kuma wata zuciyar ta hana ni.
Ba mu yi nisa sosai da hotel din na ga direban ya faka motar gafe ya fita ya zaga bayan motar ya dauki abubuwan da ya dauko a gurin taron sannan ya rufe, Ahmad kuma ya fita daga motar ya shiga mazaunin direba yaja motar, ni kam ina zaune baya abuna sai dai sanyin ac yayi min yawa har na fara jin kamar ciwon kai na son kamani.
A nesa da masallacin gada biyu ya faka motarsa ya bude ya fita sannan ya zagayo inda nake ya bude min.
“Zanje nai sallah ki dawo gaba”
“Ban iya tukin mota ba”
“Ban ce ki tuka ba, a front seat zaki zauna”
Na fito na bar kayan a baya sannan na rufe motar na bude gidan gaba na zauna ina ta mamakin karbe min waya da yai, can kuma na tuna da abunda yai min jiya, wata kila dan kar ayi ta kirana ne muna tare kuma baya son hayaniyar kiran, amman ai sai ya bar min wayata yace kar na kunna.
Ni dai ina zaune a motar har aka sauko daga sallah juma'a mutane suna ta wuce, sannan ya bude motar ya shigo yai mata key muka hau titi, a hankali yake tukun kusan ko wace mota ta zo sai ta wuce mu, kusan da mu da masu tafiya kasa duk daya idan ma akwai tazara kadan ne.
“Kin na rasa yata ko?”
Na juyo na kalleshi sai na ga ba ni yake kallo ba, amman tabbas na san da ni yake domin daga ni sai shi ne a motar.
“Eh”
“Na rasa mahaifina ma, na rasa Matata mahaifiyar Baby”
Ya sake fada still be kalleni ba.
“Allah ya musu rahama”
Be amsa da amin ba, sai yai wata maganar ta dabam.
“You got lucky baki tana rasa kowa ba, the pain of losing someone is unforgettable, mahaifina na fara rasawa, mahaifina yana da ciwon suga, a lokacin da abun ya taso masa an fitar da shi waje, a cairo ya rasu a lokacin na shiga tashin hankali sosai, kin san saboda me?”
Na girgiza kai.
“Saboda Hajiyata, ya mace zata ji idan ta rasa mijinta? Ya da zai ji idan ya rasa mahaifinsa? Ya yar'uwa zata ji idan ta rasa mahaifinta? A lokacin nauyin Hajiya da Siyama da nawa ni kaina sai taro duk a kaina, tausayin kaina tausayin Hajiya tausayin Siyama, mu biyu kawai Allah ya bashi, daga ni sai Siyama, Hajiya tana son yayana sosai, sai dai duk haihuwarta yaranta rasuwa suke daga ni sai Siyama muka tsaya, shiyasa take son Siyama sosai wani lokacin tana kiranta da autarta, kamar yadda nima take so na sosai har take kishina, tana ganin kamar wata macen zata karbe mata ni, lokacin da muka rasa mahaifi komai na mu ya tsaya cak, ciki har da rayuwarmu domin mahaifinmu shine komai na mu, kullum Hajiya tana cikin damuwa Siyama ma haka”
Yayi shiru ya kai hannunsa ya dauki gorar ruwan da ke cikin motar ya bude ya kurba sannan ya aje.
“Daga lokacin na fara tunanin gina rayuwata, da ta mahaifiyata da kuma ta kanwata, a lokacin ne na fara neman aure har akai nasara na auri wata yarinya, she's my first wife but not my first love, domin na aureta ne ba wai dan na san miye soyayya ba a lokacin, a gida daban muka tare, daga lokacin da nai aure sai rayuwa ta ta canja daga matashi wanda yake zaune a gidan mahaifinsa zuwa mai mata da yake zaune a gidansa, na aje aikin da nake na soja a lokacin na cigaba da kula da kamfanin mahaifina na zinari, a cikin na bude makaranta wa Hajiyata duk wani abu na makaranta a hannun Hajiya yake zuwa, a da kullun tare da Hajiya muke karyawa komai kusan tare muke amman da nai aure sai abubuwa suka sauya, daga lokacin sai Hajiya ta fara ganin kamar matar da na aura tana kokarin mallake ni ne, sai ta cilasta min dole sai na dawo a cikin gidan mahaifina na kama part daya na zauna da ita, ita kuma tace ba zata zauna da Hajiya ba, daker na samu kanta ta amince muka zauna tare, sai kuma ta hanani cin abincinta tana cewa zata saka min magani a ciki, ta fara takura mata ta saka abubuwan da ya kamata ace mai aiki ce zatai, da ta kasa jurewa sai ta nemi fita Hajiya tace na sake ta, a haka nai aure har uku yana mutuwa saboda takurar Hajiya, ban zamu wacce ta dade ba sai mai sunanki, mace mai hakuri kamar ke, mai kawaici da sanin ya kamata, ita ta haifa min Baby Namra, a cikinta na biyu ne ta rasu, a ranar da ya rasu ni kaina bana iya gane kaina, domin rasa abokin rayuwa yana nufin rasa wani bangare na jikinka...”
