d'umamen tuwo ta kai masa dan ya karya, a shirye ta gan shi tsaff ya na sake duba jakar shi da k ta hada masa tun cikin dare.
Cikin wata roba fara ta zuba masa meat pie sannan ta zuba masa zob'on da ta haɗa tun jiya da yamma mai daɗi a gora ta d'aure bakin ta da kyau ta saka a leda har biyu dan kar ya b'ata masa takardu ta zuba duk a jakar ta zuge,kallon ragowar meat pie din ta yi ta ga ba laifi da yawa za a samu wanda za a baiwa surukan su idan sun zo da rana dan neman auren Nafee, ɗan girki kawai zata qara yi shikenan sannan an fita kunya tunda sun san gidan da za su zo neman auren ba na masu da shi bane, d'aki ta shiga ta ga ya kammala komai ita yake jira su yi sallama,ta na qarasa shiga d'akin ya ja ta jikin shi ya na bin fuskar ta da kallo ya ce,
" My princess ba abinda zan ce maki sai dai na yi maki fatan shiga aljanna, tin da ance sai miji ya yarda da matar shi sannan za ta shiga aljanna, My Juwairiyyah na yarda da ke ina rokon Allah da ya sanya min ke a aljannah madaukakiya, ke macen kwarai ce Juwaireren mama, matar da kowanne namiji zai yi fatan samu,macen da zan iya nunawa duk duniya ta gani ba tare dana kunyata ba, Allah ya sauke ki lafiya, ya shiryar min dake , Allah ya qara miki imani, kinga ga riqe wannan ba yawa kwana biyu zan yi kamar yanda na sanar dake, ki yi ta tayani da addu'a inna samu aikin nan zamu samu hutu sosai, zan jiyar da ke daɗin da baki taɓa zato mace zata iya samu wajen mijin ta ba, Juwaireren Mama ina son ki, Allah ya yi maki albarka"
Tun da ya fara magana Juwairiyyah ke murmushi sai dai ya na cewa Juwaireren mama ta turo baki tana buga qafa,sannan ta ce masa,
" Ni dai Yah Jabeer bana so, taso ka tafi kar ka makara, Allah ya karen kai mijina kaje lafiya ka dawo lafiya, Allah ya bada sa'a a abinda aka tafi nema, inshaa Allahu kai me nasara ne akan komai na alkairi da ka sa a gaba, dan haka kar ka ji wata damuwa ko ka sa shakka a lamarin,zaka iya miji na saboda kai din na daban ne a cikin mazaje,karka manta da karanta lahaula wala quwwata illa billahi, da hasbunallahu wa ni'imal wakeel,sai kuma hasbunallahu sa'yu'utinallahu min fadhlihi inna ilallahi raghiboon,Allah zai zama jagoran ka, zai taimaka maka ya kare ka, ina son ka Yah Jabeerun Baba"
Ta karasa maganar ta tare da miqewa da sauri tana dariya bin ta ya yi ya cafko ta ya haɗe ta da gini ya na dariya Shima ya ce,
"Maimaita me kika ce in ba tsoro ba"
Turo baki ta yi cike da shagwab'a tace,
"Yo ni me nace, dan dai kawai an ga yau mijina zai yi tafiya shine za a yi min yar qure a ci zalina, Yah Jabeer irin wannan kallon da kake yi min ji nake kamar na dawwama da kai a haka a tsaye ba tare da duniyar ta juya ba"
Ta karasa maganar ta cikin yin qasa da muryar ta, wani irin farin ciki ke ziyartar zuqatan su a wannan lokacin suna jin kamar kar su rabu da junan su, a cikin ran su kowa na yaba kyau irin na dan uwan shi, sumbatar ta ya yi da salon bankwana wanda Juwairiyyah ta biye masa dan faranta ran mijin nata, Nafeesa ce ta yi sallama ta shiga dayake Juwairah tace ta zo su yi komai da wuri zata je gida a yau d'in, janye jikin shi ya yi a kasalance ya riqe hannun ta ita kuma ta kwantar da kanta a jikin shi, fita suka yi tare idon ta taf hawaye, yau ce ranar farko da zai yi tafiya mai nisa tin bayan auren su, saurin maida kwallar ta tayi kar ya gani hankalin shi ya tashi, sai dai inaa ta makaro dan kuwa ya gani,cikin muryar lallashi ya ce,
