Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rai ya daka masa tsawa. “And who are you? Mi kake takama da shi” Wani shegen kallo Ahmad yai ma Abdallah, mamaki ya kama shi wato a maimakon ya bada hakuri ya karbi laifin matarsa amman sai neman kareta yake, hakan ya kara tabbatar masa da cewar Halima bata da gata domin da tana fa shi da yau ba shi zai yi fadan nan ba wani wanda ya tsaya mata ne zai yi shi. “Kudi Alhaji......... ko baka gani ba, na isa ne isar ta isa ma matuka, kawai dan kun ga mace bata da gata sai ku yi ta taka ta any how, idan yar wani mai kudi ce ko kuma tana da wanda ya tsaya mata shashanshar matarka bata isa ta taka kofar gidansu ta fada mata bakar maganar magana ba balle har ta shigo gurin aikinta tana kiranta da suna kala kala tana cin mutuncin, so warn your wife for the last time, bilahil'azee idan ta one bad word daga bakin matarka zuwa ga Halima sai a rufeta a cell ba acikin kamfanin nan ba” Abdallah yayi murmushi yana duba agogon hannunsa, sannan ya kalleni ya sake kallonsa. “Ba kai ne mutumen da yace idan yarsa ta mutu zaka rufe Halima ba? Ba kai ne mutunen da baka yarda da kaddara ba? Ba kai ka mareta har sai da ta suma ba? Kai duk abunda kai mata ai saboda kana ganin bata da gata ne, yanzu har kana da bakin da zaka fadi haka? Mi ka sani a akan Halima? Baka san komai ba akan rayuwarta fadi tashin da tai ba ka sani ba, sai a yanzu? Tsohon dan iska shiyasa ka bata wando da riga ta saka so that ka rika kallon siraicinta? So kake ka burgeta a yanzu? Shiyasa zaka fara acting kamar wani mutumen arziki... ” Su suke fadan ni nake kuka, Ahmad be sake cewa komai ba, ya danna dan wani maballi da ke gefen teburinsa, ba a dauki lokaci ba sai ga security kamfanin sun shigo. “Ku fitar min da shi bana son hayaniya.... ” Da sauri suka nufi gurin da Abdallah yake saye sai kuma suka saka rika shi sai kokarin masa magana suke. “Karku taba shi zai fita da kanshi.... Abdallah dan Allah” Ya fada ina masa magiya, kallo yai ya dauke kai ya juya ya fice daga office din rai a bace, sai security din suka bishi a baya. Karasa matsawa nai kusa da teburin na hade hannayena ina kuka. “Ka saka a saki matarsa dan Allah, na san ka tsaneni, duk abunda zaka yi Saboda ka musguna min ne ko kuma wani na kusa da ni, idan har ya zama dole sai ka dauki mataki akan abun dan Allah ka hukunta ni ba matarsa, saboda ni komai ya faru...” Ba tare da ya kalleni ba ya nuna min wata kujera dake can kusa da kofa. “Je can ki zauna” Abun ka da mai jiran umarni sai na nufi kujerar na zauna ina kuka a hankali domin har ga Allah ban jidadin da ran Abdallah ya bace ba, kuma ban jidadin abunda Ahmad yai masa ba. “Idan kin gama kuka ga tissue box kusa da ke ki goge fuskarki, akwai ruwa a fridge” Yana fadar hakan ya dauki laptop din da yake aiki da ita ya fice ya bar ni a katon office din, ni ko ban fasa aikin kuka ba har sai da nai wanda ya ishe ni na dauki tissue na goge hancina da idona sannan na bude fridge din na dauko gorar ruwa na sha, domin makoshina ya gama bushewa. Bayan na sha ruwa na koma a inda na tashi na zauna. Kalamansa na dazun ne wuka rika dawo min a rai kamar yadda na Abdallah ma suka tsaya min, na rasa ganewa Ahmad ya fara saukowa daga fushin da yake da ni ne? Da har zai ce idan Suwaiba ta sake fada min bakar magana sai ya rufe? Ya bar ni na shigo har office dinsa ya fada min idan na gama kuka na goge fuskata na sha ruwa... Ina tsaka da tunanin sai gashi ya shigo tare da Yunus yana ta murza wani karamin turare a