Ya karasa muryarsa na rawa, hannuna na kai na dauki daya daga cikin tissue da ke cikin tissue ibox na mika masa sai ya karba.
“Thank you”
Ya tare gefen idonsa sannan ya sake kurba ruwan, ya bude gilashin motar iska ya shigo wata kila sanyin ac baya wadatar da shi.
“Sai ta bar ni da Baby, after that na sake aure biyu ya mutu, dayan saboda Hajiya dayan kuma saboda matar bata son Baby sai ta rika kishin yata tana ganin kamar ina nuna mata so da yawa ne, daga lokacin sai an gimgine maganar aure a gafe, na cigaba da rayuwata da yau da kullum, sai gashi na samu kaina cikin farinciki a haka muke rayuwa da kanwata da mahaifiyata da yata sai kuma sauran dangi na yan'uwa, amman dai a familyn mu mu kadai muka rage yayan Abbah, so the day I lost Baby, ba zan iya fada miki abunda naji ba, at first ban ji komai ba sai daga baya, kuma na kasa blaming kowa sai ke saboda a gurinta ta rasu, and she always talking about her friend i mean your daughter, tace na baki hakuri be kamata nai fada da mahaifiyar abokiyarta ba, so the day that i decided zan baki hakuri....”
A nan din m shiru yai sai hawaye ya gangaro ta gefen idonsa.
“Ina son yata sosai....”
Ya fada yana rumtse idonsa na wani lokaci kamin ya bude.
“Tana da sakewa, tana da kyauta duk da kasancewar ta karama, ga ta da wayo, ga son mutane bata da abokin shawara sai ni bata da abokin wasa daga ni sai Siyama wacce ta zame mata kamar kawa, sai kuma Hajiya wacce ta zame mata mahaifiya, Baby bata da kawa ko daya sai yarki da ta samu daga baya, that's why take yawan damun kanta kullum sai ta ganta.... ”
Ya lumshe idonsa yana sauke ajiyar zuciya da karfi.
“Abubuwa da yawa suna faruwa saboda ni, kai ma idan kana tare da ni wani abun zai iya samunka Dan Allah ka sauke ni a nan”
Na fada ina kawarda fuskata wasu hawaye masu zafi da radadi suna sauko min, a yau kan na manta da damuwata labarin Ahmad ya ban tausayi, domin rasa uba, ya, mata, abubuwa ne da basa fassaruwa da ko wane kalar yare. Murmushi yai ya miko min tissue da na bashi
“Take your tissue back”
Na karba na share hawayen, sannan ya miko min ruwa na karba na kurba sai na rike gorar, ina jin kamar wani hawayen zai sauko min.
“Can I imagine your life without your parents?”
Dam dam dam na ji gabana ya yanke ya fadi, kallonsa nai kamin na kalli gorar ruwan dake hannuna.
