ta dakko wata rigar ta doguwa ta atampa ,rigar na da fadi ta qasa ta sama kuma an dan tsuke ta da dogon hannu ,jujjuya rigar ta yi ta kara ta a jikin ta kafin daga baya cikin murmushi ta saka rigar,yanda rigar ta zauna mata abin kallo ne domin Juwairah akwai shape mai kyau, gyara gashin kanta ta yi da kyar dan yawan shi da tsahon shi ke wahal da ita wajen kula da shi, bayan ta gama ne ta kafa dauri me kyau, ta samu tiraren ta da Mama ta bata ta fesa, tana gamawa ta je wajen Maman ta ta na wani yanga ta na nuna mata yau fa Allah ya yarda 'yar ta ta yi kwalliya, ta duqa zata dau Ammar, cikin tsokana irin na tsakanin 'ya da uwar da suka shaqu da juna Mama ta ce,
" A'a kaga Juwairere saraunuyar mata,Juwairere diyar Mamanta gaye ne aka sha haka yau, to ko dai suruki na ne zai zo?"
Cike da shagwaba da nuna jin kunyar Maman nata Juwairiyyah ta ce,
"Haba Mama wanne irin suruki kuma,kawai dai na yi sha'awar na yi kwalliya ne yau, kuma ni mama na ce maki bana son Juwairere Allah dariya qawayena suke min in suka zo sukaji kina fada musamman Nafeesa"
Cikin 'yar dariya Mama ta ce,
"To in banda abinki Nafi ai qanwar ki ce kin fa bata kwana bakwai masu kyau dan haka data tsokane ki sai ki yi murmushi irin na manyan yayu saboda yarinta ce ba wani abu ba"
Dariya suka saka a tare, sosai suke dariya abun su gwanin sha'awa,Goggo Sarai ce ta ja dogon tsaki ta ci gaba da aikin ta,a tunanin ta Mama Balkin na tsokanar ta ne kawai su na yi ne dan su bata haushi , ba tare da sun ji sallama ba Juwairiyyah ta ji an kama hancin ta, muryar da ta ke tsakanin buri da muradin ji ce ta ce mata,
"Wannan dariyar taku Mama ba zata bari kuji komai ba , musamman wannan Juwaireren da ta buɗe wannan qaramin bakin nata take cika wa mutane gida da qara da wata Muryar ta se kace ta kanari"
Tsalle ta soma yi na murnar ganin Yayan nata sannan ta kama hannayen shi dika biyun a nata ta na kallon kyakkyawar fuskar shi da ta yi kewa ta ce,
" Yayana, wayyo Yayana kaine da gaske? I missed u so much Yayana, yaushe ka dawo? "
" Oh Juwaiiraah ko zama bai yi ba fa wannan zumud'i da tambayoyi a bari ya ɗan zauna ya huta mana"
"Mama rabu da ita nima ba qaramin Missing din Juwairere na na yi ba, ban ga laifin ta ba dan ta nuna murnar ta na gani na"
Murmushi Mama ta yi sannan ta fita d'ebo masa ɗan ruwa ya sha dan gidan haka suka tashi ko na karyawa ba a miqo masu ba, jawo ta ya yi kusa da shi sannan ya ce,
" Amma da Juwairere kin san na hana kwalliya ko?what if wani ya zo ya gan min kwalliyar mata ta? Ko a aike ki a haka kowa ya kallen min ke? A gaskiya ni dai bana so, ba wannan ba ma dai yanzu ai ta qare tinda ga angon ki nan ya gani kuma ya yaba kwalliya ta yi dari bisa dari"
Duqar da kan ta ta yi qasa wata iriyar murna da farin ciki na ratsa ta tunda ta ji ya kira kanshi angon ta, ga hannun ta da yake murzawa a hankali, karɓe hannun ta ta yi ta canja mazauni tana turo baki, ita a dole fushi ta fara,Mama ce ta shigo ɗauke da kofi a hannun ta ta aje masa a gaban shi ta samu wajen zama,
" Mama kin ga wannan yar rigimar ta turo baki, lallai akwai magana a cikin shi"
" A'a ni kam ba ruwana ina gefe ba a shiga tsakanin ku ai ku se mutum ya ji kunya"
komawa ya yi kusa da ita ya d'ago kanta ya na kallon kyakkyawar fuskar ta da ya ke jin zai iya shekara ya na kallon ta ba tare da ya gaji ba,
"Juwairere na me ya faru?"
