so ko Suwaiba 'Yar Abuja? Ko ba haka qawayen ki suke Kiran ki ba?"
Qara wurgata gadon ya yi da take qoqarin guduwa ya kwanta a jikin ta, kamar wani wanda aka yi wa allurar bacci nan da nan bacci ya dauke shi, kuka ci gaba da yi sosai jikin ta na yi mata ciwo, haka ta tashi ta ja jiki da kyar, ta tafi toilet, ruwan zafi ta haɗa mai zafi sosai ta shiga, tana shiga ta yi wata muguwar qara saboda azaba, a haka ta gasa jikin ta sai da ta ji ta daina jin ciwon wajen sannan ta saki jiki ta kwanta a ruwan da ta sake sanya wa nan da nan bacci ya fara diban ta a zaune a ruwan, buɗe ido ta yi ta fita ta je ta saka wasu kayan ta koma ɗaya dakin ta kwanta, ta rufa, nan da nan baccin wuya ya yi awon gaba da ita.
Da asubar fari Saudat ta kira ta a waya tana kuka, ta sanar da ita irin cin mutuncin da Alhj Kalla ya mata itama, sata ya yi ta yi ta masa tausa, har wayewar gari shi kuma ya na shaqar bacci, data fara gyangyadi ya zabga mata mari dole ta farka ta ɗora daga inda ta tsaya, kuka suka yi ta yi a tare ba mai lallashin wani, itama Suwaiba labarin nata bala'in da ta qunsa tayi sannan suka ce gobe zasu haɗu in mazajen sun fita.
Shigowa dakin suwaiba ta ji za a yi cikin sauri ta danne wayar ta kwanta ta yi lamo kamar me yin bacci, qarasa shiga Alhj Salihu ya yi ya zauna kusa da ita ya ce,
" Haba my Suwai hakuri zaki yi, ke ma kin san in rai na ya ɓaci bana son a cika tambaya ta musamman maganganu na rainin wayo, auren kuɗi ki ka yi kuma ga kud'in nan, to meye na damuna sai na maki wani abun?"
Kuka take a zuci hawaye na zuba ta gefen idon ta bata ce masa komai ba, janta ya yi jikin shi yana shafata, take ta fara sauke ajiyar zuciya tana hamma, don bacci take ji sosai, kiss ya mata ya maida ta ya kwantar yace shi zai fita, d'aga masa kai kawai ta yi ta koma ta lumshe ido, bayan ya fita ne ta yi baccin awa uku ta tashi ta yi wanka , ta haɗa abin karyawa mai rai da motsi da tea mai kauri ta ma manta jibgar da ta sha, taci tai nak abinta, Wayar ta ce ta yi ringing ta amsa da ,
" ku barta ta shigo qanwa ta ce"
Sannan ta kashe, Wajen kamar minti 5 Saudat ta shiga cikin gidan cikin shiga ta alfarma, ga wata arniyar mota da ta zo da ita driver na tuqata, ta ci gold ko ta ina hannu da qafa da kunne, dan harda sarqar qafa suke daurawa saboda wadata ba dan wani abu na,har parlourn sama mai aikin Suwaiba ta yi mata jagora ta na isa ta zauna kusa da sister din ta akan dinning table ta ja plate ta zuba chips da kwai da farfesun naman kan rago, sai tea da ta haɗa itama mai kauri ta hau sha, ba wadda ta ce wa 'yar uwar ta sannu,sai da ta gama sannan ta yada kai baya ta zame kaɗan daga kujerar tace,
" Sis ina cikin tashin hankali wanda da dikkan alama kema hakan take a wajen ki, dan ga jikin ki nan ya nuna, dubi fuskata nima ki gani"
Ta fada tana mai nunawa Suwaiba fuskar ta da ta yi jawur ta kumbura, sai rufewa ta yi da mayafi da ta shigo gidan kar a gani, sannan ta ci gaba da magana,
"Ga kuma zaman yunwa da na yi dan jiya kwata2 kasa cin komai na yi har safiyar nan, sai da na ga wannan abincin ne na ji yunwa ta motsa min"
Suwaiba ce ta yi murmushin takaici sannan ta ce,
