Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dauke kai ya kalli Mama. “Allah ya saukewa Mama, ya kamata a saka ido sosai akan yaran nan, a samu wanda zai rika kaisu ya dauko su zai fi....” “Ba sai ka fada mana ba, can baya da ake kula da su kai kake kula da su ne? Ba yara ba ne mu da zaka fada mana abunda za mu yi” Aminu ya fada cikin fusata da daga murya. Ko da wasa Abdallah be kalli inda yake ba sai yai kamar be ji abunda yake fada ba, har sai da ya duba agogon hannunsa sannan yai masa wani kallon wulakanci, cikin wata irin isa da jin kai ya zuba hannayensa aljihu yana fadin. “Magana kake Malam Aminu... Ai ban lura da kai bane Aminu... Ashe kana gurin...” Maganar Abdallah bata karawa Aminu komai ba sai fusata da kawo zuci kusa har launin idonsa ya canja. “Ya za ayi ka lura da ni ka shigo hankalinka sama” Dariya Abdallah yai kamar ba komai sai kuma ya juya ya kalli Hajiya. “Ikon Allah ashe har da mahaifiyarka ma, Na shigo hankalina yana gurin Amal ne, ka san ni Allah ya saka min son yaya musamnan na Halimatu, to sannu Hajiya” Ya karasa yana da risinawa kamar da gatse, sannan ya kalli Mama still with murmushi a fuskarsa ya ce. “Mama zan fita sai na sake dawowo” Har Aminu ya bude baki ya sake fadar wani abun sai Hajiya tai masa hani da ido, hakan yasa shi hade maganar tare da bacin ransa. Abdallah ya nufi kofar fita yana kallon Aminu fuskarsa da murmushi mugunta. HALIMATU POV. Har na yi nisa sai kuma ya juyo na dawo gurin da yake da sauri, ban same shi a gurin ba hakan yasa na daga kaina na fara waige waige a gurin, kamar yasan shi nake nema sai ya dago min hannu daga can inda yake tsaye jikin wata kotuwar mota mai ruwan toka, kamar kar na karasa a inda yake, sai dai kuma akwai tarin tambayoyin da shi kadai zai amsa min ba, akwai abubuwan da nake son a banbance min, ina son ko wane launi da zanen kaddarata ya fito min a kalarsa, fari yai fari fes bakin yai baki wulik ta yadda zai fuskanci alkibila ta, ina son sanin wanene shi, a yau ina son nai ninkaya a duniyar tarihinsa, ina son na bazama a duniyar mafarkinsa a kaina na wanzu da burinsa da dalilin bibiyata da yake. “For the last time waye kai?” Ita ce tambayar da na fara aika masa tun kamim na isa daf da shi, ina ta yawo da idanuwa a fuskarsa. “Kina da bukatar hutu, ya kamata ki huta daga baya sai mu yi maganar” “Hutu? Hutu a duniyar macen da ta zo bauta? Hutu a rayuwar matar da manta da jindadi a rayuwarta? Fada min waye kai...!” Na fada da iyakar karfina har sai da ya soma tsorata ta yanayi na. “Sunana Abraham zauna a ciki sai mu yi magana” Ya fada yana bude min motarsa. “Sunanka baya min dadi ka daina maimaita min abunda na riga na haddace, kasan me nake nufi ka bani amsa kawai” “Idan na baki amsa ba zaki guje ni ba? Idan na fada miki waye ni ba zaki kyamace ni ba? Ki min alkawari cewar fada miki waye ni ba zai kawo kiyayya a tsakaninmu ba” Kallon mamaki nake masa. “No wait.... Why all this?” “Saboda na taba cutar da ke.... ” Har lokacin da yake maganar ban kawo komai a raina har sai da ya fadi kalmarsa ta karshe, zuciyarta ta fara raya min wani abun da ban taba mafarkin faruwarsa, lalabe na fara yi a duniyar tunani na, sautin wacan muryar nake hada da wannan, ina ta kokarin siffanta surar wacan da wannan, farat daya na nemi duniyar tunanin nawa na rasa, abubuwan da nake kokarin hadawa duk suka watse, sai na ji kan nawa kamar babu komai a ciki. Tafiya nai bayabaya kamar zan fadi sai yai saurin kai hannunsa zai kamani. “Dan.... Allah... Kar.. Ka... Taba... Ni... ” Na fada a wahale, wasu zafafan hawaye