gidannan karka kori abinda zan samu, zan yi wahala ta hanyar halal na kula da abinda Allah zai bani, amma kar ka ce za a sake d'aga zancen uban d'an nan na gama da shafin shi, sabon shafi nake son budewa Baba"
Kuka ne ya ci qarfin ta sosai, wanda ya sanya Babansu hawayen tausayawa diyar tashi, yarinya fara mai kyau duk 'ya'yan shi Juwairah ce kawai ta fisu komai, amma Salma na bayan ta, dubi yanda ta koma ta jeme ta d'ashe kamar mara isashhen jini a jikin ta, har yau Salma bata rufe shekara ashirin ba, d'aga ta ya yi tsaye ya rungume ta,aiko kamar jira take yi,tunda abubuwa marasa daɗi sukai ta faruwa da ita take neman kafad'ar da zata jingina kanta ta koka baƙin cikin ta amma ta rasa, sai yanzu ta samu strong and loving arms ɗin da suka yi huging ɗin ta,hakan ne ya bata k'warin guiwar fitar da duk wani b'acin ran ta, haka Baba ya bar ta a kafad'ar shi ta yi kukan ta ma'ishi,da kan ta ta hakura ta samu waje ta zauna a gefen shi ta na sauke ajiyar zuciya.
Cikin murya mai rauni Baba ya ce yace,
"Ina zuwa Salma bari na dawo"
Mama Bilki ya kira bayan ya faɗa mata duk abinda ya faru, a tare suka shiga d'akin Goggo Sarai wadda har a wannan lokacin kuka take tare da tambayar Salma me ta yi wa Alhaji Mansur ya sake ta,Salma kuwa ko qala ta qi ce mata,Mama Balki na qarasa shiga sai ta isa wajen Salma ta zauna tare da dafa kafad'ar ta, Salma na ganin Mama Balki sai ta rungume da sauri , tana neman gafarar ta, Mama Bilki kuwa nan take ta ce,
"Salma na yafe maki Allah ya yafe mana laifukan mu, faɗa mana me ya faru"
Mama Balki na gama rufe baki Goggo Sarai ta isa gaban Salma a guje ta damqe mata baki ta na zaro ido ta ce,
"Yi shirun ki wannan sirrin mu ne kar ki yi magana a gaban maqiya"
Wani irin kallo dukkan su suka watsa mata, Salma kuwa kwace kanta ta yi a hannun Goggo Sarai ta fara magana,nan take ta sanar da su komai da ya faru tin daga tafiyar ta har dawowar ta a yau din, kuka sosai Baba ke yi duk jarumtar shi sai da ya tausaya wa 'yar shi har ya zubar mata da hawayen tausayawa,Mama Bilki ma ta yi matuqar tausayawa Salma,ita kanta Goggo Sarai abun ya dake ta kwarai,ga tausayin Salma ga kuma kunyar mutanen da ke zaune a gaban ta, ita kanta kuka take kamar an mata duka, Salma ce ta juya ta kalle ta ta na murmushin takaici ta ce,
" Yanzu Goggo a wanne hali su Adda Suwaiba suke, suna Kiran ki a waya ? kin je kin ga muhallin su ko kuma baki sani ba, kawai suna aiko maki da kuɗi ne kina ajewa ki na kashe na kashewa? Goggo baki san ina ne Abuja ba, amma tin tasowar mu kika kimsa mana son ta, yanda kika saka mana son abun duniya da hutu, da haka kika saka mana son ku kaɗai da yi muku biyayya da duk inda mu ka je aure ko min talauci da za mu zauna mu samawa kammu farin ciki,amma baki yi wannnan ba, Bama a maganar ki yi qoqarin dasa mana tsoron Allah da son Allah da yi wa Annabin rahama biyayya akan saqon da ya zo mana da shi na gaskiya, Goggo kin ci amanar kiwon da Allah ya baki, Baba na iyakar qoqarin shi akan mu kina rusawa, ni yanzu ba zan zauna anan d'akin ba, Mama Bilki ina riqon arziqin komawa wajen ki na zauna, dan tabbas nima ina zargin ciki gareni a yanzu duba da rashin ganin al'ada ta da ban yi ba,ga yawan ciwon kai da mara sai zazzaɓi da nake yawan yi, Mama Balki dan Allah ki koyan dukkan irin tarbiyyar da ya kamata nima inna haifi nawa na basu,ba irin wannan tarbiyyar mara kyau da ma'ana ba"