" Haba my Queen, ki kwantar da hankalin ki mana, inshaa Allah jibi da yamma kina maqale a jikin mijin ki kamar haka,daga wannan tafiyar ba zan sake yin wata tafiya ba ke ba ko ina zan je to fa qafa ta qafar ki kin ji"
Kamar wadda ya ce wa ta yi kuka haka Juwairiyyah ta b'are baki irin na yaran nan masu rikici ta fara kuka, rungume ta ya yi a jikin shi ta yi kukan ta son ran ta da kan ta ta yi shiru ta sake yi masa addu'a, suka fita tare har Nafee suka raka shi wajen Innarmu Itama ta masa addu'a daga qarshe ta hau tsokanar Juwairiyyah,
"Tooo kukan rabuwa da masoyi aka shaaaaa ?? Hoh yan zamani ba ko kunya to d'akko mayafi ki bishi kawai 'yannema sai kace cinye ki za mu yi kafin ya dawo"
Juwairiyyah na jin haka ta saki hannun Jabeer ta taka da gudu ta bar wajen tana dariya, suma dariyar suka yi mata, sai da taje baqin qofar shiga wajen su ta juya, dan tsuke bakin shi taga yayi alamar kiss, ta waro ido ta kalli su Baba Balarabe dake gefe zasu raka shi qofar gida, rufe baki ta yi da hannun ta ta fada wajen nasu tana dariya,
" Allah sarki mijina,kaje lafiya ka dawo lafiya cikin sa'a da nasara, tare da kariyar Allah"
Nafee ce da ta biyo bayan ta tace
" Ameen masoyan asali"
Murmushi suka yi wa junan su sannan suka shiga kitchen dan fara aikin da ke gaban su, leqa parlour Juwairiyyah ta yi ta duba lokaci ta ga har takwas da rabi ta wuce,cikin sauri ta ɗauki kwaryar da ke ɗauke da masarar da aka barza ta duba ta ga tabbas za ta isa su yi dambun masara, nan da nan suka je suka tsinko zogalen da Juwairah ce ta shuka da hannun ta da alayyahu, sai albasar su mai lawashi, gyarawa suka yi suka dake gyad'a, da kayan qamshi attaruhu da maggi da gishiri suka saka yanda zai isa ya yi daɗi suka zuba wa wankakken tsakin su suka dora a wuta.
Cikin qanqanin lokaci dambun masara mai daɗi ya haɗu, man gyad'a Juwairah ta soya da ya ji albasa, suna kammalawa Juwairiyyah ta d'akko mazubi masu kyau ta zuba komai a inda ya dace har zob'on da meat pie sai da aka zuba su a waje mai kyau da tsafta.
Nafeesa ta ji daɗi sosai dan haka duk inda Juwairiyyah ta sa kafa Nafeen na biye ta na godiya da addu'a har saida ta ba Juwairah haushi,dan kuwa godiyar ta yi yawa a cewar ta, ajewa suka yi a gefe Juwairah ta sa Nafee deb'o wani alayyahun da albasar mai ganye, ta sa ta gyara su ta daka kayan miya wannan karon harda tumatiri, jelop rice mai daɗi ta dafa wadda ta yayyanka ɗan naman a ciki qanana ,kasancewar nama bashi da yawa yasa Juwairah tace bari su yanka qanana sai a soya sama2 su saka a abincin, har da dan carrot ɗin su, nan da nan sai ga girkin da su suke ganin anyi a talauce ya koma a yalwace, dan kuwa wata macen ma ko an kawo mata kayayyakin girkin da ya fi wannan ba lallai ta tada abinci mai kyau da daɗi kamar wannan ba.
Wanka ta tafi ta yi ta sa Nafee taya ta gyara gidan, dan bata son fita ta bar gida da datti in ta dawo ranta baya yi mata daɗi, sannan kuma ta san idan bata gyara ba zata dawo da gajiya sai dai a bar gidan ya kwana da datti kenan
Wasu matan taqamar fita za su yi unguwa sai su bar gidan kamar bola su tsallake su tafi abun su,idan baki gyara ba ki ka tafi ki ka dawo ki na iya yin baqin kunya su tadda gidan ki g kaca-kaca, ko kuma ki dawo a gajiye ga shi maybe miji ya kusa dawowa, shima ya dawo yaga yanda ya fita haka ya tarar wataqila harda qarin datti ma, amma in kika gyara gidan ki fes in da hali ma har girki ki yi ki ajiye, da kun dawo wanka zaki yi kawai ki faɗa gado ki huta,maybe sai bacci ma tinda baki da aikin da za ki yi.
