Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dukanmu” Kuka yake ba dan kadan ba, kuka yake ba na wasa ba, kukan da be tana irinsa ba, kukan da be taba saka ran yinsa ba. Kukan da tun da Namra ta mutu be ji irinsa na kusanta shi ba, ko mutuwar matarsa be yi kuka haka kamar na Namra ba, tun Hajiya na taya shi kukan har ta share hawayenta ta koma bashi hakuri tana karfafa masa. Daga karshe dukan maganganun Hajiya sun shiga jikinsa ya ji karfin hali da karfin zuciyar da yake jin zai iya fita ayi addu'a ukun yarsa da shi. Haka kuwa akai ya fita ya shiga mutane ana ta masa gaisuwa yana amsawa cikin karfin hali, sai dai a duk lokacin da akai masa gaisuwar sai yaji wani abu ya tsaya masa a zuciyarsa daker yake iya hada yawun bakinaa ya hade abun, tun yana iya hadewa da yawun har ta kai sai ya kurba ruwa yake jin abun ya wuce masa, wasa wasa ya fara jin numshinsa na yin kasa har sai da ya koma ambaton mahallincinsa. Babu wanda be tausaya masa ba, duba da irin shakuwar da ke tsakaninsa kuma sanin cewar ba shi da mata a yanzu, gashi mahaifiyar yarinyar itama ta rasu, ga wata uwar ramar da yai cikin kwana biyu kawai ya koma kamar wanda ya shekara kwance yana ciwo. Bayan sallah la'asar akai addu'a sai mutane suka fara watsewa, wasu kan so su sake masa gaisuwa sannan su wuce musamman wadanda ba su samu ganinsa ba sai a yau. A cikin mutanen har da mahaifin Halimatu wanda tun da akai mutuwar kullum da shi ake karbar gaisuwar. Da hannunsa ya turo wheelchair dinsa ya karasa kusa da Ahmad ya mika masa hannu Ahmad ya mika masa nasa hannun yana amsa gaisuwar da yake masa. “Ni ne kakan abokiyar yarka Namra...” Baba na rufe baki Ahmad ya tsaya cak yana kallonsa kamin yai saurin janye hannunsa. “Me ka zo yi nan?” Baba yai shiru kamar mai tunanin ta inda zai fara. “Ka fada min cewar yarka bata da laifi? Ko kuma ka bani hakuri akan abunda tai? Ko kuma saboda ka yi min gaisuwa sai na ce na yafe mata...?” “Da dai ka saurareni d’a na” Baba ya fada cikin sanyayyiyar murya, a take Ahmad ya daga masa hannu yana mai jin baya ma bukatar saurarensa. “Bana son jin komai daga bakinka, ka fadawa yarka ta jira kiran kotu, domin ba zan kyale wannan maganar ba, yarka kake kokarin karewa ni ma kuma kadin yata zan bi” “Haba dai d'ana arzikin ba hauka ba ne ka saurareni mana” “Ni ba danka ba ne da danka ne ni da yarka bata kashe min ya ba....” Yana kawai nan ya juya a fucewa ya bar harabar gidan. Part dinsa ya shiga ya ya dauki wayarsa dake ringing sai ta ya fara amsa kiran amsu masa gaisuwa sannan ya samu damar kiran lauyansa. *** *** *** Cikin tsananin damuwa Baba ya tura kekenasa ya fita daga gidan, daman haka yake idan zai tafiya mai nisa saboda baya iya taka kafa sai ya hau kekensa a maimaikon yai tafiyar da sanda, baya damuwa yace dole sai yaje da yayansa sun turashi ko su rika shi, ganin duk yayan nasa mata ne sa maza biyu da basu gama tasowa ba. Da kansa ya tari Napep bayan ta tsaya ya mike tsaye ya taka kafar a hankali ya shiga bayan ya fada masa inda zai kai shi, mai nepep din da kansa ya fito ya kama keken Baba ya