hannun su sun mayar dashi gari, sannan su yi tuwon da za a ci a gidan, ga aikin qannen su da ya ɗora masu, walaka ta yi masu yawa kamar zata kashe su,ga qaramin ciki suna fama da shi.
Jummala ce ta fito daga d'akin su da rarrafe saboda azabar ciwon cikin da ya sako ta gaba sai murqususu take yi, cikin tsawa Talle da ke zaune ya na sauraron rediyo ya na aswaki zaune Saman tabarma ya d'aga kai ya kalli Jummala ya ce,
"Ke meye hakan zaki zo kina ma mutane kuka, kin gama aikin da na saka ki ne?"
Cikin kuka da tashin hankalin da take ji a jikin ta ta buɗe baki zata yi magana sai maganar ta maqale ta kasa fita,wani abu ta ji ya taho da gudu zai fita ta qasan ta, jini ne ya tsinke mata, nan da nan ta faɗi a wajen tasuma tsabar azaba, a gigice Marka ta yi kan ta,shi kanshi uban gayyar ya tsorata da ganin jinin da ke zuba a jikin Jummalar,daukar ta ya yi a hannu ya ɗora ta a kan machin ɗin shi, marka ma ta hau ta riqe ta, asibitin qauyen suka kai ta, bayan bincike da gwaje gwaje likita ya tabbatar masu da b'ari ta yi, sakamakon ta sha wani magani na zubda ciki, ga kuma jini yaqi daina zuba a jikin ta, suna buqatar a sai mata jini a qara mata zasu yi iya qoqarin su su tsaida jinin, Talle ne ya kalli matar shi ya ce,
" Sai ki fito da kud'ad'en da kike ajewa na tarin auren su ai mata magani ko"
Ya qarasa maganar cikin haɗe fuska, kallon shi ta yi ta sunkuyar da kai da sauri, duk wanda ya hanta a wannan yanayin bai san halin ta ba zai ce zalintar ta mijin ta ke yi, a sanyaye ta ce,
"To bari na koma gida na d'akko"
Dan rashin mutuncin Talle ko duba halin da Jummala ke ciki bai yi ba haka ya na gani Marka ta taka a qafa ta d'ebi hanyan jiki duk ya mace mata ba wannan cikar da take yi da izzar nan.
Kafin ta isa gidan ne ma likitan ta fito, take sanar da Talle Jummala dai babu ita, sakamakon shan maganin zubda ciki da ta yi ba bisa qa'ida ba shi ne ya yi sanadin zub da jini mai tarin yawa a jikin ta, kuma sun kasa tsaida jinin har rayuwar ta ta qare, dafe kai Talle ya yi, nan take nadamar rayuwar shi ta baya ta baibaye shi, kuka yake kamar qaramin yaro, nan suka samu wani mai machine d'in ya taimaka masa ya nemo mai motar da zasu kai ta gida, mai machine d'in kuwa tasha yaje ya samo masa motar, Tallen ya biya shi kud'in ya masa godiya, a motar aka maida su gida shi da gawar Jummala, Marka na shirin fotowa ta koma asibiti taga an fito da gawar Jummala, zubewa ta yi a qasa ta hau kuka da bori tare da kururuwa.......
