Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da ayyukan su, a wannan karon ba zai bari abokin nashi ya rusa masu ɗaukakar da suka jima su na ginawa ba dole ne ya taimaka masa ya kawar masa da duk wani so da qaunar Suwaiba da ya fara yi. Taɓa abokin nashi ya yi, ya masa nuni da kofar fita daga babban hall ɗin alamar su tafi kenan, miqewa ya yi da kyar jikin shi a mace suka fice, tun kafin su bar wajen kuwa mutanen wajen ke ta 'yan gulmace gulmace , ko ina ba a raba mutane da gulma,bayan sun isa gidan Saudat ne, suka shiga inda suke tattauna matsala irin haka in ta taso musu suka zauna, Alhj Kalla ne ya fara magana, dan ya kula in bai yi ba Alhj Salihu ba zai ce uppan ba, " Salihu ni ban ga abin d'aga hankali a maganar nan ba fa, duk da ni kaina a yanzu haka na fara son yarinyar can,koba komai duk matan da muke huld'a da su yaran nan na kula suna da na su sirrin daban a jikin su, ga yarin ta ga kyau, amma kasan bijirewa Oga Zaks na nufin qarewar arziqin mu, niko dana talauce gwanda na aikata abinda yake so, mu kaisu kawai,a yanke abinda za a yanke a jikin  nasu kawai, naga dai ana ciwon cancer ma a yankewa wasu nan ɗin kuma su ci gaba da rayuwa" "Ba zaka gane ba abokina, in ba wajen a ina mutum zai na hutawa? Kai ni fa bari kaji ba zan iya bane kawai, duk sokoncin yarinyar nan ina son ta, dan in tare kake da ita ta b'aro maka wani haukan sai ka ji kamar ka yi ta zane shegiya, amma kuma yarinyar tayi ta na da wani sirri na daban wanda ba kowacce mace ake samu da shi ba, banjin zan iya rabuwa da ita, yanzu ni dai shawarata shine su je gida kawai su ga gida na kwana ɗaya ko biyu in suka dawo munga ya za ayi, tinda kaga bai kamata har in ma mutuwa za su yi tsohon su bai gan su ba, dan ta uwar su ita ta jiyo banda case da ita ni" "Haka ne kayi gaskiya, to bari na faɗa masu kawai gobe su shirya zasu gida ko ya kace, dan da kaina ma zan haɗa mata kayan ta dan ta tabbatar da gaske nake tunda a ganin ta ni ne bana so su je ganin gida dama,ahmmmm ai sai ka tashi ka tafi ko?  dan kuwa ina so na yi sallama da iyali na, bamu san ya abubuwam zasu kaya ba" Dariya suka yi suka tafa,Alhaji Salihu ya ce, "Shegen sama nima ba ri na hanzarta na koma gida na taya ta haɗa kaya kuma mu yi sallama" Yanda suka tsara hakan suka gudanar, washe gari da asussuba su suwaiba suka ɗauki hanyar kano kowa da drivern ta dan wadata, ga wata mota nan shaqe da kayan arziqi na bin su a baya, haka suka isa garin Kano direct gidan su Suwaiba suka isa, Goggo Sarai duk ta baza wa dangi da 'yan unguwa zuwan su Suwaiba dan haka gidan a cike yake da jama'a kowa ka gani ya na cikin doki da murnar ganin dawowar 'YAN ABUJAn,sanda motocin suka parker a qofar gidan nasu basu fita ba sai da drivers suka fita da sauri suka buɗe musu motar sannan kowaccen su ta fito hannun ta riqe da manyan wayoyi da jakunkuna masu tsada da kyau,a hankali suke takawa tare da d'aga wa mutane hannu suna sakin murmushi kamar wasu matan gwamnoni,da Salma suka fara yin tozali kanta a bisa cinyar Mama Bilki tana mata kitso a kwance kamar wata jaririyar ta, salati Suwaiba ta yi ta kalli Saudat sannan ta ce, " Sudat me nake gani haka ni Suwaiba? Yaushe gidan ya koma haka? Da jin muryar ta Salma ta miqe da gudun ta ta yi kansu tana ihun murna ta na fad'in, " Goggo ! Goggo fito ga su Adda sun