Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haka be sake ce min komai ba sai ya ciro wayarsa ya shiga dannawa. Kallonsa nai yanayinsa da yadda yai min sai ya sa na ji babu dadi. “Kai hakuri na ja maka ba.....” Kamin na karasa ya tari numfashinta. “Ba ki ja min komai ba, ni na ja miki duk wannan abun daya same ki, ba ina fushi ne saboda abunda ya faru ba, kawai ina mamakin hali irin ba ku ne, taya za a ci zarafin mutum kuma ya hana a bi masa hakkinsa? Su ba su san da zumunci ba ne suka wulakanta ki? Har marinki fa aka ce yar sanda ta yi aka fito dake waje babu mayafi babu wulakancin da ba su muku ba, kin san abunda nake ji a zuciyata?” Kai na girgiza masa. “Babu wanda ya mare ni, kuma ba mu fito cikin gidan ba sai da mayafi, duk wanda ya fada maka tsabanin haka karya yake” “Kanwarki ta fada min kuma baza tai karya ba, kina boyewa ne kawai” Shiru nai ina tunani a cikin duka kanena babu wacce zata iya fadar haka sai Hafiza. “A ina ka ganta” “Na kira wayarki ta dauka, ita ta fada min komai” Na yi shiru domin bana son karyata kanwata a gabansa, ko ba komai gobe ba zai sake ganin girmanta ba, balle har ya yarda da ita. “Idan hankali ya gaushe hankaline yake dawo da shi, ita ita ta aikata kuskure mu be kamata mu aikata ba, ta aikata abunda ta aikata ne saboda tana tunanin ni ce silar batar danta” “Amman miyasa ke kadai zata zarga? Ya akai ta san da maganar ma? After na fada miki wa kika fadawa?” “Saboda bata so na, kuma ta fada tana tunanin na dauke Abdulhamid ne ko kuma na saka an dauke shi saboda zai yi aure, kuma saboda ya ki zama da ni, tana tunanin ni an saka Abraham ya dauke shi saboda na dauki fansa” “Amman ba ita kadai ba har wannan Abdallah.... ” “Abdallah ba zai taba min haka ba, i trust him, ba da sa bakinsa Hajiya tai min haka ba, ba zai taba bari ba, balle har shi yai min, kiyayyar da Hajiya take min a yanzu ta samo asali ne ta dalilin soyayyar da Abdallah yake min” “Miya hana ki aurenshi?” Ya aiko min da tambayar kai tsaye, kallonsa nai ina kokarin kawarda da hawayen da suke son zubo min. “ A wacan lokacin Abdallah ya nuna min soyayya ne ta hanyar da be dace ba, shi yake yawan kawo min labarin abunda Aminu yake, yana son na kashe aure na na aure, wanda a musulunce haramun ne, domin Annabi yace baya tare da wanda ya so matar wani, ko ya zuga matar wani dan ta kashe aure ta ko da kuwa shi din zai aureta, a lokacin da aurena ya mutu, sai Abdulhamid ya fito so na bayan kuma Abdallah yana so na, amman shi Abdulhamid be san Abdallah yana so na ba, Abdallah kuma be taba sanin cewa na yi soyayya da Abdulhamid a lokacin da ina budurwa ba. A lokacin ina jin tsoron abunda ya kashe min aure kar na sake fada mishi, da kuma ganin da nai Abdallah yana so na tun ina a gidan wani sai nake ganin kamar idan na aure shi, aure ba zai dade ba hakan yasa na take aurensa na auri dan'uwansa, daga lokacin sai mahaifiyarsa ta fara kina, ashe Abdallah ya fada mata yana so na, sai take ganin kamar ni na ja hankali Abdulhamid ne na aureshi saboda na batawa Abdallah, saboda babu wanda ya san mun yi soyayya da Abdulhamid saboda a boye mu kai a wacan lokacin ya hana na bayyana soyayyar, wanda ban san dalilin hakan ba wata kila saboda ba shi da lafiya ne yana tsoron soyyayyar mu ta bayyana sirrinsa, a jiya ina jin tana fadar cewar na lalata zumuncin da yake tsakanin Abdallah da Abdulhamid, ban san iya abunda ya shiga tsakaninsu ba, kuma na san saboda ni ne, komai bana yinsa daidai, yanzu ma idan aka kai Hajiya kotu