auren har nan da December”
“Sun kara wata hudu kenan”
“Allah ya kaimu ya sanya alheri”
“Amin”
Daga haka ya juya ya fice daga gidan.
HALIMATU POV.
A daren na rabawa kowa abunda zan bashi, babu wanda be yi murna ba. Washe gari aka tashi da hadari a garin sai dai hakan ba hana ni saurin shiryawa yarana suka wuce makaranta ba, ni kuma na shirya na nufi gurin aiki ina ta Allah Allah kar a sako da ruwa. Na yi sa'ar samun napep na shiga ina fada masa inda zai kai ni, mu tsaka da tafiya ya soma nuna min wata mota da ke binmu mai motar na mana hannu da mu tsaya. A lokacin da na leka sai na gane Abraham ne na rasa yadda zan yi da shi, me zan masa ya fahimci bana son ganinsa ma balle saurarensa. Ban bar mai napep din ya tsaya ba sai da muka kusan isa kamfanin sannan na bukaci mai napep din ya sauke ni, mai napep din na yin parking Abraham ya faka gaba da mu kadan ko kudin shi ban bashi na nufi gurin da Abraham din yake rai a bace. Ko da na isa ya sauke gilashin motarsa aiko take na nufeshi da masifa.
“Me kake da bukata ne? Miyasa zaka rika bibiyarta? Bana son ganinka bana son wata alaka ta shiga tsakanina da kai, dan girman Allah ka kyale rayuwata na huta”
“Ihu fa kike yi? Ba ki tsaya kin saurare abunda zan fada miki ba, na san ba kya son ana ganina a gidanmu shiyasa na biyo napep din da kika hau”
Har na bude baki nai magan sai na ji tsayuwar mota a bayana, juyowar da zan yi na yi arba da Ahmad yana sauke gilashin motarsa.
“Lafiya?”
Sai na kalleshi na kalli Abraham sannan na sake kallonsa na ce.
“Lafiya kalau”
Ban san dalilinsa na tsare Abraham da ido ba, sannan ya sake kallon yace.
“Shine mutumen da yake bibiyarki?”
Na kalli Abraham wanda yai saurin tada gilashin motarsa yana mata key.
“A a makocin mu ne”
Be sake ce min komai ba ganin Abraham din ya bar wajen, sai shima yai ma motarsa key ya karasa cikin kamfanin, sai a lokacin na sallami mai napep din na karasa cikin kamfanin da kafa, ina shiga abokan aikina suk fara min murn wai an canja min aiki an bani wanda ba shi da wahala kuma mai albashi da mai tsoka, na yi murna kamar yadda su ma suke tayani murnar sannan na wuce office dina ina sanye da tufafin da na fi so kuma suka fi karbata wato abaya.
Ganin Ahmad da nai a cikin office din tsaye jikin window ya bawa kofar baya hannayensa duka biyu zube a aljihu, gaba daya office din kamshin turarensa yake. A zatona ko na yi latti ne ko kuma wani abun na aikata ba daidai ba.
“Ina kwana ranka ya dade”
Be amsa min ba be kuma juyo ba, sai yai kamar be san da n shigo office din ba, wata kila kuma be san na shigo din ba, tun da ban yi knocked ba, hakan yasa na juya na fita daga office sai na tsaya daga bakin kofa nai knocked, ima ta jira ace na shigo amman shiru be ce min ba, ni ko na dage ina ta kwankwasa kofar a hankali. Can dai na gaji da tsayuwa sai na dan tura kofar a hankali da zimmar lekawa na ga ko ya nufo kofar ko kuma zama yai ko wani abun yake, kamar munafuka haka na leka office din kamar hadin baki sai muka yi ido hudu da shi ya juyo daga jikin window yana kallona da mamaki, saurin komawa nai na rufe kofar duk sai kunya ta kamani, amman hakan be saka na fasa knocked din ba, har lokacin kuma be ce min na shigo ba ko na tafi, lallai wannan mutum akwai girman kai tsinya, a gurin nai ta tsayuwa da na gaji na nemi guri na zauna, zan iya shiga yace na shigo ba tare da ya bani izini ba, tunda kamfaninsa ba, ko da yake na ga alamar kamar ya sauko daga yadda yake ba kamar da ba.
Ina jikin kofar ya bude ta da dayan hannunsa yayinda dayan kuma yake cikin aljihu.