💅🏼 ' YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 24:
Saudat ce zaune a tsakar gida bata jima da aiken yaro ya siyo mata gasasshen kifi mai haɗe da chips da ake gasawa ba a wani suya spot a farkon shigowa layin nasu da ta saba ci tun lokacin 'yammatancin su, Goggo Sarai kawai ta iya bawa ta sa saura a gaba ta na ci ta na kora maltina mai sanyi, Salma mai ɗauke da ciki ce ta haɗiyi yawu saboda ranta ba qaramin biyawa ya yi ba,amma haka ta danne kwad'ayin ta dan ta san ba bata Saudat za ta yi ba,sai da ta ga ta kammala ci ta wanke hannu ta koma ta zauna a kujera ta na latsa waya sannan ta isa wajen ta ta gaishe ta, a daqile ta amsa ta na karkad'a qafar ta ɗaya da ta ɗora Saman d'ayar,cikin wani maqasqancin kallo ta ce da Salma,
"Meye ki ka zo ki ka tsaya min a ka,idan gaisuwa ne ai mun gaisa ko sai a yi gaba tunda an sauya uwa,idan kuma wani abu ki ke da buqata ki yi gaggawar sanar da ni dan bana so a tsaya min aka"
Murmushin takaici Salma ta yi,nan take ta hau tuna baya yanda yayun nata ke ji da ita suke ɗora ta a hanyar karb'ar kud'in maza, ba su jin kunyar nuna mata yanda za ta yi wa namiji kwarkwasa da taɓa bikin shi san ya bata kuɗi shi ne yanzu dan ta zaɓi hanya mai kyau suke gudun ta, cikin magana mai cike da ladabi ta ce wa Saudat ɗin,
" Adda Saudat dan Allah zuwa na yi ki ɗan bani koda dubu d'aya ce ina son in ɗan ja jari ne ko Saida gishi da omo ɗan qulli ne in fara yi a cikin gida, saboda zaman haka baya min daɗi ba kud'in kashewa,ke ma kuma ina mai baki shawara da ki nemi abun yi da kud'in da ya rage maki tun kafin su qare saboda yanzu kin ga kin saba da kudi, randa kike da buqatar su kika rasa ba qaramin damuwa zaki shiga ba"
Tunani Saudat ta shiga yi mai zurfi, can ta nisa tace,
"Gaskiya kin ce wani abu kema, zan baki dubu biyar ki ja jarin, ni kuma zan fara kasuwanci ta waya da naga qawaye na da na yi a whatsapp da facebook suna yi, ana samu sosai in ka riqe amanar mutane, sai kaga ka samu riba mai yawa kana daga zaune"
"Yauwa Addana na gode sosai, sai wata magana kuma mai mahimmanci da nake so mu yi ni da ke, ina son ki gane Mama Bilki mace ce mai kirki tana matuqar son mu, sai dai tabbas tana kishi da Goggo, wanda wannan dole ne a zaman kishiyoyi dama,shiga wannan kuma ba hurumin mu bane mu kau da kai akan wannan mu bar su su yi kishin su after all miji ɗaya suka haɗa,abinda kawai za mu yi shine mu yi masu biyayya dikkan su a matsayin su na iyayen mu,"
Shiru Saudat ta yi domin maganar qanwar ta ta yau tana shigar ta dan gaba ɗaya ba qarya a ciki amma akwai nau'i na girman kai da taya Goggon su kishi a zuciyar ta,dan haka sai ta yatsuna fuska ta ce,
"Hmmmm zan duba maganganun ki na gani"
Sannan ta miqe ta d'akko mata kud'in da ta alqawarta zata bata ta bata, duk abinda ya faru akan idon Goggo Sarai ya faru, sai dai bata ji kalaman da suke yi ba ta dai ga an bawa Salma kuɗi,magana take cikin b'acin rai,
"Habaaaa Salma ai innice ke yanda na canja uwa, yan uwan ma canja su zan yi, auhoooo ba zaki iya canja yan uwa ba saboda su masu arziqi ne Zaki yi roqo za a baki , amma ita uwar ki tinda talaka ce shi yasa ki ka sauya ta"
" Ni fa Gogga ba haka bane, ya kamata ki buɗe idon ki ki gane inda gaskiya ta dosa, ki daina rufe idon ki ki na yin abinda bai kamata ba"
"Rufen baki sallamammiya kawai, an yi asiri da tuggu kala2 an raba ni dake, to ki je nima na huta da dawainiya da ɗan wani"
Juyawa ta yi tabar wajen Salma kuwa cikin qunan rai da baqin cikin halayya ta uwar ta ta shige d'akin Mama Bilki, wadda ta ji komai da ya faru, fad'awa kan cinyar ta Salma ta yi tana kukan takaicin hali irin na uwar tasu, shafa kanta kawai Mama Bilki take, bata furta mata komai ba,cikin kuka Salma ta ce,
" Mama ni fa ba kwad'ayi ne ya sa na tambayi Adda Saudat kudi ba, na tambaye ta ne kawai saboda ki na ganin ko tirare bani da shi, ga shi yanzu sai da alimun ko lemon tsami nake amfani a hammata ta a madadin tiraren,da ace ina sana'a yaushe zan zauna haka? Tunanin da na yi na ina sana'a kudin zasu taimakan wajen kula da abinda ke ciki na da ni kai na shine ya sa na tambayi Addah Saudat kuma ta bani dubu biyar na ja jari, shine Goggo take fad'an maganganu marasa daɗi akai na da abinda ke ciki na"
" Hakuri zaki yi Salma uwa ba abin wasa bace, dole mu yi mata biyayya matsawar ba sab'on Allah a duk abinda ta sanya mu,dan haka ki yi hakuri, to tin da kin samu jarin yanzu me zaki na yi na siyarwa?"
