sanya ta bada umarni a gyara iya sashen ta har da ƙara d'aki ɗaya wanda na yi zaton Baba Baballiya ta sa a yi wa shi, amma ga mamaki na sai na ga ta cika shi da kayan alatu ta ce na 'ya'yan ta ne a duk sanda suka sauka a gidan, dan kuwa a yanzu sun girmi zama a d'aki ɗaya da ita suna gogar kafad'un junan su.
Haka ta yi ta gama wulaqancin ta babu wanda ya kula ta a gidan, amma ita gani take gaba ɗaya an saka mata ido a matsayin ta na uwar masu kuɗi.
A yanzu mijin Salma kawai take jira su dawo daga qasar waje a yo mata kabakin arziqi irin na qasar waje.
Ammar ne ke ta wasan shi a tsakar gida ya na tafiya abun shi dugui2, dan ba wai tafiyar ta gama wani kwari bane,tafe yake har ya samu nasarar zuwa wajen randar ruwan Mama Bilki, da dikkan alamu qishirwa yake ji, Mama Bilki kuwa na d'aka tana baccin tsakanin azahar da la'asar.
(Bacci ne da in bawa yayi shi yake samun lada daga wajen Allah)
Ita ko hakima Goggo Sarai ana zaune a ɗaya daga cikin sabbin kujerun da aka sanya mata a d'akin ta ta na kora jus da meatpie, ga mafici a hannun ta irin wanda ake zuge shi dinnan ta kwama uban baqin glass a ido irin na ba mutunci dinnan, Baba Baballiya yau a d'akin ta yake, amma gudun wulaqanci sai dare yake shigowa shi duk ranar girkin ta,kafin tace ita ke ci da gidan ko makamancin haka gwanda ya je ya nemi na kan shi idan ya dawo ya bata duk abinda ya samo sai ya koma qofar gida ya zauna sai dare.
Ammar ne ya dakko cup ya yi ta buqawa a jikin randar a qoqarin sa na son d'iban ruwan ciki ya sha, cikin Fushi Goggo ta sauke qafar ta da ta ɗora ɗaya kan ɗaya ta cire baqin gilashin idanun ta ta qanqance Idon cike da masifa sai ta ga ashe ba randar ta ake bugawa ba ta Mama Balki ce, dariyar qeta ta saki sannan ta ce,
" Yauwa yaro fasa wa uwar taka dan arziqin da ya rage mata ka huta gadon mugun abu kawai"
Bata gama rufe baki ba ya saki fitsari a wajen da yake tsaye fitsari kuwa ya sauka qasan qafafun shi ya gangara yatafi har qofar ta da aka lailaye da tiles,nan da nan ta hasalo kamar wadda aka watsa wa ruwan zafi, ta miqe ta fita kafin ta isa wajen shi kamar ya san wajen shi za ta je ya fara qoqarin tafiya yana kuka, da alama ba iya fitsarin zai yi ba ma, daidai nan ne Mama Balki ta fito daga d'akin ta ta na miqa tare da salatin Annabi,Sallama Baba Baballiya ya yi ya na Kiran Sunan Ammar da ya gani ya na tafe ya na koke koken yaran da ke buqatar wani abin.
Kafin kowa ya ankara ko ya ce wani abun Goggo ta saka hannun ta ta wanke Ammar da wani lafiyayyen marin da ko Mama Balki akai wa sai jikin ta ya gaya mata,
"Bar ganin wannan kinibabbun iyayen naka masu son abun duniya da har suke ganin D'a namiji ya fi 'Ya mace daraja ba zai hanani cin uban ka ba, in banda baqin ciki da aka koyawa yaro qarami tin yana ciki, duba fa ku ga yanda ya tsanyaran mini fitsari a qofata ya yi gaba, to ba zan lamunta ba,haka kawai ina zaune 'Ya'Yana mata da aka tsana Allah ya ɗaukaka su sun zama wani abu a rayuwa har sun gyara wa uwar su wajen zama a zo kuma a koya wa yaro qarami mugunta ya lalata min waje,"
Tsabar Ammar ya gigice sai ya kasa kukan ma sai neman inda zai je yake garin haka har kashin da yake ji ya biyo bayan fitsarin da ya yi,zuciyar Mama Bilki tafasa kawai take da b'acin rai,tin da Baba Baballiya yake da ita bai taɓa ganin irin wannan bacin ran nata ba, ita kanta Goggo Sarai ta tsorata da ganin fuskar Mama Balki, wandon Ammar Mama Bilki ta cire ta wurga a jikin qofar da aka canja wa Goggo Sarai, qofa ce irin ta qarfen nan mai kauri milk color,sannan ta aje Ammar din ta isa jikin qofar ta samu wandon ta goga sosai har labulayen, sannan ta dawo ta d'aga hannu zata wanka mata mari, sai ta tsaya bata maretan ba , ta kafe ta da wani irin kallon da ke huda gabobin jiki da tsoka ta na nuna ta da yatsan ta manuni alamar gargad'i.
