Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi za a zauna a yi magana wato gidan su Jabeer,a cikin motar Alhaji Salihu suka tafi,bayan sun isa ne suka samu Yaya Balarabe na gida, tabarma suka sa a waje suka zauna,Baba ya yiwa Yaya Balarabe bayanin komai,bayan jimanta wannan mummunan lamari tare da yi wa Alhaji Kalla addu'ar samun rahamar Allah sai ya amince da mijin Suwaiba zai zauna a shagon gidan har Allah yasa su Jabeer su koma Abuja sai su kuma su zauna a bangaren su Jabeer ɗin,Baba godiya ya yi wa yayan nashi, ya koma gida ya bar Alhaji Salihi a nan,Alhaji salihu ya musu godiya sosai musamman da Yaya Balarabe yace zai fara koya masa ilimi na addini dan ya kula yana da qarancin shi, godiya ya yi sosai kamar zai kwanta a wajen dan kuwa ba karamar alfarma da karramawa suka yi masa ba. Nafee Baban su Jabeer ya kira ta gyara shagon, aka shimfida masa wata yaloluwar katifa da wankakken zanin gado da pillow, sai sallaya da buta da ruwa mai kyau a bokiti rufaffe saboda ko zai buqata, Abban su yace in yana buqatar zagawa zai iya shigowa cikin gidan, godiya ya yi ta musu kamar zai kwanta, zuciyar shi cike da tausayin rayuwar da zai koma, sannan qasan ta kuma cike da murnar ganar da shi gaskiya da Allah yayi. ************** Yau kwana tara kenan da haihuwar Juwairah har an yi suna an gama lafiya kuma bikin suna ya qayatar, dan kuwa Jabeer ya yi qoqari sosai, ga akwati nan biyu da ya yi ma mai jego da jaririya, ɗaya babba ɗaya qarami, gobe suke son komawa Abuja, dan wajen aikin na buqatar Jabeer ɗin da gaggawa, sun gama kwasar duk wani abu da zasu dauka mai amfani sun gama, kayan d'akin ta kuma zata barwa Addan nata da mijin ta tun da ba su da shi, a haka taje gida ta yi wa Saudat ta'aziyya ta kuma yi wa iyayen ta sallama, Juwairiyyah ta sha kuka kamar wadda za ai wa auren dole,da kyar suka lallashe ta sai da taga Jabeer ran shi ya fara ɓaci da kukan ta sannan ta hakura, sun dawo gida bayan Isha'i,Nafee ma kan ta ta sha kuka har sai da idon ta ya kumbura saboda kukan rabuwa da bestyn ta kuma yar uwar ta, sannan matar yayan ta da ke son ta,Innarmu ma ba a barta a baya ba wajen matse kwalla,tana qara bawa Juwairah hakurin zaman da suka yi a baya tare da fad'in, "Ashe ma ita duniyar ba matabbata bace, ba abinda ke tabbata sai iKon Allah, gashi dai mutuwa bata raba mu ba amma zaman a tare ya kare, Allah ya sa ku koma sabon wajen a sa'a,Allah ya yi maku albarka" Baba Balarabe ma jikin shi duk ya yi sanyin saboda rabuwa da Jabeer da Juwairah,musamman Juwairiyya dan kuwa itan yarinya ce mai shiga rai matuqa,gashi ta na da kyawawan halaye da kuma iya zama da mutane, a haka aka kwana gidan kowa da abinda ke ran shi. Washegari da sassafe Jabeer da Juwairah ɗauke da Abrar suka fito suka shiga sabuwar motar Jabeer zasu tafi Abuja, Nafee ta riqe hannun Juwairah tana matsar kwalla, Jabeer ne yace, " My little sis ki yi hakuri,kwana nawa ne zamu qara dawowa, ranar fa da Saudat zata fita takaba ranar za a fara bikin ki ko kin manta ne? dan haka ki kwantar da hankalin ki, sannan wataqila ma Salma ta haihu kafin nan zamu zo, ki yi hakuri kin ji," Hawayen ta ta share, ta yi masu addu'ar tafiya lafiya da samun sa'a da nasara a rayuwar su baki ɗaya,Innarmu da Abbah Balarabe ma haka, sai mijin Adda Suwaiba dake gefe shima yana masu fatan alkairi, motar ya tayar suka yi gaba