masu babu su babu haihuwa fa kenan"
kuka ne ya k'wace wa Baba bai san sanda hawaye suka fara zuba a idanun shi ba ya na kallon Goggo da kallon tsana da danasanin zaɓen ta a matsayin uwar Yaran shi,babu wanda baya kuka a gidan hatta Mama Bilki hawayen tausayin yanda rayuwar gidan na su cikin qanqanin lokaci ta koma take yi.
Goggo ta kasa cewa komai, bakin ta rawa kawai yake yi saboda kuka, sai zata yi magana sai ta ji bazata iya cewa komai ba sai ta sake rushe wa da kuka, Suwaiba ce ta katse su da cewar,
" Baba ina neman izini a wajen ka ka barni na yi mana d'aki a ta can wajen, dan ba zan iya ci gaba da zama da Goggo a d'aki daya ba ko kusa da d'akin ta"
Wani irin murmushin takaici Baban su ya yi yace,
" kin ji ko ? Kin ji dai da kunnen ki yau 'Yar ki ba zata iya zama dake ba a d'aki ɗaya ba saratu ? Kar ki damu Suwaiba, wannan kud'in bai kamata ki yi amfani da su ba, kamata ya yi a bada sadakar su, ina da qasa da ciment da komai dama ina da aniyar yin d'aki saboda ku idan kun kawo mana ziyara tinda na kula rayuwar ku ta sauya nima dole na sauya maku d'aki ko da bai kai na masu aikin ku a can ba,sai kawai muka tashi babu neman izini na na fita na dawo na ga ta riga ni,har tana yi mana taqama da fankama tare da gore-gore akan Yaran ta su 'YAN ABUJA ne matan masu kuɗi,dan haka yanzu da kaina zan gina maku d'akin naku"
Juyawa ya yi ya fita dan ba zai iya zama a gidan ba ya na gani Goggo Sarai b'acin rai na sake lullub'e shi,kamar abun wasa bayan kwana uku da yin maganar sai ga Baban su ya fara haɗa qasa da kan shi dan gina wa Yaran nashi d'aki tinda dama aikin shi ne,nan da nan Suwaiba da yan uwanta suka haɗu suna taimakawa mahaifin nasu da duk abinda za su iya,suna tsaka da aikin Ammar ya taka dugui-dugui ya isa wajen su ya deb'o qasar a hannun shi ya miqawa Baban su, dariya suka yi gaba ɗayan su, a haka Ammar ya zama shi ne ke saka su nishad'i har yamma ta gabato sannan suka tashi suka bar wajen dan wanke Jikin su da yin alwalar sallar magariba.
Mama Bilki ko tana can tana masu girki har ta kammala,Hajiya Goggo mai jiran gadon tafiya Makka kuwa ba wanda yake kula da yin ta yanzu a gidan tun bayan dawowar suwaiban,babu mai kula da kukan ta balle a lallashe ta.
Gaba ɗaya sun maida hankali akan gina d'akin da zasu nesanta kan su da ita, dan kuwa har sun ɗora foundation, gaba ɗayan su tattare wa suka yi suka zauna bangaren Mama Bilki, wadda yau kusan kwana uku da dawowar suwaiba duk yanda za ta yi ta nuna masu rashin dacewar abinda suke yi ta yi amma sun qi jin maganar ta.
Yauma a babban faranti Mama ta zuba masu abinci kamar kullum, kowa ya saka hannu har Baban su suka fara ci, Mama Bilki ce ta miqe Baba ya kalle ta ya ce,
" Ina zaki kuma Gimbiya?"