zo, Mama kinga su Adda sun zo, ina Baba? Baba fito ka ga ikon Allah su Addana ne a gidan yau" Shanye mamakin ganin yanayin Salma suka yi aka ci gaba da murna ana gaisawa da jama'a amma cikin ransu akwai tambayoyi masu tarin yawa dangane da rayuwar qanwar tasu Allah Allah suke mutane su tafi su zauna su ji me ke faruwa, shi yasa da sun gaisa da mutum sai su bashi dubu d'aya ko biyu, su kuma mutane ana basu kuɗi sai su yi godiya su bar gidan dama su suka kawo su,dakin su da Goggo Sarai ta sake gyara masu suka shige su na shiga ciki suka tadda  Goggo Sarai da ta danne murnar ganin yaran nata bata bazama ta taro su ba, ta yi hakan ne dan ta nuna wa mutane ita fa mai aji ce uwar matan manya,su na shiga kuwa Goggo ta fashe da kukan daɗi, bakin ta kuwa ya qi rufuwa saboda murna, su kan su su Suwaiba sai da suka zubar da kwallar farin cikin ganin mahaifan nasu basu san sun yi kewar su sosai ba sai yanzu da suka gan su, nan fa aka hau gaishe gaishe ana tambayar juna bayan rabuwa,wata shewa Goggo Sarai ta sanya ta daki cinya sannan ta ce, " Ayyyuririri ! kai yau ni saratu na ji dad'i na,shiyasa nake son Allah dan kuwa akwai shi da biyan buqatar bawa Jama'a ku dubi yarana , san kowa baqin cikin marashi, ga kuɗi ga kyau, ga hutu, na ji daɗin zuwan ku yarannan, ya mazajen naku? Su na can an baro su a Abuja , waiwaiwaiiii Allah sarki garin daɗi na nesa" Cikin murmushi da d'agun kai irin na mutanen da aka gama yi wa kirari suke jin kan su ya kumbura suke amsawa a cikin taqama, "Suna lafiya suna gaida ku, ga abubuwan kayan abinci nan da kud'ad'e da suka aiko a baku ke da Baba" Cikin murna kamar zata kifa ta dafe kudin dika har na Baban nasu, ta jibge su a gefen ta ta na ci gaba da washe baki ta na surutu,shi kuwa Baba ko wajen kud'in bai kalla ba, ya yi masu godiya, Mama Bilki ce ta shigo ɗauke da ruwan Pure water a plate ta doro masu sanyi ta kawo masu, ajewa ta yi ta zauna dan a  gaisa,Goggo Sarai ce ta haɗe fuska ta ce, "Wai ni shin gaisuwar nan dole ce ne, a bar yara su huta dan Allah, na ga dai duk baqin sun tafi dan a bar su su huta to a bar su su huta mana haba,kuma in banda abin talaka ma duba fa wa zai sha wannan ruwan, dan Allah ki je an yafe Allah ya bada lada" Goggo Sarai na gama maganar ta suka haɗa baki da yaran cikin shewa suka furta, " Hahaiiiiii Casssss sai Goggo, ashe ana nan ana ci gaba da gashi, Allah dai ya sassaka Goggon mu" Dariya ta yi cikin isa tana wani d'aga hanci ita a dole uwar masu kuɗi ,Mama Bilki ce ta tashi ta ja hannun Ammar da ke son shigowa suka yi gaba, Salma ma tashi ta yi rai b'ace ta fita,cike da mamaki suka bi su da kallo dikan su, Saudat ta ce, "Wai ni Goggo me ke faruwa ne me nake gani haka tun da muka zo?  Salma da waccan matar a tare? Me kenan?" Baba ne ya basu labarin duk abinda ya faru da salma nan da nan suka hau jin tsananin tausayin 'yar uwar su akan wahalar da ta sha, sannan ya qara masu da labari akan irin hukuncin da ta yanke na zama wajen Mama Balki, anan ne ransu ya baci sosai, suka k'wala mata kira, bayan ta shigo ne suka balbale ta da faɗa kowa da abinda yake faɗa, sai da ta tabbatar sun gama ta miqe ta yi waje ba ta tanka ma kowa ba a cikin su, da bala'i Suwaiba zata bita ta dake ta amma Goggo ta hana ta ta ce, "Ai ni yanzu na cire ta a Yarana nima, taje can ta qarata, ina da ku