na sauko min, kamar yadda shi ma idanuwansa suka fara fitar da hawayen. “I can't hide it anymore yanzu, ba zan iya cewa ba da gangan na aikata ba, i rape you amman ban tsammanci zan dawo gareki ba, and on that very night da kika fada min kin samu cikina ban iya bachi ba a ranar saboda tunani da farinciki jin haka, daga lokacin na samu kaina da kaunar ki da kuma son rayuwa da ke, because my only hope and pray is na samu haihu kamin na mutu, na san zan iya mutu at any moment, but i want to make my parents proud, and ina son ko na mutu na bar carbon copy na....” Ya karasa muryarsa a dakishe saboda kuka. Risinawa nai gabansa na hade hannayena kamar neman gafara. “Why do you rape me? Mi mai maka?” Sai shi ma ya risino saitin fuskata yana share hawayensa. “I don't know why, na san dai mijinki na je nema a wannan daren.... ” Be gama maganar ba na mike tsaye na juyo tafiya na fara yi kamar mai ciwon kafafuwa, ko wace dagawa da takawa tana min nauyi, ga nauyin zuciya da ya danne min kirji har yana neman numfashina, ina tafe wasu hawaye masu zafi suna sauko min yawun bakin gaba daya ya canja gumi na ta karyo min har kasan marata murdawa yake, ina ta girgiza kai alamar a'a a'a ban daina ba har sai da na hango Abdallah ya fito daga cikin emergency sanye da shadda hannayensa duka biyu zube a aljihu... Tsayawa nai cak ina kallonsa, a yau ji nai kamar an halittoni ne kawai domin kallonsa, kaunarsa da tausayin kazafin da nai masa wanda har ya kai ni ga furta masa. Babu kamar kai Abdallah Wallahi babu irinka, mutumen da ya kasa nuna min kyama balle yayana, mutumen da ke bani taimako da kowace hanya, mutumen da idan nai gudu naje gunsa da bukatuna da damuwata zai tara hannayensa biyu ya karbe ni, na yi kuskure tabbas na aikata kuskure na barin mutune da ya dace da zama abokin rayuwata.... “Kullum cikin kuka kike please smile....” Maganarsa ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da nake, ashe ya karaso kusa da ni ya ban sani ba, fuskarsa da murmushi yana min alama da nai murmushi da yatsan hannunsa biyu kamar yadda murmushin yake a fuskarsa. Ban tana jin kaunarsa Abdallah sai yau ban taba jin kimar Abdallah ba sai yau ba, ban taba jinjina abunda yake min ba sai yau. Murmushin nai ina hawaye. “That's my girl....” Ya furta sannan ya maida hannun aljihu yai gaba abunsa, kamshin turarensa ya daki hancina har sai da ma lumshe idanuwana.... Na samu dakika biyar a haka kamin na juya ina kallon tafiyarsa cike da kaunarsa, wata kila jikinsa ne ya bashi cewa ina kallonsa sai ya juyo ya kalleni tare da aiko min da kyakkyawan murmushin wanda ya sanyaya min zuciya ji nai kamar na ruga na rumgume shi na fada masa cewar yau Ni Halimatu ina kaunarsa..... ___________ Ana wata ga wata, ina masu team Abraham ashe abun na ku.....🤐😥 Team Abdallah Team Gwarzo Za mu ga team din da yafi yawa 💃💃 7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣8️⃣ Ban koma cikin dakin ba, a harabar da amsu jinya suke zama na samu butar wata matar nai alwala ta bani carpet nai sallah nai addu'a sannan na tashi na nufi wani bangare na asibiti gurin da aka kawata da furanni da kuma hasken fitulun kasancewar hudu ya fara. Tsaye nai a gurin ina ta kallon sama wata iska mai dadi na kadawa hawayen idona na ta aikinsu, babu abunda nake tunani sai Abdallah babu wanda nake hangowa a tare da ni sai a yanzu nake ganin dacewar tarairaya ta da Abdallah. “Uhmm na san na bata miki akan maganar da nai dazun amman iya gaskiyata nake fada, kina da damar da za ki ji haushi na ki tsaneni kuma zan jira har zuwa lokacin da