Sai da ta gama shirya wa tsaf sannan ta zauna ta ci abinci a gaggauce ta rufe sashen ta ta sanya mayafin ta ta riqe jakar ta a hannu mai ɗauke da waya da ɗan kud'in abun hawan ta ta wuce bangaren Innarmu ta yi mata sallama ta dau hanyar gida cike da zumud'i da d'okin ganin iyaye da 'yan uwa ta.
Mai adaidaita sahu na ajiye ta ta sallame shi ta shiga cikin gidan su bakin ta ɗauke da sallama,ba wanda ya ji ta ma ballantana a amsa mata saboda ta isko ana ta daru akan komawa Abuja ,ita Saudat tace bazata koma ba, Suwaiba kuma ta shirya tsaf da shirin tafiya ta na tursasa Saudat akan sai sun koma tare Goggo ma ta sa ta a gaba da magiyar ta daure ta koma, ba zai qara dukan ta ba, Shima kuma Baba ya kafe Saudat ba zata koma ba tinda bata so mijin nata ya biyo ta da takardar sakin ta idan a son shi ne ma ita kanta Suwaiban ba za ta koma ba,ganin abun ya qi ci ya qi cinye wa ne ya sanya Mama Bilki cewa,
" Ayya Goggon su tinda ta ce bazata koma ba a barta mana in aka kwan biyu kin taushe ta sai a maida ta dakin ta"
" Ba laifi yau ɗaya kin yi magana mai ma'ana,Allah ya kaimu ta huce an maida ta ɗin, dan kuwa 'ya ta ba zubin zaman Kano bace zubin rayuwar Abuja ce ah toh"
Cike da rashin kunya Saudat ta kalli Mama Balki ta ce,
" Ka ji Maman nan ina ruwan ki da sa mana baki a maganar 'yan d'akin mu? To bazan koma ba ɗin har abada, sai dai ya biyo ni da takarda ta, ke kuma Allah ya bada sa'a zaki ce na fada maki, dama saboda irin wannan halin naki na ki yarda na sanar da ke tun a can da na sanar da ke da kin sa an kashe mu a banza"
Da jin kalaman Saudat sai Mama Balki ta bar wajen ta wuce d'akin ta,Juwairah kuwa sai ta qarasa cikin sake yin sallama,ta dan duqa ta gaida Suwaiba da ke qoqarin qota ta ta wuce, cikin b'ata fuska suwaiba tace wa Juwairiyyah,
" Malama bani waje driver na na jirana ina da wajen zuwa mai nisa, ko dake ke ya za a yi ki san nisan da ke tsakanin Kano zuwa Abuja tinda kin qunshe kan ki daga Kano sai kano?"
Ta na gama magana ta saka hannu a jaka ta d'akko kudi mai ɗan yawa ta watsa wa Juwairiyyah a jikin ta tace,
"Ga shi nan dama na san gaisuwar kenan, shine ya sa ki zuwa da wuri kar mu tafi ba a baki rabon ki ba"
Ta sa kai za ta bar gidan cike da takun kasaita ita a dole ga mai arziqi, cikin qunci da haushi tare da fushi irin na masu ciki in an tab'o su Juwairiyyah ta bi bayan ta ta jawo hannun yayar ta ta, kamar yanda ta wurga mata kudin a jiki itama ta wurga mata a fuska ta ce,
"Ashe har yanzu baku canja hali ba? Ban zo dan wannan banzan kud'in naku ba, nazo dan na ga 'yan uwana dana dad'e ban gani ba da kuma iyaye na, na zo domin zumuncin Allah ne, dan haka u keep ur filthy money with u,it will help u some day"
Ta juya tare da shigewar ta cikin d'akin Mama Balki ta bar kowa na binta da kallo baki sake, tab'e baki Suwaiba ta yi daga baya ta dauke kud'in ta ta shiga mota tana d'aga ma Baban ta da Goggo hannu, suka juya birnin tarayya ABUJA.