nade ta ya saka ta a ciki sannan ya koma mazauninsa ya kunna napep din. Har suka isa gida Baba be daina tunanin maganar da Gwarzo ya fada masa ba, idan har da gaske yace zai daure Halimatu to dukansu suna cikin matsala domin za a kara mata wata damuwar ne bayan wacce take fama da ita a yanzu, ga kuma mahaifiyarta wacce ta koma sai an kwantar idan zata tashi ma sai an rikata saboda ciwonta na hawan jinin da ya saka ta a gaba. Cikin rashin kuzari ya isa gida sai da mai napep din ya fito masa da kekensa sannan ya ciro 200 naira ya mika masa bayan ya shi canja ya kwalawa dansa karami kiran. “Abbah....” Sai gashi ya fito da gudu. “Shiga da wannan kujerar koma ciki ka dauko min sandata” A nan ma da gudun ya shiga ya da keken ya dauko sandar ya kawowa mahaifinsa sannan suka shiga cikin gidan tare, a kishingide ya samu Mama saman tabarma Aisha na mata fita kofin fura a gefenta an saka kankara a ciki domin ita kada take iya sha a yanzu sai kuma maganin da aka rubuto mata asibiti. Daga inda take ta daga kanta ta kalli Baba tana ganin yanayinsa ta san ba zai bada labari mai dadi ba, sai ta maida kanta ya rufe ido. “Sannu... ” Baba ya fada sai ta daga masa kai a hankali, tana cizon baki tare da sauke ajiyar zuciya a hankali. Baba ya dubi Aisha “Aisha kin dawo?” “Eh Anty Hafiza da Husna da Inna suna can” “Ya jikin Halimatu?” “Wallahi Baba har yanzu bata magana, bata san wanda yazo kanta ba, ko motsi bata yi idan ba su likitocin suka juya ta ba sai dai tai ta kallon mutane ko kuma tai ta bachi” “Al-hamdulillah Allah mun gode maka, a nan din ma ba wani sauki, ina ganin mutanen ba za su bar maganar nan ba, ya tabbatar min da bakinsa cewar sai ya kaita kotu” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Mama ta fada a hankali sannan ta bude idonta. “Ka yi magana da shi?” “Baya son saurarena” “Ka yi magana da mahaifiyarsa?” “Shi mai karar be saurareni ba taya kike tunanin mahaifiyarsa zata saurare ni?” “Ita ai uwa ce zata fi shi hankali da tunani” “Bana tunanin ba da sanin mahaifiyarsa ko izininta yake wannan abun ba” “Idan ka yi min izini ni zanje nai magana da ita” “Ba za su saurareki ba” “Ba zan iya ganewa ba har sai na yi magana da ita, idan bata saurareni ba sai mu kai kararsu a gurin Allah” “Taya za ki iya zuwa ki yi magana da ita Mama ke da baki da lafiya ma” Aisha ta tambaya. Sai Mama ta unkura ta tashin zaune. “Zan iya Aisha ciwon Halimatu ya fi ciwona damu na” “Tashi ki taro napep mu tafi” “Da dai za ki ji magana ta da kin zauna domin ba za su saurareki ba” “Da dai ka bar ni na tafi hankalina zai fi kwanciya” “To Allah ya sa'a a dace” Shine abunda Baba ya fita da shi, sannan Aisha ta fita da kanta ta taro mai napep din ta dawo ita da Teema suka rika Mama suka saka ta a napep din. Kamin su isa har ta gaji saboda ciwon zuciya da ba jiki, ba a hana su shiga ba kusan gate din gidan ma a bude saboda masu zuwa gaisuwa da kuma wadanda ba su gama ficewa ba. Mama bata taba zuwa gidan ba sai yau saboda rashin lafiyar da ya same ta tun daga lokacin da aka kwantar da Halimatu asibiti, daga ita har Aisha