dan bata tsammaci hakan a wajen saurayi da bai taɓa aure ba kuma gidan su babu qananan yara balle ta ce ya iya reno.
A cikin kujerar basu abinci ya saka su,ya ɗorawa kowa nata abincin a gaban ta, sannan ya damqa masu cokulan su a hannun su na dama,da kyar suke riqewa saboda rashin iya hakan, yana tsaye a kan su in ya ga zasu karkace ya gyra masu, ta baya ta ziro hannun ta ta tsugunna itama ta kwantar da kanta a bayan shi ta furta,
"I love u"
Shima waiwayar da kan shi ya yi suka hada ido yace mata,
" I love u more my wife"
Tare da sumbatar goshin ta ya juya ga yaran su suma ya yi musu,Salma ta tura baki ta ce,
"Na hakura ni dai na saddaqar an fi son su akai na, ba za a taɓa yi min abu ba sai an yi musu suma"
Dariya ya yi kawai dan ya san idan zai biye mata haka za su kwana ta na masa qorafi.
Jama'a ina so mu gane cewa shi d'a na kowa ne, baka san wa zai more shi ba,shi yasa bahaushe ke cewa da d'a da dukiya ba a yi masu mugunta, in ka lalata su wataqila kai ka lalata wa goben ka da al'umma, idan kuma ka kyautata musu wataqila su amfane ka a gaba ko su amfani al'umma, wani sai ya gama tarbiyyar yaron ya girma saura qiris ya fara morar shi sai ya rasu ya bar wa duniya ta mora,wani kuma sai ya lalata tarbiyyar sai ya mutu ya bar wa duniya mugun iri ko rayuwar shi ta yi tsaho ai ta shan wahalar da shi,wanda ya kyautata ya na da lada mai yawa a wajen Allah, wanda kuma ya munana shi ma ya na da zunubi a wajen Allah .
*****************************
Talle ne ya shirya tsaf da yar jaka a hannun shi wadda ta qunshi kayan yara mace da namiji dan bai san me Salma ta haifa ba, ko ma dai me ta haifa zai kai mata kayan ya fi ya je hannun shi na dukan cinyar shi,sallama suke yi da Marka wadda can cikin qasan ranta kishi ne danqare,sai ta danne kishin nata saboda yanzu ta waye ba duhun qauyanci da mummunan jahilci a tattare da ita, miqa masa leda ta yi wadda ta daka kuka,daddawa, da kub'ewa, tace ya kai wa Salame, godiya ya yi mata,Huwaila ma shiga sashen nasu da qullin ledar gyada soyayyiya itama ta bashi, dan sana'ar ta kenan a yanzu, tace ya gaida su ya nema masu gafar ta, amsa ya yi ya fita bakin shi ɗauke da addu'ar fita daga gida........
*To masu karatu Talle fa ya yi shirin zuwa Ta dabo,kun dai ga ya koma islamiyya har da addu'ar fita daga gida...*
[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏻 'YAN ABUJA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE : 35
https://chat.whatsapp.com/I8ImAD44ZKU2x8N4dbCpDr
https://Wa.me/+2348036802447
*INA AMARYA INA UWAR GIDA HARDA MAI JOGO DA KE MAI SHIRIN ZAMA AMARYA MUNYI MAKU TANADIN KAYAN DA ZASU GYARA KU TSAB TSAB KIFITO DAGWAS DAKE KAMAR KE KIKA KERA KAN KI SANNAN KADA KU MANTA MUNA HADA JEGO PACKAGE BRADAL PACKAGE & SLIMMING PACKAGE WEIGGHT GAIN PACKAGE GA KUMA ANTI AGAIN PACKAGE SUPER WHITENING CAMBO BREAS AND HIPS PACKAGE GLOWING SET SKIN REPAIR ND REJUVENATIG PACKAGE BEAUTY START FRM WITHIN TAKE CARE OF THE*💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 35:
Ammar ne zaune a tsakar gida ya na wasa irin na yara, ƙasa ce yake kwab'a wa da ruwa a buta,tare da rero karatun da Mama Balki ke koya masa,daga ya yi na qur'ani sai ya saki ya kama na boko,ya na nan zaune ya ji ana buga kofa tare da yin sallama,tashi ya yi ya nufi k'ofar gidan da gudu tare da yin wurgi da karan hannun shi da yake juya tuwon qasar shi,ya na zuwa ya d'aga kan shi sama ya na kallon mai yi masu sallama.