Cikin 'yar kwallar da ta daddage ta taro a idon ta da ya sha kwalli ta ce,
"To ba ga shi nan ba wai Juwairere, ni Allah bana son sunan nan,gaba ɗaya kun sa Nafee na tsokana ta, Kullum ta ganni sai ta hau ce man Juwairere "
Ta qarasa maganar 'yar kwallar ta na qarasa sauka a kuncin ta bakin nan a gaba, dariya ta bashi ba kadan ba wauta da shagwabar ta na burge shi sosai
"Ki kwantar da hankalin ki princess ba zan qara faɗa ba inshaa Allah sai munyi aure"
Hararar wasa ta masa tare da jin kunyar kalmar aure da ya ce, sai kawai ta miqe ta fita a dakin da gudu tai tsakar gid tana dariya, kad'a kai Mama ta yi sannan tace
"Ni Allah dariya kuke bani yaran nan, kun iya wauta da yawa"
Cikin wata iriyar murya jabeer ya ce,
" Mama kenan ba wauta bane da gaske auren ta nake son yi, amma idan Baba zai ban ita, ko ita ɗin ma Abuja za a kai ta? Dan na ji an maida sunan gidan nan wai gidan 'YAN ABUJA saboda yaran gidan a Abuja suke son yin aure su kalar Abuja ne, ina jin haka hankali na ya tashi ina fatan Allah ya sa ba Juwairere na a cikin wannan haukan, dalilin zuwana kenan Mama wato na yad'a manufa ta na son auren Juwairiyyah, na ji a wajen Innar mu wai har an kawo kuɗin Auren wadan can marasa kunyar"
"Hhmmm haka ne Jabeer amma kasan ni ba ruwana da wannan kalmar ta 'YAN ABUJA ko? Duk inda mijin Juwairiyyah yake ina fatan ya kasance miji na gari mai addini wanda zai riqe min ita da amana ,kuma wannan magana ta Abuja su da kan su yaran gidan nan duka qirqirar wa kan su ita wai su YAN ABUJA NE ba zasu auri kowa ba sai ɗan can, in su suna faɗa kuma sun yarda zasu aure su ni ban faɗa ba, kuma ban ba 'yata izinin kiran kanta da 'YAR ABUJA ba , in da rabon can ne gidan auren ta yake Allah ya zab'a mafi alkairi in ba can bane ni ko ina albarka na ke nema mata kullum"
" Haka ne Mama, Allah ya shige mana gaba"
"Ameeén ya Allah Jabeer"
Jabeer dan gidan Yaya Balarabe ne ya dawo daga bautar qasa inda aka tura shi illorin, ya kammala karatin shi bangaren kasuwanci, to a yanzu haka yana taɓa saida jakunkuna da takalma, ba wani arziqi ne da shi ba, yayun ta sun so matuqa ace me kuɗi ne da sun aure shi ko dan kyawun shi, amma inaaaa talauci a cewar su ya dakushe tauraruwar shi.
A yan kwanakin nan kusan kullum sai ya zo gidan su Juwairiyyah ,ga saurayin Salma mai baqin naci shima kullum ya na tafe, shi ma d'an Abuja ne ya na sana'ar saida motoci, kullum in zai zo zance se ku ga ya baza uwar riga ya shigo mota mai tsada ya zo amma fa baya bata ko sisi, wataran ne ma zai dan samu ya siyo mata yar shawarma kamar mayya tana rawar kai saurayi ya siyo mata abu ta amshe ta shigo gida,itama tini ta bi sahun manyan ta amsar kudin maza da basu jiki ai tabe2 , Alhajin da ke son ta shima in yazo zancen haka yake gama lalube ta ya yi gaba abun shi.........
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 YAN ABUJA. 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 3:
An saka ranar auren su gaba ɗayan su nan da wata ɗaya, gori kam da baqaqen maganganu ba irin wanda Juwairah bata karb'a a ba wajen 'yan uwan ta, tin tana kuka har ta kai ta daina sai dai ta kauda kai su yi tayi ranta na quna, takan ji kamar ta ce Ya Jabeer ya fito ayi auren su tare amma ba za ta iya ba saboda kunya, kuma ko ba komai ai shi ne namiji shi ya kamata ya fara magana.