saboda ni Abdallah ba zai jidadi ba” Dan murmushi yai ya tabe baki “Kamar dai Abdallah nan yana da muhimmanci a gurinki” “Yes, ya taimake ni a lokacin da nake bukatar taimakon, ya rike yayana kamar nasa a lokacin da ubansu ya guje su, kuma mijin dana aura wato Abdulhamid ya nuna min baya bukatarsu, duk son da Abdulllah yake min be tana neman yin lalata da ni ko sau daya ba, mi zai saka ba zai zama mai muhimmanci a gurina na” “Duk da haka dai abunda mahaifiyarsa tai miki ba ki cancanci yayanta ba, kuma ya nuna karara bata kaunarki, domin abunda tai miki makiyi ne kadai zai iya yinsa, zai iya zama silar ajalinki da baki farka ba a yanzu yaya kenan? And tell me taya za ki auri yaya uwa daya uba daya twins ya sake ki, yanzu kuma ki yi tunanin auren kane? A addinance ba haramun ba ne, amman a al'adance haramun ne, so pls ki manta da zancen auren Abdallah for now” Da kanshi ya tashi yaje ya hada min tea ya miko min, har na karba zan kai baki sai yai saurin dakatar da ni. “Tsaya tsaya muji” Ya karba ya kurba kadan. “Yana da zafi ba ri ya sha iska” Ya fada yana kura min ido. “Ji nake kamar ace da aurena abunda nan ya faru, zan kyale Hajiyar for now, amman shi dan sanda da yar sandar da ta mareki sai na hukunta su” Kallonsa nai na dauke kaina. “Akwai damuwa karara a fuskarki” “Idan na ce babu damuwa a tare da ni a yanzu na yi karya” “Don't be afraid i will by your side, you will be safe” Kallonsa nai sai ya sakar min murmushi. “I will surprise you idan kika ji sauki kika koma aiki, a gaban kowa da kowa and i hope you won't disappoint me” Ya fada sound so serious. ABDALLAH POV. A yanzu Abdallah yana jin ba shi da babban makiyi kamar Ahmad, daman can Allah be hada jininsu ba balle kuma yanzu da ya zama sanadin tashin ciwon Hajiya sakamakom fada mata da yai Abdulhamid yana gurin Dss, ya san duk wanda dss ta kama yana aikata wani mugun abun ne, be tana zargin dam'uwansa da aikata wani mugun abu ba, a yanzu ma ba zai iya zarginsa ba domin ba a fadi abunda yai ba, be zama lallai dan yana abota da Abraham ace aikinsu daya ba, sai dai kalamar da Ahmad ya fada cewar shi ne sanadin zuwansa dss din ya fi komai tsaya masa a rai. Lokaci zuwa lokaci yake sauke ajiyar zuciya yana kallon mahaifiyarsa wacce ke kwance an daura mata mata drip a hannu sai sharar bachi take. Mikewa tai tsaye yana kallon dakin kamar wani bakonsa sai ka ce ba dakin Hajiya ba. Sam be jidadin abunda Hajiya tai ma Halima ba da ya san haka za tai da be fada mata komai ba, a dayan bangaren kuma yana tunanin ko a wane hali yanzu Halima take ciki? Har ya dauko wayarsa kamar ya kirata sai kuma wata zuciyar ta hana shi, ajiyar zuciya ya sauke a hankali zuciyarsa na sosuwa da kalaman da Ahmad yai masa, yana mamakin wai a yau har wani zai nuna masa isa da Halimatu,shi ko zai nuna masa cewar be isa ga Halimatu ba, dan murmushin takaici yai. “Mahaukaci, marar tunani, mayaudari” Ya furta murya kasa kasa, yana jin a ransa ko da shi ba zai auri Halimatu ba tun da Hajiya tai musu shamaki to ko Halimatu bata dace da auren banza mutum kamar Ahmad ba, mutumen daya gama wulakanta ta yai mata kazafin kisa, yanzu kuma ya dawo yace son ta yake dan bashi da kunya. He know shi kadai zai aureta ga rike tsakani da Allah babu wata kyama, babu tunanin komai a ransa, ba dan Hajiya ta shiga tsakaninsu ba wata kila da yanzu ya aureta ta haifa masa da namijin da yake ta mamari, yake ganin kuma zai iya samu idan ya aureta domin ita ta haifi both maza da mata ba kamar matarsa