Komawa ciki suka yi in da Baba ya shiga bangaren Mama ya isko Juwairah da Salma, Salma tana ba Juwairah hakuri akan komai da ya faru a baya, Juwairiyyah na ganin baban nasu ya shiga sai ta miqe da kyar dan ta durqusa ta gaishe shi, shi kuwa sai fad'in tayi zaman ta yake yi amma saida ta isa gare shi,ta durqusa ya dafa kafad'ar ta ta gaida shi tare da fad'in,
" Babana na yi kewar ka ba adadi ina ta so na zo na gan ku tunda Mama har yau bata je d'aki na ba ta sanya min albarka"
" Juwaireren Mama nima na yi kewar ki sosai, da fa jibi muke saka rana zani ni da Salma mu gan ki, ki rabu da maman nan taki da alama sai na fara Kiran ta tsohuwa tunda ta na yi mana halin tsoffi"
Turo baki ta yi alamar shagwab'a ta ce,
"Babaaaa"
Dan ta riga ta gano faɗa kawai Shima ya yi ba zuwan da zai yi, shi ɗin ma kamar Mama Balki yake tun da aka yi mata aure ya daina zuwa gaida yayan shi a gida sai dai ya tadda shi a masallaci su gaisa ya koma gida,dariya suka yi dikan su Mama Balki ta ce,
" Oh mai hali baya fasa halin shi an girma amma shagwab'a na nan"
Haka suka dinga hira cikin nishad'i da annashuwa, nan da nan Salma da Juwairah suka qara shaquwa, hira suka shiga yi Salma ta ba ta labarin abinda ya dawo da ita gida, Juwairah akwai tausayi da saurin kuka dama,tausayin yar uwarta ne ya cika ta tai ta kuka kamar wadda aka daka, sai da ta gama ta rungume ta tace,
"kar ki damu yar uwa, da kin haihu zaki samu miji na gari inshaa Allah mai kud'in dai da kike so da yardar Allah"
" A'a Juwaireren Mama banni da talakan ma zan zauna ni ai yanzu talauci baya bani tsoro tunda na ga na gidan Talle"
" Kaiii Salma harda ke a Kiran wannan Sunan ko"
" A'a nima yau tab'awa na yi ai, ai baki taba jin na fada ba ko? To qara'i nai na da da ban tsokane ki ba"
" To shikenan ke kaɗai na yarda ki ce man Juwaireren Mama, ke ma iya na sati ɗaya kacal"
Ta faɗi hakan cike da nuna ita ɗin yar farin maman ta ce, dariya suka yi harda iyayen su dika, anan Ammar ya tashi daga bacci saboda shewar da suke ta yi, da sauri Juwairah ta isa ta d'akko shi, sai kallon ta yake yi, wasa take masa ta ji yana qoqarin yin magana,
" Mamma"
Shine abin da ya furta, daɗi ne ya kamata ta ce,
" laaaa mama yana magana dama?"
" A'a ya dai iya barna wannan"
Dariya suka yi suna kallon Ammar da ke taya su dariyar Shima,haka Juwairah ta gama yinin ta cijin jin daɗi,dan kuwa a tare suka yi girkin rana ita da Salma,ganin suna girki tare ne ya sanya saudat fitowa ta na ta auna masu rashin mutunci kala kala,amma ba wanda ya kula ta,dan kanta ta gaji ta koma daki, kyaliyar Mama Balki suka koya irin abun nan na mugun bata wa duk wanda yake maka masifa rai.
Ta bangaren Suwaiba mutanen ABUJA kuwa sun isa Abuja lafiya a matuqar gajiye kamar ita ta yi tuqin, tana isa ta tarar da masu aikin ta sun gyara gida ko ina fesss sai tashin kamshin turaren wuta yake yi,ga girke girke nan an yi na tarbon ta,ta na gama buɗe wa ta shaqi qamahin girkin sai kawai ta saki murmushi tare da fadin,
"Amma gaskiya Saudat shashasha ce, ni yanzu ina zan bar wannan gara ta wuce ni akan zargin banza da wofi? Hummmm bari ma na je na yi wanka na zo na ci na sha na yi hani'an gidan uba babu an dawo gidan miji ai sai a shoshale"
D'akin ta ta wuce direct wanka ta faɗa, bayan ta gama ne ta shirya cikin qananan kaya ta feshe jikin ta da turare ta kwanta a gado ta na latsa wayar ta ta ce,
" Wawuya, yaushe zan bar wannan daula ta wuce ni, ana ki dawo kina wani ke gida yafi gidan miji, ai ni da barin Abuja sai da ziyarar ganin dangi"
A haka ko abincin bata samu ta koma ci ba bacci ya dauke ta, cikin baccin ta ji wani zafi kadan kamar an soke ta da wani abu mai tsini ta so buɗe ido ta ga menene amma ko bude ido bata sake iyawa ba ta lula duniyar duhu..........
