ciwo kadan, sai da na zo brush warin toothpast din ya sani amai, tin da na yi aman nan na ji daɗi daga nan ban sake jin komai ba, ni fa Ina jin ma na warke ba sai mun je ba ma"
" A'a ba haka za ai ba, ya kamata mu je asibiti muji me ke saka motsin da kk ji ko ya daina"
"Ah ah ya na yi har yanzu"
Jabeer ne ya shafa cikin nata da tausayawa, nan da nan idon ta ya ciko da kwalla ta ce,
" Ɗazu ma fa sai da ya min, ga tsoro da yake ban in ya motsa din, sai naji kamar wani abu ne a ciki"
Ta qarasa tana mai sakin kuka
" Yi shiru my princess bari kuka,ba komai inshaa Allahu sai alkairi, u don't have to worry ur self babe, koma meye zamu samu maganin shi tashi muje mu yi wanka mu shirya muje"
Tashi ya fara yi sannan ya miqa mata hannu ta kama, a hankali ta miqe tsaye sai yanzu ya qara ganin qirman da qirjin ta yayi, ga cikin ta ya dan tasa ta qasa, ta yi wani fari sosai, kamata ya yi ya zura mata doguwar riga da dan hijab din da take zuwa wanka, tinda gidan akwai suruka duk da ba sashen su ɗaya ba dai amma Juwairiyyah na gudun kar watarana a yi kicibus,sai shima ya zura tashi riyar sannan ya fara fita waje ya rufe qofar su,daga nan suka shiga wankan a tare bayan sun gama ne suka dawo suka shirya za su tafi asibitin ,kafin su fita saida ta biya wajen Innar mu ta gaida su sannan ta tashi zasu wuce,ta ji Innarmu na fad'in,
" Juwaireren Mama ki yafe wa Innar ki laifukan da ta yi miki domin Allah, sharrin shaid'an ne ya shige ni da son zuciya, amma in Allah ya yarda ya wuce ba zan sake yi maki duk abinda na yi a baya ba"
kwallar farin ciki ce ta fito wa Juwairiyyah ta godewa Allah da ya kawo mata komai da sauqi kuma cikin gaggawa,cikin murmushi ta cewa Innarmu,
" Haba Innar mu ai ba komai, ni fa 'yar ki ce, ke uwa ta ce, ban dauki hakan a komai ba face ma gani nake nice bana kyautata maki yanda ya kamata, nima ki yafe min,
Baba balarabe na d'aki yana jin dadin kasancewar Juwairah a matsayin surukar shi, yarinyar dan uwan shi na da hankali da tarbiyya mai kyau,ta samu tarbiyyar a wajen iyaye na gari.
Sun isa asibiti suka tarar mutane sun zo an cika suma dole suka bi layi kamar kowa,sanda likita ya kira ta sai aka bata gwajin jini sannan aka yi mata scanning dan ta matasa ta ce abu na motsi dole a duba mata, a gwajin farko aka gano tana dauke da cikin wata hudu da sati biyu, zaro idanu take kamar mara gaskiy, ga wata iriyar da farin ciki da suka kama ta, kunyar jabeer da tunanin ya iyayen ta da surukan ta za su ɗauki wannan labarin duk sun ishe ta ta rasa ya zata yi, janyo hijab din ta ta yi ta sunne kan ta a ciki tana dariya qasa qasa, Jabeer ta gani ya tashi ya yi sujjadar godewa Allah yana kwallar murna, itama a cikin ranta take maimaita
' Alhamdu lilLAAHi ala kulli halin, hamdan katherran ya rahman,'
Murna take yi sosai ta ji hannun jabeer a jikin ta ya ja ta jikin shi, hada fuskar su ya yi waje daya suna shaqar nunfashi junan su,cikin murya mai ɗauke da amon farin ciki Jabeer ya ce,
" Juwaireren mama kin ga ikon Allah akan mu ko,Allah ya yi mana kyauta mai daɗi da sanya farin ciki ba zato babu tsammani"
D'aga masa kai kawai take tana murmushi, Dr. ne ya ce,
"To Lovey-Dovey sai a tsaya a saurare ni kuma in an je gida an qarasa murnar a can, ina da wasu masu jira na a waje"
Shi kan shi likitan cikin fara'a da jin sun burge shi yake maganar, shawarwarin da zasu taimaka masu wajen kula da cikin da lafiyar ta ya basu, sannan ya rubuta magani inda yace su je su nuna takardar kawai za a basu kyauta ne,godiya suka yi masa mai tarin yawa sika fita, Jabeer ne ya sarqafe hannayen su waje ɗaya ya na jin son Juwairiyyah na qara shiga zuciyar shi, dan ji yake kamar ya dauke ta karta wahala da tafiya, kula da hakan da ya yi ne yasa ta tsaida su a wani wajen da ba mutane sosai tace,
" Babe Dan Allah zan iya roqon ka wata alfarma?"