Tashi zaune Salma ta yi ta share hawayen ta sannan ta ce,
" Mama Bilki ni da ina son na fara saida gishiri da omo da ɗan qulle qulle na gida, amma yanzu da na samu wannan kud'in mai yawa sai na ji ina son in fara Saida Meatpie, naga kina da injin yin taliya, kuma na kula kayan flour ana cinikin su, in ba su ba ban san me zan iya yin sana'a akai ba kuma"
Murmushi Mama Balki ta yi sannan ta ce,
" Hakan ma shawara ce mai kyau, Allah ya sanya albarka a ciki"
" Ameen mamana"
Kwantar da kanta ta sake yi a jikin ta ita kuma tana shafa gashin kan Salman a hankali.
******************************
Yau kusan sati ɗaya da kwana uku kenan Suwaiba na kwance tana jinyar qirjin ta da aka fafe wa albarkatun wajen, Alhj Salihu dayaga zata farka sai ya danna mata allurar bacci ta koma, ko ya shaqa mata wata powder ta koma baccin, a haka ta yi wadannan kwanakin,shine yake yi mata wanka ya canja mata kaya,sannan ya saka mata ruwa da allurai na kashe zafin ciwo da anti biotics,ya zama babban likita kawai a cikin gidan shi dan ya kula da Suwaiba, a haka sai da ya kula wajen ya warke tas sannan ya kyale ta da allurai na bacci da yake mata.
Ranar da ya bar ta kuwa bai yi mata allurar baccin ba da ta farka sai ta ji kan ta kamar an ɗora mata abu mai nauyi, da kyar ta tashi daga gadon ta ta isa gaban madubi a hankali ta d'aga rigar ta ta na kallon qirjin ta, nan take wasu hawaye masu azabar zafi suka hau zuba a kuncin ta, ina dukiyar Fulanin ta suke ne, me ya same ta?
Duk abinda take yi akan idanun Alhaji Salihu take aikata su, cikin rashin k'warin jiki ta koma ta kwanta a Saman gadon nata tare da nitsar da kan ta cikin pillow kuka take yi sosai mai taɓa zuciya, zama ya yi a gefen ta ya kama hannun ta ya na lallashin ta, a hankali ta d'aga kan ta ta na kallon shi,da kyar ta buɗe baki ta ce masa,
" Sweet wai me ya same ni ne, wanne mummunar qaddarar ce ta hau kirji na ni suwaiba ?"
" Shiiiiiiii kar ki na yin magana sosai, hatsari muka samu a gidan, yan fashi ne suka suka shigo a ranar da ki ka dawo kina bacci suka yanke maki nono, ni kuma dana dawo na ganki kin suma shine na kai ki asibiti aka maki aiki daga nan na dawo da ke gida nake ta kula da ke"
A firgice ta miqe daga kwanciyar da take ta ce,
" Dama abinda ya faru kenan? Yanzu tsabar rashin imani su rasa me za su cire min sai wannan waje mai daraja?"
Ta fada tare da zaro idanun ta da ke ta zubar da zazzafan hawaye, cikin kukan nata ta ce,
"Na shiga uku ni Suwaiba,ya zan rayu ba mahaifa ba nono,yanzu nan gaba me zan rasa kuma, Alhj na fa san kai ne sanadin rasa nono na ba wani 'yan fashi,Saudat ta fad'an min ban ji ba ban yarda ba, saboda ina son ka, ko da ina son kudin ka na yarda cewa a yanzu ina son ka so na gaskiya,zan iya rayuwa da kai ko ba mahaifa shine hakan be ishe ka ba sai da ka qara da wata kadarar tawa yanzu ta ya zan rayu ba nono ba mahaifa"
Rushewa ta yi da wani irin kuka mai ban tausayi, cikin tausaya mata Alhj ya fara magana"
"ki yi hakuri Baby yau zan........"