hannunsa, kallona kawai Yunus din yai be ce komai ba ya cigaba da maganar da yake da Ahmad bayan ya gama ya fice wata matar ta shigo da kofin tea guda biyu ta aje a saman teburinsa sannan ta fice. Daukar dayan kofin yai ya nufo inda nake zaune ya miko min, mamaki ne ya hana ni karbar cup din har sai da ya kalleni. Sai nai saurin girgiza masa kai na mike tsaye. “A a na gode” Kallo yai for few seconds sannan ya furta. “I'm sorry....” Ya juya yana kurba tea ya nufi teburinsa. “Be kamata ka bani hakuri ba, duk abunda ya faru laifina ne, ni na ja komai sanadina komai ya faru kuma kamfaninka ne kana damar ka yi duk irin hukuncin da kake so....” “Akan dora miki laifin kisan Baby Namra da na yi” Ta tari numfashina, wannan karon mutuwar tsaye nai, da gaske hakuri yake ba ni? Ahmad din ne ko wani dai dabam, na dan juya na kalli bayana na sake kallona. “Ki yi hakuri dan Allah” Ya maimaita min da yaren da na fi ji. Har lokacin kallonsa na ke gaba daya kaina ya gama kwancewa, mi ke faruwa ne? haka na tsura masa ido ina ta masa kallon da ban san na minene ba, mamaki kadai ko kuma har da tuannin maganar Abdallah? Da gaske hakuri yake bani ko kuma wani abun yake shirya min saboda na kashe masa ya? Kamar yadda yake zargina? “I say sorry” Na hade yawun bakina. “Ba komai ba, wannan ma yana cikin kaddarata ne” Ina fadar hakan na juya zan fice daga office din. “Ina za ki je?” “Gida” Na fada ba tare da na juyo ba, idona na cika da hawaye. “Aikin fa?” “Na aje” “Saboda me?” “Tufafin da nake sakawa be dace da ni ba” Na amsa cikin muryar kuka, har yanzu na kasa yadda Ahmad ya bani hakuri akan yarsa, har zuciyarsa yake bani hakurin? Miyasa? Taya yanzu ya yarda ba ni na kasheta ba? A take wasikar da na rubuta a jiya ta fado min a rai, ya fahimci ni ce kenan, kuma zuciyarsa ta bude har ya iya yarda a yanzu ban aikata ba, Al-hamdulillah akalla wani abun ya ragu daga bakincikin da yake raina, a yanzu yana kallona a matsayin marar laifi tun da har ya iya ba ni hakurin. Shigowar Yunus ne yasa nai saurin share hawayena sai dai hakan be hana shi fahimtar kuka nake ba. “Lafiya?” Ya tambaya yana kallo da mamaki a fuskarsa. Ban saurari abunda Ahmad ya fadawa Yunus din ba domin har lokacin kokarin tsayarda kukan farincikina nake. “Biyo ni muje” Yunus din ta fada ni kuma na juya ina rokon Ahmad amman ko kallona be yi ba. “Dan Allah ka saki matar can dan Allah” Ganin Yunus din ya fice yasa nima na bi bayansa, yana gaba ina bayansa har muka isa wani guri, hannunsa ya kai ya tura kofar sai ya bude ya shiga ni kuma na tsaya a waje har sai da ya yi min izinin shiga. Dan madaidaicin office ne mai dauke da desktops har biyu a teburi daya, sai dan karamin fridge da ac makale a dakin daga gefen ac window ne mai kofa biyu wanda yake bawa mutum damar hango windows din office din Ahmad kamar yadda shi ma zai iya hango na cikin office din idan an bude. “Kin iya typing ai ko?” Na gyada kai. “Yauwa to duk emails din da za a turowa kamfanin nan anan zai shigo wanda kika ga ya dace oga ya gani sai ki masa forward kai tsaye zuwa email dinsa, idan kuma za a aika wani abu to all ma'aikatan mu ke za a bawa ki yi typing sai ki tura, sai dai daga yanzu lokacin tashi aikinki ya canja daga 3 zuwa 5pm, amman ba kamar wacan ba ne nan ana bada abinci saboda zaman da kike” “Ban gane ba....” Na fada a hankali cikin sanyayyiyar murya. “Yanzu nan ne office dinki congratulations” “Da gaske?” “Ga zahiri kina gani” A take idanuwa suka kara cika da kwalla. “Na gode” “Oga ya kamata