“Ana ta shirye shiryen biki har yanzu baka ce komai ba”
“Allah ya sanya alheri”
Ya fada a takaice, sai kuma yai shiru kamin ya sake kallonta.
“Hajiya na yi wani laifi”
A take ta dago kai ta kalleshi da sauri.
“Mi kai?”
“Kin min tsakani da Halima, tun daga lokacin ban sake kula ta ba, sai kwana goma sa suka wuce, na ganta a hanya tana tafiya da tufafin da be dace ba, hakan yasa na tsaya na dauke a motata saboda kare mutuncinta, ki yafe min dan Allah”
“In ban da kai da abun ka, miye amfanin kare mutuncin macen da bata san mutuncin kanta ba, da wata ce ai ba zata yi shigar banza ta fita ba, talla take yi kenan Allah ya kyauta”
Yawu ya hade da karfi da ba Hajiya ba ce da be lamuncin jin wani kalami marar dadi daga bakin kowa ba akan Halimatu idan ba zai iya cewa komai ba to ba zai saurara ba.
“Wato dai na gane ba zaka iya fita daga tsafgar yarinyar nan ba, saboda ka samu salama kuma ku samu fahimta da dan'uwanka yasa na yi muku tsakani amman hakan be wadatar ba, tun da ga shi nan har yanzu ba ku jutuwa da juna, kuma ka kasa daina kulata, har yanzu dai tana nan cikin ranka, yarinyar da ta haifarda rashin jituwa tsakaninku? Yanzu shirye shiyen auren dan'uwanka ake amman babu ruwanka komai sai dai ka bishi da ido haka ake? Ku uku kawai Allah ya bani idan ba ku hada kai ba ya kuke son zama?”
“Ba daga ni ba ne Hajiya, Abdulhamid yana ta ganin laifina ne har yanzu, ko magana nai masa sai idan yaga dama zai amsa ni”
“To ai dole ya rika maka haka, taya zaka rika bibiyar matar da ya saka? Wacce ta zama makiyiyarmu? Ta ruguza rayuwarku?”
Kallon mahaifiyar tasa yai ya dauke kai, wani lokacin idan tana yin abu kamar wacce bata taba karatu ba, ne san abunda yasa son zuciya yake rinjiyarta ba. Be ce sake ce mata uffan ba har tai fadan ta gama, sannan yai mata sallama ya fice zuwa gidansa. Da dan kuzarinsa ya shiga gidan yaransa na harabar gidan suna wasa kasancewar yau Thursday after school babu islamiya a yau. Da gudu suka zo suka masa oyoyo ya daga su sama yana dariya ya sauke sannan ya rika hannunsu suka shiga cikin falon, a falon ya sake musu hannu ya nufi kitchen gurin da yake jiyo motsin Suwaiba. Daga baya ya rumgumeta yana sumbatar gefen kumatunta.
“Madam me kike girka mana”
“Me nake girkawa dai ni da yarana kai da bazawarar ka ta dauke maka nauyin cin abincin gidana”
Ta fada tana yatsina fuska. Sai yai murmushi rabon da Halima ta aiko masa da abinci tun ranar da ya dauko ta a mota, ya juyo da ita tare da saita idanuwansa cikin nata.
“Kin ga abunda ke hada ni da ke mita, da rashin yarda, wanda ya baki labarin tana aiko min abincin be baki labarin ta daina ba?”
“Kana kareta ne kawai, amman yq za ayi ta daima bayan ta fara kuma silar hakan ka daina cin abincin rana a gidanka? Daman can ai irin yan barikin zaurawan nan sun fi kowa iya karuwanci”
“Abunda take min kyautatawa ce kawai a matsayina na dan'uwanta kuma kin fi kowa sani Halima na tsattsiya ce”
Yana fadar hakan ya sake ya juya ya fice daga kitchen din fuskarsa na nuna rashin jindadin kalaman Suwaiba, tabe baki tai ta bishi da kallo haushi, ita kadai ta san abunda take ji ta rasa gane wani irin so yake ma Halima? Ko da yake ba laifinsa ba ne laifin Halimar ne daman shi namiji ai kamar yaro ne, duk inda aka bi da shi can yake, ta dade tana masa maganar abincin da Halima take aika masa a office duk kuwa da kasancewar ya sha nuna mata cewar baya son maganar, ta hanyar Yayanta da ke aiki Asibiti a matsayin nurse ta samu labarin.
