Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai kallon cikin idona yake. “Why are you crying?” Ban ma san da hawayen sun zubo min ba sai da yai maganar, shiru nai ban amsa shi ba. “Lims do you love me....?” “Ban sani ba...” Na fada da iyakar gaskiyata, wasu hawayen na sauko min, halshensa na ji a saman kunci na yana lasar hawayena. “Wannan hawayen mai sanyi ne, ni na san kina so na Lims....” Ya fada bakinsa na taba nawa murya can kasa kasa kamar mai rada, saurin lumshe idona nai muna ta shakar numashin juna.... ___________________ Ayi hakuri two days mun yi biki shiyasa ban samu damar typing ba 🙏 Gashi nan na yi muku 5k words na biya bashi 🏃🏻🏃🏻🏃🏻 *Where are are the classy ladies 🤔 mata yan kwalissa ga awwaba scent tazo maku da hadadun turarukan wuta humra body oil turaren jiki na tsuguno da kayan gyaran jiki kaman dilka scrub organic soap 🧼 da sauransu akan farashi daidai aljihu say no karnin da warin damshi na lokacin damina zaaiya samunmu a wannan lambobin 09137294470 08034236800* 7/21/21, 11:10 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 5️⃣8️⃣ Raba jikina nai da nasa. “Mutane za su iya ganinmu” Be ce min komai ba yaja hannuna ya karasa gurin motar da ni ya bude gidan baya na shiga sannan shima ya zagayo ya shigo ya rufe sannan ya rika hannayena ya soma murzawa yana kallon fuskata. “Ban miyasa nake jin ki a zuciyata fiye da kima ba, ina jin cewar na fi kowa dace a duniyar nan, a yanzu bani da wani buri sai na aurenki kuma ya cika ina son sosai, irin son da bana jin wani namiji ya taba miki shi, bana tunanin akwai namijin da ya fi ni son ki” Ya sumbanci hannun nawa. “Kamin na aureki, idan wani ya fada min zan aureki zan karyata shi kuma na fusata, amman a yau da Yayan mahaifin yai min albishir da cewar an daura aurena da ke sai na rasa inda zan saka kaina dan murna, na rasa abunda zan bashi na kyautata masa na goron abunda ya fada min, na gode da kika amince min na gode da kika ba ni damar shiga rayuwarki, na gode da kika karbe ni a duniyarki” Ya karasa tare da kai hannunsa yana shafa fuskata, sai kuma ya jani jikinsa ya kwantar da ni ya rumgume ni sosai kamar ba gobe. “I love you so much Lims” Ya fada calmly kissing my forehead, dayan hannunsa kuma yana mutsa yan yatsun hannuna. Mu kai shiru kamar babu mu a cikin motar baka jin komai sai saukar numfashinmu, can ya saka hannunsa ya dago kaina ya dora bakinsa a saman nawa kamar zai tsosa sai kuma ya bar shi a haka yana ta kallon idona da na rufe, ji nai an busa min iska a saman idon hakan yasa na bude muna hada ido sai ya hade bakinsa da nawa, a hankali yake kissing din lisp dina sai kuma ya cire bakinsa a nawa ya kai gurin tsinin hancina ya tsosa sannan yai kissing forehead dina ya sake rumgume ni a kirjinsa tsantsa yana sauke ajiyar zuciya. “What else i can say more than Al-hamdulillah, you're finally mine” Muna haka na hango mota ta faka a kofar gidanmu, ina ganin motar na san cewa Abdallah ne, Ahmad kam be gane shi ba har sai da ya fito daga cikin motar ya jingina yana lasa. Wayar da ke hannuna tai ringing kiransa ya shigo, kallon wayar nai na kalli Ahmad sai na kasa daga kiran. “Me ya zo yi?” “Wata kila yana son magana da ni ne” Bude motar yai yace min na fito muje, abunda ban so ba ke nan domin nasan ganin mu a tare da Ahmad ba karamin bata ran Abdallah zai yi ba, ba zan iya musa ma Ahmad ba kamar yadda ba zan so Ahmad yai abunda zai kara batawa Abdallah rai ba. Ya rufe motar sannan ya rika hannuna muka nufi gurin