nai ta yi ko Allah zai saka a dace.!
Bayan na gama sallah isha'i ina rike da wayata ina latse latsena kamshin turaren Abdallah yai min sallama kamin muryarsa ta daki dodon kunnena, a take na nemi natsuwata na rasa sai na ji duk na kwadaitu da son ganinsa fuskarsa a take na aje wayar na unkura ina gyara Hijab dina na mike tsaye ina juyowa sai nai arba da mutum, faduwar gaba ta same ni a lokacin wacce take yayin yin haka a duk lokacin da nai arba da Abdallah, abun ka da wacce ta rude sai na kasa komawa na zauna daman dakin babu kowa sai ni kadai da aljanuna idan ma ina da su, ratsawa nai gefensa na da zimmar na fita domin a bakin kofar yake tsaye ya zuba min idonsa kamar ya cinye ni, ban san yadda akai ba na kasa lura da kyau har na buga kaina da garun kofar a take goshina ya fara zogi ni kuma na saka hannu ina murzawa jikina na ta rawa kamar marar gaskiya, har lokacin be dauke idonsa daga kaina ba kuma be kauce daga kofar ba. A dole na koma na zauna saman kujerar da ke kusa da inda nai sallah, amman me sai na gagara samun natsuwa domin jikina na bani cewar idonsa na kaina. Sai da ya ji muryar Inna ta doso dakin tana masa lale marhabun sannan ya karaso cikin dakin ya zauna a saman carpet din da na tashi wanda nai sallah, idonsa ya koma gurin kafafauwa ya sakar musu ido kamar mai son tantance abu, ni kau na daga abuna sama na dora saman kujera na lullube su da hijab, sai kallon ya koma gurin hannayena, su ma na nade abu cikin hijab din sannan ya kalli Inna wacce ta shigo ta zauna.
“Abdallah yaushe rabonka da gidan nan”
“Bana samun zama ne sosai yanzu shiyasa aikin yana min yawa, ya gida ya kwana biyu?”
“Lafiya kalau ya gurin su Hajiya?”
“Tana lafiya tana gaishe ku”
“Muna amsawa mun kwana biyu ba muje ba itama bata zo ba, ina Suwaiba da su Inteesar?”
“Duka suna lafiya, na ga Baba a waje ai mun gaisa ina Mama?”
“Ta dan zagaya makota jikin ne idan yai mata nauyi sai ta zagaya saboda asibiti ma ance ta rika dan takawa tana shiga mutane”
“Allah sarki gidan yau ku ne akwai a ciki? Duk ina yan matan Baba?”
“Wallahi duk sun tafi wankin Amaryar da ake nan makota, kawarsu ce take aure kuma ta zama kamar yar gidan nan har yaran duk suna can shiyasa ka ga gidan babu kowa”
“Okay”
Ya amsa yana maida dubansa gurin wayata wacce ke kusa da shi, kamar na kai hannu na dauka sai ganin nai ya dauki wayar yana ta shafa screen din domin tana da password ba zai iya bude ta ba, ganin shiru yayi yawa yasa Inna ta tashi ta bar mana dakin daga ni sai shi sai fankar sama da ke ta aiki ba mu iska kasancewar akwai nepa.
“Zan nemawa su Namra transfer zuwa government schools”
Ya fada ba tare da ya kalleni ba, kamar yasan zan tambayi dalili sai ya ce.
“Saboda na san ba za ki iya cigaba da biya musu school fees a wannan private school ba”
Har ga Allah na ji babu dadi amman ban nuna masa ba, domin ban san dalilinsa na yin hakan ba, wata kila ya gaji da taimakon da yake ba ni ne a yanzu ganin kamar ba zan taba aurensa ba.
“Allah yasa hakan shi ya fi alheri”
Na fada da muryata da ke nuna lamarin be min dadi ba. Sai ya kalle ni kamar yana mamakin jin haka daga bakina.
“Ba zaki tambayi miyasa nai haka ba? Ba ki damu ki san dalili ba?”
“A lokaci da ka shige musu gaba har suka samu karatu a wannan makarantar ban tambayi dalili ba saia yanzu da zaka canja musu? Ka yi min alheri da yawa Abdallah wanda ni na san har na mutu ba zan taba iya biyanka shi ba.... Ba zan zarge ka da komai ba”
Mikewa yai tsaye ya jefo min wayata tare da jan tsaki.
“Ba ki hadu ba Halima....”
