Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ABUJA  💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 28: Duk qarfin ta ta tattara ta damqe hannayen Jabeer ta ci gaba da nishi, har babyn da ke cikin ta ta samu damar sako kai cikin duniyar tamu,cike da murna da farin ciki jabeer ya qanqame Juwairiyyah a Jikin shi ya na jera mata sannu ba iyaka, sai share mata zufar goshin ta yake yi,a hankali ya sumbaci kuncin ta,Innarmu na ganin haka ta haɗe fuska ta na ɗaukar yarinyar ta kauda kai irin na mutanen da masu kunyar nan ta ce, " Oh yarannan ba ku jin kunya ta sam, Jabeeru kalli yanda ka yi jagab da hawaye duk dan tausayin matar ka,ita kanta mai haihuwar ma ta yi jarumta ko kuka ba ta yi ba sai kai" Cikin dakewa da son boye halin da ya shiga na farin ciki bayan kukan tausayin matar shi ya ce wa Innarmu, " A gaskiya Innarmu ba abinda zan ce dake sai dai na ce kawai ubangiji ya miki rahama, ya sanya min ke a aljanna madaukakiya, ke kuma Juwairah Allah ya maki albarka, ya biya maki dukkan buqatun ki, ni Jabeer yau na qara alqawarin riqe amanar ki har qarshen rayuwata" kallon Innarmu ya sake yi ya ce, " Innarmu da ace mazaje suna shiga d'akin haihuwa da matan su su na ganin yanda mata ke k'ok'ari wajen fito da wata sabuwar rayuwar zuwa duniya tabbas da an rage mace-macen aure da wulaqanta mata, da maza sun daraja mata fiye da qima, Innarmu duba fa kiga irin wahalar da yarinyar nan ta sha, dan Allah Innarmu idan na taɓa aikata maki wani laifi ko na b'ata maki rai ba tare da na sani ba ko kuma na yi da ganganci ki yafe min, na yi alqawari daga yau zan zamo daga cikin yara masu biyayya," Nan take jikin Innarmu ya yi sanyi, dan kuwa tabbas ta san iyaye mata suna qoqari,bamu da abinda za mu yi musu da ya wuce muyi ta masu addu'a da qoqarin yi masu biyayya,a hankali Innarmu ta ce, " Jabeeru duk abinda ka fada gaskiya ne,kai d'a ne mai biyayya da kyautata wa ga iyayen shi da ma duk wanda Allah ya haɗa ka zama da shi, ba abinda ka yi min a rayuwa mara kyau da zan iya tunawa balle har na riqe a raina,kyautatawa ce kullum a tsakanin mu da kai Jabeeru, Allah ya yi muku albarka ya raya jinjirar nan cikin imani,ka ga yanzu yarinyar nan tana ta bushe wa, tashi ka je sashe na ka saka ganyen magaryar nan a ruwan zafin da na saka dan na yi wanka su tafasa tare saboda ya fidda dattin jikin yarinyar sosai,oh ni Hansai Jabeeru kazo ka dauki 'yar ma mana ka riqe matar ka kamar wani zai ɗauke ta magana nake yi amma hankalin ka na wajen matar ka" Dariya ya yi yana sosa qeya ya gyarama Juwairah zama sosai yanda zata ji daɗi sannan ya isa gaban Innarmu, kallon yarinyar yake da tsantsar soyayya irin ta uba zuwa ga 'yar shi, wani irin kyau ya ga Allah ya yi mata na musamman, wannan kyaun daga ina ta samo shi? juyawa ya yi ya samo amsar tambayar shi wajen juwairah, murmushi ya mata sannan yace, "Tabbas na samu amsar tambaya a fuskar ki, kyaun yarinyar nan duk naki ne Honey" Innarmu ce ta yatsuna fuska cikin rashin gane ne ya ce ta ce, "Meye wata Hamee ni ta shi ka dora ruwan ka dawo ko kuma ka gyara ruqon ta naje na kwaso na bangare na dana zuba d'azu dan na yi wanka,riqe ta na je na dawo" Gyara wa babyn zaman kanta ta yi dake a lankwashe a hannun Jabeer da bai iya ɗaukan jinjiraye ba sannan ta fice tana fad'in , "Yara ido ya bushe ba kunya, zamani duk ya canja iko sai lillahi ji yanda yaron nan ke abu kamar a fim din hindiya" Zuwa