da Teema daman Inna ce da su Hafiza suke jigilar zuwa gaisuwa kuma suje asibiti gurin Halimatu. Da taimakon mutane dake fitowa cikin gidan aka nuna musu kofar falon Hajiya har suka isa. Sun tararda falon a cike da mutane hakan yasa Mama ta fara gaisuwar ta kansu kamin ta kalli wacce take zaton matar gidance ta ce. “Ke ce Hajiya” “Aa ni yayarta ce Hajiya tana cikin bari a kira miki ita” Wata budurwa dake kusa da ita zaune aka aika ta kira Hajiya, sai gata ta sauko babu dadewa waya makkale a kunnenta har ta zauna, sai da ta gama wayar sannan Mama ta mika mata gaisuwa tare da ta'aziya. Hajiya ta amsa tana mata kallon rashin sani. “Hajiya zan iya kebancewa da ke? Magana nake son yi da ke” Jimm Hajiya tai tana kallonta kamin ta mike tsaye ta nufi dakin baki da ke kasa. “To sai ki biyo ni” Hajiya na gaba Mama na biye da ita tare da Aisha wacce ta rikota har suka shiga dakin. Madaidacin daki ne mai dauke da gado da katifar kasa sai kuma wardrobe da yan kayan kwaliya kadan. A saman gadon Hajiya ta zauna mama kuma ta zauna a kasa sannan ta kalli Aisha tace. “Je can waje ki jira ni” “To Mama” Amsa mata sannan ta juya ta fice sai ya rage daga Hajiya sai Mama ne kawai a dakin. “Na san baki san ni ba Hajiya baki taba ganina ba, ba kisan inda na fito ba” “Haka ne ban gane ki ba gaskiya” Hajiya ta fada tana aje wayarta a gafen gadon tare da tattara dukan hankali ta fuskanci Mama. “Ni mahaifiyar Halimatu wacce kuke zargin ta kashe muku jika....” Shiru tai na dan wani lokaci tana shawaye kamin ta cigaba. “Alfarma na zo nema gurinki Hajiya, kuma ba dan yata ta aikata abunda kuke zarginta ba, Wallahi yata mutuniyar kirkice ba, ba dab tana nawa ba sai dan zan iya shaidar halinta ko da ba yata ba ce, sannan na san ke uwa ce za ki iya jin abunda wata uwar take ji idan aka lakawa yarta sheri alhalin tana da gaskiya, kuna da arzikin da za ku iya hadawa da ni da ubanta duka ku daure amman ba shi nake son ki duba ba, adalci nake son ki yi danki kuma ki yi wa yata” “Wane irin adalci? Dazun Gwarzo ya fada min cewar mahaifinta ya zo yana rokonsa ke kuma kin zo yanzu idan har da gaske bata aikata ba miyasa kuke ta magiya? Anya mai gaskiya zai yi haka?” Mama ta daga kai ta kalli Hajiya hawaye na sauko mata. “Za ki iya ba ni kur'ane na rantse Hajiya? Wallahi ina zaune tare da ita a lokacin da jakarki ta fada rijiya, yara suka shigo da gudu suka fada mana cewar Namra ta fada rijiya, Wata kaddara ce take bibiyar Halimatu wacce ban san yadda zan kwatanta miki ita ba, ina tausayi Halimatu fiye da duka yayan da na haifa ni kadai na san halin da yata take ciki, bani da tabbacin rayuwa wata kila zan iya mutuwa yanzu ko anjima ko gobe amman ina son kamin na mutu na tabbatar yata ba zata je gidan yari da laifin da bata aikata ba” “Idan har da gaske bata aikata ba to kotu zata bata gaskiya mu ta bamu rashin gaskiyar” Kai Mama ta girgiza ta sake duban Hajiya tace. “Bari na baki wani labari Hajiya, kin taba haduwa da macen da akai mata fyade akai wa yarta kuma mijinta ya rabu da ita saboda tana kokarin kwatowa yarta hakkinta?” A take