Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
qamshi ba,kina burgeni fa ba kaɗan ba,ko ta wacce gab'a aka latsa ki kina nan kyam, a shekarun mu kina da kaifin hankalin da wani babban ma bai da shi, duba kiga yanda ki ka yi mana dabara d'azu, Innar mu da ta koma d'aki da ta ga abincin da ki ka kai mana ban san me ya razana ta ba, dan na ji harda ashar ta baza mana a dakin dazun" Nafee ta qarasa maganar ta cikin dariya, Juwairiyyah ma dariya ta yi ta ce, " kai sisto irin wannan fasa kai haka, in kk fashe man kan nawa yayan ki ya dawo kin masa bayani ai" Sallamar shi suka ji da sauri Nafeesa ta fito zata bar wajen, tsayawa ta yi ta gaida shi sannan ta wuce, tana jin Nafee ta fita ta taso cikin yauqi da tafiya mai daukan hankalin masoyi,tare da wani lumshe ido kamar mai jin bacci ta isa wajen shi, ledar hannun shi ta Karb'a, sannan ta jawo hannun shi zuwa d'akin su, suna shiga kamar jira yake yi ya d'aga ta sama ya manna ta da jikin bango,dariya take mai sanyin sauti, ta zagaye wuyan shi da hannayen ta , dora fuskar ta ta yi a kan tashi, tare da hade bakin su waje ɗaya, sai da tayi masa kiss mai tsayawa a rai, sannan ta kai bakin ta wajen kunnen shi tana mai sannu da zuwa, " Jarimin maza ina maka barka da dawowa, ina fatan yau kasuwa da mutanen cikin ta basu wahal min da kai ba ko? Dan in haka ta faru akwai hukunci mai tsanani akan su daga wajena" Hura masa iskar bakin ta ta yi a kunnen tare da yin kiss a ciki ba shiri ya nemi wajen zama da ita a hannun shi suka zauna ya na sauke ajiyar zuciya,cikin kasalalliyar murya Jabeer ya furta, " Agaskiya samun mace kamar ki Juwairiyyana akwai wahalake ɗaya ce tamkar ba iyaka, samun kamar ki a cikin mata million zai wahala, in zance zan tsaya fad'an wacece ke bakina zai rasa kalaman magana,so kawai ke kadai ce ba ta biyun ki , kuma ke ɗaya Yah Jabeer din ki ya ke so har abada ba na jin zan so wata kamar yanda nake son ki" Wani irin daɗi ne ya lullube Juwairiyyah, kamar yanda kullum take son faranta mashi rai shima qoqarin shi kenan ya ga ya faranta mata rai, basu da arziqi, ba su da abubuwan more rayuwa, amma suna da junan su, tashi zata yi daga cinyar shi amma sai da ta goga mazaunan ta a jikin shi sannan ta miqe, gwalo ta masa ta tafi da sauri zata yi d'aki, binta ya yi a baya yana fad'in, " Ai baki isa ba ki tsokanen ki gudu yarinya, tsayawa zaki ki qarasa ladan ki kawai" Dariya take tana bashi hakuri,dan ta san tabbas ya na jin yunwa, " Dan Allah Babe ka bari kaci abinci ka yi wanka, sai namaka tausa kamar kullum, in yaso in ka samu qarfin jiki yau sai abinda ka ce shi za a yi" Tana kaiwa nan ta rufe fuska tana dariya ta zagaye shi ta fita da sauri, zuwa ta yi ta haɗa masa ruwan wanka,kafin ta dawo shi kuma ya shirya wanka, shiga suka yi bandakin a tare bayan ta je ta rufe qofar bangaren su, wanka ta masa da kyau ta sa masa toothpast a brush din shi ta bashi dan ya wanke bakin shi. Mata da yawa suna cewa wai mijin su yana warin baki baya son yin brush da sauran su, shawara gare ki sister mai wannan matsala shine, ba a ce ma na miji je kai brush ko wani abu makamancin haka, dik da akwai mijin da in shaquwar ku ta kai qololuwa kina iya sanar da shi kuma ba zai damu ba dan yasan duk amfanin ku ne ke da shi, so in ba irin mijin nan gare ki ba dabara zaki yi, ki haɗa maku ruwan wanka tare kafin wankan ki tabbatar kin gama gigita shi yanda