Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
siya suka cika da kayayyaki masu kyau da tsada, Suwaibah ce ta haɗa su da manyan shagunan 'yan kasuwan da ke haɗa wa mutum lefe idan ya na da buqata a farashi mai sauqi saboda yanzu sana'ar da take yi kenan kuma ta na samun riba sosai. Cikin abinda bai fi awanni huɗu ba suka kammala da bangaren lefe suka shiga kasuwar kurmi suka sayi kayan qamshi na girki sannan aka yi masu haɗi na musamman da za su niqa su dinga sanya wa a cikin madara da zuma su na sha dan qarin ni'ima da d'umin jiki. Juwairah bata manta da Yah Jabeer ɗin ta ba dan kuwa ta lodar wa mijin ta kayayyaki dangin qanan kaya irin su vest, boxers, turaruka, takalma, da huluna guda biyu masu kyau sosai, mamaki ne ya kama yayun nata sai suka kasa jurewa sai da Saudat tace mata, "Ke kuma ya naga kina ta siyan kayan maza baki saiwa kanki komai ba sai tirare da kayan bacci," " Adda Saudat Yah Jabeer na d'ebarwa ai, ba dan komai ba sai dan yanda shima yake kyautata min yake min dukkan wata hidima da ta taso min da jikin shi da aljihun shi, na sani komai zan masa ba zan yi kamar yanda yake yi min ba, sannan wannan abun da na siya already yana da su, amma kyautata wa juna na qara danqon soyayya, kyauta tsakanin miji da mata musamman irin wannan ta tiraren da miji ya fi so, tana da matuqar tasiri a zuciyar namiji, shiyasa naga ya dace tinda ya wadata ni da kuɗi shima na sai mashi" "Lallai Juwairere ke kin ma fi Mama Bilki iya tattalin miji, na rasa waya koya maki duk wadannan dabarun da ki ke da su, ko kayan baccin ki da tiraren ki da ki ka siya duk shi za su amfana ai" Dariya sukayi, Juwairiyyah ta ce, " Salma ai gaba kin ga in ya tashi bani zai bani wanda yafi wannan tinda yasan ko me zan siya duk inda aka je aka dawo zai amfana shima ta kowanne fanni" Tafiya suke suna jinjina wayo irin na qanwar tasu,cikin jin daɗin had'in kan da ta samu da yayun nata ta ce masu, "Adda Saudat ku daina mamaki na, kowacce mace tana da kaifin hankali da basirar zaman gidan miji, bambancin mu shine wata tana shiga kwakwalwa da zuciyar ta ta yi tinani ta sama wa kan ta mafita a kan duk wata matsala da ta tunkare ta ta na tsayawa ta yi abinda zata amafana da baiwar ta wasu ma su amfana, wata kuma dunkufe kanta take yi bata son yin dogon tinani sam, bama ta son tana zurfafa tinanin ta akan komai, da matsala ta same ta sai tace sai ta nemi shawarar qawa, wani lokacin a yi sa'a ta samu shawar qwarai wani lokacin kuma ayi rashin sa'a ta samu muguwar qawa ta bata gurguwar shawara, amma in da zamuna bude zuqatan mu da maza sun ji daɗin zama damu, aure kuma daya rage mutuwa, da hakuri da sanin ya kamata ya wanzu a gidan auren mu, Adda muna a garin da ba mu da iyaye acan mu ne iyayen junan mu mu zamu taimaki kan mu, dole sai mun zama masu irin wannan tinanin gudun shiga matsala kan dayan mu ya kai mana agaji" Wani kallon so da qaunar qanwar tasu ke yawo a idanu zuwa zuqatan su, a haka suka samu abin hawa bayan an masu niqan kayan qamshin suka wuce gida a gajiye da kaya masu mugun yawa, alwala suka yi sukai sallah azahar da la'asar da basu samu damar yi ba suka bar Goggonayen su da su Mama Balki suna kallon kayan lefen daga qarshe ma maqota aka aikawa duk suka shigo suka ga kayan alkhairi,su kuwa ganin ana ta cika ne ya sa suka yi wanka suka ci abinci, sai baccin gajiya ya ɗauke su. Tin da sassafe angwaye suka jera mota guda huɗu saboda ɗaukan amaren su