Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Allah Subhanallahi, sune abubuwan da suke fitowa a bakunan mutanen da ke gurin. “Ina yata” Ya tambayi likitan. “Mahaifinta ne kai?” Runtse ido yai kamar ba zai amsa masa ba, sai kuma ya gyada masa gudun bata lokaci. “Muna bukatar jini” “Ina take?” Ya tambaya numfashinsa na fita kamar wanda yai wani aiki ya gaji. Da hannun likitan ya nuna masa kofar dakin. “Tana ciki” Da sauri ya shiga gurin, katon guri ne da ake aje mutane wasu kasa wasu saman gado ana shiga da su wani dakin likita na dubasu. Tsaye yai yana kallon yarsa kama da matacciya take masa domin bata motsi kuma babu alamar rai a tare da ita. “Baby.... ” Ya furta cikin tashin hankali. “Tana da rai jini likitan ya ce a kawo sai a duba ta, sun tafi su dauko gado... ” Be ko tsaya kallon mai matsa bayanin ba ya nufi yarsa yasa hannu biyu ya dauke ta cike da kuzari jin cewar tana da rai. Kamar wani mahaukaci haka ya fito da ita mutane sai kallonsa suke, ya sakata a mota sannan ya zagayo ya shiga mazauninsa da gudun tsiya ya bar cikin asibitin SJT hospital ya nufa da ita kasancewar ita ce asibitinsu kuma asibitin masu kudi wacce za a baka kulawa a take. Kamin ya karasa ya saka hannunsa aljihu ya lalaba wayarsa sai ya ji wayam babu komai sam ya manta da cewar a gida ya bar wayar sai yanzu da yake bukatar kiran family Doctor su. Yana isa suka karbata a take suka fara bata kulawa, jini ne abunda suka bukata bayan sun shiga da ita ICU, kamin ya kai gurin da za a dibi jinin nasa jikinsa har rawa yake. A ana cikin dibar jinin sai ga family Doc su ya shigo gurin hankalinsa a tashe. “Subhanallahi Gwarzo, yanzu ta kira tace na duba mata ko ka zo nan, na shiga emergency Doc Nura ke fada min an shiga da Baby ICU kai kuma kana nan, garin ya hakan ya faru...?” Kai kawai Ahmad ya daga ya kalleshi, shi da kansa ya karancin irin tashin hankalin da Gwarzo yake ciki ya fi gaban kwatance. After an gama dibar jinin Ahmad ya riko rigar Doc Nura da idanuwansa da suka gama rikedewa ya ce. “Dan Allah ka yi duk yadda za ka yi ka ceto rayuwar Baby, dan girman Allah” Ba Doc Nura kadai ba duk mutanen da ke gurin sai da ta ji tausayin Ahmad, gashi dai ba kuka yake ba amman idanuwansa da jikinsa da fuskarsa sun nuna damuwarsa karara, even the way da yake numfashin kasan yana cikin tashin hankali. Doc Nura ya gyada masa kai. “Karka damu In-Sha-Allah zata tashi” Sai a lokacin ya sake shi, ya dafe kansa ji yake kamar ace yana da wani abun da zai yi yarsa ta dawo normal. Mikewa yai tsaye ya bi bayansa a bakin kofar dakin da aka shiga da ita ya tsaya ya jingina jikin bangon dakin ya Runtse ido, yana jin muryar Hajiya amman ja kasa daga kansa sai kokuwa yake da numfashinsa. ABDALLAH POV. Daure da tawul ya fito daga bathroom dan karamin tawul a kafadarsa yana goge ruwan da ke kansa. “Waya kara ni” Ya tambayi Suwaiba da ke zaune bakin gadonsa. “Babu kowa” “Amman na ji wayata ta yi ringing kuma na ji kin yi picking sai kuma kika fita” “Ni ce na gwada kiran ina son na gane idan wayata tana aiki ne” The way da tai masa magana sai ya ji be gamsu da abunda ta fada ba, if gaskiya ne then why da tai picking ya bar dakin? Be sake ce mata komai ba, ya zauna gaban madubi ya soma shafa mai, jin bata zo ta taya shi ba yasa ya juyo ya kalleta. “Ba za ki taya ni ba?” Bata bashi amsa ba, sai dai irin kallon kunar zuciya da take masa ya karantar da shi damuwarta. “It seems like kamar akwai abunda yake damunki” “Yes alakarka da Halimatun nan ne ya ishe ni” Juyowa yai gaba daya ya fuskance ta. “I thought we talk about this