ya koma sabo, saboda yadda nake ta nawa kukan, idan na kalli kanena da mahaifiyata da abokiyar zamanta sai na rasa wa zan tausayawa.
Hakika mutuwa bata da dadi, duk wanda ya zo mana gaisuwa sai yai mana nasiha akan hadin kai da son junanmu, an yi ta zuwa mana gaisuwa mutane da yawa wasu har bana ganesu, abunda Abdallah yai min ya kara min son sa sosai a raina, ya nuna min na zama mai karfin zuciya da dakiya, ni ce babba idan kanena sukai ba daidai ba na musu fada kamar yadda zan yi ma yayana, ya kawo abinci mai yawa da kudi. Abdulhamid ma ya saka an kira masa ni yai min gaisuwa, Aminu kam da shi akai zaman uku har aka gama, ranar da akai sadakan ukun mama take fadin cewar Ahmad ya aiko muna da abinci da kudi mai dama kuma ya shigo har cikin gidan yai musu gaisuwa.
A daren ranar Abraham ya ziyarce ni, irin ziyarar da ya saba kawo min a duk lokacin da ya so ganina.
At first fuskata ya fara haskawa da wayarsa.
“Ki yi hakuri, rashin wani ba dadi duk da dai ban rasa kowa ba, amman na san babu dadi can I hug you”
“Na gode”
Na fada ban jira cewarsa ba na jiya na bar masa wajen, a daren ranar sai gidam ya zame mana kamar wani kango, muna ta firar Baba muna kuka, Aisha take cewa kara ni na yi aure na haihu har yaga yayana su ko auren ba su ba, sai naji duk tausayinta ya kara kamani.
Wasa wasa aka dauki sati daya babu Baba Mama da Inna suka shiga takaba, a lokacin ne na kara tabbatar da mutuwarsa, a kowace rana sai na tuna yadda nake zuwa gaishe shi da yadda yake shigowa cikin gida.
Haka na kwashe sati biyu ban leka gurin aikina ba, kowa kuma be leko ni daga can ba, sai dai wata na karewa na ga albashin 67000, maimakon na jidadi sai na ji rashinsa domin na saba a lokacin da nake aiki nakan cire wani abu nai ma Baba da Mama da Inna siyaya.
Washe garin ranar da na ga albashin na shirya na tafi gurin aikina, ban ji kowa ya min gaisuwa ba hakan yana nufin babu wanda ya san da zancen mutuwar kenan, na nufi office dina cikin rashin walwala, sai na samu matar can a ciki wato Zainab, mun gaisa da ita cikin mutuntawa sannan tai min bayani wai oga ne yace ta zauna na wucin gadi har zuwa lokacin da zan dawo.
“Okay”
“Amman ki fara zuwa ki fada masa kin dawo tukuna”
Ba musu na juya na fita daga office din na nufi hanyar da zata sadani da office dinsa, sai na shiga office na farko na shiga na biyu sannan na isa nasa. Ko da na shiga yana zaune jikin kujera yana waya, ganina ya saka ya yanke wayar ya taso da far'ar shi ta wayayin mutane kamar ba Ahmad ba ya tare ni.
“Wow my friend na dauka zaki yi wata fa”
Na yi kasa da kaina.
“Ina kwana ranka ya dade”
“Lfy kalau ya hakuri”
“Al-hamdulillah, na zo office na tararda wata”
“Yeah kin san gurin ba a barinsa hakanan ba kowa, shiyasa muka sakata kamin ki dawo, ina fatar ba mu yi laifi ba”
“Kamfaninka ne kana da dama da yancin da zaka yi duk abunda kake so, ciki har da korata ko canja min gurin”
Na fada muryata na fita so slow.
“Hajiya tace kar na koreki, yanzu ko kin min laifi bana da halin korarki tun da Hajiya ta shiga tsakani, kin shiga ranta sosai kusan kullum zancen ki muke.....”
Na yi murmushi ina murza yatsun hannuna, yatsun nawa ya kalla sannan ya kalli fuskata kamin ya juya zuwa gurin teburinsa.
“Na gode”
Daga can inda yake tsaye ya dago ya kai ya kalleni.
“Da me?”
“Da komai da komai, na gode Allah ya saka da alheri”
“Amin Allah ya bamu hakuri we almost sharing the same journey, yanzu kin fahimci yadda rashin mahaifi yake kamar ni, gashi kece babba duk wanda zai miki magana zai ce ki yi kokarin hada kan yan'uwanki right”
Ya karasa yana murmushi kamin ya cigaba.