cike da kewar juna. Salihu kuwa gaba ɗaya ya canja,fatar shi ta qara duhu saboda dama shi baƙi ne, irin baƙin nan mai haske kaɗan, Alhaji Salihu na da kyan shi dai-dai misali,tumbin nan na shi ya ragu,hakan ya ba wa kyan shi damar sake fitowa, ganin yanda ya faɗa ne ya bawa Baba Balarabe tausayi,a qasan ran shi kuma yana ayyana ko zasu fara zuwa kasuwa tare ne wajen gwanjon su da shi ne? Bayan su Innarmu sun shiga gida ne ya same shi ya masa wannan tayin, cikin jin daɗi ya amsa da zai yi ko meye in dai halal ne ba damuwa, qasa ya yi da murya da kan shi sannan ya ce, "To Baba ai ban da jari kuma" " kar ka ji komai akwai jari a wajena ,ko da dubu biyar zaka iya farawa mu gani" Godiya ya yi ta zubawa sosai har Baba Balarabe yaga dai ba zata qare ba, dariya ya yi ya shige cikin gidan ya bar shi a nan, rayuwa kenan Alhaji Salihu da ko masu aikin gidan shi albashin su daga dubu ashirin ne zuwa sama yau shi ne zai kafa jari da dubu biyar. Ba jimawa Suwaiba da mijin ta suka tare a sashen su Juwairiyyah,kuma kasuwanci ba laifi wataran a samu ya siyar da kayan dika har ma a samu ribar da ta kan kai dubu uku zuwa huɗu, wataran kuma ribar ba ta kaiwa haka, a haka ɗin shi da ya fara da jarin dubu biyar yanzu ya kai dubu goma,duk abinda aka samu na Saman ya yi wa iyalin sa hidima da su watarana ma har da su Innarmu. Salma da Huwaila kuwa kusan a tare suka haihu, Salma ta haifi Yaran ta biyu mata masu matuqar kama da iya kyawawa, ita kuma Huwaila ta haifi yaro namiji mai kama da Bangis sak, kwana tara ne a tsakanin su ,dan kuwa yaran Salma sun girmi na Huwaila. Ranar suna kuwa Salma sai da ta yi taron suna dangi suka zo suka taya ta murna da sanya albarka har ta samu kyauttuka,dan kuwa da dama an zata haihuwa ta dawo yi gida,ba wanda ya san mijin ta ya sake ta sai daga baya magana ta yaɗu a dangi, wasu suka yi mata fatan samun wanda ya fi Talle wasu kuma na Allah ya ƙara ai ga auren miji ɗan ABUJA inda ya Kaita ta zama bazawara da qananan shekarun ta. Bangaren Huwaila kuwa komai qayau-qayau su ka yi shi, ga habaici da suke sha wajen 'yan gulmar da ke zuwar masu barka da kuma wanda suka je sunan, yaron Huwaila ya ci suna Bilal,haka rayuwa ta yi ta juyawa wadannan bayin Allah da daɗi ba daɗi. Ta bangaren gidan Baba Balarabe kuwa al'amuran gidan su ya bunqasa da arziqi dan Salihu ya shiga gwanjo a sa'a, yanzu har dila biyu yake iya bud'ewa wata rana ma har uku,haka gidan Yah Jabeer ɗin Juwairere suma arziqi ya wadatu a gidan su dai-dai misali abun dai sai godiya ga Allah, gidan su da suka koma a Abuja mai kyau da shi d'aki uku ne da dinning area sai babban parlour mai ɗauke da manyan kujeru da kayan kallo, yarinyar ta sai wayo take yi cikin koshin lafiya. **************************** Shirye-shiryen bikin Nafeesa ne ya kankama gadan-gadan,wanda ya kama sauran kwana uku saudat ta fita daga takaba, a yau din ne su Juwairah da Jabeer tare da diyar su Abrar za su zo baza su koma ba har sai an gama bikin Nafeesa, Jabeer ba qaramin qoqari ya yi ba a yan watanni huɗun nan, shi ya yi wa Nafee kayan d'aki Abbah Balarabe ya bada kuɗi su Suwaibah suka siyo mata kayan kitchen da wasu abubuwan buqatar. Jabeer ya kashe kuɗi sosai dan ita Juwairah ma ba ta sani wasu abubuwan da yake yi ba, tinani take yi in sun je ina zasu sauka? Tunda bangaren su yanzu Adda Suwaiba ne a ciki da mijin