"'Yar uwa bari ki ji, ki cire komai a ranki shawarar da zan bamu shine mu cire rai a son sai sun zama mutanen kirki, tin da dai ba halin su bane, mu zauna mu mori dukiyar da muka zo Abuja domin ta, mu zama manyan hajiyoyi,mu bawa maqiyan mu kunya, dan ni kam kin ganni nan, in ba jiya dana sha jibga ba, bana wasa da abin ci ko wani nau'i na jin daɗi, sannan kuma da kk ganni nan haqqina na aure in daga yau ya ce ya daina ban ba zan damu ba ba zan sake tambayar shi ba, domin kuwa akwai hanyoyi da dama da zan iya maganin matsala ta, wanda na san kema kin san su ba sai na tsaya bayani ba, i hope ba zasu yi gangancin turamu wannan stage din ba, zasu na daure wa ko once in a while ne suna biya mana buqatun mu, to kinga ba mu da matsala da bin matan su ko kuma wani abu mai kama da shan giya, sun dad'e ba suyi ba, dan ba zan qara yarda a taba lafiya ta ba, an gama daga jiya"
" kaiiiii yar uwa wannan shawara tayi sosai"
Tafawa suka yi suka koma palour suka debo dambun nama da juice suka zauna tare da kunna kallo, sunayi suna hira qarshe waya suka dauka, suka hau kiran Goggo Sarai, suna waya, a lokacin suna tsakar gida dikkan su, Mama Bilki, Abban su Juwairah da ta kai masu ziyara sai Ammar dake zaune a cinyar Juwairiyyah, da ita kanta Goggon, wanki Mama Bilki keyi na kayan Abban su da na Ammar, ita kuma Goggon su na duba girkin ta wanda ta dad'e da dena cin abincin gidan sai dai ta yi nata, su kuma suci nasu, hakan da ta yi yaba Abban damar su samu sauqi daga dawainiya, shiyasa ma wataran suke samun abinda suke aikawa Juwairah dan Mama ta kula da rayuwar da take ciki a zuwan da ta yi sau ɗaya, amma da ta tambaye ta ya zaman nata yake a gidan ta sai ta qeqasa qasa tace ita lafiya lau komai yake tafiya masu, ganin ba zata buɗe baki ta yi bayani bane ya sa Mama yi masu addu'a kawai ta kyale ta, amma tabbas tasan akwai wata a qasa, cikin firgici ta daga kai daga tinanin ta sakamakon wata qara da Goggo Sarai ta saki......[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*SANARWA ! SANARWA !*
*Ina masu buqatar sanin yanda za su gyara jikin su ta ciki da waje? Ina nufin daga gashin kan su zuwa yatsun qafar su da qarin ni'imar jikin su?*
*Ina masu son koyon sana'o'i dan samun taro da sisi? To 'yar uwa matso kusa ba sai kin biya maqudan kuɗi ba dan ki koyi yanda Zaki yi sana'ar da zata sama maki kuɗi da #1k kacal za ki mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA*
*Idan kuma ke ma'abociyar karanta littafan Hausa ce ki yi wa HAERMEEBRAEH ❤️magana kai tsaye ta wannan No 09031416423 kai tsaye, Zaki samu Littafin MAHREEN DA KYAKKYAWAR FAHIMTA a kan farashi #500 each*
*Please share*❤️
Page 11:
Mama na juya wa sai ta ga wai ashe Goggo Sarai dariya take a hakan dan kawai ta ja hankulan su Mama Balki su ji ta na waya da 'Yan Abujan yaran ta da take alfaharin sun haye a rayuwar zaman duniya dai ba ta qiyama ba.
"Hahhhhaaaaaiiiiii kaiiii amma na ji daɗin haduwar ku gaba ɗaya waje guda, ikon Allah ana can ana cin amarci sai yau aka samu haɗuwa kenan, to ya masu gidan? Ya rayuwar hutu da jin daɗi kuma?"
Suwaiba ce ta ce,
"Lafiya qalaou Goggo, ina Baba?"
" Hmmmm ga shi can wajen waccan sallamammiyar matar tashi da ta shanye shi"
" Bashi mu gaisa kar yace bamu neme shi ba"
" Aiko bada wayata ba ehe ku kira shi a yar rakani kashin shi kawai"
Tana fada tana hura hanci tana turo dankwali gaba irin na fitsararrun matan nan? Kad'a kai kawai Baba Baballiya ya yi sannan yace,
" Allah ya kyauta"
Murgud'a baki Goggo Sarai tayi kamar wata qaramar yarinya, irin na rashin kunyar nan da raini ita a dole sai ta nuna ta fi ƙarfin mijin ta kuma ba ta jin maganar shi balle girmama shi.