“Haka akai ta min sai nake jin kamar an dora min wani nauyi akai, na rika ganin kamar ba gaske ba ne, ina ta ganin kamar idan na shiga gida zan ga Abbah, idan na kalli Hajiya ta bani tausayi haka ma Siyama, yanzu da nai hakuri na dauki nauyin sai abun ya zo kin da sauki, amman fa har yanzu Hajiyata bata yarda na girma ba, idan zan fita zata bani time din dawowa idan na dade zata kirani tace na dawo dare yayi ko rana, babban mutum kamar ni”
Daga ni har shi murmushi muke sai ya tako ya karaso kusa da ni ya miko min tissue, ashe ya lura da hawayen da suka taru a idona.
“Miyasa ba ki koma gurin Doc ba?”
Na yi shiru ban ce komai ba, be kuma be fasa kallona ba, can kuma ya karasa ya dauki wayarsa ya taba sannan ya kalleni.
“Zaki iya zuwa office dinki”
“Na gode”
Na fada sannan na juya na fito daga office dinsa na nufi nawa office din, ko da na shiga matar bata nan, sai na suke jakata na zauna a kujerar ina ta tunanin mahaifina.
Ban yi aikin kamar yadda na saba ba, domin rashin kowa a kusa da ni sai ya kara saka ni cikin damuwa da tunani kala kala ciki har da na rayuwata da kuma Kabir ko yana ina ma yanzu Allah masani.
Misalin biyu da rabi Ahmad ya shigo office dina ganinsa yasa na tashi tsaye.
“Wata takardar nake nema, ta green light company”
A take na fara duba takardun da suke gaban teburin sai kuma nai arba da ita.
“Takardun da kika san zan yi amfani da su ki rika kai min ko kuma ki bawa sakatarena”
“Okay In-Sha-Allah zan kiyaye”
Har na mika masa takardar ya juya nace.
“Ranka ya dade ina son tambaya”
Juyowa yai yana kallona.
“Dan Allah Kabir nake tambaya, wani mahaukaci wanda ya makure ni ka”
Murmushi yai.
“Mutumen da kika ja min ya naushe ni ido kenan”
Nima murmushin nai.
“Kina son ganinsa ne?”
“Eh tun ranar ban sake ganinsa ba”
“Na saka a dauke ke shi ne akai shi gidan mahaukata”
Na ji ba dadi har hakan ya kasa boyu a a fuskata, sai kallonsa nake na rasa abunda zan ce masa. Dawowa yai gaban teburin nawa ya tsaya yana kallona.
“Karki damu, ina son ki samu natsuwa ne sai mu fara processing din nema masa lafiya, tun da naga ciwonsw ya dame ki”
Da sauri na mike tsaye baki sake ina zaro ido.
“Da gaske?”
“Da karya”
Ita ce amsar daya bani ya juya ya fice daga office din yana murmushi.
__________________
Assalamu Alaikum.
Ban yi niyar cewa komai akan littafin nan ba, duk kuwa da irin comments din da nake gani musamman whatsapp, wasu na complain abunda nake ma Halima yayi yawa so so this and that, akwai ma wacce tace min tana kwankwanton imani akan irin halin da nake saka Halima, na ji zafin maganar amman nai mata uzuri saboda ina daukar tana cikin irin mutanen da ke karatu basa daukar darasi burinsu kawai a samu nishadi.
Ina son ku sani idan ma baku sanin ba, idan kuma kun manta na tuna muku tun farkon fara labarin nan sai da na fada cewar ban sani ba ko zai muku dadi ba labari ne na soyayya ba kamar yadda aka saba, labari ne na fadi tashin rayuwa, kalubalen rayuwar da na aure wanda zai tabo wani bangare na rayuwarmu ta yau da kullum.
Duk yadda kike jin dadi Wallahi baki kamo wata ko a farce da jindadi ba, haka duk yadda kika a cikin tsanani baki kai kan akaifar wata shiga kunci rayuwa ba, labarin nan kirkiren labari ne amman ni nasan ba za a rasa wandanda suke rayuwa irin ta Halima ba, domin na ci karo da wasu a lokacin da nake rubutun nan, wani jarabarwarsa kadan ne wani da yawa, kuma kowa da inda Allah yake jarrabarsa. Idan baki cikin matsala wata na ciki, kuma ban cilastawa kowa karantawa ba sai wanda yaji yana ra'ayi, dan haka dan Allah kar wacce ta sake yi min wata magana marar dadi akan rayuwar Halimatu, duk wanda ya sake fada min rashin arziki goma billahil azeem zan fada masa ashiri, ba dole sai rai na so.