zaki warke daga raunin da nai miki.... ” Juyowa nai a hankali na kalli Aminu wanda ke min maganar, sai a yanzu nake kallonsa da kyau ya rame sosai ya dan yi duhu. Dan murmushi nai na nufi wata karamar balcony na zauna sai shi ma ya tako ya zo ya zauna kusa da ni. Magana na fara yi ba tare da na kalle shi ba “A lokacin da nake budurwa idan mai ma mahaifiyata ko mahaifina wani aiki ko abunda ya faranta musu rai, sukan ce min Allah yai miki albarka ya baki miji na gari, ni kaina ina yawan addu'ar a sallah ta, a lokacin da ka zo kace kana so na ka aureni sai na ji cewar Allah ya amsa addu'o'inmu, bayan na yi haihuwar farko ka juya min baya, sai na fara addu'a ina ta fata da ganin kamar wata rana zaka daina, da nai haihuwa ta biyu sai na fara karaya, daga lokacin ne na dauka cewar aurenka yana cikin mummunar kaddarata, domin zama da mazinacin namiji ba abu ne mai sauki ba, kullum ina cikin fargaba, kullum ina cikin addu'a, kamin wani lokaci sai alakar auratayyarmu ta canja, na kuma maka kamar bakin maciji, idan nai kwaliya ina jiran ka dawo ka yaba min, ba zaka dawo ba sai tsakiyar dare, a maimakon idan ka kalleni kace na yi kyau sai ka fada min cewar siraran mata suna can suna can waje suna jiranka, a gabana kake yabon wasu mata a wayarka ko a tv saboda kawai na ji zafi, bayan ka san a lokacin da ka aureni ba haka nake ba, kyau jikina na daya daga cikin abunda ya dauki hankalinka har ka zo gurina ka nuna kana son aurena, a gidanka halitta ta canja Aminu saboda yayan da na haifa maka yasa jikina ya bude, halitta ta tashi daga budurwa zuwa matar aure, na bar iyayena na bar yan'uwa da kowa nawa na koma gidanka cikin yan'uwana da zama, amaimakon ka tausaya min ka mutunta ni sai na zama abar wulakantawa, kai ka yi min mahaifiyarka tai min yan'uwanka su yi min, ka dinga fada kana cewa na haifa maka yara da yawa zan tsofar da kai, hakan yasa na fara tunanin planning, kace na ciki kiba kai ba haka kake son mace ba ka fi son siririya, babu irin kudin da ban kashe ba akan nai slimming amman ban samu sa'a ba duka ka san saboda me? Saboda na faranta maka saboda na gyara rayuwar aurena, wani lokacin idan na unkura sai na ji kamar ba zan iya fita na bar yayana ba, hakan yasa na yarda aurenka yana cikin kaddarata, wasu akan jarabesu da kiyayyar uwar miji, ko yan'uwansa, wasu kishiya wasu mijin wasu yaya wasu rashin abinci wasu rashin lafiya, to sai aka jarrabe ni da abubuwada yawa, da gangan kake kin siyo mana abu mai dadi ko na marmari wanda za mu ci mu jidadi saboda kawai ka musgun min, ka dauki karan tsana ka dora min saboda kawai na aureka na haifa maka a yaya, a ranar da na tambaye ka 2k ka hana ni a ranar na ga alert dinka na turawa wata 30k+ ka tuna....?” Tun da na fara naganar yake hawaye har na kai aya, be iya bani amsar tambayar ba ko kallona sai ya kasa yi. Hannu na saka na share hawayena ba tare da sun bar zuba ba. “A kowa ce rayuwar aure akwai kalubale, na sani shiyasa na jure zama da kai a wacan lokacin. Amman wani abun mamaki a lokacin da kake ki na kaka nuna min kiyayya a lokacin ne Abdallah ya nuna yana so na, bashi kadai ba a duk inda na shiga maza basa dauke ido a kaina amman nawa mijin....” Kasa karawa nai saboda kukan da ya ci karfina. “Na yi miki abubuwa da yawa Halimatu, a lokacin ina jin kamar ke din matsala ce a rayuwata, ban gane muhimmancin ki ba sai bayan na rasu da ke, duk abunda zan fada miki a yanzu na san ba yarda za ki yi ba, amman Wallahi zuciyata babu wanda take mamari take kauna sai ke, na aikata babban kuskure na rabu da nai da ke, amman ko a