Goggo Sarai ce ta kwad'e mata baki da qarfi har sai da jini ya fita daga bakin Salma sannan ta ce,
"Dan uban ki to da haka ki ce ita ce ta haife ki ma mana? Ku tashi ku fice man a d'aki gaba ɗayan ku bana buqatar kowa, yaran da suka san daraja ta da qimata za su zo su kula dani, dama ke tinda aka yi auren ki me ki ka tsinana min? A wajen neman mijin me yasa baki tsaya kin nemi kamar na yan uwan naki ba ? Banda wahala me ki ka samo wa kan ki? Sai ku tattara ku je can ku qarata,jikoki kuma ko awajen yarannan biyu ba zan rasa su ba, dan ba zaman banza na aika su yi ba a gidan Mazan nasu"
Ganin cewar ita fa Goggo Sarai bama ta yi nadama ba sai suka miqe za su fita daga d'akin, Mama na yi mata addu'ar shiriya a ranta, dakin ta ta kai Salma sannan ta fita tsakar gida ta dakkowa Salman abinci ta bata, kamar mayya haka ta hau shi da ci kuwa tana hawaye, tana gama ci ta sha ruwa nan take kuwa bacci mai daɗi ya kawo mata ziyara.
Mama Bilki ce ta gyara mata kwanciya tana tsananin tausayin ta, Abba sai godiya yake mata da sanya albarka.
*****************************
Bangaren su suwaiba 'yan Abuja kuwa suna can Abuja su na cin duniyar su da tsinke hanakali kwance, su kuwa su Alhaji Kalla na can na shirya wani babban lamari akan su ba tare da sun sani ba.........[21/07, 7:46 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 ' YAN ABUJA. 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*SANARWA*
*Makaranta ku yi min afuwa shekaran jiya na tura page 20 amma suka maqale basu tafi ba shi yasa kuka ji shiru na san na tura na zaci matsalar network ne za su iso daga baya,shiru basu zo ba kuma wayata kwana biyu ta na bani ciwon kai shi yasa,amma a yi hakuri za a ci gaba daga inda aka tsaya...masu nema daga farko ku yi haƙuri a gama editing a mayar document..kar ku manta wannan ba sabon rubutu bane tsoho ne na yi shi tun 2017 editing nake yi za a gama da wuri da yardar Allah...na gode*
Page 22:
Zaune suke gaba ɗaya 'yammatan Markan a d'akin ta ta sa su a gaba ta zabga uban tagumi hankalin ta a matuqar tashe,Huwaila na kwance da gwangwanin madara da suke yin alalen gwangwani ta zuba masa qasa sai zuba yawu take yi a ciki, wani wawan tsaki Marka ta zabga ta kauda kan ta ta na kallon Jummala da ke yatsuna fuska,kan ta kai ga tambayar bahasin yatsinar suka ga Jummala ta fita da gudu tsakar gida ta na kelaya amai, kukan da Marka ke ta riqewa ne ya kufce mata, Jummala ce ta dawo riqe da cikin ta ta zube a qasan simintin d'akin daidai inda ledar d'akin ta yage ta na bin sanyin wajen,a haukace Marka ta yi kan su da duka ta na fad'in
"Ina zaune da qananan 'yan iska ashe ni Marka ban sani ba,da uban wa ku ke lalata har dika ku biyu ace wai ciki ne da ku, yau in mahaifin ku ya ji wannan mugun labarin ni Marka ya zanyi da raina, wannan abun kunyar ina zan kai shi a garin nan?"