" Baban su zan je na kira Yaya ne, mu ci abincin dika"
Gaba ɗayan su yaran sai suka zare hannayen su a abincin suna kallon ta tare da turo baki alamar basu yarda ta kirawo Goggo Sarai ba,
"Ai sai ki zauna ko? Tun da dai kin samu amsar ki a wajen Yaran dan haka zauna mu ci bincin mu"
Koma wa ta yi ta zauna jiki duk ba kwari,haka suka gama ci suka wanke hannayen su suka sha ruwa, wanke farantin Saudat ta yi ta ajiye a kwandon wanke-wanke ta dawo suka zauna suna ta hira, suna wasa da Ammar,
" Mama Ammar ya girma ya yi wayo sosai"
In ji suwaiba da ke kallon shi cike da soyayyar da bata taɓa zatan haka ake ji akan 'yan uwa wanda aka fito ba daga ciki ɗaya ba, a zaton ta 'yan d'akin su ne kaɗai 'yan uwan ta da zata so bayan su ba wata soyayyar d'an uba, Goggo ce ta yi murmushi ta ce,
" Aiko dai kinga dik sa'annin shi ya fisu girma da wayo, har yaron maqotan nan namu da ya bashi wata biyu Ammar ya fi shi wayo"
"Lallai kam ga alama nan na gani"
Mama Balki ce ta nisa kafin ta ce,
" Suwaiba, Saudat, Salma ina so ku bani hankulan ku nan dikan ku"
D'aga kai suka yi a tare suka kalle ta jin yanda ta ambaci sunayen su alamar babu wasa, amsawa suka yi gaba dayan su suka zuba mata ido,cikin kwantacciyar murya Mama ta ce,
" Ina son na baku shawara a matsayina na uwa, sannan ina son ku duba abinda zan faɗa maku da da kyau da kuma Kyakkyawar zuciya kuma ku qoqarta ku yi amfani da shi, kun ga da farko dai uwa ba kamar ta a rayuwar duniya, Allah ya ce abi shi sannan abi iyaye, Annabin rahama ya jaddada bin uwa sau uku kafin ya kira sunan uba, dan haka ni ina son ku yafe ma mahaifiyar ku abinda ta yi maku, tabbas bata kasance uwa ta gari ba wadda take bawa yaranta tarbiyyar da musulunci ya tanadar, amma ta baku so, ta nuna maku qauna, na uwa da yaranta, in kun kula ita a tinanin ta tayi abinda ya dace daku da rayuwar ku ne, amma koma dai menene ina son ku sani, wanda bai yafe ma wani ba, shima ya ji tsoron kar Allah ya qi yafe masa nashi laifukan, dan haka nake mai baku hakuri a madadin ta, ku taimaka ku yafe mata, kar ku ja wani ciwon ya kama ta dan Allah na roqe ku"
Cikin kuka sosai suka matsa kusa da ita suka rungume ta, Suwaiba ce ta yi magana a cikin su ta ce,
" Mama Bilki ke alkhairi ce a rayuwar mu, ki yafe mana abubuwan da muka yi maki a baya, tabbas mun cutar da ke da kalaman mu, da ayyukan mu, bamu zama yara masu biyayya ba, ki yi hakuri ki yafe mana"
"Indai nice na yafe maku, sai dai har yanzu baku ce min komai game da Yaya ba?"
Salma ce ta amsa masu dan Suwaiba da Saudat har yanzu akwai d'aci da wata irin qiyayya da suke ji game da mahaifiyar tasu, amma sun sani dole su yafe mata, su yi hakuri da abinda ta yi musu,
"Mun yafe mata Mama Allah ya yafe mana mu ma"
"To ya kamata yanzu ku je ku sanar da ita kar ta kwana cikin damuwa, na kula ko bacci bata iyawa tun ranar da ki ka dawo gidannan suwaiba"
Suwaiba ce ta yi saurin miqewa ta ce,
"Ni dai Mama ba zan iya zuwa yau ba, dan Allah kar ki tirsasa ni yin abinda ban jin zan iya yin shi a yanzu"
Ta qarasa maganar ta cikin kuka,baba ne ya ce,
"Bilkisu Allah ya miki albarka, amma ki bar su haka, zuqatan su cike yake da qunci akan abinda ta yi musu, daga baya a hankali komai zai warware masu"
"To Baban su Allah ya kaimu lokacin, Allah kuma ya sanyaya zuqatan ku ku yafe mata gaba daya har kai ɗin ma"
Amsawa suka yi dika da,
" Ameen"
Hankalin Goggo kam ya kai qololuwa wajen tashi da jin hirar Yaran nata da kishiyar ta da ta tsana nan take ta fara ganin wani irin duhu ya na lullub'e mata ganin ta,qoqari take yi ta buɗe ido da kyau ko ta yi magana amma ta kasa a hankali ta ji kan ta na juyawa har duhun da take gani ya mamaye ganin ta baki ɗaya ......
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HERMEEBRAERH
Page 27:
Kuka kawai talle yake ya kasa tsaida hawayen shi tsabar yanda mutuwar Jummala ta dake shi, wannan rayuwar da iyalin shi suka yi a baya ko kuma suke yi ya tabbata ba wanda ya ja ma su ita face shi, mugayen halayen shi ne da yi ma yaran mutane sakin wulaqanci da zinace-zinacen shi ne ya dawo masa ta haka.
