ba a kawon kayana nan ba, kace a bari inna zo gidan ka akwai amma ka hana ni shiga dakuna ukun can, sannan kuma in da nake ba wasu kayan kirki na saka wa"
' Yarinya wannan lokacin nake jira da zaki nemi wani abu a wajena'
A zahiri Kuma sai ya ce,
"Sorry my love ki yi haƙuri,maza shirya muje na kaiki ki siyo kayan da duk ki ke buqata, menene wani dubu ɗari biyu kuma? Ai ba abinda ba zan kashe maki ba in dai ina da shi"
Da sauri ta sauka tana murna ta saka kaya ta dauki jakar da tazo da ita ta fito ta na jiran su tafi shopping,tsaf ta ganshi a tsaye Shima ya fito yana mata wani irin shegen murmushi, fita suka yi suka dauki hanya, suna ta tafiya, sai ta ga suna barin gari suna ta wuce shaguna da super markets, kasa jurewa ta yi cikin kissa ta ce,
"Ina zamu ne haka sweety?"
Idanun sa na saman hanya ya furta,
"Wani waje zan kai ki na musamman in kk ga wajen zaki ji daɗi sosai"
"Wooow Sweety u ar so romantic , i love u"
"I love u more dear"
kiss ya yi wa hannun ta, a haka yana tuqi ta yi bacci, bata bude ido ba sai a wani qauyen da bata san ina bane, wani gidan qasa ne mai girman gaske, ko ta ina mata da yara qauyawa ne a ciki sai wasu dattijai a gefen wata bishiya, sina cin wani tuwo baqi miyar koriya sharrr da ita, da sauri ta miqe ta fara murza ido, a zaton ta mafarki take yi,cikin tsananin razana ta furta,
"Babe ina ne nan? Me muke yi anan? Ko mafarki nake yi ne?"
" Hhhhhhhh ba mafarki ki ke yi ba Salame, nan shine ya dace da ke, kuma nan ne gidan ki, na asali, can gidan gidan oga na ne daya karban auren ki, anyway sun yi tafiya shine na kai ku mu ci amarcin mu, karki damu bangaren ki yafi na dika gidan kyau, da taimakon ogana, harda TV an sa maki, tin da ko gidan uwale da ubale ai babu su ko?"
Ya faɗa yana wani shu'umin murmushi, ita ko ta dad'e da fara kuka harda majina, kuka take tana bashi hakuri ya maida ita wa Goggon ta ita ta fasa auren nashi in dai a nan zai ajiye ta, wanka mata mari ya yi mai lafiya sannan cikin fushi ya ce,
" Dan uwar ki mai kwadayin nan an gaya maki wawa ne ni? Na kashe maki yan kudaden nawa kice na maida ki gida, ai ke da gida sai kin haifi biyar a qalla, sai dangin ki sun manta dake , ba dai Abuja kk so ba, to ai nan ma Abuja ce, dan haka baki da damuwa,inna fita ki tabbatar kin biyo ni in ba haka ba a gaban su zan fara ballaki, danni ba sabon abu bane wajena dukan mace"
D'aga kai ta yi ta na kallon shi cike da tsoro da mamaki,dan yanzu wani irin tsoron shi take ji ba kadan ba, hankailin ta kuwa idan ya yi dubu to ya tafi yawo, musamman da ta shiga ta ga daki daya ne dakin nata da wata yar TV da kayan kallo, sai gado qarami da kujeru biyu, da yan kwanika da ledar tsakar d'aki, kai abun dai kamar wata mara gata, haka ta shiga tana kuka kamar ta suma take ji dan baqin cikin da ke ran ta, biyo ta ya yi yace ta biyo shi d'aki mai kallon nata, amsawa ta yi ta bishi kamar raquma, wani d'aki ta shiga mai cike da tarkace da tsohon gado, sai wata uwar datti da aka tara a gefe na kayan wanki, ga poo din kashin yaro ba a zubar ba qazanta dai ta qarshen qarni kawai, wasu yammata ne a gefe an ci mai an yi fari ta fuska an d'ashe har fuskar ta yi wani kampala kampala, ba kyaun gani, sun sha bra ta dame su anyi daurin qirji da yan wayoyi a hannun su, manyan 'ya'yan Alhaji Talle ne, a qauyen nasu duk da Talle aka san shi, ko kuma a ce masa Tallen marka wato matar shi uwar 'ya'yan shi manyan kenan.