fuskar Hajiya ta canja. “Wa aka yi wa haka?” “Halimatu Hajiya..... ” Babu abunda Mama ta rage daga labarin Halimatu sai da ta fayyacewa Hajiya komai tun daga aurenta da irin kalubalen da ta fuskanta har zuwa yau da wannan kaddarar ta mutuwar Namra ta fada mata, ba mama kadai ke kuka ba, wannan karon har da Hajiya da ake ba labarin sai da tai hawaye. “Amman kuma ita yarinyar kuka kasa kwato mata hakkinta?” “Taya? Taya Hajiya? Taya za a kwato hakkin macen da mijinta ya karyatata ya gasgasta dan'uwansa akan yarsa? Mutun yarinyar kawai za a zubar a bata mata suna ita da mahaifiyarta” Hajiya ta share hawayennta. “Wannan ba hujja ba ce be kamata ku bar wannan maganar ba, kuka kokarin boyewa ne saboda gudun kunya, na tabbatar abunda kike kokarin boyewa na hana a bi wa yarinya hakkin kina kokarin daba wuka ne a ciwo, abun nan yana kasan zuciyarku ke da mahaifiyarta, miyasa za ku boye idan har za ayi wa mata da kananan yara fyade ana boyewa babu ranar da za a daina” “Maganar ta dade da wucewa Hajiya, yanzu alfamar ki nake nema kar Halimatu ta sake shiga wani kunci” “Zan yi mishi magana, za a samu mafita In-Sha-Allah” “Na gode Allah ya kara sutura, Allah ya saka da alheri” “Ita Halimatun tana can asibitin?” “Tana can amman bata cikin hayyacinta” “Gaskiya be kamata ku bar maganar nan ba, taya? Za a ketawa uwa haddi ayi ma ya kuma ku danne wannan bakincikin ku hade saboda gudun kunya?” Mama ta unkura cike da karfin hali ta mike tsaye. “Na gode Hajiya na gode Allah yasa ki rike min wannan sirrin” Cikin karfin hali ta fara takawa zuciyarta na mata mugun nauyi ta fice daga dakin. 7/21/21, 10:45 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣3️⃣ Sai da suka gama tsara komai da lauyansa, sannan ya taso tare da shi suka shigo falon Hajiya, a lokacin 8 har da yan mintuna na dare. Da kansa ya tura kofar falon ya shiga Barrister na biye da shi a baya. Hajiya na zaune kasan center carpet Siyama ta dora kanta saman cinyar Hajiya ta lumshe ido kamar mai bachi, alhalin ba bachin take ba tsabagen ciwo kaina ya saka ta a gaba da damuwar rashin Baby Namra.   Barrister ne yai sallama Hajiya ta amsa mi shi tana kallon danta, ramarsa ta yanzu har ta fi ta dazun da jiya ga wani rashin kuzari da yake fama da shi, ko be fada mata ba ta san abunda ya kawo lauyansa a gidan, ta saurari duk wani abun da Gwarzo da Barrister suka fada mata da kuma yadda suka tsara shigar da karar, bata katsi hanzanrinsu ba har suka yi suka gama, bayan barrister yai mata sallama ta kalli Gwarzo tace. “Idan ka raka shi ka zo ina son magana da kai” Ta okay ya amsa mata sannan ya mike tsaye suka fice tare da barrister. A harabar gidan ma sun kusan awa daya suna tattaunawa kamin yai masa sallama ya sake dawowa falon Hajiya ya zauna. Shiru shiru Hajiya bata ce masa komai ba tana da kallon plasma dake falon, har sai da ya kagara da kansa yai magana. “Hajiya kin ce akwai maganar da kike son yi da ni?” Juyowa tai a hankali ta kalli gefen da danta yake zaune a saman cushion. “Zaka iya tuna lokacin da mahaifinku ya rasu?” “Eh” “Kana iya tuna silar