kun ishen rayuwar zaman duniya har ma da qiyama, kuma yanda ku ka yi jan nan da alamar kuma kuna ɗauke da ciki, dan haka jika ne nake matuqar kwad'ayi yanzu a duniya fiye da komai, ta je ta yi ta fama, ita ta sani naku sun ishen zaman duniya dai ba na qiyama ba" kallon kallo suka hau yi wa junan su,nan take Saudat ta faɗa jikin Goggo tana kuka, Suwaiba ma idon ta ya cika da kwalla sosai,cikin kuka Saudat ta ce, "Adda Suwaiba akwai abinda nake so dama in faɗa maki tun da jimawa amma na qi sanar da ke dan nasan halin ki tona mana asiri kawai za ki yi ki jawo su kashe mu a banza" Cikin zaro ido Goggo tace wa Saudat, " Suwa..... suwaye zasu kashen ku?" Kuka saudat ta ci gaba da yi ta ce, "Mazajen mu Goggo yan qungiyar shan jini ne,na gano hakan da jimawa, yanzu haka bamu da mahaifa da ni da Adda Suwaiba kuma ina zargin su ne sanadi" Wani irin mari ta ji guda biyu sun sauka a fuskar ta suna neman dasa mata toshewar majiya,da ido ta ke bin inda marukan suka fito ɗaya daga Hajiya suwaiba ɗaya daga hannun Hajiya Goggo Sarai ne (uffararan ashe basu sauke faralin ba),cikin matsanancin Fushi Goggo ta fara magana, "Dan ubanki sharri kuma zaki yi masu, mutanen da suke kasuwanci a qasashe ko ta ina, arziqi ya wadata ya bunqasa shine zaki ce haka, so kike kema ki dawo ki zauna ki jamin asara, na haifi yarinya zankad'ed'iya kamar ki da zan samu dukiya amma sai ki dankwafe kan ki ki hana arziqi rab'ar ki? To ki bude kunnen ki da kyau ki ji, ko ya ake ciki gobe zaku koma ai an ga juna ba zan lamunci asara ba shashasha kawai, ina ganin ki kamar mai hankali ashe ba ki da hankali" Cikin kuka ta rarrafa wajen Baban su ta ce, " Baba ka yarda da ni,na rantse gaskiya na faɗa, ba sharri nake yi musu ba 'yan shan jini ne, na ji da kunne na Alhaji na magana akan qungiyar su ta asiri" "Na yarda dake 'ya ta, dan baki taba fad'an hakan ba kuma da dikkan alamu akwai gaskiya a zancen ki, wannan kud'in nasu yayi yawa" "Baba ya zaka yarda da wannan maqaryaciyar ? Qarya ne fa kawai dan sun taɓa dukan mu sau biyu, shine fa ta qullaci abun take son ta gudu, to in ke ba zaki koma ba ni zan koma d'akina, ina son miji na ya na so na da kyar ma ya hakura ya bari na zo saboda baya so ina yin nesa da shi, dan haka ke ki zauna duk abinda na tsakuro na sammaki tunda haka ki ka zab'awa rayuwar ki ta qare a wahale" Cikin washe baki da jin Suwaiba ta share mata hawayen baqin cikin da Saudat ke so ta saka mata Goggo Sarai ta ce, "Yauwa 'yar albarka, ai nasan in kowa zai juya min baya ke kin haifu cikin Saratu ba za ki juya min baya ba" Duk yanda Baba ya so ya nusar da suwaiba da goggo kin ganewa suka yi dan haka haka aka tashi  kowa zuciya ba daɗi, Saudat ta kafe bazata koma ba, inda Suwaiba tace ita zata koma, Salma da Mama Bilki kuma suna jiyo duk abinda ke faruwa,hankalin Salma ya tashi amma tasan bata da abinda za ta ce su saurare ta a wannan lamarin,Mama Bilkince ta shawarce ta akan ta musu addu'a kawai, hakan aka yi kuwa ta kwantar da hankalin ta suka hau yankan farce bayan sun gama kitson. " Babyna wai ni yaushe zaki je gaida su Mama ne ga cikin nan ya yi girma kar a Kai minzalin da  baza ki iya fita unguwa ba kuma, tinda ita tana abunnan na mutanen da har yanzu taqi zuwa ta ga dakin ki," "Hmmmm kaidai bari abunnan na min zafi ace wai uwa ba zata je taga d'akin 'yar ta ba? Ba komai zan je ko gobe ne na ji dazu Nafee tace su Adda sun zo, kuma Salma ta dad'e a gida ma zan so zuwa duk mu gaisa da su," " Eh haka ne, randa na je gaida su ma na ganta ai, Allah ya kaimu goben sai na samu na kai ki da kai na ko?..........