wacan lokacin ina son ki Halima, kawai dai sherin zuciya ne da na shaidan. Amman a yanzu na canja Wallahi duk wani hali marar kyau nawa yanzu babu shi..... ” Sai a lokacin ya kalleni ya sauko daga zaunen da yake ya risina gabana. “Ki dubi girman Allah ki yafe min, ki duba yayanmu ko dan su ki yafe min, ni da Hajiya duka mun yi nadama, Wallahi babu daren da bana kukan rashinki Halima....” “Kana son na yafe maka?” Yayi saurin gyada min kai jikinsa har rawa yake kamar ba shi ba. “To ka maka dan'uwanka a kotu, ka tsaya da kafafuwanka har sai ka kwatowa yarka yancinta......” Ina fadar hakan na mike tsaye ina share hawaye na kauce daga gabansa na fara tafiya.... “Idan nai hakan zaki yafe min ki dawo ki zauna da ni da yayana?” Juyowa nai na kalleshi. “Wata kila dai zan iya yafe maka na goge sunanka daga bakar takardar da na rubuta shi, amman zancen zama aure a tsakanin ni da kai wannan har abada ne, sai dai wata mai sunana amman ba ni ba....” Ban tsaya jiran abunda zai fito daga bakinsa ba na nufi dakin da su Amal suke, har a lokacin Mama da Hajiyarsa suna dakin a zaune, kusa da Amal na karasa na zauna ina tambayar Aisha wayata. “Yaya Abdallah ya zo nan” “Eh mun gaisa da shi” Na fada ina yin kasa da idona saboda jan da sukai. “Halimatu ayi hakuri da rayuwa, mun san mun yi kuskure mun laifi amman a dubi girman Allah a yafe mana wallahi yanzu Aminu yayi nadama ......” Kaina na daga na kalli Hajiyar Aminu wacce ke maganar murya kasa kasa kamar za tai kuka, sai na kalli Mama nace. “A nan za ki kwana? Ko ni zan tsaya na kula da ita?” Sai Hajiyar Aminu tai karaf tace. “A a ni zan kwana nan kuje ku hutarwarku” Jin hakan yasa na mike tsaye nai musu sallama na fice. A daren ranar kasa bachi nai saboda tunanin rayuwar da nai a gidan Aminu, tabbas na fuskanci kalubale wanda ba ko wace mace ce zata iya jurewa ba. Da asuba bayan na yi sallah na dora da karatun qur'ane, misalin shida da yan mintuna na sha ruwa na koma bachi, bayan begen Abdallah da zuciyata ta kwanta da shi har da mafarkinsa sai da nai a bachin nan nawa na safe. Kiran waya ne ya farkar da ni duk kuwa da kasancewar bakuwar number ce hakan be hana ni dauka ba. Tun da sallamar matar ta daki dodon kunnena na gane mahaifiyar Aminu ce, ita ta fara miko min gaisuwa ni kuma na amsa mata da ina gajiya. Ta fada min wai kar a dafa komai tasa an kawo musu daga gida, ni dai da to kawai na amsa mata na aje wayar. Misalin tara na shirya na cikin bakar abaya kamar yadda na fi son sakata a duk tufafina na fita da zimmar idan na bar gidan Abdallah na je asibiti, so nake na tafi na bawa Abdallah hakuri kuma na fada masa labarin mutumen nan, and i got lucky na tarar ya shirya cikin kananan kaya na shirin zuwa office. And wani karin farincikin kuma shi ya bude min kofar da kansa yana rike da mug. “Ina kwana?” Na gaishe shi ina murmushi sai ya amsa min fuskarsa ba yaboba fallasa. “Ya kai?” “Zan iya shigowa magana nake son yin da kai.....” Daga can bayansa na jiyo muryar Suwaiba tana da fada. “To wannan abun ya wuce gona da iri, ya zama iskanci da cin fuska, kuma Wallahi ba zan dauka ba ke bakya ma jin munya bibiyar kanen tsohon mijinki... Kai tirr Halima kin yi abun kunya.... ” Da muryar da na san zata iya jiiyoni na ke fada masa cewar. “Ka ce tai hakuri na san babu dadi, amman babu abunda zai yanke alaka a tsakaninmu...” “Muje waje mu yi maganar” Shine abunda ya fito bakinsa, bakin nasa nake ta kallo kamin nai backwards na fita daga falon, wanda hakan ya bashi damar fitowa ya janyo kofar ya rufe. “Ya kai....” Yan yatsuna na fara murzawa