da Abdallah yake tsaye, daga inda yake tsayen ya dago idonsa yana kallon mu har muka iso, na kasa ce masa komai shi ma be ce min ba Ahmad ma be masa magana ba, sai kallon juna suke kana ganinsu kasan da akwai abunda kowa ya aje kasan zuciyarsa, Ahmad murmushi yake yana ta lilo da hannuna duk yadda na so na kwace hannun sai ya ki saki, na yi tunanin Abdallah zai yi wani abun ne ko kuma ya fada masa bakar magana amman ga mamakina sai ya sakar wa Ahmad murmushi ya mika masa hannunsa. “Congratulations, that's good daman ka ce zaka nuna min ko waye kai a gurin Halimatu ko? Na gani yanzu ina taya ka murna” Sai da Ahmad ya kalli hannunsa nasa sannan shima ya mika masa nasa. “Thank you” A lokacin ne Abdallah ya kalleni da murmushin a fuskarsa yace min. “Ina taya ki murna” Ni kam kasa amsawa nai sai Ahmad ne ya sake ce masa “mun gode” Sai ya bude motarsa ya shiga yai ribas ya juya ya bar mu a gurin tsaye ina bin motarsa da kallo. “Kun taba yin wata magana ne da shi?” “Eh lokacin da mahaifiyarsa ta saka aka kamaki ba, yace min wai ni waye ne a gurinki da har zan nuna masa isa, sai na ce masa zan nuna masa ko ni wanenen nan da dan lokaci” Na yi shiru bance komai ba, hakan yana nufin shi da Abdallah sun yi sa'insa kenan, wata kila shiya saka Abdallah ya nemi na bar aikin a kamfanin dan ya nuna masa ya isa da ni. Ji nai ya saki hannuna ya juyo gabana yana kallona. “Bari na barki ki huta, ki yi list din duk abunda kike so kin san yanzu hakkinki da na yaranki yana kaina, da safe zan zo na karba” Ya fada sannan ya shafa fuskata, har ya juya sai kuma ya juyo. “Ba ni line wayarki” “Why....” “Just” Ban musa masa ba na ciro line ya mika masa. “Amman akwai numbers din yan'uwa da kawaye na a ciki” “Okay idan na dawo gobe zan zo da sabon line sai ki dauki numbers din a ciki” Kai na gyada masa sai ya juya can kuma ya sake juyowa a karo na biyu yai min alama da na zo, sai na karasa kusa da shi kamar yadda ya bukata, saitin kunnena ya kai bakinsa ya rada min “Muje ki min sallama” Ko be fada kai tsaye ba na san abunda yake nufi maybe he want to kiss me or hug, ko something like that, ni kuma bana son mutane su fara saka mana ido ace mun fara yin abunda be dace ba a bainar jama'a. “Akwai mutane fa” “To muje zauren gidanku” “Nan ma za a iya saka mana ido, ka bari har ka dawo” “Ba zan bari ba....” Ya fada yana wuce ni ya nufi cikin zauren gidan a dole na bishi a baya, ko da na shiga har ya jingina da bangon gurin yana jiran shigowata, hannunsa ya kai ya kama kwankwaso na ya rike ya hade fuskarsa da tawa. “So this woman here is mine” Ya fada da sigar da babu wanda zai ji sai ni, ni dai hankali yana kan kofar gida kar wani ya fito daga cikin gida ya gan mu. Bakinsa ya saka cikin nawa ya tsosa iya yadda yake jin ya samu natsuwa sannan ya sake ni, kamar an masa shocking haka ya zabura da karfi ya bankare sai kuma ya runtse ido, kamin ya bude su a hankali ya kalleni. “Good night Sweetheart” Ya fada yana kissing kumatuna sannan ya juya ya fita daga zauren, hakan kawai na samu kaina da son kallonsa, haka n leko a zaune ina ta kallonsa har ya karasa gurin motarsa ya bude ya shiga yai mata key ya fice. Wata irin natsuwa da sakewar zuciyata da nishadi ne suka ziyarce, rumgumar da yai min sai na ji kamar mu kasance a haka har a bada, gaba daya jikina kamshin turarensa yake murmushi ya maye gurbin hawayen da nake, ina jin a raina kamar na yi dace duk da ban tabbatar din ba, sai a yanzu nake jin wata irin natsuwa da farincikin