Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dan ta taɓa shi ta tabbatar shi ɗin ne kuwa ko dai wani ne ke tsokanar ta dan kawai a hana ta cin daular da Alhajin ya tara? shi kuwa ya na jin hannun ta a fuskar shi sai kawai ya dora hannun shi saman nata, saurin zame nata hannun ta yi tare da rushewa da kuka sosai, cikin kukan tace,. "Me yasa ka ke sanar dani wannan mugun labari yanzu? Me yasa tun kafin aure baka sanar da ni ba na nemi wani mai kud'in na halal na aura na ci dukiyar shi da gaske ko da kuwa kullum safiya duka na yake yi? Ka sanar da ni ne yanzu saboda sun ce ka kai ni yanzu a yanken qafa ta ne ko hannu, Ko kuma kaina suke so a yanke yanzu kai kuma ba zaka iya kai ni ba? Me yasa ka zaɓi shan jinin mutane ka yi kuɗi? Ina da son kuɗi da son abun duniya sosai na sani, amma ba zan iya kashe mutum domin samun su ba, son kuɗi da abin duniya tane ya sa Saudat tana sanar dani na rufe ido ƙwaƙwalwa ta ta toshe zuciya ta ta rufe na qi yarda, mene ne hukuncin da ka yanke yanzu akaina har ka ke sanar dani wannan mummunan maganar?" Shi kan shi Alhaji Salihu hawaye ne ke zuba daga idanun shi,tabbas so ba karya bane ba, yanzu ya gane ya na son  suwaiba so mai tsanani, cikin muryar lallashi ya ce, "Babe Dan Allah kwantar da hankalin ki" "In kwantar da hankali na, ta yaya kenan? Bayan wannan mummunan labarin da ka sanar da ni ka ke tsammanin kwanciyar hankali daga gare ni? Ta ya ka ke tsammanin in sake yarda da kai da duk wani abu da zai fito daga bakin ka?" Ta qarasa maganar ta cikin matsanancin kuka mai cin rai, a idon ta kuwa ba wanda take hangowa sai Goggo Sarai, ta yi dana sanin kasancewar ta uwa a gare su a yau, da ace ta basu tarbiyyar mai kyau irin wadda ta dace da basu zama masu son abun duniya ba, da idon su bai rufe da son  kuɗi ba har su nemo mazaje masu yin kuɗi da sassan jikin mutane su aura har a dinga bata alamu sannan afito fili a sanar da ita abinda suke aikatawa duk da haka ta yarda ta sake dawowa saboda tsabar son abun duniya. Yanzu gata a cikin babbar matsalar da bata san ta yanda za ta yi ta kub'utar da kan ta ba. "Wayyoo Allah na rayuwa ta, yanzu ya zanyi na ci gaba da rayuwa kun riga da kun nakasa min rayuwa? ka fad'a min yanzu a wanne matsaya ake dan na tabbata wani abun aka sake buqata a jiki na za a yanke shi yasa ka damu ka ke sanar da ni gaskiya, ka faɗa min menene kuke buqata kuma a waje na yanzu !" Da sauri ya share hawayen da ke kwaranya a idanun shi sannan yace, " Ogan mu ne da muka yi yarjejeniya da shi akan in ba a kashe ki ba zan kai masa ke har na tsawon sati biyu ,shine yake da buqatar ki ko ya dauki fansa akaina, farkon zuwan ku ma sai da muka kai masa ku kuka zauna a wajen shi na tsawon sati biyu ya  huta da ku, a cewar shi Kuna da wani sirri na musamman wanda ba ya da misali, wannan shine dalilin da ya sa ya ce na kai masa ke a madadin alfarmar rashin kashe ki da ba ai ba " Wani ihun kuka Suwaiba ta sake sanya wa sannan ta miqe  ta hau kan Alhj salihu ta na duka tun qarfin ta, qarshe da taga ko gezau bai ba sai ta kife a wajen tana ta rusar kuka ta na fad'in, "Kaico na ni Suwaiba, kaico na, na shiga uku,yau ina zan saka kaina, ga abinda son abin duniya nan ya jawo min, a yau duniyar ta juya min baya, bata riqe ni a matsayin masoyiya ba kamar yanda na so ta, yanzu ni aka kaiwa dan shan