ki yiwa godiya” “Dan Allah ina rokon alfarma” “Na san kai ma oganka ne, amman kuna da kyakkyawar fahimta wata kila za ka iya yi masa magana ya ji, dan Allah ka saka ba ki ya saki matar da ya saka a ka kulle” “Ya sake ta ai, tun dazun mijinta ya tafi da ita” “Da gaske? Amman cewa yai ba zai barta ta tafi ba” “Gaskiya tun dazun aka wuce da ita” Dan murmushi nai na juya ina kallon office din. Shi kuma ya juya fice ya bar a gurin tsaye n rasa abunda zan yi murna ko kuka ko mamaki? Kasa komai nai a cikin office din sai kawai nai zaune ina ta kallon office din, misalin daya da mintuna wata ta shigo da abinci ta ba aje min, takeway ne na jalof da naman kaza a ciki. Nikam ban ci ba duk kuwa da kasancewar ni kadai ce a dakin sai na saka abina a jaka. Biyu na yi na shiga bandakin da ke office din nai alwala na fito nai sallah sannan na dauki wayata na kira gida na fadawa Hafiza ta fadawa Mama an canja min aiki dan haka yau sai 5pm zan dawo. Har karfe uku ban duba email din ba ban kuma tura komai ba, har sai da Yunus din ya sake dawowa ya nuna min yadda ake da kuma wandanda ya kamata a turawa Ahmad din. Karfe biyar na yi na dauki jakata na fito daga office din, ko da na fito Rilwal da Blessed basa gurin sun gama aikinsu sun tafi. A lokacin da na isa gida na labartawa Mama da dukan yan gidan abunda ya faru tsakanina da Ahmd da kuma abunda Suwaiba tai, a nan Hafiza take fadar wai Suwaiba ta kirata kwanan baya tana tambayar inda nake aiki ita kuma ta fada mata ba ta yi tunanin wani abun ba ashe dan ta samu zuwa ta ci min mutunci ne. Su namra na bawa abincin office din, suna ta murna sun ga har da nama a cikin gurin rabon abun har ya so zame musu fada sai da Husna ta shiga tsakani. Bayan na huta na ci abincin da aka girka gida, na watsa ruwa na sake shiryawa cikin wasu tufafin na nufi bankin da ke kusa da mu, kudin gasar da na ci nake son cirowa na samma kowa wani abu a ciki sannan nai sauran lalurorin da suke gabana. 200,000 na ciro na saka a jaka ta cikin tsoro domin a lokacin an fara kiran sallah sai nake ganin kamar akwai wasu a biye da ni duk kuwa da ba ni kadai na ciri kudi a atm din ba. Ina yin gaba kadan sai wata farar mota mai bakin gilashi ta faka a gabana, na san ba zai wuce Abraham ba amman hakan be saka ni jin tsoro ba har sai da ya bude motar ya fito. “Ki daina cirar kudi a atm idan yamma yayi, wani zai iya sa miki ido wasu ma ba diban kudin suka je yi ba kallon masu cire kudin suka je yi” Ban ce masa komai ba nai gaba kamar zan wuce sai ya saka ya cin min. “Kin gani jin labarin ki ya kara min kaunarki, kuma ya kara kafafa min guiwar aurenki, ni kadai zan rayu dake ba wata kyama ba wani tunani, ina da kudi zan sakar miki su ki jidadin rayuwarki” “Ba kudi ne jindadin rayuwa ba, da su ne da masu kudin ba su shiga kunci ba, ni farinciki nake nema da kwanciyar hankali” “Na sani shiyasa zan baki ai” “Baka isa ka bani farinciki ba, baka isa ka keta min haddi da aurena ba har nai ciki yanzu kuma ka biyo ni kace zaka aureni, addininmu dabam al'adarmu dabam, baka san zafin da nake ji a raina ba, baka san yadda mace take ji idan an keta haddinta ba, saboda kai namiji ne, mace tana jin matukar bakinciki ko hannunta a rike balle a keta haddinta, kasan saboda me? Saboda martabarta kimarta mutuncinta jindadinta farincikinta yana a nan ne, to kai ka zubar min da duka wannan ka saka uwar mijina da mijin da ya sake ni suna min kallon karuwa wacce ta zubar da mutuncinta tai fasikanci da wani namijin har ta samu ciki, wannan