❤ [21/07, 7:46 pm] asiyahabibu93: 💅🏼     'YAN ABUJA   💅🏼   WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Sis Ramlat Baba larens Aunty Ummu sokoto Cute one *Waɗannan sunayen na sama na kasa goge su a cikin sunaye kusan guda goma da na yi wa dedicating page ɗin nan, da can da ana yawan yi wa mutane dedication sai mutum ya jera Sunan mutane da yawa wanda a zaton shi masoyan shi ne na gaskiya na haqiqa😂 ashe inaaa kowa da abinda ya kawo shi rayuwar ka,dama bahaushe yace ba a San maci tuwo ba sai miya ta qare, tabbas rayuwa cike take da qalubale kala kala, wanda ya baka dariya watarana zai saka kuka, wanda ya sa ka kuka watarana zai saka dariya,Ya Allah ka ci gaba da yi mana zaɓi na alkhairi ka haɗa mu da mutanen kirki ka nesanta mu da na banza, Allah ka sa mu zamanto mutanen kirki a wajen mutane ka tsare mu cin amanar wanda suka yarda damu Ameeen...* Page 19: Yau Salma tun asuba ta tashi da matsanancin ciwon kai da mara, in da Talle hankalin shi ya tashi ba kadan ba,tsoron shi bai wuce a ce yau 'Yar mutane ta mutu a hannun shi ba,shi dai tun farko dama ba wani son ta yake ba kyan ta da dirin tane ya rud'e shi,ko ba komai ya more ta yanda ya kamata,yanzu haka ya k'yalla ido ya hango wata shi yasa ya fara tara 'yan kud'ad'en da zai yaudaro ta, ba zai yu kuwa ya kashe kud'in sa a jinyar Salma ba, tun da dama wa'adi ya debar mata lokaci na cika zai auna ta tai gaba,zaune yake a kujerar shi ta aiki a farfajiyar gidan ya lula duniyar tunani a hankali ya fara magana ya na fad'in, "Anya zan iya jiran lokacin da na ɗebar mata ya cika kuwa ? kawai bari Alhj ya fita nan dai da Kano na auna ta gida, nace sai nazo ba shikenan ba ta zauna ta jira ni idan auren da nake nema be samu ba na d'akko ta kan nan ta ji sauqi, idan kuma auren ya yuwu na aika mata takardar ta kowa ya huta, ko kuma yanzu in na shiga na sallame ta a rabu gaba ɗaya," Ya na nan zaune ya na magana da kan shi ya ji Alhjn na kiran shi, da gudu ya fita, ya je ya durqusa ya gaida Alhaji sannan ya ce "Gani Alhaji," Alhaji ya ce, " To ga wannan a kula da gida, ni zan tafi wannan karon zan ɗan kwana biyu gaskiya a gida ban dawo ba, dan kasan na faɗa maka amarya ta ta samu qaruwar d'iya mace, so ina ganin zan ɗan jima kaɗan fiye da yanda aka saba, a kula da gida, kar na dawo na ji shigen labaran dana saba ji, ba zamu kwashe da kyau ba Talle" Gyada kai yake kamar qadangare alamun ya ji gargad'in uban gidan nashi,can qasan zuciyar shi kuwa Allah Allah kawai yake yi ya tafi shi kuma ya ɗauki mota ya kai Salma tasha ya dawo, kar ta mutu a hannun shi. " Allah ya kiyaye Oga ba zaka taɓa samun wani labari mara daɗi ba" D'aga kafad'a Alhj ya yi sannan ya ce, "Ruwan ka Talle kowa ya yi da kyau zai ga da kyau ai" Alhaji na fita Talle ya rufe gate ya koma d'akin da gudu,samu ya yi Salma ta dan samu dama ba kamar yanda ya barta ba, ta fito daga toilet da alama amai ta yi,cikin hanzari da d'aure fuska ya ce mata, " Ke haɗa kayan ki yau zaki je ganin gida" Cikin kad'uwa tare da murna, a gefe d'aya kuma kunya da tashin hankalin da