Yau gashi an wayi gari tsabar lalacewa Yayan shi uwa ɗaya uba ɗaya ke neman matar shi ta sunna, Yaran yayan shi na neman na shi yaran, kaiii jama'a wannan wace irin musiba ce ta sauko mana a wannan zamani, Marka kam irin kukan qabilun nan ta dinga yi, ta yi girgiza ta yi girgiza sai ta kwarara ihu sai kuma caaan ta yi dif ta cigaba da gyad'a kai,itama abun ya shige ta sosai ba kadan ba, jummala ta mutu sakamakon yunqurin zubda ciki, ga Hawaila tana kallo a gaban ta da ciki dan kuyat ya fito a gaba,nata farkan kuwa na can gefe ya na jinyar dukan da ya sha, wace irin rayuwa suka jefa kansu a ciki ne ita da mijin ta da Yaran ta dika?
Maqota kowa ya zo ya yi gaisuwa sai ya tafi babu mai zama wai da sunan zaman makoki, ko sun shigo yada magana ne yake kawo su, wasu daga ciki ma cewa suke yi,
" Tohhhh abinda ya faru kenan hmmmm Allah dai ya jiqan ta amma zunubi kam an kwasa"
Ire-iren kalaman nan ne ke fitowa daga bakunan mutane suna yi suna kyab'e baki, wasu kuma bayan sun yi gaisuwar sai sun dora da cewa,
"Laaa ikon Allah kamar ciki nake gani a jikin Huwaila, ni dai bani da labarin auren ta, sannan mun san ba a shan ciki a ruwa, hmmmm Allah ya kyauta,gidan Talle kenan gidan ban mamaki, uwa ba kwab'a uba babu hantara"
Kusan kowa ya zo da abinda zai furta kafin ya tafi,baqin ciki kamar ya kashe Haule saboda ji da ganin munanan abubuwan da ke faruwa,wai yanzu nan ne gidan uban ta, gidan da babu tarbiyya ba kwab'a, banda Allah ya kare ta Itama da duk haka zata taso a lalace tinda duk abinda ke faruwa a gidan kenan,yanzu gashi wannan mummunan baƙin fentin ya shafeta, ai kuwa da an gama arba'in guduwa zata yi qauyen da ta ji wata qawar Marka da ta zo da jimawa ta faɗa acan mahaifiyar ta ke aure, qauyen baida wani nisa yana nan kusa da su ne,dan da alama idan ta ci gaba da zama a gidannan ko mashinshini rasawa za ta yi balle manemin aure, in ko ta koma can ko sunqi karb'ar ta ba zata dawo nan ba dole su sanya za su yi da ita.
kwalla ta share ta ja hanci, tana kallon su cike da tsanar halayen su, tashi ta yi daga wajen da su Marka ke zaune ta yi shigewar ta d'aki,addu'a take ta yi ma 'Yar uwar ta a ranta na Allah ya yafe mata, Yayan Talle kuwa bayan jinya da zaman d'aki ya jawo masa har da gudun abun kunyar da ya tafka gani yake mutanen waje sun sani, wanda bai sani ba ba wanda ya san ya na neman Marka a waje maganar iya cikin gida ta tsaya dan babu mai zamar yin kirari ya dab'a wa cikin shi wuqa a cikin su .
Duk maza da ke zama a majalisar qofar gidan su Talle sun sauya wajen zama,tabarmin da aka shimfid'a domin zaman makoki ba mutane akai da an gaishe su ake wucewa daga Baban gida da Badamasi sai Talle a wajen, Talle kuwa mugun haushin Yaran yake ji sai kallon su yake ya na jin kamar ya je ya shaqe su, amma haka ya dinga haɗiyar yawun baƙin ciki dan kuwa a irin iskancin da ya aikata a duniya ko kwata basu yi ba ya san sakayya ce yake Karb'a da hannun hagu tun a duniya.
Basu tashi a wajen ba sai bayan la'asar,Talle tashi ya yi ya hau nade tabarmar da yake kai sannan ya shiga gida fakam-fakam ya tsaya a kan Huwaila, kwalama su Baban gida kira ya yi, a tare suka isa tare da jingine tabarmar da suka zauna akai kan su a qasa kamar munafukai, cikin b'ata fuska Talle ya ce,
"A cikin ku waye me cikin Huwaila?"