Markan ce ta fito daga kicin kamar wata baqar mahaukaciya, futu2 da ita tana goge hanci da bakin zanin ta, ido ya yi mata jawur, da dukkan alamu girki take yi dan kuwa jikin ta sai qauri hayaqi da warin hammata ke tashi, cikin d'aga murya Talle ya ce,
"Dalla malama ki yi sauri yau zan koma ni"
Shiga d'akin ta yi tana bin salma da wani irin mugun kallo,cikin neman qarin bayani ta ce wa Talle,
"Wannan fa Talle?"
"Qanwar ki ce, dama na zo ne na kawo ta zan koma, ki kula da ita in ta bar gidannan kashe ku zan da ke da asararrun yaran ki, kun dai san hali na ai"
Ya na gama maganar shi ya liqe ya sa kai zai fita, Marka ta kama qugu cikin masifa ta ce,
"To ina zaka rabon ka fa da nan wata uku kenan, sannan yau kazo ko kwana ba zaka yi ba zaka wuce"
"Jarababbiya muje na maki ko sau daya ne ba dai jarabar ki in ta motsa har a gaban 'ya'yan ki sai kin nema ba"
Cikin rashin kunya ta furta,
"Eh ɗin na ji muje"
A gaba ta sa shi suka koma d'akin yaran na dariya suna tafawa, ita ko salma qafafun ta ta ja ta yi d'akin da yake nata a yanzu,gado ta faɗa tana kuka mai ban tausayi, ga mijin da take so can da wata qazama yana mu'amalar aure da ita duk suna jiyo wa, ga talaucin da ta hango tsabar shi a gidannan, yau ina zata saka kant ? Kuka take sosai ta ji an banko qofar d'akin nata da ta saya , cikin masifa ta ga wata matashiyar yarinya ta tsaya a kan ta tana fad'in,
" Malama ki je ki qarasa mana abincin tin da baba ya qule daka da marka, yunwa muke ji , dan yanzu kan su fito sai an gan su"
sShewa yaran suka yi suka tafa tare da fad'in ,
"Hahaiiiiiiiiiiii casssssssss "
Miqewa Salma ta yi ido ya yi mata jawur saboda kuka tace,
"Ni na saka uwar taku shigewa d'aki da uban naku da zaku nuna min ku fitsarraru ne?"
"Ni ki ke mayar wa da magana? Yau zamu daga maki qafa ko dan darajar Baba na gari, amma ki kiyaye mu, mu nan da ki ka ganmu zane matan baba muke yi, ki tambaya kiji, sakarai kawai, kema ba zai wuce tarkon baba kika faɗa ba ai kwadayi mabudin wahala ne dama ai,"
Dariya suka saka suka sake tafawa, wata ce a cikin su da bazata wuce shekara 14 ba ta shigo ɗauke da bokiti akan ta na markaden koko, kallon su ta yi ta kauda kai ,
" ke jummala je ki qarasa abinci marka bata kusa,"
" ku me kuke yi tin dazu baku je ba? Ba in da zani sakarkaru kawai"
wucewa zata yi Huwaila ta janyo ta ta kwada mata mari, kuka ta saka tana fad'in,
" Allah ba zan ba mugaye kawai sai dai ku kashe ni, baku da aiki sai dai kuci ku yi wanka in su yaya Baban gida sun zo su yi ta lalibe ku da sunan wasan abokan wasa kuke yi, ko ji kuke ban sani ba ne?"
Shiru suka yi suka sake ta suka kama hanyar shiga madafin nasu, kuka taci gaba da yi, daga baya kuma a hankali ta yi shiru ta daga kai tana kallon Salma, cikin washe baki ta ce,
" laaaaa kece amaryar Baba da za a kawo dama?"
Daga mata kai Salma ta yi ta shige d'akin ta, shigar ta ke da wuya Talle ya fito daga dakin Marka.............
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 ' YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
Page 6:
Talle ne ya qarasa fitowa Yana gyara wandon shi, rigar shi kuwa na yafe a kafadar shi, d'aurin qirjin gado ne a jikin Marka lokacin da ta fito daga d'akin nata ta na wata miqa , bakinnan na ta na ta fidda wani wari kamar an bude shaddar gidan haya, hammatar ta har wani kore2 brown2 take, qafar nan fururu da ita kan ya danqare, ba a qanin tsagar kitson ma, kuma gashi ita mace ce mai cika da tsahon gashi amma ba gyara ,yawu ne cike a bakin Talle na kyankyamin Marka ya je ya zubar yana masifa.