katse shi ta yi cike da bala'i ta ce,
" Kar ka sake kira na da wata baby again, i hate u Alhaji, na tsane ka, na tsane ka da dikkan rayuwa ta"
Kukan ta ci gaba da yi mai ratsa zuciyar mai tausayi kai har da mara tausayin ma,matsawa ya yi ya kamo ta jikin shi, da sauri ta zame ta ci gaba da cewa,
" Kar ka taɓa ni azzalumi kawai,ka kuskura ka sake taɓa ni ni ma sai na yanke maka inda ba zaka taɓa amfanuwa ba a jikin ka"
Cike da matsanancin fushin da bai taɓa sanin suwaiban da yake wa kallon doluwa na da shi ba ta yi maganar,nan take wani irin shakkar ta ta shige shi, miqewa ta yi cike da jiri zata fita, cikin sassanyar murya Alhaji ya ce mata,
"Ina zaki je kuma"
"Gidan mu zani, na gama auren ka, na kuma gama aure a ABUJA har abada daga yau,daga rana mai kamar ta yau bani ba Abuja"
" Lallai ma Suwaiba, abinda baki sani ba shine, ba inda zaki qara fita ko nan da can ne kuwa sai da sani na, dan kuwa ni a yanzu ba zan iya rayuwa ba ke ba, kin ga kuwa sai ki shirya zama da masoyin ki na gaskiya, na amince ni zan jure rashin albarkatun qirjin naki tunda ni ne sanadi"
"Za kuwa ka mutu dan ba abinda zai hana ni barin gidannan, ko kana so ko baka so sai na bar gidan nan, in ka barni na tafi lafiya ba hukumar da zan haɗaka da ita, amma in ka hanani ba abinda zai hana ni haɗaka da hukuma zaɓi ya rage ya naka"
Wani shu'umin murmushin rainin hankali ya mata ya ce,
"To ai baki san wani abu ba, qungiyata babbar qungiya ce suwaiban,ni ɗin ba wai qaramin mutum bane ko baki gani bane?manyan gwamnati da yan kasuwa ba wanda babu a cikin qungiyar mu, ba yanda za ai ki had'a ni da hukuma kuma a samu hukunta ni din, mata kalar ki da wanda suka fiki komai sun fi dubi kuma mun masu wannan aikin balle ke, dan haka hakuri zaki yi kawai mu qarasa rayuwa dake a haka, in kin tafi wa zai na baki abun daɗin da nake baki? wa zaina debe maki kewa? wa zai zauna dake babu nono? Hakura zaki yi kawai mu zauna a haka tun da kuɗi ki ke so ni kuma zan ci gaba da jiyar dake daɗi da dukiya ta"
Tallabo wuyan ta ya yi ya na kallon fuskar ta,iya kuwa gaba ɗaya ta qame ta dauke kan ta daga ganin shi hawaye kawai ke zuba mata, ga wani irin tsoron shi da ke kwance a qasan zuciyar ta, yau ya zata yi ta kub'uta daga hannun wannan azzalumin?
Kuka ne ya kwace mata sosai, key din motar shi ya ɗauka ya fice ya bar mata gidan, anan inda take tsaye ta durqushe tana kuka mai ban tausayi.
*****************************
Talle kam ya saka marka a tsaka mai wuya ita da yayan shi, dan baya son maganar ta fita waje shi yasa bai ce masu qala ba,sai kawai ya fito da wata mugunta, gonar shi ta daji mai shegen nisa ya ke sa su zuwa gyaran ta, duba da cewar damuna ta kusan zuwa, a cewar shi ya na da majiya qarfin zuciyar cim amana irin su ba abinda zai sanya shi biyan kud'in gyaran gona,in sun ga dama in sun shiga dajin ma su ci amanar shi ya yafe masu amma tabbas sai sun gyara masa gona kafin damina ta sauka.
kullum can suke tafiya ba abinci ba ruwa, amma shi zai je a machine din shi da abincin shi da ruwan shi ya yi shawagi ya sa ido ya ga ya aikin yake tafiya,su kuma su Baban gida gonar shi ta can wani qauyen dake kusa da su ya tura su, saboda ya yi yarjejeniya da su akan hakan, in ba haka ba ya kaisu birni ga hukuma a huhunta su akan yi wa 'ya'yan shi ciki da suka yi,da jin haka suka amince suka yi biyayya suma.