Yana fadar hakan ya fice, ban ce masa komai ba na fiddo hannuna dake cikin hijab na dauki wayata, ko da na kunna sai ganin screen din nai ya tsaga. Hakan da Abdallah yai be karamin komai ba sai kuzarin neman na kaina, kamin aikin ya samu ina son mai amfani da kudin hannuna na fara sa'a domin zaman banza ba nawa ba ne a yanzu.
Kwana uku da faruwar hakan ya kawo min takardar transfer dinsu har gida, a ranar Mama take tambayata dalilinsa na yin hakan nima na ce mata ban sani ba, sai da na labarta abunda ya faru asibiti.
“A duk yadda akai ba a iya yanke alakarki da Aminu saboda yaya sun shiga tsakaninku yaran har hudu ba ko daya ba”
“Za a iya yankewa mana Mama, Aminu ai be damu da yaran nan ba tun suna gidansa balle yanzu da ba sa tare da su”
“Ai yanzu ne yake sanin darajarsu Halimatu, ba ki lura da yadda Aminu ya canja ba? Ba ki lura da irin kulawar da yake bawa yaransa ba?”
Hafiza ta tsire baki.
“Ni fa ina ganin kamar so yake yace Halimatu ta koma masa...”
Ni ko nai karaf na ce.
“Allah ya kiyeye gatari da saran shuka, ni da Aminu a lahira idan na shiga aljanna wata kila na hango shi a bakin kofar wuta, dan yana da wahala idan Allaj ba kona shi ba akan zalincin da yai min”
“Halimatu kenan kina kara girma amman har yanzu hankali ya ki zuwa miki, kin kasa duban yaran dake gabanki ko dan su ai kya kyautata wasu kalaman akan mahaifinsu”
“Mama har yanzu ban gama warkewa daga tabun Aminu ba, saboda shi na samu kaina a duk wani hali da nake ciki a yanzu, mutumen da zai dube ni ya kira ni da mummuna yace ina ta haifa masa yara saboda na tsufar da shi, ya sake ni saboda na fada masa cewar dan'uwansa yana neman lalata yarsa? Sannan yai taraiya da kawata? Haba mama wace irin mutunci kike tunani zai shiga tsakani na da Aminu? Ni kadai na san irin kalubane da na fuskanta a gidansa”
Na karasa idananuwana na cika da kwalla, sannan na unkura na tashi na nufi inda jakata take na dauka daman da shirina na fito.
“Mama idan ko Hafiza idan su Namra sun dawo daga scul ki fada musu ba za su sake zuwa ba daga yau, saboda kar su saka rai, zan bawa Aisha kudin Napep ta je ta dauko su dan nasan kamin na dawo lokacin dawowarsu daga school yayi”
“To Allah ya bada sa'a ya tsare”
Cewar Mama. Hafiza kuma ta kalleni daga sama har kasa tace
“Allah yasa mai kamfanin yana kallonki yace ya samu mata”
Ni kuma nai dariya.
“Ai na girmi aure yanzu, ko nawa za a bani ba zan iya aure a yanzu ba, mun dai yi kuma gama da yarda Allah”
“Kara dai da kika ce da yardar Allah, aure ai shine martabar mace, kuma kin san ba ido zan saka miki kina zama a gida ba ko? Mutanen unguwa ma sai su yi ta yi da ke, musamman idan kika fara aikin nan wani ba tunanin alheri zai miki ba, yanzu sai ki ji an fara tsegumi, daman can ana lissafa mu na yan mata wai mun ki aurarda su.... ”
Mama ta tari numfashina tana ta kora bayani, ni dai kan uffan ban sake cewa ba, nai musu sallama na fice, har nai addu'a fita daga gida, ban daina mamaki da sake sake a raina ba, na kin ganin laifin da Aminu da Mama take da kokarin wankeshi a idanuwana, ga kuma zancen aure da take kokarin bijiro min da shi, anya ya gama da warke daga radadin azabar kunar da Abdulhamid da Aminu suka min da har zan yi tunanin aure? Ko da ma ace yana gabana ballantana yanzu da bana sha'awarsa.
Na isa gurin da zanje cikin lokaci domin na tsarawa kaina isa gurin da misalin tara na safe sai ga ni na isa takwas da rabi da yan dakiku a kai, duk kuwa da kasancewar babu wanda ya san da zuwana a kamfanin hasalima ni kaina ban san mai kamfanin ba ban san tsari da dokokin kamfanin ba amman ina kyautata zaton a lokacin ne za a samu duk wani wanda ake tsammani samu a kamfani.