[22/07, 8:44 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 23:
Gobe ne ranar da Jabeer zai dawo gida daga wajen interview da ya je yi a Abuja, waya suke yi da Juwaireren shi wadda ke kwance a gadon ta da ya sha gyara kamar Jabeer na gida dan,bata daga cikin matan da ke qin gyara d'akin su saboda taqamar miji ya yi tafiya,hira suke sha ta soyayya gaba ɗaya Juwairiyyah ta shagwab'e masa ta susuta masa lissafi, ji yake yi kamar ya dawo a daren ko da fuskar ta ne ya kalla, ya san zai ji nishadi, kwantar masa da hankali ta yi da cewar gobe suna tare da junan su da yardar Allah dan haka kar ya damu ya qara haƙuri,dole jabeer ya hakura ya daina yi mata shagwab'ar da ya ke sanya ta nishad'i da dariya, Itama ta na jin ta kai wata a wajen miji tinda duk girman shi ya yarda ya amince ya bayyana mata yarintar shi.
Suna gama hirar su ta soyayya ta tuna masa kar ya manta fa ya yi addu'ar bacci kafin ya kwanta,sai su ka yi addu'ar tare suka kashe waya, bayan cika juna da "I love u", haka suka yi bacci cike da matsananciyar kewar junan su.
Da sassafe bayan tayi sallahr asuba tayi abubuwan da suka zama na al'adar ta da safe kamar yanda kuka san Juwaireren Mama, taso yau ta bar gyaran lambun ta da ta yi a cikin gidan saboda sauqaqa masu wahalar rayuwa sai ta ga dacewar ta gyara ɗin in yaso daga baya ta gyara gidan ta da girke girken tarbon mijin nata.
Da misalin 9:28am Juwairiyyah ce sanye da doguwar riga mara nauyi mai hannun shimi, ta dauki kayan gyara lambun ta ta fara gyara abubuwan da suke da buqatar gyaran, da ke ta na da saurin aiki cikin qanqanin lokaci ta gama cire ciyayi da bawa shukokin nata ruwa sannan ta ajiye komai inda ya dace ta wuce d'akin ta ta gyara shi ta hanyar sauya wankakken zanin gado da sauya wankakkun labulaye.
Tattare zanin gado da labulayen da ta sauya ta yi zata fitar Nafeesa ta yi sallama, cikin ɗan haɗe fuska Nafeesa ta ce,
" Haba matar Yayah ai sai ki kirani, da wannan tsohon cikin haihuwa ko yau ko gobe Zaki zauna ki na aiki mai wahala haka? Salon kawai ki ja mana wani aikin, habaa gaskiya ban ji daɗi ba"
Ta qarasa maganar ta ta na karb'ar kayan hannun Juwairiyyah, murmushi Juwairah ta yi ta dafa kafadar Nafeesa da ke kumbura baki ita a dole Fushi take yi sannan ta ce,
"Kar ki yi fushi da ni 'Yar qanwata,na jima ina so in sanar da ke ina matuqar jin daɗin yanda ki ke bani girma a gidannan ba dan na girme ki da shekara ba sai dan sanin darajar ɗan uwan ki da kuma mutunta shi da ki ke yi har ta dalilin haka nima ki ke daraja ni,na jima ina mamakin yanda ki ka ajiye duk wata quruciya da yarinta da muka ci ki ke kasa Kiran suna na kai tsaye sai idan kin so tsokana ta, sannan tunda muke baki taɓa yi min abu cikin gadara da isa ba dan ganin ke qanwar miji na ce ki na da 'yanci da iKon yin duk abin da ki ka ga dama a gidan yayan ki,a gaskiya Nafee samuna irin ki sai an tona Allah ya barki da masoyin ki kema ya nuna mana ranar auren ku,Allah ya sa ki samu kwanciyar hankalin da tafi tawa a dangin mijin ki,Allah kuma ya qara mana zumunci ina son ki 'yar uwa ta,maza taho to ki taya ni aikin ki dena Fushi da ni,abinda ya sa ma ban kira ki ba na dauka kina taya Innarmu aiki ne shiyasa ban kira ki ba, tayata aiki ai yafi nawa ko? And dan Allah ki dena fad'ar min da gaba dika dika fa yanzu cikin ya shiga wata takwas"
Murmushi suka yi wa junan su Nafeesa ta ji daɗin maganganun Juwairiyya sai kawai ta nufi inda Juwairiyyah ke yin wanki ta ajiye kayan ta koma ta tattaro sauran 'yan kayan da ba su da wani yawa ta fara wankewa,ranar dai kusan a tare suka ci gaba da aikin su, sallah ce kawai da cin abinci ke tsaida su,Saida ya rage sauran wanke band'aki kawai Juwairiyyah ta deb'i ruwa a bokiti ta ɗauki omo da tokar murhun da ta zuba wa gishiri kaɗan ta matsa lemon tsami ta zuba ruwa akai ta nufi hanyar band'akin.
