Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya wuce sunayen Allah ta na nan zaune tana tunanin gida tare da jiran ta ga ta inda angon nata zai bullo...... [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA    💅🏼     WRITTEN BY HAERMEEBRAEH *SANARWA ! SANARWA !* *Ina masu buqatar sanin yanda za su gyara jikin su ta ciki da waje? Ina nufin daga gashin  kan su zuwa yatsun qafar su da qarin ni'imar jikin su?* *Ina masu son koyon sana'o'i dan samun taro da sisi? To 'yar uwa matso kusa ba sai kin biya maqudan kuɗi ba dan ki koyi yanda Zaki yi sana'ar da zata sama maki kuɗi da #1k kacal za ki mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA* *Idan kuma ke ma'abociyar karanta littafan Hausa ce ki yi wa HAERMEEBRAEH ❤️magana kai tsaye ta wannan No 09031416423 kai tsaye, Zaki samu Littafin MAHREEN DA KYAKKYAWAR FAHIMTA a kan farashi #500 each* *Please share*❤️ Page 4: Tana cikin wannan yanayi na tinanin Maman ta da Ammar taji hayaniyar maza na shigowa, sauri ta yi ta fito daga uwar d'akin ta da aka ajiye ta ta dawo palour ta zauna dan bata yarda wasu maza su shiga mata har dakin baccin su ba da sunan rakiyar ango dakin Amaryar shi, zama ta yi da sauri ta nad'e qafafun ta a kujerar ta rufe kanta har zuwa fuskar ta, Sallama suka yi suka shiga,dama akwai wasu daga abokan shi da basu san ta ba dan ba garin a suke ba da zama suna so su ga matar da Jabeer ya aura duba da cewa shi baya biye wa 'yan mata duk da yanda suke kai kan su gare shi kuwa. Amsa sallamar su Juwairiyyah ta yi da muryar ta mai daɗin sauraro kanta na qasa, tana tsaka da murna tare da jin daɗin babu wutar lantarki ba lallai su gani ta  ba sai nepa suka maida wutar,nan take haske ya gauraye ko ina, ai ko da sauri ta qara duqunqunewa a cikin laffayar ta ta na jin kunyar su, cikin ran ta ta na zagin Nafee da ta tafi ta barta ita ɗaya tunda ita ba wasu qawaye gare ta ba sosai, qawar ta ɗaya bayan Nafee Ita ce Shamsiyya kuma ta yi aure har da haihuwa,dariya suka yi gaba daya abokan angon har da angon,babban abokin ango ne ya ce, "To amarya ki kwantar da hankalin ki mu ba zamu takura sai kin bude mana fuskar ki ba,mallakin ango ki ce,kuma  angon naki ne ki zai bude maki da kanshi in mun tafi, sai dai akwai wasu shawarwari da nake son baku ke da angon naki  wanda na san kin san da dama daga abubuwan zamantakewar aure duba da gidan tarbiyyar da ki ka fito,ni na san ke wacece Indai ta bangaren sanin ya kamata ne, abinda zan ɗan maku nasiha akai mata da mazan wannan zamanin su na wasa da shi kuma ya na rusa aure,abun nan ba wani abu bane face, mantawa da sauke haqqin juna ko kuma na ce dena sauke haqqin juna,ta bangaren namiji sai ki ga da an kwana biyu ya daina dokin amaryar shi, sai ya fara fito mata da halayen shi mara kyau na kwadayin son ya zamana ta fara taimakawa gidan dan ya samu sauqin dawainiya wanda Allah ne ya ɗora masa wannan nauyin amma yake so ya sauke. Ba a ce mace karta taimaka wa mijin ta ba a gudu tare a tsira tare, hakan abune mai kyau dan zai qara mata samun lada mai yawa, sannan zata samu soyayyar mijin ta da yawa, amma abinda ba a so miji ya sa son zuciya ya dinga expecting ɗin matar shi dole dai ta taimaka a gida financially,in bata yi ba a zo rai na baci, yana jin haushin ta, daga nan an samu matsala, ita kuma mace ta bangaren ta kwadayin abun da mijin ta baida halin yi ta ce dole sai ya yi mata, dan ta gani a maqota kama ko jikin qawaye,abun