“Uba wani jigone na rayuwa, bayan Allah da manzosa, iyaye ne suke da muhalli na biyu a rayuwar ko wane dan'adam, daga lokacin da ka rasa uba za a fara kiranka maraya, saboda uba gangone na gingina, shi zai nemo ya kawo a ci, shi zai tufatar ya ciyar ya shayar ya ilmantar, uba wani jigone na rayuwa, gata ne, uwa kuma ita ce gaba daya rayuwar, idan babu uwa duk farincikin da zaka samu a duniyar nan ragaggene no matter what it's, uwa abokiyar tafiyar rayuwa ce, abokiyar shawara abokiyar kuka abokiyar dariya abokiyar farinciki abokiyar bakinciki, idan da yai kuka ka ji ba a rarrashe shi ba, to babu mahaifiyarsa a kusa ne, macen da zata dauki cikinka tun yana da second daya har yai wata tara ta haife ka ta jure kashi da fitsarinka ta rayu da kai a ciwo da ba ciwo, har ka mallaki hankalin kanka? Uwa ita ce gaba daya duniyar. No never... I can't imagine my life without one of them they are my super supporter's my everything”
Na karasa cikin kuka, ina jin wani irin shauki da kaunar iyayena ya kara kamami, iskar bakinsa ya busar ya jingina da kansa jikin kujerar motar yana kallona kamar bashi ba.
“Zan kai ki gida gurin Hajiya ki yi sallah”
Na share hawayena ina kallonsa.
“Mun tashi daga aikin ne?”
Na gyada min kai yana kokarin parking motar still idonsa na kaina.
“Idan haka ne ai kara na wuce gida kawai”
“No gurin Hajiya za ki yi sallah”
Bance masa komai ba sai na maida dubana gurin yan yatsun hannuna, ina jin faduwar gabana yana karuwa ga wani uban ciwon kai da ya saka ni a gaba, ban san miyasa yau Ahmad ya zame min wani dabam ba shi ba.
Key yai ma motar muka hau titi wannan karon ba mu yi tafiya mai nisa ba muka isa gidan, horn daya ya danna aka bude masa gate, ya kunna kai a cikin gidan, be yi farkin a ko'ina ba sai bakin kofar falonsu, fita yai shi kadai yace na jira shi a motar ya shiga cikin, be jima ba ya fito ya bude min motar yace na fito, haka na fito ina jin jikina ba kwari na shiga ciki, kamar dai wacan karon wannan karon ma Hajiyar da far'a ta tarbe mu sai dai yanayin yadda take kallon fuskata tana nuna alamar tausayi.
Bayan mun gaisa, tai ma Kanwarsa magana tace ta kai ni ciki nai sallah, da sauri yarinyar da aka kira da Siyama ta tashi tai min jagora har dakin Hajiyar, a bathroom dinta nai alwala ko da na fito an shimfida min carpet an dora Hijabi sama, sai kawai na dauka na saka na fara sallah azahar a lokacin uku ta kusa. Ina sallah shaidan ya fara yayo min tunani kala kala, kamin na gama sallah jikina har rawa yake, ina gamawa na cire hijabin na dauki veil din abayata na yafa na fito falon inda Hajiyar take na zauna, Ahmad ma yana zaune a falon ina son nai masa magana na kasa.
“Siyama kawo mata abincin”
Ya fada yana kallon yanayi gaba daya idona ya fito fuskata ta sauya.
“Wayata ina son magana da.... ”
Tun kan na karasa ya tari numfashina.
“Zan baki anjima”
Wannan karon kallonsa nai da kyau.
“Wa na rasa Ahmad? Uwa ko Uba, ko yaya? Ko kane? Fada min”
Mikewa tai tsaye yana kallona sai nima na mike tsaye. Can kasa kasa na jiyo Siyama na fadin.
“Ku fada mata gaskiya mana, dole ne ta sani”
“Siyama fita ki bar falon nan”
Ahmad ya fada mata a tsawace, kamar tana jira ta juya ta fice cikin fushi.
“Ka fada min wanda na rasa, ba zan iya dawo musu da rai ba, iyakar abunda zan yi hakuri ne”
“Muje na kai ki gida”
“Ka bani wayata”
Na daka matsa tsawa da wata irin murya daban taba sanin ina da ita ba, gaba daya jikina rawa yake.
“Ina da kanen, idan an rasa Uba sun zama marayu wa zai kula da su, idan na rasa Uwa wa zai maye musu gurbinta shikenan sun rasa gata”
Na fada ina rufe ido kamar mai nazari.
“Allah baya barin wani dan wani duk a can muka fito iyayenmu sun tafi sun bar mu, kuma a can zamu koma gaba daya”
Mahaifiyarsa ta fada idonta cike da hawaye, takawa na fara yi sai na ji kafar ta malgwade ina neman faduwa har sai da tai saurin rike ni, a hakan na sake unguri takawa kafafuwan suka fara rawa sai ta na tsaya cak, da nai unkuri na uku sai na tafi zan fadi har sai da Ahmad ya rike ni da kanshi ya zaunar akan kujerar.