Kuka take tana share kwalla, shirun da suka yi mata ne ya qara b'ata mata rai matuqa, watakan sun ma mai da ta yar iska kenan ko,dukan ne da alama bai shiga jikin su ba, a haukace ta fita madafin su ta dakko zankad'ed'en maburgin miyar ta ta yi d'akin ta rufe qofa ta rufe su da mahaukacin duka, ita dai Huwaila ba k'warin guduwa sai baki, nan take ta ko fara magana cikin kuka ta ce,
" Allah marka ki kyale mu ai iskanci ba kan mu farau ba, kuma naga iyayen yaran na gida ne ba bare ba su bangis ne fa, Baban su na gidannan shima yana zuwa lalubar ki duk daren duniya baku ko gajiya ko d'aga wa juna qafa ko ji kike bamu sani ba? Na san komai duk mun san ki na da hannu a qullawa Salame sharri ke da Baban Bangis dan asirin ku ya rufu ku ci gaba da watsewa idan Baba baya gari,dan haka mu ki daina dukan mu kema ai duk ɗaya muke da ke gwanda ma mu bamu da aure, kuma shikenan dan naki bai fito ba namu ya fito ba za ki kashe mu a banza ba, kika qara dukan mu sai na faɗa ma Baban mu in ya dawo kuna kub'ewa keda yayan shi"
Da sauri Marka ta sa labccen hannun ta ta damqewa Huwaila da ke tona masu asiri baki,ta na ta zaro ido da waige waige tare da fatan Allah ya sa ba wanda ya ji wannan mummunan sirrin da suke b'oyewa, ashe dama yaran kallon su kawai suke yi sun san komai?
Ji suka yi an banko qofar da mugun qarfi, wani tsoro ne ya kama ta ba ta san sanda wata muguwar tusa ta kwace mata ba, zama ta yi kusa da yaran ta na jiran taga wanda ya ke son shigowa d'akin kamar aradu,yaran kuwa sai toshe hanci suke tsabar azabar warin tusar da ta sakar musu.
Talle ne ya bayyana a gaban su idon shi ya kada ya yi jawur akan wanda yake da shi, idan aka ce Talle zai iya kisa a wannan yanayin ba mai yin musu,nan take ya damqo wuyan Marka ya mata mummunar shaqa, ya ja ta suka fita har tsakar gida yaran su na biye da su cike da tsoro, qananan sai kuka suke yi,'Yan matasan kamar su Haule kuwa sai bin su suke suna mamakin abinda ke faruwa yau a gidan nasu , har qofar sashen yayan nashi ya je ya wurga Marka a jikin shi,shi kuma a daidai wannan lokacin ya fito da tabarma a hannun shi na dama ɗaya hannun nashi na hagu riqe da buta za shi zaman qofar gida na safe da suke yi, janye jikin shi ya yi yana wani ja baya tare da fad'in ,
" Subhanallah,meye haka zaka rab'an matar ka a jikina, bayan kasan ba muharrama ta bace ba"
Wani gigitaccen mari Talle ya bankawa yayan nashi, buɗe baki ya yi zai yi magana Talle ya qara make shi Saida ya tintsira ya faɗi qasa tabarmar hannun shi da buta tini sun yi nasu waje,shiru ya yi ya damqe bakin sa saboda tsoron kada wata kalma ta fito a sake banka masa mari ya tabbata asirin su ne ya tonu dan shine kaɗai zai bawa Talle yi masa wannan rashin mutuncin,nan ya samu waje ya yi zaman 'yan bori a wajen ya hau kuka, Marka kuka Yaya kuka saboda nadama da kunyar abinda suka dinga aikatawa, wani haushi ne ya kama Talle kukan uban me suke yi kuma yanzu, kuka ai shi ya kama, miqewa ya yi a haukace ya bisu da duka, duk wanda ya samu ya maka har yayan nashi,wata iriyar tsanar su ke huda zuciyar shi, sai da ya yi masu lilis sannan ya fice ya bar gidan,jiki duk tsami baki kamar an liqa masu super glue haka suka kad'e jiki kowa ya yi d'aki dan kuwa yanda Talle ya jibge su ba tare da ya tona asirin abinda suka aikata masa ba suma haka za su yi gum da bakin su, to in ba su yi shiru baaa me za su ce wa yaran da ke ta koke koke saboda ganin yanda Talle ke jibgar su? Hannun Yayan Talle ne ya kumbura ta wajen tsintsiyar hannun haka ya karasa shigewa d'akin shi ya na numfarfashin wahala dan ya san tabbas sai ya ga mai dori a ja masa hannun.