Cikin zumud'i Jabeer ya ce,
" Anything for u my love,just say it, inshaa Allahu in baifi qarfina ba i will do it for u"
Murmushi ta yi ta sunkuyar da kai qasa sannan ta ce,
" Yah pls don't tell anyone that i am pregnant plssss"
Ta faɗa tare da qara damqe hannayen su waje ɗaya,
" But why, abun murna ne fa ya same mu da ahalin mu baki ɗaya? Don't u want them to be happy for us, and must importantly to pray for us, and our baby"
Ya qarasa maganar shi cikin rad'a,
" Eh Ina so mana sosai amma ka fahimce ni, kawai ni kunya nake ji, yanzu fa kowa sai ya san me na yi na samu cikin nan har fa Babana"
Kiran Baban ta da ta yi sai ya sa ta sake jin wata kunya ta qara kamata kamar yama ji labarin ta na da cikin, dariya Jabeer yake yi sosai yana riqe ciki,cikin dariyar ya ce,
"Amma dai gaskiya baki da wayo na kula, to bari kiji tin kan a kawo ki aka san in an maki aure zamu yi abin da zaki samu cikin,me yasa ake hana 'yammata biye wa samari kafin aure? Ai saboda gudun kar su samu zunubi sannan kuma kar su samu ciki kafin aure su haifi dan shege, come on wuce ni mu tafi gida rana na dukar min ke"
Maqale kafad'a ta yi tana turo baki,
"Yanzu menene kuma?"
" Yah Yunwa nake ji sosaiii"
"Amma dai naga bamu jima da cin abinci ba muka fito ko?"
"Eh na sani, ni dai ina jin yunwaaa"
Yatsina fuska take kamar in bata ci ba wani abu zai same ta ne,
"Ok to yanzu me kk so?"
" Yah ga me agwaluma can ita nake so, kuma ina son waccan zogalen dafaffe"
"Ikon Allah, ashe kwadayin da kk ta min kwanaki babyn mu ne ke saka ki"
"Yah ni dai agwaluma kuma dan Allah Yah ka taho mun da gyad'a mai gishiri, ka had'o min da rake, yauwa ka siyo agwalumar mai yawa fa",
Gani ta yi ya saki baki ya na kallo ikon Allah, daga baya ya fashe da dariya,kawai sai ta saka masa kukan shagwaba,da sauri ya yi maza ya kama bakin shi alamar yayi shiru, sannan ya ce,
" Yi hakuri ba zan sake ba kin ga a titi muke duk da katangar nan ta kare mu kinga masu agwalumar zasu iya maki dariya"
Narke fuska ta yi sannan ta ce,
" Oh ni Juwairah yau naa ga tsokana da ranar Allah dan Allah ka yi sauri"
"Auuuuu kin fi son a tsokane ki da dare dama? Ohhh to kar ki damu wannan ma ba a barmu a baya ba ai bari mu koma gida"
Da sauri ya yi wajen masu agwaluma yana dariya dan ganin yanda take banka masa harara ,zura hannun ta ta yi a riga tana shafa cikin ta dayake a lafe kamar ba komai sai ɗan tudu da ya yi ta qasan marar ta, amma a haka tana jin motsawar shi kadan kadan,
" Ikon Rahman Ar-raheem kenan,wato wai ni Juwairah ke dauke da ciki ban sani ba, Allah na gode maka, kasa duk abin da zan haifa ya zama musulmi mumini salihi, Allah ka sani na bi dukkan yanda Annabin ka ya tsara mana don samun 'ya'ya na gari, tin kafin aure na har yanzu da ka ban wannan arziqi, Allah ka sa su zama wadan da muslunci da musulmai zasu yi alfahari da amfanuwa da haihuwar su, Allah na gode maka ka ba wadan da basu da shi, ka sauqaqa min wajen haihuwa"
Hannun shi yasaka a gaban fuskar ta ya ce,