And wandanda suka tuna mahaifansu jiya, wasu har da kuka, ina addu'ar Allah ya jikansu, mu kuma ya sa mu cika da imani.
Ameen thumma Ameen.
7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
4️⃣8️⃣
Tun daga yanayin tafiyata zaka fahimci ina cikin wani irin nishadi marar misaltuwa, na fito daga cikin gidan na nufo inda motar Ahmad take fake ya sauke gilashin motar yana kallona har na karaso, da kansa ya miko hannunsa ya bude min motar, na shiga ciki na zauna ina gyara jakata. Sai yai motar key muka hau titi sannan ya kalleni.
“Happy?”
Na gyada masa kai idanuwana suna kokarin cika da hawayen jindadi.
“Yes”
Sai yai kyakkyawan murmushin daya karawa fuskarsa kyau.
“Thank You”
“No thank you da kika amince, hop dai kin fada musu ke za ki yi ba ni ba”
Na yi shiru ina kallon gorar ruwan daya dauka zai sha.
“Sun jidadi sosai, kuma sun yi supporting”
Murmushi kawai yai ya kalle ya karasa kurbe ragowar ruwan, ba mu yi wata tafiya mai nisa ba ya faka gefen titi yana kallona.
“Bari na karbo ruwa shagon can, bana iya zama ba ruwa a mota”
Bude motar yai ya fita, da wani irin kallo na bishi na jindadin daukar nauyin duba lafiyar Kabir da yai, haka Allah yake lamarinsa idan ya zo taimaka maka sai ya maka hanyar samun abun ko ta ta silar wani ne, and farincikin dana gani a fuskar yan'uwan Kabir a yau da naje musu da labarin ya kara faranta min rai fiye da kima. Wata farar mota ce ta faka gaban ta Ahmad sam ban kawo komai a raina ba, har sai da na hango Aminu ya fito daga cikin motar a fusace ya nufo inda nake, ganin hakan yasa na bude motar na fito na rufe tun kan ya karaso.
“Halima me kike a cikin motar nan?”
Haka ya aiko min da tambaya kamar wani ubana.
“Ban gane mi nake a ciki ba?”
“Abunda kike be dace ba, tun dazun na hango ki a cikin motar nan ina biye da ku har kika shiga wani gida kika fito, ya kamata ki san abunda kike fa wannan ba muharramin ki bane, kuma ki rika tunawa cewa kina da yara”
“Wace irin magana kake yi haka Aminu?”
“Kin san me nake nufi”
Ya fada yana kara hade fuska, sai wani huci yake kamar ba shi ba.
“Ya akai?”
Ahmad ya tambaya yana kallona hannunsa rike da gorar ruwa biyu.
“Ba komai”
Na fada ina dauke idona daga barin kallon Aminu.
“Oh ba komai za ki ce masa? Malam akwai komai wannan mata ta ce, miye hadin ka da ita?”
“Who's this?”
Ahmad ya tambaya yana kallona. Sai Aminun ya amsa masa da kansa cikin fusata.
“Mijinta ne uban yayanta”
Wani kallon uku saura kwata Ahmad yai masa.
“Sannu Uban yaya, da alama dai kana shaye shaye, domin mai hankali ba zai yi abunda kake yi ba”
“Ba shaye-shaye nake ba, ciye ciye nake, ka fita hanyar tun kamin dare yai ma, domin matata ce”
“Babu wani abu a tsakanina da shi Aminu, boss dina ne a gurin aiki, kuma kai baka isa ka hanani magana da wani namijin ba, domin babu igiyar aurenka a kaina”
“Amman akwai yaya a tsakaninmu ko?”
Ya fada cikin daga murya mutane har sun fara mana taro, Ahmad ya bude min front seat.
“Shiga ki zauna”
Ina kokarin zaunawa Aminu ya fisgo Hijabina har sai da fuskata ta daki ganbun motar.
A take Ahmad ya wulgar da gorar ruwan dake hannunsa ya zabgawa Aminu mari cikin zafin nama.
“You're very very stupid”
Aminu ya zaburo zai rama Ahmad ya rike masa hannu ya wulgar.