******************************
Allurar bacci Alhaji Salihu ya yi wa Suwaiba da ya dawo ya tarar ta fara bacci,sai kawai ya tsaya akan ta yana qarewa qirjin ta kallo,duk kyan wajen nan yanzu haka za a je a yanke su ba ko d'igon imani? Alfarma ɗaya Oga zakas ya yarda zai yi masa, alfarmar kuwa itace tinda yana son matar shi to a yanke mata irin yankan da bazata mutu ba wajen yin shi, in an gama gudanar da tsafin za a yi mata operation yanda daga baya zata ji sauqi a hankali su ci gaba da rayuwar su, hawayen tausayin ta ne ya zubo masa, wanda hakan sabon abu ne a wajen Alhaji Salihu,bai taɓa zuwa gabatar da wani aiki ya ji tausayin da ya sanya shi zubar hawaye ba,hawa gadon ya yi ya rungumo ta ya ɗora kan shi a qirjin ta,hawaye ya dinga zubarwa tare da ɗora hannun shi a Saman qirjin ta cike da jimanta lamarin, ya jima a haka ya na zaune da kyar ya hakura ya dauke ta ya yi mota da ita,dajin da suke gudanar da tsafin su ya nufa ma'ana gidan Oga Zaks.
Hankalin Alhj Kalla a tashe yake ganin rashin dawowar Saudat,ta ina ma zai fara tunkarar shugaban qungiya ya ce matar shi bata dawo ba bayan ya san an yi masu duk wata alfarma da za a iya yi masu?
Ta ina zai fara samo wadda za su yi aikin akan ta a wannan qurarren lokacin? Anya ma zai iya kyale Saudat haka kuwa ba tare da ya lahanta rayuwar ta ba? Yanzu idan yace zai yi mata wani abu kuma asirin su ne zai tonu akan na da,dan tabbas tunda Saudat ta qi dawowa zargin shi ya tabbata ta san komai game da su kuma ba za ta kasa sanar da dangin ta ba.
Ya na nan ya lula duniyar tunani da damuwa tare da neman yanda zai ya shawo kan matsalar da yake ciki Alhj Salihu ya yi masa waya yace shifa ya ɗauki hanyar zuwa wajen Oga zaks amma ya ji shiru bai ji daga gare shi ba,
"Ka na nufin Suwaiba ta dawo ita?"
"Kwarai da gaske,me yasa ka tambaye ni bayan a gaban ka muka yi waya da ita ta ce min suna hanyar dawowa? Ko dai Saudat bata dawo bane?"
"Ina fa ta dawo aboki na, ka je gani nan nima ina nan tafe yanzu nan"
Ya na kashe wayar shi ya lalubo lambar 'Yar Gwal,kamar ba zata ɗauka ba sai da ta kusan katsewa ta d'aga ta na wani yauqi da yanga, Alhaji Ƙalla kuwa a ran shi ya yi murmushi ya ce,
'Duk wanda yaci ladan kuturu dole ne ya yi masa aski'
Ita kuwa 'yar Gwal ta ɓangaren ta murna take dan ta san Alhajin akwai kashe kuɗi,a bai bata kuɗi masu yawa ba yana bata dubu ɗari biyar sai kuma abinda ya yi sama,cikin yauqi da yanga ta ce,
"Hello Alhajina yau ka tuna da ni kenan"
"Kwarai kuwa, kin san har yau madam bata dawo ba ina gayyatar ki wajen shaqatawa ta nan da rabin awa kar ki b'atan lokaci zan kirawo zinariya idan ki ka wuce lokacin da na qayyade maki"
"Baka da matsala Alhajina"
Da hanzari ta tashi ta hau shirye-shiryen fita, qawayen ta ne suka fara tambayar ta ina zuwa da safennan, bayan qa'idar su fitar dare ne? Sanar da su ta yi inda zata je ta yi,shewa suka ɗauka saboda sun san kuɗi sun zo kenan,wasu a cikin su kuma suka tab'e baki saboda baqin ciki suke yi kar ta samu kuɗi sama da yanda suke samu.
Ko wanka bata tsaya yi ba ta shirya a gaggauce ta tafi, a qofar gidan ta same shi ya na jiran ta sai zuba qamshi yake ya haɗe cikin manyan kaya farare tasss sai jar hular su ta zuwa gidan Oga Zaks, motar shi ya nufa ta mara masa baya ta na taku cike da yanga buɗe wa suka yi suka shiga, Alhaji Kalla ya kalli 'Yar Gwal ya na kashe ido da murya ya ce,
"Ya kamata yau na kai ki wajen shaqatawa na musamman mu yi aqalla sati a can muna more rayuwar mu ba mai takura mana ko ya neme mu"
Wani juyi ta yi da mazaunan ta a kan cinyar shi da tunda suka shiga motar ta haye sai ta sakko ta zauna a gefen shi amma rabin jikin ta na nashi,cike da kissa da murmushi ta sumbace shi a kuncin shi, ba tare da sun sake magana ba Alhaji Kalla ya kunna mota suka bar gidan suka ɗauki hanyar dajin Oga Zaks.