Nafee na ganin haka ta bi bayan ta ta amshe wankin toilet ɗin, bayan ta kammala ta fito da komai ta ajiye inda ya dace ta kalli Juwairiyyah ta ce,
"Wai nikam me zaki dafa wa Yah Jabeer ne naga baki fara batun girki ba ga shi yamma ta yi"
"Abinda ya fi so zan dafa masa, da kud'in da ya bani kafin ya tafi, jiya na yi aike kasuwa aka siyo min k'wai, nama dankalin turawa, da cabage sai carrot da green beans kin san bani da su a lambu na dama zan iya noma su har su zan saka tinda Yah Jabeer na so a yi girki da su, sai flour ina da mai dama, an siyon yan kayan qamshi da maggi, ɗan wake zan yi mishi mai ajiiiii Hajiyata kin san shi a duniya na kula yana son abunnan"
"Waiiii sosai ma kuwa, baki gan shi bane yana satar danwake a tukunyar Innarmu da sai kin sha dariya, Innarmu in ta kama shi sad'af sad'af take tafiya ta damqe hannun shi ta matse da ludayin tsamar danwaken, shi kuma ya yi ta ihu dan azaba ita kuwa ta qi saki sai ya wahala ta sake shi ta na bin shi da zagin ya na mata satar ɗan wake a tukunya ni da baba mu yi ta musu dariya"
Dariya suka yi tayi sosai dan kuwa Juwairiyya bata taɓa jin labarin ba sai yau, miqewa suka yi suka fara gyara dankalin, suka yanka veges harda na lambun nata da zai tafi da kalar girkin da zata yi,musamman alayyahu da albasa mai ganye, sai da suka yanka komai ta wanke tsaf ruwan jikin su ya tsane sannan ta shiga soya dankalin turawan da ta yi wa yanka a tsaye,sannan ta dakko dafaffen naman ta da ta yanka qanana-qanana ta soya sama-sama ta aje gefe, sannan ta rage man suyar ta dakko jajjagaggen kayan miyar ta, da ta sanya tumatur guda biyu jal ta zuba, ya na tsaka da soyuwa ta zuba kayan qamshi da na dandano,bayan miyar ta soyu ne ta dakko wannan veges din ta zuba, ta bari ya dahu har sai da ruwan jiki ya qame tass sannan ta zuba dankalin ta soyayye da dafaffen k'wai a ciki ta juya ya haɗe jikin shi da kyau.
A gaban Nafeesah ta d'akko flour da wani gari ta zuba kuka ta juya sosai sannan ta fara kwab'a wa da ruwan kanwa, cike da mamaki Nafeen ke bin ta da kallo, cikin tuhuma ta tambayi Juwairiyyah ta ce,
"Wai nikam Matar yayah wannan garin meye ne naga kin zuba a cikin flour ɗin kuma?"
"To Hajiya tambaya an fara tambayar ko, to garin wake ne na niqa da yar dawa kadan sai alabo shine na haɗa da flour din, ɗan wake yafi dad'i sosai idan aka saka su"
" Auuuuhooooo, to ai sai ana yi ana tambaya ko kinga laifina ba gashi yanzu na qaru ba?"
" Ban ga laifin ki ba Hausawa sun ce matambayi baya bata ai"
Hira suka ci gaba da yi ita kuma ta na kwab'in danwaken ta,bata bar kwab'a wa ba har sai da ta ji ya yi laushi sosai sannan ta buɗe
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 25