Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da ya ga ya na yawo a Saman screen ɗin wayar shi ne ya bashi mamaki ko dai har maganar rasuwar Alhaji kallah ta riske shi ne? " Oga Zaks" Shine Sunan da ya karanta a Saman wayar tashi,tsaki ya yi ya d'aga cikin dakiya ya kara a kunnen sa, kafin ya yi magana Oga Zaks ya riga shi, " Salihu kaji abinda wani ya kira ni yake faɗa min? Kana ina yanzu haka,shin da gaske ne Kalla ya mutu?" " Ni ma ban sani ba sai na isa wajen na gani, ka kashe wayar na kusa isa ga mutane can dai an taru a wajen sosai" kashe wayar ya yi ya qarasa,halin da ya ga abokin nashi a ciki ya gigita ƙwaƙwalwa da tunanin shi dan haka nan take ya yanke jiki ya fadi, wasu ne a gefe suka taimaka suka watsa masa ruwa ya farfad'o,da rarrafe ya yi wajen abokin nashi yana kuka, riqe shi mutanen wajen suka yi suna bashi hakuri, umarni ya basu akan su taimaka mai su d'aga gawar akai masallaci mafi kusa a yi masa wanka da sallah a binne shi kawai,dan kuwa basu da kowa balle a ce sai an kai shi gida wajen dangin shi,haka ko aka yi, nan take mutane suka taimaka aka d'aga gawar Alhaji Kalla aka kai wani masallaci da ke kusa,waya ya zaro ya sanar da Oga zaks, jikin Oga zaks ya yi sanyi amma dake zuciyar ta dake ko kuka bai yi ba, sai dai ma kawai ya masa ta'aziyya kawai yace in an kai shi yaje yana son ganin shi, kashe wayar shi ya yi yace, "Ba dole ma na fita daga wannan muguwar ƙungiyar ba, ai ko ba komai Kalla ya yi wa qungiya hidima ya cancanci azo kan gawar shi a mai addu'a amma wai in an kai shi na je, ko baka ce ba zaka ganni kuwa" Share hawayen shi ya yi shima yabi bayan yan tsiratun mutanen da suka gama rife Kalla a makwancin shi na gaskiya,mota ya fada ya yi gidan shi, tattaro duk wata dukiya tashi ya yi, yaje ya dakko ATM cards din shi, da makullan motocin shi, da takaddun filaye da gidajen shi da kamfani da komai ya zuba a akwati ya wurga cikin motar shi, ya sa kai dan zuwa gidan Oga zaks, Haka ya shiga motar shi ya tuqa bai zame a ko ina ba sai qofar gidan Oga Zaks, yana isa a tsaye a ka ya tsaya ma Oga Zaks , cikin bacin rai Oga Zaks ya ce, "Ya haka Salihu zaka zo ka tsaya min akai kamar wani sanda" Duk wata dukiya da Alhaji Salihu ya tattaro ya zube ta gaban Oga Zaks cikin haɗe fuska ya ce, " Oga ina son barin qungiya ba dan komai ba sai dan ina son na koma tsaftatacciyar rayuwa na tsira daga azabar da Allah zai yi min,sannan abinda ya faru yau da Kalla ya qara min son barin wannan qungiyar" Nan take ya kwarorowa Oga Zaks duk abinda ya faru da Kalla da shi kafin hatsarin da ya yi, nan danan jikin Oga Zaks ya ɗauki rawa, qaton cikin nan kamar ana buga ganga haka yake qara da karkarwa, maganganun sun shige shi sosai sun bashi tsoro,cikin rawar murya Oga Zaks da ya zama shi ne ya qirqirar masu wannan ƙungiya ta shaid'an ya ce, " To salihu ba za ai haka ba ka fita kai ɗaya? Ni kai na na wa'azantu da wannan abinda ya farun,yau kuma a yanzu zan tara mutanen mu na sanar da su abinda yake faruwa kuma ni da kai mun shirya barin wannan ƙungiya ko da za mu rasa ran mu kuwa, zaɓi ya rage wa sauran,wanda yaga zai fita ya biyo mu, wanda yaga zai zauna ga waje nan, amma zan so ace yanda ni ne na assasa wannan qungiya na rusa ta da kai na, dan ko na tafi zunubin zai ci gaba da bina" Wani irin farin ciki ne ya lillibe