masallacin har an yi magariba makararru ya samu aka ja su jam'i suka yi sallar,lokacin isha'i na yi aka kira sallah aka tada sallah,ana idarwa kuwa Talle ya miqe ya koma gida,tafe yake cikin sauri fakam fakam ya qarasa tsakiyar gidan nashi,Marka ya yi wa sallama ya faɗa dakin Salma wadda ya tadda ta sha gayu sosai da yan kayan da take da su, ta dan fesa turaren ta da ya kusa qarewa dan kale ma take yi, yana shiga d'aga sama Talle ya yi yana juyi da ita,ita ko sai dariya take yi, sumbatar ta ya fara aika mata da shi tana mayat mashi da martani, suna tsaka da wasannin su ya katse ta ya ce,
"Ni fa yunwa nake ji, mu fara cin abinci kannan yarannan sun yi bacci sai mu dora daga inda muka tsaya, dan yau kam sai yanda hali ya yi,"
Cikin jin daɗi Salma ta saki dariyar murna,a haka ta tafi ta dakko masu abinci suna ci suna hira Salma cikin shagwab'a ta ce,
" Babe me yasa ka amshen waya ta ne, tinda nazo yanzu kusan wata bakwai da wasu kwanaki ban ji muryar kowa nawa ba"
Wani mugun kallo Talle ya buga mata daya sa cikin ta kad'awa, dan dai Tallen Tallen ne fa kar ta ga ya na biye mata ta kawo masa raini, sunkuyar da kan ta ta yi qasa cikin kwantar da kai tace,
" Ka yi hakuri ba zan sake zancen ba dama na yi kewar Goggo da Baba ne"
Wasu hawaye ne masu zafi suka sauka a fuskar ta, hannu tasa ta share su kamar ba ita ta yi kuka ba, ta dakko cokalin abincin ta kai bakin shi, amsa ya yi ya dan sake rai kadan, a haka har suka gama, Huwaila da Jummala kamar yanda suka saba sun fita zance amma zancen da su Badamasi ne, ana can ana latse2 da tabe2 da tsotse2, ita kuma Marka sun gama shirya duk abinda ya kamata cikin duhun nan ita da Yayan Talle, da zata wuce ne ya daki mazaunan ta ta baya, juyo wa ta yi ta hau masifa,
" kaifa yayan nan jarababbe ne, kwana dayan nan da mukai ba a tare ba duk ka zama kamar ka dauke ni mu gudu, to ina sanar da kai ka iya takun ka, kasan Talle ya fika wayo ko dan ba soko bane kamar ka, zai iya gane wa"
kad'a mata kai ya yi alamar zai kiyaye, shigewa tai d'akin ta,Salma amarya ana can ana soyewa ita da me gida, Sun yi nisa ba sa jin kira, komai ya kankama, suna cikin raya daren nasu cike da kewar juna ne su ka ji motsi ana sand'a, gaba daya Talle ya cika wajen na su da gurnanin shi, Marka kamar ta mutu dan kishi da baqin cikin da ke cin ranta, sai kaiwa da komowa take a d'akin, tana jin motsin Itama tace,
" Alhamdu lilLAAHi ƙarshen tika tiki tak"
Da sauri ta manna kan ta a jikin qofa dan ta ji ya za a kaya,
" Salame bude qofar mana na iso, me kike yi ne baki riga kin buɗe ba sai na zo ina bugawa sun ji kamar rannan, so kike wannan shegiyar kishiyar taki mai baqin tsiya ta ji ta leqo irin na rannan, Salame ya dai na ji ki shiru, dan Allah ki yi sauri mana ki buɗe muyi mu gama na tafi a matse na zo yau"
Talle da ya gama jin komai wani shaqa ya yi ma Salma da idon ta ya firfito waje tsabar mamakin abinda kunnuwan ta ke jiyo mata,da sauri ya sake ta ya sauka ,ya saka wando shi jin da ya yi ba a daina taba qofar ba,kuma ba a daina kiran Salma ba, ai ko mai maganar da ya leqa ta bular da yake hango su yaga yana tahowa da gudu ya kwasa ya yi waje, yana fitowa da hanzari yaga an gilma da gudun tsiya komawa ya yi d'akin, dan ya san laifin ta ne koma wanene ya zo da ace bata bada qofa ba babu mai zuwar masa kwartanci.