ta yi sashen ta ta zuba ganyen magaryar a ruwan ya ci gaba da tafasa sannan ta kwashe ta qara wani,ta taho da shi sashen Juwairiyyah,yarinyar ta Karb'a a hannun Juwairiyyah da Jabeer yake wa tsiya ta fara wanke wa, mamaki ne ya ishe ta ganin Jabeer na gyara Juwairah kamar ya san ya ake kula  da mai jego, "Sai wani tsokanar ta ka ke yi ta ji zuwa na ta na so ta ajiye yarinya, ba gwanda ita ba da sauran kunyar ta a Jikin ta,kai ni fa sai na bar maku wajen ku ku qarata, wannan rashin kunya har ina, wa ya koya maka yanda ake ma mai jego ni Hansai" Cikin dariya Jabeer yace, " Innarmu na koya ne a wani littafin anti-natal ɗin ta da na ke karanta wa lokaci zuwa lokaci, littafai ne da suka qunshi yanda ake renon ciki da haihuwa da kuma yaran kansu, da irin taimakon da uba zai ba uwa in ta haihu, ina fatan kin fahimta, baya daga cikin kyautatawa namiji ya bar mace ta yi ta wahala ita ɗaya bayan tare suka samar da abinda aka haifa ko za a haifa ɗin, yana daga cikin karamci da kyautatawa tare da soyayya namiji ya shiga dumu-dumu a yi komai da shi, hakan na qara ma ma'aurata fahimtar juna da so da tausayi, sai kiga aure ya dad'e ba fad'a ba yaji bare kai qarar miji gida" Innarmu gyada kai kawai take yi dan kuwa gaskiya Jabeer ya faɗa ,  amma fa gaskiya ita kunya suke bata, shiru ta yi kawai bata ce komai ba, Jabeer ne ya kammala gyara wajen ya tallabe Juwairah suka fita tsakar gida, kujera ya bata ta zauna ya fita wajen Innar mu ya deb'o ruwan zafi, ya shigo da shi cikin babban bokiti, ya raba biyu, ɗaya a babbar roba ɗaya na wanka, kai mata ya yi ya koma d'aki ya dakko ruwan kal fari ya zuba kamar murfi uku a ruwan da zata zauna din, ya je ya fara tayata wankan,cike da shagwab'a Juwairiyyah ta ce, " Yah Jabeer dan Allah ka bari zan iya yi da kai na,Innarmu fa na nan, ta yi shiru ta kyale mu ne  amma na san ba zata so ganin hakan ba,na san akwai fahimta a tsakanin mu da ita amma wani lokacin yawan zaqewar ka zai iya jawo min qiyayya wadda bana fata, ka je zan iya da kai na na gode, ina son ka da yawa" " ke ba abinda zata gani kar mu b'ata lokaci, maza bari na gama maki kan ta gama da Babyn mu ki ka sani watarana ba a gaban su Zaki haihu ba za mu yi rayuwa a inda daga ni sai ke kawai kin ga dole ai ni zan yi maki ko?, ya kamata ma muje asibiti a duba ki duk da na ji Innarmu ta ce ba ki samu wata matsala ba" A haka Jabeer ya kashe bakin ta da zance ya mata wanka ta zauna a ruwan ta ji daɗi sosai, ya koma ya qaro wani ya saka ta a ciki, ya qara ruwan kal din a ciki. ( ma'ul kal, wato ruwan kal yana wanke datti shima sosai, ya fidda qarni da warin HQ sannan yana matse mace, ya gyara ta, sai dai ba a so in ba kamar yanzu da aka haihu ba a cika amfani da shi, da shi da bagaruwa, baya-baya ake son amfani da su, dan kar su yi illa ma wajen, kuma ana son in ana amfani da su a yawaita cin fruits da veges da kuma shan zuma mai kyau da zam-zam, dan su zama sun saukar da ni'ima) Bayan sun gama wankan ne Jabeer ya fito daga band'akin sai ga Nafee ta dawo daga makaranta, shigowa ta yi da gudun ta, sakamakon kukan baby da ta jiyo, ai suna ido huɗu da Juwairah ta kwasa da gudu ta isa wajen ta ta rungume tana murna ta ce, "Sannu matar Yayah Allah ya qara maki lafiya ya raya mana abinda muka samu" "Ameen Nafee sannu da dawowa" Jabeer ne cikin salon wasa ya ce wa Nafee, "To malama sake ta haka ta ji da kanta" Sakin ta ta yi ta na