Alhaji Salihu dan bai taɓa zaton hakan ba, ya zaci zai sha wahala kafin ya amince mai, waya yasa ya kira mutanen su baki ɗaya,kusan awa biyu suka ɗauka kafin kowa ya hallara, fuskar Alhaji Salihu da ta sha kuka ya ba wa kowa mamaki, nan take kuwa Oga Zaks ya fara zayyana masu komai, cikin qanqanin lokaci wasu da dama suka aje makaman yaqin su, wasu kuwa suna ganin ai su akwai sauran lokacin tuba,tsawar da Oga Zaks ya daka masu ce ta dawo dasu daga cece kucen da suke ta yi, cikin bada umarni ya ce, " Na yanke hukunci wannan qungiya rushe ta zan yi da hannu na kamar yanda na kafa ta, wanda ya sake kafata shi ya sani, amma ni kam na gama , dan haka daga gobe zan rushe ta, tsakanina da dodo ko kashe ni ya yi babu komai fata na shine na kubuta daga cutarwar shi da ikon Allah,ina neman gafarar Allah ya yi min afuwa, ya ba wa wadan da na zalinta ikon yafe min a filin qiyama" Nan da nan sai ga Oga Zaks na yin kukan nadama,tabbas Allah shi ne mai shiryar da duk wanda ya so a lokacin da ya so, basu rufe baki ba suka ji gidan na wani irin qara mai firgitarwa,da jin haka kuwa mazajen nan suka hau gudun ceton rai, Alhaji Salihu ne ya ke ta qoqarin taimaka wa Oga zaks su gudu ya kasa saboda tsabar qiba da nauyin shi,sai ya kamo shi su tashi sai ya koma shab'ar ya zauna,daga ƙarshe dai dole ya dakatar da shi ya ce, " Salihu kai ta kan ka kawai, ni nasan tawa ta qare, da wannan uban tumbin nawa kake tsammanin samun gudu a gareni? Ka dube ni fa ka gani na ninka ka sau bakwai, ka barni kawai, abin da na aikata zan girba, a shirye nake dan na sadaukar da rayuwa ta na fanshi taku, saboda ni ne na fara komai, i think it has to end with me, just go now ! Ka gudu ! Kar ka juyo kar ka dawo baya, kar ka manta da ni ka dinga nema min gafarar Allah idan ka yi tsawon rayuwa," Tura Salihu ya yi da qarfi a dai-dai lokacin da wani qaton baqin zaki ya fito daga wani baqin d'akin da suke ajiye mutanen da suke tsafi da su yayo kansu, Salihu ɗiba ya yi da gudu ya bar wajen, Oga Zaks salati kawai yake ya na Kiran Sunan Allah tare da neman gafara a wajen Allah,tsabar tsoro da shiga tashin hankali har ya cika wandon shi da fitsari shataf bai sani ba, nan take ya hau tunanin ashe haka waɗanda suke bawa dodon tsafin nasu suke ji kafin su mutu, nan take ya ji qirjin shi na wata iriyar muguwar bugawa,cafka zakin nan ya kaiwa wuyan shi ya hau cinye shi,shure-shure ya hau yi na azabar fitar rai kafin daga qarshe ya yi shiru alamar ya mutu,Oga Zaks kam an tafi inda Kalla ya tafi, Salihu kuwa gudu yake kamar zai tashi sama , mota ya gani da makulli a jiki me ita wataqila tsabar tsorata ne ya hana shi ci gaba da tada ita ya gudu, dan harda takalmi qafa daya a cikin ta a ajiye, ruwa duk ya jiqe mazaunin driver maybe fitsarin shima ya sake kafin ya gudu,take Salihu ya tada motar ya debi hanyanyar kano dan bai ga ta zama a garin Abuja ba. ****************************** Tinda suka tashi daga bacci suka yi sallah suka hau gyaran gidan nasu tare da yin abincin safe zuwa rana, bayan sun gama ne suka yi wanka suka hau shirin zuwa ganin babyn tasu. Suwaiba aiki kawai take yi amma Jikin ta duk babu kwari,sannan ga wata iriyar fad'uwar gaba da take ji,Saudat ma in banda sharar d'akin su ba abinda ta tsinana, Salma da Suwaiba ne suka fi yin aikin gidan, ta rasa dalilin da