“Ni ka mara? Ni ka mara? Na san ko ni wanene? Akan matata?”
Shine abunda yake ta fada yana nufi gurin motarsa ya dauko wayarsa daga can gurin motar ya tsaya yana wayar, kamar yadda Ahmad din ma yake waya a kusa da ni. Faruk naji ya kira sunan mutumen sannan ya fada masa abunda yake bukata tare da bashi addireshin inda mike. Sannan ya juyo ya kalli gefen goshina dake zubar da jini. Zagayawa yai ya bude motar ya dauko tissue ya mika min.
“Sannu”
Ya fada cike da nuna danuwarsa. Sannan ya kalli Aminu dake kokarin shiga motarsa yace.
“Indai ka cika kai dan iska ne ka tsaya nan”
A take Aminu ya rufe motar ya sake nufo inda muke.
“Me kake nufi? Tsoronka ake ji? Uban waye kai a cikin garin nan? I warning you Wallahi Wallahi idan na sake ganinka da matata sai na halaka ka, dan iska kawai marar mutunci mai neman matar mutane”
Uffan Ahmad be sake ce masa ba, sai danna wayarsa yake. Aminu kam duk maganar daya yago sa ya yabawa Ahmad, ban tana ganin bacin ran Aminu irin na yau ba, tun da be tana fada a kaina ba, be tana nuna damuwarsa dan wani ya kula ni ba sai yanzu, jikinsa har wani rawa yake, kana kallonsa ka san kishi ne ke dawainiya da shi, kuma na banza domin a yanzu kam na masa nisa.
“Ina kokarina ashe kai ke dauke mata hankali, wawa kawai”
Ya karasa yana kai kafarsa ya shuri motar Ahmad, har lokacin Ahmad be kula shi ba, sai da motar soja ta iso, da hannu Ahmad ya nuna musu Aminu.
“Ku masa shegen duka sai ya dawo hayyacinsa”
Ba ni kadai ba duk wanda ke a titi kallon motar sojojin yake, a yadda naga yana wayar na dauka police zai dauko ashe uban police ne, kamar sun samu nama haka suka ka kama Aminu, suka ci kwalarsa amman be daina bala'in ba.
“Ni zaka saka a ciwa mutunci? Sai na wulakanta ka wallahi, ka shirya haduwa da ni...”
Ko da suka saka shi motar har sun fara dukanshi. Mutane sai bin motar sojojin da kallo suke kamin su juyo kan mu kallo ya dawo gurinmu. Ba mu bar gurin ba sai da Ahmad ya kira direbansa ya tafi motar Aminu sannan ya shiga tashi motar yai mata key.
“Kin yi kokari haka kika zauna da mahaukacin nan? Be cancanci mata irinki ba, tun farko ya kamata ayi bincike kamin a aura masa ke, how will you face the world ki ce wannan uban yayanki ne? Wani irin hauka yake haka?”
Ni dai bance uffan ba bayan hawayen da nake.
“Shiyasa yake cin zalinki, komai akai miki sai kuka da abun dariya dana bakinciki ko wane kuka dai i wonder how your next husband will handle you”
Ya fada da kamar fada, sannan ya faka motarsa gefen titi ya fita, ya bar ni a cikin motar ni kadai. Tun ina hawayen da gaske har ya daina zuwa sai da ya leko ta gilashin motar ya kalleni sannan ya bude ya shigo muka cigaba da tafiya. Asibitin da aka taba kwantar da ni a lokacin da Baba ya rasu ya nufa da ni, sai da ya faka motar sannan ya zagayo side dina ya bude min motar ba tare da yace min komai ba, ni kuma na saka kafafuwana waje na fito sannan ya rufe motar yana gaba ina biye da shi har muka shiga cikin asibitin, har office din likitan muke da kansa yaja min kujera ya zauna sannan ya zauna a dayar kujerar ya risino yana kallona.
“Bari likitan ya zo yanzu kin ji? Sannu”
Ya kasa dauke idonsa a kaina ni kuma na gagara daga nawa idon na kalleshi.
“Ji yadda ya gusar da farincikin da kika ji dazun, cikin kankanen lokaci, ina mamakin yadda akai kika auri mutunen nan tun farko....”
Ya fada yana kallon likitan daya shigo office din, wacan likitan ne dai wanda ya duba ni a wacan karon. Sai ya daga fuskata ya duba goshin nawa sannan ya tambayi abunda ya faru.