Tsaye yai yana kallona ni kuma na tashi tsaye ina sadda kaina kasa.
“Office din nawa ne ko naki?”
“Amman ai kamfanin na ka ne, kai ke da ikon office din”
“Office din nawa ne ko naki?”
Ya sake tambaya.
“Nawa ne”
“Idan wani abu ya bata a office din nan ke za a tuhuma, ba a farin office bude kamar yadda kikai, ki rika kula da wanda zai shigo ko ya fita a office din”
Ya karasa yana nuna min security camera dake bakin kofar office din, sai a lokacin na lura da ita.
“Ke zaki bawa mutum izinin shiga office dinki ba wai ki tsaya jiran ya baki izini ba”
“To idan na shiga kace na maka ba daidai ba fa”
Barin jikin kofar yai ya karasa gaban teburin aikina yana duba wasu takardu dake wajen. Hakan yasa na shiga office din naja kujerata na zauna.
“Me kake nema?”
Be amsa ni ba sai duba takardun yake har ya dauko wata takardar ya nuna min ita saitin fuska.
“Wannan.....”
Juyawa yai ya nufi kofa har zai fice sai kuma ya juyo ya kalleni da manyan idanuwansa masu daukar hankali.
“Miyasa ba ki yi reporting mutumen nan gurin police ba?”
“Shi ma ai dan sanda ne, kuma yace min ya tuba ya ba ni hakuri, kuma yace zai musulunta ya aureni”
“Dan sanda? Ya akai kika sani?”
“Ranar da naje kai kara a office din akan shi sai n same shi a office din kuma kamar shi ma yana da mukamin a cikinsu m dan oga ake kiransa”
Dawowa yai gaban teburin ya tsaya yana kallona.
“Fada min one good reason daya saka shi yi miki fyaden a wannan ranar byan kin ce dan sanda ne, da kakin ya tafi”
Kallonsa kawai nai na ki na amsa masa, shi kuma ya tsare da ido irin na babba da yaro, fuskarsa na nuna alamar ya fusata.
“Ok fine...”
Ya furta yana dauke idonsa daga kaina zuwa ga takadar da ke hannunsa.
“Fuska a rufe da bindiga mijina suka je nema a lokacin baya nan shine suka ce za su bar masa sako”
“So yanzu kin yafe mishi kenan? And you believe zai musulunta, kina ganin da gaske yayi nadamar da zai saka ya iya bayyana knsa a matsayin wanda yai miki fyade? Kina ganin zai yrda ya bar aikinsa da sana'ar saboda ke? Domin bayyana kansa a matsayin wanda yai miki fyade yana nufi rasa komai nasa ne, and what makes you think musulunci da gaske zai yi shi? Baki tunanin idan ya samu sa'arki zai iya aurenki ya dauke ki ya maidaki wani gurin inda baki isa ko harrarsa ki yi ba, addinin kuma sai yaga dama zai yi?”
Na yi shiru ina ta nazarin kalamansa.
“Fada min miyasa ya dawo gurinki?”
“Yace yana bukatar haihuwa, saboda zai iya mutuwa a ko yaushe”
“Hakan yana nufin yana neman haihuwa kenan be samu ba, sai da yai min miki fyade that's why ya kawo kansa, ina yar'uwar takardar nan?”
Ya karasa yana nuna min takardar, a take na shiga dubawa zuciyata cike da tunani, duk wani duba takardun da nake idonsa na kaina.
“Kin san wani abu? Kina da saurin yarda da mutane, kina da tsoron fushin wasu, kina iya shanye bakinciki dan wani yai farinciki, sune abubuwan da suke kara saka ki a damuwa, rayuwarki abar tausayi ce Wallahi, a yanzu ma za ki iya fadawa a wani tarkon”
Ya fada yana kallona kamar ba shi yai maganar ba, domin bubu alamun hakan a tare da shi.
“Ban ga takardar ba”
“Kije reception ki tambaya inda suka tura takardar ki karbo”
Yana fadar hakan na nemi guri ya zauna, ni kuma na saka kai na fice har an isa reception din suk fada min office din da zanje, wani bangare na kamfanin office din yake a lokacin da na isa tsayawa nai jikin kofar na kwankwasa har sai aka bani damar shiga sannan na shiga na gaisa da matar na fada mata abunda nake bukata sai ta dauko wasu files ya duba ta miko min takardar.