Kamar dai ko wane kamfani shi ma wannan yana da masu gadi dake sanye da uniform mai sunan kamfanin wato Crown Company Limited. Sai dai ba su kadai ba har da Sojoji a gurin.
Sai da suka auna jikina idan bana dauke da bom sannan suka ba ni damar shiga ciki, ba ni kadai suke yi wa haka ba, har masu mota sai sun bude musu bayan mota sun duba sannan su basu damar wuce ciki.
A iya zamana garin gusau ban taba shiga cikin kamfanin ba, to me ma zai kaini tun da ba siye ko siyarwa zan yi ba, a yanzu ma dan ina neman aiki ne kamar yadda nake cewar kamfanin yana neman ma'aikata yan boko wadanda za su iya communicating da wasu mutanen amman da yalshen nasara wato turanci.
Sai dai ban san inda ake bi a shiga kamfanin ba, domin na lura da kofar kamfanin ta kasu gida uku wasu na fita da shiga a ta farkon wasu a ta biyu wasu a ta uku, tsaye nai a gurin ina ta tunanin wacce zan shiga, ta farko haka zuciyata ta raya min dan haka na nufi kofar gadan gadan, a nan ma wasu matsaran ne rike da abun awonsu kamar dai na bakin gate.
Sai dai da alama su basa barin mutum ya shiga sai idan ya nuna musu wata yar takardar wacce nake ganin kowa yana ba su su duba kamin su barshi ya shiga ciki. Hakan yasa ban karasa a gurin ba sai na juyo na nufi kofar tsakiya wacce mutane suka fi fitowa a cikin, wani abun burgewa ma kofar ita take bude kanta sai jujjuyawa take gwanin sha'awa, ina kokarin kutsa kai na shiga cikin kamfanin na Abban Baby Namra ya fito daga ciki yana sanye da shadda mai ruwan madara, ba laifi na dan saki fuskata domin har ga Allah na yi nufin gaisheshi sai kawai na ga ya hade fuska kamar bakin hadari daman can fuskar tashi ba a washe take ba, balle yanzu da ganina yasa ya kara hade ta kamar yaga mala'ikan mutuwa. Hakan kuma be hana na mika masa gaisuwa ba, amman sai yai min banza ya wuce abun shi, a take na ji duk na muzanta domin akwai mutane a kofar kuma na san wasu sun ji gaisuwar da na mika masa. Sai kuma duk na ji haushin kaina, miyasa na gaishe shi tun da farko ma? Miyasa ban kyale shi ba na yi tafiyata? Why na nuna na sanshi ma?
“Miya kawo ki nan?”
Kamar daga sama na ji tambayarsa da wata bakar murya tashi, har daka min tsawa yake kamar wata yarshi.
“Ban sani ba”
Na fada cikin tsiwa ba tare da na kalleshi ba na cigaba da tafiyata ina jin haushin kaina, na gaishe shi ne saboda ina ganin kamar akwai mutunci a tsakani ko dan abokatar da ke tsakanin Baby Namra da Namra, ko da yake daman daga ganinsa ba zai yi mutunci ba sai wani jijji da kai sai kace shi yafi kowa arziki a gari, Allah kadai ya san abunda ya kawo shi kamfani ma wata kila shi ma wata alfamar ya zo nema amman sai son nuna isa.
“Wai miya kawo ki nan”
Na fada a fili ina tsire baki har wani namijin da ke reception din ya dago ya kalleni.
“Na'am....”
Sai na dan saki fuskata nai masa murmushi.
“Sannu dai Malam daman na ji kamar ance kamfanin ku yana neman ma'aikata”
“Eh amman ba zuwa ake ba, ta email ake turo mana sako”
“Minene mail dinku?”
Ya fada min sannan na sake ce masa.
“Sai dai matsalar ban taba zuwa kamfanin ba, ban kuma san tsare tsaren kamfanin ba ban san mi kamfanin yake ba”
“Kamfanin mu yana siye da siyar da zinari tare da narkawar da kuma saffarashi ta hanyar yin abun wuya dan kulleni ko kuma wani abun na kayan ado na jiki ko na riguna”
“Na gode sosai, ta mail din zan tura cv na?”