“Buguwa tai ta murfin mota”
“Ayyah sannu”
Ya fada sannan ya juya ya fita, ba dade ba ya dawo dauke da wani karamin akwaiti sai ya hanyo dayar kujerar ya zauna.
“Cire Hijabinki”
“Ba sai ta cire ba”
Ahmad amsa masa tun kamin nai wani unkuri.
“Indai gyaran kake so a mata dole sai hijabin ya matsa daga goshinta”
Doc Nura ya fada yana kallonsa, sai ya taso ya karaso kusa da ni, ya daga fuskata sama ya saka hannunsa ya janyo hijabin nawa ya raba shi da fuskata kamar zai cire sai kuma naji ya yagashi, sannan ya maida min shi a jikina ya zamana kaina na iya wucewa hijabin ya sauko saman wuyana.
Murmushi kawai likitan yai ya dauko safar hannu ya saka sannan ya soma gyara min goshin, idan naji zafi sai ya rumtse ido and Ahmad na kusa da ni yana min sannu. Bayan likitan ya gama ya saka min bandeji sannan ya rubuta mana magani.
“Zaki iya jirana a mota”
Ya fada yana mikomin key din motar, ba musu na karba na juya na fito daga office din, ina tafe ina tunanin haukar Aminu har na isa gurin motar, amaimakon na bude na shiga ciki na zauna sai kawai na zabi tsayawa har ya fito, ya dauki lokaci a ciki kamin ya fito ya nufo inda nake tsaye jikin motar, hannu ya miko min na bashi key din ya bude ya shiga sannan nima na shiga.
“Kika yi ta tsayuwa waje? Ko baki iya budewa ba ne”
“Na iya”
Kallona yai kamar zai yi magana sai kuma ya dauke kai yai ma motar key muka kama hanya, ba kai ni gida ba sai da ya biya ta wani shopping yai min siyaya sannan ya shiga da ni cikin unguwarmu.
“Ban san ko kina son na kai ki har kofar gida ba ko kuma na aje ki a nan”
“Nan din ma yayi na gode sosai, dan Allah kai hakuri da abunda Aminu yai maka....”
“No karki damu, ni be min komai ba”
Ya mika hannunsa baya ya dauko ledodin ya miko min.
“Ki rikawa yara wannan, and ina son na yi miki maganar karatunsu?”
Na masa kallon rashin fahimta.
“I mean idan kin amince i will take them back to Gwarzo International school”
“A a suna makaranta a yanzu, da na yi deciding na canja musu sai kuma na yanke shawarar kara na bari har su kai Secondary school sai na nema musu private”
“Baki son makarantarmu ne? Then i will pay su shiga wata private school din”
“Ba haka ba ne...”
“Ba haka bane minene?”
A yadda na lura Ahmad yana daya daga cikin irin mazan nan masu saurin fushi, kuma abun kankane kan iya bata masa rai, domin tun kamin na karasa ya tari numfashina cikin muryar dake nuna fusatarsa a fili, jin na yi shiru ina kallonsa sai yai sauke ajiyar zuciya ya fara magana slowly.
“Kin dai ga mahaifinki ba wani kula zai yi da su ba, ke kuma a yanzu kina neman mai taimaka kiki ne, to miye a ciki dan na dauki nauyin karatunsu? Uba kamar wannan? Zai tsaya ya damu da rayuwarsu ne ma balle karatu? Idan mutum ne mai hankali da natsuwa zai same mu a titi ne yana ihu and called you his wife? Imagine?, i said idan makarantar ne baki gamsu da ita ba zan iya biya su yi wata makarantar, idan kuma taimako na ne bakya so then get out of my car”
Ya karasa fuskarsa babu alamun wasa, ni kan kallonsa kawai nake mamaki cika ni, to ana taimako dole ne? Idan ya maida su a makarantar wani abu ya faru sai kuma a sake ciresu? Bana son yawo da karatunsu a yanzu domin shine rayuwarsu. Bude motar nai nai fita.
“Okay fita kika yi? Fine...”
Jin ya fadi hakan yasa na dawo cikin motar na zauna cikin damuwa.
“Nace ki fitar min daga mota”
Yawun bakina na hade na na kalleshi a natse nace.
