Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ban ga komai ba indai gata ne da kulawa, daga gurin yan'uwan Ya Omri kamar wandanda basu taba samun haihuwa ba a dangi sai a a kaina haka suka rika kula ni kamar zasu dafa ni su cinye. Madara aka siyo ana hada musu da ita domin nonon baya isarsu bama kamar mazan da ba su iya sha kadan ba. Kayan barkar da Ya Omri yai min sai kace hauka ne ko kuma be san zafin kudi ba, ban cin wadanda nai ta samu gurin yan uwansa da kuma nawa dangin domin kowa ya ji na haifi yan uku sai yayi mamaki kuma ya zo ganinsu. Har abokansa ba a bari a baya na gurin bawa yaran kyauta da zuwa ganinsu ga su farare sol gwanin sha'awa ni kaina burgeni suke balle kuma ubansu da ya rasa inda zai dauka ya aje su wanda hakan shi yafi komai yi min dadi, at least na haifa wa wanda yasan darajar yaya kuma ya san kimata domin kullum a cikin tausayina yake da nuna min kauna. Ranar wata Monday akai suna wanda ya kama sati biyu kenan, dayan aka saka masa sunan mahaifin Ahmad wato Muhammad wanda akai wa lakabi da Sudais dayan kuma aka saka masa sunan mahaifin Hajiya Abubakar aka masa lakani da Shuraim, mace kuma aka maida sunan Namra, sai dai ita ana kiranta da Little Namra. An yi shagali iya shagali har abunda ban taba mafarkin za a raba ba anyi, a ranar daga ni har su mum sha bachin gajiya daman tun da suka zo dubiya ba su da aiki sai bachi sai kuma shan nono. Kusan rabin rainon su a hannun Ya Omri na yake indai yana gida to babu ruwana da su sai idan nono za su sha ko madara, idan kuma baya gida ga Baba mai kula min da su ba ni da matsalar daukarsu dan wani lokacin shi da kansa zai musu wanka ko ya wanke musu kashi ko tsarki. Sai da su kai shekara biyu da wata biyar sannan Ahmad yasa aka maido da su Namra da Amal da Aiman da Adnan a gidan, sai dai matan dakinsu dabam mazan ma haka, hakan kuma ba karamin faranta min rai yai ba, hakan ne ya kara tabbatar min da cewar lallai Ahmad ya rike yayana kamar nasa, lokaci lokaci Aminu kan kira shi ya tambayi lafiyarsu wani lokacin kuma sai ya aiko da mota a dauke su ya tafi da su yai musu shopping ya dawo da su, shi kansa rayuwarsa abar tausayi ce a yanzu domin matarsa bata haihuwa ba har yanzu wata kila ma su Namra da yak wulakantawa a baya su ne kadai ya'yansa tun da ita wacce yake aure ta riga ta lalata mahaifarta. Ga dan'uwansa wato Sadi ya zama aban tausayi domin ciwo ya kai shi kasa babu kyau gani, sam ba zaka ganshi kace shine ba, nikam hakan dadi yai min domin kuwa Allah ne ya nuna masa iyakarsa tun a yanzu kamin ayi wani hisabin a lahira.... Kiri da muzu Ya Omri ya hana ni zuwa barkar haihuwar da Suwaiba ta sake yi na macen da Abdallah baya so, duk kuwa da kasancewar ita din ta zo a lokacin dana haifi yan uku, sai dai mijinta be zo ba kuma be aiko ba be kuma kira ba. Sai na rasa yadda zanyi taya zata haihu na ki zuwa bayan kuma na sani, ai sai ga rashin kyautawa ta, da na san zai hana ni tun farko da ban tambaya ba sai na masa wata karyar na tafi. “Idan ban je ba ba zata jidadi ba ko Mama ba zata jidadi ba kuma Wallahi ban kyauta ba, komai fa ta wuce abunda ya faru duk a baya ne” Banza yai min yana ta wasa da yaransa sai kyalkyalar dariya yake shi da su kamar ma be san ina zaune a dakin ba. Can ya dago ya kalle ni. “Magana kike?” “Barkar Suwaiba” “Idan ba bacin raina kike son gani ba ki daina min maganar nan, haka kawai ki taka ki tafi gidansa yai ta kallonki” “Ba zanje lokacin da yake nan ba” “Na ce ba za a je din ba, ko a munafunce ban amince aje ba” Ya fada fuskarsa babu alamun wasa, har yanzu yaki yarda Abdallah ya daina so na ya kasa manta abunda ya faru na rasa wane irin kishi ne Ya Omri yake fama da shi ko mai sunan Abdallah baya so, Aminu ma dan ya zame masa dole ne. Duk yadda na so nai convincing dinsa ya amince fir ya ki a dole na hakura sai dai na siye abubuwa na bada nace a kai mata wanda na san hakan ba zai mata dadi ba. Ranar wata Lahadi ina zaune dakina rike da waya ina chat ya shigo rike da wasu takardu ya zauna kusa da ni yana fadin. “Ina tunanin bana da mu za a yi hajji” Ban san lokacin dana jefar da wayar hannuna ba na tashi na fuskance shi baki sake ido har gurin gira. “Da gaske?” “Yes tun da yara sun yi kwari ai ya kamata ke ma ki kai ziyara, sai mu koma tare, idan Allah kuma ya amince mana kuma sai mu yi ummara idan lokcin