“Yes idan sun duba suka ga kin cancanta za a kira sai ki zo”
“Na gode”
Na fada masa ina dariya.
“Your welcome.”
Tare da murmushi as respond. Ni kuma na jiyo na fito daga kamfanin, abun ka damai salo sai da nai ma security guard din sallama sannan na kama hanya, ban yi wata tafiya mai nisa ba na hango Kabir zaune a gafen hanya tufafin jikinsa sun yi datti ga surar kansa ta taru gaba daya ya soma canjawa ga wani abun datti da jikinsa yai. Karasa gurinsa nai da sauri ina kiran sunansa sai ya dago kansa da sauri ya kalleni ban san lokacin da na fashe da kuka ba. Hannu na saka a jakata na dauko dubu biyu na mika masa, be karba ba ba kuma yi min alamar zai karba ba, hakan yasa na risina na aje masa kudin na soma tafiya ina hawaye ina waigensa, har na tari napep na shiga be daina kallona ba kuma be kai hannu ya dauki kudin ba.
Gaba daya rayuwarsa ta baya sai ta dawo min sabuwa, Kabir mutum ne mai tsafta ga far'a da son mutane, musamman ni yana kula da ni yana nuna min kauna, duk kuwa da yake haramtacciyar kauna na nemana bayan yasan ina da aure.
Na fi alakanta ganin da nai a haka da rashin mahaifiya a raye domin na tabbatar da ace mahaifiyarsa tana raye ba zata bar danta a haka ba, domin ba duka yake ba balle ace ana gudunsa ba zagi yake ba, kusan sun ta haukar nan ta same shi ko magana baya yi.
Wallahi har na isa gida hawaye ba su daina zubar min ba, sai da zan fitaa napep din sannan na share hawayena na sallame shi na shiga gida, ashe wani kukan zan tarar a gidan mu, na shiga n samu hankalin kowa a tashe, ka rasa wanda zai fada min cewar Amal ta samu hatsari.
“Wai miya faru ne?”
Na tambaya ganin kowa yana ta bina da kallo.
“Amal ta samu hatsari”
Inna ta fada min muryarta a hankali.
“Ko dai ta mutu? Ku fada min?”
“Ba mutuwa tai ba tana asibiti ma”
Hafiza ta amsa min.
“Garin ya ta samu hatsarin?”
“Aisha taje daukarsu daga school sai ta tarar wai Aminu ya dauke su, sai ga kanwarsa ta zo yanzu ta fada mana wai Amal ta samu
Hatsari, so yake ya kashe miki yayan”
“Wace asibiti?”
“Wai Yarima bakura yanzu yanzu ta bar gidan”
Ko jakata ban aje ba na ja kanwata Husna muka nufi asibitin domin an fada min Mama da Aisha suna can sun tafi, haka muka shiga cikin asibitin mukai yawon duniya muka gama ba mu gane inda aka kwantar da Amal ba, daga karshe n yanke shawarar kiran Aminu a kan dole na tambaye shi, shi ma nai ta kiran wayarsa ya ki ya daga har yamma.
Ga shi daga Mama har Aisha babu mai waya balle na kira su, hankali yai mugun tashi, wata zuciyar na ce min naje gidansu Hajiyarsa na tambaya sai kuma na ji kamar ba zan iya zuwa ba, ba hatsarin Amal ne kawai ya daga min hankali ba har da rashin ganin Adnan Aiman Namra da ban yi ba domin ance suna can tare da shi.
“To ko kuma din sun samu hatsarin ne?”
“Waya sanar mishi? Mu dai kar ya kai mana uwa ya halaka”
“Wai ina ka kai min yara ne Aminu.....”
Kamar hadin baki ina rufe baki sai ga kiransa ya shigo a wayata. Da sauri na daga jikin har ba ri yake.
“Ina Amal din ina yarana...”
“Muna nan Royal Hospital tare da su”
Tsakanin akatse kiran wayar da mikewa ta tsaye bana jin ya ci dakika daya ma, cikin sauri na fita cikin gidan na isa titi na hau achaba na nufi asibiti. Sai da na sake kiransa na tambaye shi gurin sannan na karasa, a waje na samu Mama da Hajiyarsa suna zaune kamar abun arziki, Hajiyarsa na ganina ta taso ta tare ni da yar far'arta ni kam ko kula ta ban yi ba na tura dakin na shiga. Daga Aiman har Adnan da Namra da Aminu da kuma Aisha suna cikin dakin, Amal na kwance an saka mata bandeji akai sannan an saka mata wani karfe a baki an kware bakin ga halshenta da dinki.