“Sai na ci miki mutunci Wlh, sai na bayyana halinki a gaban kowa, daga lokacin zan gani idan za ki sake bibiyar Abdallah banza ballagaza kawai, in banda jahilci taya zaka auri yaya kuma ka koma bibiyar kane, kaji iskanci, sai an tozarta ki Wallahi”
Ta fada tana kwafa sannan ta juya ta cigaba da aikinta...
AHMAD POV.
tukin motar kawai yake amman hankalinsa yana can ya tafi gurin labarin da ya ji, sai a yanzu ya fahimci a kashi 100 na kaddarar rayuwa shi ko kashi daya be dauka ba, domin shi ya da mata sai mahaifi kawai ya rasa, amman ita ta rasa abubuwa da yawa a ciki akwai farinciki akwai gata akwai mutunci, a haka kuma har tana filin sake daukar wani kalar bacin rai a zuciyarta, tunawa yai da yadda take yawan masifa wata kila saboda tana cikin damuwa ne, ta yi kokari ta jajirce da har bata haukace ba ko kuma wani ciwon ya hana ta tashi kamar yadda shi a yanzu ciwon zuciya yake neman kai shi kasa. Tunawa da yai da irin abunda yai mata a wacan lokacin da kuma kadeta da yai yasa jin wani iri, anya mai irin wannan rayuwar ya cancanci a sake shimfida masa wata bakar magana ma balle har a aikata masa wani abu marar dadi? An keta mata an keta haddin yarta shi ya fi komai tsaya masa a rai, see yadda yake kyamar auren matar da ta auri wani auren sunna ma, to ita faya zata ji an yi mata da karfi? And ayi wayarta yar da bata san komai ba? And a lokacin kwatar hakkin yarta mijinta ya saketa bayan kuma kanensa ne ya ketawa yar haddi, wani irin mugun miji ne wannan? Baya son ta aureta ne? Ko dole akai mata? Aunata yake a matsayin Siyama, ya zai ji idan wani ya taba masa kanwa kamar haka? And the most saddest thing bata da mai tsaya mata tun a wacan lokacin, she's the first born ya tuna a cikin wasikarta ta fadi hakan, and the other sad part is ya kara mata damuwa da zarginta da mutuwar Namra, sai a yanzu yake gode Allah da Hajiya ta hana shi daukar mataki a kai da ya cutar da innocent soul.
“Gwarzo... Ba gida za mu je ba?”
Sai a lokacin ya tuna ba shi kadai yake a motar ba, Hajiya tana baya tare da shi.
“Gida za mu je”
“Na ga ka dauki wata hanyar ne”
Sai a lokacin ya lura, bakinsa ya cikawa iska ya busar sannan yace.
“Zagoyo zan yi”
“Okay, bikin nan ya kayatar sosai fiye da yadda aka saba yinsa a shekara, wai ka gane wacce ta ci gasar nan kuwa?”
Hajiya na yin maganar zancen yaranta ya fado masa, na cewar idan ta ci zata biya musu kudin makaranta.
“Wow....”
Ya furta a fili yana jinjina irin jarumtarta da karfi zuciya. Hajiya kuma sai ta dauka da ita yake sai kawai ta cigaba da shimfida masa labarin.
“Wannan ce fa mahaifinyar su Namra yarimyar da ke tare da Baby Namra, ashe har yanzu bata manta da ita ba, tace idan ta ci sadaukarwar ta Baby Namra ce”
Be ce komai ba sai tukin yake a hankali yana jin wani abu na masa yawo a zuciya na rashin jindadi har suka isa gida.
“Labarin ma da aka karanta ina kyautata zaton na mahaifiyar yarinyar nan ne Halima.... ”
“Halima...... ”
Ya maimaita sunan yana kokarin juyowa ya kalli Hajiya, be taba sanin sunanta ba sai yau, duk kuwa da aikin da take a kamfaninsa, sunan da ya fi ko wane suna yi masa dadi a duniya, har yanzu yana ganin yadda ya wulakanta a kamfaninsa a lokacin da ya bukaci a canja mata position sai a yanzu yake ganin hawayen da take da irin rokon da ta soma masa tana kuka tana fadar dan Allah kar ya koreta tana bukatar aikin nan, and in the restaurant a vip 1 a lokacin da ta zauna a saman kujerar sa matarsa take zama, he remember wadansu kalamai da ta fada, wacce take nan ta yi sa'ar ba kamar ita ba, daman duk wannan take nufi?