“Ke ce sabowar ma'aikaciyarmu ko?”
“Eh”
Na amsa mata, tare da mika mata hannuna kamar yadda take miko min nata.
“Yayi kyau sunana Zainab”
“Halima”
Sannan na jiyo na fito daga office din na nufo office dina, wannan karon ma sai da nai knocked sannan na shiga, jakata na tarar a bude hannunsa kuma rike da wayar da nake kyautata zaton tawa ce to me kuma ya kai shi a gurin jakata da har zai saka hannu ya dauko wayata, da sauri na kai hannu na fisge wayar ina bata fuska alamar ban jidadin abunda yai min ba.
Uffan be ce min ba sai kallona yake, kamar ance min na duba a saman tebur din sai na kyalla ido na hango wayata kusa da jakar, hakan na nufi wayar da na karba ba ta wa ba ce kenan tashi ce. Aiko ba shiri dora tashi wayar a saman tebur din na dauki tawa ina jin kamar kasa ta bude na shige ciki.
“Takardar...?”
Ya tambaya fuskarsa babu alamar dariya, sai a lokacin na tuna da abunda naje neman, mika masa takardar nai ya karba ya mike tsaye.
“Miye aikin shi da har yan fashi za su nemansa?”
Da gangan nai kamar ban ji shi ba badan komai ba sai dan ya fita ya bar min office din. Ban bashi amsa ba har ya kai hannu ya dauki wayarsa yana ta kallona ya fice.
Sai a lokacin na samu natsuwa har na cire wayar tawa a password na, kamin na taba komai sako ya shigo min da wata bakuwar number.
“Fatar kina cikin koshin lafiya, na yi ta kira baki daga ba kina rejecting calls din, ko ba komai Halima ko dan yyanmu ai kya raga min ba kisan maganar da zan miki ba, izuwa yanzu idan ba rain kike son ya bar jikina ba ya kamata ace kin tausaya min, Wallahi kullum abunda na aikata yana damuna, na rasa samun sukuni idan har baki dawo gareni ba Halima ban san halin da zan kasance a gaba ba, tabbas Gobena zata zama mai rauni kuma abar tausayi”
Ina gama karanta sakon na goge, sai yanzu na gano dalilin dauko wayata ta Ahmad yai wata kila kiran yai yawa ne shiyasa ya dauko yana mim rejecting kamar na saka shi.
Na yi aikina kamar jiya yau ma ban ci abincin sai dai na sha ruwan lemun da aka kawo min tare da takeaway.
Misalin biyar na tashi ban bar office din ba sai da nai sallah la'asar, daga office din na wuce gidan kawata Hajara, mun dade muna fira na labarta mata abubuwan da suka faru tun bayan rabuwarmu wato bayan zuwan da nai na karshen a gidanta.
Sai magariba na baro gidan, kamar koyaushe napep yar gidana na hau na doshi hanyar gida.
Ina fitowa daga napep din nai arba da Abraham dake tsaye jikin kofar gidanmu, sanye da riga da wando na shadda har da hula guluf din dake bakin kofarmu na haska fuskarsa tufafin sun masa kyau kamar ba shi ba, waiga nai ko'ina ban ga motarsa ba, ban ga alamunta ba, bayan na sallami kai napep din na nufi inda yake tsaye yana kallona na ce.
“Minene kuma?”
“Tambayarki na zo yi, bayan mutumen dazun? Wa kika fadawa na miki fyade kuma ina bibiyarki?”
Shine abunda ya fito daga bakinsa yana ta kallona fuskarsa babu alamar wasa.
“Babu shi ma kuma fada masa nai ba”
“To ya akai ya sani?”
Na masa shiru sai kallon mamaki nake masa.
“Waye kai Abraham ina son sanin tarihinka, waye kai?”
A maimakon ya bani amsa sai kawai ya amsa min da.
“Sirrina nawa ne ni kadai, sai ke ya kamata ki san da wannan”
Yana fadar hakan ya daga jikin kofar gidanmu ya nufi hanyar titi da kallo na bishi har na daina hangoshi, sannan na juya ina kokarin shiga gida Namra ta fito da saurinta ganina yasa ta tsaya.
“Momy yi sauri ga Daddy nan ya zo, ya mana siyayya har da ke”
“Kai Kai Kai..... Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”
Na furta da karfi ina dora hannu saman kai.....