jini har tsahon kwanaki goma sha huɗu bai biya sadaki na ba, sannan yanzu da aure na za a sake Kai masa ni na tsawon wasu kwanaki goma sha huɗun,lallai ni suwaiba yau na ga yanda rayuwa a Abuja take," Qanqame ta Alhj ya yi yana shafa bayan ta da sigar lallashi, fizgewa ta yi cikin son jin qarashen labarin nasa ta ce, "Uhumm ina jin ka? Kana nufin kai masa ni ɗin za ka yi shiya sa ka zo kana sanar da ni wannan mugun labarin ko me?" Da sauri Alhaji Salihu ya ce, "Ko ɗaya suwaiba ba inda zan kai ki, da ina so na kai ki ai ba zaki sani ba ma zan kai ki, da da muke diban jinin ku dik wata sani ku ka yi?" Zaro ido ta yi kamar su fad'o qasa dan firgita da tsoron shi, baya ta fara ja ta durqusa a guiwowin ta ta na kuka ta ce, "Dan son ka da annabin rahama kai yi min rai kar ka qarasa ni,dan kuwa yanzu ni da mamaciya bamu da maraba, banda mahaifa, banda nono, jini na duk wata ake kwasa kamar a teku, an kaiwa wani qato ni ya gama kwana da ni kamar wani miji na, yanzu kana shirin maida ni sai ta Allah kuma, ina ga sa'i na ne ya zo,Allah ka ji qai na ni suwaiba" Matsawa ya yi zai riqe ta ta ko falla da mugun gudu ta yi d'aki ta na ihu, kan ya isa ta fara qoqarin rufe qofar,ya yi saurin saka qafa ya tokare, ihu ta zunduma tana bashi hakurin ya yi mata rai ta tuba, ya maida ma baban ta ita, dan yanzu ta tsani Goggo Sarai shi yasa ko tunanin ta bata yi ba, ya taimaka kar ya tsotse mata sauran jinin nata da ya rage, tura wa ya yi da qarfi ya janyo ta jikin shi cikin ɓacin rai ya ce, " Ke! Ki nutsu dalla malama kar ki taran mutane ni, in da zan kai ki da tini  ban kai ki ba ko kuwa sauran duk sanin an je ki ka yi? ba sai yanzu dana sanar dake bane ki ka sani? Na faɗa maki ne saboda ina son na maida ki gidan ku da kaina, in yaso duk abinda zai min ya min, na sadaukar da rayuwa ta domin taki ta tsira, Suwaiba wannan shine iya adadin soyayyar da nake maki, ina son ki suwaiba zan iya sadaukar da rayuwa ta saboda taki ta tsira" Ya qarasa maganar shi a hankali wanda ya sa jikin ta yin sanyi, qanqame shi ta yi tana kuka sosai,Itama ta ce, "Ba na son na rasa ka Alhajina, nima ina son ka sosai, ban san sanda na fara son ka ba nima, a da kam tabbas kud'in ka nake so, amma yanzu kai nake so, bana son abinda zai raba mu" Jin kalaman ta ne ya sanya Alhj Salihu kuka kamar wani yaro,haka so yake,shi  SO ba ruwan shi da girman ka ko qanqantar ka in ya shige ka yana saka aikata abinda ba hurumin ka bane aikatawa, haka suka yi ta kuka ba mai lallashin wani, ba su ankara ba sai kiran sallan farko suka ji na asuba, kasancewar dama bai dawo gidan da wuri ba tun safe da ya fita. Suwaiba tashi ta yi daga jikin Alhajin nata jiki duk ba k'wari,yau ce rana ta farko a rayuwar ta da ta yi alwala dan wani abu na damun ta take son ta roqi Allah akai dan ya yaye mata damuwar ta. Shima Alhaji daya ga haka alwalar ya yo, ya kabbara salla ta na bayan shi suka yi nafila,suka hau addu'a akan Allah ya yafe masu, ya gafarta masu zunuban su, ya kubutar da su daga wannan al'amari da suka tsinci kansu a ciki, bayan sun idar da addu'ar ne suka yi sallar subh  suka tashi suka hau gado, bacci mai nauyi ne ya dauke Alhj amma ita kuwa inaaaa yaushe taga na barci ana shirin kaiwa matsafi ita, lallabawa ta yi ta buɗe wajen da take aje kud'ad'en da yake bata ta d'iba, ta dakko akwatin ta ta