Badamasi ne ya nuna Bangis da sauri, shi kuma Bangis sai ya qara duqar da kai qasa,kallon su Talle ya hau yi daga sama har qasa cikin qunar rai ya ce,
" Yanzu yarannan wai har kunyi girman yi wa wata ciki? Ko dake maganar wai kun yi girma ma bata taso ba tinda ga misali kun bayar, kun yi sanadin mutuwar ɗaya ga ɗaya nan da tambarin abin kunyar da zai bi zuri'ar mu har abada, dan haka sai ka bari ta haihu a maku aure kun reni ɗan shegen cikin gidan da kuka samar tare,"
Ita dai Marka bata cewa umm bare A'a, ta yi dif sai hawayen nadamar rayuwar su ke fita daga idanun ta, a cikin zuciyar ta tana ayyana wannan lamari ba laifin kowa bane face na shi, daya tsaya ya tsare mata sha'awar ta da buqatun ta da bata yi zina da auren ta ba.
Ni kuwa na ce wannan ba hujja bace ga matan da suke ganin dan mijin su baya sauke haqqin shi akan su bari su bazama neman mazan waje, ko su fara aikata wani abun da ya kauce hanya, su sani Allah zai masu hukunci dai-dai da abinda suka aikata ne shima mijin Allah zai masa hukuncin abinda ya aikata,dan haka ni a ganina ba dabara bace aikata Zina da aure, wadda ke da matsala da mijin ta ta bangaren auratayya ta gaggauta neman mafita ta hanyar shari'a ko sulhu ita da mijin su rabu ta nemi wani, ko ya bi duk wata hanya ta halal da ya san zai katange ta daga fad'awa haram,bai halatta ta faɗa halaka ba da sunan rashin kulawar miji mu kiyaye.
Miqewa marka ta yi zata shiga d'akin ta, Talle ya dakatar da ita,cikin muryar da Marka bata taɓa zato ba ta ji Talle na fad'in,
" Marka ina neman yafiyar ki akan dikkan abubuwan da suka faru tabbas laifi nane, da na tsaya na zama namijin kirki da duk haka bata faru ba, ki yafe min mu dawo mu gyara rayuwar auren mu,"
kauda kan ta ta yi saboda kukan da yake neman cin qarfin ta ga wani haushin shi da take ji na jefa su wahala da ya yi, Yayan shi ne ya fito daga ɗan qaramin d'akin shi ya zube akan guiwowin shi ya na hawaye ya ce,
" Talle qanina ka yafeni na biye wa son zuciya, da rudin shed'an na aikata mummunan abun da ko mutuwa muka yi sai yabi zuri'ar mu domin kuwa shi mugun labari kamar tusa ne a wajen bodari ba ya riquwa watarana sai ta fita, ka taimaka ba dan ni ba domin Allah da zumunci ka yafe min"
kuka ya kifa hannayen shi a fuskar shi yana yi hakan kuwa ba qaramin bawa kowa tausayi ya yi ba har ta kai da Talle ya daga shi sannan ya ɗan daki kafadar shi dan shima kukan yake ji, kauda kai ya yi zai shige d'aki yaji maganar Yayan nashi na fad'in,
"A gaskiya sai mun haɗu mun gyara rayuwar gidannan namu kan komai ya tafi mana dai-dai yanda ya kamata cikin tsari da tarbiyya irin ta islama, na farko sai Marka kin gyara yanayin shigar ki a tsakar gidan, dan kuwa yanayin yanda iyalin ka take yawo a tsakar gidannan ne ya jawo min matsananciyar sha'awar kasancewa da ita,haka za ka ga tana yawo ba isasshen kayan da ya rufe dikkan jikin ta, tana tafe tana juya dikkan jikin ta, sannan ga maganganun ta da na ke jiyo wa wanda yawancin su akwai sakin layi, ma'ana akwai batsa da watsewa a cikin su, wajen kallon ta da maganar ta bata kiyayewa, wadannan abubuwan sun ja ra'ayina matuqa ainin, dan haka in muna son mu samu kwanciyar hankali da kiyayewar zinace-zinace a tsakanin mu sai mun kiyaye,sannan sakewa yarannan da muka yi shima ya jawo wannan bala'i da muka shiga har ya yi sanadin mutumar Jummai, Yaran nan kan su ba su yin shigar arziki ga mazan da ba muharraman su ba a cikin gida,mu na ji za su dinga mugun wasa a tsakanin su ba ma hana wa a haka muna ganin ai 'yan uwan juna ne,to wannan sakacin namu duk