amincewa da nai, wata kila dazun ba kukan bakinciki nake ba, kukan farinciki nake ban gane ba, da kuma yadda abun ya zo min a bazata. “I love you so much Lims” Na yi murmushi ina jindadin tuna kalmar daya fada min a dazun, har yanzu bana jin ina son sa kamar yadda bana jin tsanarsa ko kasan a raina, amman am happy I'm now officially Mrs hakan ma wata martaba ce babba, na juyo na nufo cikin gida, sai da na gama sallah isha'i sannan na bude ledodin da ya kawo min, kaza ce babba har guda biyu da lemu sai kayan tea da katon burodi da kuma ku a cikin farar takarda 20k. Washe garin ranar na tashi cikin walwala ba laifi ina ta jin nishadi a raina, bayan su Namra sun tafi Islamiya sai ga Aminu ya sallamo ya shigo cikin gidan, kamin ya karaso falon Mama nai saurin dauko Hijabinta na saka ya rufe jikina sannan na dawo falon na zauna. Ya shigo da sallama na amsa masa ina murmushi kamar ba ni ba. Shi ma murmushin ne kwance a fuskarsa sai dai ba irin murmushin nan na jindadi ba irin murmushin nan mai kamar na dole. “Ina kwana” “Lfy kalau” Ya amsa yana ta kallona kamar be taba ganina ba, a raina na raya cewar da ace Ahmad nan Aminu yake min kallon nan da yanzu wani abun ya faru, ban san lokacin da wani murmushin ya subuce min ba har sai da na ji Aminu na tambayar. “Me kike yi wa murmushi?” “Ba komai” “Na ga alamar dai kina cikin farinciki” Na yi kasa da kaina ban ce masa komai ba. “Daman na zo ne na taya murna, na ji abunda ya faru ance kin yi aure jiya, shine nace abun babu gayyata” “Nima abun ya zo min bazata ne shiyasa” “To congratulations Allah yasa alheri Allah yasa wanda zai rike ki amana ne” Yanayin yadda maganar ta fito daga bakinsa kana ji kasan ba dadi ya fade ta ba. Ni dai na amsa da Amin. “Nima na zo na fada miki ne zan maida Murja” Kallon Mamaki nai masa. “Murja da wacce ta ci amanarka?” “To ya za'ayi? Nima ba amanar wasu na ci ba? Kin mutum mai irin matsala ba ko wace mace yake aure ba, kuma idan nace zan nemi mace mai irin ciwona na aura, ban fallasa sirrina ne kawai, kara dai mu rufawa juna asiri ni da ita mu yi zama na tsakani da Allah” “Allah yasa hakan shi ya fi alheri” Na fada cike da tausayawa. “Amin ina fatar dai yarana ba su san da maganar nan ba” “Ban fada musu ba, kuma ba zan taba fada musu ba In-Sha-Allah” “Na gode” Ya ciro kudin da za su kai 30k ya miko min. “Ga wannan kwai siye wani abu” “A a muna da komai” “Haba dai hakkina ne ai” Na kai hannuna na karba sai ya sakar min murmushi. “Ina taya wanda ya aureki murna, hakika ya samu mata mai kawaici, mai hakuri, kuma kyakkyawa” A yau Aminu da kansa ne yake fadar ina da kawaice abunda be taba fada ba a lokacin da nake gidansa, a yau shi da kansa yake kina da kyakkyawa kyau da ya kasa gani a lokacin da nake kusa da shi. “Ina fatar mutumen da kika aura zai rike miki yaranki” “Ka yafe mushi su ne?” “A irin wannan condition din dole nai nesa nesa da su, kuma kin san masu irin matsalar mu musamman maza ba wani dadewa suke a duniya ba, bana son na mutu na barki da dawainiya, ina son ko da zan mutu at least ace kina samun wanda zai taimaka miki wajen kula da su, maybe ma su ne kadai yayan da Allah zai ba ni a duniya i don't know” Ya karasa hawaye na cika idonsa. “Cuta ba mutuwa ba ce Aminu...” “Tawa ta mutuwa ce Halima, kawai dai ki yi ta saka musu albarka” Ya mike tsaye. “I wish you all the best” “Na gode” Murmushi yai min as respond sannan ya saka kai ya fice, ni kuma na tashi na nufi dakina na saka kudin a cikin jakata, sannan na