da wasu kayan nasu,Jabeer ma ya dakko hanya shima amma bai iso ba Innarmu ta zo gidan da sassafe dan a yi komai gaban ta, amare na ta dan koke koken rabuwa da gida na al'ada, Saudat kuwa tsoro ne fal cikin ta na komawa Abuja, ji take yi kamar ta fasa auren amma ta dake, tana son ta yi wa mijin ta kyakkyawan zato, Adda Suwaiba anyi anyi ta yi rakiya tace ita da Abuja ko a film ba ta so taga Ali Nuhu a can balle ita ta sa qafarta a Abuja, haka aka hakura aka barta wataran zata je ne da kan ta, Jabeer ne ya iso nan ya tsaya Shima aka yi sallama da Amare daga nan ya ɗauki matar shi suka wuce gidan iyayen shi dan ya huta gajiyar aiki da ta tuqi. Bayan tafiyar su ne Hajiya Goggo Sarai mai niyyar zuwa Makka ta na tsaye tana zabga masu addu'a da fatan alkairi,haka ma Baba Baballiya da Mama Bilki ba a bar su a baya ba wajen amsawa da Ameen tare da ɗora tasu addu'ar akan ta ta,kwalla Goggo Sarai ta share na tsoro da tausaya wa yaran nata dan bata san wannan karon me zai faru da su ba, gaba ɗaya son Abuja ya bar ran ta a cewar ta koda Makka za a biya mata ta na rokon kar a ce jirgin su zai tashi ko ya sauka ta Abuja dan akan ya bi ta Abuja sai ta fasa zuwa Makka,Mama Balki ce ta ga yanda take cikin damuwa a hankali ta dafa kafad'ar Goggo Sarai ta ce mata, " Addu'ar fatan alkairi zaki ci gaba da binsu da ita kamar yanda ki ka fara ,ki daina zurfafa tunani, ki yi masu kyakkyawan zato Yaya," " To Bilki Allah ya kai su lafiya, Allah ya zaunar da su lafiya da alkairai maras yankewa" Amsawa dukkan su suka yi da " Ameen" suka koma cikin gida. ***************************** A gidan su Jabeer kuwa ya na can bai samu hutun da ya so ya samu ba ba dan komai ba sai dan tafiya da su Ammar da Abrar da suka yi, dan ma yaran sun shaqu sosai da Suwaibah musamman Abrar, amma ganin Jabeer sai ya sa Abrar maqale masa ta na yi masa rikici, daga qarshe da ya gaji ya tattara su ya kai wa Suwaibah su dan ya huta. Ko da aka kai wa Suwaibah su nan da nan ta karɓe su Ammar ɗin ta hau yi masu wasa, Ammar ya damu sosai da rashin Adda Calman shi, fitowa Suwaibah ta yi zata deb'o masa dambun naman da ya ragu a kitchen wanda akaiwa amare, tana tashi Abrar ta dinga tsaga kuka kamar ana zare mata rai ita ala dole Suwaibah ba zata tafi ta bar ta ba sai dai su tafi tare, Jabeer da Juwairiyyah na kwance a parlour sun d'aga labulayen d'akin su dan su sha iska su na hango duk abinda ke faruwa, mamaki ne ya kama Jabeer dan ganin yanda Abrar ke matuqar son Suwaibah, Juwairiyyah ce ta yi murmushi ta ce "Haka suke fa, in dai Addah Suwaiba na kusa to fa ni na huta,sai mu yini ko nono bata nema ba, sai dai ta yi ta bata kunun ta, idan kuwa na gama bata nono ban mayar da ita wajen Addah Suwaibah ba kuka zata dinga yi min kamar na sato ta" " Ikon Allah lallai akwai soyayya mai qarfi a tsakanin su," Lokacin bacci na yi Suwaibah ta d'akko Abrar dan ta dawo da ita wajen iyayen ta,Ammar kuma zai kwana wajen ta kafin gobe a maida shi gida Shima,tunani ta hau yi, 'Yanzu shikenan idan su Abrar suka koma gida na maida Ammar zan dawo na ci gaba da zama babu d'a babu jika, dama bahaushe ya ce son zuciya ,b'acin ta' Bayan ta yi sallama Juwairiyyah da ke kwance a jikin Jabeer suna kallo ta miqe ta buɗe qofar ta yi wa Yayar tata izinin shiga ciki, miqa mata Abrar ta yi ta na murmushi sannan ta ce, "Ga Iya rigima nan ta yi bacci sai da safen ku," Murmushi Juwairiyyah ta yi ta ce, "Iya rigimar gaske, ai