issue kuma kin fahimce ni” “No i didn't,and i won't” Kai tsaye ta amsa masa da kamar fada, mikewa yai tsaye ya dauki wayarsa ya cire password din ya shiga call list ya duba mai kiran, bakuwar number ya gani a take ya aikawa Number kira, sai da tai ringing har ta katse ba a dauka sannan ya sake kiran layin aka daga cikin muryar kuka Salma take magana. “Hello.. Ya Abdallah” “Miya faru?” Ya tambaya ba dan ya san mai maganar ba, sai dai ita Salma tana da number sa. “Anty Halima ce sume” Gabansa ya fadi. “Ta suma kamar ya?” “Dazun ba Anty Halima ta kira ka ba? daman muna asibiti wannan Namra ce ta fada rijiya shine babanta yanzu ya mari Anty Halima ta suma” “Kuna ina?” “Muna asibitin Fmc” Be saka cewa komai ba ya katse kiran, zuciyarsa bata bashi kowa ba sai Namra ta ya akai ta fada rijiya ita tambayar da ta fado masa a rai, and why Aminu zai saka hannu ya daki Halimatu bayan ita take dawainiya da yarta, saboda kawai ya mayarda ita wata banza shine yake ta yi mata yadda ya ga dama. “Miyasa bata kira wani ba a family sai kai? Bata fi kusa da Abdulhamid ba shi da ya aureta ya saketa cikin mutunci? Ji yadda kake zanzana kamar.... ” Kan ta karasa ya daga mata hannu. “Please....” Sai kuma ya juyo daga jikin wardrobe da yake tsaye ya kalleta yana gyara hannun rigarsa. “Alaka ta da Halimatu ba ta yankewa matukar ina da rai, saboda haka ki sakawa zuciyarki salama, idan za ki iya yarda da mijikin fine, idan kuma aka samu akasin haka za ki wahalar da rayuwarki ne kawai, na fada miki kuma a yanzu zan sake maimaita miki hakan, for now on ba saboda na auri Halimatu nake wannan abun ba i just want to make her happy....” Yana kawai nan ya nufi gurin da kananan abubuwansa suke ya dauka ya saka aljihu ya fice daga dakin cikin sauri. Kamin ya isa asibitin zuciyarsa ta cika, ransa ya bace sosai from now on zai rika defending Halimatu as her brother, taya wani can wai shi tsohon mijinta zai saka hannu ya daketa saboda kawai yarta ta fada rijiya. “Ji wani irin zalimci” Ya furta yana jin wani irin bacin rai an taba masa Halimatu, a take wani bangare na zuciyarsa ya aika masa tambayar da ya rasa amsar ta. “Miyasa na damu har haka? What if mutane suka zargi wani abu? Miyasa nake ta zurfafa lamarinta a raina har yanzu....?” Yayi farkin motarsa gurin da kowa yake fakin sannan ya fito ya nufi cikin asibitin yana kokarin sake kiran Salma dan sanin inda suke a cikin asibitin. HALIMATU POV. Ashe suma na tana da dadi kamar dai shan maganin bachi, ta kan mantar da kai duniyar da kake ciki da kuma duniyar kuncinka balle kuma wata damuwa da fargaba ko kuka da tsoro. Indai har haka itama mutuwar take to ni kam ina maraba da ita daga yanzu har zuwa lokacin da zata sallamomin. Sannu sannu Halimatu. Muryoyi biyu na ji wadanda ba zan iya tantancewa ba kamar na Inna da Mama kuma kamar ba na su ba, iyakar unkurin da nai na bude idanuwa ne sai na ji sun min nauyi sosai, a cikin kaina kuma kamar babu komai ina jinsa kamar fanko. Ban ankaro ba na ji numfashina yai nauyi gurin fita daga kirjina haka ma gurin shiga sai na yi da karfi yake wucewa. Da wani irin karfi na umkuro na tashi zaune tare da bude idanuwa har sai da Inna da rike ni. Tabbas Inna ce ga fuskarta nan ina gani kamar a mafarki bakina na motsi amman ban san mi nake cewa ba, kai na daga sama gaba daya komai kamar ba gaske ba nake ganinsa. Kamar a min shokin sai na ji na farko daga mafarkin da nake. A zahirin ma ga Inna nan rike da ni Sai Salma da Aisha da Fati tsaye a kaina, Salma ta rufe bakina tana kuka tana kallona kamar yadda Inna ma take kuka ita da