ba zai maki musu a ba, daga nan sai ku yi wankan tare, in ba ku yi tare ba ma saboda maybe yanayin gidan naku, sai ki saka masa ruwan ki kai masa da kayan wanka, sannan ki saka mai toothpast a brush ki aje mai a kusa, ba yanda za ai ya qi musamman yaga kin saka maku tare, kinga ba zai zargi kina jin wari bane daga wajen shi, har ya yi feeling bad kuzo kuna samun sabani. A d'aki ma Juwairiyyah Bata bar jabeer ba sai da ta gyara mai jiki tare da feshe shi da tirare, palour ta dawo da shi yana biye da ita kamar raqumi da akala, abinci ta zaunar da shi ta bashi, yana ta santi " kaiiiii amma ba qaramin birge ni ki kai ba, kin san rabona da faten wake har na manta kuwa?" "Alhamdulillah na ji dad'i da yabawar ka Hubby" kusa da ita ya matsa sannan ya ce, "Ai dole in yaba saboda ke din ta daban ce, komai naki daban ne,Allah ya barmu tare har a aljannah" Murmushi suka yi dikan su suka ci gaba da cin abincin su, kiran sallar magrib ne ya katse su suka tsaya suka saurara sannan suka bi kiran sallahr suma, bayan an idar ne suka yi addu'ar da ake yi ba yan idar da kiran sallah,wato " Allahumma rabba hadhihidda'awatittammah, wassalatil qa'ima, a ti muhammadal wasilata wal fadeela waddarajatirrafee'a wab'athhu maqamam mahmudan lladhi wa adtah." Sannan suka dora da salatin annabi ingantacce, addu'a suka d'aga hannayen su sama suka yi a tare ita da shi, suna idarwa suka tashi suka yi alwala, shi ya tafi masjid ita ta yi sallar ta a gida, bayan ta idar ne tayi azkar din bayan kowacce sallah ne, sai ta samu ta yi kuma azkar din yamma, tana idar wa ta miqe ta je d'akko dan ragowar abincin nasu ta juyo masu ta kawo ta had'o da ruwa da komai da ya dace ta ajiye a gefe, d'aki ta shiga ta saka rigar baccin ta mai matuqar kyau da daukan hankali, sai ta ɗora zani akai da hijab tana jiran sallar isha'i bayan tayi sallar ne da minti 15 Jabeer ya shigo,abinda ya tsayar da shi kuwa sai da ya biya wajen Innar mu ya gaida su, baban shi na ta sa mai albarka, ita ko ta cinkishe fuska tana hura hanci, daya tambaye ta ne ke damun ta sai ta yi qaryar kanta ke yi mata ciwo, dan yau wuni tai da yunwa bata ci abinci ba, can kuma sai ta saki fuska ta ce, " kasan da yake bana son faten wake, kuma bana son bawa yar albarkar nan aiki shiyasa, amma da shinkafa zan bata ko gwangwani dayar nan ne ta dafa min, tinda Nafee ita har yau bata iya tsantseni irin na Juwairah ba" " Ba komai Inmar mu kawo na kai mata za ta yi maki ai, ba zai yu ku kwan da yunwa ba" Dan haka da sallama ya isa sashen su riqe da ledar shinkafar a hannun sa,daidai Juwairah ta fito daga d'akin ta ta cire zanin ta da hijab din ta, tana qarasa shafa mai a cinyar ta, ko da ya higo tini ta sauya salon shafawar, sake baki ya yi kamar dolo yana kallon ta, qarasa shigowa ya yi ya aje ledar shinkafar a qasa still idon shi na kan Juwairiyyah, juyawa ta yi ta koma d'aki tana tafe tana juya bayan ta tana waigowa tana masa wani mayen kallo da murmushi, ni dai tin da ya shiga suka ja qofar ban qara ganin me suke aikatawa ba sai dai kunnuwa na sun jiyo man Jabeer na sambatu da bana gane yaren da yake yi, sayyarar qafa ta na ja na yi waje, ji nake kamar na kai wa Innarmu gulmar me ke faruwa. Qarfe hudu na asuba suka fito suka yi wanka tare da alwala mai kyau suka koma dakin su, bayan sun shirya ne suka fara gabatar da nawafeel, kowa ya fara addu'ar shi, Jabeer ne ke hango