wanne ido zata kalli su Juwairah da Mama Bilki ne suka mamaye ta, Uwa uba kuma Goggon ta, tace mata waye mijin ta idan ta je gida driver ne ko mai gadi? Zubewa ta yi a katifa cike da wani irin had'ad'd'un yanayi mabanbanta da suka cud'e mata, a hankali ta furta, " Nikam Sweet na fasa ba yanzu ba ka bari na murmure, sannan mu dan samu kuɗi, ko a haka zan tafi ganin gida, ai sai a zage ka a ce baka kula da ni"  "Ah ah a zage ki dai yo ni meye nawa a ciki? in zaki miqe ki miqe ki kwashi dan abinda zaki iya dan kin ga ni daga yanzu ma barin gidanan nan zan ko kin dawo ba ganina zaki yi ba nima na bar aiki anan daga yau, dan na kwashi rabona wajen Alhj, qauye zan koma, na ji da iyalina, kuma dai ba sanin Sunan qauyen mu ki kai ba, ba kuma ki san hanyar bama, dan haka in kin tafi ki manta da wani mai suna Talle, ko in ce Alhj Mansur da kika taba aura, ki manta kin sanni, sai dai in kin tashi tuna ni ki min godiya a ranki na sama maki hanyar zuwa ABUJA, harda qauyen ta ma, dan haka ga wannan" Takarda da kuɗi dubu goma cass ya miqa mata, a zaunen ta daskare, bata gaskata me yake faɗa mata ba sai da ta ji tsawar shi yana maimaita mata da kuma bata umarnin ta tashi su gudu dan kuwa tana b'ata masa lokaci zai fita ya gudu nashi waje shima, wanda qarya Talle yake mata ba inda zai gudu kawai sanin bata ko san sunan inda suke ba shi ya sa shi fad'in haka, baya son ta yi tinanin dawowa rayuwar shi kwata kwata. Miqewa ta yi da taimakon shi saboda wani irin jiri da tashin hankali da ta ji ya mamaye jin ta da ganin ta,nan take ciwon kan ta ya dawo sabo dal,da kyar ta samu natsuwa ta ɗan shige ta ta fara haɗa kayan ta a haka ta gama komai, ta kasa tambayar shi dalilin yi mata wannan wulaqancin, ta kasa cewa uffan saboda kalamai sun qauracewa bakin ta. Duddubawa ya yi duk abinda bata ɗauka ba ya ɗaukar mata yana bata a hannun ta ita kuma tana riqewa, idon ta a tsaye suke kuma hawaye na zuba, haka ya gama ya sata gaba ya kulle qofar ya dauki wata jaka dan tsabar ya raina mata wayo ta zaci tare zasu bar gidan, mota suka ɗauka ya saka ta suka bar gidan kifa kanya ta yi a cinyar ta ta yi ta kuka. Su na isa ta tasha ya yi parking a bakin tashar ya sauke ta ya yi gaba ko waiwaye bai yi ba balle ya ga a halin da ya bar ta,a haka ta samu ta isa cikin tashar bata ko ganin gaban ta da kyau tsabar hawayen da ke zuba a idanun ta, in da ta ji ana kiran Kano ! Kano ! nan ta isa ta shiga wata mota sauran mutum biyu ta cika ma,tana shiga wata arniya ta shiga itama, sunayen su aka basu su rubuta, amma ita ta yi shiru ta kasa rubutawa, kuɗi suka buqata ta miqa masu dika kud'in hannun ta ba tare da tace komai ba,ko da ya qirgi iya kud'in shi sai ya miqa mata sauran ta nade a hannun ta,ta jingina kan ta da jikin gilashin motar ta dinga raira kuka mai sauti ba tare da ta damu da kallo da qusqus ɗin da mutane ke ta yi akan ta ba, a haka har mota ta cika. Har suka isa kano Salma bata daina zubda hawaye ba, adaidaita sahu ta ɗauka ya kaita har gida ta miqa masa kuɗi ta yi gaba shi kuma ya na neman canjin da zai bata,har ta yi gaba ya bita ya miqa mata a hannun ta, ya tafi yana fad'in, " Allah ya kyauta" Shiga gidan su ta yi babu ko sallama, Goggo Sarai tana zaune a kujerar da ke kallon duk wani mai shiga da fita a gidan tana kad'a qafa akan kujera, hango Salma a