shi ya jawo mana komai,Su ma kuma yaran mata kamata ya yi idan maza suka kawo maku hari irin wannan ku na sanar da iyayen ku da wuri gudun kar abun ya ci gaba har a samu matsala yarinya ta lalace a gaban iyayen ta,iyaye kuma idan yara sun kawo masu magana makamanciyar wannan su wayar wa da yaran su kai akan yanda za su kare kan su da kuma karb'ar maganar su dau mataki akai kar su hantari yaro dan gudun zubewar mutuncin mutumin da ke neman cin zarafin yaran nasu ko gujewa tonuwar asirin yaran su, a dinga ɗaukan mataki saboda rage faruwar haka a cikin al'umma"
Talle ne ya amshe maganar da sauri ta hanyar gaskata yayan nashi,sannan ya basu tabbacin dawowar shi qauye da zama, don ya gama zaman birni kenan har abada, murna a wajen Marka kuwa da jin wannan labari mai daɗi ba a magana,sai dai ta bar wa ranta ba ta ce komai ba har wannan lokacin,a haka suka watse kowa ya kama inda zai yi cike da alhinin mutuwar Jummala.
******************************
A cikin sati uku Baba da 'yan taya aikin shi ko na ce 'yan taya hirar shi suka kammala ginin babban d'akin su suwaiban, da yake filin dama ya na da ɗan girma,sai dai kuma ba filasta ba fenti, sai ledar d'akin da suka fara shimfida qaton buhu a qasa sannan suka saka ta, katifa biyu suka yada, babba da qarama, sai kayan sawar su da suka kwaso suka zuba a ciki, d'aki yayi ba laifi, kullum dare Suwaiba sai ta yi kukan rashin mijin ta da kuma yanda ta koma mara amfani a cewar ta, yanzu wa zai aure ta a haka? Yaushe Salihu zai aiko mata da takardar sakin ta ko kuma ya zo ta gan shi? haka za ta yi ta saqe-saqe har bacci b'arawo ya ɗauke ta.
Hajiya Goggo kuwa mai niyyar hawa jirgi a je Makka bata samu hawa jirba ta samu mummunan hawan jini, sakamakon sanya tinani da damuwa da ta yi a ran ta,ta riga da ta saba a Koda yaushe Yaran ta na manne da ita suna shan hira,amma yanzu tsakanin su gaisuwa ne kawai,Shima dan ta san Mama Balki ta matsa masu ne da ba za su gaida ta ba,in suka gaida tan suka tafi sai dai ta jiyo hayaniyar su da Mama Bilki tana koya masu abubuwa masu amfani a rayuwar su ta duniya da lahira, wanda ita ya dace a ce ta koyar da su tun farko,gefe d'aya kuma haka za ta ji suna wasa da Ammar kamar ciki ɗaya suka fito da shi, abun ba qaramin d'aga mata hankali yake yi ba,uwa uba Baba ya juya mata baya, baya kula ta, baya cin abincin ta ballantana kwana a dakin ta,Goggo ta je asibiti a kwanakin nan yafi sau uku, dan kuwa wata rana sai kawai tana zaune ta ji wani jiri da duhu ya mamaye ganin ta har sai ta suma, haka za su kaita a bata magani su yi qoqarin da zasu yi akan ta, da ta farfad'o su sallame ta Baba ya maido ta gida, a kullum takan ce a cikin ranta,
'Oh ni Sarai naga duniya, Yarana da nake taqama da su a idon duniya su suka juyan baya yanzu, Allah gani gare ka ka dawo da hankalin su kai na'
Yau Goggo ta tashi da matsanancin ciwon kai, in da ta dinga kiran Suwaiba ta na zaune tana jin ta amma ta yi shiru, Mama Bilki ce ta leqo ranta a b'ace tace wa suwaibar,
" Suwaiba kina son shiga aljanna kuwa? Mahaifiyar ki na kiran ki kina ji amma ki yi shiru? ki kiyayi Allah, ki kiyayi fushin uwa akan ɗan ta suwaiba, meyasa kk da ruqo ne, shi wancan mijin naki mai qaton ciki ba dan d'an kyaun da yake da shi ba meye abin so a wajen shi, duk da wahalar da suka jefa ku ciki kina nan kina faman son shi, kina begen shi sai uwar da ta haife ki ce Zaki kasa yafe mata? To na qara jin tana kiran ki kina ji ki zauna kiga ya zamu qare da ke a gidannan shashasha kawai,kin miqe ko saina kwad'o maki wannan murfin kwanon a ka?"