" Shin me Juwaireren mama take tunani haka? Gani na dawo ina tsaye baki ji ina maki magana ba, wato har zaki fara manta ni ko saboda kin samu baby"
Ya fada yana shagwabe baki kamar yanda take yi,
" Ba komai muje gida na yi na sha abunnan yunwa ta qaruwa take yi"
Dariya ya yi suka kama hanyar fita suka samu abin hawa sai gida, lokacin da yake fadawa innarmu Juwairiyyah na da cikin gudu ta saka ta yi bangaren su tana dariya, kowa murna yake a gidan kamar me, labari nan danan ya bazu a dangi Juwairah na dauke da cikin wata hudu da sati biyu, kowa na murna da saka albarka, jin wannan labarin da Goggo Sarai ta yi ya daga mata hankali, domin tunanin ta ya tafi akan dama yaran ta ne suka sama mata jika, ko dan samun wani kaso na dukiyoyin surukan nata,nan take tinanin Salma ya faɗo mata a rai, wayar ta ta d'akko ta yi ta zabga kira ana mata turanci, hankalin ta ya tashi sosai musamman da ba gane ne ake faɗa take yi ba,mayafi ta yafa ta leqa ta kira Baban su, ta bashi ya ji me ake faɗa, ce mata ya yi
"Wai an ce layin baya aiki yanzu,"
"Wai ni wa kake kira ne malam Salma fa na ce ka kira min"
"Ita dai ki ka kawo waya na kira kuma aka ce No ta ta daina aiki,"
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una me yake faruwa ne? Malam wannan Yarinyar Salma so take ta kashe ni da tashin hankali da damuwa, ka na gani dai duk 'Yan uwan ta sun yi waya gida an ji daga wajen su amma ita shiru yau wata kusan bakwai, ga wannan mummunan labarin da ya iske ni na samun cikin wannan kodadiyar"
"Mummunan labari kuma, a wajen wa kenan? A wajen ki dai amma ko? Hmmmm Sarauta kenan a gabana ki ke son ki ciwa 'yata fuska wai kodaddiyar 'ya na gode, Allah zai raba su lafiya, ita kuma Salma Allah ya sa ki same ta a wayar, in kun yi magana kin sanar da ni"
Ya na gama maganar shi ya yi shigewar shi cikin gidan, wayar suwaiba ta kira ,tana dauka itama tambayar ta ta yi tace bata ji daga wajen Salma ba ko ta kira iya Goggon sun gaisa? Nan dai Goggo Sarai ke sanar da Suwaiba abinda ke faruwa.
Saudat ma da ta kira ta amsa ɗaya ta bata da ta suwaiba,daga qarshe dai suka haɗu suka kwantar mata da hankali akan cewa ta yu ma sun fita qasar waje ne da mijin ta honeymoon shiyasa ba a samu ta,wani farin ciki ne ya maye damuwar ta suka ci gaba da hirar su wadda rabi da kwatan ta ta yanda suke cikin rayuwar jin daɗi da hutu ne a Abujan ita kuma ta na sukar su Mama Balki da Juwaireren ta.
**************************
Salma kuwa wadda yaran Talle suka mayar mata da suna Salame ana can qauye jikin ta qaura ya yi la'asar, ba kowa ne da yasan ta a da ba zai iya gane ta ba a yanzu, duk ta kode ta jeme ta rame, wahala daga ta gama wannan ta faɗa wannan,har kuma wannan lokacin Talle bai sake waiwayar su ba.
****************************
Watan karb'ar jini a wajen su Suwaiba ya zagayo,Oga Zaks ya buqaci ko a kai su, ya qara sa musu albarka irin tashi ko kuma akai jinin su kamar yanda qungiya ta bukata zaɓi ya rage ya na su Alhaji Salihu......