tabon ba zai taba gogewa ba, idan kuma ka zo ne saboda ka kashe ni da bakincikin kallonka da nake kana da dama” Na karasa cikin kuka. “Idan nisanta kaina da ke zai saka ki farinciki, i will do that, amman bana da niyar saka ki bakinciki, sai dai sama miki farinciki ada bakincikin fyaden da nai miki kawai yake damuna, amman a yanzu har da rayuwar kuncin da kike ciki, kina da zuciya mai kyau kuma kina da hakuri” Bayan ya fadi haka ya bude motarsa ya shiga yai mata key ya bar ni a gurin tsaye. Sai da na daina hango motarsa sannan tari napep na shiga. Ko da na isa gida har an gama magariba, bayan na sallame mai napep na lura da motar Abdallah, na yi zaton yana cikin gidan ne sai ji nai ya kirani, ina juyowa na hango shi ya fito hanyar masallacin unguwar sai ya nufi gurin motarsa ya tsaya, hakan yasa nima na karasa kusa da shi na tsaya. “Ki yi hakuri da abunda Suwaiba tai miki, ban san yadda akai taje gurin ba kuma ban fada mata cewar kina kawo min abinci ba, kin san zuciya kowa da irin tasa ba tai tunani ba a lokacin da ta aikata abunda ta aikata dazun kuma ban jidadi ba” “Tana da gaskiya Abdallah, tana tsoron wata ta karbe nata miji mai karamci da sanin ya kamata, mai kula, mai tausayi, mai taka tsantsan akan komai, kai kadai ka yarda da ni Abdallah baka taba yarda cewar na aikata laifi ba, kai kadai ka yarda cewar ban aikata zina, kai ne kadai ka yarda fyade ka min har na samu ciki, amman Hajiyarka da Abdulhamid ba su yarda da ni ba, kai na zarga a lokacin da aka min fyaden kuma na fada maka, amman gujeni ba baka kyamace ni ba, baka fasa so na ba, baka kasa taimaka min ba, so na be taba sa ka nemi aikata alfasha da ni ba, baka taba kyamar yayana ba, Wallahi ina son ka Abdallah ina son ka har kasan raina” Na karasa cikin kuka mai tsanani. Har ga Allah ban taba jin son wani da namijin a raina kamar yadda nake jin Abdallah a raina ba, sai bayan komai ya lalace na gano shine mutumen da ya dace da ni. “Ke dai ba kya gajiya da kuka, shiga ciki Suwaiba tana jiranki” “Ina son na fada maka wani abu, mutumen da yai min fyade, ya dawo yan so na” “Wooo What....!” Ya furta da karfi muryarsa na amayar da mamakin da ke cikinsa. “Waye? A ina ya ganki?” “Labari mai tsawo ba zai yiyu a yanzu ba” “Waye shi kin san shi ne?” Na girgiza kai. “Ban san shi ba, sunansa Abraham, dan sanda ne, yana aiki a unguwar gwaza, kuma shi ba musulmi ba ne” Na daga kaina sama ina shanye kuka. “Abraham.....” Ya maimaita sunan sannan ya jinjina kansa. “Shiga ciki za ku yi magana da Suwaiba” Na gyada kai alamar gamsuwa sannan na saka hannuna na share hawayena sannan na juya na nufi gidanmu. Ko da na shiga na samu Suwaiba zaune falon mama tana ta rutsar kuka kamar ba ita ba, tana ganina ta soma bani hakuri tana fadin na yafe mata, a iya sanina Abdallah baya duka balle nace dukanta yai ya cilasta mata zuwa ta ba ni hakuri sai dai idan wani abun ya fada mata ko kuma cilastata yai. 7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: I think you'd like this story: "GOBE NA (My Tomorrow)" by KhadeejaCandy on Wattpad https://www.wattpad.com/story/247701926?