" ke ba a binda ki ka iya sai aukin son a kwanta da ke, in ba ai maki yanda ki ke so ba ki tara wa mutane jama'a ba ki kunyar Idon kowa,a dai biya maki buqata kawai,gaki nan ne kawai baki san ya ake gyara ba sannan in na nema a wani wajen ki fi kowa kishi da nuna jin zafi, to bari ki ji ba zai yu ba, ko ki canja hali ko wannan karon inna tafi sai na yi wata shida ban dawo ba"
" ka yi hakuri Talle amma dai kasan ba laifi na bane ko, kana ganin baka bar mana komai ka ke tsallake mu ka yi tafiyar ka, ni ke wa kai na komai a gidannan ba mai taimaka mana,a hakan dai nake samun abinda nake yi wa nawa yaran da na haifa da ciki na,sannan ga wadannan shegun 'ya'yan da iyayen su ba sa nan, duk a kaina, yaushe nake da lokacin gyara? Kawai hakuri za kai, in ka gyara kaga gyara, in baka gyara ba ka ga dan gundun uban qazanta a gidan ka ah toh,ko 'yan iskan da ka ke bi ai kai ka ke kahye musu kuɗi suke yin gyaran ko kuma wasu 'yan iskan su kahye musu kuɗi su gyara ka tsinci dami akala"
Ta qarasa maganar ta tare da murguda baki ta wuce tana kada manyan duwaiwakan ta, tsaki Tallen ya yi sannan ya ce,
" Ga mace dai a nan har mace da mutum zai huta amma an kashe waje da qazanta Allah wadaran naka ya lalace jakin dawa ya ga na gida"
Zubda yawu ya qara yi har zai fita ya tina da salma, leqawa ya yi yaga tana kwance har lokacin sai kuka take, dakin ta ya tura qofa ya shiga sannan ya hau gadon ya sa hannu ya d'ago ta, saka ta ya yi a cinyar shi da niyyar ya lallashe ta, nan take wani irin wari ya kai wa hancin ta ziyara, yunqurin amai ne ya taso mata, da gudu ta fita waje ta hau kakarin amai amma kuma ta kasa aman ga wahala duk ta ishe ta saboda yunquri, kuka ta fashe da shi na takaici, cikin ɓacin rai Talle ya biyo ta ya tsaya a kan ta babu ko digon tausayawa a tattare da shi ya ce,
" Ke dan uwar ku mai shegen kwadayin tsiya ni zaki wa iskanci? Ni zaki fito kina toshewa hanci kina qoqarin haras wa? Yau zaki ci uban ki kan na tafi kuwa"
Janta ya yi da qarfi ya yi d'akin nata da ita yaran nashi manyan suna labe suna jiyo kukan ta, ya wurga ta gado ya cire kaya ya hau kusantar ta da dattin jikin shi da warin da najasar da ya gama saduwa da Marka,Salma kuwa da ta ji azaba kuka take tana kakarin amai amma saboda yunwa ba komai a cikin ta sai aman ya qi fitowa banda wahala babu abinda take kwasa, cikin kuka da nunfashin wahala ta ke fad'in,
"Ni ka daga ni kaje kai wanka kasan ba zan qi ka ba, wannan warin zai kashe ni in baka tashi ba,nimfashina kamar zai dauke haka nake ji "
Mari ya sakar mata ya ci gaba yana cewa,
" kema sai kin shaqa dan uwar ki niba a haka aka sani na yi har sau biyu ba ban tsinci komai ba? Dan haka dole na sauke akanki dan inna tafi ban san randa zaku ganni ba"
A haka ya gama abinda zai ya tashi gajiya fal jikin shi, ba wankan tsarki balle na daud'ar daya kwasa haka ya fice ya sa kai ya yi cikin garin Abuja,inda ya tafi ya Salma a nan kamar matacciya, ita kuma Marka ana can gabam murhu anyi goho ana hura wuta, Itan ma ko wanka bata damu da ta je ta yi ba, gaba daya murna ce fal cikin ta, yau Talle ya biya ta bashin da take bin shi, hankalin ta kwance take ayyukan ta dan kuwa ta sani talle ba qaramin gwarzon maza bane, ya qi tsayawa ne kawai ya kula da ita da iyalin shi dika, ga girma na kama su, dan