An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: https://chat.whatsapp.com/G0Tst06uPc12T74oZhhCa2
💅 ' YAN ABUJA 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Assalamualaikum my beautiful mutanen kwarai, ga Editing ɗin littafi na na biyu da na farayi a duniya, a karanta da hankuri*
*2018/2024*
*Dan Allah da kun ga an fara posting ku ɗan dinga adanawa saboda ba sai na yi nisa ba ku tambaya a dawo baya, Na gode.*
PAGE 1:
Gidan malam Baballiya gidane mai girma na qasa a tsakiyar garin kano, wanda ya qunshi mata biyu, Goggo Sarai itace uwar gida, sai Mama Bilkisu itace amarya, malam Baballe yana da yara guda huɗu dika mata ne, se dai a kullum ya na roqon Allah da kuma burin Allah ya azurta shi da d'a namiji mai albarka, wanda ko bayan ba shi zai kula da wannan zuri'a tashi mai cike da rikici, domin tin yaran nashi mata na qanana gidan yake a cikin rikici, wanda Goggo ce sanadin komai wato Sarai, ita Mama Allah ya sa mata sanyin hali, amma kome za ai bata yarda a taba mata 'yar ta tilo ba wato Juwairiyyah, dan haka in dai aka ji rikicin ta to fa akan 'yarta ne, ko shi ma ba zata tsaya aita bala'i ba , za dai ta tabbatar ta karb'ar wa 'yar ta 'yanci sannan ta ja ta su bar wajen, a haka Allah ya raya masu yaran su guda hudu, Goggo Sarai nada Suwaiba mai shekara 19 ,se Saudat me shekara 18, sannan Salma me shekara 16, Mama Bilkisu kuma na da Juwairiyyah wadda take sa'a ce ga Salma kwana uku ne tsakanin su kawai,a yanzu ta na dauke da tsohon ciki gashi nan haihuwa ko yau ko gobe.
Sai dai muyi fatan Allah ya amsa addu'ar Abba Baballiya wannan karon a samu biyan buqata wato ya samu d'a namiji,domin kullum fatan shi Allah ya dube shi ya bashi namiji, mutum ne shi mai sanyin hali saidai sanyin halin shi be hana shi yin iya qoqarin shi na ganin ya isa da gidan shi ba, badan ma qoqarin da yake ba da tabbas Goggo Sarai zata zama itace mijin a gidan.
*****************************
Da misalin 11:45am Juwairiyyah ce ke ta aikace aikace a tsakar gida, inda Mama Balki ke d'aki ta na naquda ba tare da sanin kowa ba, azaba ta yi azaba ta ga abun ba zai yiwu ba kawai sai ta buɗe murya ta na neman taimakon Allah da na 'yar ta ta da ke taya ta aiki.
"Wash Allah na, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Juwaira, taimaka ki kira min Abban ku a waje"
Yarinyar da aka kira da sunan Juwairiyyah ce ta miqe tsaye da sauri ta dau mayafin ta da ke kan qofa ta yafa ta fita, a bakin kofar gidan ta tadda mahaifin nata zaune ya na sauraren rediyo, sai ta durqusa cikin ladabi sannan ta ce,
"Abba Maman mu na kiran ka,ka yi sauri Abba bata da lfy kamar ma haihuwar ce ta zo dai ina jin"
Ya na jin haka ya miqe tsaye da sauri ya shura takalman shi dan ya saka,gaba ya yi ya bar su a wajen dan kuwa takalmin ma yaqi qarasa shiga qafar tashi sai kawai ya afka cikin gidan direct ya wuce sashen Mama Balki,labulen d'akin ya buɗe ya shiga, ganin mawuyacin halin da take ciki ne ya sanya shi cewa,
" Subhanallahi Gimbiya, haihuwar ce ta zo mana bagatatan haka? Sannu Gimbiya"
( Yana kiranta da Gimbiya ne don a ilimin shi na addini ya san cewa kiran sunan mata da suna mai daɗi sunna ne, inda yake kiran Goggo Sarai Sarauta)
Cikin tsananin azabar da take ji ta na ratsa ta ta ce,
" Malam taimaka min na samu na kai uwar d'aka bana son zama a nan na haihu a rumfa"
Cikin sauri ya kamata ya riqe da kyau a jikin shi sannan ya ce,
"To Gimbiya, bismillahi,amma kuma mun shigo d'aka ko dai muje asibiti ne ?"