Sun jima suna tafiya kafin su isa, suna isa wajen taga wajen cike da motoci kala kala, ga maza da mata nan ko ta ina sanye da kaya iri ɗaya kamar ankon biki, wani abu ta ga su na yi a matsayin gaisuwa, sannan suka shige cikin qaton gidan gaba ɗayan su kamar dama su ake jira.
Ko da suka shiga gidan sai ta ga sun zagaya bayan asalin ginin gidan inda wani qaton waje yake ga wani sassaqen icce nan kamar gunkin mace lullub'e da jan kyalle iya rabin jikin ta an zuba wani jan abu a qasan qafafun ta mai kama da jini,sai wuta da ke ci a cikin wasu tanderu na qasa kai da ka ga wajen ka san waje ne na tsafi ko bautar gunki, kafin su isa taga dukkan Alhazawan nan da suka zo da mata sun d'akko wani jan yadi a aljihunan su sun nuna masu suna kalla har ita sai suka zube a qasa, ita dama Oganniya Suwaiba ta dad'e a sume, ɗaukar su suka yi suka aje a wani gadaje da aka tanadar masu na musamman sai ƙwarya a kowanne gado wadda aka yi wa fenti da jar kala, Oga zaks ne da sauran mutanen wajen kowa ya cire kayan shi, haka suka tsaya zigidir babu kaya a jikin su,kowannen su hannun su ɗauke da wuqa kowa ya kama wadda ya kawo da niyyar aiwatar da ayyukan da ke gaban su, muryar su ta karad'e wajen da Kiran Sunan gunkin da suke yi wa tsafi.
Alhj Salihu ne ya zo gaban Suwaiba da wuqar hannun sa ya na yi wa gunkin tsafin nasu kirari zuciyar shi a cunkushe da baƙin ciki, ji yake kamar ya bijire ma Dodon nasu,amma tinawa da azabar da zai shiga indai bai yi wannan abun ba,sai kawai ya saka ma nonon Suwaiba wuqa ya yanke shi ya tara jinin a kwaryar gaban shi jinin suwaiba na zuba a ƙwarya hawayen shi na zuba a Saman fuskar ta,haka sauran ma suka yanke wa matan da suka kawo nonon su dukkan su suka tari jinin a irin ƙwaryar da Alhaji Salihu ya yi amfani.
Kuka Alhj Salihu ya fashe da shi wanda ya yi sanadiyyar jan hankulan mutanen wajen, kowa daya kalle shi ya ga yanda yake kuka ga uban ciki a gaba ba tufafi a jikin shi, ga uban baqi da ya yi yana zufa yana maiqo, sai dariya ta kama shi haka suka dinga yi masa dariya, saida Oga Zaks ya daka masu tsawa suka nutsu, cikin haɗe fuska Oga Zaks ya ce,
" Me yasa ka kuka kai Salihu?"
Cikin kuka Alhaji Salihu ya bashi amsa da Cewar,
"Ina son mata ta Oga a san ya za ai a mata aiki a shafe wajen kar ta mutu , ka taimaka min Oga kumin alfarmar nan oga ka yi alqawari ba zaka bari mata ta ta mutu ba Oga"
Dariya sosai Oga Zaks ya yi sannan yace,
"Kar ka damu Salihu zan cika maka alqawarin da na ɗauka, ni nace maka zamu san ya zamu yi matar ka ba zata mutu ba, ita waccan guduwa ta yi ne na ga an kawo wata a madadin ta ko ka na nufin ba zan gane ba ne Kalla?"