Wata rana ta na zaune tana yanka alayyahu wa Maman ta sai Adda Suwaiba ta fito ita da Salma,a tare suka kalli Juwairah suka sheqe da dariyar shaqiyanci sannan Salmah ta ce wa suwaibah,
"Hhhhhhh Adda dan Allah ki ga yarinyar nan, a kyau dai duk gidanan albarka tafi kowa, amma wai ta tsaya ta mori kyawun na ta inaaa ba rabo, ta tsaya ta na yi wa kanta baqin ciki da mugunta , ban taba ganin irin wannan yarinya ba"
Suwaibah ce ta yatsine fuska kafin ta ce,
"Hhmmm ina ruwan ki uwar kinibibi taje ta auri wanda ta gadama ma ba Jabeer ba, danni bari ki ji, ba kyau ba, ba ilimi ba, in dai baka da farare bugun Abuja, sannan ba zaka aure ni ka kai ni Abuja ba kayi kyawun banza da kyawun halin wofi, dan ba su zan ci ba ah toh, ai ka auri me nera wanda za ka ci me kyau ka sha me kyau ka kwanta a qaton gida mai kyau shi ne magana"
Tafawa suka sake yi su na dariya tare da riqe baki kamar wasu 'yan daudu su a dole sun ma ta rashin mutunci, girgiza kai Juwairiyyah ta yi tace
" Adda Suwai kenan, ina kyautata zaton kun manta wa keyi, sannan kun manta dawa kuke jayayya, wanda duk zai wa wani gorin talauci to ya sani ba da wannan bawan yake ba da ubangijin bawan yake yi, bayan haka ba fa kusan sana'ar mazajen ku ba gaba ki dayan ku damuwar ku kawai a kai ku Abuja, ku kawai matan Abuja ne, matan manya, bana maku baqin ciki, zanfi murna ace kuna gidan hutu dan nima ina ma kaina fatan hutawa, amma zan baqin ciki ace baku da alkibla saita kudi da son abun duniya, Allah ya kyauta, ammmm for ur information, ni haka nake son Yah Jabeer ba dan dukiyar shi ba ba dan komai ba , Son shi ni kaina ba zan ce ga daga in da ya fito ba, na tsinci kaina ne da So da qaunar shi tun kafin na san menene so da qaunar kan su,dan haka wannan matsalar ku ce wai rashin kudin shi, tinda ya zama jinin jikina ba zan iya rayuwa ba shi ba kun ga ko ko a wanne hali yake zan iya zama da abu na mtwss"
Tafi ta ji ana yi mai cike da shauqi idon Jabeer tap kwallar dad'i da murna da farin ciki, Mama na d'aka tana mamakin yanda 'yarta ta ta iya zaro magana haka, lallai yau an kaita maqura kenan, Juwairiyyah ce ta d'aga kai ta ga Jabeer yana qarasowa gaban ta, wata irin kunya ta ji ta lullub'e ta da ko guduwa daga wajen ma kasawa ta yi, dan tinda suke bata taba zayyane masa yanda take son shi ba se dai ya na ganin alamu, kafad'un ta ya riqe ya juya ya kalli su suwaiba, inda suka qame qam suna wurga idanu alamun rashin gaskiya dan kuwa ya musu zuwan bazata, shi kan shi be san zai zo ba ya na komawa gida ne ya yi tunanin ya gan ta shi ne ya biyo,murmushi ya yi ya ce,
"Princess wad'annan kalaman naki sun qara dasa man zazzafar qaunar ki da son ki akan na da, ba zan iya rayuwa ba ke ba nima, dan haka nake roqon Abba da ya taimaka ya aura min ke nima a haɗa gaba ɗaya da na waɗannan fitsararrun marasa tarbiyyar, ba dan komai ba sai dan a kafa tarihi an yi auren ku tare kar muzo lissafi yana kwace mana Ko ba haka ba Suwai?"