mutuwarsa?” “Ciwon suga ne” “Matarka fa?” “Hadarin mota ne” “Miyasa ba kai karar likitan da ya duba mahaifinku ba a lokacin da ya rasu? Miyasa ba jai karar wanda ya kirkiro motar da tai silar mutuwar matarka ba?” Kallon rashin fahimta yai mata, why Hajiya zata bijiro masa da wannan maganar? Taya zai yi karar wanda ya kirkiro motar da tai silar mutuwar matarsa? Taya zai yi karar likitan da ba shi ya kashe mahaifinsa ba? “Fada min? Ko kuma ka fi son Baby Namra ne akan mahaifinka? Ko kuma ran Baby ya fi na Matarka daraja?” “Ba... Ko... Daya...” Ya amsa kamar ana matso maganar daga bakinsa. “Then why zaka yi karar matar nan Gwarzo? Miyasa kake son dora mata laifi? Kana da wata hujja da ke nuna cewar ita ta kashe Baby Namra?” Wani dogon numfashi ya ja ya sauke, sai a yanzu ya fahimci inda zancen Hajiya ya dosa. “Saboda matar bata da mutunci ko kadan, kuma a yadda take da zafin zuciya zata iya aikatawa, kuma idan har bata aikata ba miyasa suke jin tsoro ita da iyayen?” “Da zaka ji labarin matar nan da ka tausaya mata, kaddara ce ta fada mata kuma mahaifiyarta tai min rantsuwa....” Saurin saukowa yai daga saman kujerar yana hade wani bakin abu daya tsaya masa a makoshi. “Hajiya dan Allah? Bana son na ji duk wani abu da ya shafe ta, ba ina kokarin kai kararta ba ne saboda na danne mata hakki no hakki yata nake kokarin kwatowa?” “Wace hujja kake da ita wacce ta nuna maka cewar matar nan ita ce ta kashe Baby? Haba Gwarzo ya kake neman zautuwa akan mutuwar da ba yau ta saba bakuntarka ba?” Sakin baki yai da mamaki yana kallon Hajiya miyasa tai saurin canja har take kokarin hana shi bayan ita ma a da tana goyon bayan karar? Siyama ce ta tashi zaune ta tana kallon Hajiya da mamaki. “Hajiya be kamata a kyale wannan maganar ba, taya zata kashe Baby kuma a barta?” Hajiya ta daka mata matsawa. “Kar na sake jin bakinki ba ki san komai akan rayuwa ba, kuma idan manya suna magana karki sake tsoma bakinki” “Amman gaskiya ta fada Hajiya indai suna da gaskiya kotu zata ba su gaskiyarsu mu kuma ta ba mu rashin gaskiyar” Kallonsa Hajiya tai da kyau “Mutuwar nan ta dauke mahaifinka ta dauke matarka, yanzu kuma ta dauke yarka, wata rana ni zata dauke kuma ta dauke kanwarka kamin ta dauke ka, wata rana zata zo da zaka rasa wanda zai hana ka aikata ba daidai ba balle ya fada maka kuskurenka....” “Bana tunanin idan wannan ranar ta zo zan iya rayuwa Hajiya, na rasa babana na rayu na rasa matata yes na rayu yanzu kuma na rasa yata still zan rayu amman bana tunanin idan na rasa ki zan rayu, ku kadai kuka rage min a yanzu daga ke sai Siyama ku kadai nake da ku a yanzu, Allah ya min kyautar mata ya karbe, ya ba ni ya ya karbe, mahaifina ma ya karbi abunsa, ba ni da kowa a yanzu daga ke sai yar'uwata sai dangi” Ya fada hawaye na sauko masa, sannan ya taso daga inda yake zaune ya nufa inda take ya rumgumeta. “Na bar maganar nan har bada Hajiya, Wallahi na barta” Hajiya ta lumshe idonuwanta dake cike da hawaye zuciyarta cike da tausayin danta. “We're three mu kadai muka rage, babu Baby babu Daddy” Cewar Siyama tana fashewa da kuka