wannan kyanta kawai a yaye ta ma dan ba wani shan nono take yi ba da dare" Da sauri yarinyar ta sake qanqame Suwaibah ta na so ta yi kuka, Jabeer ne ya tashi ya yi dabarar karb'ar ta a hankali sannan suka yi sallama da Suwaibah ta juya dan komawa sashen ta, ta na juyawa hawayen da suka taru a idanun ta suka zuba da qarfi a kuncin ta, zafin su ne ya sanya ta saurin sanya hannu ta share su sannan ta sa hannun ta na dama ta shafa marar ta, hawaye na ci gaba da fita a Idon ta. Ta na shiga sashen su ta tadda Alhaji Salihu zaune ya miqe qafa ya na jiran dawowar ta,ya na hango ta cikin wannan halin ya tashi cikin hanzari ya isa gareta, rungume ta ya yi dan ya fahimci halin da take ciki, kuka ta saki mai ban tausayi ta ce, " Yanzu Mine shikenan ba zan haihu ba, d'a ko 'ya ba zasu taba samun mazauni a wannan marar ba? Ya zanyi da son yara dake addabar zuciya ta Mine?" Kuka shima yake sosai, sai da suka yi ma'ishi sukai shiru dan kan su, sannan Alhaji Salihu ya ce, " kiyi hakuri ni na jawo maki wannan nakasar, ki gafarta min, nima ina cikin quncin rashin haihuwa,musamman inna kalli yanda Abrar ke son ki take matuqar qaunar ki,ba dan zaluncin da mu ka yi maku ba da na san zaki haifamin yara kyawawa kamar ta, amma na yi mana mugunta ba zamu ga k'wan mu ba a duniya Allah wadaran rayuwata bata da amfani" Da sauri Suwaibah ta sa hannu ta rufe masa baki ta ce, "Dan Allah kar ka sake cewa haka Mine, Allah ya albarkaci rayuwar ka Mine, ka ci gaba da gyara kurakuren ka na baya, ka duba ka ga ni fa yanda Allah ya maka albarka a kasuwancin nan, har fili ka siya, nan gaba kadan gida zamu yi na kammu mu koma, mu ci gaba da jin daɗin rayuwar mu, to meye na d'aga hankali har ka na wa kan ka mummunan kalami? Allah ke bada haihuwa fa, kuma ya na bawa duk wanda yaso ne,mu ba zamu yi kuka da Allah akan bai bamu ita ba,saboda mu da kan mu muka yi wa kammu mugunta dan haka hakuri zamu ci gaba da yi," Juwairah ce ta koma sashen ta da gudu tana kuka, sai da Suwaibah ta koma sashen ta ta tuna da turaren da ta siya masu da garin kayan qamshin da bata bata nata ba saboda ba su samu zama ba, shi ne dalilin da ya sa ta biyo sahun ta dan ta kawo mata nata sai kuma ta ji duk abinda ke faruwa a tsakanin ma'auratan, kuka take sosai har tana shessheka, wani irin tausayin su ne cike a zuciyar ta, Jabeer gaba daya ya rud'e ya rikice sai ya kama tambayar Juwairiyyah ya na fad'in, " Babe me ya faru ? Me aka yi maki ki ke kuka haka?.... Ya Allah Sanar dani abinda ke damun ki ko zan iya sama maki kwanciyar hankali, ki sanar dani kome ki ke so na yi miki , kukan ki na d'aga hankalina" Da sauri ya maida k'wallar Idon shi dake barazanar fitowa saboda rashin son ganin Juwairiyyah a cikin damuwa, cikin shessheqar kuka Juwairiyyah ta ce, "Sweet one ka taimake ni ka bawa su Adda Suwaibah Abrar" Maganar ta ta yi matuqar dukan shi,anya ba gamo matar tashi ta yi ba kuwa? Kyautar fa gudan Jinin shi k'walli ɗaya jalli jal take so ya yi? to ta yaya ma zai iya yin kyautar ɗan mutum balle Abrar ɗin shi farin cikin shi? Duba da yanayin damuwa da tashin hankalin da take ciki ne ya sanya shi rungumar ta ya na lallashin ta dan ta dawo hayyacin ta da wuri ta bashi labarin abinda ke faruwa. Sai da ta nutsu ta daina kukan ne Jabeer ya umarce ta da ta sanar da shi akan wane dalilin zai ba da yarinyar shi guda ɗaya tilo,babu bata lokaci kuwa Juwairiyyah ta yi masa bayanin duk abinda ta ji Suwaibah da