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Dan Allah masu tambaya daga farko ko wasu pages da ba su karanta ba ku yi haƙuri a gama dika a had'a document sai ku karanta, zan yi qoqari na yi saurin gama editing ɗin kamar yanda na yi na sauran,na gode*
page 13:
Alhj Salihu da Alhj Kalla Mazajen su suwaiba da Saudat ne ke zaune a wani wajen shan iska da suka tanada na musamman dan tattaunawar sirri,bayan doguwar shawara da neman mafita ne suka samu nasarar tsayar da hanya ɗaya da za su samu jinin su suwaiban da qungiyar asirin su ke da buqata a duk ƙarshen wata cikin sauqi,bayan samun mafita da nasara antattaunawar da suka yi sai suka bushe da dariy a tare suka tafa tare da furta kalmar
" 'YAN ABUJA"
Tashi suka yi suka shige motocin su masu gadin wajen shaqatawar nasu suka buɗe gate su ka hau daga masu hannu tare da yi masu addu'a da fatan alkhairi, direct clube suka wuce kamar kullum,sai dai yau basu wani dad'e ba dan kuwa sha ɗayan dare suka dawo gida.
Cikin kwalliya ta alfarma kowannen su ya tadda iyalin shi, an sha kayan ado masu tsada, fatar nan har wani sheqi take sabida jin daɗi da hutu.
Kowaccen su kamar abin had'in baki tashi ta yi ta nufi mijin ta domin yi masa barka da dawowa, dan kuwa qorafi ba nasu bane yanzu tsoro suke ji kar su sha jibga a banza.
Bayan sun gama kulawa da Mazan nasu an ci an sha an yi wanka sun zauna su na hutawa a parlour suwaiba ta hau wata karairaya ta zauna a gefen Alhaj Salihu kamar za ta shiga cikin shi, cike da shagwab'a ta fara gabatar da uzurin ta a kunnen shi kamar yanda Goggo sarai ta koya mata,
" Mine "
"Na'am"
Sake mannewa ta yi a jiki shi sannan ta ce,
" Dama cewa na yi ko zamu je asibiti a duba mu ne ni da kai saboda a ga ko lafiyar mu qalaou kuwa har yanzu shiru ba ciki ba komai, dan ni fa har period na dena yia zatona ma ciki ne amma kuma gaskiya ban ga wata alama ba ni dai ina jin tsoro dan Allah za ka kai ni asibiti mu ga likitan? Ko ka san yanzu haka qanwar mu Juwairiyyah da aka yi bikin mu tare ta na da ciki,hakan zai zame mana abin gori mu da mahaifiyar mu ace mu uku babu mai ciki har yanzu"
Wani wawan mari ya antaya mata, ya hankada ta qasa sai da ta kifa,cikin ɓacin rai ya kalle ta ya na nuna ta da yatsa ya ce
" Dan uwarki ni zaki mayar qaramin mutum qaramin yaro? Wanda bai san me yake yi ba? Ohh wato ki haihu na samu magaji ko? Ko kuma ki kashe ni ki karɓe dukiya ta ko? To bari kiji wani abu, wannan dukiyar daga karuwai sai masu saida giya su zasu more ta in dai ba Zaki kwantar da hankali ki ci arziqi ki barshi a mazaunin shi ba,ni babu tsarin yara a rayuwar nan tawa, ban sani ba ko a gaba, amma a yanzu kam ban da wannan burin da kwadayin yaran da ke zaki sani neman haihuwa kamar ni an faɗa maki Banda ra'ayin kai na sai naki,"
Cikin kuka suwaiba ta rarrafa ta kama hannun shi ta ce,
" Dan Allah ka saurare ni ka kuma fahimce ni"
kafin ta qara magana kwakkwara ya rufe ta da mugun duka ko ta ina tare da fad'in ,
" Ke kin zama jaka ko? Baki yarda ki daina sa in sa da ni ba ko, ina faɗa kina faɗa kamar ki na magana da sa'an ki, yau kuwa Zaki ji a jikin ki sai soyayyar yara ta fita a zuciyar ki har abada",
Wayar charging phone ɗin shi ya ciro ya dinga zabga mata, tin tana kuka ta na bashi haƙuri karshe ma sai faɗuwa ta yi ta rufe idon ta a wajen ta daina motsawa, a haka ya samu damar ida qudirin shi na yi mata allurar bacci, ya debi jinin ta dan mugunta har leda uku, yana gamawa ya yi ma mijin Saudat magana ta waya dan sanin halin da suke ciki, mijin saudat tambayar shi ya yi ko lafiya ya ji ya na haki, nan take ya bashi amsa da cewar,
"Sai da jakar taci duka tukunna, wai ni zata yi wa zancen haihuwa"
" Ale Salihu ka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 25