tare da rumgume Hajiya. “Allah ya musu albarka” Hajiya ta fada da muryar kuka, hakan yasa Gwarzo tashi ya bar falon yana share hawaye wasu na sauko masa. HALIMATU POV. Na ga abubuwa daya a cikin dogon bachi na, abubuwa mabanbanta, masu rikitarwa wadanda ba zan iya fassawaba, tabbas bachi da na dade ina yi a yau yana daure da mafarka kalakala. Ina ji a jikina kamar ban taba bachi mai nauyi irin wannan ba, domin ba jikina kadai ya mutu ba har fatar idona ji nake kamar ba zan iya budewa ba, numfashin ma idan ya fita daker ya ke dawowa, a duk lokacin daya dawo sai na ji wani bari da ban gama tantancewa daga ina yake fitowa ba, sai dai na sa tabbas ba na muhallina ba ne. A zuciyarta nake ta amboton mahallincina hakan ba karamin taimaka min yai har na samu karfin buden idon ba, sai kuma nai saurin maidawa na rufe sakamakon hasken da na ji yai min yawa idon har wani yaji na ji suna min. Cikin karfin hali na kai hannuna na murza idon sannan na sake budewa ina karewa dakin kallo sai a yanzu nake gane ko warin asibiti ne nake ji, amman miya kawo ni asibiti? Shi nake kokarin tunawa, a take kaina ya tsara na nemi duka tunani na rasa sai na sake rufe idon ina jin bakina da daci. Tuna abunda ya faru yasa ni saurin bude idon a nan abun neman ya samu hawaye suka fara aikinsu, unkurin tashi nai zaune amman na kasa saboda rashin kuzari. Hakan na cilasta min cigaba da karewa dakin kallo, ina haka aka turo kofar dakin wani ya leko ni sai kuma ya rufe dakin, da alama wani yake nema domin haka wasu suke idan suna neman wani sai su rika bibiyar daki suna lekawa. Har na lumshe idona sai kuma na sake jin an bude kofar a karo na biyu sai dai wannan karon na ji alamar shigowa duk kuwa da kasancewar idon nawa a rufe suke. Wani irin fitinannane kamshi turare na ji ya maye gurbin warin asibitin da nake ji hakan yasa ni saurin bude idon karaf nai arba da wani kyakkyawan farin mutum wanda ba zan iya kiransa da saurayin ba ba kuma zan ce masa mai aure ba tunda ban san gaibu ba, yana da manyan idanuwa ga dogon hanci, bakar rigar dake jikinsa ta haska fuskarsa gwanin daukar hankali. Matsowa yake ta yi kusa da ni yana kallon fuska kamar mai son tantance wani abu, van yarda a zahiri nake kallonsa ba har sai da na runtse ido na sake budewa, sai a yanzu na fahimci mutumen dazun ne da ya leko ni ya sake shigowa. “Sannu.... ” Ya furta min yana cigaba da kallona. “Yauwa” Na amsa daker, sai ya kalli kofa ya sake kallona. “Ya jikin?” “Al-hamdulillah kai likita ne?” Jimm yai kamin ya bani amsa, hakan yasa ni tsaye na kare masa kallo da kyau, kusan a kuskure nai arba da sarkar cross din dake wuyansa wacce nake kyautata zaton ta zinari ce, kamar yadda hannunsa yake dauke da agogo da awarwaro na zinari haka ma zoben hannunsa, ba rigar jikinsa kadai ba har jean da ke jikinsa kana kallonsa kasan mai tsada ne. “Yes ni Doctor ne how are you feeling now?” Yana fadar hakan ya nufi gurin files dina ya bude yana dubawa sai dai babu alamar natsuwa a tare da shi in each seconds sai ya kalli kofa kamar mai tsoron shigowar wani. Ba zan iya karyata