loda kayan ta a ciki, ta fita ta dauki makullin mota babbar ciki a motocin shi,Saida ta loda kayan ta a ciki sannan ta hau ta nufi gate mai gadi ya buɗe mata ta fice ta bar gidan a guje. Hanyar kano ta ɗauka duk da cewar bata gama gane hanyar ba ta tabbata zata iya kai kan ta gida,haka suwaiba ta dinga bin rubutun Sunayen garuruwan da ke kan hanya tana shara gudu a Saman titi har ta isa cikin garin Kano Haka ta isa gida a firgice, Alhj kuwa bai farka ba sai azahar, miqa hannu ya yi dan ya tab'o Suwaiba yaji wayam, bai kawo komai ba a ran shi dan ya zaci ta shiga toilet ne, komar da kan shi ya yi ya lumshe ido,tunani yake ya kamata ya haɗa mata kaya ta tafi gida in yaso duk yanda suka yi da Oga Zaks daga baya ya dawo da matar shi, miqewa ya yi zai shiga toilet din in ma wanka take suyi tare ya na shiga yaga wayam ba kowa a ciki, fita ya yi palour nan ma bata nan, leqa kitchen da sauran dakunan ya yi yaji shiru bata nan, a hargitse ya fita waje wajen gate man ya ce, "kai Audi ina Hajiya?" " Alhj ta fita da kaya da motar ka babbar tun da sassafe" Cike da damuwa ya hau shafa kanshi, komawa ciki ya yi zuciyar shi cunkushe da tunani kala kala,shin ya take a yanzu, ta samu nasarar isa Kano lafiya ? Tinda iya sanin sa bata gama kware a tuqi ba, gashi a yanzu tana cikin halin tsoro da firgici, kar wani abu ya je ya same ta a hanya. Ɗaya bangaren na zuciyar shi ya ji haushin yanda ta iya guduwa ta bar shi ba tare da sun yi koda sallama bane,ta san ya na son ta ba zai bari wani abun cutarwa ya sake rabar ta ba, kuma Itama  ya ga soyayyar shi a tare da ita. Wayar  shi ya dakko ya hau kiran ta dan ya ji ina take idan kanon ma ta gudu ya ji shin ta isa lafiya ko ta na hanya ne bata isa ba,wayar na ta ringing bata d'aga ba, hakura ya yi da Kiran ta ya je ya yi wanka ya yi sallahr da ya jima da dena yi sannan ya fita ya bar gidan. Qarfe uku na rana a qofar gidan su ta yi mata, hankali tashe ta kashe motar  ta buɗe ta fada gidan tana kuka, da sauri Salma da Saudat dake tsakar gidan suna murza meatpie din da Salma ke sana'ar shi a yanzu suka je za su taro ta, sai dai ganin ta shiga da uban gudu ne ya sa suma suka so kwasa da gudu amma suka yi ta maza suka tsaya, tsayawa suka yi suga me ya koro ta shiru ba wanda ya biyo ta,ta na qarasa shiga ta fada jikin Salma tana kuka tare da fad'in , "Na shiga uku Salma na halaka kai na da kai na, Saudat kinyi gaskiya Alhj da kanshi jiya ya tabbatar min shi ɗan qungiyar asiri ne masu shan jinin mutane da tsafi da sassan Jikin su, duba ku gani yanda aka maida ni mata maza" D'aga masu rigar ta ta yi suka ga yanda qirjin ta ya koma babu komai fayau kamar filin ball,a daidai nan Goggo Sarai ta fito cike da tashin hankali sakamakon jin abinda Suwaiban ke fada............ [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 ' YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 26: Kamar yanda mata da dama ke kokarin kyautata wa mazajen su ta fannin kula da gida, kula da kawunan su ta bangaren tsaftar Jikin su, mahallin su da ta Yaran su, ya na da kyau su ma maza a same su da kula da tsaftace Jikin su da duk abinda ya kamata su yi dan faranta wa matan su rai da tabbatar da cewar matan su sun dawwama cikin son su da qaunar su tare da burge su,ba ya daga cikin adalcin zamantakewar aure ace koda yaushe mace itace