“Oh ya rabb”
Ya furta a fili gaba daya zuciyarsa ta daure ta yi nauyi da tausayin Halima. Can ya tsinkayo Hajiya na kokarin fita motar tana fadin.
“Domin labarin da mahaifiyarta ta ba ni, yayi daidai da abunda aka fada a gurin nan kuma ga shi taje tare da yaran, ina jin labarin na gane ita ce, cikin ma uwar bata fada min duka ba, tun da wani abun sai a yanzu na ji, amman matar nan ta ga rayuwa Wallahi ban san lokacin da nai kuka ba”
Fitowa yai daga motar yana kallo mahaifiyarsa wacce ke sanye da tsadadden lace.
“Amman Hajiya ba ki taba fada min ba”
Hajiya ya kalleshi da kyau.
“Ina zan fada maka labarin makiyiyarka? Matar da kace baka son jin komai nata”
“Da kin fada min ko da a tsawace ne, ko kuma ki cilasta min saurare ai dole zan ji, wani mai imani ne zai ji labarin matar nan be ji tausayinta ba?”
Ya fada yana hade yatsunsa fuskarsa dauke ta tausayi.
“Duk lokacin da nai unkurin fada maka sai kace ba zaka saurara ba, tausayinta ne yasa na hana ka kaita kotu ai, ko lokacin da aka fada maka bata cikin hayyacinta ba cewa kai karya ne ba, saboda kawai ta kashe maka ya ne? Ni ko na san mai imani ba zai kashe rai ba sai idan wata kaddara ta fada masa, sai a yanzu da Allah ya kaddara ya bude maka zuciya ka ji komai”
Yes he remember an fada masa she's unconscious ya ki yarda, and he remember how her father beg him akan case din amman be saurareshi ba, and the slap a lokacin da ta kawo Baby Namra asibiti ya mareta har sai da ta fadi..... Ji yai wani irin abu na rashin jindadi da kyautatawa ya mamaye shi, be taba jin tausayin wani abu mai rai kamar a yadda ya ji tausayin Halima ba a yau, a waje daya kuma yana ta jinjina karfin hali da dakiyar zuciya.
Part dinsa ya nufa yana ta tunani kala kala yes hak rayuwa take zaka ga mutum kawai sometimes a cikin farinciki amman ba san abunda yake zuciyarsa ba, ba zaka iya fassara damuwarsa ko nasararsa ba, da ace be ji labarin Halimatu ba da har yanzu be daina mata kallon makiyiyarsa ba, wata kila da Allah kadai ya san irin abubuwan da zai mata....
A dare kwana yai da tunanin abun a ransa, duk kuwa da yasan condition dinsa rage yawan tunani yana ciki.
HALIMATU POV.
Labarina ya taba zuciyar mutane da yawa a guri kuma nima ya taba ni a karan kaina, domin sai rayuwar da tunanin gobena ya dawo min sabo. Iyakar kokarin da nai kar nai kuka a bainar jama'a ne, sai dai na zubar da hawayen da ban san adadinsu ba, an rayuwata ta lalace kuma an bata ta yata, amman na yarda da wani abu daya, ko dan yayana zan rayu, zan kara jajircewa zan tsaya tsayin daka na amsa sunan da Ummulkhar ta kira ni da shi wato Jaruma.
Rai na ya kwadaitu da zancen kudin da ta ware min a cikin albashin kamar yadda ta fada, sai dai ina tunanin karbarsu abu ne mai wahala a gurina domin zai iya zama silar da zata saka a gane ko wacece ni wanda hakan zai hanani sakewa cikin mutane.
Ba mu tashi daga taron ba na ji alert a wayata, na naira miliyan daya, aiko a take na nemi damuwata na rasa farincikin ganin kudin ya maye gurbinta.
Cikin murna muka fita daga taron wani abun burgewa sai muka zama abun kallo har da masu dauka hoto a tare da mu da award din da aka ba mu, ina yin gaba kadan na hadu da blessing abokiyar aikina, sam ban san ta zo taron ba sai da tai min magana mun gaisa da ita ta tayani murna sannan ta gaisa da su Namra tana fadin ashe ina da yara. Sai nai murmushi.
