ba kwari.
Ta na zama ta ji wayar ta na ringing a gefen ta, dauka ta yi taga Nafee ce cikin murna ta amsa suka yi wa junan su sallama tare da gaisuwa,cike da jin nauyi Nafee tace,
" Matar yaya kunyi min mantuwa fa, kun manta tsimi na ba a sako da shi ba"
" Subhanaka ya raheem, ai ko kinga har yanzu ba wanda ya kula, babu damuwa ai kinga yanda na haɗa maki wancan ko? ki haɗa wani kawai,idan yaso wannan na bawa su Adda Saudat, keee ! Ban faɗa maki ba, an daura auren su ma jiya, tarewa kuma ance ba yanzu ba sai sun shirya magana da mazajen su, iyayen sunce basu buqatar komai sai matan yaran su za a kai masu kawai kin ga kuwa Ina kyautata zaton ba za a ɗauki wani lokaci mai yawa ba za su tare"
Cikin murna Nafee ke addu'ar Allah ya basu zaman lafiya, bayan gama murnar ne tace,
"Ni fa matar Yaya na manta wasu abubuwan ɗan sake faɗan mana pls"
" kai Nafee ko dai angon ya kwashe har da basirar ki ne?"
Dariya suka yi Nafee tace cikin shauqin son mijin nata,
" Matar yaya wato My love daya ne tamkar da ba iyaka acikin mazajen wannan zamanin"
" Oh ni Juwarah yarinya ta fitsare bari nayi na gama faɗa maki na kashe wayata, ina nan ina tausayin ki ashe ke kin gama zama yar hannu ma abin ki,"
Dariya suka yi tayi kafin Juwairah ta ce;
"kanin fari Zaki sa a siyo maki kadan zaki saka ba mai yawa ba, saboda masu magungunan gargajiya da na asibiti na ji sun tabbatar da cewa shan shi da yawa na kawo ciwon hanta, dan haka ki saka kaɗan sai citta mai dan yawa,da minannas, sai ki matse ruwan rake mai yawa, ba a qara wani ruwan da wannan ruwan raken Zaki yi amfani, Zaki samu rake ne iya adadin yawan da ki ke so yawan tsimin ki ya kasance, sai ki samo zuma mai kyau sosai ki saka sai ki dake kayan qamshin nan ki saka a ciki, sai kin ga ya yi kauri kadan ma'ana bai yi irin ruwa tsululu ba, zumar ce zata saka ya yi kaurin, ki dinga sha da yamma,amma pls wajen nemo zumar ku tabbatar me kyau ce kin san yanzu an b'ata zuma sugar wasu ke saka wa,idan taso na baiwa su Adda saudat wannan nakin nima na dan sha kafin na koma nawa gidan"
"Na gode matar yaya sai an jima ki shafan min kan bbyna, ina gaida yaya"
" Ni ma ina gaida angon ki" .
Washe gari sallama ta yiwa Innarmu ta tafi gidan su ba zata dawo ba sai an gama tarewar yayun ta, ta kaiwa Yayun nata wannan tsumin, sannan tun da suka faɗa mata mazan su sun ce ai nan da kwana biyar za su tare, Juwairiyyah ta shiga hidimar taya su gyaran jikin su,sai ga su Saudat sun fito fess da su fata na sheqi da kyalli , itama kanta uwar gyaran jiki sai da ta gyara dan a cewar ta itan ma amarya ce, tin da ta je gidan take ma su kwad'on zogalen daya sha timatir da cucumber,haka take wa zogalen tafasa ɗaya ta kwashe shi da ruwa-ruwa a babban mazubi,ta yanka manyan timatir masu yawan gaske sannan ta zuba masu qulin da ya ji kayan qamshi.
(Wannan haɗin ba k'aramin ƙara ni'ima yake yi ba sosai)
Duk daren duniya kuwa ta na samun kabewa ta yi ta haɗa masu da madara da zuma suna sha,( wannan haɗin yana gyara skin da qarin ni'ima)
Suna cikin lokaci na mangwaro ne, dan haka Juwairiyyah sai ta sa a siyo masu mangwaro mai yawa su zauna suna sha suna zuba hira abun su gwanin ban sha'awa.