Murmushi ta yi kawai dan sanin cewa qarfin hali ya yi dan ya kwantar mata da hankali ya fad'i hakan ta san bashi da kuɗin yin hakan, ko na mota basu da shi, shi kuma ba mai kwad'ayi ba ne da zasu samu a wajen Goggo Balki, dan 'ya'yan ta kyawawa ne dukan su su na kawo mata kuɗaɗen da bai san ta hanyar da ake samo su ba shi yasa baya ci,ita kuwa Goggo Sarai ta kan ce, ta gode wa Allah da ya bata 'ya'ya 'YAN ABUJA , dan haka ne auren su sai mai kudi, dalilin wannan ne yasa take samun kudi sosai, duk da fadan da Abba Baballiya keyi akan su daina biyewa samarin banza, amma se suka yi kunnen uwar shegu da gargad'in shi, da taga ya yi musu wuta2 kuma ya fara kullen su a gida , sai ta fito da dabara tunda shi mai son ilimi ne musamman na addini sai ta saka su Islamiyya,daga sun fita zasu bi gidan qawaye su canja kayan su, su qara gaba neman mazan da zasu aure su su kai su Abuja, gaba ɗaya basa hulda da qawyen su na unguwar, sai 'ya'yan masu kudi, saboda anan suke saka ran samun nasarar samun mazajen aure yan Abuja, kullum su na cikin zuwa biki da partyn qawaye na birthday.
Kukan jariri ne ya dawo da Abba daga tinanin ina zai samo kuɗin kai ta asibiti ta haihu lfy?
Da hanzari ya qarasa taimaka mata yaro ya fad'o har da mabiyya, nan take ya taimaka mata ya gyarata ya aje jaririn ya fita qofar gida da hanzari ya na hamdala, Mama kuwa cikin raunananniyar murya ta ce,
"Juwaira ɗora min ruwan zafi da ya tafasa ki sanar da ni , Allah ya sauke ni lafiya"
"Alhamdulillahi... Alhamdulillahi to Mamana sannu"
Cikin zumud'i da washe kyawawan haqoran ta farare masu dauke da hushirya a saman su ta nufi gaban murhun nasu dan cika umarnin mahaifiyar ta na ɗora ruwan zafi, se dai ta na zuwa ta ga ba icce, amma duk da haka bata karaya ba ,sai ta je ta dakko tukunya ta wanke ta zuba ruwan ta kawo wajen murhun ta ajiye, zata juya kenan ta ga mahaifin ta na shigowa da icce a hannun shi na dama, hannun shi na hagu kuma riqe yake da baqar leda qarama, da hanzari ta isa ta karbi iccen tana mai yi masa sannu da zuwa, komawa ta yi ta haɗa wutar ta ɗora ruwan shi kuma ya yi d'akin da mai jegon take.
Kamar saukar aradu ta ji an yi tsaki a gefen ta, qin juyawa ta yi dan tasan ba zai wuce ɗaya daga cikin 'yan uwan ta ba koma Goggo da kan ta.
"Aikin banza sai rawar qafa ake, duk dai abun mutum mace ya qara haifa balle ai mana wani rawar kan uwa ta haihu"
"Hhmmm Allah ya kyauta ya kuma shiryar da ku dika idan ku na da rabon shiriya, to bari ki ji Salma 'yar baqin ciki, wannan karon namiji Mamana ta haifa, dan haka baqin ciki ya kashe duk wani dan hassda"
Wani uban ashar Salma ta saki ta saki jikin ginin da ta riqe tai sashen su da hanzari,kafin ta isa cikin rashin sa'a bokitin gaban ta ya bige tukunyar da take girka masu farfesun naman kaza,ai ko tini komai ya zube a qasa, nama ne na kaza cike da tukunyar wanda da gani yafi qarfin kaza ɗaya, ko kulawa ba ta yi ba ta shiga d'akin su da gudu tana faɗin,
"Goggo ! Goggo ! Wai ni kina ina ne wannan mummunan labari ya same mu?"