Suwaiba ba da ke haihuwar mata. *** *** *** Wasa wasa aka kwashe sati daya kullum sai an sakawa Hajiya drip duk da bi ta rame kamar ba ita ba. A ranar hankalin Abdallah ya tashi sosai ganin halin da mahafiyarsu take ciki, kusa kullum a gidan yake wuni domin shi yake kuka da ita, a yau ma sai da ya tabbatar bachin Hajiyarsa yayi nisa sannan ya kama hanyar gidansa da tunani kala kala. Yana isa harabar gidan su Inteesar suka zo da gudu suka tare shi kamar yadda suka saba, sai ya fito daga motar yana murmushin karfin hali ya rika hannunsu suka nufi cikin falon. Ko da ya shiga Suwaiba na zauna a falon, ta kashe dauri sai kamshin turare take. “Sannu da zuwa” “Yauwa” Ya amsa mata cikin yanayin da ke nuna damuwarsa karara. “Ya jikin Hajiya?” “Al-hamdulillah” Ya kalli Plasma da take kallo kamin ya sake kallonta yace. “I think ya kamata ki koma can gaba daya, saboda kula da Hajiya” Ta dan wara ido. “Ah Doctor Idan na koma can to yara fa?” “Za ku koma can har su in yaso driver ya rika kaisu school daga can, idan ta samu sauki sosai sai ki dawo” Juyar da Fuska tai gefe ta bata rai alamar ita akam fa baza tai ba. *** *** *** Duk wani shiga da fita babu irin wanda Abdallah ko yan'uwansa ba su yi ba amman shiru labarin Abdulhamid har suka fara zargin ko dai an kashe shi ne. A week later in the evening aka dawo da su Gusau bayan hukumar ta bada umarnin rufe duk wani guri da Abdulhamid da aikinsa Abraham suke saida motoci, sakamakon kamasu dan akai da safarar makamai, ga kuma fashi da makaminda Abraham ke yi ta karkashin kasa bayan aikin police din da yake, da bakinsa ya fadi mutane da suka yi wa ciki har da makocin su Abdulhamid wanda babban dan siyasa ne, suka kashe a lokacin da suka je unguwar a ranar da ya so ya kashe Abdulhamid, ba a dawo da su gida ba sai da suka fadi komai ciki har da yadda suke shigo da makaman da kuma wandanda suke kaiwa da inda suke karbowa. ______________________ It's 4200k words today 🙌😊 7/21/21, 10:48 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 5️⃣5️⃣ Idan na ce zan iya fadar kulawar da na samu a gurin Ahmad da mahaifiyarsa na yi karya, domin a kwanan da nai asibiti kullum sai na yi bachi yake tafiya gida, mahaifinyarsa kuma sai tavaiko mana da abinci safe, rana da na dare, sau uku tana zuwa duba ni asibiti, a duk lokacin da ta zo tana yi min kalaman da suke kara min kimarta a idona kuma su kara kwantar min da hankali. Tana yawan fada min cewar nai hakuri, kuma na cigaba da yarda da kaddara kamar yadda nake, kar nai tsammanin Allah ba zai sake jarabata ba, kuma kar na tsammaci sake samun wata kadarar a gaba, na kyautata zaton kuma nai ta addu'ar, haka zata zauna tai ta fira da Mama ko Inna kamar ba matar babban mutum ba ko kuma na ce uwar babban mutum, da aka salleme mu a asibitin ma sai da ta kira ta ji muryata. Yau kam na kara yarda da maganar mutane da suke cewa duk abunda ya baka tsoro wata rana zai baka tausayi, duk kuma abunda ya baka tausayi wata rana zai baka mamaki. Idan nai na hada kalubalen rayuwar da na fuskanta da na Aminu da Abdulhamid, sai na gane cewar ni din ban ga komai ba, domin a halin yanzu Allah ya min mafita kuma ya wanke ni, wani kalubalen a farkon rayuwa yake wani a karshe, wani a tsakiyar rayuwarsa, ba duka arziki ne na halal ba, na kuma ko wane arziki ne na haram ba, ba duka talauci ne kunci ba, ba kuma duka kunci ne takauci ba, saboda ina cikin takauci ba shi yake nufin ba zan jidadi rayuwa ba, idan kuma ina da arziki baya nufin aki jarabbatata.   