Murmushi Talle ya yi da ya ga yaron nan take ya hango kamannin da ke tsakanin Salame da yaron, a hankali ya durqusa dai-dai tsahon Ammar ɗin sannan ya ce,
" Yaro ina malam,"
" Faya nan" ( Baya nan),
Talle ne yaga yaron ya kalli gaban shi yana dariya daga baya kuma ya fita da gudu yana fad'in
" Babana Oyoyo"
Wajen da Ammar ya nufa Talle ya bi da kallo,idanun shi ya sauka cikin na Baban su Salame,da saurin shi ya isa gaban Baba ya durqusa, gane wanene a gaban shi ne ya sanya Baba ya sauya fuska daga fara'a zuwa bacin rai, a hasale ya ce wa Talle,
"Me ya kawo ka k'ofar gida na a yau?"
Cikin sunkuyar da kai cike da tarin nadama Talle ya ce,
"Baba dan Allah da son Annabin rahama ka yi hakuri ka saurare ni,Baba na san na tafka babban kuskure a rayuwa ta wanda zan mutu ina nadamar aikata shi dan Allah Baba ka yafe min, tabbas na kasance daga cikin jahilai, marasa sanin Allah a baya, sakamakon jahilcin da ya mamayi zuciyata, kuma naqi na nemi sanin Allah da dokokin shi, ina jin girman kai da ganin na wuce na nemi ilmin addini na yi girma da hakan, shiyasa na aikata munanan abubuwa a rayuwata kala-kala waɗanda naga isharar su tun kan aje ko ina, babbar isharar da na fara gani shine mutuwar 'ya ta,sannan na kama dan uwana Yayana da mata ta suna zina, ɗaya 'yar tawa ga ta can da ɗan gaba da fatiha, babbar isharar da ke d'aga min hankali itace rabuwa da Salame da na yi, ta tafi da cikina na rabu da ita rabuwa da ban nuna tausayi da imani a ciki ba,a yanzu nayi nadama, na koma islamiyya ni da iyalina dika, ka yafe min ba dan halaye na ba sai domin Allah"
kalaman shi sun saka jikin baba ya yi sanyi amma sai ya wuce cikin gida kamar bai ji shi ba, yana shiga Mama Bilki ta sauke shi da ruwa da abinci, ga kuma ruwan wanka ta kai mashi bayi,zufa ta hau goge masa tare da jera mishi sannu da zuwa cikin tattausan lafazi, umartar ta ya yi da ta kira yayar tata,miqewa ta yi ta tafi Kiran Goggo, ta na shiga ta tarar da Goggo Sarai ta yi zurfi a cikin tinani har bata san shigar ta d'akin ba ma, yanzu da hankali ke qara shigar ta ba qaramin kunyar Mama Bilki take ji ba akan abubuwan da ta yi mata a baya, saqon Baba Mama Balki ta isar mata ta fita ta fara yin gaba,itama tasowa ta yi kamar wadda kwai ya fashe ma a ciki, ta bi bayan ta ta na shiga ta gansu zaune ita kaɗai ake jira ta samu waje ta zauna ta ce,
" Ga ni baban su"
D'agawa ya yi ya kalle su cikin sha'awar yanda suka koma a nitse ba hayaniya ko mummunan kishi, Ammar ne yaje wajen Goggo Sarai ya zauna a cinyar ta, shafa kanshi ta yi tana mai murmushi, cike da natsuwa Baba ya labar ta masu zuwan Talle da abinda ya sanar da shi, sannan ya tabbatar masu da cewar yanzu haka Tallen na qofar gida, haquri ya bawa Goggo Sarai da ya ga ranta ya baci, ya na juyawa yaga fuskar Mama Bilki ma a b'ace, mijin Salma ko da ba matsafi bane ya cutar da ita a zamantakewar su shima ba qaramin azzalumi bane, kwantar masu da hankali ya yi da dad'ad'an kalamai a hankali suka sauke fushin su, aika Ammar waje ya yi yace yaje ya shigo da baqon nan, cikin tsalle-tsallen yara ya tafi ya sanar da Talle Baba na Kiran shi.