Kan kuce me Marka ta fita hayyacin ta, 'yan mazaunan nan da ake kad'awa ana jan hankali da su duk sun zube, duk ta dame qashi ya fito mata ko ta ina,mutanen gari kuwa sai gulmammaki suke yi akan abinda ke faruwa a gidan Talle, kowa da ruwayar shi akan abinda ke faruwa amma ba wanda ya san gaskiyar lamari.
Kowa ya rasa gane dalilin Talle na aikata haka, da damar mutane sai suka alaqanta hakan da tsantsar rashin mutuncin shi, su Huwaila kuwa kullum sai sun yi surfen abinda za ai tuwo da shi sun dake da hannun su sun mayar dashi gari, sannan su yi tuwon da za a ci a gidan, ga aikin qannen su da ya ɗora masu, walaka ta yi masu yawa kamar zata kashe su,ga qaramin ciki suna fama da shi.
Jummala ce ta fito daga d'akin su da rarrafe saboda azabar ciwon cikin da ya sako ta gaba sai murqususu take yi, cikin tsawa Talle da ke zaune ya na sauraron rediyo ya na aswaki zaune Saman tabarma ya d'aga kai ya kalli Jummala ya ce,
"Ke meye hakan zaki zo kina ma mutane kuka, kin gama aikin da na saka ki ne?"
Cikin kuka da tashin hankalin da take ji a jikin ta ta buɗe baki zata yi magana sai maganar ta maqale ta kasa fita,wani abu ta ji ya taho da gudu zai fita ta qasan ta, jini ne ya tsinke mata, nan da nan ta faɗi a wajen tasuma tsabar azaba, a gigice Marka ta yi kan ta,shi kanshi uban gayyar ya tsorata da ganin jinin da ke zuba a jikin Jummalar,daukar ta ya yi a hannu ya ɗora ta a kan machin ɗin shi, marka ma ta hau ta riqe ta, asibitin qauyen suka kai ta, bayan bincike da gwaje gwaje likita ya tabbatar masu da b'ari ta yi, sakamakon ta sha wani magani na zubda ciki, ga kuma jini yaqi daina zuba a jikin ta, suna buqatar a sai mata jini a qara mata zasu yi iya qoqarin su su tsaida jinin, Talle ne ya kalli matar shi ya ce,
" Sai ki fito da kud'ad'en da kike ajewa na tarin auren su ai mata magani ko"
Ya qarasa maganar cikin haɗe fuska, kallon shi ta yi ta sunkuyar da kai da sauri, duk wanda ya hanta a wannan yanayin bai san halin ta ba zai ce zalintar ta mijin ta ke yi, a sanyaye ta ce,
"To bari na koma gida na d'akko"
Dan rashin mutuncin Talle ko duba halin da Jummala ke ciki bai yi ba haka ya na gani Marka ta taka a qafa ta d'ebi hanyan jiki duk ya mace mata ba wannan cikar da take yi da izzar nan.
Kafin ta isa gidan ne ma likitan ta fito, take sanar da Talle Jummala dai babu ita, sakamakon shan maganin zubda ciki da ta yi ba bisa qa'ida ba shi ne ya yi sanadin zub da jini mai tarin yawa a jikin ta, kuma sun kasa tsaida jinin har rayuwar ta ta qare, dafe kai Talle ya yi, nan take nadamar rayuwar shi ta baya ta baibaye shi, kuka yake kamar qaramin yaro, nan suka samu wani mai machine d'in ya taimaka masa ya nemo mai motar da zasu kai ta gida, mai machine d'in kuwa tasha yaje ya samo masa motar, Tallen ya biya shi kud'in ya masa godiya, a motar aka maida su gida shi da gawar Jummala, Marka na shirin fotowa ta koma asibiti taga an fito da gawar Jummala, zubewa ta yi a qasa ta hau kuka da bori tare da kururuwa.......
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 25:
Tun fitar Alhaji Salihu da safe suwaiba ke zaune tana ta saqa da warwarar neman mafitar yanda za ta kubuta a gidan amma shiru bata samu mafita ba,ta yaya aka yi ta rasa albarkatun qirjin ta? Ko dai da gaske 'yan fashin ne suka yi mata wannan ta'asar, anya kuwa ba maganar Saudat bace gaskiya Alhaji ɗan qungiyar asiri ne masu tsafi da sassan jikin bil'adama? Waɗannan tambayoyin da ma wasu tunane tunanen ne suka haɗu suka yi wa suwaiba yawa ta yanda ko sallah bata tashi yi ba balle ta nemi abinda za ta ci duk tsawon lokacin nan.