ya kama daga kan sutura, abinci, da abin hawa, sai ta fara nuna halaye na kwadayin abin duniya wataran har ya kai ga tana sabon Allah dan ta samu kudin wadannan abin da ya fi qarfin ta da mijin ta , kinga kenan ta biye wa son zuciya daga nan aure sai ya lalace azo ana samun matsaloli, zan barku anan saboda dare nayi kuma na san amarya ta gaji tana buqatar hutu ko ba haka ba?" Murmushi ta yi kawai mai sauti tace, "Mun gode Allah ya saka da alkairi" " Ameen" Suka amsa gaba daya, anan wani abokin su kuma ya amsa ya yi masu addu'a mai yawa wadda zata yi masu matuqar amfani a rayuwa in Allah ya amsa masu, a haka ne suka ce bari su tafi, ya tashi zai raka su, yana miqewa ya bige yar qara ya yi, Juwairiyyah ta yi sauri ta dago tana mai sannu, ido abokan shi suka zuba mata suna mamakin kyaun matar Jabeer ɗin, ganin haka ne yasanya kishin Jabeer motsa wa cikin haɗe fuska ya sauri ya yi gaba yana fad'in , "To kuzo mu tafi mana" fita suka yi suna zuwa soron gidan yace "To abokai na ni zan koma na gode Allah ya bar mana zumuncin mu da amana" " Ameen" suka amsa, wani ne a cikin su cikin tsokana ya ce, " kai dai ba sai ka kore mu ba muma sauri muke yi dare ya yi muna da mata kai da ma farin shiga ne a wannan lamari na aure,amma gaba ɗaya ka matsu ka koma ba zaka iya koda qara second ɗaya bane anan" Dariya suka yi gaba ɗayan su Jabeer kuwa ya yi wuf ya shige yana daga masu hannu, sai da ya rufe gidan sannan ya leqa sashen iyayen shi ya ji shiru da alama sun kwanta bacci, direct sashen su ya wuce,ko da ya shiga sai ya tadda Juwairiyyah Zaune ta haɗe kai da quiwar qafar ta, bayan ya yi sallama ta amsa ne ya qarasa shiga ciki, kusa da Ita Jabeer ya je  ya tsugunna ya na bin dukkan jikin ta da kallo a hankali ya sa hannun shi ya riqe nata ya na murza wa, yanda nunfashin shi ke sauka a kan hannayen ta daya riqe ne ya sa zuciyar ta sauri wajen bugawa, ga wani irin tsoro shi da take ji a lokaci d'aya kuma  wani feelings sabo da bata taɓa jin irin shi ba ya na shigar ta, " Princess kin ga yanda ki ka yi kyau kuwa? Ba dan kar na yi qarya ba da sai nace tinda nake a duniya ban taba ganin kyakkyawa irin ki ba" Cikin sarqewar murya ta furta , "Kai Yah Jabeer wannan kowa ya ji ya san daɗin baki ne kawai ka ke min" Matsawa ya qarayi sosai fuskokin su na daf da na junan su, sannan yace, " Hmmm ke ki ka ga hakan amma ni iya gaskiya ta na fada" Wani irin abu ta ji  a jikin ta wanda bata taba jin irin shi ba ya na mata yawo daga kanta zuwa qafafun ta, 'Dama wannan ne rayuwar auren da ake faɗa ana tsorata mutane?, da na zaci wata azabar ake sha kamar yanda shamsiyya da akai wa aure ta faɗa min ni da Nafee, Dafa ta Jabeer ya yi sannan ya ce mata, "Me ki ke tinani haka" Ya qarasa faɗa ya na ɗora labb'an shi Saman nata,da sauri ta miqe tsaye ta yi breaking kiss din da yaso ya yi mata, ta hau kame2 tama rasa ina zata shiga, d'aki zata ko waje zata yi ne? kamo kafadun ta ya yi dika biyun ya miqar da ita tsaye a jikin bangon da kusa da bed room din su. " calm down my princess, na ga kina tsoro na kamar wani dodo" Murmushi ta yi na yaqe sannan  tace, " Yah bacci nake ji jikina ciwo yake min" " Ok to muje ki yi alwala mu yi nafila sai ki samu ki rage kayan jikin ki mu kwanta zan maki tausa ma in ki na so" Baki na rawa cike da sauri  da in-ina tace, " Aaaa..... bama....bama sai .. ka min tausaaa ba " Dariya ya yi mata ganin yanda hankalin ta ya tashi kamar wadda ya yi wa