dariya, bakin ya qi rufuwa kamar gonar audiga, d'aki Jabeer ya wuce ya bar su tsaye Juwairiyyah na takawa a hankali suna hira da Nafee za su shiga d'aki,su na nan tsaye Jabeer ya fito hannun shi riqe da zanin haihuwar ya aje mahaifar a cikin leda zai wanke zanin,Nafee ce ta yi sauri ta yarda jakar  ta a qasa ta ajiye mayafin ta a igiyar shanya tai wajen Jabeer zata karbe wankin, "Yah Jabeer barmun na wanke ni ban yi komai ba ai" " A'a sis basshi yanzu kika dawo daga school bana son ki wahal da kanki, kayan jini ne ke kuma baki son su suna sa ki jiri dan haka ki bari zanyi, bayan haka kin san Innarmu ta tsani wanki a kaf aikace-aikace ni me nake yi da ba zan wanke ba? Yanzu dai ita  Juwaireren Mama ta yi me wuyar da ta haifo mana queen of beauties, shiga ki ga inda ake kyau yarinya barakallah Masha Allahu" Ta na jin haka ta bar su a wajen ta yi d'aki dan kuwa sai ta ji ta qara kwadaita da ta ga yarinyar, tana isa ta zube gwaraf gaban Innarmu,Innarmu kuwa ta gyara yarinyar ta sha kwalli rambad'ad'au, ta yi matuqar kyau, idon ta bude fes kamar haihuwar sati, cikin zumud'i ta amshe ta tana yi mata addu'a Juwairah ce ta shigo da sallama d'aki,Idon ta na sauka akan jinjirar Itama ta hau tasbihi ga Allah tana matuqar godiya daya sauke ta lafiya ya bata Kyakkyawar yarinya kamar wannan, Mama Bilki ta sha addu'a yau a bakin Juwairah, kallon gefen ido take yi wa yarinyar saboda kunya,a ranta take ayyana; 'Ikon Allah ke nan yanzu da wanne ido zani gida na kalli Mama da Baba tinda dama dai su sun qi zuwa gidan nan saboda kunya, wai yau ni Juwairiyya ce na haihu" Shafa cikin ta tayi da ya yi mata babba kamar bata haihu ba ga nankarwa da ta ji yayi rad'o-rad'o, murmushi ta yi ta qara gode Allah, nan da nan ta hau shiri ta d'akko man kad'en ta ta shafe cikin da shi sosai ta mulke shi da man har sai da ta ji ta daina jin maiqon shi sosai a hannun ta, murmushi ta yi dan tunawa da yanda cikin nata ya sha gashi wajen Yah Jabeer don jinin ya samu fita ita kan ta mamakin yanda duk ya iya abubuwan nan take yi duk da ta san yana karanta littafan ta na rainon ciki amma bata zaci ya riqe komai akan shi haka ba, bayan ta gama murje cikin ne ta kwalama Nafee kira dan ta zo ta d'aure mata cikin, zuwa ta yi ko ta tamke mata shi tsam, kayan ta ta saka atamfa riga da zani ya mata kyau sosai, kalar atamfar ruwan kwai ce dika, sannan ta feshe jikin ta da turarika masu daɗin qashi ta fito parlour zata zauna,a dai-dai wannan lokacin Jabeer ya gama komai ya yi wanka shima ya shigo, sannu ta yi masa da addu'ar Allah ya saka masa da alkairi, ya yi murmushi yace, " Is my duty love, so ki daina damun kan ki da yi min godiya, amma fa bacci ya kamata ki yi bayan kin ci abinci yanzu" Murmushi ta yi masa wanda  tasan yana biyan komai a wajen Yayan nata, kad'a kai ya yi alamar zamu haɗu ne, ya wuce d'aki dan ya shirya. Ya na gamawa ya fita palour ya tadda su dika a zaune Juwairiyyah ta gama shan kunu da tuwon da ya sha man shanu, gyaran murya ya yi ya kalli Abban su ya gaida shi, dan kuwa yana shiryawa ya shigo shima a yi murnar zuwan jikar tasu da shi,Abbah ya yi ma yarinya addu'a, Nafee na ta masu tsiya shi da Innarmu akan tsufa ya qara kama su sun zama kakanni,miqa wa Jabeer babyn Abban su ya yi shima ya yi mata addu'a, sannan ya faɗi sunan da za a ana kiran ta da shi, wato Hafsat sunan Innarmu kenan, Innar mu har kukan daɗi sai da ta yi dan jin