Idan aka zo maganar tsarki da had'in ta na musamma da bata gajiya da haɗawa sai Salma ta yi ta jin kunya kar a gan su ace su na rawar kai,haka za su haɗu a d'akin su su yi ta mata faɗa musamman tunda ita ta haihu ta fi saudat bukatar wannan gyaran.
Goggo Sarai gaba ɗaya jikin ta ya yi sanyi qalou da lamuran gidan ganin yanda Mama Balki da 'yarta ke k'ok'arin ganin nata yaran sun je gidan Mazajen su da martaba da k'ima, tabbas Allah shine mai azurtawa ba mutum ba, duba da cewar gashi dai duk bala'in son kuɗin ta ta kai yaran Abujar kuma sun wahala babbar 'yarta ma har da nakasa, finally gashi yanzu Allah ya basu inda za su huta ɗin cikin sauqi ba tare da sun wahala ba sannan mazan nasu ' YAN ABUJAn ne dai ba wani garin na daban ba, hawayen da take qoqarin mayar wa ne wani ya gangaro,Mama Balki ta kalle ta ta ce,
" Yaya ki daina kuka, in yaran nan suka gani zaki d'aga masu hankali"
" Hmmm Bilki dole abun ya dame ni, ban zamo uwa ta gari ba sam sam a gare su, na tsani rayuwa da turbar dana ɗora yarana akai a baya"
"Hakane Yaya kinyi kuskure babba a baya, amma yanzu ai ya wuce ya zama tarihi,kuma in shaa Allah hutun da kike nema masu a rayuwa zasu same shi, kai sun ma same shi da iKon Allah"
Cikin gyad'a kai da yarda da maganar ta ta ɗauki kwanon abinci ta isa d'akin su ta miqa masu ta fice..........
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 34:
Labarin kyautar Abrar zuwa ga Suwaibah da mijin ta babu inda bai shiga ba a dangin nasu baki ɗaya har ma da mutanen unguwa, inda kowa yake farin ciki da irin wannan kyautar da Juwairiyyah ta yi wanda ba kowa ke iya yin irin ta ba, banda sanya albarka da fatan alkhairi ba ka jin komai a wajen mutane, sai kuma addu'ar Allah ya ba wa su Suwaibah iKon kula da tarbiyyar yarinyar.
Ya ku masu yi wa wanda Allah bai ba wa haihuwa ba gori ku ji tsoron Allah ku bari dan kuwa shi ke bayarwa ba mutum ne zai ba wa kan shi ba, da mutum ne yake ba wa kan shi da wata ba zata haifi yaro mai kalar baqi ba fari zata ba wa kan ta, da mutum ke ba wa kan shi da wata ba zata haifi fari ba baqi za ta baiwa kan ta, kun ga kenan Allah shi ne yake bawa wanda ya so ya hana wanda ya so ba dan baya son shi ba.
A yanzu wai mutane idan baka haihu ba ka zama mutum mara daraja a idanun su har kalmar juya za su dinga Kiran ka da shi, wannan matsala tafi fitowa daga dangin miji, musamman idan aka yi rashin sa'a basu da ilimin addini da wayewar ilimin zamani, jahilci ya musu yawa to daga ranar ka shiga uku in baka haihu ba, ba sa tinanin cewar ma ko laifin daga ɗan su ne? Ko kuma jinkiri daga Allah ne, ko wata rashin lafiyar da za a nemi maganin da ya dace da an samu haihuwar,su na mantawa komai himmar ma'aurata ba za su samu haihuwa ba sai da izinin Allah,mata masu gorin haihuwa mu sani kowacce mace dangin miji ce, ki kyautata kema sai a kyautata maki.
Da yawan gorin ma idan ki na da yaran wata bata da su ne zai hana ki zama kamar Juwairah? Ba zaki iya ba ko? To kar ki sake shiga hurumin Allah,idan kuma ba haka ba ki sa a ran ki ba da wadda bata haihun ba ki ke yi da Ubangijin ku da ya baki ita kuma bai bata ba da shi ki ke yi, sai ki jira amsawar shi domin kin tab'o shi.