wani abun, alwala suka yi sannan ya ja  su suka yi salla raka'a biyu bayan sun idar ne ya kama kanta, ya fara kwararo addu'o'in da suka zo a sunna ana yi wa amare,kamar haka, " Allahumma innee as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha a laihi wa a'udhu bika min sharri ha wa sharri ma jabaltaha alaihi" Bayan sun gama ne ya koma palour inda ya ga an jera mata plates a 'yar qaramar  kitchenware ɗin ta ya dakko sannan ya dauki ledar da abokan shi suka aje masa mai kaza a ciki ya shiga d'akin, zama ya yi a gefen ta ya juye masu kazar a plate wadda aka gasa  ta aka zuba soyayyan chips din da yasha hadin hanta da kayan kamshi, ga attaruhu da albasa sai tashin qamshi suke yi, kamshin ne duk ya karade d'akin har ya yi sanadiyyar motsa mata da yunwar da take tare da ita, madara mai sanyi ya zaro a Leda ya ajiye a gefe da jus ɗin exotic na kamfanin Dansa, niyyar ta ta qi ci, dan qawar ta Shamsiyya ta ce in an bata kar ta ci, in taci sai ta biya shi da jikin ta,amma ina Juwairiyyah ba zata iya jure kamshin fa ke dukan hanci ta ba har ya yi sanadiyyar farfaɗo mata da yunwar ba,cikin ran ta take ayyana, 'Yana bani zan amshe ba zan iya fulako  ba ina dalili? iyaka da ya ce na biya shi na fara kuka nasan zai hakura ya kyale ni tun da baya son ɓacin rai na' Kamar Jabeer ya ji huɗubar da ta ke yi wa kan ta ya yanki wata tsoka mai gwab'i ya miqa mata bakin ta, ta kuwa buɗe bakin ya saka mata ta hau tauna wa cike da jin kunya,a haka ya na bata yana ci suka gama cinye wa tasa suka sha madara da jus ɗin su, bayan sun gama ne ya fara qoqarin rage mata kayan jikin ta dan ta ji daɗin bacci a cewar shi. Dan kuwa da kan shi ya zaɓo mata rigar da zata sanya ya ajiye a gefen gadon ya na mata murmshi,wurga ido kawai Juwairiyyah  ke yi ko ta ina ta na mamakin lamarin da ke faruwa,a hankali idanun ta suka fara cikowa da ruwa, Jabeer na kula da haka ya sakar mata riga da ya kama zai taya ta cire wa, baƙin ta na rawa ta furta, "Yah Ka bar ni na cire da kai na," " Ok cire ki kwanta dare ya yi" Sai ya ja baya ya je ya fara cire nashi kayan ya saka na bacci a gaban ta, a lokacin da ya cire rigar da wandon shi a gaban ta ba ko kunya sai ta zaro ido waje ta na sake mamakin abubuwan da ta ga Jabeer na yi ba ya ko jin nauyin ta, hankalin ta ya yi mugun tashi dan ganin yanda jikin shi yake a murd'e kamar na masu ɗaukan qarfe,take jikin ta ya fara bari ta yi saurin kauda kai gefe, cike da tsokana kuwa Jabeer ya ce, " Ki na son abinda ki ka gani ne? " Da hanzari Juwairiyyah ta sake juya masa baya ta ce, " No i don't, in fact banga komai bama ni, ba kuma na so na ga ni" Muryar ta na rawa ta qarasa maganar,Jabeer kuwa cewa ya yi, "A gskiya Naseer ya kyauta min da ya mata min na yi wanka kan mu zo amma da ban san ya zan ba yanzu dan a matse nake zuwa wankannan batan lokaci za yi" Zaro ido ta qara yi kamar za su fado qasa, ta ce, " Yah to ka tashi ka je toilet mana tinda ka matsu?" Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce, " Hmmmm gama ki ga me nake nufi" Tare da kashe mata ido ɗaya ,take hankalin ta ya tashi dan ta gano me yake nufi yanzu, a hankali ta d'au kayan ta zata fita palour ta canjo ta dawo amma Jabeer ya hana ya ce anan a gaban shi zata sauya,ba yanda ta iya a dole haka ta sauya kayan ta a gaban shi, sai binta yake da kallo kamar wani maye,ta na gamawa ta zauna bakin gado ta yi addu'ar bacci ta shafa a jikina ta, ta kwanta a farkon gadon kamar a ce kyat ta zura da gudu,gashi basu baro gida an kawo ta d'akin miji ba sai da Inna Deeje ta sanya ta yi mata alqawarin bazata guji mijin ta ba , zata bashi duk abinda ya nema a wajen ta mudin bai sab'awa Allah ba, janyo ta ya yi jikin shi, yana shinshina qamshin ta, Cikin dasasshiyar murya Jabeer ya ce, " kaiii amma princess gaba ɗaya qamshin nan ya sa na qara qaguwa na kasance da ke" Shafa ta ya fara yi yana mata salon da ita kanta ba zata so ya daina ba, a wannan lokacin Yah Jabeer ya fara qoqarin cika aiki, sai ta ji ya fara addu'a ta saduwa da iyali, kamar haka, " Bismillahi Allahumma janibnash-shaidhana wa jannibash-shaidhana ma razaqtana" Kukan da take son yi ta mayar ta had'iye, bata qaunar yin abinda da zai b'ata ranshi ya fasa cimma burin shi,amma daga qarshe dai dole da kuka da roqo da aka tashi wasan, har cewa ta yi tama fasa son nashi, tinda haka ne abin baya tausayin ta, bayan komai ya dawo masu daidai ne ya mannata da qirjin shi yana mata addu'o'i da saka albarkan da ya faranta ranta matuqa, hakan da ya yi mata ya nuna mata mahimmancin kawo budurcin ta da ta yi lafiya gidan auren ta , da kuma  illar abinda da zai same ta da bata kawo ba din, kuka take ta yi qasa qasa, Jabeer sai ya tashi ya saka kayan shi ya fita ya haɗa mata ruwa mai dumi ya dawo ya ɗauke ta ya kai ta bayin su da ya kewaye masu su kaɗai ya sata cikin roba mai faɗi da ya zuba ruwan. Godiya Juwairiyyah ta yi masa dan kuwa ta ji daɗin ruwan sosai bayan sun gama suka yi wankan tsarki suka fito suna koma wa d'akin sai ta hau abin sallah ta tada sallah dan kuwa lokacin qarfe 3:30am ya yi, sallolin nafilar ta ta yi bayan ta idar ta kwanta ta na tasbihi bacci mai daɗi ya ɗauke ta a wajen,sai shi ya daga ta bayan ya idar da tashi nafilar suka yi baccin su tare da addu'ar Allah ya basu ikon tashi su samu sallar asuba akan lokacin ta...... Ɓangare'YAN ABUJA matan manya kuwa bayan sun sauka a filin jirgi  sai suka tarar da motoci na jiran su, nan aka kwashe su sai babban hotel ɗin da za a yi dinner mai suna Chelsea hotel................. [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA    💅🏼     WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *SANARWA ! SANARWA !* *Ina masu buqatar sanin yanda za su gyara jikin su ta ciki da waje? Ina nufin daga gashin  kan su zuwa yatsun qafar su da qarin ni'imar jikin su?* *Ina masu son koyon sana'o'i dan samun taro da sisi? To 'yar uwa matso kusa ba sai kin biya maqudan kuɗi ba dan ki koyi yanda Zaki yi sana'ar da zata sama maki kuɗi da #1k kacal za ki mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA* *Idan kuma ke ma'abociyar karanta littafan Hausa ce ki yi wa HAERMEEBRAEH ❤️magana kai tsaye ta wannan No 09031416423 kai tsaye, Zaki samu Littafin MAHREEN DA KYAKKYAWAR FAHIMTA a kan farashi #500 each* *Please share*❤️ Page 5: Tinda suka je farfajiyar hotel ɗin bakunan su Suwaiba yaqi rufuwa, ganin irin manyan motocin da suke ta gani an parker sai kwadayin arziqi da samun dukiyar su ya ninka na da,basu taɓa ganin manyan motoci haka ba a zahiri sai a American movies, wasu ma basu taba ji ko ganin su ba duk Yawon su da kallace kallacen fina-finan nasu, ( abun ku da masu idon cin nera ga Yawon tsiya gidaje da bukukuwan masu kuɗi) hankalin su ya kai qololuwa wajen kwadayin son suga mahallin su ma'ana wajen da za a kai su ya zama shi ne gidan su. Sun shiga wajen da ake gabatar da dinner tare da angwayen su