wani mawuyacin hali da ta yi sai da Goggon ta kusa tintsirawa qasa tsabar tashin hankali,da gudun ta zani na warwarewa tana gyarawa ta taro ta ta na fad'in, " Lafiya Salma,Me nake gani haka? Ina mijin naki? Daga wace qasar kuka dawo haka? Fashi aka yi muku a hanyar ku ta shigowa Nigeria? " Haka Goggo Sarai ta dinga jerawa Salma tambayoyin nan amma bata samu amsa ko ɗaya ba, d'aki ta ja ta suka shiga sai waige waige take da fatan babu wanda ya gan su, har Mama Bilki zata fita dan jin Goggo Sarai ta kira Sunan Salma amma Baba ya riqe ta, ya ce, "Gimbiya bassu ni na je,yanzu da kin je sai abun ya koma tashin hankali kuma da. cewa za ta yi gulmace ta kai ki ba komai ba" " To Baban su Allah ya jiyar da mu alkairi" " Ameen" Fita ya yi ya isa dakin, zaune Salma take a gefen gado idon ta na kallon waje ɗaya kawai ko qiftawa bata yi, kukan kuma ya tsaya cak kamar wadda aka cire wa batiri, tambayar duniya Goggo ta yi mata amma taqi magana, Goggo banda kuka ba abinda take yi a haka Baba ya shiga ya tadda su, cikin damuwa da jimanta lamarin Baba ya ce, "Subhanallahi, me ke faruwa ne haka sarauta ki ka tasa yarinya a gaba kina ta kuka, Ke Salma ki yi mana bayani me akayi miki, ina mijin naki kuma? Daga ina kika fito a haka?" Da jin murya da kalaman Baba Baballiya sai Salma ta saki wani kuka mai cin rai, nan take ta dakko takardar da Talle ya bata ta miqawa Abban nata, dan yanzu haushin Goggo take ji sosai, ta dalilin ta ta shiga wannan halin quncin da qananan shekarun ta tinda ai duk ita ce bata basu tarbiyya mai kyau ba, uban su kuma na son ya basu ta musu hudubar shed'an ta hana su saurara, wannan wace irin rayuwa ce haka, Salati suka ji Baba ya sake ya aje takardar ya zauna tare da dafe kan shi,cikin kuka Goggo Sarai ta ce, " Malam me ya faru? Ku sanar dani ko hankalina ya kwanta dan Allah" Cikin dakiya Baba ya kafe Goggo Sarai da idanun sa da suka yi jajawur saboda b'acin rai sannan ya ce mata, "Mijin nata ne na can garin ABUJAN YA SAKE TA SAKI UKU" Ɗora hannu a ka Goggo Sarai ta yi ta kurma uban ihu kamar wata qaura,sannan ta miqe a harzuqe ta hau jibgar Salma tana fad'in, " Shegiyar yarinya me kika masa ya sakon ke, yanzu gashi kin yi mana asara, mutumin da ya fitar dake qasar waje Kuke shaqatawar ku cikin jin daɗin rayuwa, ki zalunce ni ki zalunci kan ki Salma ki sa ya sako ki, da dukkan alamu ma ciki ne da ke, amma shine tsabar baqin ciki ba zaki bar ɗan ki ya taso cikin jin daɗi ba sai da ki ka yi abinda ya maki sakin kare dangi" kalmar ciki ne da ita da Goggo ta yi ba qaramin razana Salma ya yi ba,nan take ta sake tabbatar da Talle ya yi mata illa ba kaɗan ba,dan ko giyar wake ta sha a yanda ta san waye Talle ba ma zata yi gigin ta haihu ta kai dan ta qauyen su ba wanda shi yake ganin bata san Sunan qauyen ba amma a iya watannin da ta yi har qauyukan kusa da su ta san Sunan su, ai kamar yanda yace sun rabu ta manta da shi hakan za ta yi,ture hannun Goggo ta yi a jikin ta ta je gaban Baban ta ta durqusa ta ce, " Babana ka yafe min, ka ji tausayi na ba dan halayyata mummuna da na yi a baya ba, ka duba girman Allah da soyayyar ɗa da iyayen shi ka yafe min duk abinda na aikata mara kyau a baya, ka tausaya ma abinda ke ciki na in ya tabbata ina dauke da cikin kenan, kar ka yi fushi da mu, ka bamu wajen zama a

Chapter 13 of 25