ya sa take jin wani yanayi a tare da ita,ko da ta sanar da Mama Balki sai ta koyar da ita wasu addu'o'i, nan take ta yi ta maimaita addu'o'in a bakin ta, bayan sun gama shiryawa ne suka yi wa su Goggo Sarai Sallama su ka ɗauki hanyar gidan Juwairah me jego, sun isa dai-dai Jabeer ya fito riqe da towel din da yake gasa mata jiki da shi sai suka tsaya kallon shi,daga bayan shi kuma Juwairah ce ta fito tana fad'in, " Ni dai gaskiya a canja min me yi min wanka a gidan nan kai gaba ɗaya mugunta ka ke yi min, ni ban ma taɓa jin inda aka ce namiji ke yi wa mace wankan jego ba dan h.......... " Maganar ta ce ta maqale dan ganin yayun nata na shigowa, niyyar ta ta koma bandakin dan juyawa ta yi tare da damqe bakin ta zata shige bayin, cikin dariya Saudat ta yi sauri ta isa ta ruqo ta, " Me Yah Jabeer din ya ke maki? In kina son a canja maki mai wanka sai na dinga yi maki, amma ni sai ruwan ya tafasa sau uku sannan zan yi amfani da shi" Zaro ido waje Juwairiyyah ta yi sannan tace, " A'a Adda Saudat a barmin Yah Jabeer ɗin mu lallaba a hakan" Dariya suka kwashe da shi, Jabeer yace, " ku ji yarinyar nan fa, wai zata lallab'a a haka sai kace wani muguntar nake yi mata" Nafee ce ta amshe da cewa, " Hmmmm Yah ayi shiru kawai da wannan maganar amma ko d'azu na jiyo qarar ta" Hararar ta ya yi yace, " Suwaiba ku shiga ciki mana kuka tsaya a waje" shiga suka yi har me jegon, Nafee ce ta bar d'akin sakamakon kiran ta da Innarmu ke yi, zuwa ta yi ta bata wani kwanika biyu ɗauke da abinci ta kawo wa juwairah, amsa ta yi ta tafi bangaren juwairah, sallama ta yi musu kafin ta shiga suna ta hira kowa na yaba kyaun jaririyar da sunan ta, "Wannan suna na :yan gayu anya kowa zai iya fada kuwa kar a je a b'ata mata suna kin san halin mutanen mu" Cewar Salma, dariya Nafee ta yi da ta qarasa aje kwanon gaban Juwairah dake shafa man kad'e a cikin ta ta ce, "Ai jiya sai kun sha dariya dan daga Innarmu har Abban mu basu iya fada ba, Innarmu Abaras take cewa Abbah kuma Abra" "Ai ko wannan suna zan so jin shi a bakin Goggo" Cewar suwaiba da ta tuna da Goggo Sarai, dariya suka bushe da ita dikkan su sun san a kwai case din fad'an Abrar a bakin Goggo sarai, Juwairah ce ta gama shiryawa Suwaiba ta d'aure mata cikin ta, sannan Jabeer ya shigo ɗauke da plate da Spoon da cup sai tea spoon, gaishe shi suka yi dikan su ya amsa su cikin sakewa, nan dai suka yi masa barka da samun wannan qaruwar da aka yi mai albarka, godiya ya yi ya isa gun kwanukan ya buɗe, farfesu ne na naman qaramar dabba, yasha kayan qamshi irin na jiya harda rid'i a ciki, gefe kuma kabewa ce innar mu ta dafe ta ta yi laushi ta dame ta ta yi kamar kunu, sannan ta zuba masa madarar shanu mai matuqar yawa sai zuma, zuba mata ya yi a cup din ya zuba mata naman a plate ya haɗe fuska alamar ba wasa ya ce, " Gashi maza taso ki ci ki shanye, dan bana son kina zama da yunwa" Turo baki ta yi gaba ta ce, "Ni fa na qoshi Yah Jabeer,dazu da asussuba na qarasa cinye naman jiya saboda yunwar dana tashi da ita, yarinyar nan ci gare ta kamar Innar ta Salma" Dariya suka sanya dikkan su, Jabeer ne ya ce, " Ai kuwa baki isa qoshi ba da dan ragowar naman nan, in baki matso kin fara ci ba zan maki d'ura a gaban su," zaro ido ta yi waje sai gata a qasa ta saka pilo ta haɗe qafafun ta waje ɗaya ta miqe su tare da