hakan, sannan yace ma Juwairah, "To ai sai ku nema mata sunan ku na yan gayu da na san dole sai kun saka mata," Nafee ce ta kalli Juwairah tace, "Matar yaya sai ki bamu suna ko?" Juwairah murmushi ta yi sannan ta shiga tunani,daga baya tace, " Na saka mata Abrar, wato mai tsoron Allah" " Oh ni Hansai yanzu ina ni ina iya fad'an wata Abras fisabillahi" Dariya suka kwashe da ita har  Abbah, Abban ne yace, "Haba Innarsu, yanzu Abrah ɗin ne zai gagare ki?" Haba me zasu yi in ba dariya ba dan shima kan shi Abbah ya kwafsa, gyaran murya Jabeer ya yi ya fara magana cikin tsantsar farin ciki da annashuwa tare da son sanar da su abin farin cikin  da ya same su yace, " Abba, Innarmu,Juwaireren Mama, and my little sis Nafeesa, ina mai farin cikin sanar daku ci gaban da ya same mu, a yau kuma a d'azu dana dawo na zo da labari me dad'i na samun aikin da na yi a NNPC na can Abuja in da suka ban gida dake kusa da gidan man da zan yi aikin, a unguwar Jabi har ma da mota, sun dauke ni a matsayin Manager na wajen gaba ɗaya, sanan kuma ɓangaren kasuwanci na yau na biya ta kasuwa, Saifullahi dana kan bari ya min jiran wajen in bana nan ya d'akko min kud'ad'e masu tarin yawa, da kuma wasu jakunkunan da na saro ba su iso ba daga malaysia , to a yau suka iso, har wasu yan kasuwan sun yi sari ma, shine ya bani kud'in da suka kai dubu dari biyu da talatin cif a hannuna, nan take na bashi talatin ɗin nayo gida da sauran gasu" Juye-juye ya fara yi yaga ina ya wurga ledar da yazo da ita, dubawa ya yi ya hango ta can hanyar shigowa inda ya yar ya iso wajen matar shi mai naquda, kasa kudin ya yi kashi biyu, sannan ya qara kasa kashi daya biyu, miqawa Abban shi ya yi kashi ɗaya, sai kuma ya ɗauki dubu goma ya bawa Nafeesa sauran dubu arba'in ya bawa Innarmu, yace gashi su sa mai albarka,Abbah ne ya ce, " Lallai wannan yarinya ta zama mabudin alkairi a gidannan, muna ma Allah godiya, nayi murna da farin ciki sosai na jin wannan abun alkairin daya same mu, Allah ya taya ka ruqo da gaskiya da amana, Allah ya qaro maka arziqi mai yawa mai albarka," Amsawa suka yi gaba ɗaya da, " Ameen" Innarmu kuwa kukan daɗi take ta yi tin da aka fara maganar, dan bata taba tunanin riqe kuɗi rabin wannan bama a lokaci d'aya dan tasan ba ta dasu, bata bawa kowa ajiya  ba,yau gashi an mallaka mata su,shi ya sanya take kukan farin ciki, ta ma kasa magana sai kukan murna take na ɗaukakar da Allah ya yi wa d'an ta a lokaci d'aya,Nafeesan ce ta ce, " Innarmu ki bar yin kuka, addu'a da sanya albarkar ki Yah Jabeer ya roqa a wajen ki" Juwairah ma sai murmushi take zabgawa a lokacin da ta sake kurbar shayin da Nafee ta hada mata mai kauri da d'umi, innarmu kuwa share hawayen ta ta yi tace, " Jabeeru ba abinda zance sai dai nace Allah ya qara maka albarka ninkin ba ninkin akan wadda ya maka, ina alfahari da kai a matsayin ka na d'a na, Allah ya kare min kai daga sharrin maqiya" Amsawa suka yi dikka, Nafeema ba a barta a baya ba wajen taya murna da godiya balle mai jego Juwairiyyah,kiran sallah ne ya karad'e wajen tare da duhun da ya bayyana hakan ya nuna masu cewar magrib ta yi, miqewa suka yi bayan sun gabatar da addu'a, suka yi alwala mazan suka tafi sallah matan suka yi a gida Juwairiyyah kuwa d'aki ta je ta kwanta, ana cewa ana bacci bayan an haihun ita dai gata nan ido biyu, bata sani ba ko dan ta na cikin matsanancin farin cikin samun aikin da Yah Jabeer ya