Ya maida tambayar shi kan Kalla wanda ya zaci ba za a gane ya yi sauyi ba,
" Eh Oga ba ta biyo 'yar uwar sun dawo tare ba da suka tafi ganin gida sai ita ta qi dawowa, a min afuwa Oga sanin mahimmancin wannan rana a gare mu ne ya sa na gaggauta samo madadin ta"
"Babu damuwa yanzu ɗauke ta kai salihu ka kai ta d'akin duba marasa lafiya a duba ta"
Da gudu Alhaji Salihu ya ɗauke ta ya yi d'akin duba marasa lafiya na cikin gidan ya shimfide ta a gado Doctors biyu ne suka hau kula da ita shi kuma ya koma wajen tsafin nasu dan su ci gaba da gudanar da tsafin da suka zo domin shi, layi suka bi suka dinga zuba wannan jinin a qafar dodon tsafin nasu sai su d'aga kwaryar a gaban ta sai su shanye ,haka suka dinga bin layi layi suna yi har kowa ya gama,bayan sun kammala komai ne wasu qarti suka shigo filin wajen suka tattare matan suka kai su wani d'aki mai duhu.
Bayan an gama yi wa suwaiba dinkin da ya dace da duk wata kulawa sai suka bashi matar shi ya sanya kayan shi ya kaita mota, Alhaji Kalla na biye da shi a motar shi hankalin shi kwance, horn ya yi ta wa abokin nashi yanda suka saba in zasu rabu amma bai mayar masa ba tsabar damuwar da ke cikin ran shi, kad'a kai Alhaji Kalla ya yi ya wuce abun shi, sai ya ga ai ba ma amfanin ya koma gida ba mata kawai ya yi kwana ya tafi club.
Alhaji salihu kuwa yana isa gida ya d'akko Suwaiba a hannu kamar yanda ya fita da ita a hannu ya shiga d'akin shi da ita, kan gado ya ajiye ta, ya zuba mata ido ya na kallo yanda a cikin qanqanin lokaci ta d'ashe ta yi fari alamar ba jini sosai a jikin ta, kwanta wa ya yi kusa da ita ya rungume ta, a haka Shima ya yi bacci.
Bashi ya farka ba sai sha ɗaya na safiya wanda ta sanadin motsin Suwaiban ne ya sa shi tashi, hannayen ta biyu ta miqar dan ta yi miqa an tashi daga bacci sai ta yi saurin sauke su saboda wani azababben ciwo da ta ji ya soki qirjin ta , komawa ta yi ta kwanta cikin zubda kwallah ta ke son sanya hannu ta tab'o qirjin nata, da sauri ta sauke hannayen nata saboda jin zafi da ta yi sannan ta ji wayam alamun ba komai a wajen,mamaki take yi ina kayan wajen suka tafi dan kuwa ta sani Allah ya azurta ta da su manya ma kuwa amma me yasa ta ji wayam sannan take jin wajen kamar an yanke ta??? Ni kuwa 'yar kawo maku rahoto na ce ba kama bane Suwai matar manya da alama dai kin zama Nonoless ..............
[21/07, 7:46 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 ' YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 21:
Yau Juwairiyyah ta tashi da aikace aikace da yawa amma dik da haka ta sa a ran ta a yau take son ta je gida dan su gaisawa da 'yan uwanta dan bata san ranar komawarsu ba, da farko Jabeer yaso hana ta ta bari sai jibi tace sam zata iya ba wani gajiyar da zata yi, haka ya hakura ya barta, tana idar da sallahr asuba ta ninke hijab da abun sallah ta ajiye ta fara da gyaran d'akin ta ta na yi ta na azkar,a haka ta gama da d'aki da parlour sannan ta nufi kitchen dan yi ma Jabeer abinda zai samu ya tafi da shi Abuja wajen interview da aka kira su na wani aiki da ya nema a NNPC, dubawa ta yi taga basu da wasu kayan abinci sosai kamar kullum, ragowar Flour da ba zata wuce gwangwani biyar ba ta dakko da ɗan kifin da ta siyo a jiyan na naira dari biyu da attaruhu da albasa ta gyara su ta ajiye, sai ta samu guntun cabbage da take da shi ya riga ma ya kusan qarewa sauran irin qasan nan sai ta yanka shi da albasa mai ganye ta wanke ta tsane su,sai ta koma ta daka attaruhun ta haɗa da ɗan kifin nan, ta soya sama2 ta zuba wannan cabbage ɗin da ganyen albasa.
Ta na kammalawa da wannan sai ta ajiye dan ya sha iska tunda ta masa irin suyar nan ne da ruwan jiki ya qafe tass, kwab'in meat pie ta yi wa flour .
(Mata a dinga faɗad'a tunani saboda a samu mafita mai girma)
Tana kammala meat pie ta ɗora ruwan kunu bayan ya tafaso ta dama masu koko da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 25