Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kunna data dama bana samun hawa online sai da dare idan yara sun yi bachi kuma na gama komai, grps din muna na Nothen Women's Advice na fara budewa na duba chat din sannan na shiga na Salma pre-order na duba abubuwan da ta turo cikin har da injimin wanki wanda na fi kowa bukatarsa a cikin gidan nan saboda wanki da nake na yaran nan gashi kwana biyu sun lalata. Ban bar online din ba sai kusan sha daya da rabi na dare, sannan na tashi Amal wacce a lokacin ta dade da fara bachi a take ta saka min kuka daman ta saba ko ba ai mata komai ba tana kuka balle kuma an yi da dalili. A haka nai mata wanka na saka mata tufafin bachinta na goyata saboda na samu ta daina min kukan. Dakin yaran na koma na ciro musu dayan set din uniform dinsu na dora musu a inda na saba aje musu sannan fito na shiga kitchen din n dauko abincin Abbah Namra na kai masa dakinsa duk kuwa da na san ba lallai ne ya ci ba domin ba ko da yaushe yake cin abinci a gida ba. A falo na fito da laptop dina na duba document din da oga Dahiru yace na shigo da su na fida su dabam a cikin wata folder sannan na rufe laptop din na koma dakin yara na kwantar da Amal. Na shiga nawa dakin nai wanka na saka kayan bachi na dawo dakin Abbah su na kwanta a take bachi yai gaba da ni abun ka da wanda ya gaji. Can cikin bachin nawa ina jin lokacin da Abbansu ya shigo duk yadda na so na dago nai masa sannu da dawowa sai na kasa saboda bachin da ya ci idona. Washe gari tun da asuba na tashi, sallah ce farkon abunda na fara yi sannan gabatar da addu'o'ina suma ba duka ba daman idan ba weekend ba bana samun tsayawa nai yi su gaba daya, ina saukowa kasa na shiga kitchen na shiga shirya musu abincin makaranta da kuma na karyawarmu, bayan na firaye dan na fasa kwai sannan na shiga dora ruwan zafin, Amal ce farkon tashi daman haka take tafi kowa rigima ko a dare idan ta motsa bata ji ba, indai yan rigimar suna nan sai ta saka kuka ta dawo dakinmu ta kwana. “Ommy Ommy” Ta fada tana murja ido cikin kuka. “Minene Amal?” “Bachi” “Je ki dauko zane” Sai kawai ta fashe da kuka, haka yasa dole na cire dankwalina na goyata da shi na cigaba da aikina. Ban tashi su Adnan ba sai da na tabbatar na shirya musu komai na makaranta sannan na tashe su nai musu wanka suka sauko kasa na hada musu tea kawai suka sha suka hau sama suka shirya cikin uniform dinsu kasancewar yau monday. Ni kuma na shiga cikin dakina na dauko kudin napep na saka hijab dina na fito na saka yarana a gaba muka fito har Amal muka nufi titi ina kokarin taron napep sai ga makocinmu kuma mijin kawata Hajara ya faka gefenmu tare da yaransa a cikin motar ya sauke gilashin motar yana miko min gaisuwa, sai da muka gaisa sannan ya ce da su Adnan su shigo motarsa suka shiga da saurin ganin yaransa daman can makarantarsu daya kuma yana yawan wucewa da su idan zai kai nasa yaran, wani lokacin ma har gida yake aikowa yace su fito zai kaisu makaranta. Sai da suka shiga motarsa sannan na juyo na dawo ni da Amal ina yanje da hannunta muka shigo cikin gida. Tea ta na dazun da bata karasa shanyewa ba na mika mata sannan na nufi dakin Abbansu, tufafin daya cire na jiya na fara dauka dan hade su da waendan kayan daudan nashi, al'adata ce duba aljihun rigarsa da wando kamin na saka su a kayan dauda saboda cire masa duk wani abu nasa da yake cikin aljihu. Rigar na fara dubawa sannan na saka hannuna