“Ke ma ai kin san ina da yaya”
“Eh amman ban dauka har hudu ba, kuma kyawawa da su har sun fiki kyau”
Dariya nai sai ta soma tambayar dalilin rashin zuwana aiki kwana biyu. Ban boye mata komai ba na fada mata cewar wani dan'uwana ya hana ni aikin ne saboda uniform din be dace da ni ba. Dariya ta fara min tana ta mamakin wautata, wai ya zan daina aikin ban je ma fada musu dalilina ba idan ba su aminta su canja min kayan ba ko kuma gurin aikin ba sai na daina amman a haka ai ba ni da hujja kuma na bar damata ne. Ta yi tamin magiyar na je gobe na fada musu haka idan basu yarda ba sai n aje aikin, ni kuma na amsa mata da to duk da nasan ba za su yarda su canja min ba, amman yanzu na samu kudina zan iya yin sana'a ta kamin na samu wani aiki, tare muka jera muka fita tana fada min wata mata da ke yawan zuwa nemana tun da na daina zuwa aikin har number wayarta ta bari tace idan na zo a kirata. Ni kam mamaki ya cika kuma tsoro ya kama ni wacece kuma? Allah yasa ba wani karin damuwar ba ne, can kuma matar Kabir ta fado min a rai wata kila ita ce, dan nasan wannan mugun Ahmad din ba zai kyale shi ba, domin ko a yanzu na lura da kallon bakincikin da yake min, na ja masa fada da mahaukaci kuma ga shi na ci gasa na san hakan ba karamin zafi yai masa ba.
Idan na naje aikin Yunus din zan yi ma magana ko Tahir wanda shi ne shugaban sashen mu, shi kam na san ko kallo ban ishe shi ba kuma ba zai saurare ni sai dai ma ya fada min wata bakar maganar.
A ranar gidanmu ya cika da murna ba mu kadai ba har da makotan da suka samu barin sai da suka zo taya mu murna, Inna da Mama duk tsoro ya kama su wai kar a biyo dare ace sai an bada miliyan din, har ta hana a fadawa. Ba su kadai ba ni kaina na kwana da tsoro a ranar saboda halin tsoro da kasar nan take ciki abu kadan zai tsonewa wani ido.
Washe garin na tashi raina fes zuciyata kal babu damuwa ko kadan sai farinciki da annushuwa rabon da na samu kaina a haka har namanta, domin a yanzu bayan damuwata har da ta Abdallah tana damuna, tun daga wacan lokacin da yai min magana ban sake sakewa ba, su namra ma baki har kunne suna ta far'a, ban barsu sun je makaranta ba sai da nai kusu kashedi akan kar suje suna fadin abunda muka samo a school din, kuma su fadi gaskiya cewar kudin yana cikin account ba a hannu ba.
Bayan sun tafi nima na shirya cikin riga da zane na atamfa na saka hijabina, sannan na shiga dakin Mama na fada mata cewar zan tafi kamfanin na nemi alfamar canjin tufafi ko gurin aiki kamar yadda blessed ta bani shawara, daman tun da dare na labartawa Mama abunda ya faru da kuma matar da ke nema, har ta farara min kuiwa yin haka daman tana da complain cewar na daina aiki ba tare da na yi magana ba ban san ko za su aminta su canja min aikin ba.
A yau ban fita ba komai ba a hannuna da sunan kawai Kabir ba duk kuwa da kasancewar zuciyata na raya min na rika masa wani abu kamar yadda na saba, domin tun a lokacin da na daina zuwa aiki na daina kai masa abincin, haka ma take away da nake sakawa a kaiwa Abdallah na daina kasacewar hanya daya ce da gurin aikina a ko yaushe ina bada kudi na ce a kai masa idan 1pm ta yi ko 12,30pm.
Napep din da na tara akwai mutane biyu a ciki ni ce ta uku, a dole sai da ak saukesu inda za su je sannan aka kai no kamfanin wannan karon har bakin gate din kamfanin aka sauke ni, tsabanin da da ake sauke ni kusa da Kabir sai na bashi abincin sannan na wuce, babu irin dubawan da ban yi ba amman ban ga Kabir ba hakan kuma ba karamin haifar min da tsoro da zullumi yai ba, ina ta rokon Allah yasa ba mugun can yai masa wani abun ba.