Satin su Juwairiyyah uku da komawa Abuja har ta fara sabawa da rashin Abrar a tare da ita,ta bi duk wani process na yaye dan ta samu jikin ta ya zauna da kyan shi,ta yi had'in Sabaya wanda ta qara masa da dankalin hausan da ta busar aka niqa mata da sauran kayan had'in, sannan idan ta tashi sha ta na zuba madara sosai ta shanu,da yamma kuma ta markad'e ayaba da gyad'a ta zuba madara ta shanye,gefe ga man kaɗanyar ta da ta kwaba shi da man hulba da na Habbatussauda ta na shafawa a qirjin nata,cikin qanqanin lokaci ta yi wani irin kyau ta yi fresh ga cikakkiyar ni'ima da had'in ya qara mata,Jabeer ba ya gajiya da hidimta mata da ya ji ta ce Yah Jabeer siyo min kaza a guje yake siyowa dan ya san karshe shi zai amfana da hakan.
( Dan Allah maza ku sauya hali ku gyara matan ku na gida sai ku jima kuna morar su,ko da za ku ƙara aure ba zaku wulakanta na gida ba saboda duk abinda wadda Zaku kawo gidan Itama ta gida ta na da shi,duk abinda zaku yi wa matan na kyautata wa wallahi ba ku faɗi ba riba ce a wajen ku duniya da lahira, kai kuma saurayi da ka ke shirin yin aure ka dai ji yanda Jabeerun Innarmu ke kula da matar shi,ke kuwa uwar gida ko amarya kin ga yanda Juwairiyyah ke qoqarin gyaran jiki, tsafta, shagwab'a,iya girki,kula da miji a azaroom da duk wani abu da ya dace, dan Allah kowa ya gyara saboda rayuwar aure ta yi kyau ta yi qarko)
Yamma ce sakaliya, gari ya yi luf luf gwanin sha'awa kasancewar lokaci ne na damina hadari ne ya ke son haɗuwa iska sai kad'awa take mai sanyi,a daidai wannan lokacin kuwa Juwairiyyah ta gama duk wani abu da ya kamata ace macen kirki ta aikata shi kafin dawowar mijin ta daga aiki,irin su girki, gyaran gida, wanka, da kuma tsaftace ko ina na jiki da muhallin ta tana zaune tana jiran Haerbeebeen ta ya dawo,ko me ta tuna sai kawai ta miqe ta shiga kitchen ta sanya hannun ta ta d'akko wata roba da ta cika ta da niqaqqen garin rid'i, a hankali ta fara jin wata iriyar kasala na shigar ta ta na jin jikin ta ba kwari tin kwana biyu da suka wuce ta fara jin hakan, cup din da ke hannun ta ta matsar jikin robar domin ɗiban rid'in,tana bud'ewa qamshin kantun da take so ya daki hancin ta ta ji gaba ɗaya ya hau kan ta,a haka ta daure ta saka spoon ta d'iba sannan ta buɗe robar kayan kamshin da ta niqa na had'in kaninfari minannas da citta ta deb'o kadan ta zuba, zuwa ta yi tukunyar da ta dafa madarar shanu wadda Jabeer ke nemo mata a cikin wani qauye anan Abujan ta d'ebi yanda zai ishe ta ta zuba, zuma asalin mai kyau mara haɗi ta d'iba ta zuba a cup ɗin ta hau juyawa, a haka ta isa parlour ta samu waje a ɗaya daga cikin kujerun da suka yiwa palourn qawanya ta zauna, bayan ta yi bismillah ta riqe cup din da hannun ta na dama ta kai bakin ta da sauri ta sauke shi saboda wani irin amai da ya taso mata, da gudu ta miqe zata yi hanyar dakin su dan ta je toilet,ta ci karo da Jabeer wanda shigar shi kenan gidan,kafin ta yi yunqurin kauce masa amai ya taho da gudu nan take ta wanke masa jiki da amai, jikin ta har rawa yake yi kamar mai jin sanyi, wani irin zazzaɓi ta ji ya rufe ta a lokaci d'aya, ajiye jakar shi ya yi hankalin shi a tashe, ya kama ta ta duqa tana ta ci gaba da kwarara amai, sai da ya zamana bata iya fitar da komai sai yunqurin azaba sannan ya ja ta zuwa toilet ɗin da ke a cikin parlourn su, sai a sannan ne ta tuna da samuwar shi,tun Juwairiyyah na iya amsa sannun Yah Jabeer har sai da ta dawo gyad'a masa kai kawai ko ta lumshe masa ido.