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZkyWKvWuHXhIRzZDEluZ%2BuUXayIbDBikXAQA%2BM4xeAsJY%2Fh9rtovTCoQphCdFYUPM4K1nHTquOLcFfifZUhwZ0RRyERddTi4AY1OYORg8gUhN9fNU%2FLr6t3SMGO9O8M2 *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 4️⃣5️⃣ ABDALLAH POV. Zuciyarsa cike take da tunanin abunda Halima ta fada masa, ba sau daya ba ya sha jin sunan Abraham a gurin Abdulhamid, sai dai da kamar wuya ya iya fada mta kai tsaye idan har shi din ne? Mi zai saka ya tonawa kansa asiri? Mi mai zai saka yayi mata fyaden tun farko? Miyasa yai shigar yan fashi? Sai dai ya yarda Halima ba zata masa karya ba, tun da ita din bata san Abraham ba, kuma bata san cewa shi din ba musulmi ne ba, idan har ba shi ya fada mata ba. Yana tsaye jikin motar Suwaiba ta fito daga cikin gidansu Halimatu ta nufo i da yake da hijabinta har kasa, be tsaya jiran ta karaso ba ya bude side dinsa ya zauna yai ma motar key tana shiga ya tashi motar. Ta yi zaton hanyar gida zai nufa sai ta ga ya dauki hanyar family house dinsu. “Doc baka hakura ba?” Ta tambaya cikin kuka, ko kallon inda take be yi ba har ya shiga titin unguwarsu. “Na ba ka hakuri kace ita zan bawa hakuri ita ma na bata, amman be isa ya saka ka yafe min dan abunda nai ba” Sai a lokacin ya kalleta. “Dan abunda kika yi? Da ne ma? Kin san irin kuncin da Halima take fuskata kike neman kara mata wani? Ko ba u so a tsakanina da ita ai ita din yar'uwata ce kuma kin sani, ko dan yan'uwantakan da ke tsakaninmu be isa ya saka ki raga mata ba ko da ma ace ita ce ta nemi fada da ke? Ko karuwata ce ai ya cancanci ki kyaleta saboda mutuncina, amman wai dan shashanci da aurena akanki ki shiga public place kamar nn kina magana any how, idan auren zan yi kin isa ki hana ni ne ko fadan ki sai ya saka na fasa?” Tun da ya fara fadan take kuka har ya faka bakin kofar gidansu. “Da gaske sakina din za ka yi?” “Ko dai ban sake ki ba, dole na samawa su Inteesar wata uwar mai tarbiya da sanin ya kamata” Da sauri ta hade hannayenta. “Dan Allah kai hakuri, ka sake ni idan sakin zai saka ka huce haushi daga baya sai ka maida ni amman karka kara aure dan Allah, wallahi na bari ba zan sake ba” “Yanzu kuma na gano har da hankali baki da shi, idan aure zan yi kin isa ki hana ne? Ba a aure na aureki? fitar min a mota” Ya fada a tsawace fuskarsa babu alamar wasa. “Dan Allah ka yi hakuri...” “Nace ki fita....” “To yaushe zaka dawo ka dauke ni?” “Ban sani ba” Yadda ya daka mata tsawa ne yasa ta saurin bude motar ta fita. Sam bata taba ganin Abdallah a cikin irin wannan yanayin ba, su kan samu sabani wani lokacin ko da shine da gaskiya sai tai fushi da shi a haka kuma zai bita ya bata hakuri su shirya, amman be tana yunkurin fada mata bakar magana ba, yau kam ta kai ya saka hannunsa ya mari fuskata hakan be masa ba sai da ya cilastata ta je ta bawa Halimatu hakuri abunda yafi kona mata rai kenan, bayan yai mata baraza da saki yanzu kuma ya cilasta mata zama gidansu har yana zancen kara aure. Lallai sai yanzu ta tabbatar ba kadan yake son Halimatu ba, saboda kawai ta taba yau duk yai mata wannan har yana fadar wai ta taba mutuncinsa, bata kara jin ta tsani Halimatu ba sai da yai reverse da motarsa ya barta bakin gate din tsaye tana kallonsa. Kai tsaye gidan Hajiyarsa ya nufa, har lokacin tunanin abunda Halima ta fada masa yake, yana ta neman dalilin da zai saka mutumen yi mata fyade, yana bukatar fadada bincike, kamar yadda yake bukatar jin komai daga bakinta. Sai da yai parking sannan fita daga motarsa ya nufa kofar falon Hajiya wacce ke bude, hango ana mopping yasa shi tsaya bakin kofar yana kallon Hajiyar wacce ta nufo inda yake rike da filo. Fitowa tai waje harabar kofar da aje fillon saman wani center carpet da aka shinfida mata gafen kofar ta zauna, tana tsastsagar hakora hakoranta biyu na makka suna bayyana. A gabanta yaje ya zauna, yana mika mata gaisuwa. “Lafiya Kalau, Husaini ya gida? Wani gurin ka