ta,bata da masaniyar d'aki daya da bandaki da palour madaidaicin da Jabeer ya masu a filin dake gefen gidan su wanda yake kamar kango ne a da, sai yar tsakar gida madaidaiciya, ba laifi ginin ya yi kyau,sai wajen azahar suka iso, ta ce wa Jabeer ya fara kai ta ta gaida su Innarmu idan yaso sai ya maida ta gidan su ta kwana,shiru ya mata ya na murmushi har suka isa gidan nasu,wajen Innarmu ta shiga cike da kewar ta, Nafee da gudu ta je ta rungume ta suka hau murnar yaushe gamo..... *Juwaireren mama na gayyatar dukkan fans din novel din 'YAN ABUJA zuwa wajen bikin Nafeesa, Allah ya bada ikon zuwa ameen😂*[04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 31: Hankalin Talle yanzu ya koma kan Salma, dan kuwa ya san a yanzu ta haife abinda ke cikin ta,ya na sane da cewar ciki gare ta shi ne dalilin da ya sa tai ta wannan ciwon kafin su rabu, fatan shi yanzu ta yafe masa tunda ya san babu wata maganar kome a tsakanin su duba da cewa saki uku ya yi mata a lokaci d'aya,bayan haka ma wannan rayuwar da yake ciki ba irin ta Salma ke da buri ba sam ko a baya ta aure shi ne saboda kwad'ayi da tunanin shi wani ne, addu'a Talle ya d'aga kan shi ya na yi; " Ya Allah ka bata ikon yafe min a duk sanda na bayyana a gaban ta ina mai neman yafiyar ta ko ban samu zuwa ba mutuwa ta riske ni Allah ka wakilci ce ni a zuciyar Salma ta yafe min abinda na yi mata" " Haba Talle, sai yaushe zaka daina zubda hawaye ne? Na baka shawara mu kama akuya ɗaya mu siyar ka samu na mota dana guzuri ka je wajen yarinyar nan ka nemi yafiyar ta, amma ka kafe kace a'a to ta yaya kud'in zasu samu idan baka samar wa kan ka su ba? In aka siyar nima ba sai na samu na kafa wani jarin ba ai ya fi zaman nan da muke yi da ni da kai ba abin yi ko? Koda nera ɗari biyu zuwa ɗari uku yau muke samu a rana a matsayin riba ai zamu toshe wata kafar, balle nasan zamu samu ma yafi haka,ni yanzu babban tashin hankali na be wuce b'atan Haule ba, duk da ina kyautata zaton gajiya ta yi da halayen mu ta gudu wajen mahaifiyar ta, amma abun na matuqar damuna" " Dan ta zancen Haule kwantar da hankalin ki ta na wajen mahaifiyar ta mantawa na yi ban sanar da ke ba,da ta je ma da kyar suka amshe ta, amma yanzu baki ga gatan da take sha ba in ji abokina da ya min hanyar auren babar ta, yana ta mun godiyar kyautawa da na yi na barta tazo ta ga mahaifiyar ta" " Allah sarki, a gaskiya mun tafka babban kuskure a rayuwar mu Allah ya bamu ikon gyarawa, me zai hana ka samu a islamiyyar malam Sallau kaga ana karatu kyauta, awa biyu zamu bayar a kwana uku kawai, dan akwai jahilci mai tarin yawa a rayuwar mu sai mun kawar da shi ibadar tamu ma za ta karb'u,ka ga kai kuma sai ka na zuwa ta bayan isha'i kai da Yaya" "Gaskiya kin kawo shawara mai kyau dan abubuwan da muka tafka da da ilimi a tattare damu musamman na addini da bamu yi ba, Allah ya yafe mana" " Ameen" "Ni wai ina yarinyar nan Hawaila? Ki taran su har Baban gidan zuwa anjima za ai maganar auren ta, gobe juma'a, suna da d'aki a bangaren su da katifa dan haka ban ga dalilin da zai sa ta ci gaba da zama a gaban mu ba a zo ana maimaita 'yar gidan jiya,ko ba gaskiya ba, kin ga a hankali muka samu sai mu yi mata kayan d'aki kamar kowacce 'ya" " Wannan ma shawara ce mai kyau, ai duk yanda za a rufa wa juna asiri yi za a yi, tin da ga yaron su nan Umar Allah ya bayar gwanda ai