Idan hasashen shi ya zama gaskiya to fa wannan karon Juwaireren shi ta haɗu da ciki mai laulayi da wahalar wa, dan ya kula kwana biyu kenan tana fama da wannan zazzaɓin da kasala da kuma yawan amai,a lissafin shi ya kamata ace tun sanda suka dawo daga Kano ta yi al'adar ta amma ya ji shiru wanda ita ta ma manta gaba ɗaya.
Bayan ya taya ta wanke bakin ta ne sai ya fara cire masu kayan jikin su ya saka a washing machine sannan ya tara ruwa a kwamin wanka mai d'umi kamar yanda yake so dan kuwa Jabeer na son wanka da ruwan zafi baya son ruwan sanyi a cewar shi ruwan sanyi na sanya shi kasala da zazzaɓi shi ne dalilin da ya sa ko da zafi ne sai ta kashe masa sanyin ruwa ya iya wanka da shi,wanka ya musu tas suka fito a tare, bayan ya shirya ta ne ya kwantar da ita a a gado ya je ya gyara parlourn sannan ya shirya shima,zuwa ya yi kusa da ita ya kwanta ta bayan ta ya riqe ta tsam a jikin shi, a hankali ta furta,
" Honey ka je kaci abinci na ajiye maka komai a inda ya kamata idan kuma ka na buqatar wani abu ka kira ni, na gode da kulawar ka a gare ni Allah ya yi maka albarka"
"Ameeen tare da ke,na san kin gama komai 'yar aljannah ta da yardar Allah,bana jin zan iya cin wani abu bayan ki na cikin wannan halin,yanzu menene ke yi maki ciwo, me kike son ci? dan daga ganin ki da kuma aman da kika yi na gane baki ci komai ba in ba wainar flour ɗin da ki ka yi mai manja ba da safe,"
Turo baki ta yi daga baya ta kwab'e shi irin na shagwab'abun nan, shi kuma yana jin yanayin saukar nunfashin ta ya san kuka take yi, saurin juyar da ita ya yi suna fuskantar juna ya ce,
"Ki sanar da ni duk abinda ki ke so zan yi k'ok'arin sama maki shi in shaa Allah"
kukan da take son yi ne na shagwab'a ta fara sauke masa shi, rungume ta ya yi yana sumbatar goshin ta a hankali yana shafa bayan ta,sai da ta yi kukan da ita kan ta take mamakin dalilin yin shi sannan ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ta fara yin magana,
" Yah Jabeer bani da lafiya, kwana biyu jikina ciwo yake yi min sosai, ga zazzaɓi da amai da nake fama da shi, abubuwan da nake so a da yanzu sai na ji bana son su,"
Sai kawai ta sake b'arkewa da sabon kuka cikin murmushi Jabeer ya ce,
"Shhhhhhhh ! ya isa haka to, yi shiru Babyn Yah Jabeer,ki daina kuka kin ji? ko zaki yi gwajin ciki a gida ne na d'akko maki PT strip ɗin ki?"
Jimm ta ɗan yi kafin daga baya ta wuntsila daga gadon cikin d'oki da zumud'i, binta ya yi a baya yana mata dariya, dan ya kula bata kawo hakan ba sam a kan ta tun fari sai yanzu, zuwa ta yi tai gwajin ta fito ta na murmushi cike da jin kunya ta nuna masa layuka guda biyu da ke jikin tsinken, kwab'e fuska ta yi cikin shagwab'ar da ta san ta na birkita Yayan nata tace,
"Ni dai ban gane komai ba,"
"To ko asibiti zamu je kawai a tabbatar?"