cewar shi din ba likita ba ne domin ban san a wace asibitin nakr ba, ba kuma zan iya gasgata cewar shi din likita ne ba domin ban ga alamun hakan a shigarsa da natsuwarsa ba, ko da yake likitoci ma sun fi saka kananan kaya. “Ina mijinki?” Ya tambaya yana kai hannunsa ya taba jikina. “Miya faru?” “Akwai maganar da nake son yi da shi” Ya fada babu alamar wasa a tare da shi. “Idan wani abun ne ka fada min likita ba ni da aure a yanzu zaman kaina ke” Shiru yai yana kallon na dan wani lokaci kamin ya kai duka hannayensa ya rika ni ya tashe ni zaune, sai dai har lokacin ba shi da natsuwa. “Haihuwarki nawa?” “Hudu na samu miscarriage daya” “When last kika samu miscarriage?” “Ba a dade ba be wuce wata biyu zuwa uku ba” “Mi kikai aka kawo ki asibiti mi yasa kike kuka?” Hannu na kai na taba fuskata sai na ji sanyin hawayen dazun da ba su bushe ba. “Wata yarinya ta fada rijiya kuma ta mutu shine abun ya firgita ni” “Shiyasa kika samu kanki unconscious?” Kallon rashin fahimta nai masa. “Miyasa kake ta min wadannan tambayoyin?” “Sun shafi lafiyarki ne, na duba files dinki na ga komai after that kina fama da cutar damuwa, kin sha maganinki yau?” “Ban san an kawo ni asibitin ba sai yau” Saurin tashi yai tsaye sai ya kai hannunsa a karo na uku ya taba fuska, sai kuma ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayar da ban taba irinta ba ya miko min. “Saka min Number ki a nan zan, akwai bayanin da zan miki akan ciwonki yanzu sauri nake yi” Tsakanin wayar da fuskarsa sai idanuwa suka kasa tsayawa kallon abu daya, fuskarsa ko kuma wayar ko tambayar da ta cika min zuciya? Mi zai saka likita ya tambayi number wayata? Wane irin bayani ne da ba zai iya yi min ba? “Wane irin likita ne kai? Wane bayani ne da ba zaka iya yi min ba? Ni ban gane ba? Waye kai? Ka bar ni na ji da abunda yake damuna dan Allah” “I'm sorry” Ya fada sannan ya nufi kofar fita kamin ya fice ya sake waigo ya kalleni. “i'm sorry” Sannan ya fice, ni kuma na lumshe idona ina maida numfashi a hankali, tsakanin fitar Mutumen da ban san wanene da sake turo kofar dakin a shigo be wuce minti biyar da yan dakiku ba. Da sauri na sake bude idon a zato na shine ya sake dawowa sai ni arba da Abdallah ido cikin ido wani irin faduwar gaba na ji wanda ban taba jin irinsa ba, sai na ji yayi min wani irin kwarjini kimarsa ta cika ido, hakan yasa ni kawarda kaina daga barin kallonsa har ya karaso kusa da ni, yawo ya rika min da hannunsa a fuskata kamin ya kai hannunsa ya taba ni. “Halimatu....” “Na'am” Na amsa ba tare da na kalleshi ba, ina iya jiyo sautin fitar iskar bakinsa kamin ya kai hannunsa ya daga idona. “Sannu yaushe kika tashi?” “Ban dade sosai ba” “Okay” Da kanshi ya shiga ba ni kulawa kamin ya fita ya hado min tea ya dawo. Ya mika min tea na saka hannu na karba idonaa na kaina, yana ta kallona kamar be taba ganina ba, har na gama shan tea na aje kofin be dauke idonsa daga gareni ba. Dagowa nai na kalleshi a zatona zai kawarda idonsa ne amman kamar jiran yake mu hada sai ya cigaba da kallona ido cikin ido, hakan yasa sai duk na

Chapter 26 of 55