mijin ta suna tattaunawa akai cikin kuka batare da ta rage komai ba, shi kanshi Jabeer labarin ya taɓa zuciyar shi sosai, " Tabbas sun cancanci wannan kyautar daga gare mu,nima Allah ne ya ban ita ai ba ni naba wa kaina ba,dan haka na basu ita halak malak, ko bayan raina Abrar wato Hafsat 'yar su Suwaiba da Salihu ce" Sai Jabeer ya wani kashe murya dan ya sake sanya ta farin ciki ya ce, "kinga da mun koma gida sai mu samu qanwa ko qanin Abrar ko? Idan mace ce a sanya mata Sunan Mama Balki idan kuma namiji ne mai rabo ya ɗauka tsakanin Abbah da Baba ko?," Yana maganar yana shafa cikin ta yana murmushi,cike da narkewa a jiki shi Juwairiyyah ta ce, "Ni dai Yah Jabeer anan nake so, sai mu haɗa da addu'a Allah ya sa a dace, ka ga daga gobe ma zaka iya fara kira na da Maman Abbah" Dariya ta sanya ta kai masa dukan wasa saboda ta bawa kanta da kanta kunya, shi kuwa sai ya goce ta daki iska ya shiga d'aki da gudu ta bishi suka kashe fitila, abinku da makauniya ido sai da gilashi sai na fito na basu waje. Da misalin ƙarfe goma na safe su Juwairiyyah ne suka gama shirin tafiya Abuja sun shirya kayan Abrar da komai da take da buqata a wani akwati,Sallama suka je yi ma su Innarmu tare da qudirin sanar da su hukuncin da suka yanke suna zama su suwaiba da Salihu suka shiga,cike da fara'a suka gaggaisa, Abrar na ganin Suwaiba ta hau yunqarin zuwa wajen ta, cikin shauqi da kewar yau zata rabu da Abrar ɗin ta ta ɗauke ta ta rungume tana kissing din ta, ita kuma sai dariya take yi ta zaci wasa ake yi mata, k'walla Juwairah ta share ta tsananin son 'yar ta ta amma haka zata bawa Addan nata ita dan kuwa gaba ɗayan su sun san matsalar da take ɗauke da shi na rashin haihuwa,cikin murmushi Juwairiyyah ta miqa wa Addah Suwaibah akwatin yarinyar tace, " Addana daga yau kin zama Ummu Abrar, dan Yah Jabeer ya miki kyautar ta gaba ɗayan ta, kin cancanci zama uwa a gareta, dan haka ga ta nan dama ita ba wai ta damu da nono bane, kunun nan da kike bata shi yakamata ki ci gaba da bata, Allah ya raya maku ita da imani mu zamu wuce muna yi maku fatan alkhairi" Ta ja baya Suwaibah da Salihu tare da Innarmu da kuma Abbah Balarabe sai suka shiga wani irin yanayi na tsakanin mamaki da ta'ajibi, Abbah ne ya iya magana ya ce, "A gaskiya Juwairah ke alkairi ce ga rayuwar zuri'ar mu baki ɗaya daga birni har qauye, tabbas Qanina da Bilkisu sunyi matuqar qoqari wajen baki tarbiyya managarciya, baki nufin kowa da sharri a rayuwar ki kullum alkhairi ne a tsakanin ki da kowa,wannan shine dalilin ne ya sa kika zamo mai samun nasara da ɗaukaka a rayuwar ki, Allah ya yi muku albarka, kai ma Jabeer na ji daɗin wannan kyauta da ka yi, duk da nasan ita zata saka ka yi, amma da baka aminta ba da hakan bai samu ba," Sai a wannan lokacin ne su Suwaibah suka fita daga yanayi na mamaki suka hau godiya ba qaqqautawa, Innarmu ce tace, " Suwaiba Allah ya taya ku riqo, ya sa ki qoqarta bata tarbiyya mai kyau yanda zata tashi abar so ga kowa" Cikin kukan farin ciki Suwaibah da mijin ta ke gyad'a kai alamar za su yi duk abinda ya dace dan baiwa Abrar rayuwa mai inganci,daga qarshe Suwaibah zuwa ta yi ta rungume qanwar tata tare da durqusawa a gaban Jabeer ta na kuka, d'ago ta ya yi ya na buga bayan ta da sigar lallashi, yana kada mata kai alamar ta dena kuka,Salihu ne ya je ya miqa mai hannu daga baya ya rungume shi ya saki kukan murna Shima dan kuwa sun yi masu kyautar ba zata, " Na gode ! na