yi ne ya sa ta kasa bacci? bayan ya dawo ne ya d'akko kaza a akurkin su, ya yanka guda biyu ya kaiwa Innarmu ya ce a dafa wa Juwairiyya,Nafeesa ce tace ita za ta yi dan ta san yanda take son ta. D'auka ta yi ta koma ɓangaren Juwairah ta d'akko ridin da suka daka tare , da madarar shanun dake aje a randar sanyi,sannan ta dakko kayan qamshin da suka niqo harda minannas a ciki ta gyara kayan miya ta soya sama sama ta tsaida ruwan dahuwar kazar kasancewar ta ta Hausa to fa dole sai an qara ruwa kafin ta dahu da kyau. Zuba wannan kayayyakin kamshin ta yi ta zuba kazar da ta gyara ta wanke ta yayyanka a ciki, amma banda madarar ta ajiye ta sai naman ya dahu sannan zata zuba, sai da farfesun ya dahu sosai sannan ta zuba madarar shanun, tana tafasa ɗaya biyu ta sauke ta juye  a mazubi Mai kyau ta kaima Juwairah mai jego. Godiya ta yi mata Jabeer na shigowa ya zauna zai saka hannu, Nafee ta riqe ta ce, " A'a Yah ga tamu can wajen Innar mu wannan nata ne, ita fa ta haihu ba kai ba, sannan na zuba mata maganin basir a wannan ka jira tamu" Dariya ya yi sosai har yana kama ciki ya ce, " Yarinya ni za ki yi wa qaryar? zaki yi bayani ne kice kawai Nafeesa na hada maki kayan da zaki warke da wuri to da kyau Allah ya baki lafiya,ke kuma me maganin basir ki dena qaryar,banqi ba in an hanani ci saboda ita ta haihu ta yi wahala ya kamata taci ta yi qat, amma batun ace wani maganin basir ne ma bai taso ba, in haka ne ai na fita basir ɗin nifa namiji ne zaman kasuwa waje ɗaya wasa ne?" Dariya suka dinga yi dikan su, Wajen jaririyar ya je ya ɗauke ta yana kallon ta yana mata wasa kamar gane wa take, wani farin ciki yake ji a ran shi, nan take ya hau yi mata hotuna, yana gamawa ya danna kiran Baban su Suwaiba dan  tun da aka yi haihuwar ya kira sau biyu bata shiga ba, sai ya sa a ran shi ko ba wuta an kai caji ne, shi yasa ya sake gwadawa. Su kuwa a can gidan Baba Baballiya duk suna zaune a tsakar gida gaba ɗayan su har da Goggo Sarai, duk da ba wani sake mata kowa ya yi ba sosai amma sun rage gudun ta, sallama ya yi ya sanar da shi haihuwar, cike da murna kowa ke amsar wayar suna gaisawa, Juwairah kuwa sam taqi karb'ar wayar wai kunya take ji, dariya suke ta mata Suwaiba tace sai gobe zasu zo, dik da mamakin da ke a zuqatan Jabeer da Juwairah har ma da Nafee Hakan bai hana su suma sakewa da ita ba suka yi ta hira. Bayan sun gana ne Juwairah ta ɗauki pillow da aka kawo mata dan ta zauna ta jefawa Jabeer, tana buga qafa cike da shagwab'a ta ce, "Ni baka fad'an zaka kira su ba kawai sai dai naji kana waya da Baba, kuma wai Babana ka ke iya fad'awa na haihu, wayyo ni Allah da wanne idon yanzu zan kalle su?" "Da idon da ki ke kallo na yanzu mana" A haka Juwairiyyah ta miqe da Baby Abrar suka wuce d'aki dan ta kwanta ta shayar da ita Itama ta ɗan rintsa dan kuwa yanzu ne take jin bacci na ratsa idanun ta......... [04/08, 11:01 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA. 