auren gobe komai ya wuce,Allah ya sanya mana albarka dikkan mu, ya yafe mana" " Ameen na gode maki da ki ka canja halaye daga munana zuwa kyawawa, yanzu kyaun ki ma ya fitowa matata, nima ina fatan kin ji daɗin canjawa ta?" Talle ya fada yana mai matsawa kusa da ita, ita kuma tana wani sissine kai, wai kunya take ji. "Na ji daɗi sosai mana Talle na, nan gaba ma swatyn nima zan dinga kiran ka irin yanda kk cewa Salame, ko mata kawai ake kira da haka?" Dariya Talle ya kwashe da ita da ya gane inda ta dosa ( Sweety) shine abinda take son cewa. "Ana Kiran mace da namiji Sweety, ina godiya ni kuma daga yau sai na koma ce miki honey" ******************************* Duk wani gyaran jiki da ya kamata a yi wa amarya Juwairiyya ta gama da wannan fannin,da yamma za a tafi dinner kowa ya sha gayu an yi kyau gwanin ban sha'awa, ba a cika wa Nafee irin kwalliyar nan ta yanzu da ake yi ba har a kasa gane asalin fuskar mutum, sai aka yi mata sassauqa saboda ta riga da ta sha kyaran jikin da ya fito da kyaun ta, ( aikin Juwaireren mama kenan) ba qaramin kyau ta yi ba, sun so kwarai a aske mata gira a yi shaping ɗin ta amma Juwaireren mama ta hana, domin kuwa hakan haramun ne, tinda akwai abinda ake yi a danyi dabara kamar an yi shaping ɗin ba zata bari a aikata sab'on Allah ba da Sunan kwalliya, aiko nan take Adda Suwai nonoless ta qara gyara Nafeen ta na gasgata Juwairiyyah tare da shigar mata faɗan da qawayen Nafeen ke yi akan ai yanzu haka ake ya yi ya kamata Itama ranar auren ta ta tafi da zamani, bayan Suwaibah ta gama gyara mata kwalliyar ta ne kowa ya tabbatar da lallai ado da kwalliya ba sai an sab'i Allah ba yake kyau,mutum zai iya kula da Fatar shi da asalin halittar da Allah ya yi masa kuma ya yi kyau ba sai ya yi bleaching ba ko saka gashin doki ko aske gira da qara farce ba. Nafeesan ta yi matuqar yin kyau, haka ma Saudat da Salma maman yan biyu ba a bar su a baya ba wajen cakarewa su da yaran su, ga wani irin qamshi mai daɗi da sanyi dake tashi a jikin Yara mai ni'ima kowa son ɗaukan su yake yi, Shamsiyya, Innarmu, Goggo Sarai Mama Bilki da sauran dangi sun sha kwalliya suma irin ta zamani,sai dai fa angwaye sun yi sanarwar ba za a je da iyaye ba, nan fa ran Goggo Sarai ya ɓaci ta tashi fidda hali, "Ni dai gaskiya ko su Bilki ba zasu ba ni a tafi dani, dan nasan irin wajejen nan akwai k'walama ba zai yu na ci kwalliya haka ba na zauna a gida" Wani kallo Suwaiba ta yi mata sannan ta ce mata, " Haba Goggo har zuwa yaushe zaki daina wannan halayen ne dan Allah?" Yashe baki Goggo Sarai ta yi cike da jin kunya ta ce, " 'Yannan wasa dama nake ina ni ina zuwa wajen matasa, ai irin wannan hidima sai ku" Can qasan ranta kuwa ba qaramin son zuwa dinner take yi ba,haka ta hakura ta danne ta tashi ta fita wajen masu soyawa amarya ka ji da za a tafi kai ta gidan miji da shi,saboda hanyar akwai nisa sosai, kuma a cikin garar ta Jabeer yace a saka harda kajin shine dalilin da ya sa ake soya su da yawa,ta na isa wajen ta danna hannu a kan wanda aka soya ta ɗauki yanka ɗaya ta yaga cikin tsinkewar yawu tace; "Wannan biki ana abin arziqi da yawa, in ban ci a wajen dinner din ba na ci anan ai," Kad'a kai kawai Salma ta yi da ta ji me take faɗa, mai hali baya fasa hali sai dai ya lafa kawai,in dai abun nashi ya motsa sai ya yi yake jin daɗi. Wajen dinner ya qayatu da ado, angon