gode ! Ban taɓa ganin mutanen kirki irin ku ba,baku yi la'akari da rayuwata ta baya ba kuka mana wannan kyauta Allah ya faranta maku, ya baku yara masu albarka,Allah ya bamu iKon kula da ita fiye da yanda za ku yi mata," "Ameen" kowa ya amsa sannan su Juwairiyyah suka ja akwatin su suka tafi zuwa mota,suna barin qofar gidan nasu Juwairah ta saka kukan rabuwa da 'yar ta, hannun ta Jabeer ya kama shima yana jin wannan kewar na damun zuciyar shi, amma ba yanda zasu yi dole su yi haƙuri na ɗan lokaci ne, Allah ya basu ladan abinda suka yi a hankali Juwairiyyah ta warware suka hau hira har daga baya bacci mai daɗi ya ɗauke ta........ [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA    💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 32: Ba a tafi kai amarya Nafee d'akin ta ba sai da misalin 10am saboda kukan da suka tsaya yi ita da Innarmu da Juwairiyyah sai kace idan an rabu ba za a sake haɗuwa ba, kuka suka dinga zuba wa har sai da suka ba wa mutane tausayi shaquwar da ke tsakanin Innarmu da Nafee ba karama bace domin kuwa ko hutu Nafee ba ta zuwa gidan kowa kullum ta na tare da Innarmu su yi faɗa su yi daɗi,sai gashi yanzu aure zai raba su zai kai ta can nesa garin da ba ta da kowa, nasiha aka dinga yi masu tare da nuna masu ai rabuwa ba mutuwa bace wata rana za su gana,har a cikin mota Nafee bata daina kuka ba a haka suka kama hanyar garin Kebbi dan kuwa anan ne za ta tare. Mama Balki da Saudat na daga cikin 'yan kai amarya gidan ta dan kuwa kowa ya san halin Goggo Sarai idan aka ce ta je zuwa za ta yi ta zubar wa da Nafee mutunci a gidan surukan ta musamman da yake su na da rufin asiri,har yanzu halin ta na son abin duniya na nan sai dai kwad'ayin ace yaranta ne ke da dukiyar ya ragu gudun kar a koma 'yar gidan jiya, ga wani irin  jiji da kai da take yi, ta ji zafin rashin tafiya da ba a yi da ita ba amma haka ta jure ta danne saboda kar ta yi magana a yi mata caaa dan ta kula dangin mijin nasu haushin ta suke ji tun da suka samu labarin abinda ya samu su Saudat. Juwairah ta so matuqa ta je amma Abrar ta sha gajiyar biki bata da lafiya dan haka Jabeer yace ba inda zata kar su je gajiyar hanya ta sake sanya 'yar shi rashin lafiya,ai kuwa haka ta zauna ta dinga kuka har dai daga qarshe ta ba wa kan ta da kanta hakuri. Cikin masu kai amarya har da qannen Abbah Balaraben su  Goggo Karima da Goggo Mero,sai ta bangaren Innarmu ma mutum biyu aka zab'a Inna Fateema da Inna Aishe, sai kuma wata aminiyar Innarmu wato Baba Maryam,lokacin da suka isa Birnin Kebbi dare ya yi sosai gaba dayan su jikin ta qaura ya yi la'asar, a unguwar Alieru Quaters motoci guda ukun da suka d'akko amarya suka tsaya,tun daga yanda gate ɗin gidan yake zaka gane fasalin gidan nasu gidan ya bambanta da na sauran mutanen unguwar,kana kallon gate ɗin zaka san gidan masu akwai ne, yan uwan ta sai san barka suke su na yi mata addu'ar Allah ya zaunar da ita lafiya ya sa gidan zaman ta ne na mutu ka raba, kwanan su biyu suka fara shirin komawa Kano,Saudat kuka tasa data tuno nisan hanyar da suka kwaso, sai lallashin ta ake abokin angon daya tuqo su yana ta mata dariya ya ce, " A gaskiya zan faɗa ma Umar farouq ya shirya matar shi raguwa ce" Ta na jin haka ta miqe ta goge hawayen ta tare da zabga masa harara ta ce, "Inji waye ya ce maka ni raguwa ce? Ni kar ka wani fada masa komai mu tafi" Dariya aka saka a wajen banda Nafee da take rab'e a gefen mijin ta ta