fito ne hala?” “Eh Suwaiba na kai gidansu” “To wani abu suke a gidan ne?” “Kai ta nai ta kwana biyu dai” Hajiya ta tashi daga kishingiden da take tana kallonsa abunda bata taba ji ba. “Ban gane ta kwana biyu ba? Miya faru? Tsabani kuka samu ne” Be boye mata komai ba daga abunda ya faru har hakurin da ya saka ta bawa Halimatu, a maimakon Hajiya ta bata laifin sai ta koma ganin laifin Abdallah. “Wato sai yanzu na gano ba karamin so kake ma matar nan ba, nima dan ina mahaifiyarka ne na hana ka kuma ka hanu, miyasa za ka ga laifin Suwaiba? abunda Halima take ni kaina ina jin haushi balle kuma ita da take matarka” “Matata Hajiya na sani, amman ba zan lamunci matata ta ci mutuncin yan'uwana ba, ko akwai so ko babu Halima jinina ce, yadda mahaifinmu be yarda mu raina yan'uwansa ba haka ba zan yarda ni matata wacce na auro take karkashin kulawata ta raina min yan'uwa ba, ta tsaya a matsayinta na matata, Halima kuma tana nan a yar'uwata” “Uhm Allah dai ya kyauta idan baka mutu ba komai gani kake, ita ma dai ban da iskanci ya zata rika aika maka da abinci guri aiki neman suna? Bayan tasan kai kanen mijinta ne? Wallahi yarinyar nan bata da kunya sam na raina tarbiyarta” “Hajiya kin dai tsani Halima kuma bata miki komai ba, matsalarta daya ta auri Abdulhamid kuma Abdulhamid din nan danki ne, ina laifi ta taimaka masa ta aure a halin da yake ciki? Amman kin dauki tsana kin dora mata bata miki komai ba Hajiya, yanzu ai zaki ga ranar ta, zaki gane ta yi jihadin auren danki, ba aure zai yi ba? Yanzu ba budurwa zai auro ba? Duk wanda be san ba shi da lafiya ba yanzu zai sani, ke da shi yanzu za ku gane idan Halima tana da hakuri ko babu” Tun da ya fara maganar ta zuba mishi ido, ta rasa gane wani irin so yake ma Halima nan, da baya ganin laifinta kuma baya son a ga laifinta. “Ta dai rubuce ka ta shanye Huisani ina tunanin ko ni da nake mahaifiyarka ba ka so na kamar yadda kake son matar nan, bata samu kan dan'uwanta ba kai ta samu kanka shiyasa kullum ciki mata bauta kake ita da yayanta” Murmushi yai. “Hajiya miye laifin Halima dan ta auri Abdulhamid kuma bata aureni ba? Kuma ba cewa tai dole sai ta aureni ba” “A lokacin da ka ce min kana son ka aureta, wallahi na yi murna sosai, kuma na jidadi domin na fi kowa son hada zumunci da iyala Malam Usman saboda alakarsa da mahaifinku, kuma ita wannan Suwaibar ba kiba take ba zaka auro mai dan kubakuba Wallahi naji dadi tunda ita Halima jikinta luwailuwai yake, aa wai kawai sai na ji zance ya canja ban san yadda akai ta ja hankalin Hassana ba ko dan tana ganin kamar ya fika arziki oho, shi da ba ruwansa da zancen aure ma taja hankalinsa har ya zo da maganarta, kuma bayan tasan kana sonta, yanzu da auren ya dora da sai ka rika kallonta a gidan dan'uwanka kuma kana sonta? Wani abun haushi ma har da aurenta take neman maza waje ko shiyasa ta aureshi dan ta samu damar hakan Allah masani, yanxu kuma aure ya mutu kana nuna alamar sonta taya zamu shirya da dan'uwanka? Kuma jama'a ku ce musu me? A family ayi ta mana kallon tumakai” Kamar yace wani abu sai wata zuciyar ta hana, ya san dai duk yadda zai yi ma Hajiya bayani ba fahimta za tai ba, ba kuma zata daina ganin laifin Halima ba, shi kanshi be jidadin abunda tai ba a wacan lokacin sai dai ya dauki abunda ta aikata da rashin tunani da kuma kaddarar da ke binta. Agogon wayarsa ya kalla. “Hajiya zan wuce gida sai da safe” “Allah ba mu alheri, na manta ban fada maka ba, surukan Hassan sun kira sun roki alfarmar a daga

Chapter 36 of 55