Hakan take so dan kar ta ba wa kan ta false hope akan abinda ta gani a jikin tsinken gwajin, dan haka cikin zaquwa ta ce,
"Ehhhh Yah mu je dan Allah,ina zuwa na shirya"
Barin toilet ɗin ta yi da hanzari taje ta sauya kayan jikin ta zuwa doguwar riga da babban mayafin da zai rufe har mazaunan ta, Jabeer ma tuni ya shirya cikin doguwar Jallabiyyar shi kalar blue mai farin aiki,ya ɗauki makullin mota suka jera a tare suka fita zuwa asibiti
A wani private hospital suka tsaya wadda yake a unguwar Jabi, suna zuwa suka yi duk abinda ya dace dan ganin likita, daga nan ma'aikatan wajen suka shiga yi mata gwaje-gwaje bayan an d'ebi Jinin ta da kyar sai kuka take saboda bata son allura sam,bayan kammala komai ne lab suka bata result su kuma suka kai wa likita, likitan ya tabbatar masu da tana dauke da ciki na sati uku, wata irin murna ce ta kama su gaba ɗayan su, Jabeer ba ko kunya ya daga ta sama ya hau juyi da ita, ita ko sai dariya take yi su asibitin ganin hakan ba sabon abu bane a wajen su, dan kuwa shi kan shi likitan sai yaba wa yanda ya ga suna son juna da kulawa da junan su yake yi,sumbatar labb'an ta ya yi sau ɗaya sannan ya ajiye ta,hamdala ya dinga yi ga Allah sannan ya hau godiya ma Dr. da bakin shi ya qi rufuwa, bayanan yanda zasu kula da cikin ya yi musu, wanda sun riga da sun sani tunda wannan ba shi ne na farko ba,amma sai suka koma kamar ba su taba ma sanin ya ciki yake ba tsabar murna, bayan sun gama ne suka fito Jabeer na wani lallaba ta kamar k'wai ita kuwa abin nema ya samu sai wani narkewa take yi kamar cikin ya yi watanni a jikin ta,cike da kulawa Jabeer ya ce,
" Babe me kike so ki ci kinga kar kina barin kan ki da abinda zaki haifa mana da yunwa"
kad'a kai ta yi a hankali sannan tace,
"Ni ba komai kawai ina son wainar flour ne irin ta dazu,"
Babu b'ata lokaci ya saka ta a mota suka yi gida, suna zuwa ya shiga kitchen da kan shi ya hau yi mata wainar, cup ɗin da ta yi haɗe haɗen ta ya gani a fridge sai ya tuna sanda ya na gyara parlour ya gan shi ya dawo da shi fridge dan kar ya ɓaci,dakkowa ya yi ya na murmushi, ya juye wainar da ya gama ta qarshe ya kai mata da yaji mai daɗi da ya ji garlic da busasshen soyayyan nama a ciki, tana cin wainar ta yana shan had'in, cikin santi ya ce,
"Lallai babyn nan da qoqarin shi ya zo,da alama baya so ki na shan irin wadannan abubuwan"
Dariya suka saka dikkan su Juwairiyyah ta ce,
"Idan ban sha ba ai kai gaka nan ka na sha ko?"
Qara fashewa da dariya suka yi a tare,
Hadin kantu da madarar shanu ko ta ruwa ta gwangwani ko da nonon Raqumi,had'i ne tested and trusted dake saukar da ni'ima sannan ya yi maganin wasu cututtukan jiki in baka da nonon Raqumi sai kai da madarar shanu.
*****************************
Wata iriyar shaquwa ce mai tsafta tare da so da qauna da tausayi ke wanzuwa a tsakanin Saudat da Farouq ɗin ta,wanda a kullum ganin ta ya ke yi kamar sabuwar budurwa, lallab'a ta yake yi kamar k'wai baya son duk abinda zai taɓa masa ita tsakanin su akwai tazarar shekaru bakwai, shi yasa take zuba shagwab'ar ta yanda take so musamman dan har mantawa take yi da ta taɓa aure sai wani dalili ya faru da zai tuna mata da hakan.
Wasannin su suke ta yi a palourn su kamar wasu ƙananan yara, irin wannan rayuwar Umar da Saudat ke buri a rayuwar su sai gashi sun samu abokan cika burin nasu,qafar saudat ce ta tafi gaba sai ta yi kamar za ta faɗi, da sauri Farouq ya isa gaban ta ya riqe ta ya na tambayar ta lafiya take dai bata ji ciwo ba ko ? Ganin yanda ya rikice ne ya sanya saudat murmusa wa ta kama fuskar shi a tafukan hannayen ta ta na kallon k'waryar idanun shi daga baya ta lumshe Idon ta a hankali ta sumbace shi.
Lumshe nashi idanun ya yi kafin daga baya ta janye cikin murya mai taushi ta ce,
"Me ma ka ke tambaya ta d'azu?"
Murmushi ya yi ya sauke idanun sa qasa sannan ya sake kallon ta cikin sarqewar magana ya ce,
"Amm...nace...ammm.."