danna hannun ta a plate ɗin naman. ( haka ake so mai haihuwa tana zama, kai ko ba haihuwa ba ma, ba a son zaman nan na ware qafa da wasu matan ke yi, kabewa kuma da madarar shanu da zuma duk wadda ta haɗa ta sha zata bada labari bazan ce komai akai ba) Kaiwa baki ta yi ta fara ci, wani daɗin da ya ziyarce ta ne ya sa bata san sanda ta cinye ba ta shanye kabewar dika,murmushi Jabeer ya yi da suke ta hira da qannen na shi ya ce, "Da kyau yarinyar kirki" Sumbatar Saman kan ta ya yi sannan ya dauke kwanukan zai fitar Salma ta yi saurin Karb'a dan ta fitar da su cikin jin nauyin shi ta ce, "Haba yayah muna nan ai sai ka bar mana aikin in mun tafi ka ci gaba" Murmushi ya yi ya sakar mata yace tare da cewa, "Ni bari naje na shirya zan wuce Abuja yau dan zuwa qarasa shirye-shiryen komawar mu bayan suna" Anan ne ya sanar da su komai game da aikin da ya samu a Abujan, murna suka taya shi , da fatan alkairi suwaiba da saudat har ma da Salma suna jinjina iko na Allah, ko da suka auri mazajen da ke son su kuma masu kuɗi ba wadda ta taɓa samun irin kulawar da Juwairiyyah ke samu, gashi kuma yanzu Allah ya nufa ashe ita ce asalin 'YAR ABUJAN gasken,wanka ya shiga ya yi, ya dawo d'aki ya wuce su dan ya shirya,Juwairah ce ta tashi taje wajen shi ta zauna a gefen gado yana shiryawa suna hira tana haɗa masa kaya a jaka, duk da hana tan da yayi sai da ta haɗa masa, bayan ya gama ne ya dauki Abrar ya mata addu'a tare da sumbatar fuskar ta, sannan ya haɗe babyn da maman ya rungume, a bakin kofar fita daga d'akin su zuwa parlour suka gama Sallamar su ya yi wa su suwaiba sallama ya fita, bai jima da fita ba ya yi mantuwa dole ya dawo dan daukar mantuwar da ya yi, " Af nayi mantuwa" " Me ka manta honey?" Matsawa ya yi kusa da ita ya janyo ta jikin shi yana mata kallo qasa-qasa cikin sauri da gane mantuwar da ya yi Juwairiyyah ta hau ja da baya ta na son kwace kan ta a hannun shi ta ce, "Yah Jabeer ka bariiii su Addah Suwaiba na nan fa, ni dai dan Allah ka daina bani kunya a gaban mutane," Ta qarasa faɗa tana 'yar kwallar ta dan ya kyale ta, lakece mata hanci ya yi yace, "Ina baki kunya fa ki ka ce? Ai shikenan mun kusa komawa gidan mu mu uku, mu yi abinda muke so ba tsoron zan kunyata ki a gaban mutane ko?" Dariya ta yi na samun nasara akan shi ya hakura da yin abinda ya fake da mantuwa ya dawo domin sa, Juwairiyyah ta yi masa addu'a ta rako shi suna zuwa palour ta yi fuska ta zauna kamar ba tare suke ba, kunya ce da ita kamar me shi kuma duk abinda zai yi matsawar bai saɓa wa shari'a ba babu ruwan shi kowa ma ya gani, meye abin jin tsoron kar wani ya ga ya na kyautata wa matar shi? dariya suke yi mata Salma tace, " kin ji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa, mu zaki layancewa?" Dukan wasa ta kai wa salman tace, " Adda Suwaiba kin ganta kooo" Dariya suka yi, suwaiba ta ce, "Juwaireren Mama ya kamata ki rage shagwab'a yanzu kin haihu," Nafee ce ta fashe da dariya,ita kuwa Juwairiyyah sai ta murguda mata baki sannan ta kauda kai, ranar a gidan Juwairiyyah su suwaiba suka wuni da yamma Suwaibah ta yi wa Juwairiyyah wanka, nan take Juwairiyya ta ce wankan ta ya fi na Jabeer daɗi ta dinga yi mata ko da ya dawo. ******************************* Ahj Salihu ya iso kano lafiya, da kyar ya gane gidan su suwaiba saboda ko a da ba su zuwa