Fati. “Anty Halima...” Aisha ta kira sunana tana kallona kamar a firgice. “Na'am” Na amsa mata ina kokarin tuna abunda yasa aka kawo ni a nan. Na tuna Namra ta fada rijiya muka kawota ko? Sai aka mare ni? Amman waya mareni? Miyasa aka mareni? “Ina Namra take?” “Babanta ya dauke ta” Salma ta amsa tana share hawayenta. Daga lokacin ban sake sanin inda nake ba, sai na ji kamar wata tsotsa tana min yawo akai. A lokacin da hankalina ya dawo sai na ga Abdallah da wasu likitocin uku tsaye a kaina suna kallona. Wannan karon Salma hannu ta dora saman kai tana hawaye, Aisha ma kuka take. “Wai miya faru? Namra ta mutu ne?” “Bata mutu ba... ” Abdallah ne ya amsa min yana saka hannunsa a aljihu. “Ina son na ganta” Ina kokarin sauka daga kan gadon ya ce. “Akwai drip hannunki ki zauna sai ya kare” “A a ba zan iya ba ina son na ganta” “Ba mu san inda ya kaita ba” Ya amsa min fuskarsa ba yabo ba fallasa. Hakan yasa na koma na kwanta sai kuma na ji yana maganar hoto. “Idan drip din ya kare Mama za ta kaita ayi mata hoto” “Ba ni da lafiya ne?” Na tambaya sai yai saurin ba ni amsa. “Lafiyarki kalau” Bayan ya amsa min ya cigaba da kallona kamar mai tunani. “Ina son ganin yarinyar nan ina son ganinta ta mutu bata mutu ba ban sani ba i need to see her!” Na fada a tsawace kamar ba a hayyacina ba. “Idan ka san inda take a kaita ta ganta” “Ban sani ba amman zan bincika” Yana fadar hakan ya juya ya fice daga dakin sai sauran likotocin suka bi bayansa. Ni kuma na lumshe idona ban bude ba har sai da na ji motsin shigowar mutum, Hafiza ce ta shigo hankalinta a tashe tana sharar kwalla. “Sannu Halimatu” Haka take kirana yana da wahala ta ce min Anty indai ba mutane sai arzikin ke saman kanta ba. “Yauwa, yarinyar ta rayu” “Ance tana da rai, mahaifinta ya kaita wata asibitin aka ce” Ban sake ce mata komai ba, har sai da Abdallah ya shigo da kansa ya karaso ya cire min drip sannan ya ciro wayarsa ya kira wani likita da ban san wanene ba ya ce. “Zan dauketa na kaita ta ga yarinyar yanzu idan mun dawo i will call you” Daga haka ya maida wayar aljihu ni kuma na sauko daga saman gadon na biyo bayansa, a harabar kofar shiga Ward din inda mutane suke shinfida tabarma suna zaunawa na hango Inna sai ta taso ta tare ni. “Halimatu kin taso” “eh zan kaita ta dubo Namra ne idan mun dawo sai a je da ita gurin hoton” Abdallah ne ya bata amsa a madadina sannan tai mana Allah ya tsare ta bimu da kallo, yana gaba ina biye har gurin motarsa, da kaina na saka hannu na bude motar na shiga na zauna daga lokacin kuma ban sake sanin inda nake ba. Sai can na farka na ga yana kallona. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Shine abunda ya furta, kallonsa nai kamin na kalli titin sai a lokacin na lura da motarsa fake take a gefen titi kuma ba a cikin asibitin muke ba, Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tashi motar muka hau titi, SJT hospital muka shiga, babbar asibiti mai zaman kanta a zamfara, asibitin masu kudi domin ko katin ganin likita kawai ya isa siyen wani maganin a yadda nake jin ana fada domin ban taba zuwa ba. Agurin da aka tanada domin faka motoci ya faka motarsa sannan ya bude ya fita, ni ma na bude na fita sai wani irin sanyi baibaye ni sanyi ba na wasa ba, a take hakorana suka fara haduwa da juna. “Koma cikin motar ki zauna” Ya fada min sannan ya ciro wayarsa ya kira Hafiza yai mata kwatancen inda muke, tun da ya soma wayar na ke kallonsa har ya gama ya cigaba da latsa wayarsa, sak Abdulhamid nake gani a sura da hallitarsu sai dai shi ya dan fi Abdulhamid kwauri kadan, a hallaya kuma sun