As usual sai da na gaisa da masu gadin sannan na shiga ciki, kai tsaye reception na nufa fuskarta dauke da murmushi da sauri blessed ta zo ta rumgume ni.
“Oyoyo we miss you”
Ta fada sai kace wani dade muka yi muna aikin tare, ko da yake komai gamon jini ne. A nan fira ta kaure tsakanin na da su suna ta tambayar dalilin rashin zuwana aiki na fada musu sannan suka rika taya ni murna wai blessed ta basu labarin na ci gasa, a lokacin ne nake tambayarsu macen da take zuwa nema sai Rilwal ya ce
“Ai zata zo kullum sai ta zo nemanki a nan”
Na bukaci number wayar da suka ce ta bari tace a kirata idan na zo, sai Rilwal ya nuna min ita a wayarsa, na yi ta karanta number ban gane mai ita ba, sai kawai na zuba numbobin a wayata, ga mamaki sai sunan Suwaiba ya fito, miyasa take nema anan? Ba tasan gidan mu? Kuma tana number wayata idan har son ganina take? Wata matsalar ce? Ko wani abu ya faru da Abdallah? Haka zuciyata tai ra raya min abubuwa kamin na basu amsar cewar na gane mi number, nan suke fada min cewar babu wanda ya shigo a cikinsu daga sarkin girman kan har Yunus din da Tahir, hakan yasa na nemi guri na zauna dan na jirasu, ni kaina na san na yi sammako sai dai na zo da wuri ne saboda gudun na na zo suna tsaka da aiki a hana ni ganinsu tun da komai an kamfanin a tsare yake.
Ban yi minti goma da zama ba naji ana nuna domin sam ban lura da mutane da suke shigowa ba hankalina yana ka ce wayata, ina dago kaina nai yi arba da Suwaiba ta nufo inda nake rai a bace tana tafiya kamar ta fadi abun ka da siririyar mace.
“Kashedi na zo nai miki, ki fita hanyar mijina”
Ta fada cike da masifa tana daga murya iya karfinta, hakan yasa hankalin kowa ya dawo kaina.
“Ki fita hanyar mijina, yafi karfinki”
“Ba ki isa da mijin na ki ba ne shiyasa har kika zo baina jama'a kike min ihu, da ni nake auren Abdallah Wallahi idan na hana shi kallon wata macen ya hanu.... ”
“Ina zan isa da shi kin masa magani kin malleke shi bakar bazawara.... Yar duniya mai bibiyar mazan mutane, aure biyu kika kashe kina bibiyar mijina, marar mutunci kin zubar da yara hudu kin bar ubansu kina bibiyar nawa mijin, dan kawai ba ki san darajarsu ba...... Wani irin karuwanci ne da zaki rika aika masa abinci kullum..... Mijinki ne ko danki?”
Kalmar bazawara bata taba min zafi ba irin yau, ashe akwai ciwo idan aka maka gorin zawarci, a take na ji muzanci ya kamani tace na kashe aure ina bibiyar mijinta ko da karya ta fada wasu zasu gasgatata, na ci mutunci na a bainar jama'a ta gama da ni. Duk yadda na so na ki yin kuka sai na kasa hawaye suka fara min zuba bakina ya kulle gam na rasa me zan ce mata jikina sai rawa yake ina jin kamar na dake ta.
“Securities arrest her...”
Kamar saukar aradu haka muryar Ahmad ta dira a kunnena, da juyo idonw da hawaye na kalleshi yana tafe cikin kamfanin tare da Yunus, a lokacin da Security kamfanin suka nufo inda muke tsaye na yi zaton ni za su rike, sai na ga su kama Suwaiba macen cikinsu ta fisgeta da karfi.
“Ku rufe min ita a kamfanin nan sai ga uban waye mijin naki da za ki zo cikin kamfanin mu kina mana hankali how dare you”
Ya sake fada, a rikice na kalleshi ina hawaye. Sai ya karaso cikin kamfanin yana kallon amsu kallon fadan mu fuska a hade.