da abokan angon da suka masu rakiya, inda suka qarasa wajen hight table din da za su zauna, iyakar ganin idanuwan su iya ganin jajayen hulina  da fararen kaya da sirkin ja a jikin farin kayan ne, daga matan har mazan shigar kenan, sune kad'ai suka saka baqin lace da ratsin fari a jiki, mazan su ma farar shadda da jan aiki a jiki da jar hula ne akan su. Wani mutum babba suka gani a gefe mutane kowa ya shiga sai ya gaida shi, ya hakimce a wata qatuwar kujera, suma tashi suka yi suka kai masa gaisuwa sannan suka koma mazaunin su an fara gudanar da dinner lfy, inda daga baya aka umarci kowa yaje ya yi serving kan shi abin da zai ci a wajen, wajen maza daban wajen mata daban,a bangaren Mazan akwai wani irin nama na daban da aka zo dafawa aka masa dahuwar laushi sosai duk abin mutum ba zai gane na meye ba,  matan kuwa kaji ne da sauran tarkace abinci kala2 a wajen har da na qasashen waje, sun ci sun sha, daga baya akai ta rabawa mazan wani ruwa a wata kwalba mai duhun kala, jikin su har rawa yake dan murna, kowa ana bashi yake kafa kai tas zai shanye ya ajiye kwalbar ya na lasar baki. Bayan an yanka cake ne da sauran bidi'o'i aka tashi daga wajen dinner din,daga nan angwayen suka kama matan su suka shigar mota sannan suka ba su wani ruwa a cups masu kyau da sirkin wani magani a ciki, suna sha take bacci ya dauke su, madadin su yi gidajen su na aure da matan sai naga sun ɗauki wata hanya kamar za a bar garin basu tsaya ba sai a dokar daji, wani katafaren gida ne suka isa mai gate guda uku manya, katangar gidan duk maitar mutum na ya gudu ba zai samu dama ba saboda tsayin su, suna isa wasu qattai ne naga sun fito murdaddu sun sha baqaqen kaya da neck tie red, daukar su Suwaiba suka yi a hannu suka shiga da su gidan, a wani qaton parlour suka aje su kan kujeru suka juya suka fita,angwaye kuwa na tsaye su na jiran fitowar Ogan nasu su ji wanne umarni kuma zai basu, ji suka yi wata qatuwar murya ta yi magana, "A kai min ko wacce d'aki, a haɗa su a gado daya," Ko da na duba sai na ga wannan turmusheshen mutumin ne na wajen dinner ya fito ba riga daga shi sai gajeren wando, nan take tunanin inda aka samu telan da ya iya dinka masa wannan wargajejen wandon ya faɗo rai na, ba karamin qaton mutum bane shi ɗin ,gaba ɗaya ya haɗa komai na zama qato ga tsaho ga qiba, ga tumbi, da sanqo, ga gashin baki, gana hammata nan cunkus, ga idonnan jawur, kamar gauta, ba zan taba iya kwatanta girma da yanda yake ba abin sai wanda ya gani kawai, haka ya tako da fataken qafafun shi ya kalli mazajen sukuma sai suka duqa masa alamun gaisuwa, d'aga masu kai ya yi ya ce, " kuje sai nan da sati biyu ku dawo,dan ban taba ganin mata masu kyau irin wannan ba," ya qarasa yana lashe baki, d'aga masa kai suka yi suka amsa da, " Tah oga zaks," Suka furta a tare, fita suka yi kowa hankalin shi kwance dan sun san samun su zai rubanyu da yawa, Nicon hotel suka wuce su hole abun su, dan su dama sunyi auren ne dan gudun maganar mutane, amma ba dan sun damu da auren ba, tinda a cewar su mata na nan kamar jamfa a jos. Shigar Oga Zaks dakin keda wuya ya isa gaban gadon, yana lashe baki, kashe wutar ya yi ya kunna bed side lamp, cire masu kaya ya yi ya dakko wani magani ya shaqa masu, maganin bacci ne, wanda zai kai su kwana bakwai cif suna bacci ba tashi, ina ganin zai zame rugegen gajeren wandonnan nai gaba da gudu, ba dani za ai kallon tashin hankali ba. Oga Zaks ba shi ya fito