Kafin ya koma d'akin Salma ta zura rigar ta tana ta kukan wannan masifa da ake neman jefa ta a ciki,nan take ta furta kalmar
" Marka"
Dafe kan ta ta yi, da ta sani da bata tsuye ta ba ta bar su da halin su, gashi yanzu ta jawa kanta masifa da bala'i,Talle na isa gaban Salma ya hau dukan ta ko ta ina,it a kuwa sai ihu take tana fad'in ya tsaya yaji me ya faru ita ba ta da laifi, inaaa dukan ta yake tin tana kuka tana bashi hakuri sai da ta koma ajiyar zuciya, sai da ya tabbatar ta kasa motsa ko da ya tsan ta ne sannan ya fita zuwa d'akin Marka, tana bude qofar ta Talle ya talle fuskar ta da wani azababben mari sannan ya ce,
" Dan uban ki kin san hakan na faruwa ashe kika munafurce ni baki gaya min ba ko da ta wayar yarannan ne su Bangis ? Ga shi kwarton na ta ya ce kin gansu da Idon ki"
kuma ta fara yi sosai dan kuwa marin ya yi matuqar shigar ta,cikin shassheqar kuka ta ce,
" Inna faɗa maka ba yarda za ka yi ba cewa zaka yi kishi ne ke damu na shi yasa nace Allah ya nuna maka da kan ka wataran ka gani ba gashi yanzu ka gani ba"
Kwafa ya yi yace ,
"Ai kuwa zata ci uban ta na san maganin ta ai,"
komawa ya yi ya kwanta a dakin markan, nan take kuwa Marka ta manne masa ba ko kunya da nadamar sharrin da ta qullawa salma,matsawa ta yi da zummar kwanciya gefen shi, da dabara ta kwanta a bayan shi wata ajiyar zuciya ya sake da sauri ya ja ta jikin shi, nan take Marka ta sanya murmushin samun nasara,ina ganin haka na fita kofar dakin na ja kujera 'yar tsuguno na zauna dan na jira masoyan biyu.
Ina nan zaune bacci ya fara ɗauka ta na jiyo kukan Marka ta na ba wa Talle haƙuri akan ya kyale ta ta gaji, karshe dai Saida Marka ta gwammace ba tayi wa Salma mugunta ba a ranar, Talle kuwa ce mata ya yi,
" Dake da iya duk sai kunci uban ku, zan maganin kowa a cikin ku, ki min shiru ko na farfasa maki baki"
Tare da kaiwa bakin nata duka, dip tai bata qara kokawa ba kuwa sai kukan zuci, da sassafe ya shirya ya daukar wa Salma kayan ta suka wuce cikin garin Abuja, Marka kamar ta mutu dan haushi da baqin ciki, ita da ta so a barta ta zauna da su dan ta rama abinda ta yi mata kawai ai a d'auke ta a Kai ta cikin birni? kai wannan abin haushi da yawa yake.
Sun isa Cikin garin Abuja lafiya da rana wajejen 12pm, gidan Alhjn shi ya kaita, wannan karon ma sun qara yin tafiya, amma wannan karon d'akin shi na gidan na mai gadi nan ya kaita ya ajiye ta ya yi ficewar shi yawon shi, miqewa ta yi fuska ta kumbure mata ta yi sintim da kyar take gani,a haka ta jingina da gini ta rungume guiwowin ta tana kuka mai ban tausayi
A rana irin ta yau Salma ta yi nadamar zuwan ta ABUJA, wato in baka iya kama barawo ba shi ya kama ka, wannan shine ya faru tsakanin ta da su Marka.
***************************
A can garin Kano kuwa jabeer ne ya yi sallama ya shiga gidan su fuskar shi cike da fara'a kamar wanda ya yi tsintuwar dimond.........
*Too Yan Jabeerun Innarmu da Juwaireren mama minana kakawa murna hakan ga?"
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 ' YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 14:
Itama sallahr ta samu waje ta tada, domin dama da ta yi wanka kafin ta fito daga band'akin ta yi alwala ta saboda idan lokacin sallah ya kamata a ko Ina ne za ta yi sallar ta, cike da murna Juwairiyyah ke kallon Babyn Shamsiyya da ke goye a bayan ta ta na sallahr.