“Ku kuma me kuka tsaya yi kuna kallo ana insulting dinta instead of ku yi wani abu kowa ya saki ido fools”
Yana fadar hakan sai kowa yai saurin kama gabansa, shi kuma ya wuce ta gabana ba tare da ya kalleni ba ya bi hanyar da zata sada shi da office dinsa.
7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: I think you'd like this story: "GOBE NA (My Tomorrow)" by KhadeejaCandy on Wattpad https://www.wattpad.com/story/247701926?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZkyWKvWuHXhIRzZDEluZ%2BuUXayIbDBikXAQA%2BM4xeAsJY%2Fh9rtovTCoQphCdFYUPM4K1nHTquOLcFfifZUhwZ0RRyERddTi4AY1OYORg8gUhN9fNU%2FLr6t3SMGO9O8M2
*GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
4️⃣4️⃣
Rasa nai abunda zan yi, na bishi nai masa magana ko kuma na zauna ko na tafi gida? Ya Abdallah zai ji idan aka ce wani ya tsare masa mata saboda kuma a kamfaninmu, no ba saboda ni ba ne saboda ta yi hayaniya ne dan haka babu ruwana a ciki.
Akai akai mutane suke ta kallona, har na soma tsarguwa, tashi nai koma can wani gefe da ba a ganina sosai na zauna, wata zuciyar na fada min cewar naje nai maganar aikina sai dai kuma idan na yi maganar aikin aka koreni ba tare da an gama maganar Suwaiba fa?
Na kusan awa daya a gurin ina ta tunanin abun ne naje nai masa maganar Suwaiba ko ta aikina, amman ina ruwana da matar da ta ci min mutunci a bainar jama'a, ai kara a kira Abdallah din domin na san ba da saninsa ta zo nan ba.
Ban raba daya biyu ba, aka aiko wata mai sanye da suit kirana, haka ta saka ni a gaba ina baya har muka isa office din Ahmad. A one of visitors chair na tarar da Abdallah zaune, ni kuma sai na tsaya daga bayansa tun da ba a bani izinin zama ba, juyowa Abdallah yai ya kalleni sai kuma ya kawardar fuskarsa ba tare da yace komai ba.
“Look man aiki bake fa zaka tsayar da ni anan for more than 20 minutes, ba kallo office dinka na zo yi ba”
Abdallah ya fada a fusace, hakan yana nuna alamar Abdallah ya dade da zuwa kenan. Da hannu Ahmad yai min alama dana zauna ba tare da ya kalleni ba. Ba musu na zauna a kujerar da ke kusa da Abdallah ina ta kallonsa shi kuma sai yai kamar be san da ni a gurin. After like 5 minutes Ahmad ya kalleshi yace.
“Aiki nake yi ko baka gani ba? So kake na aje aikin na kula ka? Kai da ka zo ganina ba appointment? And you got lucky na barka ka shigo har office dina ka zauna tare da ni, ban barka visitors room ba?”
“Ba kai na zo gani ba, Matata na zo na ji dalilin riketa da kuka a nan”
“Bata fada maka abunda tai ba? Ko a hanya kawai za mu ga mace a hanya mu dauko ta?”
Babu wasa a fuskar Ahmad a yayinda yake wannan maganar, kamar yadda Abdallah ma nake ganin abun ya masa zafi.
“Matarka ta zo nan tana mana ihu na rashin tarbiya tana fada akanka, tana fada da ma'aikaciyarmu ba za mu dauki wannan ba”
“Kai kuma ka rufe ta, saboda gaka hukuma”
Ahmad ya kwanta jikin kujerar yana masawa Abdallah cikin zafin rai.
“Yes ko akwai abunda za ka yi? Kana ta son nuna isa, bayan you are nothing wanda be isa da iyalinsa ba har ya isa yace zai fito waje yai yi takama? It's a shame”
“Family issues ne wannan babu ruwanka a ciki”
Abdallah ya fada yana kokarin danne fushinsa.
“Family in my company? Public place?....”
Ganin abun kamar zai zame musu fada yasa nai hanzarin cewa.
“Na yafe ni tai wa cin mutunci na yafe mata, dan Allah ka barta ta tafi”
Ina fadar hakan Abdallah ya daga min yatsansa alamar babu ruwana a ciki, Ahmad kuma ya tari numfashina
“To ni ban yafe ba...”
Ya fada kai tsaye yana kallona. A lokacin ne Abdallah ya mike tsaye cikin bacin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 55