Talle ne ya shiga kai a duqe qafa duk ta sage masa saboda tsaiwa, waje baba ya nuna masa a kan tabarma, tsakiya ga abinci nan da ruwan sha, Goggo Sarai ce ta qaro ruwan sha da ɗan abin motsa baki dangin su cincin ta ajiye musu, ci suka yi suka qoshi, sannan Baba ya kira su baki ɗaya suka zo suka samu kujeru na tsugunne suka zauna kowaccen su sanye cikin hijabi,bayan sun gaisa da Talle ne Baba ya ce,
" To da farko dai zan fara cewa alhamdulillah,dikkan godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai,sannan in sanar da kai dukkanin mu nan iyayen Salma mun yafe maka abinda ka aikata a baya, kuma muna saka ran itama ta yafe maka, tabbas ka cutar mana da yarinya, ka zalunce ta, amma duba da cewar muma masu zunubi ne a wajen Allah kuma mu roqe shi ya yafe mana banga dalilin qin yafe maka da muka yi ba, daga qarshe ina mai sanar maka yanzu haka Salma na Abuja gidan kuɗi gidan hutun dai da take fata da buri a rayuwa ita da yaran ka, dan kuwa biyu ta haifa dika mata,kuma ta samu miji saurayi ya dauki yaran kamar shi ya haife su, ni ba zan sanar da kai ina Salma take ba a yanzu dan ta fara samun farin......."
" Ban katsi nunfashin ka ba baba, amma tabbas nima ba zan so abinda zai hana ta farin ciki ba a dai-dai wannan lokacin, tabbas na amince su ci gaba da rainon yara na a tare ba dan ina gudun d'awainiya ba, lokaci zuwa lokaci zan dinga zuwa nan ɗin dan mu gaisa,ga address d'ina saboda wataran ko za a buqaci hakan,"
Takardar da ya rubuto adireshin sa tun a gida ya zaro ya miqa ma baba, idon shi ya kad'a ya yi jawurr, tabbas har yanzu akwai son Salma a ran shi, wanda a da ya ɗauka sha'awa ce kawai sai yanzu da hankalin shi ya dawo jikin shi ya gane ba hakan bane,miqawa baba ledar hannun shi ya yi ya masu sallama dan komai dare gida yake son ya kwana zaman Kano ba nashi bane, Mama Balki ce ta d'akko hotunan yaran guda uku ta bashi ya riqe ya na kallo hawaye na zuba a idanun shi.
Kaff haife haifen da sauran matan shi suka yi ba wadda ta haifi 'yan biyu, sannan babu mai kyaun wadannan da ya kora tun kafin su zo duniyar, tashi ya yi bayan ya sake yi masu sallama da godiya ya isar da saqon su Huwaila da Marka,godiya suma suka yi masu tare da bada saqon gaisuwa a Kai masu, ya kama hanya ya tafi sai qauyen su.
*BAYAN SHEKARA UKU*
Yau ta kama ranar Asabar ce kowanne ma'aikacin gwamnati ya na gida ya na hutawa da iyalin shi, bangaren 'Ya'yan Alhaji Baballiya kuwa su na can sun tare a Abuja gaba ɗayan su, Suwaibah da Abrar ne suka kai masu zira wanda da kyarrr aka samu Suwaibah ta yarda ta sanya qafafun ta a garin Abuja dan kuwa har a wannan lokacin ba ta jin so da qaunar Abuja a ran ta, Alhaji Salihu kuwa shi ya biya kud'in jirgi suka tafi ya ce idan an gan shi a Abuja to gawar shi ce amma ba dai ya koma mata ba da rayuwar shi da kuma qafafun shi.