shi zai yi shekara 47, ita kuma zata yi 38, lokaci ne da ya kamata su zauna su mori rayuwar su kafin tsufa ya rufe su,amma inaaa kowa da nashi matsalar, tin asali ita ta bazama shi neman mata saboda muguwar qazantar ta da rashin sanin ya kamatan ta, shine sanadin kwadayin matan waje da yake yi a Koda yaushe musamman in ya gansu fes da su a cikin gari, daya shigo dan ya sauke buqatar shi sai ya ganta duqun2n kamar jakka, ai kuwa nan take haushi zai kama shi ya ji kamar ya rufe ta da duka, a hankali ya fara da marin ta in ta cika masa ciki, sai duka ya biyo baya, a haka har halayen shi suka munana, lokacin da take son ya gyara lokacin shi kuma idon shi ya buɗe da matan waje, still ita kuma bata gyara ba, ita ba ma ta ganin wai laifin daga gare ta ne balle ma ta ɗauki matakin gyarawar,ga yaran su da suka lalace duk a sanadin muguwar tarbiyyar iyayen na su, tinda in suka tashi kusantar juna ba ruwan su da yaran za su ji ko baza su ji su ba,kawai zasu yi abun su kamar dabbobi su fito suna zagin juna ko yabon juna a gabam yaran, ta haka Huwaila babbar yar su ta fara miqawa Baban gida cousin din su jikin ta yana lalubewa, domin so take itama ta ji me Marka kewa ihu tana nuna jin daɗin ta akai, ana haka Badamasi shima ya ke jan Jummala su yi nasu, kafin kace me yara idon su ya buɗe, Haule ce kawai Allah ya sawa nutsuwa a yaran Talle kaf, dan ita har makaranta take zuwa, kuma mamar ta daban a gidan,bata san ta ba, shi kanshi bayace ga uwar ta bama, tinda ya saki uwar ta da za ta tafi ta ajiye masa Haulen ba ta sake juyowa ba, dan gani suke gidan shi ba abin son haɗa zuria bane ba sam qaddara da tsautsayi ne ya sa auren su ya qullu shi yasa ta yafe masa 'yar ta cire ta a ran ta ta qara gaba.
Kullum haka rayuwar gidan Talle take, gidan babban gida ne na gado tare yake da yayun da wato iyayen su Badamasi da Baban gida, iyayen su sun rasu, suma Su Badamasin Mahaifiyar su bata da rai sai mahaifin su, watan ta shida da rasuwa, sun rasu ita da jaririn ta da tazo haihuwa, dan haka daga su sai uban su da yaqi aure sai bin 'Ya'yan jama'a sa'annin su Jummala, gidan su Talle gida ne na marasa da'a da tarbiyya, ko kadan ba mai kwab'a a gidan balle ya tsawatar akan abinda ake aikata wa mara kyau.
Lokuta da dama Marka na leqawa dakin Yayan mijin ta su watse tare ba tare da kowa ya sani ba,sakamakon nesa da mijin na ta ke yi da su,idan ya tafi ya na jimawa bai waiwayi gida ba dan kuwa watarana idan ya sa kai ya yi gaba sai ya yi watanni shida zuwa bakwai bai dawo ba yana can cikin garin Abuja, wannan ta'asar da ake ta tafkawa a gidan gaba ɗaya yaran da manyan gidan duk basu sani ba,domin a fili nunawa suke yi su ko gaisuwa ma basa yi da junan su sun tsani juna, amma da dare yayi in wani na buqatar wani zasu qwanqwasa qofa a bude su shige su gama su fice ba wanda ya sani, wannan shine Gidan Tallesious.
**************************
A bangaren amarya Juwairere kuwa, suna shaqar amarcin su cikin jin daɗi so da amince wa juna tare da girmama junan su, rayuwar ta na yi mata daɗi matuqa dan kuwa ba ta da damuwa ko kaɗan ko kewar gida ta yi Jabeer na kore mata damuwa a gefe d'aya Kuma ga qawar ta kuma 'yar uwar ta Nafeesa itama ta na debe mata kewa sosai, tare da taya ta aiki in Yah Jabeer ya fita kasuwa wajen saida jakunkunan shi.