za ya yi ta kokarin faranta wa mijin ta rai tare da neman mallake shi shi kuma miji ya zauna ba ya wani yunqurin burge abokiyar rayuwar shi. Wannan dalilin ne ya sanya Jabeer zuwa aski aka wanke masa qafar shi tass, duk da a baya kafin Juwairiyya ta samu ciki ita ke wanke masa qafafun da har sai sun yi karr da su kamar na jinjiri saboda ta na amfani da kayyakin da muke da su na yau da gobe wajen gyara qafa, kamar su lemon tsami,baking soda,gishiri kaɗan, toothpaste na kamfanin Colgate sai zuma, ta na haɗe su waje ɗaya ne ta juya ta shafe musu qafafun su da shi idan ya kai minti 15 sai ta wanke masu da soson wanka da ruwa mai d'umi ta tsane masu qafafun su idan sun tsane ta shafe su da man kad'anya da ta haɗa da man kwakwa da man zaitun. Hannun shi riqe da qaramar ledar da ya siyo mata shaving stick da sweets ya shiga gidan,duba wa ya yi bai ganta a parlour ba,direct d'aki ya shiga dan ya san dole ta na can idan bata zaune a parlour ko tsakar gida ko kuma wajen Innarmu,ya na shiga kuwa ya gan ta a d'akin,cike da mamaki ya kalle ta ya ce, "Yanzu baby idan ki ka yanke fa? Na ce ki jira a yi sallah na je aski na dawo zan taya ki tunda yanzu ba ki iya yi da kan ki amma kin kasa jira na, kuma kin san reza sai dai ta ji maki ciwo amma still ki ke yi da kan ki,ni ban san me yasa yanzu ki ke kin jin magana ta ba,bani nan" Kwalla ce ta taru a Idon ta ta miqa masa rezar hannun ta ya Karb'a ya ajiye a gefe sannan ya rufe qofar dole na koma parlour na zauna zaman jiran masoyan. Bayan mintinan da baza su wuce biyar ba Juwairiyyah da Jabeer suka fito sai tura baki take ita a dole fushi take yi an yi mata faɗa, ba tare da Jabeer ya kula ta ba ya wuce wajen murhu inda ta ɗora ruwan da ta ke haɗawa na tsarki shi ya ɗauka ya juye a babbar buta ya surka mata daidai yanda zai ɗauke ta ba tare da ta ji zafi ba ya miqa mata. (Abinda ake tafasawar sune kaninfari ,ganyen magarya, lalle kaɗan da ɗan gishiri sai ganyen garahuni) Jabeer gani ya yi ta karɓi butar kanta na kallon wani waje ta na tura ciki gaba da baki murmushi ya yi dan kuwa ya san ba halin ta bane, ta fara yi masa irin haka ne tun sanda suka gano ta na ɗauke da ciki, abu kaɗan za a yi mata ta yi Fushi,dan haka cikin sigar lallashi ya ce, " Haba Juwaireren Mama Juwaireren Yah Jabeer, me kuma ya faru, me kk so na yi maki? Ni ne na yi maki faɗa? To yi hakuri kin San fa ni gaba ɗaya bana jin daɗin rasa murmushin nan naki mai kwantar min da hankali,ni fa da ki hana ni murmushin ki gwanda ki hana ni ruwan randar sanyin nan idan na dawo daga kasuwa a gajiye" Murmushi ta saki ta na qunshe dariyar ta ta shige band'aki ta yi wanka ta gyara Jikin ta yanda ya kamata sannan ta fito, gani ta yi ya gama kashe wutar da ta hura ya deb'i garwashi a kasko ya sanya masu turaren wuta sannan ya fito ya kama hannun ta ta sauka daga tudun band'akin, alwala ta yi sannan suka wuce d'aki tare ba tare da ta ce masa komai ba, sai dai wannan karon fuskar ta sake take babu wani b'acin rai a tattare da Ita. Sai da Juwairiyyah ta shirya cikin kayan bacci sannan ta ɗora after dress d'in ta ta sanya hijabi ta tada sallahr ta, ta na idarwa ko azkar bata yi ba ta kalli Jabeer da ke zaune a gefen gado ya na latsa waya ta tashi da kyar ta kwanta a gefen shi ta hau kukan shagwab'a ta na fad'in, " Baby ni agwaluma nake son sha fa, ka