Makaranta kunsan fa shi murguda bakin ma kala2 ne, akwai sexy murguda baki mai daukan hankalin oga, ya ji dole sai ya kai nashi bakin a naki sabida yanayin yanda ki ka yi shi da salon jan hankali, sannan akwai na rashin kunya kamar na Goggo sarai kenan.
Ganin yanda take masa rashin kunya gaban matar shi da yara shi ne ya sanya shi tashi dan ya je waje ya sha iska sai wayar shi ta hau ringing, d'agawa ya yi da sallama muryar su Suwaiba ya ji a tare su na gaida shi kamar ba sa son gaishe shi,ya kula sarai amma sai ya danne ya amsa tare da tambayar su gidajen su tare da Mazan sannan ya qara da fad'in,
"Ku na nan dai lafiya ba wata matsala ko?"
Cike da rashin kunya suka buga shewa tare da fad'in
'Hhhhh Baba do u really have to ask ? To muna lafiya qalou alhamdulillah, komai normal kamar dai yanda ka sani Baba mazajen mu masu kuɗi ne, so ina ganin ai bamu da wata matsala mu a rayuwa, sannan gida da mazajen namu duk suna lafiya da Fatan mun amsa tambayar ka"
Cikin qunar rai Baba ke magana,
" Suwaiba ni mahaifin ku ne dan haka ba zan gaji da yi maku nasiha akan ku bi duniya a sannu ba, yau in kaine gobe ba kai bane, dukiya da abinda ke cikin duniyar nan ba komai bane face rudin shaid'an ga wanda ya mai da su abin bauta, kuji tsoron Allah a lamarin ku, Hello ! Hello..... "
Shiru ya ji ashe sun dad'e ma da kashe wayar tin da ya fara wa'azi suna ta fad'in yanzu zai takura masu, mamaki ne cike da zuciyar shi Baba ya ce,
" Yaran nan ni suka kashewa waya?"
" Baban su ka yi hakuri komai zai daidai ta da qarfin addu'ar da zaka dinga wa iyalan ka, Allah zai shirya maka su inshaa Allahu, adduar iyaye amsasshiya ce a wajen Allah, Allah ya shirya mana zuria"
"Hmmmmm Ameen Gimbiya ta Allah ya albarkace ki da zuriar mu duka"
Daɗi ne ya kama Mama mara musaltuwa kwatankwacin daɗin da take ji a duk sanda ya yi mata irin wannan adduar,
" Ameen a bin sona"
Murmushi suka yi wa junan su wanda ya sanya shi ya ji baqin cikin shi ya tafi gaba ɗaya ,ruwan wankan da ta saka masa ya ɗauka ya tafi ya shiga wanka abin shi ya fito tsaf,ita kuma Mama sai ta fara qoqarin dora masu abincin dare.
Magidan ta ku dinga qoqarin yi wa matan ku godiya da addu'a musamman ta nema masu albarka a wajen Allah, in albarkar nan ta samu a garesu zata shafe ku kuma da zuri'ar ku kenan,ku kuma mata ku dinga yawan yin abinda ku ka san zai faranta wa Mazajen ku rai su yi maku addu'a, soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa.
Juwairiyyah bata bar gidan nasu ba sai yamma liss cike da tunanin halin da rayuwar gidan su take ciki.
****************************
Bayan kwana biyar da zuwan Juwairiyyah gidan iyayen ta suna hira da Nafee da safe suka shirya yanda suke so Watarana su kai wa Shamsiyyah qawar su ziyara,nan take Nafee ta ce me zai hana su kai mata ziyarar a yau? Juwairiyyah sai ta nisa sannan ta ce,
"To bari mu gani Allah ya sa aiki be sha min kai ba lokacin"
Cikin ran ta kuwa ta na tunanin yawan fitar da take yi a 'yan kwanakin gashi ita ɗin ba ma'abociyar yawan fita bace.
Da yamma kuwa sai ga Nafeesa ta shirya tsaf cikin riga da skirt na atampa, tayi kyau sosai ta taho bangaren su Juwairah, ganin Juwairiyyah ta yi na harkokin gaban ta ba ma ta da niyyar fita,cikin jimamta lamarin ta ce,
"Matar Yayah ya na ga baki shirya ba kin saka dan guntun wando da vest an faka gashi gefe?"