Shi kuwa Alhaji Salihu yana can ana sa toka sa katsi tsakanin shi da Oga Zaks akan wata yarjejeniya da suka kulla wadda ko Alhj Kalla bai san da ita ba,kafin Oga zaks ya amince za su bar suwaiba a raye ba za su kai ta d'akin duhu ba dodon tsafi Itama ya zuqe Jinin ta bayan an yanke nonon ta, sai da Alhaji Salihu ya ɗauki alqawarin idan ta warke an kwana biyu zai kai wa Oga Zaks ta yi sati biyu wajen shi, wannan yarjejeniya ce ta d'aga masa hankali har ya je wajen Ogan nasu dan a bincika idan akwai wani abu sassauqa a sassauta masa ya aikata,dan kuwa a wannan karon ba zai iya bada matar shi a Kai wa wani qaton ya na kwana da ita ba ko da na kwana ɗaya ne balle har tsawon sati biyu,ya kamata a kyale ta haka ta wahala kuma shi fa yana son matar shi yanzu.
Duk bayanin da Alhaji Salihu ya yi wa Oga Zaks sam ya qi aminta da shi,yace shi fa bai san zance ba, nan da sati ɗaya zai buqaci a Kai Masa ita in dai ya na so dukiyar shi ta dore ba tare da ya samu matsala ba, dan kuwa idan har bai kai masa ita ba duk abinda ya same shi shi ya sani ya kuka da kan shi kar ya ɗora laifin akan kowa, hankalin Alhaji Salihu a tashe ya koma gida.
Zaune ya tadda ita ta fada dogon tinani ba ta ma san shigar shi parlourn ba, qarasa wa ya yi ya zauna kusa da ita a doguwar kujera, a hankali ya zame ya ɗora kan shi a cinyar ta ya rufe idon shi, cikin kulawa da tsoro ta fara shafa kanshi sannan ta ce,
" Alhjna me ya faru? Me ke damun ka haka? Dan Allah ka barni na koma gida na amince zan rufa maka asiri ko dan darajar son da nake yi maka, ba wanda zan sanar da halin da ake ciki ni dai ina so rayuwa ta ta tsira"
Bai bata amsa ba sai ma hawaye da ta gani ta gefen idon shi suna sauka, hawaye ne na nadamar shigar shi wannan qungiya da ya yi tun farko a rayuwar sa, dan yanzu soyayyar Suwaiba ta yi masa yawan da ta sanya shi farkawa daga baccin son abin duniya da yake yi,duk da ya san ita har yau tana nan akan bakan ta na son cin daula,matsala ɗaya wannan babban rashin kadarar qirjin ta da ta yi ya sani da zata samu wata damar da zata zauna da shi ko dan kud'in shi, a hankali ya ce,
" Baby ki kwantar da hankalin ki akwai maganar da zamu yi dake yanzu, wadda na san kin sani an kuma sanar dake gaskiya tun kan ku dawo son abun duniya ne ya rufe maki ido ki ka sake dawowa,"
Tashi zaune ya yi da kyau suna fuskantar junan su ya riqe hannayen ta ya fuskance ta suna shaqar nunfashin junan su, kanta har juyawa yake saboda tsoro, tana matuqar jin tsoron ya tabbatar mata da abinda Saudat ta faɗa duk da ta ga manyan alamu a yanzu,tun da gashi ya yi nasarar maida ita Nonoless and mahaifaless,tinanin ta ya katse ne a daidai lokacin da kalmar da take matuqar jin tsoron tabbatuwar ta ta daki dodon kunnen ta,
" Ni Alhaji Salihu ɗan qungiyar shan jini ne, domin samun kuɗi ɗaukaka da qarfin iko"
Wani irin ihu suwaiba ta kurma ta dafe qirjin ta da yake a shafe kamar na matashin saurayi,miqewa ta yi jiki na rawa kamar mazari dan ta nesanta kan ta da shi amma jiri da duhun da take gani sun sanya ta komawa ta zauna ,lallai maganar Saudat ta gama tabbata a yau, maganar zargi da waiwai ta qare,hannun ta ta kai jikin fuskar shi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 25