yayi” Rumgume shi nai cikin wata irin murna marar misaltuwa sai ya fara dariya yana fadin. “Idan mun dawo zaki karo min yan uku” “Har yan goma zan karo maka” Ya fara dariya yana rumgume ni. “Kamar gaske, salon kukan ya dawo ta fitina ko” Murmushi nai sai ya rike fuskata yana kallon cikin idona kamar ba gobe. “I love you so much” Ya fada da rada sai ya sumbanci goshinsa na mayar masa. “I love you more” Abunda ban sani ba, ba ni kadai Ahmad ya biyawa ba har da har da Mahaifiyarta da Inna, bayan gyaran gidan da yai musu ga dawainiyar kai abinci duk wata kusan hidimarsu ta dawo kansa, tsanannin dadi da farinciki har na rasa inda zan saka kaina. A tare mu kai hajjin da su wanda su kansu ba su taba saka ran wata rana za su tafi ba balle kuma ni, sai gashi komai ya canja mana kamar ba mu ba, bayan wuya sai dade kuma mai hakuri kan dafa dutse, abunda ban taba zato da tsammani ba shi yake ta zuwa min ba ni da matsala da Hajiya sai dan abun da ba a rasa ba, kusan ma yanzu tafi son jikokin fiye da da domin a yanzu Siyama tai aure tana dakinta ta bar Hajiya sai idan ta kawo ziyara, kamar dai su Hafiza da Husna da Aisha hankalina a kwance yake a yanzu ga yara a gabana gwanin sha'awa muna rayuwa cikin daula kamar gidan ubansu. Gobena tai kyau, Gobena ta zo min ta inda ban zata ba, Gobena ta same min mai Annuri da haske. ***** ******* ******* ***** AFTER SOME YEARS... Da gudu Amal ta fito dakinsu Adnan ta ho kaina kamar zata fada kan tsohon cikin da ke jikina sai kuma ta dawo bayana ta boya, Adnan din sai kokarin kamota yake. “Ya akai?” “Momy wai ina operating system tazo ta karbe” “Momy ba tashi bace ta Anty Namra ce kuma tace kar na bari ya dauka” “To ina ruwanki ki bani karatu nake” Sai a lokacin na daga kai na kalleshi. “Kai ina taka?” “Ya ki tashi Sudais ne ya saka mata ruwa” “Amal ba shi idan ya gama sai ya baki ki aje masa” “A a Momy tace kar na bashi” “Zan barshi ya doke ki fa” “Ni dai ba zan bada ba gaskiya” Ta fada tana make kafada. “Je ka dauko ta Aiman kyale ta yar neman fitina” Da huci ya nufi dakinsu yana fadin duk da shiga hannunsa sai ya doketa, daga inda take tsaye ta rika masa gwalo tana cewa. “Ai dai na hana, kuma idan ka dake ni idan Daddy ya dawo na fada masa, ai yace ka daina dukanmu” “Bana son hayaniyar nan sauka saman kaina” Na daka mata tsawa sannan ta sauka saman kujerar ta nufi gurin Lil Namra, tashi nai na nufi bedroom dina ina tafiya daker...... *TAMMAT BI HAMDILLAH* Godiya ga Allah mai kowa mai komai wanda ya bani ikon fara rubuta labarin nan 8 months ago har na kawo yau. Darasin da ke cike Allah ya bamu ikon amfani da shi ya yafe mana kuraruranmu. Godiya ga makaranta labarin Gobena a duk inda suke, da yawa mun fara rubutun nan da wasu amman ba mu karasa tare ba, sakamakon yanayin labarin, wasu sun fada min basa son labarin da babu soyayya wasu su ce min wahalar Halima ta yi yawa sun daina karantawa so so kaza kaza, a haka dai na daure na cigaba da rubutawa, Na fada tun farko cewar ban sani ba ko labarin zai muku dadi ko akasin haka domin ba zallar soyayya ba ne, rayuwace ta kalubalen da fadi tashin na rai da kaddara, ni na san akwai wadanda suka fi Halima shiga gararin rayuwa a zahiri, kuma bayan wuya sai dadi, sai gashi ina tsaka da rubuta nai ta haduwa da mutane masu kwatanta rayuwarta da ta Halima wata ma idan ta fada min halin rayuwarta wallahi har ta fi Halima shiga matsala, ban da wace akwai tace min sak yadda Aminu yake haka mijinta yake, akwai wacce tace min yadda Sadi ya lalata yar dan'uwansa Namra, haka kanen mijinta ya lalata yarta, wasu kuma matsin lamba ce daga iyayen miji kamar yadda Halima take sha. Ina matukar godiya kuma ina jinjina gurin wandanda suka jure karanta wannan littafi har muka kawo yanzu Allah yasa mu amfana da darasin dake ciki. Godiya gare ku yan wattpad, da yan Whatsapp, da facebook i love you All Fisabilillah ina godiya sosai Allah ya bar ran so. 1 ina ya fi burge ki a cikin littafin nan? 2 Mi ya fi baki tausayi? 3 ina ya fi baki haushi? 4 ina ya fi saki dariya? 5Wane darasi kika koya a cikin littafin nan? 6 Any kuma zaku iya yarda da kaddararku kamar Halimatu? Ance bayan wuya.......☺ *** *** *** Sai kuma idan mai kowa mai komai ya amince min mun hadu a littafi na gaba. Best regards 💚💛💜💙❤ Khadeeja Candy 🌺😍😘 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 55 of 55