7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: I think you'd like this story: "GOBE NA (My Tomorrow)" by KhadeejaCandy on Wattpad https://www.wattpad.com/story/247701926?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZkyWKvWuHXhIRzZDEluZ%2BuUXayIbDBikXAQA%2BM4xeAsJY%2Fh9rtovTCoQphCdFYUPM4K1nHTquOLcFfifZUhwZ0RRyERddTi4AY1OYORg8gUhN9fNU%2FLr6t3SMGO9O8M2
*GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
4️⃣6️⃣
Bayan tafiyar Aminu, Abdallah ya kira ni a waya sai na tashi na bar dakin na shiga dakin inna inda babu kowa ina amsa masa wayar, tambaya yake akan Abraham din ina fada masa abunda na sani da kuma farkon haduwarmu har abunda ya kawo isuwa yau.
“Bayan ni akwai wanda ya san da wannan maganar”
“Eh ogan mu na gurin aiki”
“Halima kin amince masa da yawa, kin manta waye shi ne?”
“A a babu wani aminci a tsakaninmu, ya nemi yafiyata ne, kuma na rubuta labari ne a ranar children day a gurin ya gane cewar ni ce saboda labarin yarsa ya shigo ciki da kuma na kamfaninsa”
“Ban gane ba zuwa kikai kika fallasa kanka abayyanar jama'a”
“Aa....”
Daya bayan daya na bayyana masa yadda abun ya faru har da zancen siyen tikitin da Abraham yai, hakan kuma ba karamin bata masa rai yayi ba.
“Wayuya kawai taya shi Abraham din zai siya miki ticket kuma ki karba ki je”
“To ba gashi na ci gasar ba”
“Dalla can Sakarya kawai”
Ya kashe wayarsa, a iya tunanina nikam ban ga illar zuwa bukin da nai ba, to ina ruwana da shi ai ba san shi na je ba, dan yarana. Ko da na fito dakin dukansu suna zaune a tsakar gida har Mama sai zancen Aminu suke, kusa da Inna na zauna ina sauraren Mama da ke fadin.
“Namiji dai ba shi da kunya, yanzu duk abubuwan nan da Aminu yai miki har yana iya murje ido yai miki siyayya ya kawo miki yana rokon ki koma masa?ya manta irin cin mutuncin da yai miki ne ko kuwa ya runtse ido ne ya zo?”
“Hmmm Mama ke ma dai kya fada, ni wallahi yanzu ko mai sunansa bana son ji sai na rika ganin kamar ma halinsu daya”
Na Fada ina tabe baki,Sai Inna tai dariya tace.
“Kuma kin ga fa inda rabon shiryarwa sai a shirya tun da akwai yaya har hudu, ai ko aure kika yi a wani wajen hankalinki yana kansu, nikam da za ki bi ta tawa da kin koma masa tun dai ya gyara halinsa kuma mahaifiyarsa ma yanzu tana sonki”
Mama ta tari numfashin Inna tana girgiza kai.
“A a wahalar da ta sha ta isa haka nan, ai ba ayi rai dan wani rai ba, wani lokacin mai hali baya fasa halinsa, Allah dai ya baki wani na kwarai wanda zai so ki tsakani da Allah, wanda zai kaunace ki har karshen rayuwarki, ya zame miki gata hawayen da kika zubar ya share miki su, kuma ya so yayanki kamar nasa, wanda zai rika jin tausayinki yana tsoron cutar da ke”
Dan murmushi nai.
“Samun irin wannan namiji yana da wahala Mama, mutum daya na san zai iya min haka, shi kuma babu wannan damar a yanzu, nikam na yanke kauna daga yin aure a yanzu”
“Haba dai fata na gari lamiri, idan ba ki yi aure ba ki yi me? Aure ya haife ki kuma ya haifa miki yaya, ina kan fatana na ganki a dakin mijinki”
Aisha da Hafiza da Husna kamar jira suke suka hau yi mata yaya, ba ma kamar Hafiza sarkin Baki.
“Mu da ba a kauna ai sai a kai ku kofar gida a aje, wai har wani fata ake mata ga ku zaune, ita ba kara ita ba tayi auren har ta haifi amsu yi mata addu'a, mu da ko mashinshinin ba mu da fa?”