" Nafeesa kenan da dikkan alama kin manta yau Yaya da wuri zai dawo gida ko? sannan yau ranar dana ware ce domin gyaran lambu na ko duk kin manta qafar yawo? Sannan ga girki da zan yi da wasu aikace2n, kuma sanin kan ki ne ni fa yawon shiga nan shiga can dinnan ba son shi nake yi ba, shike kawo mace ta daina kula da iyalan ta da gida tana qarewa a titi"
Cikin mutuwar jiki Nafee ta ce,
"Hakane kuma gaskiya ki ka faɗa,amma gaskiya ni dai zan tafi gidan Shamsiyya na gaida ta dan na riga na yi niyya kuma na yi mata alkawarin zani yau din, na zaci zamu tare ne tinda na ga ke kin dad'e baki je ba, sai na dawo to"
" To ki dawo lafiya, ina gaida ta da yaran"
Fita Nafee ta yi ta tafi gidan Shamsiyya, ko da ta isa gidan Shamsiyya sai ta tarar da ita a gida tare da yaran ta biyu mace da namiji, Farha da farhan, goyo take yi na 'ya macen , gaba daya gidannan sai a hankali, komai da kan shi yake zaune a inda bai kamata ba,cike da kyankyamin halin da ta samu gidan qawar tasu ta shiga parlour ta zauna a kujera ta na qarewa parlourn kallo,da sauri ta miqe tana duba skirt din ta daya jiqe, hannu ta sa ya tab'o skirt ɗin sannan ta kai hancin ta,wani irin mugun zarnin fitsari ta shaqa, da sauri ta kauda kanta ta fita tsakar gidan ta ɗauki buta ta sa ta ruwa ta wanke hannnun ta sannan ta saka a skirt d'in ta tana masifa ba tare da ta amsa lale maraban da Shamsiyya ke yi mata ba,
"Ni gaskiya shiyasa bana son zuwa wajen ku shamsiyya, ga gida har gida Allah ya hore maki amma sai uwar qazanta, duba dan Allah daga zuwa na na zauna akan fitsari , ko da Juwairah bata haihu ba na san abin da ba za a taba samun ta da shi ba kenan a duk lokacin da ta haihun, yanzu haka saboda gyaran gidan ta da kula da haqqin mijin ta yasa taqi biyo ni, Juwairah na da lokutan yin komai na kula da iyalin ta da gidan ta, tinda ba za a hadu ace kullum zaka haɗa kowanne aiki kayi ba zaka gajiya watarana, sai wanda suka zama aikin yau da gobe, dan Allah ki gyara, dan yana ɗaya daga abinda yasa Baban Farhan yake neman aure duk.da ya faɗa maki amma kin qi gyarawa haba Shamsiyya"
"kaiiii Hajiya bala'i daga zuwa.sai wannan dogon karatu? To dan Allah ya kuke so nayi? Ga aikin gida gana miji gana 'ya'ya, ni dai gaskiya abun ya min yawa ya kuke so na yi ne wai"
Kawai sai ta fara hawaye wai ita a dole komai ya mata yawa, kama hannun ta Nafeesa ta yi suka koma palour ta zaunar da ita a kujera, sai da ta laluba wata kujerar ta ji ba jiqa sannan ta zauna ta fiskanci Shamsiyya ta ce,
"Qawata ki yi haƙuri ki daina kuka ni ba wai ina maki faɗa dan ranki ya baci bane"
" To dan meye? Saboda kowa ya tsane ni sai a dinga ce min qazama ? Kalmar qazama fa na da ciwo tsakani da Allah"
Majina ta sharb'a tana goge hancin ta da zanin ta,Nafee na ganin haka ta ji kamar ta kwad'a wa Shamsiyyah mari,cikin karkace kai ta ce,
" To yanzu kin ga hakan da ki ka yi ni da nake budurwa Banda miji ba zan yi shi ba, da na goge majina da zani na gwara na je na wanke hancin gaba ɗaya, ai in kk ji ance qazama akwai kalmar tsafta kuma ko? To ni so nake ki cire kalmar da kowa ke kiran ki da shi na qazanta ki mai da shi mai tsafta, yanzu ki fa duba kiga Mama Bilki, kullum kika shiga wajen ta feeesss za ki gan shi, kin ga dai ta girma ko tunda Babar aminiyar ki ce ba yarinya bace, saboda tsabar qamshi da tsafta ba zaki so barin d'akin ta ba, come to think of it ba fa ta da kuɗi ma a hakan da wadata kamar yanda ki ke da shi? Dan Allah kema ki gyara ki rage son jiki,son kallo da karancr2n nan na zamani har sai kin gama komai sannan ki ɗauka ki ta yi,ina fatan wannan ya zama na qarshe da wani zai baki shawara ko za a zage ki akan tsafta, in baki gyara ba Abban Farhan yace maki zai qara aure kuma ya fara nema in kika gyara nasan bari zai dan matsalar shi dake kenan ba wani abu ba"