fito na fara gyare gyare dakina da dakin Mama daman Aisha ta share dakin Inna. Da azahar aminiyata Hajara ta shigo gidanmu da murnarta kamar zata cinye ni, wai ita babu abunda yai mata dadi kamar yadda Ahmad yafi dukan mazanjen da na aura rufin asiri, domin da ce wani makaskanci na aura da yanzu makiya sun saka min dariya amman duk wanda yaji ga wanda na aura sai yace hakurin da nai ne Allah yai min wannan sakamakon, ni kan har ta ci ta shude ban ji komai araina ba wai dan Ahmad yana da arziki, wata kila saboda dukiyar tasa bata gabana ne, ni yi mamakin inda ta ji domin ban fada mata ba gashi line ma yana hannun Ahmad balle nace ko kiranta nai, ashe abun har ya fita da goron da aka raba a makota da kuma can family mu wannan ya fada wancan jin babban mutum ne nn da nan maganar ta yadu ita ma gurin wata kawarta tace wacce ita kuma yar'uwarmu ce. Sai yamma ta tafi gida, bayan Abban Afrah ya zo daukarta da kansa har da shi yake min murna wai ya ji na yi aure Allah ya sa alheri, a wunin ranar na damu matuka da ban ji daga Ahmad ba, duk be wani saba min sosai da kira ba amman a yanzu ai ni matarsa ce ya kamata ace ya kira ya ji tashina, ko da yake line yana can hannunsa kuma ban san uzurinsa ba. Can da la'asar sai ga Siyama ta shigo gidanmu, sai da ta gaisa da kowa sannan ta bukaci ganina aka fada mata ina dakin Inna, ina zaune a dakin ta shigo sanye da atamfa mayafinta a hannunta tare da jakarta, da sauri ta zo ta rumgume ni. “Matar Yaya” Na yi dariya ina dan jin kunyarta sai ta zauna kusa da ni muka gaisa cikin far'a. “Hajiya tace tana gaishe ki” “Ina amsawa” “Yaya yace ya zo na karbi takardar idan kin rubuta” Sam ni na ma manta da zancen wani rubuta abubuwan da muke bukata sai a yanzu. “Wallahi ban rubuta na manta” “Ayyah za ki iya rubutawa a yanzu?” “Ko kuma mu bari har gobe ko jini saboda ko na rubuta wani abun zan iya mantawa da wani a yanzu” “Okay to ba matsala” Ta saka hannunta a jaka ta dauko sabon line ta miko min. “Ga line yace ki saka zai kira ki” “Okay lafiya yake” Na tambaya bayan na karba. “Lafiya kalau” Sai ta mike tsaye “Ni zan tafi in-law Allah ya baki ikon rike min brother na da gaskiya, because yayana yana son ki sosai, Hajiya da ni duka muna son ki Allah yasa kar ki ba mu kunya” “Allah ya bani ikon kula da ku duka” Na fada ina murmushi sai ta amsa da amin ta fice rike da makullin motarta. Ban tashi daga inda nake ba na kira Aiman ya dauko min wayata na saka line ciki, ina kunnawa kiransa na shigowata sai nai picking na kara a kunne tare da sallama. “Tun dazun nake ta kiran line ne ina son ki saka na ji muryarki, ya kike?” “Ina lafiya, Siyama ta kawo min shi yanzu nan” “Na sani kin bata list din” Yanayin yadda yake amsa min kamar a wahale, ni kuma na amsa masa cikin sanyi jikina. “Aa na manta ban rubuta ba sai gobe” “Ba ki da matsala Queen, za mu yi waya anjima” Daga haka ya kashe wayar. ABDALLAH POV. Har a yanzu bana ganin laifin Halima a iya abunda yake gani Ahmad kamar ya mata cilas ne tun da gashi abun daga sama suka ji daurin auren. Zai iya rasa komai ya hakura ban da Halima, in his own life ya san Halima ba son Ahmad take ba, kuma yana ganin Ahmad kamar ba zai iya rike Halima da gaskiya. Duk kuwa da irin kirarin da mahaifiyarsa take na cewar wai daman can Halima haka take so ta bata alakar da ke tsakaninsa da dan'uwansa yanzu kuma ta hana dan'uwansa aure kuma ita ta yi aurenta, a yanzu babu abunda Hajiya bata sani ba na abunda Abdulhamid ya aikata da alakarsu da Ahmad