Bayan sun idar da sallar ne suka hau gaishe gaishe, Juwairah ta karɓi Farha ta na mata wasa tare da tsokanar Shamsiyya ta na fad'in Farha fa ta isa yaye,cikin sauke ajiyar zuciya Shamsiyyah ta ce,
"Hmmm ke dai bari sis ai maganar yayen ma na daga cikin abinda na ke son ki bani shawara akai sis, ya zanyi na gyara jiki na musamman kirji na dan kuwa nan da sati uku nake son yaye ta, nono gaba daya ya koma slipas ba kyaun gani duk ya zube ya barni da fata, gashi duk nankarwa ta b'ata shi, hatta da ciki na ma nankarwar ce tun ta haihuwar farhan haihuwa, dan ma Allah ya sa Abban su mutum ne mai kawaici baya son ya b'ata raina amma ba namijin da zai so hakan, dan kafin su zube su yamushe ɗin nan na kula yana matuqar son wajen,"
"Sister kin ko kawo kuka wajen maganin ki" Inji Nafeesah da ke sauraron hirar tasu.
Dariya suka saka gaba dayan su Juwairah tace,
" Nafee kina ban matsayin da bai kai nawa ba fa"
" Ba haka bane dear a gaskiya kina burge ni wajen hangen nesa na san ba komai bane ya jawo haka sai mai da hankali da ki ka yi kika koya wajen Mama Biliki a fa gani muke kamar wahala take baki duk da kasancewar ki a matsayin 'yarta, komai a gidan fa da ke ki ke yi, to yanzu gashi yana maki amfani"
"Haka ne kam, dan ko ni a da wataran sai na ji na gaji bana son taimaka mata, data fahimci haka bata mun faɗa amsa take tayi takan ce jiki da jini,Allah dai ya karawa iyayen mu lafiya da imani..... to tanzu dai kin san me zaki yi yar uwa? Da farko ki nemo wadannan alkama,Fatar shinkafa,dankalin Hausa,(a wanke a fere a yanka a shanya ya bushe a inuwa) aya, gyad'a mai bargo,kantu/rid'i, plantain ki busar da ita,jar dawa,hulba,dabino ki same su gaba daya ki gyara ki kai a niqa maki ki dinga damawa da kunu ki na saka madara ki na sha, sannan za ki iya haɗawa ki sha ko ba madara, idan kuma mai haɗe haɗen magunguna ki ke so,to ki nemo wadannan magungunan a wajen masu maganin mata ko maganin Hausa sai ki haɗa da wadancan abinciccikan da na lissafa maki,ga abubuwan kamar haka, NONON KURCIYA, GANYEN BAFULATANA, GADALIN NONO, su ne abubuwan da Zaki nema, sai kuna na gaba,mai sauqi kuma yana yi sosai shima, wanda zaki samu farar shinkafa ki wanke ki jiqa ta akai markade ta zama kamu, sai ki daka bagaruwa da ake tsarki da ita idan ta yi laushi sai ki ajiye idan Zaki dama kunun shinkafar sai ki tafasa cokali ɗaya a ruwan da Zaki dama kunun da ita ki sha da madara bayan jin gama damawar,ya na da kyau ki kiyaye ki na yi kullum ki na sha dan ba a son qiwa kiyi yau kiqi yi gobe, sannann ana son ayi kamar na wata ɗaya ne, zuwa yanda ki ke son qirjin naki ya tashi ya gyaru,sai kuma ki siyo man kwakwa Mai kyau ki haɗa da man hulba ki na shafawa a wajen ki yi massaging ma'ana ki ta murzawa har sai kin ji man ya shiga Fatar jiki ki sosai.
Ta bangaren nankarwa kuma ki samu man kad'e(wanda ake shafawa faso ko kaushi) sai kina shafawa a jikin ki da duk inda ta fito musamman ma a cikin naki da duk inda nankarwar ta fito maki, kinji wadannan a sauqaqe kenan"
" kaiiiii amma yar uwa na gode sosai, Allah ya saka miki da alkairi, Allah ya sauke ki lafiya, ya bamu bby mai albarka,"
Sunkuyar da kai ta yi a ranta ta amsa,
" Dalla in zaki amsa ki amsa ba ma son gulma karshe dai gaki nan ciki ne da ke dai"
" Sannu Nafeesa sarkin rashin kunya na gode dani kike wannan maganar tin da ni nayi abuna"
Cikin kad'uwa da tsoro Nafee ta hau zare ido ta na kallon ta inda maganar ta fito, gaba ɗaya ta tsorata ta kasa magana,su kuma dariya da kunya ce ta kama su musamman ma Juwairah ashe Yayan ta ya dawo su na ta surutu ba su ji ba gashi duk ya ji su.