Ta wani bangaren na kanyi mamakin abunda ya kai Abdulhamid aikata wannan mummunan abu, ko da yake ko wane bawa be isa ya wuce kaddararsa ba. Kamar yadda ban wuce komai ba sai da ya same ni. Ba ni kadai nake cika da mamaki ba har da Mama da Inna, da duk wani wanda ya san waye Abdulhamid, mutumen da magana ma bata sha masa kai ba, dole kowa yayi mamakin wannan abun, wata kila Abraham ne yaja zuwa ga mummunar rayuwa, wata kila kuma shi yaja Abraham din, gaskiyar abun yana a tsakaninsu sai kuma bincike idan ya tabbatar. Dago kaina nai daga kallon wayar Hafiza da nake wacce ke dauke da hotunan su Abdulhamid, da Abraham da wani wanda ban wayance shi ba, an saka musu handcuffs, police na tsaye a bayansu an jarida kuma nata aikinsu. Na mika mata wayar ina fadin. “Abdulhamid ya ban tausayi” “Tausayi? Tausayi fa kika ce Halima? Haba mutumen daya sakeki har wani tausayinsa zaki ji, ke dai Wallahi kina da matsala” Na yi shiru domin na san ba zata taba fahimta ba, sai dai abunda ya fi tsaya min a rai shine shin Abdulhamid ya san cewar Abraham ne yai min fyade? Da saninsa akai? I need to know, na fada ina sauke ajiyar zuciya a hankali. Na unkura zan tashi kenan sai ga su Namra sun shigo da gudu kowanensu rike da leda a ko wane hannu, ledan kuma ba karama ba irin babbar ledar nan ta super market. “Momy Guess what...?” Aiman ya fada yana wani irin murmushin jindadi. “What it's?” Na tambaya da mamaki a fuskarta. “Wannan Boss din naki, baban su Baby Namra ne ya dauke mu daga school ya je da mu wani katon shago yace mu dauka duk abunda muke so” Wannan karon Adnan ne yake magana, sai Namra ya kyalkyale da dariya. “He say we should called him Daddy, wai yana jiranki a waje yana can cikin mota” Kana kallonsu kasan suna cikin farinciki, jin cewar yana waje yasa na dauki Hijabina na saka na leka kofar gidan, sai ko na ganshi daf fa kofar ya faka motarsa. Ganina yasa ya sauke gilashin motar yana miko min murmushi. “Lims how far” Dan murmushi nai nima “Mun gode Allah ya saka da alheri, kana ta dawainiya da yara” “Bude back seat din nan akwai na ki” Ya fada yana dauke fuskarsa kamar baya son nai masa godiyar. Na yi kamar yadda ya umarta na bude gidan baya na dauko katuwar leda na fito da ita. “Na siyo miki turare duk da ban san choice dinki, amman ni nafi son irin wannan wanda na siyo miki, na mata ina son na ji mace ta saka shi” “Na gode Allah ya saka da alheri” “Ki dai shirya komawa aiki on Monday, tun da lafiya ta samu sosai” Na gyada masa kai sannan na ce. “In-Sha-Allah, amman dan Allah ina neman wata alfarma” Kashe motar yai gaba daya, ya fito daga ciki ya zagayo inda nake ya saka hannayensa duka biyu aljihu yana min wani irin kallo wanda da ace akwai wani kusa da ni da sai na ji kunya, domin idonsa ya sako min sosai kamar zai cinye ni. “Name it” Ya fada kamar mai rada. Kasa nai da kaina ina wasa da ledar da ke hannuna. “Lims..... ” Ya kira sunana cikin wata irin siga wacce ta saka sigar jikina tashi, da na kalleshi kuma sai na kasa jure irin kallon da yake min. “Okay Babe mu shiga mota sai ki fada min idan ba zaki iya fadi in public ba....” Idan ban yi kuskuren fahimta ba kamar yace Babe right? Mistake yai ko kuma da gangan ne? “You know bani da wannan hurumin da zan rumgume ki na kallashe ki na tambaye ki abunda kike so, so please just tell me idan ba so kike ki wahalar da zuciyata ba” The way da yai maganar kamar yana rokona ta shigar lallashi akan na fada masa abunda ni nake da bukata. “Daman ina son na tambaya ne ko