a aljihun wandonsa, sai na ji abu kamar kwalin wani abu ina cirowa na ga kwalin kwandon sai dai ba cikakke ba da alama an yi amfani da shi. Ni a Kadai na san abunda na ji a wannan lokacin a take jikina na dauki rawa kamar dai yadda zuciyata ma take ta bugawa da karfi idanuwa na cika da hawaye. Juyawa nai ina rike da kwandon din a hannuna na kalli Abbah Namra da yake kwance saman gado yana ta sharar bachinsa hankalinsa kwance ni kuma nawa hankalin a tashe da kwandon a hannu. Dayan hannuna na saka na share hawayena da suka zubo na dauke kayan na fita da su, sai dai har nai aikin da nake na shirya Amal nai wanka nai shirin aikina hawayen ba su daina min zuba ba, ni kuma ban fasa sharewa da hannuna ba. Kamar yadda na saba yau ma na hada masa komai nasa na karyawa na shigar masa da shi dakinsa na kai masa, sai dai ban same shi a kwance ba sai na samu ya shiga bandaki da alama yana wanke baki ne, a can na baro Amal na fito na sauko kasa na nufi dinning na hadawa kaina tea amman sai na kasa sha saboda bacin rai da ke cikin raina, i decided na aje tea din na dawo saman cushion na zauna na dafe kaina. Wannan karon ba hawaye na ke ba wani abun ya ke jin ya tsaya min a zuciya marar misaltuwa daker na ke iya hadeye yawu da numfashi. Na kai minti talatin a haka sannan na tashi na koma dakina na dauko kwalin condom din na nufi dakinsa, kamin na kai hannu na tura kofar dakin na jiyo sautin dariyarsa hakan ya tabbatar min ko dai yana magana da Amal da take dakin ko kuma waya yake, ban yake dayan biyu ba na ji yana fadin. “Na samu hutu satin nan ina kike son muje?” Hakan yasa ni dauke hannuna daga jikin kofar daman can rikawa kawai nai ban tura ba. “Kaduna? To yayi ba matsala zan shirya mana komai, amman kamin na turo account dinki zan saka miki wani abu sai ki yi siyayyar da kanki kin san ni ba zan iya zuwa siyayya yanzu ba, kuma kin san idan ina fita da ke yau da gobe za a iya fara cewa wani abu” Kadan kadan yake maganar amman hakan be hana ni ji ba, domin mutun ne mai daga murya idan yana magana da wani ko da kuwa kadan-kadan yake yi. Ji nai kamar ba zan iya sauraren firarsu suka ba hakan yasa na murda kofar dakin na shiga ina kokarin maida hawayen da suka cika min ido. “Oh Okay Faruk sai na shigo” Shine abunda ya fada sannan yai hanzarin kashe wayar, ya gyara zamansa yana kokarin fara cin abinci, ko da wasa ban bar wata alama da zata nuna cewar na fahimci da mace yake waya ba, duk kuwa da kasancewar bana iya sauya yanayi na rashin jindadi da walwala dake tare da ni a yanzu. Zaunawa nai gabansa. “Ina kwana” Na fada ba tare da na kalleshi ba. Shi ma bana tsammani ya kalleni kamin ya amsa min sai Amal kawai yake wasa da ita yana bata abincin shi ma yana ci. “Jiya Hajiya ta sake min maganar kudin ac” “Ai sai ki ce mata kin fada min magana, ni Wallahi na manta amman yau zanje na fada kudin In-Sha-Allah” “To Allah ya bada iko” Be amsa min da amin ba sai ya dago ya kalleni. “Ya akai kin san bana son ana tsare ni idan ina cin abinci akwai wani abun ne?” Har zan mishi maganar condom din sai kuma na hade yawu na gabatar masa da abunda na san ba lallai ne yai min ba. “Jiya ne naga wani injimin wanki da ake order daga waje shine na ce ko zaka saka min wani sai na hada da abunda yake hannuna sai na siya na huta da kai wanki” “Ba ni da kudi yanzu, ina albashinki? Ko aikin kawai kike ba a biyanki?” “Ana biyana mana kai ma ai ka sani domin da su