amman saboda bakar kiyayay ta kasa daina ganin laifin Halima, a ganinta ai saboda ita asirin Abdulhamid din ya tonu gashi ta kassarasa masa rayuwa ita ta gyara nata. Abdulhamid ma da Hajiya ta kai masa labarin auren Halima kam yayi farinciki da ba Abdallah da aura ba duk kuwa da ya san Hajiya ba zata bari ba amman auren Abdallah zai fi komai tsaya masa a rai idan har ace haka din ta kasance. Babu abunda yafi yi ma Hajiya ciwo kamar sanin cewa mutunen da Halima ta aura a yanzu yafi yayanta rufi asiri, babu abunda take fata take kuma son ganin kamar lalacewar auren ko kuma Halima ta shiga wani hali. A ranar da za a fara shiga kotu da Abdulhamid da Abraham da wasu mutane hudu babu irin kukan da Hajiya ba tai ba sai ta ji kamar ta hade zuciyata ta mutu dan bakinciki. AHMAD POV. A ranar da ya bar gidansu Halima be iya kai kansa gida ba, saboda wani irin azababben ciwo da ya rika jin yana masa yawo a jiki, a dole ya faka motarsa gefen titi ya kira driver din gidansi yace ya zo ya tuka shi. Da suka isa gida sai ya wuce part dinsa ya kwanta yana ta jin abun na masa yawo a cikin jiki sai dai hannunsa ya fi ko'ina yi masa zafi domin yai masa nauyi kuma ya masa kamar an dora shi akan garwashin wuta. Duk yadda yake da juriya da iya dakewa a daren kasa hakuri yai idan yai tsaye ya zauna ya tashi haka yai ta yi har garin Allah ya waye. Da asuba ma kasa sallah asuba yai saboda bala'in ciwon da hannun yake masa, gumi sai ke to masa yake ta ko'ina kamar wanda maciji ya tsara, kamin haske ya dan shigo Hajiya ta shigo part dinsa ganin shi be fito ba har jin yai kamar ba zai rayu ba. Tana ganin halin da danta yake hankalinta yai mugun tashi da taimakon mutanen gidan suka saka shi mota aka nufi asibiti da shi, wani abun mamaki da aka yi kwaje kwaje aka duba hannu ba a same shi da komai ba, amman Ahmad azabar ciwo yake masa sosai idan ya samu sauki sai idan an masa allurar kashe ciwo sannan zai ji abun ya kwanta masa amman ko allurar bachi aka masa baya jin sauki domin ciwon baya bashirin bachi. Sai dai likitocin sun fada masa yawan yi masa allurar matsala tun da ba aiki za ayi masa ba, hakan yasa shi da kansa ya shirya fita waje ganin likita, ko da wasa be fadawa Hajiya cewar tun daga lokacin daya gaisa da Abdallah abun ya sameshi ba domin baya son tai blamed Lims dinsa, secondly kuma ya hana kowa ya fadawa Halima halin da yake ciki saboda kar hankalinta ya tashe kuma kar canfin da take na cewar duk wanda ya kusance ta sai wani abu ya same shi ya tabbata, yana son ganinta amman ba dama sai dai ya kirata a waya, ko video call be son yi da ita saboda kar ta fahimci halin da yake ciki. HALIMATU POV. Wasawasa aka kwashe kwana takwas ban saka Ahmad a ido ba hakan kuma ba karamin damuwata yai ba, domin sai na ji kamar na saba da shi a kullum ne, zai kira ni a waya da safe da rana haka ma da dare amman hakan be wadatar ta da ni ba. Ya aiko an karbi list din duk abunda na rubuta an siyo har ma da wanda ban rubuta ba duk an siyo kuma ba kadan ba da yawa aka siyo wanda zai dauke mu tsawon lokaci muma amfani da shi. A iya sanina yadda Ahmad yake nuna min kauna kamar ba zai iya kwana biyu be saka ni a ido ba balle kuma yanzu da nake matarsa, amman miyasa ya dauke min kafa tun daga wacan ranar? Ko dai shi ma mahaifiyarsa bata so? Ko kuma wani abun ne? Ina tsaka da tunanin nan wayata tai ringing ganin kiransa ne yasa nai hanzarin dauka. “Hey Babe na ykk” “Ina lafiya” “How are my kids?” “Suna lafiya” “Na kira na ji