ana barin mutum ya ga Abdulhamid” Na fada cikin tsoro da fargaba, runtse ido yai ya bude ya sake kallona. “Abdulhamid....” Ya maimaita sunan. “Why?” “Akwai tambayar da nake son masa, ina son naji amsar daga bakinsa ne kawai” “It's necessary?” Na yi kasa da kaina, sai yai saurin matsawo kusa da ni. “Okay Okay Okay... Kin san irin criminals din nan ba kowa ake barin yana shiga ganinsu ba, saboda gudun abunda zai faru, tun da suna tare da miyagun mutane ne, but idan kina son ganinshi i can talk to my friend sai yai mana hanya ki ganshi, idan ya bada date zan fada miki sai ki shirya na kai ki” “Thank you so much” “No Lims dadi nake ji idan kika bukaci wani abu nai miki, so thank you so much for the offer” Ya fada sound so serious, sannan ya zagaya zuwa side dinsa yana kallona tare da fadin. “But make sure ba wani kalma mai dadi za ki fada masa ba, ba zan jidadi ba idan kika furta wata kalma mai dadi ga wanin Ahmad, saboda Ahmad yana da kishi sosai idan yana da da dama ma, ko a unguwarku ba kowa za ki yi wa magana ba i swear” Ya bude motar yana min murmushi. “Take care of yourself” Sannan ya shige motarsa yai mata key ya bar ni tsaye a gurin ina mamakin kalamansa. Yace Baby at first, and second to the last sentence ya fadi wasu abubuwa da ban gane ma kansa ba, i thought ba soyayya muke ba, but why yake irin wannan behaviors din? Na san ko bw fada min ba abunda yake min da kuma kulawarsa akaina tana nuna damuwarsa ne, kuma akan damune ne da abunda ake so, ko kuma ya zama muhimmin a rayuwa. Sai dai ni din a yanzu ban shirya ba ban kuma san ranar da zan shirya din ba.   Ko da na koma cikin gidan an tarar sun bude abubuwan da ya siyo musu suna ci, sai labarin abubuwan da suka gani suke badawa, ni kuma an zauna saman tabarma na bude ledar, kananan cakes a ciki sai wata kyakyawar sarka mai ruwan zaiba, turare ya fi yawa sai man shafi cream and lotion, da shower gel, kana ganinsu kasan masu tsada ne.   Ina jin yadda kannen suke kamgama shi ni dai bance komai ba, har suka ci suka shude sannan na dauki kayan bayan na basu cake din na nufi daki na aje. Kamar wasa da dare Ahmad ya kira ni a waya ya fada min crwarna shirya gobe misalin ten zai zo ya dauke ni ya kai ni can abokinsa yace zai bar ni na shiga nai magana da shi, a lokacin kuma dai na ji kamar bana son zuwan wata zuciyar tai ta raya min cewar miyasa na bukaci haka? Ban kwanta ba sai da na fadawa Mama abunda nake da kudiri akai. “Amman dole ne sai kin yi magana da shi? A iya tunani na Halima, ya kamata ki nisanta kanki da yayan Hajiya, ba nuna nufin ki yanke alaka ba, a a ki yi nesa nesa daga duk wani abu da zai iya sakawa a zarge ki, iyakar cin mutuncin da nuna kiyaya Hajiya ta yi miki shi” “Na sani Mama kawai ina son na masa wata tambaya ce, wacce nake son amsar ta daga bakinsa” “To Allah ya tsare, tare za ku tafi da Ahmad din?” “Eh In-Sha-Allah” “To yayi kyau” Shiru ne ya biyo baya kamin ta kalleni tace. “Ba zan matsa miki ki yi aure ba, kamar yadda ba zan hana ki sauraren kowa ba, sai dai duk wanda kika san ba aurenshi za ki yi ba, to ki sallame shi da wuri ba sai yayi ta wahala a kanki ba” Ko bata fito fili ta fada min ba, na san Mama tana magana ne akan Ahmad kuma tana da gaskiya, ya kamata na dakatar da shi daga abubuwan da yake min ko ya fara min, kar abun yai nisa ya zame min wata sabuwar matsala.   