na ke rage wasu abubuwan nawa” “To ki siya da shi ni ba ni da kudi yanzu, da kin ga mutun ya zauna kin fara masa maganar kudi kenan shiyasa ko zama gidan nan bana son yi kuma baki da lokacin magana sai lokacin da nake cin abinci” “Irin wannan lokacin kawai nake samun damar magana da kai Abban Namra, baka dawowa da rana sai idan wani abun zaka yi da dare kuma sai 12 ko 1 kake dawowa” “To ni dai ba ni da kudi yanzu” Ya fada yana wani kara hade fuska. Sai na aje masa condom din da ke hannuna murya a sanyaye na ce. “Ga wannan na gani a cikin kayan da ka cire jiya” “Oh jiya Bala ya bani ajiyarshi na manta na bashi abarsa” Ya fada kai tsaye kamar gaske ba tare da ya kalleni ba. Idanuwana cike da kwalla na ce “Ko dai na wanene Allah ya sani kuma yana jiran kowa a madakata” Ina fadar hakan na mike tsaye sai dai kamin na kai tsayen ya rigani yana daka min tsawa. “To me kike nufi? Zagin kike ko kuma Allah ya isa za ki min? Wai mi yake damunki ne Halima? Daman munanan mata kun fi komai bakin hali ku ba kyau ba sai sakawa mutum damuwa da bakin zargin tsiya” “Ba ni n hallici kaina ba Abban Namra, kuma saboda bana da siffar da kake so a jikin mace ba shi yake nufi ka bi wasu matan ba, kai kanka kasan ba haka ka aureni ba, auren shekara goma sha biyu bana kwana biyu ba ne, dole wani abu a jikina ya canja, na haihu har hudu dole jikina ya bude, ka dinga jin tsoron Allah Abban Namra....” Kamar jira yake na kare a take ya wanka min wani mahaukacin mare mai zafi kamar garwasun wuta, kamin nai ihu Amal ta fara fashewa da kuka ta rike masa kafa damn ta saba masa haka ida da su Namra da Adnan idan yana dukana, ni kuma ban tsaya komai ba ya juya da sauri na fice daga dakin ina kuka. “Dacan bana tsoron Allah aka ce miki? Wawuya kawai” Shine kadai abunda na ke iya jiyo yana fada bayan na baro dakin, da gudu na dawo dakina na zauna kasa na fashe da wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya. 7/20/21, 8:28 AM - Buhainat: https://my.w.tt/kmm6u2LFKbb *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 3️⃣ Kuka nai mai isata sannan na tashi na shiga bandakin na wanke fuskarta na fito na nufi gaban madubin na dan shafa mai kadan da hoda sai dai hakan be boye kumburin da fuskata da kuma idanuwana sukai ba. Hijab din da yai yanayi da farar atamfar da nake saye na dauka na saka sannan na dauki wayata na saka a jakata na dauki laptop din na saka takalmi na fito daga dakina. Yau ban tsaya bin ta kan Amal ba balle har na kaita da kaina gidan kanensa daman wani lokacin shi yake kaita idan na fita na barta a gunsa wani lokacin kuma ni nake kai ta sai dai idan ni na kaita ta fi min kuka saboda takuwa irin nata. Na saba daman a duk lokacin da zanje aiki sai dai naje a napep ba dai ya kai ni ba, kusan tun da na fara aiki sau biyu ya taba rage min hanya ya kai ni da motarsa, babu kuma yadda ban yi ba da shi akan ya siya min mota amman ya ki ba dan bashi da hali ba, sai dan ya fi son nai ta wahalar zuwa aiki a napep ga kuma kai yara scul da nake duka a napep, ya bar ni da dawainiya kala kala kamin a dan bashi da halin dauka ba sai dan keta irin na shi. Har na shiga napep ban daina tunanin wayar da naji yanayi da wata ba, ciki har da zancen kudin da zai bata bayan ni na roki alfarmar ya cika min na samu na siye injimin wanki yace min ba shi da su, ga kuma zancen hutun daya samu har yana fadin wane gari take son suje, ada can kam na kasa yarda