A gidan Juwairiyyah duk suka taru, duba da cewa Jabeer shi ne babba sai ta ci wannan girman ake yawan taruwa a gidan ta, hira suke ta sha tare da tuna yarintar su suna dariya ma junan su,wayar saudat ce ta yi qara alamar shigar saqo ta na dubawa ta ga mijin ta ne, murmushi ta yi ta samu wata kujera ta zauna ta na ci gaba da hira jefi-jefi sannan ta na chatting da mijin ta da ke can k'aramin parlour shi da Jabeer da Ibraheem.
Abrar ce ta shiga da mashacin gashi da kibiya ta zauna a jikin Suwaibah ta ce,
"Mom dan Allah ki yi min kalba guda huɗu irin na 'yan biyu ya bani sha'awa"
"Ah toh dai,a ce wai mutum baya son kitso sam a rayuwar shi gashi Allah ya hore masa gashi?"
"Ni dai dan Allah Mom kar ki yi faɗa zan yi kuka"
Gum Suwaibah ta yi da bakin ta ta karɓi kayan kitson ta raba mata kanta huɗu ta fara kitse mata, suna ci gaba da hira.
'Yan biyu ne suka shiga da gudu su na wasa yara sun girma sosai, dika-dika ba za su wuce shekara uku ba, amma iyayin su da maganar su sai mutum ya rantse sun kai shekara huɗu ko biyar,wasa suka hau yi suma Salma na yi masu faɗa akan yanda suke ta rikici,sam ba su zama waje ɗaya ba su yi faɗa ba, sannan kuma ba su iya zama ba tare da junan su ba,Ibraheem ne ya yi sallama ya shiga,bayan sun amsa ne yaran suka nufe shi da gudu suna fad'in,
"Daddy !"
"Na'am yaran Daddy,wa zai je play ground?"
"Niiii, ni daddyna zan je"
In ji Hassana da ta maqale masa wuya tun qarfin ta, Hussaina ce ta janye hannun Hassana a wuyan shi ta ce,
"Dalla sake masa wuya malama kuma Daddy na ne ba naki ba, ke ba ga Mommy can ba ita ce Mommyn ki?"
"Ah ahhh daddy na ne, ko Daddy? Ai dai kai nawa ne ko?"
Yaron da Juwairiyyah ta haifa takwara ga Abbah Balarabe ne ya isa gaban su ya ce,
"Dattyna ne"
Dariya suka sanya a wajen gaba dayan su,har saudat mai latsa waya,Salma ce ta miqe ɗauke da yarinyar ta a hannu ta dungure kan Hassana da ke kukan banza ta ce,
"Na ji kar a so nin, nima ga Faihah nan Allah ya bani in ta girma za ta ce ni Maman ta ce sai me"
Saudat ce ta sauke wayar ta qasa ta ce wa Salma,
"Why are you like zis Maamaa? Are you jealous?"
Dariya suka sake sanyawa, Abrar ta miqe da sauri ta sumbaci kuncin Suwaibah tare da furta mata,
"I love you Mommy sai mun dawo"
"I love you too baby a dawo lafiya"
"Mommy zan siyo maki kayan daɗi "
"Ina nan ina jira my love, kar ku manta a yi addu'a kafin a fita daga gida,ki kuma d'akko hijab ɗin ki ko d'ankwali a rufe kai"
"Toh Mommy bye"
A haka Ibraheem ya kwashe yaran dika suka bar gidan, dan shi ba mai yawan surutu bane, da ya zauna ya na hira da mutane ya gwammace ya yi ta hira da yara,shi yasa Farouq da Jabeer suka fi shaquwa dan kuwa idan suka haɗu suka fara hira kamar ba za su daina ba.
Bayan fitar su ne Juwairiyyah ta miqe ta ce,
"Sisters a shirya tunda yaran sun fita kuma bayin Allah'n can na hira a parlour ku zo mu tafi shopping akwai wasu sabbin abubuwa da nake so mu siyo"
Cike da murna da ihu Saudat ta ajiye wayar ta ta na fad'in,
"Yeeeehhh shopping"
Salma ce ta kalle ta ta ce,
"Kaiii Addah Saudat ke dai ba kya girma you are very childish"
"Yess I am, saboda har yanzu ni kaɗai ce babyn miji na dole na yi abinda na ga dama,wata kuwa an fi son yara akan ta woooo"
Dariya suka sanya Salma ta ɗauki pillow ta wurga wa Saudat ta na cewa,
"Addah Suwaibah kin gan ta ko?"