Kamar yadda ya fada min zai zo da ten ya dauke ni, sai nai gaggawar yin duk wani abu da nake kamin lokacin na sallami yarana suka tafi Islamiyarsu kasacewar yau Sunday suna zuwa makarantar safe ne, sannan ni kuma na shiga nai wanka na shirya cikin bakar abaya, na yafa farin veils karama wanda ya tsaya min iya wuya, ban shafa komai a fuskata ba bayan powder sai dan man baki dana goga, na feshe jikina da turaren da Ahmad ya akwa min jiya, turare ne mai dadin kamshi ina jinsa a gurin manya mata idan na shiga buki ko office. Sako ya turo a waya cewar yana waje yana jirana. “Hey Beb ina jiranki a waje idan kin shirya” Bayan na karanta sakon na samu kaina da faduwar gaba, ina ta jin tsoro zuwa bayan kuma ni na bukaci haka, sai da na sanarwa Mama sannan na fita ina addu'ar fita daga gida. Ina fito daga cikin gidan ya sauke gilashin motarsa yana kallona har na karaso, da kansa ya fito ya bude min motar ni kuma ban shiga ba sai da na fakaici idon mutane, bayan na zauna ya maida motar ya rufe sannan ya zagayo side dinsa ya rufe gilashin motar yana kallon. “Kin san Allah? Da kika fito daga gida na hango ki ji nai kamar naje na rumgume ki? And the way you're walking wow Ma-sha-Allah” Na yi murmushi ina kallon yadda black suit din da ke jikinsa yai masa kyau sai mu ka yi anko kamar na fada masa nima bakin kaya zan saka. Ya bata minti goma a gurin baya aikin komai sai kallona can kuma ya shaki kamshin turaren da ke jikina ya lumshe ido, kamin yai ma motar key mu kama hanya. Kamar wacce tai masa maganin kallo haka ya saka min ido yana ta kallona yana murmushi kamar ba driving yake ba, har tsoro na rika ji kar ya mu yi accident. Mun yi tafiya mai nisa sosai sannan muka isa gurin daga ba a bar mun shiga cikin ba sai da abokin nasa ya fito, the way da abokin ya rika min magana sai na fahimci cewar Ahmad ya fada masa cewar ni matarsa ce wata kila, domin a cikin kalamansa har da zancen wai mijina yana so na sosai duk yabi ya dame shi shi dai matarsa matarsa. Kallona kawai Ahmad din yai ya kashe min ido yana murmushi, can kuma muna sake hada idon sai ya sake kanne min ido daya ya leko da halshensa kadan yai min gwalo still yana murmushi. “Gaskiya Ma-sha-Allah ka yi dace mata, Allah....” “Na sani, zamu iya shiga ciki?” Tun kamin mutunen ya karasa Ahmad ya katse shi yana hade rai kamar ba shi ba. Dariya mutumen yai ya juya muka nufi cikin gurin, nesa da ni Ahmad ya tsaya dan bani damar yin sirri, ni kuma na karasa ciki na zauna a gurin da aka tanada, ta ko'ina akwai security amman hakan be hana ni jin tsoro ba, gabana sai faduwa yake, duk bayan minti daya sai ya juya na kalli Ahmad sai ya dago min hannu ya aiko min da sakon murmushi. After like 14 minutes aka fito da Abdulhamid daga shi sai vest da gajeren wando, gaba daya ya canja, daman can ba jikin ne da shi sosai ba sai ya kara ramewa fuskarsa tai kamar wanda ya shekara be ci abinci ba. Har ya zauna a kujerar dake facing dina be kalleni ba.   Yana ta murza wuyan hannunsa, tsakanin ni da shi sai aka rasa wanda zai fara yi ma wani magana, sai da na sake juyawa na kalli Ahmad ya dago min hannu yai min murmushi sannan na ji karfin guiwa fara ambatar sunansa. “Abdulhamid....” “Miyasa kika zo nan?” Na tari numfashina ba tare da ya kalleni ba. “Kin jidadin abunda ya same ni ko?” A lokacin ne idona ya soma cika da hawaye. “Mi zai saka na jidadi? Ko da ban san ka ba, ballantana kai din dan'uwana ne jinina” Sai a lokacin ya dago ya kalleni. “Ina son nai maka wata tambaya wacce nake son jin amsarta daga bakinka” Na hade yawun bakina sannan na ce. “Miya hadinka da Abraham?” “Abokina ne more than 11 years,

Chapter 45 of 55