Tashi ta yi ta ja labulen ta fita wajen shi kan ta a qasa ta ce,
" Sannu da zuwa mine"
"Yawwa princess, ya ki ke jin jikin naki yanzu?"
"To alhamdulillahi da sauqi gaskiya sosai,amma fa kaina yanajuyawa wani lokacin kuma cikina na motsawa sai na yi ta jin tsoro kuma abin na min daban haka"
"Ki yi ta hakuri kin ji princess u will be fine inshaa Allah, kawai hakurin nan naki dana san ki dashi zaki ci gaba zamu iya komai a tare Allah ya shige mana gaba"
Murmushi kawai ta yi dan kuwa ta amsa a ran ta shima murmuahin ya yi tare da sumbatar gefen kunnen ta a hankali,cikin sauri da kuma shagwab'a ta ce,
"Yayaaaahh"
Murmuahin ya sake yi mata sannan ya ce,
"Yanzu tinda shamsiyya ta zo bari na je wajen Innar mu na yi hirata nima"
Gaishe shi shamsiyya ta yi ya amsa tare da yi ma Farha wasa ya tafi, Nafeesa ta aika da abincin shi da komai da zai buqata can wajen Innarmu da kyar ta karba dan kunya da tsoron Yayan nata take ji ya kamata ta na surutu akan shi, dariya suka yi ta mata,bayan ta dawo ne ta ce,
"Laaa Matar Yayah na haɗa mana kwad'on zogalen da rama?"
Cikin tsinkewar yawu Juwairiyyah ta ce,
"Kaiii Nafee amma Allah ya yi miki albarka, dan Allah haɗa mana"
Ta shi ta yi suka fita tsakar gidan a tare Nafee na hadawa suna hira ta saka komai zata yanka albasa kenan, Juwairah ta dakatar da ita da sauri ta ce,
" Nafeesa kar ki sa mana albasa sai dai a naki dan mu muna da masu shinshinar bakunan mu kar su ji warin albasa na tashi,baki san ba a son in yamma ta yi mace ta ci albasa ba? Dan haka ki kiyaye ko dan gaba idan kin yi aure musamman idan miji na gida ki hakura da albasa kawai ,in ko kinci ki tabbatar kin wanke bakin ki tass yanda ba yanda za ai ya ji warin ta kuma ki qara da abinda zai qamsasa bakin naki"
Cikin farin ciki suka haɗa baki wajen gode mata,dan kuwa duk wanda ya zuba da ita sai ya qaru shamsiyya tace,
" Lallai zan yawaita zuwa gidannan don na samu sirrin da yasa baki taba faɗa da mijin ki ba kuma kk iya controlling din shi haka"
"Hhhh haba shamsiyya ai mace bata controlling miji sai dai ya zamar mata bawa a lokacin da itama ta zamar masa baiwa,shi kan shi na miji ba ya sanin ya zama maki bawa sai dai yaji mutane na cewa ya zama mijin hajiya, ko mijin kan tace, da sauran su, babban abinda ke jawo ma mace hakan kuwa shine, neman soyayyar Allah makadaici, in mace ta nemi soyayyar Allah, ta kuma samu, to tabbas zata samu soyayyar mijin ta cikin sauqi, wanda hakan ya yi qaranci a cikin mu mata, daga wajen boka sai dora rai akan maganin mata shi kaɗai ne maganin matsalar auren mu,bayan ba su kadai ne ke riqe zaman aure ba, wallahi in Allah ya so mace ta gama samun dacewar duniya da lahira, dan haka ni sirrina na zaman gidan aure shine son Allah da neman Allah ya so ni, saka soyayyar namiji a saman ta Allah shi ke saka mata fadawa halaka, daga zuwa wajen boka, zuwa zinace2, da dikkan abin da ya kauce hanya dan haka ina horon ku da neman soyayyar Allah kafin ta mazajen ku, sannan ba wai ba ma faɗa da junan mu bane, mu na yi, mun dai zaɓi soyayyar junan mu akan fushin mu ne shi yasa da mun yi fad'an muke shirya kammu ba wanda ya ji ko ya gani balle ya raba mu,"
Wani irin daɗi ne ke ratsa su dikkan su, musamman Jabeer da ya kawo kwanuka da niyyar yin alwala ya tafi masjid, godiya ya dinga yi wa Allah a zuciyar shi sosai da samun mace kamar Juwairah buta ya ɗauka ya fita ba tare da sun san ya shiga ba.