Ko me ta tuna ta tsaya bata mare ta ba oho, sai kawai ta duba ta dauki Ammar da ke ta kuka yaqi yin shiru ta je ta fara gyara shi ta bashi ruwa da abincin shi ya sha ya yi bacci,sai da ta gama kula da yaron ta tsaff sannan taje ta dauke wandon nashi ta wanke ta shanya ta hau kiciniyar ɗora girki,wata irin wuta aka ɗauke a gidan gaba daya, kaff cikin gidan har Baba Baballiya ba mai iya cewa komai, Goggo Sarai na tsoron tace kanzil yanda Mama Bilki ta b'ata rai bata san me zai je ya zo ba, ita kuma Mama Bilki ta fasa marin ta ne ganin datajar Baba Baballiya dake bayan ta, shi kuma ya fuskanci hakan, sannan ya yi shiru ne saboda kar ya bata damar magana ya san kuka zata yi dan zuciyar ta cike take da baqin ciki, sai da ya tabbatar ta fara sauka tinda gashi ta ci gaba da 'yan aikace2n tsakar gida sannan ya samu waje a tsakar gidan ya zauna ya cewa Goggo Sarai,
"Yau kin ban mamaki Sarai ba kaɗan ba, ki duba ki ga abinda kika aikata, yanzu marin da kika yi wa yaron nan ko ni ki kaiwa ai sai na ji shi a jikina ba shi ba ma, dubi yanda yatsunki suka kwanta a kan fuskar shi kamar qunar wuta, haba dan Allah, kin kyauta kenan, baki taɓa ganin fushin Bilkisu a kaf rayuwar ku ba irin haka ko kin taɓa gani? to ina mai tabbatar maki ki kiyayi sakata a irin fushin nan bana kusa, dan duk abinda ta aiwatar akan ki ke kika jawo wa kan ki da kan ki tunda baki iya riqe girman da Allah ya baki ba,a iya yau dai ai kin ga misalin abinda zata iya aikata wa ko?"
Sai a sannan ne Goggo Sarai ta samu bakin magana,
" Eh tinda kun haifi ɗan gwal, dole mana ku fifita shi akan komai, to da dan da uwar na san meye matsalar ku ba komai ke damun ku ba face baqin ciki, kuma nan gani nan bari dumamen mayya in dai nice ni da 'Ya'yana yan albarka mun fi ƙarfin ku"
Cikin Fushi ta juya ta tafi fuuuu ta hau cire labulayen dika d'akin ta watso su tsakar gida ta dauki ɗaya a ciki ta goge qofar dakin da ya ɓaci da kashin Ammar da shi, ta saka ruwa ta wanke, ta qara gogewa da labulayen masu kyau din,duk kyau da tsadar labulayen haka ta saka hijab din ta ta fita waje ta watsar ta dawo, tana wani isa da taqama taje ta canja wasu,ta buga shewa da gud'a ta ce,
" Ahayyyeeeeee ayyuuuuririiiiii, to bari ku ji sau goma wannan shegen tsinannen yaron zai b'atan qofa sau go......."
Goggo sarai bata samu damar ida fad'in me take so ba ta ji qummmmmm a bakin ta, Mama Balki ce da ta hasala dan jin ana tsinewa ɗan ta ta saita bakin Goggo Sarai da ludayin da take juya miya ji ka ke kwalll ya daki fuskar ta, ihu Goggo Sarai ta saka ta na zagin Mama Balki, ita kuwa kamar ba ita ta aikata hakan ba ta je ta durqusa ta dauki ludayin ta ta juya ta ci gaba da aikin ta.