A haka rayuwar su ke ci gaba yau da gobe ana cin daɗi saboda garar da aka kai ta da shi, amma bahaushe ya ce zara bata barin dami, sai ibtila'in talauci ya ziyarce su,kasuwa ta kulle sai ya fita Watarana ya gama wunin sa be fi a sai takalmi ɗaya ba ko ya dawo ma Watarana ba a sai komai ba, Juwaira kuwa bata taɓa nuna masa wani sauyi ba sai ma qara masa qwarin gwuiwa da take yi a kullum.
A cikin wannan yanayin da ake ciki ta fara fuskantar canji daga wajen Surukar ta wato Hansai wadda suke kira innarmu, bata nuna mata a fili sai dai a qasan qasa ta yanda ba mai sanin halin gallazawar da take yi wa Juwairiyyah, ga shegen habaici kamar wadda ke tare da kishiyar ta,ta na so ta fito fili ta nuna wa Juwairiyyah qiyayyar da take yi mata amma ta kasa saboda ba qaramin kwarjini Juwaira ke mata ba.
Ba komai ke jawo wa bawa kwarjini ba kaga yana da maqiya amma su rasa ya zasu yi da shi face tasbihi,zikiri , da yawaita hailala da istigfari, komai maqiyin ka zai yi maka sai dai ta bayan Idon ka ba dai ta gaban ka ba domin kuwa Allah zai kare ka ko abun ya same ka ka sani yana daga cikin jarabawar rayuwar ka shiyasa u can not escape it, iya hakurin ka iya lada da daukakar ka,sannan yana sa maqiyan ka su dinga shakkar ka, ga soyayyar Allah da mala'iku da bayin Allah managarta, mu riqe ambaton Allah a koda yaushe, kina tuqa tuwo ne, kina shara ne, kina tafiya ne, kina ma megida wanki ne ko guga, kina ma yara wanka ne, ko zaki sauke tukunya ne, ki yi bismillah, komai zaki ki sa ambaton Allah a ciki rayuwar ki zata zama abin so wajen kowa, sannan Allah zai so ki ya ambace ki a tsakanin mala'ikun shi.
Wannan dalilin ne yasa ta fito da dabarar yi mata zagon qasa wajen Yah Jabeer tunda ta kasa musguna mata gaba da gaba.
Wata rana Juwairiyyah ta fito daga d'akin ta dan ta yi abinci sai ta fara da share madafin ta ta gyara shi tsaf,sannan ta qara dauraye tukunyar ta , ta haɗa wutar murhu ta dora ruwan zafi,sai ta deb'o waken ta ta fara gyarawa, ta gama gyara waken kenan ta wanke ta zuba sai ta yanka albasa a ciki dan ya yi laushi da qamshi, dama tasan ba su da kayan miya man da za ta yi miyar kan shi manage za ta yi da shi bashi da yawa, kuma da dikkan alamu in suka ci wannan na dare sai dai ai hakuri, ta kammala dafa waken kenan sai nufi d'akin ta dan dakko shinkafa ta rege sai shinkafa tace ɗauke ni a inda ki ka ajiye,duban duniya Juwairiyyah ta yi amma haka ta nemi shinkafa ta rasa.
Hankalin ta ya tashi sakamakon duba lokaci da ta yi ta ga lokacin dawowar Yah Jabeer da ya kusa, cikin tsananin damuwa ta zauna ta zabga tagumi tare da fad'in,
" Oh ni Juwairah yanzu in ya dawo me zan bashi, ya wuni kasuwa bai ci komai ba, sannan ya bada kuɗin cefane daidai gwargwadon ikon sa a masa girki, kawai sai ya dawo ince shinkafar ta b'ata?"