zance gidan su sai dai su su suwaiban su je hotel su same su a can,a qofar gidan su ya tsaya....... [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 30: Jingine yake a Jikin motar da ya je da ita saboda rasa ɗan aike da ya yi,bayan haka Alhaji Salihu yana matuqar jin nauyi, kunya, da tsoron wacce Karb'a za a yi masa a gidan su suwaiban,juyawa ya yi ya kife kan shi a Jikin motar ya na fidda wani irin numfashi wanda ke nuni da halin damuwar da yake ciki. Mai adaidaita sahu ya na ajiye su ta gane mijin nata,domin kuwa da shi take kwana da shi take tashi a ran ta, Alhaji Salihu kuwa na nan tsaye wasu siraran hawayen nadamar rayuwar shi ta baya na bin kuncin shi, ga rashin babban aboki kuma ɗan uwan shi da ya yi, a gaban shi zakin nan ya kaiwa Oga Zaks cafka a wuya, da sauri ya d'aga kan shi cike da damuwa ya ke tunanin yanzu me zai faru idan Shima zakin ya biyo shi har nan dan ya hallaka shi? Anya hakan ba zai jawo wa Suwaiba da iyayen ta da 'yan uwan ta matsala ba? maybe this is a bad idea for him to risk there life for his mistake,juyawa ya yi dan ya bar wajen cikin gaggawa kafin wani ya gan shi, cikin wata iriyar murya mai cike da shauqi da kewa ta kirawo Sunan da take Kiran shi da shi, " Baby ! kai ne a qofar gidan mu da gaske? Me ka ke yi a nan?" Qarasawa ta yi da gudu ta faɗa qirjin shi tana kukan kewar shi da ta yi, shima rungume ta ya yi kamar wani zai k'wace masa ita, gyaran murya Salma ta yi masu ta ce, " Adda a waje kuke fa kin san halin mutanen mu, ba za a yi tunanin mijin ki bane za a fara qananan maganganu mu shiga daga ciki " Janyewa suka yi daga yanda suke ta ja hannun shi zuwa cikin gidan su ta tsaida shi a soro, Saudat kam ta qame qam a wajen, dan zuciyar ta bugawa kawai take yi, ina nata mijin yake? Ya aka yi suka rabu yau bata gansu a tare ba bayan ta san ba sa rabuwa? Wannan tambayoyin Salihu ne kawai zai amsa mata su bayan ya samu nutsuwa, dan ta kula shima ba a nitse yake ba, Salma da ta yi gaba ne ta dawo baya ta ja hannun yayar ta ta suka yi cikin gida, ta kula da cewar Saudat na cikin damuwa tin safe yanzu kuma data ga Salihu shi ɗaya ba nata mijin damuwar ta ta qaru akan ta da, ko ba komai tana son mijin ta kawai halayen shi ne yasa ta gudowa ta qi komawa gare shi dan ba zata zauna a kashe ta a banza ba. Sun riga da sunyi Sallahr la'asar a gidan Juwairah dan haka bayan sun shiga sanar da Baban su suka yi zuwan Alhaji Salihu ga kuma a yanayin da suka gan shi a ciki, da fari Baba ya hasala ganin rashin kunyar Alhaji Salihu na zuwa gidan shi bayan abinda suka yi wa yaran shi,da suka samu ma bai kai ƙarar su ba shi ne har zai zo to ya ce musu me? amma da Mama Bilki ta taushe shi sai fushin nashi ya sauka, ta shawarce shi da ya tafi cikin nutsuwa ya buɗe ma Salihu zuciyar shi ya ji me ke tafe dashi, in yazo da rainin hankali gidan su yazo duk abinda Baba ke so zai iya yi masa ya huce haushin shi, ta bashi goyon baya ya yi masa duk abin da yaso, kad'a kai ya yi cikin qunan rai ya fita amma sai ya danne bacin ran nashi, kamar yanda matar tashi ta bashi shawara. Sallama ya yi masa ya miqa masa hannu dan su gaisa,amma sai Alhaji Salihu ya noqe ya qi miqa nashi hannun ya durqusa qasa yana mai sakin kuka mai ban tausayi tsakanin kukan shi ya fara magana, "Baba ni mai laifi ne babba a wajen Allah da