Suma sallahr la'asar suka yi, suka raka Shamsiyya ta hau abin hawa ta tafi, tana cike da farin cikin samun qawa kamar Juwairiyya.......
[18/07, 8:26 am] asiyahabibu93: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 16:
Hannayen shi biyu boye a bayan shi ya qarasa sashen na su da ke share kwal, yashin wajen har wani zanen tsintsiyar kwakwa ya yi gwanin sha'awa, duk da cikin da Juwairiyyah ke da shi bai sa ta zama qazama ba, sanda ba ta da lafiya ba za ta iya aiki ba sai ta zauna ta huta,da Jabeer ya kula shi kuma zai taya ta, lokacin da take da lafiya kuwa zata haɗe gidan dika ta yi masa gyara na musamman.
Juwairiyyah kuwa ta sowa ta yi da niyyar mishi sannu da zuwa yanda suka saba, sai taga ya maqale a jikin gini yana mata dariya, daga girar ta ɗaya ta yi tare da lumshe su cikin wani salon daukar hankali ta ce,
"Yayana me kake boyewa baka son na ganiiii"
Kwaikwayon yanda ta yi masa ya yi sannan ya ce mata,
"Matso kusa ki gani manaaa"
Matsawa ta yi, kusa da shi sosai idan ta matsa sai yace ta qara matsawa kusa kaɗan, haka ya dinga yi mata har sai da jikin ta ya zama gaba daya a nashi sannan ya fidda hanneyen shi ta bayan ta ya rungume ta ya sumbaci kuncin ta da goshin ta, sannan ya kama ta suka zauna, miqa mata leda ya yi ya tallabe fuskar shi yana kallon ta da murmushi, bude ledar ta yi itama tana murmushi tana kallon shi tana kuma kallon ledar, tana budewa taga wayar da zata kai ta dubu sha biyar a ledar, buɗe baki ta yi cikin murna da tsalle, ta dane shi tana ma sumbatar shi ko ta ina, kama ta yai ya riqe kafadun ta sannan ya ce,
" My princess ki nutsu kina girgiza mana baby, so kike ku ji ciwo?"
" Kaiiii amma mine na gode, na gode , na gode, Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya sama dukiyar ka albarka da rayuwar ka gaba ɗaya, Allah ya jiqan iyayen ka ya sa su cika da imani"
Hannu ya sanya a Saman labb'an ta ya ce,
" Shhhhhhh wai wannan godiya haka kamar na sai maki mota?"
"Hmmmm kai ka ga bai kai na yi wannan godiyar ba amma ni na san ya wuce haka ma, kai ma kasan ina da son waya, a matsayina na wacce ba ta taba riqewa ba yau na samu ai sai godiya ko, bayan haka ma macen kwarai dole ne ko tsinke mijin ta ya kawo ya bata ta nuna masa godiya da murnar ta akan abinda ya bata, in ba haka ba ta yiwa kanta baqin ciki dan gaba ba zai ji qwarin guiwar kawo mata komai ba"
" wannan haka yake macen kwarai, macen da zata zamo daga cikin matan aljanna in shaa Allah, Juwairah in dai ta dalilin miji ake shiga aljanna na maki alqawarin na yarje maki ina fatan Allah ya karb'i roqo na ya sanya min ke a aljannah"
Wasu irin hawaye ne masu dumi ke bin fuskar ta, wanda duk ya kalle ta a wannan lokacin ya san ta na cikin tsantsar farin ciki da nishadi, ga wani sabon son Jabeer ɗin da ke ratsa ta,a hankali ta furta,
" Yah Jabeer, na gode sosai Allah ya bar mu tare , mu je aljannar tare, domin kaima ka shiga cikin alqawarin Allah duk mai kyautata wa iyalin shi zai shiga aljanna, kana ɗaya daga cikin mazan da suke koyi da halayen Annabin rahama da sahabban shi na tabbata nima Allah zai amsa addu'a ta mu shiga aljannah a tare"
Haka suka yi ta yi ma junan su dad'ad'an kalamai wanda suka tabbatar da har abada ba za su taɓa manta wannan ran mai cike da farin ciki ba.