" Na gode qawata, ba wanda ya taɓa zaunar da ni ya min bayanin ya shige ni kamar yanda ki ka yi min yanzu"
"Ba godiya a tsakanin mu, Allah ya baki ikon gyarawa"
Murmushi suka yi wa juna shamsiyya ta miqe ta fara tattara kayan wajen data loda a kujera, nan da nan Nafeesa ta taya ta suka gyara gidan ya dau haske da qamshi, girki suka yi mai rai da lafiya kala2, wajejen la'asar Nafeesa ta bar gidan cike da tsaraba daga wajen shamsiyya, a ranar ta sha wanka da gaye, Abban Farhan daya dawo ya sha mamaki amma bai nuna ba, sai ya nuna mata matuqar jin daɗin shi, dakuma yabawar shi tashi ya yi ya je dakin shi yace,
"Ina zuwa"
wata sarqace ta gold mai kyau d'akko a cikin wani madaidaicin box kalar maroon,ya na fitowa ya zagaya ta bayan ta ya d'aura mata a wuyan ta ya na shafa sarqar da wuyan nata, a hankali ya kai duban shi inda yaran shi ke kwance har sun yi bacci ta saka masu pampas da kayan baccin su wanda tun da su na da shi amma baqar qiwa ta hana ana saka masu,Nafee ce ta koya mata yanda zata na qoqarin sanya yaran baccin da wuri kafin baban su ya dawo, watarana kuma ta bar su ido biyu dan su masa sannu da zuwa su yi wasa ya gan su su gan shi suma, godiya ta yi ta masa shima yana godiya da sabon sauyin da ya gani a tattare da ita, a daren ranar saboda kulawar da ya samu a wajen ta ya yi mata alqawarin zancen aure ya rushe sai dai idan ta koma yar gidan jiya ne, cikin salon lallashi ya ce,
" Baby ki kwantar da hankalin ki dan ni ba mai ra a yin mata biyu bane ko sama da haka tun tini, tsaftar ki da rashin tsaftar ki in ni me ra ayi ne ba zata hana min yin aure ba, na faɗa maki ne dama dan ki gyara mu more rayuwar auren mu yan da ya kamata, tun da ko shekara biyar ba mu yi ba har yanzu amma duk kin dena kulawa da ni da gida da yaran ki,masu shekara arba'in su na can su na more rayuwar aure su"
Ta ji daɗi sosai da wannan albishirin da aka yi mata,iya kuwa ta qudurta ma ranta zama mace mai tsafta ta bugawa a jarida kuwa dan ganin ta faranta wa mijin ta, yanda kowa ya yi mata tambarin qazanta sai an buga mata na tsafta in Allah ya yarda.
Ni ko na ce to Allah ya yarda ya shirye mu mu gane tsafta na da kaso mafi tsoka a rayuwar aure.
Bayan Juwairah ta gama komai ta yi wanka ta kwanta tana hutawa ne bakin ta na ta yin tasbihi ga Allah bacci mai daɗi ya dauke ta,Jabeer ne ya shigo ya ga yanda ta kwanta ta na bacci ba qaramin kyau ta yi masa ba,zama ya yi a gefen ta ya sa hannu ya na yi mata tafiyar tsutsa a qafar ta,a hankali ta farka amma idon ta na qara lumshewa saboda baccin da ke damu ta, juyi ta yi ta cusa kanta a cinyar shi ta ci gaba da baccin ta, a hankali ya janye ta ya gyara mata kwanciyar ta dan ya kula a gajiye take, da kan shi ya tafi d'aki ya cire kayan shi ya ajiye inda take aje masu kayan wanki bayan ya ninke su, ya na yi ya na tuna da idanun ta biyu ba zata bar shi ya yi duk haka da kan shi ba, maida shi take kamar wani sarki a wata Babbar masarauta, murmushi ya yi sannan ya tafi wanka dan har da ruwan wanka Juwairiyyah ta aje masa kan ta kwanta.