Da saurin su suka fito dikkan su daga d'akin,ana can an qule a d'aka ana hasafin kuɗin da suka samo, suna bata labarin mazajen da ke son su turo ai zancen auren su da su, cikin d'aga murya Goggo ta ce,
"Ke meye haka duk kin bi kin fadar min da gaba kamar an ce maki matar uban ki Bilki ta haifi saurayi"
"Hhmmmm ai kin ji ashe kece ke yi mana mugun fata baki da tinani sai wannan, gashi nan to ya tabbata ai Mama Balki ta haifi yaro namiji"
Damqo Salma Goggo Sarai ta yi da qarfi cikin zare ido take tambayar ta
"Me kk nufi salma?"
Cikin rashin kunya da murgud'a baki da idanu Salma ta ce,
" Ina nufin Mama Balki ta haifi saurayin d'a namiji,tunda ke kullum kk mana mugun baki akai to gashi ta tabbata"
Wani wurgi Goggo ta yi da Salma gefe, ta kuwa qume kai da gini ji ka ke quuummm,Goggo da sauran yaran nata dika suka yi gaba zuwa dakin Mama Balki, Salma ma miqewa ta yi ta na lailaya goshi ta bi bayan su, babu ko sallama suka afka d'akin, daidai Abbah Baballiya ya dauki gasasshen naman rago ya sa wa Mama Balki a baki, Goggo ce ta dafe qirji saboda abinda idon ta ya gane mata ta buɗe baki ta ce,
"Me nake ji ne da gani yau kuma ni saratu? "
Suwaiba 'yar boko kuma 'YAR ABUJA ce ta karkata baki ta ce,
"No i can't believe this, what is going on here, ina jaririn yake?"
Suwaibah na da kwalin ta na NCE ,ita kuma Saudat kwalin secondary ne kawai a hannu wanda duk daya take da su Salma da Juwairiyyah ,sai dai Juwaira tana son ta ci gaba da karatu amma ba halin yin hakan saboda babu arziqi,wannan shine dalilin da yasa ta hakura, amma sakamakon ta yayi kyau sosai, both WAEC & NECO, ganin yanda suke wani cika su na batsewa ne ya sanya Abbah Baballiyaya ce,
"Haba Sarauniya ta ya zaki shigo d'akin ma'aurata da yaran ki gaba ɗaya haka babu ko sallama? Kuma bama ki tambayi yaya ko ta haihu lfy ba? Aa tambaya kuke ina jaririn? Anya wannan rayuwar da ku ke yi ta dace kuwa?"
Cikin yatsine baki da fari da ido kamar wata qaramar yarinya Goggo ta ce,
"Eh ban ga zan iya sallamar ba ne shiyasa banyi ba, tambaya ɗaya kuwa da zan yi shine me aka haifa? Da gaske ne namiji aka samu?"