kuma ku, babban mai zunubi ne ni Baba,na taso ban san menene ilimin addini ba, duniya kawai na saka a gaba, bani da ilimin addini daya ratsa zuciya ta da zai hana ni aikata dukkan abubuwan dana aikata a baya, dan son ka da Allah da Annabin shi ka yafen abinda na yi wa Suwaiba, ka yafewa abokina d'iban jini da cire wa Saudat mahaifa da ya yi domin ya mutu a yau, a dazun nan ta hanyar hatsarin mota" Wani qara kunnuwan saudat suka ɗauka shuuuuuu, tabarmar da ta d'akko dan ta kawo wa Alhaji salihu da ruwa a jug ne suka zube a qasa, kafin ta qara d'aga qafar ta ta isa wajen su Baba ta yanki jiki ta faɗi, da gudu Baban su ya yi kanta, ya d'aga ta ya yi ya shige ciki da ita, ruwa suka yayyafa mata ta sauke ajiyar zuciya mai karfi daga nan kuma a hankali ta fara buɗe idanun ta,a kan Alhaji Salihu idanun ta suka zuba wanda ya shiga gidan ba tare da izini ba dan ganin halin da matar abokin nashi ta shiga, kuka ta saka ta kai masa wani wawan naushi a baki tare da fad'in , "Mugaye azzalimai kawai, wato kashe shi kuka yi ko? Dan na san yanda Kalla ke sona zai biyo bayana ko bajima ko ba dad'e, shine kuka kashe shi saboda ba ku son ya bar azzalumar ƙungiyar ku ya zo gare ni," " Saudat ya kamata ki natsu,abinda ki ke zargi ba shi bane ya faru,ni da ki ka ganni ni na shawarce shi akan mu fita daga qungiya dan son da muke maku, da kuma tsoron Allah daya shige ni a wannan lokacin, amma Kalla ya qi ya mun bayanin shi akwai sauran lokacin tuba ba zai fita ba, na masa nasiha da in mutuwa ta riske mu kan tuban fa, yace akwai lokaci, yana fita ya yi hatsari mummuna, kan shi ya fashe qafarshi ta......." " Stop it ! Stop ! Ba na son ji..bana so..bana son ji" Fashewa da kuka ta yi mai ban tausayi, a nan dai Alhaji Salihu ya qarasa labarta masu komai daya faru har da shugaban qungiyar tasu wato Oga Zaks. Goggo Sarai ta fito dan ta yi wa Alhaji salihu masifa akan rufe su da suka yi da zaluncin da suka yi wa yaran ta ta ji abinda ke faruwa,nan da nan sai jikin ta ya yi sanyi,sai kawai ta koma kwallar tausayin yaran ta,tabbas wannan ba laifin kowa bane illa laifin ta, ba su taɓa sanin Saudat na son mijin ta haka ba sai yanzu, a zaton su tun da ta taho ta bar wata soyayya da duk wata rayuwa da ta yi a baya jira kawai take ya zo dan kan shi ya sake ta ta sake sabuwar rayuwa, taimaka mata Mama Balki ta yi ta kai ta d'akin su ta kwantar da ita, kuka kawai take yi ta na jin kamar a gaban ta komai ya faru da mijin nata,cikin tausayawa Mama Bilki ta ce; " Saudat ki yi hakuri , na san rashin masoyi akwai zafi, amma soyayyar da zaki nuna wa kalla a matsayin shi na mijin ki shine addu'a, tinda bai sake ki ba ke ki ka qi komawa, dan haka daga yau zaki fara takaba, har tsawon jini huɗu da kwana goma,dan haka har abada mijin ki na buqatar addu'ar ki, baya buqatar kukan ki, kin ji" Ta qarasa tare da shafa kan ta cike da tausayawa, cikin sakewar jiki ta dora kan ta a kan cinyar Mama Bilki hawaye masu zafi na fitowa daga idon ta, nan take ta hau kwarorowa mijin nata addu'a, mama Bilki na amsawa,a haka har ta samu sauqin zuciyar ta itama, Salma na maqale tana tina nata tsohon mijin tana hawaye, ga tausayin Addar ta ta da ya dame ta. Alhaji salihu kuwa bayan ya yi alwala ya yi sallah ne ya zauna cin abinci Abba ya ce idan ya gama su je gidan Yayan

Chapter 21 of 25