cewar Aminu yana neman matan banza duk kuwa da kasancewar ina ganin chat dinsa da wasu matan wani lokaci ko kuma na ji yana fira da su, sai dai a nawa tunanin irin chatting din nan ne na budurwa da saurayi da maza suke yi, wanda ba zaka iya raba maza da shi ba, sai dai ganin condom a aljihun wandonsa ya tabbatar min da abunda Abdallah yake yawan fada min, sukar auren da yake min na uban diyata yau na tabbatar da shi, no matter what Aminu zai fada min ba zan taba yarda ba, taya abokinsa zai bashi ajiyar condom miyasa shi ba zai aje da kansa ba sai ya bashi ajiya? Ban san lokacin da kuka ya kubuce min ba, ashe tun da na soma tunanin nake hawaye ban sani ba. “Hajiya Lafiya dai?” “Lafiya kalau dan Allah juya da ni inda ka dauko ni” Na fada ina jan majinar hancina,tare da saka hannuna na share hawayena. Kamar yadda na umarce shi haka ya juya ya koma, sai dai ban bari ya karasa ba na tsayar da shi na sauka na bashi kudin shi, daman ba gidan zan koma ba, gidan su kawata Hajara zan je na saba zuwa can a duk lokacin da abun duniya ya taru yai min yawa ita kanta da zarra ta ganni ta san akwai wata matsalar. Sallamar da nai cikin muryar kuka ce ta karantar da ita ina cikin wani hali. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u” Shi ta furta amaimakon ta amsa min sallamar, ta aje Affan da ke hannunta saman kujera ta taso ta nufo inda nake ta dafa ni ganin kamar ba zan iya karasowa saboda kukan da ya koma min sabo. “Halimatu” “Na'am” Na amsa daker, sannan na zauna a kujerar da ke kusa da ni ita ta zauna kusa da ni tana ta kallon kukan da nake cikin damuwa, har sai da nai wanda zan iya sannan na labarta mata abunda ya saka ni kuka a yau. “Wata kila da gaske ajiya aka bashi, ki rika kyautata masa zato dan Allah” Kaina na daga na kalleta. “Idan wacan ajiya aka bashi wayar da na ji yana yi fa?” Sai tai shiru domin a nan bata da amsar ba ni, ina da tabbacin babu wani abun da zata fada da zai kare shi a nan. “Ba zan ce kunne ki be ji daidai ba, amnan ina son ki sani yawancin mazan nan haka suke, suna nan kashewa matan waje kudi ko da kuwa ba su yi ma na gida ba, ki yi hakuri Halima” “Ko da yaushe idan na fada miki damuwa nai shiru kike cewa, ba ki tunanin hakurin nan zai iya zame min illa? Wallahi na gaji Haraja na gaji” “Karki gaji da bautar Allah, ki dauki aure a matsayin idaba kuma ibadar da ta fi ko wace wahala, dan'adam be tana yin hakuri ya kasa cin ribar hakurin ba, idan rashin kyautawa Aminu baya kyauta miki amman ki yi hakuri wata rana za ki ji dadi” “Yaushe zan jidadin? Tun da na haifi Adnan nake fuskantar wulakanci daga gurin Aminu har yau, haihuwa ta hudu kawai yake min wannan abun ime kike tunani a gaba? Ya GOBE NA zata kasance? Ina jin kamar babu wata matar auren da zata iya hakurin zaman auren da na ke da Aminu, shi ya min yan'uwansa su min ya zan ji?” Dafani tai tana min magana a hankali “Suna nan da yawa wadanda suka fi ki hakuri Halimatu, wasu ko abincin basa samu amman haka suke hakuri su zauna, ke ko har yana aje miki abinci ko da bashi da dadi ya dai baki lokacinsa ne kawai baya bashi da wasu hakokin, shin idan ba ki yi hakuri ba Halima so kike na ce ki kashe aurenki ki koma gidanku da zama cikin kannenki? Ya matan gidan ku a yanzu taskwas ne so kike a fara kirgawa da ke a zaurawan unguwarku? Ki tashi hankalin iyayenki da na yayanki? Kina da tabbacin shi wani mijin da zaki aura baya nema mata ko kuma zai baki lokacinsa? Ki bar yayanki su tashi a hannun wata wacce ba uwarsu ba? Adnan shekararsa goma sha daya kuma shine babba shi din ma kina da tabbacin zai iya yi ma kansa wata lalurar balle kuma sauran?” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u.” Shine abunda nake ta furtawa na dafe kaina. “Ki yi taka tsantsan da aurenki Halima saki daya ya rage a tsakaninku, wani abun ko dan yaranki ai kya yi hakuri ki zauna da mijinki a haka, kuma ki gode Allah da har mijinki yana amfani da Condom din, wasu mazan kamar tumaki suke babu ruwansu da kariyar kai, kuma wani lokacin mu kan mu mata muna da matsala, Halima ko yan gyare gyaren nan ba ki yi su kuma maza basa son haka, mace sai da gyra ko da ko baki haihuwa ba balle kin yi haihuwa har hudu” “Namijin da ba ya maka kallon sha'awa Hajara wani gyara zan tsaya yi akansa? Idan ma nace zan yi gyara zan bata kudina da lokaci na ne a banza” Na fada ina share hawayena. “Ba haka ba ne, ba jira za ki yi har sai shi ya kawo kansa gareki ba, ke ma zaki iya yin wasu abubuwan na wayewa da janyo hankalin mijinki izuwa gareki, su ma matan waje ai ai janyo hankalin mazanjenmu suke har su kao garesu” Kallonta nai ina sauke ajiyar zuciya. “Hajara yace na daina burge shi wai shi baya son mata masu kiba, kuma shi yanzu farar mace yake so ni kuma ba fara ce fes ba, kuma ina da ji ba siririya ba ce ni, bana ganin ina da wani sauran digon kyau da zan iya jan hankalin Aminu da shi a yanzu” “Bayan jan hankali, zamantakewar aure tana bukatar tattauna da fahimtar juna, kin rigani aure Halima amman kamar na riga ki karanta halin maza, ki zauna da mijin ki bashi hakurin abunda ya faru dazun ki nuna masa ke ce mai laifi ko da kuwa shi ne da laifi kuma ki fada masa zaki kiyaye, abu na biyu ki lura da abunda zaki iya canjawa sai ki yi kokarin yi, yar kwaliyar nan t tarbon miji ki rikayi mana haba Halima sai kace ba wayayya ba?” “Namijin da baya dawowa sai 12 ko 1 na dare shi zan yi ma kwaliya? Kuma ya riga ya furta cewar bana burgeshi a yanzu duk wani abun da zan yi aikin banza ne Hajara” “Ki gwada dai, akwai wasu kayan mata masu kyau anjima za a kawo min zan aika miki ki gwada amfani da su, ki maida komai ba komai ba Halima dan Allah ki yi hakuri ki zauna ko dan yayanki” “Da ma kin bar kayanki, rabon da Abban Namra yai mu'amala da ni tun daga lokacin daya fahimci ina da ciki, daman can ba bukatana yake ba balle kuma yanzu” “Ba daga nan take ba, ke dai ki yarda da ni ki gwada dan Allah, wanna kam ba mota ba ko jirgi kika ce kina so sai ya siya miki” Kai na gyada mata ina tabe baki gare da sake share hawayen da suke min zuba, jin motar mijinta yasa na mikewa tsaye, kamin mijinta ya shigo falon nai mata sallama na fita da sauri domin ba kasafai na ke son yana ganina a gidan ba, ba dan komai ba sai dan tsaron mutuncin aurena. Daga gidansu Hajara kai tsaye gurin aikinmu na nufi, sai dai ban shiga Office ba sai da na biya ta gurin masu printing na cikin company nai printing documents din sannan na shiga cikin office din. Na shiga a lokacin da wasu sun dade da shigowa ma'aikatar wasu kuma yanzu suke shigowa a yayinda wasu kuma sai anjima za su shigo kowa da yanayin aikinsa da kuma lokacin shigowarsa. A inda muke zaune mu uku ne a Office din daga ni sai wasu abokan aikina biyu duka maza, daga ni sai Kabeer sai kuma Emmanuel wanda yake ba bahaushe ba. As usual idan na shiga ina gaishe da duk wanda na