baqi, a gefen shi dan ba wuta sai ta wayar shi suka kunna, miqa hannu ya yi dan yaga meye a wajen, dagawar nan da zai yi sai ya ga shinkafar da Innarmu ta bashi ce jiya a dafa mata, cikin damuwa da tashin hankali ya ce, " Ya salam ! Tab lallai da safe na shiga magana wajen innarmu, aiko ni ta yi fa jiya na kawo ki dafa mata wai yunwa take ji, tin safe bata ci komai ba, bata cin faten wake, shine gaba ɗaya na manta" "Haba Yah Jabeer bai kamata ka manta da wannan mahimmin abu ba kuwa, domin yunwa ba ta da mahadi ai bayan haka Innarmu ce fa ta baka umarnin a yi abu be kamata ka shagala ba gaskiya ban ji daɗin abinda ka yi ba," A qasan ranta kuwa jinjina wa Innar mu take wajen iya hada makirci, matar da taci ta tande kwano, har ta aiko wai a dad'a mata in akwai, tace babu shine take cewa ba ta ci, ikon Allah, lallai Allah mai jin qan bawan sa ne mai tinawa da shi a kowanne hali yake musamman idan bawan na yawan neman taimakon Allah a dikkan lamuran shi, da bata zama mai neman taimakon Allah a komai ba da bai taimaka mata jiya ba,gashi bata san me aka qulla mata ba Allahn ta ya kare ta, kiran sallar asuba ne ya katse su daga mayar da magana akan abinda ya faru jiyan Jabeer ya tashi ya fita masjid ana yin sallah ya dawo, ita kuma tayi tata a gida tayi azkar da karatun asuba da take yi kullum ba fashi komai aikin da ke gaban ta sai tayi ko rabin shafi ne kan ta tashi, tana rufe qur'ani ya shigo, lokacin gari ya dan waye, daki suka shige suka ɗan miqe dan su maida bacci,tund Nafeesa ke abin karyawa a gidan, in ba arziqin abin karyawan ma da dama koko kawai zasu dama su sha a ci gaba da rayuwa, har bacci mai nauyi ya fara ɗaukan su suka jiyo sallama daga bakin kofa......... [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼    'YAN ABUJA.  💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 8: Nafeesa ce ta tsaya tun daga bakin kofar shiga sashen su Juwairiyyah ta kwankwasa tare da yin sallama,bayan an bata izinin shiga ne ta qarasa shiga ciki,gaishe da Jabeer da Juwairiyyah ta yi sannan ta kalli Jabeer ta ce, " Yah Jabeer Innarmu tace wai ka bada shinkafar na kai mata tin da ta yi wuyar dahuwa" "Inna lillahi,  kin gammu yanzu haka zancen shinkafar muke yi ni gaba daya mantawa na yi shaf dana shigo, dan Allah ki bata hakuri kice yanzu za a dafa mata a kawo" Dariya Nafee ta yi sannan ta ce, "Tace idan ka faɗi haka na ce ka bata ta fasa wataran an dafa mata" "Oh my God yau ya zan yi na iya zuwa gaida Innar mu? Dan Allah Nafee ya kika ga fuskar ta ta yi fushi sosai ko?" Cikin jimamta lamarin Nafee ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Hmmmm ba kadan ba kuwa Yah Jabeer, amma tace kar na fada maka ta yi fushi" Juwairah a ranta kuwa sai tace 'Ina fa zata so ya sani tinda tana son nakasani ta qarqashin qasa' Ba yanda ya iya haka Jabeer ya ya miqa mata shinkafar yace ta bata hakuri sosai kan ya shigo, fita ta yi da ita tana masa dariyar zaka amsa ne in ka shigo kai da Innarmu ka san halin ta ba ta da sauqi. Sai da su Juwairiyyah suka taɓa baccin su sannan suka tashi suka yi wanka tare da brush, d'aki suka shiga su ka shirya cikin shiga mai kyau da burge junan su ta qananan kaya, hijab Juwairiyyah ta ɗora akan kayan ta matsattsu da ta yi ma mijin ta kwalliya da su kafin ya fita kasuwa, a tare suka shiga bangaren na su Innar mu lokacin ta gama raba abin karyawa tace akai masu sai