Mai Baba Baballiya zai yi da ya wuce, cikin dariya ya ce,
" Kai amma Gimbiya yau kam sai dai ace na zama munafukin mata, amma kin burgeni, ke kuma ɗan da kk kira shege, duniya ta san ni ne uban shi, sannan, tsinanne da kika kira min d'a ba za ki ga tsinewa a 'ya'yana ba inshaa Allah ina mai musu addu'a komai abinki Allah zai karen su, sai dai kiga tsinewar a kan kan ki dan ba yau na fara jin kin kira min D'a da wannann sunan ba, ke yanzu ba abin kunya bane ace ki na faɗa akan qaramin yaro har irin haka na shiga tsakanin ku ke da abokiyar zaman ki? To ina qara gargadin ki ki kiyayi randa bana gida ki taba wannan baiwar Allah ina tausaya maki "
Ya qarasa maganar cikin dariya ya fita qofar gida, duk abinnan da ake Mama bata ce uppan ba aikin ta take kawai, nan da nan kuwa bakin Goggo Sarai ya haye sama,to abinka da farar mace fatar wajen kanta ta yi jawur, d'aki ta shiga ta d'au waya ta danna Numbern su Suwaiba, dannawa ta yi tayi tana kira amma ana mata turanci, gashi yau harda Malam din aka yi fad'an ba mai duba mata yaji me ake fada, kama kan ta ta yi da taji yana ciwo ta hau kuka, zama ta yi a gefen tamfatsetsen gadon ta da ta sake mai matuqar kyau da girma, kukan ta sake fashewa da shi, sai da ta yi kuka ma'ishi sannan ta miqe ta kwanta, yau ita Bilki ke bigewa baki da luddai?
'Oh duniya, da kudin ka da komai ba za a ji tsoron ka ba yanda naga ana yi wa masu kudi, to kwarjini ne bani da shi ko me,'
Miqewa ta yi ta je gaban madubi ta kalli kanta daga sama har qasa, ga atampa nan mai tsada ta saka ta haɗa da sarqar gwal da zobuna komai ya ji, dubawa ta yi ta ga ashe fa har yanzu ko umara bata taba zuwa ba balle Hajji? Murmushi ta yi tace,
" Gaskiya mana, to ai ko kashin ku ya bushe dan kuwa dole ne wannan shekarar a sauke farali da ni naga ta raini"
komawa ta yi ta kwanta baccin wuya ya dauke ta cike da mafarkai kala2 na ban tsoro, ta dad'e tana irin mafarkan nan,a mafarkin sai ta ga 'Ya'yan ta na cikin matsala, amma sai ta dangan ta shi da sharrin maqiya masu yi masu hassada, in suka zo ganin gida za ta saka su a gaba su je neman taimako.
*****************************
Yau ce ranar da Juwairiyyah ta fi yin gyaran jikin ta kasancewar ta ranar jabeer na gida ba ya fita kasuwa,ta yi sa'a kuwa Yah Jabeer ɗin ta na gida bai fita ba,tun kafin ciki ma duk in da hannun ta ba zai iya kaiwa ba shi yake taimaka mata ya yi mata,kamar dai yanzu ma ba dika take iya wanke bayan ta ba,gashi kuma wannan abin gyaran jikin da zata yi yana buqatar a taimaka mata.
Zaune suke a tsakar gida sun fara haɗa kayan gyaran jiki,
Lemon zaqi 2,lemon tsami 1, sugar cokali 2 , Zuma cokali 1,gishiri qaramin tea spoon,dika waɗannan abubuwan ta matse ta zuba a mazubi ɗaya ta juya har Saida komai ya narke sannan ta d'akko soson wanka, ta miqa masa ta juya baya, Jabeer ne zaune a kujera 'yar tsuguno daga shi sai gajeren wando, dan kuwa ya shirya wa aikin Shima, ya na jin daɗin irin wadannan ayyukan saboda su na saka wa ya ji shi ma wani basaraken ne tun da dan shi ake gyarawa.
Gyara zama ya sake yi a Saman kujera 'yar tsuguno ya nad'e soson zai tsoma a wannan haɗin Juwairiyyah ta yi saurin riqe hannun sa ta ce,
" Yah Dan Allah sammin zan sha ya ban sha'awa"
Ta na magana tana turo baki cike da shagwab'a,
" ke fa kika ce kin ware kwanon nan ne dan gyaran jiki ko abu za a debo a ciki kin dinga kyankyami kenan shine yau zaki sha abun cikin shi?"