Bayan ya fito daga wanka ya gama shirya wa ne ya ga kamar bata ci abinci ba, sai ya ya shirya abincin ya zo ya qara tashin ta amma still bata farka ba sai ma magagin bacci da take yi masa,da alama dai bacci ne a idon ta sosai, a haka ya daga ta ya zubo abincin yana bata yana ci duk abinnan da ake idon ta rufe yake sai ta fara taunawa sai bacci ya fizge ta ya tada ta ta ci gaba da taunawa, cikin gigin baccin ta furta,
" Yah Jabeer ka dawo?"
" Eh na dawo princess"
" Sannu da zuwa"
"yawwa, meke damun ki ne yau?"
"Bacci nake ji na gaji ne sosai, ga jiri danake ji, tin shekaran jiya kuma sai naji cikina na ciwo ciwo, kamar ana min motsi a cikin shi"
Har ta gama maganar ta idanun ta a kulle suke, cikin damuwa Jabeer ya hau shafa cikin nata ya na fad'in,
" Subhanallahi, gobe zamu asibiti mu ga likita, shiyasa kika ji kwanaki ina ce maki sai naga kamar baki da lafiya, abinda ke kwantar min da hankali kawai ganin yanda jikin ki ba wani damuwa sai kyau da kike qarawa ma, nan din ki har wani kyalli suke"
Hannun shi ya kai saman rigar ta yana shafawa, a hankali ta janye hannun shi ta juya baya ta ci gaba da baccin ta, wani yawu ya hadiya, ganin yanda hips din ta suma suka ciko sosai kamar su yi magana, tashi ya ui ya maida plate din ya wanke bakin shi da hannu ya rufe ko ina ya dawo ya ce,
" princess ko dai fushi kikai ban dawo da wuri ba yanda na saba? Shi ne kike share ni kik eson yin bacci?"
Shiru yaji ta yi babu amsa,matsawa ya yi jikin ta ya janyo ta, bacci yaga tana yi sosai abunta hankali kwance,bai so hakan ba sam, gaba ɗaya shigar ta ta rikita shi, amma haka ya hakura dan yasan ba halin ta bane kyale shi koda tana cikin fushi ne, ja masu abin rufa ya u
yi tare da yi masu addua ya shafa masu, suka kwanta bacci........
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*SANARWA ! SANARWA !*
*Ina masu buqatar sanin yanda za su gyara jikin su ta ciki da waje? Ina nufin daga gashin kan su zuwa yatsun qafar su da qarin ni'imar jikin su?*
*Ina masu son koyon sana'o'i dan samun taro da sisi? To 'yar uwa matso kusa ba sai kin biya maqudan kuɗi ba dan ki koyi yanda Zaki yi sana'ar da zata sama maki kuɗi da #1k kacal za ki mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA*
*Idan kuma ke ma'abociyar karanta littafan Hausa ce ki yi wa HAERMEEBRAEH ❤️magana kai tsaye ta wannan No 09031416423 kai tsaye, Zaki samu Littafin MAHREEN DA KYAKKYAWAR FAHIMTA a kan farashi #500 each*
*Please share*❤️
Page 12:
Da asuba da Juwairiyyah ta tashi ta duba sai ta ga har ya fita masjid, addu'ar tashi daga bacci ta yi
"Alhamdu lilLAAHi alladhi ahyani ba'ada maa amatani wa ilaikannushour"
Sannan ta sakko daga gadon ta je ta yi alwala ta dawo ta gabatar da raka'atanil fajr ta yi sallar subh tare da azkar din safiya, tana gama wa wanka taje ta yi ta sake yin brush, gaban madubi ta zo ta warware kitson da ta yi da yamma kafin ta yi bacci guda biyu akan ta sakamakon ba ta son kitso sosai kuma shima Yah Jabeer din nata yafi son tana masa adon gashin haka ba tare da ta kitse ba.
Idan mijin ki mai irin ra'ayin Jabeer ne to ya na da kyau mace ta iya yin kitso biyu irin na indiawan nan da muke gani ana raba kai biyu a kwantar gefe da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 25