Murmushi kawai Suwaibah ta yi hankali ya game jikin ta a yanzu bata cika hayaniya ba sam.
Jabeer ne ya yi sallama shi da Farouq da sauri Saudat ta miqe ta na wani yanga, Jabeer na shiga ya sauke idanun shi akan Juwairiyyah da ta riga shi kafe shi da nata idanun tin shigar shi parlourn,
"Ni ma ina baby na take? "
Cike da jin daɗi Juwairiyyah ta isa gare shi ya rungume ta sannan ta ce masa,
"Gani nan yayana, ya na ga kun ɗauko car keys sai ina?"
"Wai da fita muke dan so mu yi da ku tinda wancan baban yaran ya deb'i yaran shi sun fita suma"
Kallon juna matan suka yi dan kuwa sun so su tafi shopping ɗin su su kaɗai su sai abinda suke so, dariya suka sanya a tare Jabeer ya bi su da kallo ya ce,
"Lafiya?"
Da sauri Juwairiyyah da Salma suka ce,
"Babu komai,"
Sun yi haka ne dan hana Saudat faɗan abinda suke shirin yi, yanzu ita ce ta ɗauke halin Suwaibah na surutu, Farouq ne ya ce,
"To Babban Yaya a saki madam ta d'akko hijabi mu wuce ko?"
Dariya suka yi suka tafa, sannan Juwairiyyah ta wuce d'aki ta yi shigar ta ta Ninja in ji cewar Saudat, dan kuwa hijabi dogo take sanyawa da niqabi ba ruwan su da wai sun yi kuɗi yanzu bari a saka matsattsen kaya sannan a yafa siririn gyale, ko zata saka mayafin to fa kayan ta na da wadataccen ɗinki ba a matse yake ba.
Suna gama shiri Juwairiyyah ta kira mai aikin ta Huda ta ce ta dafa mata doya irin yanda take dafawa kafin su dawo ta na da miyar taushen ta a fridge dumamawa kawai za ta yi ta yi masu sakwara da sun dawo.
Motar Jabeer Suwaibah ta shiga suka nufi ShopRite, wanda da kyar Suwaibah ta saki jikin ta saboda tunawa da baya da ta yi yanda suka dinga kashe kud'in haram a ire-iren wuraren nan.
Bayan sun kammala siyayyar su ne suka tafi shan ice-cream,anan suka kirawo Ibraheem ya zo da yaran, su na gama sha kowa ya yi wa dan uwan sa sallama ya kwashi iyalin shi suka koma gida.
Haka rayuwar su Suwaibah, Saudat, Salma, da Juwairiyyah ta ci gaba da tafiya cikin farin ciki da tarin nasarori tare da albarkar rayuwa, Juwairiyyah da Jabeer basu taɓa nuna wa Suwaibah Abrar 'yar su bace ko su nuna suna son su karɓe ta, lokuta da dama ma Suwaibah ke haɗa Jabeer da ita idan ya je gaida su Innarmu aka yi sa'a ana masu hutu sai ya tafi da ita da an gama hutu ya dawo da ita gida,ita kan ta yarinyar ta na jin daɗin samun iyaye har guda huɗu dan kuwa har gori take yi wa wasu yara,ta san Juwairiyyah ce ta haife ta amma kuma Suwaibah ita ce Mommyn ta, rayuwa suke yi cike da fahimtar juna da soyayyar 'yan uwantaka, gaba ɗayan su sun kama sana'a duk da Jabeer ya ce tun da haihuwa ta yi jinkiri ma Juwairiyyah zai maida ita ta ci gaba da karatun ta, da jin haka Farouq da Ibraheem suka ce suma za su maida matan su karatu, karatu ba ya hana sana'a da kula da iyali, Alhaji Salihu kuwa ya ce kasuwanci kawai Suwaibah za ta dinga yi dan kuwa da kan ta ta ce bata son yawan shiga mutane saboda gudun kar watarana garin surutun ta ta bada labari rayuwar ta ta baya.