Murguda baki Suwai ta yi ta na qunquni ta wuce d'aki, tsugunnawa Jabeer ya yi a gaban Juwairiyyah ya ci gaba da taya ta aikin yanka alayyahun,ita dai kunya ta ishe ta a haka suka gama yiwa mama girki ko leqawa gaida maman bai ba ita ma Maman ta kasa fitowa dan komai akan kunnen ta aka yi, Abba ne ya shigo da sallama bayan sun amsa ne yace,
" A'a Juwaira !Jabeer ! yau kune kuke mana abincin daren? "
Ya faɗa cikin dariya, sosa qeya Jabeer ya yi ita kuma Juwairyyah ta rufe fuska ta je ta amshi ledar hannun Abban, ta yi d'akin Mamar ta da shi, ta na shiga ta ga dakin ya sha gyara har da qamshin tiraren wuta irin na tsinke, Maman ce ta zo ta wuce su da ruwa a bokiti kanta a qasa dan yau dai yaran sun bata kunya sosai, Jabeer ya na dariya yace,
" Hajiya Maman mu yau kuma kunya ta kk ji ne? Shi yasa sai yanzu ki ke fitowa da kk ji Abba ko? Ai dana sani to tafiya na yi da muka gama hirar tamu"
Soson hannun ta ta wurga masa ta ce,
"Wannan d'anneman tsokannen dole se ya sa ni magana duk kauda kaina da na ke yi wato dai sai ka nuna min kai ɗan zamani ne ko? Ai gashi kun ja min makara yin wanka sai da Abban nasu ya dawo"
Dariya suka yi dikan su, Abban ne ke tambayar me ya faru ne, da hanzari Juwaira tace,
"Ba...ba..komai Abba hira kawai ake yi"
Dariya Mama da Jabeer sukai Mama ta wuce su Jabeer ne ya ce,
"Abba ka huta akwai magana a bakinnan nawa mai mahimmanci, ni dai in ke ba ki da abin cewa ni ina da shi yarinya,"
Roqon shi take da ido akan ya bari sai gobe yau kunyar zata mata yawa, amma se ya kanne ido ɗaya yana mata gwalo, shi fa ba ruwan shi sai ya faɗa a yau, tura baki ta yi ta wuce daki, bayan sun gama komai taa yi wanka sunci abinci, in da wajen cin abincin ma Jabeer rashin ta ido ya so yi ta qi bashi haɗin kai, wai shi da sai dai suci a kwano daya, da taqi sai ya zauna kusa da ita, in ya faki idon kowa sai ya zura hannu a nata ya d'iba ya kai bakin shi yana lumshe ido, can sai yace,
" Ke ni fa ban yarda ba ya akai naki ya fi dad'i? "
Cikin muryar shagwab'ar da ta zame mata jiki ta ce,
"Kai Ya Jabeer da rigima kk, ni duk d'aya ne kai ne dai ka ji haka"
"To kawo mu yi canjen kwano in dai ki na da gaskiya baki qara komai a naki ba"
Miqa masa nata ta yi ya bata nashi suka ci gaba da cin abincin su, can ya qara zura hannu a wancan da ya bata, ya debo ya ci har ya na wani lumshe idanun shi ya Kalle ta ya ce,
" Tab in ba sai an qara canjawa ba me ki ke fakar idona ki ke sawa naki ne wai?"
Cike da muryar da ke nuna alamun ta na so ta yi kuka ta ce,
"Yahhhhh Jabeerrrr"
Ta qarasa tana turo baki cike da shagwaba,Abbah ne ya Kalle su ya ce,
"Wai ni da ka ke wannan maganar ta ya aka yi kasan nata yafi dadi?"
Saurin tashi zata yi daga wajen ya sa hannun shi ya danne hannun ta dole ta koma ta zauna kan ta a qasa saboda kunya,
" Abba loma d'ai-d'ai na yi a dikka kwanon na ji"
"Abbah yafi loma ɗaya ya yi"
" Hmmm Abban su dan Allah ka rabu da shirgin yaran nan mu ci abincin mu bana son kana wasa da cin abinci kar wani ciwon ya kama mana kai"
Jabeer ne ya kashe wa Juwairyyah ido tare da matsa wa kusa da ita,ya kai bakin shi daidai kunnen ta ya ce,
" To kin ji yanda ake wa miji ko, sauran mu yi aure kina raba mana kwanon abinci irin haka"
Dariya ta gimtse, kamar daga sama suka ji muryar Goggo Sarai na faɗin,
"Hmmmmmm bariki kenan, watohar da 'Ya'yan ake zaune ake iskanci a tsakar gida, sannan in nawa yaran sun fita ace masu yan iska, to ai bahaushe yace, qazantar da baka gani ba tsafta ce"
Cikin jimanta maganar ta Abbah ya ce,
"Subhanallahi, me kk fada ne ke kuwa a gaban yara,kin wani tattaro su gaba ɗaya kun taho, ina za ku je haka?"