Nafeesa Shima na da kyan shi dai-dai shi, sai suka fito kamar wasu wata da zara dan kyau,tun da su Salma suka isa wajen dinner mazaje ke ta binta da kallo, wasu ma har magana suke yi mata saboda yanda ta ɗauki hankulan su,yaran ta kuwa su na wajen Suwaiba nonoless, Salman sai ta fito kamar wata budurwa ba mai jego ba, Saudat ma ta yi kyau mai ban sha'awa, abokan ango da suke zaune kusa da ango ne wasu daga cikin su suka qura ma su Salma ido kamar su sace su su gudu da su, ana tsaka da rawa da shagalin biki ne samarin suka taso wanda da gani babu tambaya alamu sun nuna gidan su ɗaya,saboda tsananin kamannin da suke da shi, Sallama suka yi wa su Salma da ke manne da juna su na rawa a gefe dai-dai hanyar fita daga hall ɗin,juyawa suka yi a tare suka amsa da karfi suma saboda samarin su ji muryar su da kyau. Nuni suka yi wa su Saudat da wajen zama mai ɗaukan mutum shida amma ba mutane akai saboda duk ana wajen rawa,ba musu Salma ta yi gaba saurayi ɗaya ya bi bayan ta suka zauna,a gefe kuwa Addah Suwaibah ce da Juwaireren Mama suna hango abinda ke faruwa, Saudat kuwa jikin ta rawa ya kama yi a zuciyar ta ta na tinowa da Kalla, ɗayan ne yace mata, " Haba sarauniyar kyawawan duniya ina zaki je kuma bayan ga sarkin ki ya iso domin ya ɗauke ki ya kai ki masarautar masoya?" Murmushin da bata shirya wa zuwan shi bane ya k'wace mata,amma can qasan zuciyar ta tunanin tsohon mijin ta ne danqare da zuciyar ta, ji take kamar ta zura da gudu. Jiki a sanyaye ta bi bayan shi suka zauna suma a kujerun da ke wajen tana ta wasa da hanun ta, ɗayan ne yace ma Salma, " Angel da farko ni suna na Ibrahim aboki ne ga ango, wannan kuma yaya na ne farouq, tin da kuka zauna anan muka sa idon mu ana ku mu ka ji ba zamu iya barin ku ku tafi ba ba tare da mun isar da manufar mu ba a gare ku, dan da dikkan alamu ku yan uwan amarya ne duba da kamannin da kuke da ita," Cikin nuna kulawa Salma ta kalle shi dan itama sai ta ji ya yi mata ta ce, " Eh mu yayun ta ne, amma bayin Allah ba ku sammu ba, baku san ya rayuwar mu take ba, kawai sai ku fara isar da manufar ku a gare mu? Gashi wajen ma duk hayaniya da kid'a ya yi yawa, to da farko dai ku duba kuga waɗan can yaran na hannun yayata ku kalle su da kyau sai mu ci gaba da maganar da za a yi" Duba Yaran suka yi suka ga kyawawan yara, sannan suka dawo da kallon su suka ce, "Masha Allah ga yara kuwa kyawawa qannen ku ne?" Murmushi Salma da Saudat suka yi a tare sannan Salma ta ci gaba da magana dan bata son abinda zai karya masu zuciya gaba ɗayan su, tunda har suka kasa haƙuri su samu wajen da ya fi wannan natsuwa su bayyana soyayyar su to fa ba za su bari abu ya yi nisa ba suma,gwanda a yi maganar gaskiya da gaskiya ,Salma ta kula dikkan su samari ne basu taɓa yin aure ba ma,cikin nuna masu gaskiyar da ke zuciyar ta ta ce, " Waɗancan 'yan biyun nawa ne ni na haife su ba qannen mu bane, sai dai ni aure na ya mutu, ita kuma wannan yayar tawa mijin ta Allah ya yi masa rasuwa ne har ma ta fita a takaba," Cike da mamaki da tausaya wa a gare su suke kallon su,amma dai duk yanda aka yi mijin daya saki Salma na da tab'in hankali ko kuma shafar aljanu, hauka ne kawai zai sa kana da mace kamar wannan ka sake ta, nan take suka yi wa Saudat ta'aziyya sannan farouq yace, " A gaskiya ni har yanzu ina ciki kai fa ɗan uwa? Dan ba zan taba barin wannan