Duk dariya muka saka har ita, sannan su ma tai musu addu'ar. Sai a lokacin na dauko siyayar da Aminu yai min na bude ina dubawa, Atamfa ce har biyu da turare da sabulun wanka da wanki sai yan kayan tande tande, komai ban dauka a gurin na rabawa Mama da Inna atamfar salubun wanka da wanki kuma na bawa kanena turaren na bawa Baba, sauran kayan tande tande kuma a nan na bar su a tsakaninsu suka raba suka cinye.
Ina zaune a gurin amman ko chocolate din ban ci ba, sai aikin danna wayata nake.
“Gobe idan Allah ya kaimu ina son zuwa gidan Gwaggo Ramatu”
Mama ta fada.
“Gaskiya kam kin kwana biyu ba ki leka ta ga, gata ita kadai ta rage muku cikin Gwaggonin”
Na fada still idona yana kan wayata.
“Shiyasa ai nake son zuwa, sai na siya mata salubu na kai mata”
Da gangan na kalli Hafiza na ce
“Ga sabulun Hafiza nan ta baki ki kai mata”
Wata uwar harara ta watsa min.
“Eh ni da ba kya kauna, to ba zan bayar ba, kuma Mama dakinki zan aje shi idan ma ban ganshi ba ba ruwana ni”
Ta fada tana tashi ta bar mana gurin.
“To idan ba ruwanki ai ba ruwan kowa”
Na fada ina dariya Inna ma dariya take, haka ma Mama daman sun san Hafiza bata da na biyu a cikin gidan indai babin fada ne da matsifa, sai dai fa akwai son yan'uwanta kamar ranta, hakan yasa baka iya banbanta ni da ita kace kowa da uwarsa, mu zama kamar uwa daya daman kuma uban ne ya hada.
Washe gari ta kama friday farar rana kuma kuraren lokaci, hakan yasa na gama shiryawa su Amal da wuri suka wuce makaranta ni kuma na shirya a yau ma abayar na saka sai dai wannan maroon color ce, sai da nai musu sallama sannan na nufi gurin aikina.
Tun daga lokacin dana fito gida nake saka ran haduwa da Abraham saboda sabon da yai min na bibiya a baya wani lokaci amman har na isa ban ganshi ba, a yau ma ban ga Kabir ba, hankali ya dan tashi daman na san Ahmad ba zai kyale shi ba bayan abunda ya faru, to amman ina ya kai shi? A wane hali yake? Har na shiga cikin kamfanin ban daina yiwa kaina tambayoyi a game da Kabir ba. Can zuciyata ta kawo min cewar na taimaka masa da kudin na da samu ko zai samu lafiya, ba karamin dadi na ji ba da wannan idea ta fado min a rai.
Ina isa office dina na tura kofar na shiga, kamar dai jiya yau ma na tarar an goge ko'ina an saka air freshener mai kamshi, jaka ta na fara dorawa a saman tebur din na kunna desktop din sannan na nufi window ma bude, tsaye na hango shi jikin windows din office dinsa hannunsa daya a aljihu dayan kuma rike da cup. Maida window nai na rufe na dawo na zauna na bude na fara duba abubuwan da suke kan teburin. Misalin 12pm Yunus yai knocked ya turo kofar ya shigo.
“Halima ko?”
“Yeah”
“Kuna da meeting yau, ba ki duba takardun ba”
“Na duba amman ban gane ba, ni? Kasan ni bana zuwa meeting”
“Idan general ne dole da ke saboda mail din kamfanin na is under your control”
“A ina ake meeting din?”
“Karma hotel, ku kadai ake jira tuni sun fara taronsu ma”
Na mike tsaye da sauri.
“To ni da wa zan je?”
“Ki dauki Laptop dinki ki samu Oga a waje, yana mota yana jiranki”
Na dan ji wani iri, da shi kuma?
“Ba ni da Laptop”
“Shi zai baki”
“Okay”
Na fada ina daukar jakata na rataya sannan na nufi kofar fita ina gaba yana baya sai duk na ji na tsawwala ba dadi namiji ya saka ka a gaba ban san mi yake kallo a bayana ba duk kuwa da kasancewar na san abayar jikina bata matse ni ba sai dai hakan be saka na natsu ba har sai na na saka shi gaba ni na koma bayansa ina tafiya.