" Eh abinda ka ji na faɗa mana ko maimaici ka ke buqata na qara karanto maka?"
"To bari kiji mara kunya, Jabeer ya tabbatar man da auren Juwaira yake son ya yi, yana son a haɗa dana sauran ayi baki daya kuma a rana ɗaya, dan haka wannan shiriritar taki da gore-goren taki ta tsaya haka,ya ishe ki haka, duk abinda ki ke a gidan nan ina sane da shi"
"Aiko ba wanda ya isa ya haɗa mana aure da wadannan yan maulan"
Kan suwaibah ta rufe baki ta ji duka fauuu an make bakin da qarfi, saida bakin ya yi jini, cikin masifa da bala'i Goggo ta ce,
" Kan uban nan Jabeer me suwaiban ta yi maka da zaka mata wannan dukan, ko uwar ka Hansai ba zata yi ma 'yata hukun ci ba a gaba na balle Uban ka Balarabe"
Wani dukan ya sake kai wa Saudat dake kusa da shi sosai mai qarfin da ya fi na Suwaibah dan kuwa sai da ta kifa ta yi taga taga za ta fadi Goggo ta taro ta, cikin ɓacin rai Jabeer ya nuna Goggo ya ce,
"Duk rashin kunyar da ki ka yi ma Abba kan 'Ya'yan ki marasa tarbiyya zan fanshe"
Salma cikin d'aga murya ta hayayyaqo wa Jabeer ta na faɗin,
"Sannu uban mu, se ka kashe mu idan ka tashi"
Aikuwa bata rufe baki ba ya cire takalmin qafar shi ya murde hannun ta ya yi ta maka mata shi a duk inda ya samu, sai ihu take ta na neman taimako, Abbah na gani be ce komai ba dan ya jima ya na so shima ya yi musu duka da kan shi amma bai samu dama ba, Jabeer kamar taimakon shi ya yi Goggo ce taje da niyyar kwace Salma a hannun Jabeer ya sakar mata wani kallo da ya sa hantar cikin ta ta kad'a ta yi baya da sauri tana faɗin,
" Allah ya isan su baqin mugu kawai"
Sakin ta ya yi ya sa takalmin shi ya yi waje ba tare da ya kula kowa ba, Abba, Mama da Juwairah da idon ta ya cika da hawaye suka shige daki suma suka rufe qofa suka bar su nan tsaye su na cika su na batsewa tare da zage zagen rashin mutunci.......
***************************
Washe gari sai ga Baba Balarabe yazo batin auren Juwaira da Jabeer, sadaki dubu ashirin, a taqaice dai dubu Hamsin ya miqa masu kudin komai dan iya su ya ke da, take ita ma aka shaida hada bikin su dana yan uwan ta, sunyi murna sosai, inda suka sha gorin cewar " dadin ta kudin auren ma kamar anje siyan yar tsana a gwanjo dan ko matsayin kasuwa ma ba a samu ba" suna yi suna dariyar rainin hankali, ba wanda ya kula su, sauran dubu darin da yake da ita kayan gado masu sauqin kudi yaje ya siyo mata da kujeru, irin na talakawannan, Jabeer ya yi qoqari sosai Abba na ta hana shi amma ya qi, karshe cewa Abbah ya yi ai dama a musulunci haqqin miji ne duk wadannan amma al'ada ta sauya abun, dan haka na bar ku da siyan yan kayayyakin kitchen, Allah ya hore mana mu samu aiki mai kyau Abba kasuwancin nawa ya bude, komai zai zama tarihi, addu'a sosai Abban ya masa tare da godiya.
Daki aka gyara mata a main house din su ya kewaye mata guda biyu da dan wani qaramin waje a matsayin kitchen sai wani budadden bandaki mara rifi daga cikin kewayen nasu dai, ba laifi daidai talaka, yanzu jiran ranar biki sike nan da 'yan satika.