sai hawaye. “Daman na zo ne na baka hakuri akan abunda ya faru..... ” “Ai na ce miki ya wuce ko? Ni ban rike ki da komai ba tun wacan karon na ce na yafe miki” “Ba shi ba, akan duka abubuwa da nai maka” “Na yafe miki Halimatu....” Na kalleshi cike da kaunarsa wacce ta mamaye qalbina take taraiya da numfashina a yanzu, kai na gyada masa alamar gamzu. “Kuma ina son ma fada maka wani abu....” Sai yai hanzarin katseni. “Bana son jin komai a yanzu pls” Na sake gyada kan a karo na biyu ina hade yawuna. “Amman magana ce mai muhimmanci akan maganar fyaden..... ” “Oh Please haba dai bana son jin komai a yanzu” “Shikenan, zan jira har zuwa lokacin da kake son ji, zan tafi amman dan Allah ka rika daukar wayata idan na kiraka kuma ka rika min reply idan ka ga sakona pls dan Allah” Be ce min uffan ba har na juyo na fara tafiya, sai jin mutum nai a gafena yana takawa tare da ni. “Dan Allah Halimatu ki cire komai a ranki, ki nemi aiki ko wata sana'a zaki iya tallafawa kanki ki rage damuwa kin ji? Ki cire kowa a ranki” Tsayawa nai na kalleshi. “Babu kowa a raina a yanzu, na cire komai na fahimci komai, babu wanda yake cikin raina Abdallah sai kai....” Kallon mamaki yake min is like kamar be yarda da ni ba, juyawa yai ya kalli bayansa kamin ya nuna kansa. Ni kuwa na gyada masa kai cike da kuzari, can ya busar da iskar bakinsa. “Ya rabb, wato baki daina shayeshayen nan da na ce ki daina ba ko?” Na matso kusa da shi ina girgiza masa kai. “Ban sha komai ba Wallahi a hayyacina nake” “No Halima ba zata fadi haka a hayyacinta ba, ko dai damuwar nan ta dawo miki ko kuma kin koma ma shaye shayen” “Wallahi ban sha komai ba” Na fada ina masa magiya kamar zan fasa kuka. “Shikenan ki tafi gida” “Zan tafi duk abunda ka ce zan yi Abdallah” Kamar umarninsa nake jira sai na juya da sauri na fice daga gidan. AHMAD POV. Glass cup ne a hannunsa yana kurba lemun a hankali, while idanuwansa suna watching plasma but his heart is one where else. Yana jin tsananin damuwa da kadaici a rashin Baby Namra da Matarsa da kuma mahaifinsa a rayuwarsa, sai dai his try be strong for him mother and his sister Siyama, domin su kadai suka rage masa a yanzu, he feels like da ace mahaifinsa yana raye da abubuwan sun masa sauki, kamar yadda da ace Baby Namra tana nan wata kila da be shiga damuwa haka ba damuwar da ke taba lafiyarsa ta taba rayuwarsa, he missed his wife his father his daughter. Be dawo daga duniyar tunanin Gobensa ba har sai da Hajiya ta soma magana da shi ayayinda take zaune saman sofa Siyama na kasa tana matsa mata kafafuwanta. “Dazun Laraba ta kirani tace wai dan Allah a taimaka mata a dauki danta aiki a kamfaninku...” A hankali ya juyo ya kalleta. “Ai ba irin su muke dauka ba, yan boko, kuma kin san Attahiru ba wani boko yai mai zurfi ba, idan ma yayi ba zai wuce secondary school ba” “To a duba masa dai haka nan tunda har ta roka sai a samu inda aka laba shi” “Hajiya ki dai fada mata masu ilmi muke dauka saboda kamfanin a yanzu yana bukatar gogaggun.....” Be marasa ba ya fara tari da sauri ya aje lemun hannunsa ya ciro handkerchief dinsa ya tari jinin da ya fito daga bakinsa. The white handkerchief din ya bawa Hajiya da Siyama damar ganin jinin da kyau, daga Hajiya har Siyama sai ka rasa wanene hankalinsa ya fi tashi... “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un... Mi zan gani haka?...” Cewar Hajiya. Sai yai murmushi yana nuna mata cewar ba komai ba ne. “Habo na ke yi, daji ne ya kamani da mura ba wani abu ba” “Brother yaushe ka fara haka?” Siyama ta tambaya hawaye na sauko mata, kallonta