banbanta, tunawa da Abdulhamid sai ya haifar min da wata kalar damuwa a cikin raina. “Abdallah” Ni dai na san na kira sunansa har ya dago ya kalleni ban kuma san dalilin kiran nasa da nai ba, bayan ga wannan ban sake sani ko jin abunda ya fito daga bakina ba, kamar an min shocking dai na ji na dawo normal, amman a kasa nake zaune fuskarta har da hawaye da ban san yadda akai suka zubo ba, saurin tashi nai zaune na saka hannu na share hawayena a lokacin da na kalli Abdallah sai na ga idonsa cike da kwalla yana ta min kallon tausayi. “Miyasa nai hawaye? Mi yake faruwa da ni...?” Na tambaya ina kokarin fashewa da kuka, sai ya busar da iskar bakinsa “Ba komai” Da kansa ya kai hannunsa ya bude min motar. “Shiga ciki ki zauna na ce” “Ina son ganin yarinyar” “Idan Hafiza ta zo zamu shiga ciki ki ganta” Zaunawa nai cikin motar sai a lokacin na tuna da yata. “Ko ina Namra take? Ko har da ita ta fada rijiyar? Kamar bata fada ba ko?” Na tambayi kamar ya san amsar. “Tana nan lafiya kalau” Ban sake cewa komai ba, har Hafiza ta isa sannan na fito daga motar daman kafafuwa na waje suke, shi kuma ya rufe motar yai gaba muka bishi, mun yar tafiya mai dan ni sa sai dai ba sosai ba har muka isa bakin wasu dakuna, daki na hudu ya tura kofar ta bude sai ya tsaya be shiga ba yai min alama da na wuce. Ni na fara shiga sannan Hafiza sai kuma shi. Baby Namra ce kwance saman gado tana bachi jini na ta shiga a jikinta. An saka mata wani abu a wuya an daure kafarta da hannu a gefen idonta ma bandeji ne. Mutum hudu muka tarar a dakin ciki har da mahaifinta, kamar wanda ya ga bakin maciji haka yake kallona fuskarsa babu annuri, ban taba hada ido da wani naji firgita kamar yadda na ji a lokacin da na kalli Abban Baby Namra ba, a take na nemi natsuwata da karfin halina na rasa, na rasa sai fargaba da razana suka lullube ni, kamar wata karamar yarinya haka na zama na rasa sukuni har sai da na koma bayan Abdallah na tsaya. “Kina da wani irin karfin hali, how dare you” Babu wanda yace uffan daga mutane da suke dakin har Abdallah da Hafiza. “And let me tell you Wallahi idan yata ta mutu i will make your life miserable, you will die in jail kina ji kina gani zan tarwatsa rayuwarki, you will pay for this, ba kin zabi kashe min ya ba?” The word jail ta saka ni jin wani iri, is like kamar ban taba jin kalmar ba, kuma kamar ance min gunduwa gunduwa za ayi da ni. Ba tsoron gidan yari nake ko police ba amman ban san abunda ya saka ni tsoro ba har jikina ya fara rawa kamar wata bakuwar kalma haka na rika jinta a kaina, a take garin ya fara sauya min zuwa wani yanayin dabam, can na tsinkayo Abdallah nayi masa magana. “Taya mace da ta haifa ta san zafin haihuwa zata dauki yar wani ta jefa rijiya? Ya kake magana kamar ba namiji ba” Wani banzan kallon yai masa irin na sai a yanzu na lura da kai din nan. “And who are you? Her husband?” “No I'm her brother” “Just?” Ya tambaya da irin sigar rainin wayo. “Just ne?” Abdallah ya tambaya a fusace. “Who do you fucking think you're? After all the slap da maganar da ka fada mata yanzu and you want to deal with me? Daga ganinka ba ka yarda da kaddara ba” Sai ya daga wa Abdallah gira. “Yes ban santa ba, saboda ban hada hanya da ita ba, akan yata?..... Hummmm” Wata budurwa ce ta taso ma Abdallah budurwar da na tana gani a gidansu lokacin da naje. “Excuse me man, yar mu aka taba kasan darajar ranta?” “Hey young lady control yourself, and ban sani ba kuma ba na son na sani” Juyowa yai ya kalleni. “Muje Hafiza riko hannu” Yana fadar hakan ya fice, a maimakon ya ta kama hannun nawa kamar