ga su sun shiga, duqawa Juwairah ta yi har qasa suka gaisa, " Ya jikin naki Juwairah,ai Nafeesa ta ce min ba ki ji daɗi bane shi yasa ya ajiye shinkafar bai baki kin dafa min ba duk da tsananin yunwar da nake ji jiyan" Zare ido Juwairiyyah ta yi cikin duqar da kai da sauri ta furta, "Da sauqi Innarmu na ji dama sosai alhamdulillah" " To Allah ya qara lfy, yasa amarya za ai min ko ango, danni na gaji da lafiya sa banga qaho ba aure wata na biyar kenan shiru ba magana?" Innarmu ta fada a matsayin wasa take yi, amma duk wanda ya kula ya san magana take faɗa mata, murmushi Juwairiyyah ta yi sosai sannan tace, " Innar mu karki damu komai lokaci ne amare za a samo maki masu yawa da masu kawo cefane har sai kince sun isa haka" Tana fadar haka ta miqe ta yi wajen Baba Balarabe ta gaida shi, sake baki Innar mu ta yi ta na bin Juwairiyyah da kallon mamaki, shiko gogan be gane magana suka sakar wa juna ba, daɗi ma yake ji a ganin shi Innar shi da matar shi sun fahimci juna sosai akwai shaquwa ta musamman a tsakanin su, tun da har suke irin wannan maganar ga junan su, matsawa ya yi kusa da Innarmu ya ce, "Akwai abinda zan taya ki ne Innata?" Murmushin qarfin hali ta yi sannan ta furta, "Eh toh ba a rasa ba ai, A qoqarin ta na hana shi ya koma wajen da matar shi take, Can bangaren kuma Juwairiyyah da Baba Balarabe ne ke gaisawa cikin sakewa da mutuntawa, " Babana ina kwana?" "Lafiya qalaou d'iyar albarka, kina lafiya dai ko?" " lafiya qalaou nake babana" "To madallah, Juwairah ina son ki yi ta hakuri da wannan Innar taku, wani hali ta d'akko  na daban wanda har ni kaina ta canja min kwata2 ba kamar yanda na santa ba, dan haka kema sai kinyi hakuri, abotakar ta da Goggon ku ba abu ne mai kyau ba, na yi nayi na raba su amma abun yaqi yuwuwa, da dukkan alamu daga can ta samo wadannan sabbin halayen dan kawai kar a zauna lafiya" " Babu komai Baba , ai ita ɗin uwa ce a wajena ko da ace ba matar ka bace ba mahaifiyar Yah Jabeer ai uwa ta ce, tinda ita ta haife shi kuma shi din mijina ne, in ban so mahaifiyar shi a tawa ba ni kaina ba zan samu kwanciyar hankalin gidan aure ba, rikicin yawa zai yi min, dama kuma ko da asalin mahaifiyar mutum ma ai ana samun sab'ani dan haka ita ma uwa ta ce,watarana ba zata yi ba" " Allah ya miki albarka , halayyar mahaifin ki da mahaifiyar ki sak ki ka dakko ba wanda ki ka baro" Murmushi suka yi dikan su ita da Baba Balaraben, bayan Jabeer da Juwairiyyah sun gama gaishe2n su sai suka koma sashen su suka karya, suna gamawa ya sauya kayan da zai fita kasuwa da su sannan ya ɗauki makullin shagon shi da duk abinda yake da buqata ya fito hannun sa riqe da hular shi ya na gyara karin ta, ya na gamawa ya kafa ta akan shi ya kalli Juwairiyyah ya ce mata, "To ni fa na fito zan wuce sai na dawo, ki kular min da kanki, kar ki wahal da kanki da yawa Allah ya yi miki albarka " Tashi tsaye ta yi ta isa gaban shi cikin yanga da kashe ido da murya sannan  ta zagaye hannayen ta a wuyan shi ,shi kuma ya zagaye qugun ta, sannan  ta ce, "Allah ya kiyaye hanya, zan yi kewar ka da yawa a cikin waɗannan awannin da za mu yi ba ma tare" Cike da shagwab'a da tura bakin ta kaɗan gaba take maganar,Jabeer na ganin haka kuwa ya qarasa da fuskar shi jikin ta ta suka hau sumbatar junan su, da kyar Juwairiyyah ta kwace kanta a hannun Jabeer, sai wani shinshina ta yake ya na jin kamar kar ya fita,cike da