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 29: Alhaji Kalla gaba ɗaya ya tattare hankalin shi ya mayar kan Alhaji Salihu da ke yi masa wata maganar da yake jin ba mai yiwuwa bace a gare shi,cikin nuna kafiya akan ra'ayin shi ya ce wa Alhaji salihun, " kai nifa ba qungiyar da zan bari gaskiya, habaawaa yo me ma aka yi da maza? har yanzu fa da quriciyar mu Salihu ko hamsin bamu rufa ba, akwai sauran rayuwa a gaban mu na tuba, me zai sa kuma mu katse rayuwar mu tun kafin mu more ta?" "Hmmmm Kalla kenan, kai abokina ne wanda na ke matuqar so saboda tare mu ka taso da kai tun mu na yara,kar ka manta dika iyayen mu da wasu daga cikin 'yan uwan mu mun bada su ta wannan harka, kana ganin zunubin bai isa haka ba? Tin da ba yanda za ai mu dawo da su? Ka duba fa in bamu tuba ba yanzu kowanne lokaci mutuwa na iya zuwa, ita bata sallama bare qwanqwasa qofa in......" Cikin haɗe fuska da taurin kai irin na mutane marasa rabon shiriya Alhaji kallah ya d'aga wa Alhaji Salihu hannu tare da fad'in, "Malam dakata, yau kuma da abin da kazo kenan? i am very sorry to disappoint you my friend, cos i am not ganna buy this shit, akan me ina tsaka da jin daɗin rayuwa ta kace na koma rayuwar talauci, bayan kasan sharad'in fita daga qunyiya mai da duk abinda ka mallaka ne dai-dai da allura ba a yarda ka ajiye ba ballantana ba ma za su ajiyu ba wuta ce zata cinye su ko ka manta me ya samu sauran mutanen da suka bijire wa qungiya? Idan na bar qungiyar me na tanada wanda ba daga qungiya bane kuma ka ke ganin ba zai kare ba ballantana na yi rayuwa mai daɗi ko bayan babu ƙungiyar? Haka siddan mad'alaqan kasa na koma almajirin qarfi da yaji? kan kuma ka fita kar ka manta sai an yi asiran rufe maka tinanin ka na gidan Oga da qungiya gaba ɗaya wanda a kallah zai kai nan da sati ɗaya, kai ka san dan mun riga da an bamu ɗaukaka a qungiya ne yasa akai mana wannann alfarmar da qananan yan qungiya ne kashe ka za ai ko da tinanin nan ka yi, ni dai ina nan kai kuma Allah ya taimaka ka fita lafiya, amma ka sani sisina ba zan taimaka maka da shi ba in ka talauce,amma kuma abotar mu na nan har yauma ta nade" Baza babbar rigar shi ya yi ya fice ya bar Alhj Salihu da tinani, wata zuciyar na kwad'aita mai ci gaba da rayuwar hutu, ɗaya ban garen na nuna mai illar hakan, in ya ci gaba da zama ɗan qungiya ya kai soyayyar Suwaiba kuma inaa? da ace ya rasa abar son shi gwara ya hakura da qungiyar nan Allah zai kawo mai wata hanyar, miqewa ya yi dan shima ya bar wajen, yana tashi kuwa wayar shi ta hau ringing, dubawa ya yi yaga kiran Alhj Kallah, tsaki ya yi kamar ba zai ɗauka ba, dan abin da ya masa d'azu ya sosa ran shi sosai, amma sai ya lallashi zuciyar shi ya d'aga dan yaji ko ya canja ra'yi ne zasu fita tare, yana d'agawa ya ji wata muryar daban da bai san ta waye ba, cikin mamaki ya ce, "Waye kai ina mai wayar?" "Ranka ya dad'e mai wayar Allah ya masa cikawa,yanzunnan ya samu hatsari da wata babbar mota hakan ya yi sanadiyyar fashewar kan shi nan take sannann qafar shi ta dama ta karye" Komawa ya yi Saman kujerar da yake kai ya dafe kan shi tare da Kiran Sunan Allah cike da jin tsoron Allah na sake huda naman jiki da b'argon shi ya furta. "Innalillahi wa inna ilaihirra ji'un" Itace kalmar da yake maimaitawa a bakin shi,qarar message ne ya maida shi cikin natsuwar shi,cikin tashin hanakali ya duba sai ya ga address ɗin inda Kalla ya yi hatsari aka turo masa, kamar wanda aka ma allurar bacci haka ya miqe ya na jin wani jiri ya na d'iban shi,tafe yake yana fad'in, " Allah na tuba ka yafeni, Allah ka gafarta min ni Salihu daga yau na yi alqawarin tuba daga zunubaina na daina harkar nan ko zan rasa raina ne" kuka yake yi sosai kamar zai shid'e a haka ya kai zuwa inda motar shi take ya tada ita ya yi inda aka kwatanta masa, wayar shi ce ta qara ringing ya miqa hannu ya ɗauka,Sunan

Chapter 20 of 25