samo min agwaluma" Cike da kasala Jabeer ya zuba mata idanun sa yana kallon ta, dan kuwa a gajiye yake amma ba yanda zai yi dole ya yi mata abinda take so ya san ba yin kanta bane,ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce mata, "Kin tabbata ita kike so yanzu?" Ya qarasa maganar shi yana shafa cikin ta, saurin kauda kai ta yi gefe,dan kuwa kallon nashi na ratsa ta da yawa,bata so ma ya bata tausayi tace ta fasa dan kuwa muguwar sha'awar agwalumar take yi, d'aga kai kawai ta yi alamar Eh agwalumar take so, murmushi ya yi ya miqe tare da ajiye mata wayar shi a gefen ta ya tashi ya ja rigar shi ya sanya ya na fad'in, "Bari na je na kawo maki kada sai sun tashi ki sa min kuka ki ce baki hakura ba sai na nemo ta" Murmushi ta yi na jin daɗi, Jabeer ya sunkuya ya sumbaci goshin ta sannan ya bar gidan dan zuwa nema mata abinda ranta yake so tun da akwai inda za a samu ɗin a unguwar tasu, jabeer na daga cikin irin mazan nan da ke bawa matan su mahimmanci sama da danna wayar su ko wani abu a rayuwar su. Jabeer bai dawo ba sai da ya samo wa Juwairiyyah agwalumar kalar wadda take so mai zaqi,zama ta yi ta sha ta qoshi,shima ya ɗauki ɗaya ya sha ya na ta yamutsa fuska kamar an mare shi, kafin daga baya ya miqa mata duka ya ce, "Gashi nan ki yi ta fama," Dariya ta yi ta karɓi abunta ta yi masa godiya,gidan ya je ya rufe tare da tofe ko ina da addu'a sannan ya dawo ya rufe qofar palourn su, ya na zama ta tashi ta nufi d'akin baccin su Jabeer Shima ya kashe fitila ya bi bayan ta. ****************************** Fad'uwar Goggo Sarai ce ta ja hankalin su Suwaiba suka yi kanta gaba ɗayan su da gudu,kwance take magashiyan a qasa ta na bin su suwaiba da kallo kamar waɗanda suka sake sabuwar halitta a Jikin su, (ai ba qarya Hajiya Goggo suwaiba kam ta sauya halitta lols) idonta a buɗe hawaye na zuba ya wanke mata fuskar ta take qoqarin yin magana amma ta kasa,da karfi ta sa hannun ta ta toshe bakin ta ta sake fashewa da sabon kuka sai kace wadda aka aiko wa da rasuwar iyayen ta a qauye. Ganin halin da take ciki ne ya sanya Mama Balki daure wa ta isa wajen ta da sauri, dan ta kula gaba ɗaya yaran nata kallon ta kawai suke ba wanda ya yi yunqurin d'aga ta daga qasa, d'aga ta ta yi da kyar ta kai ta kan kujerar dake daf da bakin qofar shiga d'akin ta ta zaunar da ita,sannan ta tafi cikin hanzari ta ta deb'o ruwa a randar sanyin ta ta miqa mata a cup, kasa shan ruwan ta yi tana ta kallon Suwaiba da ta haɗe girar sama da qasa, qarshe ma sai ta yi hanyar d'akin Mama Bilki. Kuka ne ya k'wace wa Goggo Sarai da ta ga gaba ɗaya yaran ta duk sun bar wajen ma sun yi dakin kishiyar ta da ta dasa musu tsanar ta a ransu tun suna 'yan qanana,sai gashi tun ba a je ko ina ba yau ita suke nuna wa soyayyar su, wani gululun baqin ciki ta hadiya ta kalli Mama Bilki da ita ɗaya ce a kanta ta kauda kai taci gaba da zubda hawaye har wannan lokacin ta kasa magana. Baba ne ya yi sallama ya shiga gidan,Mama Balki ke da girki ranar dan haka can ya nufa zai shiga,sai dai kukan da ya ji ana yi a d'akin Goggo Sarai ne ya tsaida shi, sai da ya tabbatar da gaske kuka yake jiyo wa kuma da alama na Goggo ne sai ya wuce d'akin nata dan ya ji me ke faruwa. Ko da ya shiga sai ya tadda su Mama Balki a d'akin,ba kalar magana da lallashin da bai yi wa Goggo ba dan ya ji me ya