Dariya suka sanya baki ɗayan su kafin Umar ya ce,
"Ina son ki mata ta"
"Ni ma ina son ka miji na fiye da yanda ka ke so na"
Nan da nan ya shagwab'e mata ya na buga ƙafa irin yanda take yi masa ya ce,
"Ah ahhhh ni dai na fi son ki"
Itama ta shagwab'e fuska ta ce,
"Ban yarda ba ni ce na fi son ka"
Dariya suka saka sosai har tana riqe ciki, d'aga ta ya yi ta bayan ta suka samu wajen zama a kujerun nasu, bayan ya kwantar da ita a kujerar ne ya kwanta ta bayan ta Shima ya rungumo ta ta ciki ta,suna ci gaba da hirar su, a hankali suka yi shiru yana mata wasa da gashin ta ta ce,
" Babe me yasa baka damuwa da batun rashin haihuwar da kasan ba zan yi ba, bayan kasan babu mahaifa a jiki na? Kuma kai baka taɓa yin aure ba, ko dai ka na da qudirin qara aure ne a nan gaba?"
Murmushi ya yi mai sauti ya sake rungume ta a jikin shi cikin kulawa da tausayawa ya ce,
" My dear ina so ki san cewa da auren da haihuwar duk nufin Allah ne, tayu a baki da mahaifan mu haihu saboda Allah shi ya san yanda yake yi ya azurta bawan sa mu namu hasashe ne da k'ayyade sai muna da kaza sannan kaza zai iya faruwa,sannan ta yu ba za mu haihun ba, to ina son ki sani, haihuwa is a blessing that everyone will love to have, amma ni bana daga cikin waɗanda suke ganin in mace bata haihuwa bata da amfani a wajen su,to ina soyayyar da ake yi mata? Dama dan Yara kawai aka aure ta? Ita ce take bawa kan ta? Idan zan maki kishiya saboda baki haihuwa tabbas na zama daga cikin azzalumai, na kuma zama daga cikin masu butulci ga Allah, domin ya min kyaututtuka mara iyaka da ba zan iya qirga su ba, to me zai sa dan akan abu ɗaya dana ke so ban samu ba na yi mai butulci? Ba zai yu ba, daga ranar da kika ji na qara aure ki tabbata na qara ne kawai dan ra'ayin kai na ko kuma ina son matar ne ya sa na aure ta Saudat, ba zan qara aure wai dan baki haihuwa,dan haka ki kwantar da hankalin ki ni ba mai ra'ayin tara mata bane bama, bana son hayaniya, ban son takura, mata da yawa na saka ni damuwa dan bana son raba fada kullum,"
Maganganun shi ba k'aramin kwanciyar hankali suka saukar wa da Saudat ba,har sai da hawayen farin ciki suka dinga fita daga idanun ta, tabbas Allah ya azurta ta da namiji ɗan gaske, Allah ya qara masa hakuri da juriya akan hakan ta ayyana a ranta.
Ci gaba da shafa wuyan ta zuwa bayan ta ya yi da sigar lallashi,a haka bacci mai daɗi ya ɗauke su.
*****************************
"Ki taho da fidar yaran nan da tissue love"
Salma amsawa ta yi shi kuma Ibraheem ya zauna yana masu wasa, bayan ta iso ne ta zauna kusa da su ta miqa masa abinda ya ce ta kai, cikin tura baki irin na shagwab'ar nan Salma ta ce,
" Ni dai gaskiya ban yarda ba nima sai an min wajen zama a nan, dan wayo kullum ni a qasa ko gefe zan zauna su kuma a cinyar ka?"
Driya ce ta kama Ibraheem, sai ya dauki Hassana ya ɗora a wuya, sannan ya d'ago Salman ya saka a cinyar shi ta na facing ɗin Hussaina,murna ta hau yi tare da sumbatar kuncin shi ta ce,
" Na goooode na zaci ai ce min za a yi na yi hakuri yaran su zauna na yi girma kamar yanda ka saba,da kuwa yau ba zan yarda ba sai dai a maida su d'aki ni na hau"
Ta ƙarasa maganar ta tana sauka daga cinyar tashi, dariya yake sosai dan ya kula da Salma ta na kishi da yanda yake share ta idan ya na tare da yaran, gani take yi gaba ɗaya ya kwashe soyayyar ta ya basu dika, lokacin shi gaba ɗaya nasu ne in yana gida, amma a qasan ranta ba qaramin daɗi take ji ba saboda yanda yake son yaran kamar nashi, hankalin ta a kwance yake
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 25