A harabar kamfanin na samu motar Ahmad fake ina fitowa sai direban dake gaban motar ya fito ya bude min motar, abunda ba a tana min ba, kuma ban tana ganin Ahmad wani yana jan shi a mota ba sai dai shi yaja amman yau hakimce yake gidan baya ya saka suit dark blue, kallo daya na masa na dauke kaina a yau kam kyaunsa har wani tsoro ya bani ko dan ban taba ganinsa hakimce kamar haka bane? Ko kuwa dan ban tana ganinsa da kalar tufafin bane oho, sai kamshin turare yake.
“Ina kwana...”
Ya furta min so calmly kamar ba shi ba, ganin cewar ni ban gaishe shi ba, wata kalar kunya naji sai kaina yai girma kamar dutsen dala.
“Ina kwana...”
Na mayar masa, be amsa ni ba ya maida hankalinsa gefen titi, har muka isa be kalli inda nake ba, nima kuma ban sake kallonsa ba har muka isa. Direban ya zagaya ya bude masa nikan ban jira a bude min na bude na fito daga motar mai sanyin ac wacce har ta fara saukar min da mura.
Wata yar karamar laptop direban ya miko min da pen sai wani littafi mai kamar diary, sannan dauko wata jaka wacce nake kyautata zaton ta Ahmad ce yai gaba ni da Ahmad din muka rufa masa baya, kana ganin kofar shiga dakin taron kasan taro ne na manyan mutane, domin an zuba securities a gurin gwanin sha'awa. Na yi zato ko sai mun yi musu wata magana ko nuna wani abun sannan su bar mu shiga ga mamaki ne sai kawai na ga an bude mana kofa, daf da zamu shiga cikin gurin Ahmad ya risuno saitin kunnena ya rada min.
“Ki kashe wayarki”
Yana fadar hakan yai gaba abunsa ya shiga cikin gurin, ya bar a bakin kofar tsaye da mamaki, to miye wani abun mamaki? Wata kila baya son aji muryarsa ne shiyasa yai haka. Umarninsa na bi na dauko wayar na kashe sannan na maida ta a jaka na shiga cikin gurin.
Ina shiga na fara rabon ido, babu mutane sosai amman kusan rabin taron duk turawa ne, wasu a taeburin manyan baki wasu a teburin masu daukar darasi irinmu, ga wani katon majigi da ke saman gurin wanda da shi suke ta nunawa mutane abubuwansu.
A zagayayyen tebur muka zauna ni da shi, sai dai kujerar tawa tana fuskantar tashi ne kamar yadda shi ma yake fuskanta ta, amman idonsa yana gurin abunda ake nunawa a majigin.
Nikam sam hankali baya gurin abunda ake fada yana gurin mutanen dake gurin ne, idan na kalli wannan na kalli wacan har na kallo Ahmad, da idon yai min alama da na maida hankalina gurin abunda ake, ba musu na tattara hankalina na maida gurin mutanen, muna zaune a gurin har kusan karfe daya. Direban dazun ne wanda ya kawo mu ya sake shigowa gurin ya nufo inda muke zaune ya kai bakinsa saitin kunnen Ahmad ya fada masa wani abu. A take na ga yanayinsa ya sauya, sai ya tashi tare da diraban suka fita, ni dai ina zaune a gurin har ya dawo a yanzu kuma baya kallon kowa sai ni, just me and me alone, har aka tashi daga taron 1,30pm bayan an bi ko wane tebur an dora takeaway da ruwa da lemu.
An yi mana hoto da turawan da kuma sauran wadanda suka zo taron, sannan mutane suka fara watsewa, nima na tashi ganin ogan ya tashi shi be dauki komai ba daga abunda aka kawo masa na sha da ci sai direbansa ne ya dauka ni kam na kai hannu na dauki abuna, ko ruwan ban bari ba, balle kuma yar karamar takadar da aka dora mana sama wacce nake kyautata zaton kudi ne. A kofar fitowa suke bawa mutane memo da magazine da kuma calender.
Sai da muka shiga motar sannan ya kalleni ya kalli kayan hannuna har na ji yar kunya.
“Ina wayarki?”
“Tana cikin jaka”
“Mu gani”
Ya zuro min farin hannunsa.
“Na kashe ta fa”
Ganin be janye hannun ba kuma be dauke idonsa daga kaina ba yasa na saka hannu a jakar na dauko wayar na mika masa, a zato na dubawa kawai zai yi ya bani sai na ga ya zura ta aljihu, kamar nai magana sai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 55