tsaleliyar ta wuce ni ba na yi asara, domin da dikkan alamu akwai tarbiyya awajen ku" A sannan ne Saudat ta yi magana ta ce, " Yanzu dai yanda za a yi ku yi hakuri zuwa har a gama biki da komai da komai sai kuje can gida ku samu mahaifin mu ku gabatar da kan ku,duk abinda mahaifin mu ya ce maku shikenan da shi za mu yi amfani dikan mu" Godiya suka yi sosai kuma suka qara tabbatar da tarbiyyar su, karbar No wayar su suka yi tare da yi masu sallama suka tafi. Adda Suwaiba ce ta dawo kusa da su ta zauna ita da Juwairah, suna zama Salma ta labarta masu duk abinda ya faru, suna cikin addu'ar neman zabin Allah Hussainar Salma ta hau kuka, kuka take sosai har Salma ta rude kamar za ta yi kukan itama,miqo masu hannu suka ga anyi ta sama; "Hey baby how are you?" Ibrahim ne ya karɓe ta ya na kallon kyan yarinyar ta yi kama sak da maman ta,jijjiga ta ya yi ya tafi wajen yayan shi suna ta hira da sauran abokai ko damuwa da yanda take zuba masa yawu a jiki bai yi ba,haka abokan ango suka dinga ɗaukan ta, daga wannan ya karbe ta sai wannan ya karbe ta, daga qarshe Ibrahim ya karɓe ta ya sanya ta a kafad'ar shi har ta yi bacci,cike da yabawa abinda ya yi Salma da yan uwan ta ke kallon shi. An gama dinner za a tafi gida ne ya iso ya miqa wa Salma ita, godiya ta yi ta masa har sai da yace, "Ya kike man godiya ne haka? A gani na dan uba ya kula da yar shi ai ba wani abu bane ba ko?" Murmushin jin daɗi ta yi idon ta cike da kwalla ta gyad'a kai ta yi gaba, bayan sun fita ne suka fuskanci basu da abin hawa ga dare ya yi dama a adaidaita sahu suka zo, su Farouq ne suka zo a motocin su suka parker a gaban su salma,sun so matuqa Juwairiyyah ta bi su su sauke ta a gida amma ta qi ta ce Yah Jabeer na nan tafe ɗaukar ta. Tafiyar su da wasu 'yan mintinan da ba za su wuce biyar ba kuwa ya iso ya ɗauke ta, a hanyar su ta komawa gida ne take sanar da shi labari mai daɗi game da samarin da suka nuna suna son su Salma. Murmushi ya yi tare da fatan alkairi ya ce, "Allah dai ya kaimu gida lafiya baki ji yanda na gaji ba sai kace ni ne angon wanka nake so na yi da ruwa mai dumi ko na warware" Murmushin Itama ta mayar masa sannan tace, "Hmmm Abu Abrar kenan na gane in da ka dosa, to yau kam dole a min hakuri dan kuwa ni kaina a mugun gajiye nake" Dariya Jabeer ya yi yace, "To za mu gani dai Allah ya kaimu gidan lafiya, ni da na san halin ki ai sai dai na ba wa wani labari ki 'yar mama" Jabeer ya kashe mata ido ɗaya ya ci gaba da murmushi ya na tuqin shi, kauda kai ta yi tana murmushin itama a ran ta ta na fatan Allah ya kai su gida lafiya dan kuwa ita ɗin ma ta yi kewar shi....... [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 33: Washe gari angwaye zasu zo dan tafiya da amaren su da kan su tsabar zumud'i, dan kuwa ji suke yi kamar sun auri sabbin 'yan mata duba da yanayin kyan jiki da su Salma ke da shi babu mai cewa sun taɓa yin aure idan ba an sanar da mutum ba, su Goggo Karima ana nan sune yan rakiya zuwa Abuja. Da wuri suka shirya dan su shiga kasuwa Juwairiyyah ce ta dage sai sun je sun yi siyayyar lefen su saudat ɗin da mazan su suka damqa masu kud'ad'en a hannun su anan garin kano,sannan su sai wasu abubuwan amfanin gida dan kuwa a ɗan zaman da ta yi a Abuja har yanzu bata gano inda ake Saida wasu abubuwan da take buqata ba,akwatuna masu kyau da sha'awa suka

Chapter 22 of 25