Kusan abinda aka rasa kenan a wannan zamanin,sai ka ga saurayi zai je zance ko ta waya ya yi ta yi wa budurwar shi dad'ad'an zance kafin a yi aure, amma da anyi auren aka yi kwanaki ko watanni ko shekara ɗaya zuwa biyu ya daina kenan, itama kuma haka sai a dawo kowa na dana sanin auren dan uwan shi, auren duk da muke ganin yana dad'ewa wallahi ba sa dai na yabon junan su kamar ranar suka fara haɗuwa, kowa a kullum yana son ya fidda sabon salon da zai faran ta ran ɗan uwan shi ne, dan haka mu ci gaba da nemawa juna farin ciki sai auren mu ya yi qarko, idan ki na yi wa mijin ki ko ka na yi wa matar ka abubuwan alkhairi da soyayya bata kulawa to da wato da hikima da dabara ake nuna masu sai suma su koya, duk taurin namiji ko mace kyautatawa na karkato da hankalin su ga junan su,haka su juwairiyya suka kwana suka hantse cike da farin ciki bata huta ba sai da ta dinga kiraye kirayen waya bayan ta nuna wa Innarmu ta sanya mata albarka.
****************************
Bayan kwana biyu da sanin cewa basu da mahaifa,Suwaiba da Saudat sun fara sabawa da wannan mummunan labarin da suka juyo wa kansu, Saudat ta fara neman dalilin da zai sa ta san me ne ne silar rashin haihuwar su, watarana Alhj Kalla zasu tafi meeting gidan Oga Zaks shi da abokin cin mushen shi,already har an kusan fara tattaunawar da za a yi mutane duk an hallara, a cikin waɗannan kwanakin Sudat ta fahimci ko su Alhj Ƙalla su waye kuma ne suke boye masu,sai dai ta qi gayawa Suwaiba dan ita akwai wauta, da ta sani zata fasa kowa ya san sun sani, idan haka ta faru ta tabbata za ta jawo masu masifa ne kawai, sai da ta gama jin gaba ɗaya hirar tasu ta sabon member da suka samu da zai shiga qungiyar tasu amma bai san location ba, take Alhj Kalla ya fara bashi address, Saudat kuwa na boye tana kwafewa, ta gama kenan zata tura a riga Alhj Kalla ya fito, gaban ta ne ya yi mummunar faduwa amma sai ta yi qoqari ta dake, ta ci gaba da jan rigar ta kamar tana gyaran rigar ne tun farko,kallon ta ya yi ya na murmushi ya ce mata,
" Ohhh mata kenan, daga kwalliya sai saka kayan ado, sai gyare2 kawai kar dai aga munin ku"
Dariya suka yi gaba dayan su,kafe ta ya yi da ido sannan a hankali ya furta,
"D'azu ina ta kiran ki ina palour ban ji kin amsa ba min ba"
Take ta gane wayo yake son yi mata,dan haka sai ta ce,
" Ayya ka yi haƙuri ban jiba bane Alhj na, ni da nake nan kana can,wataqila ma da ka daga murya dana jiyo ka, tinda kai ba zaka yi amfani da waya kana kirana ba , sai ka yi ta kira in ban ji ba kace na yi laifi"
Murmushi ya yi a ranshi ya tabbatar bata ji komai ba na daga hirar su,
"Ok shikenan je ki dakko min ruwa na sha anjima kaɗan zan fita"
Tashi ta yi tana kad'a jiki tana yauqi ta fita, tana isa kitchen ta qarasa da hanzari ta ciro takardar ta wulla a bayan fridge din dan ya fi kusa da ita, motsin shi ta ji ya biyo ta Shima kitchen ɗin, bude fridge ta yi kan ya qaraso ta dakko ruwan da cup, yana isowa tace masa,
"Hmmmm Alhj na kana sona da yawa na kula 'yan kwanakin nan kamar ka maidani rigar sawa ko ina zaka sai dani"
Murmushi ya yi yace,
" Ai ke kk koma haka shiyasa na koma hakan nima"
Sannan ya karbi cup din ya haɗe da hannun ta ya matse saida ta yi qara, ya zaro mata idon shi jajaye yace,
"Ki kiyayi bincike domin yana kai maiyin shi ga halaka"
" Bannnn......ban ganee...baaa? Me ka ke nufi?"
"Dalla malama rufe min baki, ji kike ban san kina bin waya ta ba? Ko bibiyar inda na fita? Ina nake zuwa me
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 25