A hanzarce ta miqe tana kallon hannun Mama Bilki mai riqe da kwano, shigewa dakin Goggon ta yi tana zumbura baki ta ce,
" Gani"
Ta ja ta tsaya a kan ta,a hankali Goggo ta buɗe baki ta ce,
" Suwaiba nice fa Goggon ki abar son ki, Suwaiba ba dan Adam ɗin daya wuce kuskure a rayuwar shi na san na yi kuskure,amma yanzu na yi nadama ku yafe ni ke da yan uwan ki, na san ban zama uwa ta gari ba a gare ku,ko wannan ciwon da nake fama da shi ya ishen azaba suwaiba, kullum da ciwon kai nake kwana ba qaqqautawa, na rasa ya zan kuma duk na san sanadin juyan baya da kuka yi ne, a tinani na a da rayuwa mai kyau nake baku ashe ban sani ba ina tura ku ga halaka ne, dan Allah suwaiba ku yafe wa Goggon ku kun ji?"
Kuka Suwaiba take yi sosai harda majina, kusa da goggon ta ta je ta zauna ta dora kanta a kan cinyar goggon ita kuma ta hau shafawa hankali, ba wanda ya qara cewa komai a cikin su, nan take Goggo sarai ta ji kamar ana zare mata ciwon kanta,damuwar ta na raguwa.
****************************
Jabeer ne ya sauka a saman machine cike da matsanancin farin ciki, bakin shi washe ya kasa rufe shi kamar gonar audiga ya shiga gidan, qoqarin shi bai wuce ya ganshi a gaban mahaifan shi ba da matar shi.
Cikin murna ya qarasa shiga bangaren Innarmu ya na kwala mata kira, sai dai abinda ya bashi mamaki be wuce ganin sashen nata wayam da ya yi ba an karo qofar sashen, bangaren su ya yi cike da doki da zumud'in ganin Juwairiyyah, durqushe ya ganta gaban ta robar da ta haɗa zuma da ruwan zam-zam ne da ta yi wa fatiha qafa bakwai, falaqi bakwai,nasi bakwai, da suratul ikhlas bakwai, sai Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla wa anta taja'alal hazna idhashi'ita sahla qafa bakwai tana sha tinda cikin ta ya yi wata takwas dan samun sauqin haihuwa, ta shan ye ya kai rabin robar tsabar azabar da take ji a Jikin ta, zufa kuwa sai karyo mata take ko ta ina, sai addua take tana qarawa,
" Allahu Allahu Allahu rabbi la ushrika bihi shai'an wa huwassami'ul aleem"
Shine abinda take faɗa tana maimaitawa, da sauri ya isa gare ta, ita kuwa ruwa ya fashe mata tana wani irin nishi na son ta sillub'o koma meye a tattare da ita, sauri ya yi ya juya ta daga durquson da ta yi sabida kar ta haihu a haka ta samu mummunan tsaga, zaunar da ita ya yi ta gaba ya koma bayan ta yana qoqarin taimaka mata, dan a yanda ya ganta da yanda suke karantawa shi da ita a wani littafi mai suna EVERY WOMAN ya san haihuwa ce ta zo, ba yanda zai ya fita da ita asibiti haka zata iya haihuwar a hanya.
Suna haka suka ji sallamar Innarmu ta zo da kwad'on rama zata bawa Juwairah,
"Ki na ina? Fito na samo maki ramar da ki ke so har na ma sa mata kuli na kwad'anta ta, ai ina zuwa gidan Iya mai rama na yi sa'a har zata fita talle na samu na samo maki"
Jin nishin Juwairiyyah da maganar jabeer ne ya sanya Innarmu saurin shiga parlour ganin gwagwarmayar da ake yi ne ya sanya itama ta duqa ta hau taimaka masu, nan take Juwairiyyah ta fara yin nishi mai qarfin gaske...........
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 ' YAN
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 25