shagwab'a ta furta, " Yah zaka makara fa, ka tafi cikin kariya da amincin Allah, Allah ya bada kasuwa mai yawa mai albarka, ya kare ka daga haramun komai qanqantar ta, Allah ya haɗa ka da halal komai qanqantar ta, ka kular min da kan ka, ka tsaida sallah akan lokacin ta, in kaji yunwa ka taimake ni kaci abinci, kaga yanzu ba da bane, ba abubuwan da zan iya ci gaba da dafa maka kana tafiya da shi, karka barmin kan ka da yunwa kaji Yayana?" " Karki damu,duk abinda ki ka ce an ma gama shi kawai ur higness" Yanda ya duqar da kai a gaban ta da girmamawa ne ya bata dariya, ai kuwa sai suka fashe da dariya a tare, ta sanya hannun ta cikin nashi ta raka shi har waje,bata dawo ba sai da ta ga tafiyar shi sannan ta dawo d'aki ta hau gyara wajen da suka ci abinci. **************************** A can gidan Baba Baballiya kuwa Goggo ce ta fito daga d'akin ta ta na qarasa d'aura dankwalin kan ta, cikin masifa ta duqa ta d'aga wani food flask Mai kyau sannan ta ce, " kai jama'a wai dan tsabar baqin ciki na aje flask din nan a can amma  na zo na tarar an d'aga an kai min shi nan, ko uban wa ya ce a taba min kaya oho, shikenan mutum idan yana jin haushin talaucin da ya yi masa katutu sai ya dinga taba kayan da ba nashi ba yana canja masu waje? Oh ni sarai na ga abin da ya ishe ni yau" kamar Mama ba zata amsa ta ba amma sai taga dacewar ta bata amsar, dan haka ita ma sai ta ce, " Hmmmm Allah nawa in ji bamaguje, to ai dai har yau wata kusan biyar ban ga ɗaya daga YAN ABUJAN sun yi koda waya bane balle nace ko an yi maki wani aike na azo a gani, ana nan dai yanda ake jiya iyau, ba wani hura hancin da za ai mana kuma, flask ne fa tun wanda aka samu a gudummawar biki ba wata tsiyar ba, sannan ban taɓa sanin gyara kayan ka zai zama sauke mu raba ba da ban kawar maki da shi ba na bar awaki sun tattake" kamar dama Goggo jira take Maman  ta tanka mata, sai kuwa ta hau masifa da bala'i kala kala har ta na jin kamar ta ari baki dan tsabar masifar da ke cin ta,nan da nan ta taso wa Maman a lokaci daya ta dinga zage zage da kira mata alkaba'i kala kala, har da su gori ta dinga yi ta na fad'in ai abinci ma wataran ita ke taimakawa da shi a gidan ba dan haka ba sai dai yunwa ta kashe su, 'yan Abujan da aka sanya wa ido su ne suka bata kud'in da take ci da su sai dai baqin ciki ya kashe Mama, Mama tace daga yau in Goggo ta haifu cikin Mahaifiyar ta karta qara taimakawar ta ga in bazata rayu ba ita da danta. Ammar ne ya kama hannun maman shi yana kuka dan kuwa su na tsorata shi da hayaniyar da suke yi baya son hayaniya shi sam, ɗaukar shi Mama ta yi suka yi daki abun su suka bar Goggo na kumfar baki ita kaɗai. ************************* Oga Zaks ne da mazajen su Suwaiba tafe sun fito daga wani d'aki mai tsananin duhu sosai, Alhj Kalla dauke da Saudat a hannun shi sai kallon fuskar ta yake yi abokin shi kuma aminin shi Alh Salihu na dauke da Suwaiba, suna fitowa daga dakin, Oga Zaks ne ya furta, " To ku maida masu sabbin kayan da kuka zo da su kuyi gida,nan da awa uku zasu farka, kuma ku kwanta gefen su da sun farka su yi tozali da ku, domin wannan magungunan da suka yi ta sha zasu sa masu kasala da ciwon jiki, na kammala duk wani aiki da za ai akan su na wannan watan, za ku yi kuɗi na ban mamaki, domin kuwa kuɗi kuma sai kun ce sun ishe ku, dan mahaifar su na da kyau sosai, Dodo yayi farincikin samun ta, ba a taba