“Ba wai bana son karatun nasu ta dalilinka ba ne, bana abunda ya faru da su a baya ya sake faruwa yanzu, ko a da na dawo gida a lokacin da aurena ya mutu Abdallah ne yake kula da su ya saka su a makarantarku, daga baya kuma sai ya cire su wanda hakan be min dadi ba, a dole tasa na dawo da su makarantar gwannati”
“Sai kuma aka fada miki kowa kamar Abdallah ne idan na saka sun cire su zan yi”
“Shi ma ba da son ransa ya cire su ba, mahaifiyarsa ce ta cilasta shi saboda bata son alakar da ke tsakaninmu, bana son hakan ya sake faruwa”
“Babu abunda zai sake faruwa, Hajiya bata da matsala da ke, kusan ita ta fara min magana tun kamin na yi tunanin yin haka, so if you want zan aiko direba gobe ya dauke su, idan kin yi shawara pls let me know”
Ya karasa yana miko min katinsa. Na kalli kattin kamin na kalleshi na ce.
“Na amince”
Murmushin yai har lokacin be janye katin daga miko min da yake ba, wata kila son yake na kira so that ya samu Number na, domin tun da nake a rayuwata be tana kirana ba bamu tana waya ba.
Ganin na ki karba yasa ya maida katin ya aje, ni kuma na rufe masa motarsa, na kama hanyar gidanmu na barshi a gurin tsaye ni dai har na shige gida ban ga motar ta bar gurin ba.
Ina shiga gida hankalin kowa ya tashi ganin goshina da bandeji. A falon Inna na zauna ina labarta musu a abunda ya faru.
“Kai amman wannan mutunen ya burge ni, ai daman Aminu daidai ne ya samu mai cin ubansa....”
Hafiza da fada cikin jindadi, kamar daga sama muka ji Namra dake sanye da uniform ta fashe da kuka. Husna ta nuna da hannu tana fadin.
“Kin ga wacan kin ga wacan munafukace, ke yanzu duk abunda ubanki nai muku har son shi kike?”
Mama ta tari numfashinta tana fadin.
“Karki ga laifinta a duk yadda uba ya lalace ko uwa ta lalace ko da ya lalace akwai kauna a tsakani kuma baka son wani abu ya same shi, amman dai yakamata ki masa magana kar ya saka su masa mugun duka fa su ji masa ciwo ko su kashe shi ma”
Sai a lokacin wannan tunanin ya zo min, kar su masa dukan mutuwa laifi ya dawo kaina, daman kuma ga halin da nake ciki, ko kuma shi Ahmad din na ja masa matsala.
Haka na wuni da tunanin abun, sai a lokacin na ji haushin rashin karbar number sa da ban yi ba. Bayan an sallame sallah magariba Mama take min wata magana wacce ban taba kawo ma kaina ba.
“Halimatu, ya kamata ki daina shiga motar maza haka nan, ba mutuncin ki ba ne, yanzu ne sai ki ji mutanen unguwa sun fara magana, ni kaina ba zan so ace yau kina cikin motar wannan gobe kina wannan ba inda ba ta kama dole ba”
Gaskiya ta fada min wacce babu mai fada min ita sai mai kaunata, be kamata ina shiga ko wace irin mota ba, na sani yanxu ne sai a fara magana a unguwa ana cewa na lalace ko kuma ina jaye jayen maza barka, wasu ma kan iya dogara da cewar ganin mahaifina baya raye ne.
“In-Sha-Allah zan kiyaye Mama, amman yana da wahala na shiga motar wani idan ba da wani dalilin ba, amman duk da haka zan kara kiyayewa”
“Hakan yayi, Allah ya fito miki da mijinki na gari ki yi aure”
“Amin”
Na amsa tare da amsa sallamar yaron dake ta doko sallama tun daga kofar gida.
“Wai ance ana sallama da Halima”
“Je kace waye”
Yaron ya fita be dade ba ya dawo yace.
“Yace wai Abraham ne”
“Je kace gani nan zuwa
Bayan yaron ya wuce Mama ta kalleni tace.
“Abraham kuma? Wane irin sunana ne wannan?”
“Mama bari na dawo dai”
Na tashi already ina sanye da Hijab dina na nufi kofar waje, a inda ya saba tsayuwa ya tsaya, ni kuma na karasa gurin ina tunanin da me kuma zo wannan karon.
“Gani”
Na fada ina kallonsa. Sai ya fito daga cikin motar da yake zaune ya kalleni.
“Na taba fada miki ina son ki”
“Ka sha fada min”
Sai yai murmushi mai sauti.
“Ina son ki
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 55