Cike da mamaki yake kallon ikon Allah,Sake kwab'e fuska ta yi irin na yara masu son yin kuka ta ce,
" Ni dai zan sha a haka Yayahhh"
Ɗiba ya yi a spoon din da ta gama juyawa ya bata, aiko ido a lumshe ta shanye kusan sai da ta shanye rabin haɗin, Jabeer na ganin haka yace,
"Tsaya,shin za mu yi abunnan ne ko na dawo ta gaba na qarasa baki ki shanye?"
Kad'a kai ta yi alamar A'a su ci gaba da gyaran jikin, sai sud'e baki take kamar ta ci wani kayan daɗi, fara wanke mata fuskar ta ya yi zuwa wuyan ta har bayan ta da wannan haɗin da soson,sai ya d'aga hannun ta ya wanke mata hammatar ta, sai ya dawo ta gaba ya wanke mata tsakanin cinyoyin ta zuwa cinyoyin da guiwar ta a haka saida ya hade kaf jikin ta ya wanke mata shi da wannan haɗin da soso, bayan sun gama ne ta yi masa godiya, tare da furta masa kalmar da ta zama masu al'ada wato,
" Ina son ka"
Maimaita mata shima ya yi ya d'aga ta, cikin nishi ya ce,
"Wai wai waiiii Babyna gaba ɗaya kin yi nauyi yanzu, da kyar fa na d'ago ki"
Turo baki ta yi kamar zata yi kuka, dama yasan za ai haka tsokana ce kawai da ta masa yawa ya sanya shi tanka qibar ta,dariya ya fara yana kame bakin shi, tura hannun shi ta yi daga kafadar ta zata fara tafiya, cike da tsokana Jabeer ya furta,
" Mai ciki ihmmm ganinan tafe, me ciki, wallahi bani son sunan nan,"
Juyo wa ta yi ta biyo shi suka fara zagaye bangaren na su tana kukan shagwaba, tare da fad'in,
"Inna kama ka yau a gidannan sai ka yi tsallen kwado,"
Sai huci take yi tsabar ta gaji kuma da gaske ta ɗan qara qibar, dariya Jabeer yake tayi mata harda riqe ciki dayaga ta gaji ta nemi waje ta zauna kuwa sai ya je ya duqa tare da kama kunnen sa kamar na masu tsallen kwado, cikin marairaice murya yace,
" Haba Babyn Yaya, kiyi hakuri, in dai nine na yi alqawari ba zan sake tsokanar ki ba na tuba a yafe min"
Ya qarasa maganar tare da karkata kai gefe alamun yayi nadama,murmushi ta yi sannan ta ce masa,
"Na hakura amma ka jawa kan ka kai zaka kaini toilet a hannun ka ka dawo da ni, dama na kula tinda cikin nan ya yi girma sai dai ka tallebe ni ta gefe baka daukata, bazan lamunci hakan ba ehe"
"An gama ranki ya dad'e da imani"
Murmushi suka yi wa junan su a tare suka furta,
" Ina son ka/ki"
Wucewa ya yi ya je ya haɗa mata ruwa wanka mai d'umi ba mai zafi ba,sannn ya je ya ɗauke ta kan su tafi band'akin ne tace masa
"Ina zuwa zan dau wayata,"
A haka ta na hannun shi ya kaita d'aki ta miqa hannu ta dauki wayar ta,
" Kashhhh ashe ma Nafee bata da waya, bari inna fito na leqa na karbo dankalin in ta gama hada min din"
kai ta band'akin ya yi ya dauraye mata wannan danqon, sai ga jikin ta yana wani laushi da haske, kamar wata matar masu kuɗi irin wanda fatar su ta ji hutu ɗin nan, sun fito kenan yana dauke da ita a hannu ya bada baya za su shiga parlour Nafee ta yi sallama, dakata wa ta yi, sai da aka bata izini sannan ta shiga,baje ta tadda Juwaira a kujera a zaune cike da tsokana ta ce,
"Me ciki ! Auuu Yi haƙuri na manta,ga dankalin na mai da shi ya yi laushi kamar yanda kika ce na saka lalle da k'wai amma ba dika k'wan na juye ba farin ruwan kawai na saka, bayan na haɗa na zuba gishiri da kuma manjan kamar dai yanda ki ka ce,ai d'azu da ki na nan da sai kin ci dariyar Innarmu , wai fa cewa take wani abun daɗin za a haɗa, wai Nafee, irin abun rannan zaku mana mai kwai?"