yai he know he can't hide anything from her domin karatun likita take kuma ta fi kowa sanin waye dan'uwanta. “Can we talk private?” Hajiya tai saurin amsawa tana girgiza kai tana kuka. “No I'm your mother be kamata ka boye min komai ba, how do you expect your own mother to live after you death? How? Ku kadai kuka rage min daga kai sai wannan” Ta nuna Siyama hannunta na rawa tana fashewa da kuka. Da sauri tashi yai ya koma gabata. “Wallahi Hajiya ina shan magani kuma i believe zan ji sauki, duka duka ban hi sati da fara wannan tarin jinin ba, kuma na ga different doctors sun bani magani ina kan sha” Siyama ce ta taso ta zo bayansa ta rumgume shi ta fashe da kuka. “Please Brother we love you..... ” He feel so hopeless, so emotional but a haka yake kokarin ganin ya zama very strong for them. 7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣9️⃣ Tun daga lokacin da Hajiya ta lura da halin da danta yake ciki bata sake yarda ta barshi ya zauna shi kadai ba indai yana gidan to yana falo tare da ita ko kuma yana harabar gidan suna fira, a ganinta sakewarsa zai taimaka masa fiye da kadaicewar da zai yi shi kadai yana tunani da saka kansa a damuwa.   Kamar yadda ta saba masa after dinner suna zaune dinning ta dauko masa zancen aure domin shi ne abunda ta fi son taga yayi a yanzu ko zai rage masa damuwa har ma ya kawo masa farincikin samun wata haihuwar. “Tun kwanan baya na maka magana akan aure kace zaka yi tunani ba ka ce min komai ba” Ya kurba ruwan da ke gabansa kadan yana dan murmushi. “Hajiya bana son zancen aure a yanzu” “Saboda me? If saboda ni ne zaka iya zama a wajen gidan nan da matarka, and ba zan cilasta maka auren Ikilima ba, sai ka dauko budurwa da kake so ka aura” “No ba wai Budurwa ko bazarawa ba, a halin yanzu mace bata gabana, ni ban ki na mutu a haka ba” “Saboda me? Ni bana son ganin jikanka ne? Ku kadai Allah ya bani ai zan so ku yi aure ku yi juri'a da yawa ba kamar ni ba” “Kawai ina ganin kamar idan na sake haihuwa rasata zan yi, ni kuma bana son abunda zai sake kasani a damuwa yanzu” Hajiya ta yi murmushi. “Baka da karfi zuciya sai kace ba namiji ba” “Hajiya ba zaki san abunda nake ji ba, babu wanda zai shiga a irin halin da nake ciki a yanzu ace be samu kansa a damuwa ba” “Yes dole na ka damu an sani ai, amman ka rika sassautawa rayuwarka, ita daman rayuwa tana tafe da kalubale kala kala, wani mai sauki wani mai wahala, sai dai duk halin da zaka shiha ka rika tunawa akwai wadanda suka fika shigarsa, idan arziki ne akwai wadanda suka fika, idan talauci ne da damuwa akwai wadanda suka wankeka suka shanye, kai mata kawai ka rasa sai ya kuma uba, akwai wata macen da na gani na ita tana da uwar a raye uba a raye dukan ya'yanta suna nan, amman kalubalen rayuwar da ta shiga ko kan akaifarta baka shiga ba, tun daga lokacin da na ji labarin matar nan abun ya tsaya min a rai” “Indai har tana da kowa a raye mi zai saka ta a damuwa” Har Hajiya ta bude baki ta fara labarta masa labarin Halimatu sai ga Siyama ta dauko fuskarta dauke da damuwa taja kujera ta zauna tana fadin. “Ni kam i don't think zanje gaskiya” Ahmad ya kalleta. “Why? Saboda Baby bata nan? Mu da Hajiya za mu je kamar yadda muka saba a kowace shekara” Yana fadar hakan ya mike tsaye ya bar dinning table din ya nufi hanyar da zata fitar da shi daga falon zuwa part dinsa. Hajiya ta kalli yarta cikin kwarin guiwa tace. “Idan ba mu karfafa masa ya manta da komai ba, taya za mu taimaka masa wajen tunawa da abunda zai tsaya masa arai, a kowa ce shekara shi yake bada kaso 50

Chapter 30 of 55