Tana tsaka da tunani da damuwa ne ta ji muryar Nafee na fad'in,
" kin kusa gama abincin ne ? Dan na fara jin yunwa , Innarmu ma na can tana neman abinci yunwa take ji sosai"
"Na shiga uku ni juwairah, kin ga Nafee anan na aje shinkafar daga kewayawa bayi kan na fito na rege na saka ban ganta ba, na neme ta sama ko wasa na rasa "
Cikin mamaki Nafeesah ta kalli Juwairiyyah ta ce,
"Baki ganta ba fa ki ka ce, to Ina zata ke ita ba qafa ba?"
kuka Juwairah ta fara ta koma daki ta yi tagumi ta rasa abin yi,ta na nan zaune dabara ta faɗo mata, tashi ta yi ta samu wannan waken ta rage masa ruwa sosai, ta samu dan man daya rage masu, da dan wani magi da take da guda uku, sai gishiri ta zuba a ciki ta qara albasa sosai, inda suke shuka alayyahu ta je ta yanko mai yawan gaske ta zauna ta cinke ta gyara ta wanke sosai ta zuba, nan da nan abinci ya haɗu murna ta dinga yi tana godewa Allah da wannan dabarar da ta yi, duk da qarancin shekaru irin nata amma hakan be sa ta tsaida tunanin ta waje ɗaya ba, sai ta faɗad'a tunanin ta ta yanda har sai da ta sama wa kan ta mafita, bayan ta gama ta zubawa kowa ta kai masu, ko da ta shiga d'akin Innarmu bata gan ta ba sai ta yi zaton ko ta na makewayi ne,kawai sai ta ajiye ta yi wa Nafee magana ta wuce sashen ta, kan ta fita daga sashe su Nafeen ne ta ji Innarmu da wani yaro tana ce masa,
"ka siyar shamusu nawa ya baka me shagon?"
Kasa kunne Juwairiyyah ta yi amma bta jin me yaron yace,sai ta sake jin muryar Innamu na fad'in,
" Amma dai bai kyauta ba gaskiya, a fa wajen shi Juwairah ta sai shinkafar amma shine ya rage har nera saba'in ɗan nema mai kan buta kawai sallamamme shi yasa shagon ya qi ci gaba gashi nan jiya iyau"
Kafin ta dawo Juwairiyyah ta bar wajen cike da mamakin da ya cika mata ciki, dama Innamu ce ta dauke shinkafar? Me hakan yake nufi?dama Innarmu bata qaunar ta? Bata son zaman lafiyar da suke yi da Yah Jabeer?shin me yake faruwa ne?
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
Page 7:
Juwairiyyah na nan tsaye cike da tarin tambayoyi da mamaki ta ji Innarmu na fad'in,
"Shegiyar yarinya, daga zuwa komai na mu ya fara tabarbarewa, gaba ɗaya Jabeeru ya tare a qasan ta, ko shigowa gida ya yi da mun gaisa wuf ya tashi ya tafi wajen ta, ya dan zauna ma mu yi hira yanda muka saba sam ai yake yi,to an janye mai hankali, to ni ba zaki mulkar min d'a kamar yanda uwar ki ta yiwa uban ki ba in dai ina raye, haka kawai, ke na haifarwa dan? To mu zuba shege ka fasa tsakanin ni da ke"
Kuka ne ya kusa kwace ma Juwairah jin kalaman surikar ta, wannan wace irin rayuwace kuma?
" Ya Allah ka taimake ni na ci wannan jarabawar"
Abinda ta iya furtawa kenan ta share hawayen ta ta koma ban garen ta, qarasa gyara wajen ta yi tai wanka, ta yi brush sai ta koma daki ta tsaya cikin madubi ta gyara gashin ta da ta wanke ta shafa wa mai sannan ta taje shi ta daure a bayan ta, buɗe wardrobe ɗin ta tayi ta tsaya kallon kayan ta ta na nazarin wanda zata saka, kafin daga qarshe ta yanke shawarar dakko wasu riga da wando rigar pink wandon baqi siriri Wanda ake kira da pencil, Inna Deejee ce ta siyo mata su a 'yan gwanjo,tin su dai basu da halin siyan sabbi,kayan sun amshi jikin ta ba kadan ba, fita ta yi ta debo garwashi ta saka tiraren wuta, sannan ta feshe jikin ta da tirare ta qara da humra, kyautar Goggon ta Kareema kenan wato kayan qamshi, kafin kace me sai ga Juwairiyyah ta fito chass da ita,da ka kalle ta zaka dauka yar wani hamshaqin me kudin ce, ko matar wani attajirin, Nafeesa ce ta shigo tana murmushi ta ce,
"Dad'i na da ke matar Yaya ba dai tsafta da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 25