Dariya suka saka harda jabeer, sai da suka yi mai isar su sannan ya b'ata rai ya ce,
"Ya ishe ku haka Innata ce fa"
Dariya suka qara tintsirewa da ita harda shi din,sannan Jabeer ya ce
" Feena taso ayi wannan dake, kuma kiyi a hankali kar ki ji ma mata ta ciwo"
" Hummmm Masu mata"
Nafeen ta furta a hankali Jabeer kuwa ya ji ta amma sai ya ce,
"Me kk ce?"
Cikin sauri Nafee ta ce,
" Niiiii me na isa cewa, ba abinda na ce ko nake shirin faɗa ma"
Dariya suka bawa Juwairah ta yi ta yi kuwa, daga baya suka samu wannan haɗin suka yi ta murza mata a jiki kamar dilka, kafin kace me juwairah ta yi kamar wata amarya, suna cikin yi Nafee ta miqe ta dakko ayaba daya, da k'wai, sai zuma da markadadden dankalin hausan da ta markade ya yi laushi, haɗe su ta yi har ayabar suka yi laushi sosai ta koma ta saman kan Juwairiyyah tana tsaga gashin kan ta tana shafawa a can qasan gashi,shi kuma Jabeer yana yi mata dilka, bayan ta kusa gamawa ne Juwairah tace,
" Amma dai Nafee baki saka albasa a hadin yau ba ko? Dan na ji ba warin ta"
"Eh ban saka ba na san ba zaki so ba maybe ya saka ki amai shine na bi ɗaya hanyar da ki ka taɓa faɗa min na yi wannan ɗin"
" kaiiii amma ko na gode yar uwa Allah ya kawo miji na gari mumini salihi wanda zai so ki ya qaunace ki fiye da yanda Yah Jabeer ke yi min, ko dake anya za a samu kamar Yah Jabeer d'ina a wannan zamanin kuwa?"
Ta karasa maganar ta cike da tsokanar Nafeen da ta kasa amsa addu'ar saboda kunyar Yayan nasu.
Wannan haɗin na dankalin turawa da lalle da kwai da manja kaɗan da gishiri ko baqar mace ce take yi zai sanya ta yi haske mai ɗaukan hankali,dan kuwa ya na fitar da kalar mutum ta asali ya sa kalar ta yi kyau, ga laushin jiki da santsi da yake sanyawa.
Shi kuma haɗin dankalin hausa yana qara tsahon gashi ne da hana shi karyewa,sannan ana yin zallahn na albasa madadin dankalin ko dankalin a madadin albasa, kowanne yana fidda gashi sosai kuma ya hana shi karyewa, ya yi laushi da santsi, sai dai na albasa na da wari, dan haka in uwargida ta gama ana son ta samu abun wanke kai mai qamshi sosai ta wanke kuma in an saka ana son a yi massaging scalf din sosai ya shiga ko ina.
Ba su suka gama ba sai wajejen azahar, Juwairiyyah tayi bacci kafin su gama, tashi Jabeer ya yi yana miqa ya ce,
"Wai gayu da daɗi da wuya"
"Hhhhh Yah to ai kai zaka mora gwanda ka taɓa ka ji ya take ji da da take yi ita daya"
"Waya faɗa maki da din ban taya ta wasu qana nan abubuwan? Ban dai taba irin wannan me hawalar bane, ashe haka take shan wuya duk dan ta burgeni baiwar Allah"
Ya fada yana shafa gefen fuskar ta, bude idon ta ta yi ta ce,
" Ku kuma ne kuke faɗa?"
Nan da nan ta tsargu ta zaci suna magana ne akan qibar da ta yi, haɗe fuska ta yi kamar bata taɓa dariya ba, Nafee kuwa da ta gane dariya ce taso kwace mata, amma tace bari nasan me zan yi masu na gudu na bar shi da aikin lallashi,
" Ni dai daya faɗa cewa na yi ba ruwana in kika ji, dan haka ba ruwana yanzun ma ni tafiya zan yi innarmu na kirana, Yah ka fada mata"
kama baki ya yi yana mamakin sharrin da yarinyar ke son haɗa masa, kan ya yi yunqurin wani abu yaji ta janyo hannun shi gaba daya ya zube agefen kujerar da take zaune hawaye ta fara ta dora kanta a qafar shi ta rushe da kuka,
"Shikenan yanzu dan na yi qiba sai a dinga tsokana ta, ai ba muni na yi ba, kuma da na haihu zan dawo daidai"
Tana magana tana shan majina irin na masu kuka, rasa me zai yi ya wanke kan shi ya yi,dan yasan sharri kam Nafee ta gama haɗa masa shi ta yi gaba bai da hanyar fita, kamo ta ya yi ya hau massaging kafadun ta sannan ya ce,
" kiyi hakuri princess, dama gani na yi cikin ya yi girma sosai shine nace ko yan biyu zaki haifa?"