kawo masa irin wannan ba, nima kuma shaida ne, hahhahaahhha" Cikin farin ciki su Alhj Ƙalla suka haɗa baki wajen fad'in, "Godiya muke Oga Zaks" Sannan suka ajiye su suka canja masu kaya suka yi mota da su sai cikin garin Abuja, suna isa cikin gari kowa ya ɗauki hanyar gidan shi, fad'ar kyau da tsaruwar gidajen nasu ma b'ata baki ne kawai, gidaje ne irin ginin qasashen turai wanda ko a turan ma sai masu kuɗi ke da irin wannan gidan, ko ta ina ka gilma masu hidima ka ke gani sun gyara sun tsaftace gidan sai sheqi da kyalli tare da ɗaukan ido yake yi ga qamshi kamar a qasar Arab. Bayan gaisawa da masu aikin gidan ne kowannen su ya shige da matar shi d'aki ya ajiye ta a gado sannan suka kwanta a gefen su suka hau baccin asara ba sallah  ba salati,basu suka farka ba sai wajen la'asar, miqa Suwaiba ta yi ta na hamma, tana kallon d'akin nata, yanda ta zaci za ta zo Abuja ta zauna a gida mai kyau sai ta ga gidan ya wuce zaton ta da tunanin ta,ko ta ina d'akin ya gama rud'a ta da kyau da qayatuwar shi, shiru ta yi ta na son ta tuna abubuwan da suka faru tun da aka gama dinner bikin su ta kasa, lokaci take kallo ta na tunani anya time na tafiya daidai kuwa? Qoqarin kawar da wannan tunanin ta yi ta miqe ta hau takawa kamar mai koyon tafiya ta na so ta ga ya wannan gidan na ta mai dimbin kyau yake, taku ɗaya biyu ta yi a na uku ne ta ji wani irin ciwo a cikin ta  mai tsanani da sauri ta komawa ta zauna, tana fad'in , "Wasssshhhhhh Allah na ciki na, me ya samen a ciki kuma nake ji na haka? Gashi ina jin duk jikina ya na min ciwo" Kusan a tare suka farka su ke yin wannan maganar ita da 'yar uwar ta Saudat, Saudat da tafi Suwaiba raki ma harda kukan ta, a rude mazajen nasu suka tashi kamar ba abinda ya faru suka hau tambayar su da me ya faruwa, Suwaiba ce ta langwab'e jikin mijin ta ta na wani karya wuya sannan ta ce masa, "Ciki na na min ciwo" Tashi ya yi ya duqa gaban ta ya d'aga rigar ta ya leqa cikin tare da shafawa a hankali, sannan ya ce, " Ayya kiyi hakuri zai warke ne a hankali hatsari muka samu a hanyar mu ta dawowa gida daga wajen dinner  sai muka kai ku asibiti ke da 'yar uwar ki, kwalbar glass ce ta yayyanke ku shine muka wuce da ku asibiti aka yi maku dinki a wajen, so a hankali zamu jira ya warke mu ci gaba da shan amarcin mu ko?" Ya qarasa maganar shi tare da jawo ta jikin shi yana shafa ta, kwantar da kanta ta yi a jikin shi, ta na tunani ya akai shi babu ciwo ko ɗaya a jikin shi? Da sauri ta kawar da wannan tunanin sakamakon tashi da ya yi ya fita dan ya hado mata abinci, tana daga kwance a gadon ya dawo ɗauke da wani ɗan qaramin teburin cin abinci Saman shi an aje plate ɗin abinci da cup ɗin juice sai mug ɗin tea,gefe kuma ga wani plate nan an yanka fruits a Kai sai ya ajiye mata a saman cinyar ta,sannan  ya zauna yana bata a baki, wani daɗi ne ya lullub'e Suwaiba yau mafarkin ta ya zama gaske ta samu fiye da abinda ma take kwadayin samu a auren d'an Abuja. Tana gama wa ta dauki wayar ta da ke kashe ta kunna ta kira Goggo,wayar na shiga Goggo ta ɗauka kamar wadda ke gadin wayar ta na jira a kira, cikin kuka Goggo ta ce, "Haba 'yar nan yau wata biyar kenan da kwana uku, kun tafi shiru ba waya ba aike meke faruwa ne Suwaiba?" Cike da Mamaki Suwaiba ta furta, "wata biyar da kwana uku kuma Goggo?????............ [18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN

Chapter 5 of 25