tarar a office din, idan kuma su suka tarar da ni suna miko min gaisuwa cikin mutunci da girmamawa. Yau kam Kabeer kawai na tarar na office din hakan na nufi ya riga Emmanuel shigowa kenan. “Good morning Kabeer” “Morning Halimatu” Na mika masa gaisuwar a lokacin da nake kokarin zaunawa, shi kuma ya amsa min yana baro bangarensa zuwa inda nake zaune. “Kamar kina cikin damuwa yau kin karya kuwa?” Haka yake min a lokacin dana shigo office din yana kokarin kula da ni kamar matarsa duk kuwa da na san kular bata Allah da Annabi ce ba, na san yana da wata manufar akaina Hannu ya kai zai taba jikina sai nai saurin buge masa hannun na mike tsaye cikin bacin rai na ce. “Miye haka Kabeer taba ni za kai? Ka manta da ina da aure ko me? Wai miyasa kake min wasu abubuwan kamar baka cikin hayyacinka ne?” “Halima kenan, ni da ke mun zama daya a nan fa? Miye laifin dan na na taba jikinki?” “Idan a gurinka ba laifi ba ne ni a gurina laifi ne, ina da aure har da yara hudu abunda ban aijata shi da budurcina ba ba zan aikata shi da aurena ba” Ina fadar hakan na dauki documents din na wuce zuwa office din ogan mu, na yi zaton yana cikin musamman da na ga ya kirani jiya yace na shigo da takardun nan a zaton ko da saffafe zai duba su amman sai gashi ban same shi a office din ba. Hakan yasa na dawo nawa office din na zauna na soma aikina, gaba dayan ranar Oga Dahiru be shigo ba, haka ma wunin ranar Kabeer be ga wata sakewa a tare da ni kamar yadda ya saba gani ba. Har muka tashi daga aikin ban sake ce masa komai ba shi ma kuma be yi kokarin yi min magana ba. Kamar yadda na saba bayan na taso daga aiki na wuce gidansu Baban Sadi wato kenen mahaifinsu domin dauko yarana daman yana daukarsu tare da yaransa ya kai su gidansa idan an tashi scul har sai idan na taso aiki na biya na dauko su a Napep mu dawo. A bakin kofar falon muka gaisa da matarsa sannan na kirasu suka fito banda Namra. “Ina Namra?” “Tana can part dinsa ai kin san indai yana nan to tana can part dinsa, ko fita zai yi da ita yake fita Allah ya hada jininsu” Cewar Safiya matarsa. Ni kuma nai murmushi ba tare da tunanin komai ba na kalli Aiman na ce yaje ya kirata na saka Amal da Adnan a gaba muka nufi gate da zimmar Namra da Aiman su cin mana. Kamin mu fice daga gate din gidan sai gasu sun ci mana Namra na ta sharar kwalla idonta ya yi ja sosai. “Ke lafiya?” “Cikina ke ciwo” “Oh wannan ciwon cikin ya matsa miki, bari yanzu idan muka muka je gida su Adnan suka wuce Islamiya sai na kai ki asibiti” “To Momy” Ta amsa min cikin kuka har sai da ta bani tausayi. Napep na tara na saka yarana sannan na shiga muka nufo gida. Indomie na fara dafa musu suka ci sukai shirin islamiya sannan na dora tuwo na shiga nai wanka nai ma Namra na shirya ta, sannan na fita na kira Kausar wata kanwar makociyata wacce budurwa ce daman na kan kirata ta rika min wasu abubuwa. Ita na barwa girkin sannan na ja Namra muka nufi Asibitin Yarima ganin likitan yara na maraice. Ba mu tararda jira kamar safe ba, daman da maraici ba a cika taruwa ba, a lokacin da muka shiga dakin likita ya tambaye ta komai ta fada masa yadda take jin cikin nata yana mata ciwo, sannan na rubuta mana hoto da awon fitsari sannan na rubuta mata magani. Sai da na kaita akai mata hoton fitsarin kuma suka ce a kawo na safe wanda zata fara yi kamin ta ci komai. Maganin ne kawai ban siya mata ba muka dawo. A saman kujera ta kwanta

Chapter 2 of 55