"Eh na miji Allah ya bani, me za ki yi, me zai faru? Me ya sa ba zaki yi hakuri kema Allahn da ya bani ya baki naki ba ,ai ba wai ya manta ki bane kema in ki ka yi hakuri watarana samu za ki yi,dan haka ku fita min a d'aki tinda ba arziqin yi min sannu ne ya kawo ku ba"
Gaba dayan su shewa su ka ɗauka sannan suka tafa kamar wasu 'yan daudu Goggo ta ce,
"Hahaiiiiii Cassssss, eh lallai ne, kinyi d'a na miji na gani tabbas, shine ya sa zaki fara min kitifi ko Balki ? to bari na baki wani labari, a da kam na damu amma a yanzu wani tinani ya wanken damuwa ta tass, Shi Uban yaran me ya ke da shi, me ya tara da zan damu raina akan haihuwar d'a namiji da girma na haka? Bayan ga 'Ya'ya mata Allah ya bani na zuwa Abuja ? Ki kalla da kyau duka Yarana kowanne namiji mai lafiya ya gansu sai ya yaba, dan haka bama zan bar labarin nan ya kwana ba"
Bakin ta suwaibah ke son rufewa tare da faɗin " Goggo ki bari ba yau ba kin sanar da su in komai ya kankama, ko kin manta halin yan baqin cikin ne? Se a shiga malamai a hana lamarin faruwa ai"
"A'a Suwaiba banni na fada masu su ji duk wani d'an baqin ciki se dai ya mutu, yarana guda biyunnan sun samu mazajen aure mazauna Abuja, dan haka sai ka bude kunnen ka kaji, zan basu izinin su turo magabatan su a zo ai komai nan kusa ba da jima wa ba"
Abbah Baballiya ne ya ce
"Hhmmmm Sarai kenan wato kece ma mijin yau ni ne matar ko? Umarni kk ban akan za su ce mazajen da za su aure su turo ko? Ba bincike ba komai kawai su turo, to bari ki ji na fada maki zan ba 'ya'yan ki mijin da suke so amma komai yaje yazo ki kuka da kanki kina jina ko? Fitsararriya mara kunya mai raina mijin ta a gaban 'Ya'yan ta dan su koya suma"
Ranshi a bace ya ke sanda ya yi maganar kawai se ya matsa kusa da Maman yana ci gaba da bata naman a baki
Shewa Saudat tayi tace
"Ikon Allah wai na kwance ya faɗi"
Dariya Suwaiba ta yi ita da Salma suka tafa har da uwar tasu suka fice suna dariya, can qasan maqoshin Goggo balki kuwa kishi ne damfare, kada kai ta yi a ranta tace,
'Kun yi ku gama da 'ya'yana sun tafi ABUJA aure kashin ku ya bushe a gidannan'
A kwana na bakwai da haihuwa aka yi suna yaro ya ci sunan Ammar kyakkyawa da shi sak mahaifin shi,ba wani taro aka yi ba da yawa saboda babu abin hasafin, ba qaramin so da gata yake samu ba a wajen iyayen shi da yayar shi Juwairiyyah ba, zaune suke a shimfidar tabarma a tsakar gidan inda ya sha shara ko ta ina yayi fes da shi ta na masa wasa kamar ya na jin ta, can cikin d'akin su kuwa qamshin turaren wuta na tsinke ne ke tashi, Sallama Abban su ya yi ya shigo jikin shi a mace, amma dik da haka sai da ya yi masu Juwairiyyah wasa ya sumbaci Ammar ya shafa kan Juwaira sannan ya shiga cikin d'akin Goggo Balki, kwalama Juwaira kira ya yi yace ta kira mishi Goggo Sarai.........
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 2:
Juwairiyyah bata b'ata lokaci ba wajen isar da saqon Abbahn nasu a wajen Goggo, da kyar ta amsa mata sannan Juwairiyyah ta koma bangaren su,da isa da qasaita Goggo Sarai ta shiga parlourn Mama,hakan ne ya sanya Abban murmusawa duk da cewa ranshi na matuqar quna game da abubuwan da take yi mishi.
"Sarauta kenan yi ki qaraso mu yi abinda zamu yi na fita sallah ko?"