muryarki, kuma na miki albishir cewar Kabir yana ta samun sauki ana tunanin end of this month ma su sallame shi, domin an masa tiyata an kwashe jinin daya taba kwakwalwarsa yanzu sun dora shi akan magani ne” “Ma-sha-Allah Allah ya saka da alheri” Na fada cikin rashin far'a kamar ba labarin nake son ji ba, ban san abunda ya hana ni jindadi ko murnar samun lafiyar Kabir ba bayan kuma na dade ina fatar samun haka. “And... I think gobe ko jibi zan je United Kingdom wato London for some works” Na y shiru ban ce komai ba, domin ban san abunda zan ce ba gaba daya jikina sai ya ba ni kamar ba lafiya ba. “Idan akwai abunda kike bukata ki fada min” “Kai nake bukatar gani Ahmad i need to see you” Daga can cikin wayar ya jiyo sautin murmushinsa mai kama da dariya. “Wow i got lucky Matata tana so na da yawa haka nan, idan na dawo zan zo In-Sha-Allah” “Ba zaka zo mu yi sallama ba?” “Ba zai yiyu ba ne yanzu haka ina Abuja, daga can zan wuce i'm ban fada miki ba, but karki damu next time tare za mu tafi In-Sha-Allah” Jin na yi shiru yasa shi cewa. “Kin ji Baby na? Are you there” “Allah ya tsare” “Amin i love you” Na aje wayar ina ta kallon screen din, idan har da gaske wani aikin ne zai kai shi da sai yaje da ni, ko dai shi ma mahaifiyarsa ta masa katanga da ni ne? Ko ba da amincewarta ya aure ni ba? Tun da akai auren ba ban taba gaisawa da ita ba, ni kam dai ina rashin dace da in-laws, but wait miyasa zan zargi mahaifiyarsa? What if ba shi da lafiya? Domin a duk lokacin da nake waya da shi ina jin muryarsa ba a yadda na saba jinta ba. A take gabana ya fadi hankalina yai mugun tashin da sauri na dauki wayar na aika masa da kira amman haka tai ringing har ta katse be dauka ba..... __________________ Ina yan Team Kabir kun ji ya fara jin sauki 💃 Jiya wata yar Team din Abdallah tana ta min rankwashi a kai 😢😪 To ai ba san maci tuwo ba sai miya ta kare 😥🙄 *Where are are the classy ladies 🤔 mata yan kwalissa ga awwaba scent tazo maku da hadadun turarukan wuta humra body oil turaren jiki na tsuguno da kayan gyaran jiki kaman dilka scrub organic soap 🧼 da sauransu akan farashi daidai aljihu say no karnin da warin damshi na lokacin damina zaaiya samunmu a wannan lqmbobin 09137294470 08034236800* 7/21/21, 11:10 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 5️⃣9️⃣ Kwance take a dakinta tana kallon windows din dakinta da suke bude, pillow na rumgume a kirjinta babu abunda ke fita daga idonta sai hawaye masu zafi.   Mai aikinsu ce Hindatu ta turo kofar dakin ta shigo da sallama. “Assalamu Alaikum, Siyama Hajiya na nemanki” “Ki ce zan zo” Ta amsa ta ba tare da ta juyo ta kalleta ba. After like one hour Hajiya ta turo kofar dakin ta shigo. “Siyama....” Sai a lokacin ta fara kokarin yin kamar bachi take, hakan yasa Hajiya ta karasa kusa da gadon ta zauna leken fuskarta da hawaye ya gama yi mata kwalliya. “Miye abun kuka kuma? Me yake damunki?” Juyowa tai da kyau ta kalli Hajiya wasu hawayen na cika mata ido. “Hajiya...” Sai kuma tai shiru ta tashi zaune tana matsar yatsun hannunta. “Ba ki fito kin ci abinci ba, ko yau ba kya zuwa makarantar ne?” “Hajiya bana son na sake rasa kowa” Ta fada cikin hawaye. “To wa za ku rasa?” “Ban sani ba, amman yanzu idan ciwo ya kama wani a cikinmu sai na rika ganin kamar zan rasa shi ne, i don't want to be alone....” Ta fashe da kuka, tana kwantawa jikin Hajiya. “Babu abunda zai samu yayanki zai samu sauki In-Sha-Allah, ki daina tada hankalinki kin ga nima kina daga

Chapter 48 of 55