“Miya same ta me kai mata?”
Na tambaya a tsawace ina kallonsa. Sai ya kalleni a sanyaye ya kasa ce min komai. Sai mahaifiyarsa ce ta amsa min.
“Ya dauko su daga Scul ne yana kokarin tsallaka titi da su sai wani mai Napep ya hade Amal”
“Momi kuma halshenta ya cire yanzu aka dinke mata shi..... ”
Aiman ya karasa mata, ban san lokacin da na kalli Amal ba na sake kallon Aminu ya ce.
“Kaga abunda ka ja min a gurin ya ko? Miya kaika daukar min yara?”
“Mhaifinsu ne ni Halima ki rika tunawa da wannan... ”
Ya fada ido raurau kamar zai fashe da kuka.
“Sai yanzu ka san kai mahaifinsu ne? Sai yanxu kasan su din yayanka ne?....”
“Haba Halimatu”
Mahaifiyarsa ta tari numfashinta sai yai saurin daga mata hannu.
“Barta ta fadi duk abunda take son fada Hajiya...”
Wannan karon nuna shi nai da yatsa.
“Ba fada kawai zan yi ba, gargadin ka zan yi akan yarana? Karka sake kula su ko kallonsu karka sake yi balle har ka dauke zuwa wani gurin karka sake nuna hada jini da ni...”
“Ba zan yi abunda zai jefasu a matsala ba, abunda ya faru kaddara ce wacce ko wane dan'adam be isa ya wuce ta ba, kuma ina son ki rika tunawa cewar har gobe ni mijinki ne domin akwai yaya a tsakanin mu kuma ba a san abunda gaba zata haifar ba..... ”
Taba sanin cewar kiyayya Aminu a zuciya ta kai min makura ba sai a wannan lokacin, tasss na wanke masa fuska da mari, mari daya be min ba har sai da na kara masa na biyu ina kokarin yin na uku Namra ta rike min hannu tana kuka sai ta rumgume Babanta. kasa cewa komai nai na fice daga dakin ina hawayen da ban san na minene ba. Ko da na fito ana ta kiraye kirayen sallah mutane waje kowa harama yake hakan yasa na nufi gurin da aka tanada dan aje motoci na zauna saman wani tebur da wasu maza suka tashi, a lokacin da na zauna sai na saka kaina cikin kafafuwan na rushe da sabon kuka, ji nai an zauna a saman tebur din da nake zaune da sauri na dago kaina na kalli gefena. Abraham ne sanye da blue T-shirt da facing cap black kamar yadda wandonsa yake, ko da wasa be kalli inda nake ba sai raba ido yake yana kallon harabar asibitin, Bluetooth din dake gefen kunnensa na ta balli da jar wuta.
“Mi kike yiwa kuka?”
Kawar dai nai wasu hawayen na sauko min.
“Abubuwa da yawa da yawa da yawa... ”
Na kasa daina fadin da yawa din har sai da ya kalleni.
“Kamar me da me?”
“Ba za su lissafu ba, idan na fita daga wannan na shiga wannan na gaji da rayuwar nan, na rasa yadda zan yi.... ”
Ji nai ya rika hannuna...
“I will be safe in this hand of mine, fada min matsalarki kuma ki fada min wanda ya saka ki a damuwa yanzu nan... I can give you another life..... ”
Kamar an min shocking haka nai saurin fisge hannuna na mikewa tsaye ina kallonsa. Kamar yadda shi ma yake kallona.
“I will take the pain,.... take it away....”
Hannu na saka na share hawayena na nufi inda na fito da sauri na barshi a gurin zaune.
#Team Gwarzo
#Team Aminu
#Team Abdallah
#Team Abdulhamid
#Team Kabir
#Khadeeja Candy
#GOBENA
7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
3️⃣7️⃣
ABDALLAH POV.
After ya bar gidansu Halimatu ya koma office, sai dai ya kasa natsuwa da abunda Hajiya ta saka shi ya aikata kuma yana ganin be kyautawa Halimatu ba, yanzu dawainiya za tai mata yawa. Haka dai yai aikin da tunaninta a ransa kamar kullum bayan ya tashi office yai sallah masallacin asibitin sannan ya nufi gidan Hajiyarsa.