Qarasa shiga ta yi tana hura hanci ta zauna a gefen hannun shi na dama, inda Mama Bilki kuma ke zaune a gefen shi na hagu, cikin wani irin yanayi mara misaltuwa ya buɗe baki ya fara magana,
"Da farko dai zan ma Allah godiya daya kawo min wannan rana da nake ta buri, duk da cewa ta zo min a bazata kuma ba a yanda na so zuwan ta ba, amma dai Alhamdulillah,a yau ne manema auren yaran nan su Suwaiba, Saudat da Salma suka zo, kuma mun karbe su a gidan Yaya Balarabe cikin aminci da mutunci, inda suka damqa mana dukiyar auren yaran, Suwaiba kudin sadakin ta da na gani ina so da kudin da zata hada lefe dika, an bamu million huɗu da dubu ɗari biyu, sai na Saudat Ita kuma Million biyu da dubu ɗari bakwai, a gaskiya na so na qi karba saboda kudin sunyi yawa, kamar wasu wanda zamu saida 'ya'yan?....... "
A hargitse cikin damuwa da jimami Goggo Sarai ta ce,
"Abban su ina fatan dai baka yi mana baqin ciki irin na iyayen zamani ka sa an rage kudin nan ba?"
Cikin ɓacin rai Abbah ya kalle ta ya ce,
" Amma dai na rasa me yasa baki da d'a'a Sarai? Ya ina magana ban qarasa ba zaki katse ni? Har kina ikirarin zan ma 'ya'yana baqin cikin iyayen zamani? Anya rayuwar da kk ɗora yaran nan akai za ta ɓulle da ku kuwa? Gaba ɗaya kin sa tarbiyyar yarana ta zamo a lalace? Kin raina ni baki ganina da qima da mutunci? Kedai harka in ba ta kudi ba baki san komai ba? Na gode Allah da yasa ina iyakar qoqarin riqe gidana ni Baballiya da ke kam na san da karuwanci zaki saka 'ya'yana yi su na kawo maki kudi, haba, bai ishe ki misali ba akan Balki da 'yar ta guda ɗaya tilo? 'Yarta ɗaya amma ta tsaya wajen bata ilimin addini dana zamani daidai iyawar ta, ke kuwa in ba Salma ba da ta yi sauka yarannan biyu ba zasu iya bude qur'ani su yi karatu mai kyau ba, Salman ma gashi nan ne dai kawai, to ina mai maki nasiha da kiji tsoron Allah akan abinda kk yi, ina jiye maki ranar kuka, ranar dana sani, ranar ni 'yasu,........ "
Da sauri ta d'aga masa hannu ta na yatsine ta ce,
"A'a faaaa, bafa zaka sani a gaba ba kana min mugun fata da kuma maganganu na nuna baqin ciki qarara a wannan al'amari ba, 'Ya'ya dai nawa ne, nice na yi naqudar su na haifa abina, ba wanda ya taya ni lokacin da nake qafa ɗaya a lahira, d'aya a duniya ko akwai? Dan haka sai wanda naga damar su aura sannan zasu aura, nifa takura ce bana so tammm, yanzu ka bamu kuɗin lefen da na sadakin dan musulunci bai yarda kowa ya taba dukiyar auren yara ba sai su ehe"
"Hmmmmm Sarai kenan, ke kaɗai ai ki ka yi cikin su ki ka haife su ba da ni ba dole ki ce yaran ki ne ke kaɗai,to bari kiji iya kuɗin lefe zan baku, sauran kuwa sai sanda akai auren su zan baki su,wai da ke a taki qaramar kwakwalwar sai na dauki wannan maqudan kudin na baki dika? Haka kawai aje wani abu ya faru bana fata ba ai aure ba ku barni da biya da tashin hankali? To bazai yu ba"
Bala'i ta miqe tana zazzagawa son ranta ita sai an bata kudin, tashi ya yi ya kad'e rigar shi ya fice dika a gidan, daidai lokacin da Mama Balki ke cewa,
" Ubangiji ya sanya alkairi da albarka, Allah ya kare dukkan abinqi ya basu zaman lfy"
"Hahaiiiiiiiii Cassssss, ni zaki wa bariki Balki? Zuciyar ki cike da baqin ciki amma wai kk addu'a mai daɗi irin haka,to dama dai ba daga bakin ki ta fito ba dana ce ameen"
Sa kai ta yi ta fice ta shiga madafin su ta hau aikace2, tana yi tana masifa kamar wadda ta zautu, yaran ne suka dawo daga yawon tazubar din su da sunan Islamiyya suka tarar ta na masifa, tambayar ta Saudat ta yi da cewa,
"Wai Goggo me ke faruwa ne gaba daya muryar ki har qofar gida ana jiyowa"
"Ba ni da wannan sallamammen uban naku ba ne, an kawo kudin auren ku sun riqe shida Balarabe, to ni ba zasu nuna min isa da iko ba, sai sun kawo kudin nan dika"
Cikin qasa da murya Suwaibah ta ce,
"Goggo kwantar da hankalin ki tashi mu shiga ciki ki gani"
D'aki suka shiga ta d'akko mata maqudan kudi a jakar ta ta zube mata su a saman gado, tsabar razana da ganin yawan su se da Goggo tai baya dafe da qirji ta na zaro ido,
"Suwaibah waya baki wannan kudi haka me yawa?"