yadda ya fada sai ta tsaya yi musu bayani. “Ku fahimce mu, Halima ba zata kama yar wani ta jefa a rijiya ba, ko da kau bata santa ba balle ta santa, yanzu haka ba a hayyacinta take ba amman ta damu sai an kawo ta ta ganta, tun daga lokacin da ka mareta bata sake zama mutum kamar kowa ba, daga ni har ita ba mu san yadda akai yarka ta fada rijiya ba.... ” “Aljanune da ita kenan? Shiyasa ta dauki Baby ta jefa rijiya, daman ai ba tai kama da masu hankali ba, ita aljannu take takama da su ni a kaina rauhanai ne, na fita hauka” “Ba haka nake nufi ba...” “Idan baki min shiru ab har da ke zan daure fita ki ba ni guri” Ita yake ma masifar ni ce da jin tsoro sai hawaye nake kamar domin hawayen kawai aka hallaci ni. Hannu ta rika muka fice daga dakin ita hawaye ni hawaye har muka isa gurin motar Abdallah. Gidan baya muka zauna ni da ita, kamar uwa da ya haka kanwata ta rumgume ni a jikinta sai na fashe da kuka mai tsanani. “Gida nake so dan Allah ka kai ji gida... ” Na furta cikin kuka, shi dai be ce min uffan ba har muka bar asibitin. 7/21/21, 10:45 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣1️⃣ ABDALLAH POV. Tukin motar kawai yake zuciyarsa na sosuwa da kukan da Halimatu take yi, on the other part kuma maganar da Ahmad yai ta tsaya masa a rai. A iya tunaninsa duk mai kokarin cin mutunci Halima yana yi ne saboda yana ganin bata da mai tsaya mata kuma ana ganinta a mace mai rauni. “Wata kaddarar, ta kan zabi wasu mutanen ta tare musu ko wane irin fada, ta tsaya musu ta hana ni ganin abun ki ko damuwa. Wata kaddarar kuma jefa wasu take a damuwa da bakinciki ta saka har duniya ta juya musu baya, mi yake damuna ne? Miyasa komai ni ce komai ni ce? Na gagara samun farinciki ko dan kankane dan kannen kamar haka...” Ta nunawa Hafiza yatsanta tana hawaye. “Komai ni ce, komai ni ni din dai Halimatu na fi kowa shiga cikin matsala, mutane gasu nan ina ganinsu suna farinciki amman ban da, kin gansu?” Hafiza ta kasa ce mata komai sai kuka take yana rike mata hannu. “Ga su nan fa ina kallo ke ba ki gansu ba?” Ta fada tana nuna gilashin motar, da gaske mutane take gani kwakwalwarta na kawo mata abubuwa da yawa, ciki har da rayuwarda tai a baya duk abunda ya zo daga bakinta fada take, abubuwan da take fada ba komai ba ne sai damuwarta. Kuka take tai dariya a lokaci daya kamar wata tabbabiya. Ta kalli Hafiza dake mata kallon tausayi tana hawaye. “Wacece ke? Na baki labarina? Ni wata mace ce mai haduwa da abubuwa kala kala” Sai kuma tai shiru ta sake kallon Hafiza ta kalli kanta. “Wacece ni?” Abdallah na jin hakan ya busar da iskar bakinsa ya faka motarsa gefen titi ya fita be dade ba sai gashi ya dawo rike da gorar ruwa ya bude motar ta gafen da Halima take ya cire murfin gorar ya kai mata ruwan a baki, a Hankali yake bata ruwan tana sha sannan ya cire gorar daga bakinta ya kai bakinsa ya kumda ruwan a bakinsa ya fesa mata a fuska, runtse ido tai na yan dakiku sannan ta bude kyakkawan idanuwanta sukai arba da na fuskar Abdallah. “A ina muke miya faru?” “Babu abunda ya faru” Mikewa yai tsaye ya bayan ya bata amsa ya rufe motar ya zagaya ya shiga side dinsa ya tashi motar. “Miya faru miyasa na jike ina zamu je?” “Asibiti” “Ka kai ni gida” Ta fada kai tsaye. “Kina da bukatar ganin likita” “Bana bukata Abdallah bana bukatar kowa ya rabe ni a yanzu balle har ni na rabi wasu, duk wanda ya rabe ni sai wani abu ya faru da shi....” Bata gama fadar abunda take fada ba ya daka mata tsawa. “Ya isa haka kike sakawa kanki tunani kala kala har abun yana taba kwakwalwarki, I'm sure idan level din gushewar