A yau harabar gidan ya tararda ita ta shinfida katuwar tabarma ita da yar aikinta suna ta fira. Kusa da inda suke zaune yai parking sannan ya fito daga cikin motar fuskarsa na nuna alamar akwai damuwa a tare da shi, tun kan ya karaso mai aiki ta miko masa gaisuwa sannan ta tashi ta koma cikin gidan.
“Hajiya sannu da hutawa”
“Yauwa”
Ta amsawa tana kokarin kawarda fuskarta daga damuwarsa, shi kuma ya zauna kusa da ita sosai ya soma mata magana a hankali.
“Hajiya da dai zaki duba maganar”
“Maganar Halimatu ko? Ko gaisawa ba mu gama yi ba za ka dauko min zancenta”
“Wallahi Hajiya tun daga lokacin da kika shaya mana katanga a tsakani sai na shiga cikin damuwa, ba aurenta zan yi ai Hajiya, bayan soyayya akwai tausayinta a zuciyata wanda shine makasodin karuwar soyayyarta a raina, hanani taimakonta da kika yi sai ya jefani cikin damuwa”
“Indai kana neman albarka ka bi umarnina ka huta”
“Amman Hajiya harda yaranta?”
“Har da su....”
Ta amsa masa da karfi alamar ta fusata sosai. Sai yai kasa da kansa, na wani lokacin kamin ya tashi ya saka takalminsa.
“Hajiya zanje gida na huta, a tashi lafiya”
Shine last word dinsa da ita sannan ya nufi motarsa ya shiga, a maimakon ya nufi gidan kamar yadda ya fada sai ya juyarda motarsa zuwa gidan iyayen Halimatu, hakuri yake son ya bata akan abunda ya faru dazun, if ba zai iya taimakonta a yanzu then ba shi da yancin fada mata bakar ji yake kamar yai mata wani aibi, daya bayan daya yake ta tunanin maganganun da yai da ita dazun a lokacin da yaje kai mata takardar transfer dinsu Namra, even if be fada mata bakar magana ya kamata yai mata wata maganar da hankalinta zai kwanta ba wai ya barta a cikin duhu ba za tai ta zarge zarge akansa hakan kuma ba karamin jefata zai yi magana damuwa ba.
Yana isa ya fita daga motar cike da gwarin guiwa ya nufi cikin gidan, sai da gaisa da kanenta sannan ya nufi dakin Mama.
“Mama bata nan Halimatu ma bata nan sun tafi asibiti”
Ya juyo yana kallon Ramla wacce ke masa maganar.
“Waye ba lafiya?”
“Amal ce aka ce ta samu accident on their way back to school”
“Subhanallahi suna wace asibitin?”
“Royal”
Da sauri ya fice daga gidan be ko tsaya gaisawa da Inna ba, hankalinsa ya tashi sosai a take tausayin Halimatu ya kara kamashi.
“Oh Allah.... ”
Ya furta yana hannunsa na hagu saman kai. Tunanin halin da Halimatu take ciki yake gashi ba shi da halin taimaka mata a yanzu. Ya busar da iskar bakinsa yana girgiza kai.
Sai ya shiga cikin asibitin sannan ya ciro wayarsa ya kira Halimatu domin sanin a inda suke, a maimakon ya ji muryar Halimatu sai muryar Aisha ta daki dodon kunnensa, itace ta kwantanta masa inda suke ya karasa gurin da kuzarinsa, sai dai yana bude kofar dakin ya shiga idonsa sukai arba da Aminu sai wani rashin jindadi da walwala ya mamaye masa zuciya. Da Mama kawai ya gaisa sai Aisha da ta miko masa da gaisu, ko da wasa be kalli inda Aminu yake ba balle mahaifiyar Aminu da ke binsa da kallo.
“Mama garin haka ya faru?”
“Wallahi suna kokarin tsallaka titi ne wani mai achaba ya kade ta”
“Subhanallahi”
Ya karasa kusa da Amal yana dubata, sai Aiman ya zo ya kama hannunsa yana kiran Uncle. Dan murmushi kadan Abdallah yai masa domin yau babu walwala da far'a a tare da shi, hannu ya kai zai shafa kansa sai Aminu ya kai nasa hannun ya fisgo Aiman yana jin wani irin kishi da kiyayyar Abdallah na taso masa. Da gangan Abdallah yai masa wani shegen kallo na uku saura kwata, kamar zai yi masa dariyar abunda yai sai kuma ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 55