Tarbiyya da sanin ya kamata sun wadatu a gidan Talle sakamakon sauke girman kai da suka yi suka koma islamiyya baki ɗayan su, dan kuwa yanzu Talle ya zama babban mutum har ya na yi wa wasu wa'azi musamman ta hanyar basu misali da rayuwar shi.
Saudat da mijin ta, sun fawwala ma Allah dukkan lamuran su game da rashin haihuwa suna ta baza soyayyar su kamar sabbin aure.
Alhamdulillahi anan na kawo ƙarshen labarin mu mai suna 'YAN ABUJA,kuskuren da na rubuta a cikin shi Allah ya gafarta min ya shafe shi a rubutu na da zuqatan duk wanda suka karanta,Allah ya sa wannan rubutu ya zame min sadaqatul jariya ko bayan babu raina, Allah ya yi wa dikkan masoya na masoya littafai na gafara da rahama da albarka.
Thank you so much my beautiful mutanen kwarai masu albarka.
Allah ya albarkaci rayuwar mu baki daya
*DAGA TASKAR HAERMEEBRAEH*❤️
1- WATA UWAR
2- 'YAN ABUJA
3- 'YAR RAWA
4- KALAN DANGI
5- DA SANIN SU
6- KAI NE JARUMI
7- MIJIN YA TA KO MIJI NA
8- KUN MAKARO
9- MAHWISH
10- MAHREEN
11- BIYAYYAH
12 - A GARIN MU
13- DAGA TUSHE
14- MUGUN MIJI
15- MUGUN HALI
16- KYAKKYAWAR FAHIMTA
17- MAZAUNA GIDA
18- ALBASA BATAI HALIN RUWA BA
19- TAUBASHI
20 - ALMAJIRI NA
21- AURI SAKI
22- SANADIN FYAD'E
23- RIKICIN KISHI
24- AND NOW............
SHARHIN ASIYA HABIBU
Duk littafan nan na karantasu,kuma babu na Bari a cikin su wlh,saboda ko wanne Yana dauke d darrusa da ilimin daya shafi rayuwar duniya data lahira da kuma zamantakewa
Yan Abuja ya nuna mana illar kwadayi daga bangaren su suwaiba,ya nuna mana illar sakawa Yara dogon buri a rayuwarsu daga bangaren goggo
Ya nuna mana bangarori na zamantakewar aure tun daga gidan mama bilki har izuwa gidansu juwairere mun ilmantu da abubuwan gyaran jiki fannin iya tattali da kuma mace tazama me hikima
Taubashi y nuna mana illar barin sakewa sosai tsakanin cousin saboda komai na iya faruwa a tsakani (na dauki wannan ilimin kwarai d gaske)
Biyayya ya nuna mana muhimmancin yiwa iyaye biyayya akan abunda suka bamu umarni akai,domin duk dadewa zamuci ribar hakan
Kaine JARUMI ya nuna mana illar hassada sannan kuma y nusar damu muhimmancin zumunci
Mugun miji ya nuna mana halin wasu mazan mugaye irinsu abashe🙄🙄mazan da basa kishin matan su kuma basu dauki Mata wasu abun darajawa BA a rayuwarsu,daga karshe kuma suzo suna nadamar hakan
MAHREEN bantaba karanta littafin da komai na cikinsa y kasa barin zuciyata BA kamarsa wlh,na Jima kuma ina jinjina abubuwan d suka faru a cikin SA,
Hakuri
Juriya
Jajircewa
Addua
Kawaici
Zamantakewa
Komai de ya hada
Hakuri da duk Abinda Allah y jarrabeka dashi,d kuma hakuri d duk Abinda y sameka
Yarda d qaddara da karbar ta adik yanda tazo maka
Addua mahreen bata taba karaya BA wajan kaiwa Allah kukanta akan duk halin da ta tsinci kanta ta kasance me neman taimakon Allah akan duk halin data tsinci kanta
Takasance jajirtacciya kuma me tsayuwa akan raayinta me kuma bayyana gskyr ta ko a gaban waye bata taba kasa fadar gskyr Abinda yake ranta ba❤️.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 25