yi kalar tausayi, ai ko suna barin qofar gidan nasu ta fashe da nata kukan,'yan kai amarya na hanya suna tausayin Nafeen, ganin yanda take zubar da hawaye ne ya sanya angon ta ɗaukar ta cak a hannun shi ya yi ciki da ita yana lallashi, mijin Nafee ya na son ta sosaiii ya na da kirki gashi da kulawa da tattali gefe d'aya kuma ya na tausayin matar shi duba da garin da ya kawo ta bata da kowa sai shi. Bayan dawowar su Saudat Kano lafiya ne aka kai kowa gidan ta aka aje ta, abokin angon daya kawo su Mama Bilki ne ya tsaida Saudat, cikin kashe murya ya ce, "Ba daban Farouq ya rigani ba yana da kirki da nagarta tabbas dana kawo kaina nima,zuciya ta ta kasa haƙuri ta ce kar na tafi ban sanar dake sirrin dake raina ba,Saudat na kamu da son ki a kwanakin nan da muka yi tare, ina maki fatan alkairi, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mumina saliha" Saudat ta ji daɗin yanda ya ke da fahimta da addu'o'in da ya musu,ta kula shi ɗin mutum ne mai natsuwa da hankali, murmushi ta yi sannan ta ce, "Na gode sosai da soyayyar ka a gare ni, ina ma ka fatan alkairi, Allah ya baka wadda ta fini, tabbas abotar ku akwai amana kuna da halin manya," Murmushi suka yi sannan daga baya ya mata sallama ya ja ya tafi. Kwana biyar tsakanin bikin Nafee masoyan huɗu suka hau musayar saqwanni da jaddada manufar su ta son auren su Saudat ɗin, dan haka su kuma suka ce su zo su sami Baban su a San da zaman su. Babu b'ata lokaci kuwa wata ranar lahadi da yamma wasu dattijai suka zo gidan Baba Baballe dan nemawa Farouq da Ibraheem auren su Saudat ɗin,a wasu manya-manyan motoci suka zo wanda yasa baba jin tsoron kar a maimaita 'yar gidan jiya fa,daga ƙarshe dai Baba  ya kirawo yayan shi wanda ya jima da fara bincike akan zuri'ar gidan su Farouq ɗin tun da Jabeer ya sanar da shi labarin da Juwairiyyah ta faɗa masa game da yaran, ya na zuwa ya tabbatar wa da Baba Baballiya ai mutanen kirki ne a nan take suka roqi arziqin a d'aura auren in babu wata damuwa, saboda ba a kusa suke ba kowa da garin da yake aiki, shi Abban su Farouq mazaunin Abuja ne sai qanin shi dake lagos, dayan kuma a kebbi yake, Baba Baballe sawa ya yi a kira wani kawun su daya rage masu da abokin shi babba ga kuma Yayan shi aka haɗu aka daura auren su Saudat da Farouq, Salma da Ibraheem akan sadaki naira dubu hamsin hamsin, tare da alqawarin Ibraheem zai riqe yaran Salma kamar nashi in sun masu izinin hakan, su Abbah sun yarda amma sun qara da cewa in babu takurawa sun masa izini,su kuwa iyayen su Farouq suka jaddada masu cewa shi Ibraheem da kan shi ya sanar masu ba Salma kawai yake so ba, har da Yaran ta ya gani ya kamu da qaunar su dika,Baban su Suwaiba ya ji daɗin hakan sosai, a haka taron ya tashi cikin farin ciki da yarjejeniyar sanda duk Amaren da angwayen suka shirya a tsakanin su sun tare. Bayan wannan daddad'an labarin ya iske dangi kowa ya yi murna Juwairah ta roqi Jabeer akan ya barta har a gama hidimar tarewar Yan uwan nata kan ta koma, ya amince mata ta zauna amma shi da yamma zai koma Abuja sabida aikin shi, sun bari akan in ta kammala ta sanar da shi sai ya zo ya ɗauke ta, kuɗi ya bar mata mai yawa a hannun ta kan ya tafi saboda hidimar yau da gobe. Haka Jabeer ya tafi suna jin kewar junan su dan kuwa  basu son abin da zai raba su sai dole,gashi bata san ma ranar tarewar amaren ba ta yi azarb'ab'in cewa a bar ta,haka Juwairiyyah ta dawo daga raka shi jiki

Chapter 23 of 25