hankalinki ya wuce iya nan ko yayanki ba za su zauna da ke ba....” Ta dago kanta ta kalli Abdallah ta madubin gaban mota idonta cike da kwalla. “Ba ni da hankali kenan? Shiyasa na ke jin kamar ina bachi kamar na suma, ashe gushewar hankali ne? Kenan haukace ta kama ni?” Ta lumshe ido ta a hawayen da Abdallah yake jin zubarsu har cikin zuciyarsa, har yaji ina ma be fada komai ba ina ma furta komai ba! Har ya kai ta kofar gidan ta bude mota ta fita ta shiga gida be daina kallonta ba, sai ta shige gida sannan Hafiza ta bude motar ta fita sai ya kirata. “Hafiza dan Allah a kula da ita, bana son nai mata cilas a zuwa asibitin ne yanzu, amman zuwa gobe zan turo direba ya maida ita kin ga ai ba su bata sallama ba kuma tana bukatar kulawar likitoci, and karki barta ita kadai pls shi ke kawo yawan tunani ku rika yi mata abunda zai sauke mata hankali” “In-Sha-Allah, mun gode Ya Abdallah” Be ce mata komai ba yai ribas ya dauki hanyar gidan Hajiyarsa zuciyarsa cike da tunani kala kala. Sai da ya faka motarsa harabar gidan maganar Halimatu ta fado masa a rai. Tabbas sukan kaddarar kyakkyawa ta musu rumfa ta tare musu ko wane fada, ta musu gata, bayan kuma ba zabin su ne ba hukunci na Allah. Idan auna yadda rayuwa ta shimfida musu kyakkyawar rayuwa da kuma rayuwar Halima sai ya ji imani da tsoron Allah ya kara kama shi, lallai ba yin kansa ba ne, domin yana da tabbaci da bawa ne yake zabawa kansa irin rayuwar da yake so da Halimatu bata zabi rayuwar da take a ciki ba a yanzu. A duk takunsa sunan Halimatu ke yawo a kansa, ko ina zai motsa tausayi ya mamaye shi, ya kasa ganin laifinta ya kasa samun hanyar rabuwa da ita a kullum kaddara kara kusanto masa da ita take. Ko da ya shiga falon idonsa ya canja kala saboda damuwa. He got lucky Hajiya ce kadai a falon tana kallon wayarta. Sai da ya tsaya ya cire takalmin kafarsa sannan yai sallama ya shiga cikin falon, a kujerar da ke fuskantar ta Hajiya ya zauna yana gaisheta. Ta amsa masa tana aje wayar a gafenta domin ta hango damuwa a fuskar danta kamar yadda ko wace uwa mai kula take gane idan danta yana cikin bacin walwala ko kishiyar hakan. “Husaini lafiyar ka yau kuwa?” Dagowa yai ya kalleta a hankali. “Ban san yadda za ki ji idan na tambaye ki ba, ban san ya zaki dauki tambayar ba, amman Hajiya kin taba tambayar kanki ko ki yi tunani miyasa Allah yai mu masu rufin asiri kamar haka?” Sakin baki tai tana kallonsa kamin ta amsa. “Ah Ah daman can Allah ya kaddara mu din masu arziki ne” Ya gyada kai. “Haka ne da yai mana arzikin kuma sai ya hada mana da farinciki, wasu kuma ya ba su arzikin ya hana su farinciki, wasu kuma ya ba su farincikin ya hana su arzikin, wasu kuma ya hana su arzikin ya hana su farinciki yadda ya so haka yake haka yake kasancewa, duk a cikin ikonsa ne” “Wai miya faru ne, ban gane wannan maganar ba?” “Halima Hajiya” Yana fadar sunanta sai yai shiru kamar ba zai cigaba ba, Hajiya kuma ta gyada kai. “Zancen kenan Halimatu Halimatu, ka kasa cire matar nan a ranka” “Hajiya ta ya zan cire abunda ba ni na sakawa kaina shi ba? Da ina da iko da dama da ban bar zuciyata ta kamu da son Halimatu ba tun farko” “Dan Allah na hada ka da girman Allah ka bar yarinyar nan, ka daina shiga zabgarta ka manta da ita a rayuwarka” “Idan umarni ne zan bi, idan kuma shawara to zan amsa miki da cewar Wallahi ba zan iya ba Hajiya, Soyayyar Halimatu a zuciyata kaddara ce, Hajiya na san Halimatu tun kamin tai aure, amman Allah be dora min kaunarta sai da tai aure ta haifi yara biyu, da igiyar aurenta na kamu da sonta Hajiya, shim

Chapter 24 of 55