**************************
A yau ne dimbin mutane manya masu manyan motoci da qanan mutane marasa abun hannun suka shaida daurin auren wadannan bayin Allah kamar haka, Suwaiba da Alhajin ta Salihu mai tumbin Nera, Saudat da Alhaji Kalla na Abuja, Sai Salma da Alhaji Mansur, sannan kuma qaramar su Juwaira da Jabeer din ta, surutu kala2 ke yawo a tsakanin mutane wasu na sanya alkairi, wadan da suke bin bashin magana kuma suna gulmammaki akan su Suwaiba sun dakko ruwan dafa kan su ne basu sani ba dan kuwa manyan attajirai ne mazan nasu ba na wasa ba, Juwairiyyah kuwa bata da wayo, duk kyaun ta ta buge da auren talaka? Kowa dai da abinda yake fada, a haka aka tashi daga daurin aure, inda mazajen su Suwaiba suka ce su fa basu yarda ai komai a kano ba Abuja za a wuce ai dinna babba mai qayatar wa da abokan su, sai matan abokan su, ko dangin su ba za a dauki ko ɗaya ba dan kuwa abin na manya ne, shi dai mijin Salma shima cewa ya yi a bashi matar shi ya wuce da ita Abuja domin shi ba abokin mijin su Suwaiba bane tafiyar shi daban,sai dai mazajen su Suwaiba sun roqe shi akan yaje ai komai tare yaqi, dan haka kawai kauda maganar ya yi yace zasu tafi ba damuwa dangin shi da abokai na jiran shi za ai dinner, Ita kuma Juwaira sun yi yar walima kafin dare aka gama, YAN ABUJA kuwa jiki na rawa da daren aka shirya su Goggo na kuka suna kuka suka fita suka shiga manyan motoci aka kai su filin jirgi suka d'aga sai ABUJA.
Bayan tafiyar su Suwaiba kuma Juwaira ce zaune a gaban Innar ta da tazo biki mai suna Inna Dije tana qara bata yan kayayyakin matan da ta haɗa da natural abubuwan mu na abinci,wanda ta hada madara da zuma da ta sha dakakken kayan qamshi cikin babban kofi tace ta shanye, dama ta yini da yunwa tini ta shanye tsaf, ta qara mata da dafaffiyar kaza da ta sha kayan qamshi itama ta ci iya itawar ta, ( ita ni'imar mace ana son ta da dumi yan uwa, ba a son ni'ima da sanyi, dalilin haka ne ake son muna yawai ta amfani da kayan qamshi su citta kaninfari masoro, da dai sauran su, suna saukar da dumi ga jikin mace, ko had'in su kankana da su cucumber, ko mai mutum zai ci ko ya sha na garin ni'imar yana hadawa da kayan qamshi, suna qara mai daɗi da qamshi da amfani a jiki,) a haka aka sa ta gaba ta yi wanka me kyau da dan tiraren su na wanka dan d'uri, dan basu da arziqin siyan mai tsada, a cikin makewayin ta samu ruwan d'umi mai had'in ganyen magarya da kaninfari kadan da turaren almiski a ciki ta yi tsarki da shi sai qamshi ke tashi ko ta ina, tana fitowa Inna Dje ta bata misk mai kyau ta qara sawa a HQ ɗin ta,sannan ta miqa mata brush din ta ta wanke baki duk tana tsaye a kanta, ita ko kunya duk ta dame ta ga mutane ba a gama tafiya ba, ai ko tana gama wa ta sata ta yi alwala suka yi d'aki batansa ta shafa wani kwalliya mai nauyi ba, iyaka ta gyara ta ta samata qanan kaya daga ciki riga da skirt masu matuqar kyau, sannan ta sa mata laffaya a sama ta yi mata nadi me kyau, ga wani irin qamshi na tashi ko ta ina, kunshin nan ya zanu kannan ya dau gyara na musamman , yan daukar amarya ne suka zo a mota biyu, tana kuka tana komai aka fiddata, wata goggon Su ce mai suna Kareema tace,
"Yanzu Bilki ba wata yar nasiha haka za a fidda ta zuwa gidan miji baku mata ba ke da yaya?"
" Hmmm Kareema kenan, ai Juwaira bata buqatar wannan, Alhamdulillah na san wacece Juwairere na,yanzu nasiha ta ma ba zai mata amfani ba, ta je gidan mijin ta da sawar albarkar mu a rayuwar su dika"
A haka ta tafi daki ta zauna saboda yanda take jin zuciyar ta, ta na zama a bakin gadon ta kuwa sai hawayen rabuwa da 'yarta take abar son ta, an kai Juwaira lafiya d'akin ta, daga nan kuma kowa ya kama hanya ya dawo wasu suka wuce gidajen su,ita kuwa an barta daga ita sai halin ta tana ta zare ido dan hawayen sun qare mata tasss,ba abinda take ambata da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 25