Fari ta yi farrrr da idanun ta kafin ta ce,
" Alhaji Salihu mai tumbin Nera kk ji Goggo, cewa ya yi ga su ko zan qara wasu abubuwa a lefe yaso bayar wa a can wajen karbar sadakin se ya fuskanci za a iya cewa sun yi yawa, shi kuma yana ganin ko nawa ne zai iya kashewa ya samu yar zumar shi"
( Sunan da yakan kirata kenan lokacin watsewar su) dariya Saudat ta yi ta ce,
"Aaaaa kice Adda Suwaiba Alhaji ya ji zuma yau"
Dariya suka yi dika har uwar tasu suka tafa, baqin cikin ma da take ciki tuni ta manta da shi, ba sallah ba salati suna nan zaune ana maida yanda akai da yanda za ayi.
**************************
Washegari Juwaiirah ce zaune saman sallaya da goshin asuba ta na ta ibada, kamar wata babbar mata, Maman ta ta saba mata da tashin dare, dan ta sanar da ita cewar duk abinda bawa ke so ya roqi Allah da ikhlasi da yaqinin Allah zai biya masa buqatar shi to fa ba makawa Allah zai biya masa buqatar shi musamman in bawan nan ya yi addu'ar a lokutan karbar addu'a, wanda qarfe uku zuwa asuba ko huɗu zuwa asuba Allah na amsa addu'ar bayin shi dan lokaci ne mai mahimmanci ga bayin Allah, sannan ba a son mutum mumini ya zage ya dinga kwasar bacci daga farkon dare har zuwa qarshen dare ba tare da ya farka ya yi nafila ko da raka'a biyu bane,mu ke da buqata a wajen Allah Allah ba shi da buqatar mu, ya na daga cikin cikar imanin mutum ya dinga rokar Allah ya bashi ikon ganawa da shi a cikin dare ko da ya na jin kiwar yin hakan da kan kan shi ,to sai Allah ya bashi ikon tashi ɗin.
Hannu ta daga sama cikin qasqantar da kan ta a gaban mahaliccin ta ta ce,
" Ya Allah kai ne masanin abin da ke zuciya ta Allah ka biya min dikkan buqatu na na alkairi Ka sa Yaya Jabeer ya zama shine mafi alkairi a rayuwa ta duniya da lahira....."
Wannan addu'ar ce tafi daukan hankali na, nace tooooo waye kuma Yaya Jabeer? Addu'ar ta ta ci gaba bayan ta gama ta yi wa iyayen ta da yan uwan ta da dikkan muslmi, bayan ta idar ne ta hau karanta Qur'ani da zazzaqar muryar ta, har aka kira sallah ta gabatar da sallar asuba ta dora da azkar da karatu har gari ya waye, a sannan ne ta samu ta dan koma bacci zuwa qarfe takwas ta tashi, ta fara taya Maman ta aiki, bayan ta gama gyara gidan dan ba su ke girki ba balle ta taya ta aikin girki, wanka ta shiga ta fito,haka nan taji tana son yin kwalliya yau dan ita ba ma'abociyar yin kwalliya bane a koda yaushe,sai lokaci lokaci ta kan dan taɓa ,ta na gama sheqa kwalliyar ta me kyau ta buɗe akwatin ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 25