Cikin zumud'i tashi zaune ta na goge hawayen ta ta kalle shi tace
"Allah yasa yayana"
" Ameen to tashi muje mu yi wanka an kusa kiran sallah"
miqewa ta yi da kyar, a ranshi yace,
'Waiii Allah ya taimake ni, Nafee Allah na son ki da ta burkicen yau sai kin wahala kema'
Wanka suka yi ya gyara mata kan ta ya saka mata riga doguwa har qasa mai bud'ad'd'en qugu, ba qaranin kyau ta yi ba, kallon ta yake kamar kar ya daina, ita ko murmushi take ta danga wa dan ganin kyau da laushin da fatar ta tayi sai fidda wani annuri take yi, bayan sunyi sallah ne Innarmu ta aika masu da abincin su suka ci, tin da ya saka mata ruwa ta sha ta bingire a zaunen ta hau bacci, daga ta ya yi da kyar ya na nishi ya kwantar da ita a Saman gado shima ya kwanta a gefen ta dan sha baccin su tare.
Yah Jabeer kam ya dad'e kan ya samu wannann bacci ya ɗauke shi, dan kuwa haƙuri kawai ya yi ba qaramin kyau Juwairiyyah ta yi masa ba, ga princess din shi a kusa da shi,yawan bacci irin na me ciki ya hana shi more gayun da ta sha domin shi,ni ko nace sai kun tashi asha bacci laaaafiyaaa masoya......
[21/07, 7:46 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 20:
Alhj Kallah, Alhj Salihu, Oga Zaks, su kad'ai ne mutanen da na iya ganewa a qaton table din da yake cikin wani makekeken waje a zazzaune, taron wajen ya haɗa da wasu manyan Alhazawa masu ji da kuɗi, izza, taqama da qarfin iko, wanda adadin su zai iya haura mutum ashirin.
Gaba ɗayan su sanye suke da shigar tasu da suka saba yi wato shigar farin kaya da ratsin ja, kowa ka gani a wajen muzurai yake kamar su na jiran wani abu mai mahimmanci,haka zalika kowa ji yake da kan shi tare da ganin Shima ya kai wani jan wuya a wajen.
Oga Zaks ne ya yi gyaran murya, sannan ya fara magana kamar haka,
" A'a Salihu, wannan qorafin naku bai karb'u ba, kun san qa'idar qungiya, an baku damarmakin da ba kowa aka bawa irin su ba, ba dan komai ba sai dan babbar gudummawar da kuke bawa qungiya,ku kadai nake bawa damar da ban ba kowa ba a wajen nan,dan haka a wannan karon zan faɗa maku gaskiya kun bani kunya, kun karya dokar qungiya wanda ban yi zaton haka daga wajen ku ba, dan haka dole ne ku biya abinda ku ka yi,a matsayi na na shugaban wannan qungiya ina baku umarni ba shawara ba, ku je gida ku kawo matan ku nan wajen,dole ne a yanki abinda ake buqata daga wajen su, ba dan komai ba kuwa sai dan cika sharuddan Dodo, dan haka na baku nan da kwana uku, kuje ku gama sallama da su ku kawo su"
Miqewa ya yi cikin izza da fushin b'acin ran da su Alhaji Kallah suka sanya masa ya nufi hanyar waje, tafe yake dif dif dif ya na uban nishi tsabar qiba masu tsaron lafiyar shi na take masa baya,Alhj Salihu ne ya kife kan shi a Saman table ɗin gaban shi, dan a qashin gaskiya ya fara son Suwaiba duk da wautar ta da gab'untar ta,Alhj Kalla na kula da shi ya gano abinda ke cikin zuciyar abokin nashi tun ba yau ba dama ya jima ya na jin tsoron faruwar hakan dan shi Alhaji Salihu zuciyar shi bata kai ta Alhaji Kalla bushewa ba wasu lokutan ya na tausayi ko kuma ya ji ya na son mutum, wanda hakan ya sha kawo masu cikas wajen gudanar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 25