daga dakin nan ba tin daren sai qarfe tara na safe hamma yake yana miqa ya wani bangare ya shiga wani daki, waya ya yi naji yana, " ku shigo, " Sannan ya aje wayar ya shiga wanka, wasu mata ne dattijai suka shigo, dakin da su Suwaiba suke nan suka shiga, suna gyara su suna tausaya masu, ɗaya daga cikin matan ne tace, "Hmmmm wama ya sani ko garin shegen son abun duniyar su ne suka haɗu da su, ai kinga ban ga laifin mazan da suka kawo su ba kwadayi mabudin wahala" Jikin ajiyar zuciya d'ayar ta furta, "Haka ne kuma Allah dai ya kyauta" Bayan sun gama shirya su ne suka tafi suka bar su suna ta shaqar bacci, a palour suka haɗu da Oga Zaks yana zaune, ya baza uban tumbi yana kwasar girki,cikin qatuwar muryar shi ya furta, " Daga yau duk wata shegiyar tsohuwa a cikin ku da ta qara gulma akan matan da suke shigowa gidannan sai na mai da ita matata kuma ta inda baku tsammata ba tanan zan na amfani da ita, munafukan banza da wofi ku bace min da gani," Jiki na rawa baki na kyarma suka hau bashi hakuri, korar su ya yi ya barke da wata mahaukaciyar dariya. ************************** Salma kuwa matar Alhaji me saida motoci,wani qaton gida ya kaita a wata unguwa a gwarinpa, gidan ya haɗu iyakar haɗuwa dan kuwa tun daga baƙin gate d'in gidan za ka san cewa nera ta zauna, bayan ya tsaida motar a bakin gate d'in ne ya fita da kan shi ya je ya bude gate sannan ya koma ya shigar da motar cikin harabar gidan,a tare suka fito daga motar sannan ya daga ya riqe ta a jikin shi, bayan sun shiga cikin gidan ne Salma ta hau zare ido dan ganin uwar  dukiyar dake gidan. Wani d'aki ya kaita mai kyau, suna shiga ba tare da aikata komai da ya kamata amarya da ango sun gabatar ba a daren su na farko ya ja ta gare shi ya fara aika mata saqonnin shi da ya jima ya na jiran irin wannan ranar ya isar da su gare ta, dan kuwa shi dama bai wani more ta ba sosai, kuma babu laifi Salma bata yi irin wayewar su Suwaiba ba ko ya je soyayyar tasu bata wuce kiss da shafe shafe bata taɓa bashi dama ya kusance ta ba,haka angon Salma ya fara qoqarin cika burin shi a kan ta babu sallah ba salati ba godiya ga Allah na daren farko na ma'aurata ba adduar komai haka ya maida ita cikakkiyar mace,ai kuwa yasha kuka da zagi a wajen Salma, dan ashar sai wanda ta manta, bayan sun kammala komai ne ya yi ta rarrashin ta,a qasan zuciyar shi yana ayyana, 'Zakici uban ki ne wannan zagin da dukan da kk mun duk sai na rama na fanshe abuna, yar me kwadayin tsiya' A zahiri kuwa wani irin lelen ta yake kamar kwai, a cikin sati dayan nan ya nuna mata gata sosai, wanda ta dinga hango gidan su tana ayyanawa a ranta 'Dama haka rayuwar Abuja take da daɗi, ga miji gangariya na samu, ga kayan alatu na ci na sha na kwanta miji namin hidima, tab amma an bar Juwairiyyah a baya ina tausaya ma rayuwar ta, dan kuwa haka zata qare ta cikin talauci da babu' Shafa gefen  fuskar ta Alhajin nata ya yi tare da fad'in, "Tinanin me kike yi haka ?" Cike da shagwab'a ta kwanta a jikin shi ta ce, "Ba komai, ina tinanin ka ne kawai" Ta qarasa  maganar ta tana wani karairaya tare da qarasa haye cinyar shi, " karki damu ai gani kome kk so naki ne, nema kawai zaki a baki baby" Dariya ta yi tana shafa jikin shi tana limshe ido, sannan ta kashe murya ta furta, "Da gaske Alhaji na?" Da gaske mana tambayi ki ga aiki da cikawa" "Hmmm ni dama dubu dari biyu kawai nake so zan je na dan siyo kayan sawa na gida, dan na ga

Chapter 3 of 25