sanya ta kuka amma ta ƙi magana,iyakar abinda Mama Balki ta sani ta sanar da shi sai kawai ya fita ya koma d'akin Mama Balkin dan ya tabbatar da maganar ta na cewar suwaiba ta dawo. Ya na shiga ya tarar da suwaiba na kuka da sauran 'yan uwan ta, " Suwaiba ke nake gani a gidan? Meke faruwa ne wai na ga kuna kuka? ku sanar dani damuwar ku yarana, duk da banda arziqin da zan maku maganin ta amma Allah ya hore min bakin yi maku addu'a akan ko meye matsalar ku" Suwaiba ce ta je gareshi da gudun ta ta rungume shi, shima rungume ta ya yi a Jikin shi, nan da nan lokacin yarintar ta da tashin ta kafin ta girma ya dawo zuciyar mahaifin nasu,suwaiba kuka take mai ban tausayi,Baba ya kyale ta bai d'ago ta ba sai da ta yi kukan ta ya ishe ta sannan ya zame ta a Jikin shi ta zauna a qasa a gefen qafar shi,a hankali Baba ya ce, "Sanar da ni damuwar ki d'iyata,ku zo duk ku fad'an damuwar ku na ji ko zan iya yi maku maganin ta" Cikin shassheqar kuka suwaiba ta ce, "Baba.... Baba ka yafe min, Baba ka yi hakuri akan qin jin maganar ka da na yi abaya,Baba nadama ta same ni a qurarren lokaci...." Da sauri Baban su ya dakatar da Ita cikin tausayawa ya ce mata, " Ah ah Suwaiba karki ce haka, lokaci bai qure maki ba 'yata" Da sauri Itama ta katse shi ta hanyar d'aga rigar ta ta ce, "Baba duba ka gani" Cikin kukan da take yi ta juya wajen Saudat tace, " Saudat nuna masa cikin ki kema ya gani" Saudat ma nuna masa cikin ta ta yi dai-dai inda aka yi masu aiki aka cire masu mahaifa,. "Me ke faruwa ne ku buɗe baki ku yi min bayani" Baba ya faɗa cikin tashin hankali saboda ganin da ya yi Suwaiban su ta zama Nonoless, "Baba mazajen da muka aura ta dalilin mugun son kud'i da abin duniyar tare da zuga da muka samu daga Goggo ashe 'yan qungiyar shan jini ne, Baba matsafa ne masu yin kuɗi da sassan jikin mutane" Suwaiba ta qarashe maganar ta cikin qunar rai da d'acin da take ji a wuyan ta, a tsorace Baban su yace, "Suwaiba ! Ki ka ce me? Shan jini fa Suwaiba, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Ya Allahu ya rahmanu wannan wace iriyar rayuwa muke ciki mai cike da rud'ani da tashin hankali? Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Zama ya yi ya dafe kan shi da yake jin ya yi masa nauyi sosai,ya jima a haka kafin daga baya ya ce, " Sanar dani me ya sami qirjin ki da kuma gefen cikin ku gaba dayan ku ke da yar uwar ki?" Kwashe duk abinda ya faru ta yi ta faɗa masa, cikin kid'ime wa da tashin hankali ya miqe ranshi ya gama ɓaci da jin abinda ya samu yaran shi, duk ta dalilin matar shi da ta kasa taimaka masa wajen ba yaran shi tarbiyya, ficewa ya yi a d'akin ya nufi d'akin Goggo cikin sauri kamar zai faɗi tsabar damuwa da tashin hankalin da yake ciki, da wata iriyar murya Baba ke wa Goggo Sarai magana ya ce, "Shikenan yanzu hankalin ki ya kwanta, Saratu hankalin ki ya kwanta nace an maida min Yara marasa haihuwa, ba zan taba ganin jikokina ba ta bangaren su kenan,saratu bana manta wa ke da kan ki ki ka yi kutun-kutun ɗin da ya sa ki ka tsaida haihuwa, wai yaran sun ishe ki, wace irin mace ce ke? Da baki yi haka ba da na tabbata zuri'a ta tafi haka yawa a yanzu,Ki duba kiga Suwaiba an yanke mata nono gaba daya, banda jinin yaran nan da ake diba duk wata, tsahon wata takwas, ina zaki kai alhakin su saratu? Ga mahaifa an cire

Chapter 18 of 25