“Ki natsu sai na kai ki gida”
“Ka kaini yanzu”
Na fada kai tsaye tare da mikewa tsaye na fara tafiya cikin karfin hali, ba shiri na ji numfashina yai sama wani hudu ya baibaye idona, jikina kuma yai arba da kasa.....
__________________________
Allah ka jikan mahaifina kai masa Rahama ka saka aljanna ta zama makomarsa, Mahaifiyata kuma ka karasa mata lafiya da kwanciyar hankali da natsuwa ka yafe mata kurakuranta kasa ta cika da imani 🙏 da duka sauran iyayenmu musulmai 😭🙏
Rashin iyaye wani ciwo ne da ba a manta shi 💔💔💔 may Allah see us though. 🙏
7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: *GOBE NA...*
By Khadeeja Candy
4️⃣7️⃣
A yau kam kamar an halittoshi ne kawai domin kallon Halimatu, ya kasa zama kamar yadda a tsayin ma ya kasa yin nesa da ita sai daf da gadon da take kwance, fuskarta yake kallo, be taba tsaya ya kalleta kamar haka ba, daman can ahali shi ba mutum ne mai tsaya ya kwankwace mace ba.
Amman a yau yana jin kwanciyar hankali da natsuwa a kallon Halimatu, dogon hancin ya fara kurawa ido kamin idanuwansa su sauka akan karamin bakinta, fuskarta circir bata da rama kuma bata kumbura sosai ba ta cike abunta gwanin sha'awa, farin fuskarta dana jikinta har wani shining yake, ga jikinta Ma-sha-Allah irin wanda ake so a mata, tana da jiki sai dai ba can sosai ba, akwai kurciya sosai da yarinta a siffarta da surarta amman ba irin ta under 20 ba, irin wacce zaka kalleta kai zaton Amal ce yarta ta farko ba Adnan ba, babu abunda ta rasa a siffar ya mace sai na tsuwa da kwanciyar hankali.
Ta saman idonta yake hango damuwarta, labarin abunda ya same ta ta kuma yadda yake tunanin Gobenta zata kasance, be san miyasa yake tausayinta da yawa ba, yes be taba jin labarin daya taba masa zuciya ya hana hankalinsa kwanciya ba kamar nata, sai dai be taba tunanin hakan zai saka wani kusanci a tsakaninsu ba, the way da ya daukota ya kawo gurin Hajiyarsa, yadda yake ta kokarin boye mata mutuwar mahaifinta and ya bata tahirin rayuwarsa a free, ko da yake yayi hakan ne saboda kawai ya nuna mata ko da ta rasa ba ita kadai ce a cikin jarrabawa ba.
Kansa ya daga sama ya sauke numfashi a hankali, hannayensa duka biyu na zube cikin aljihu, can kuma ya sauke kan yana cigaba da kallonta, wani sinadarin tausayinsa ke fita daga cikinta yana shiga zuciyarsa, tausayinta ta cika zuciyarsa makil, a yadda take ya mace ace tana cikin irin wannan kalubalen na rayuwa ita din abar tausayi ce matuka.
Hannunsa ya saka aljihu ya fiddo wayarta, hakan nan kawai yaji yana sha'awar kunnata, and he press the power button ya kunna wayar. Hoton yaranta hudu a screen din wayar, he found himself smile yana shafa screen din wayar.
“Beautiful kids”
Ya furta yana maida hankalinsa sosai gurin kallon Amal, a zatonsa ita akai wa fyaden tunda ita ce karama marar wayo. He was just imagine if ace shine mahaifinta, ya zai yi wa mutum yana jin aransa zai iya kashe wanda yai wa yarsa haka, but look at them a maimakon ma ya yarda da mahaifiyarsa sai ya karyata ya saketa akan hakan, tunawa yai da lokacin da Namra ta bata har ya tsinceta, yanzu ya gane duka responsibility na yaran akan mahaifiyarsu, shi uban babu ruwansa, zuciyarsa ta cika da tsananin mamaki ashe ana samun useless father like her husband? Wayarta ce tai ringing sunan Abdallah ne rubuce a saman wayar, haka yai ta kallon wayar har tai ringing ta katse be dauka ba, at the end yai deciding ya sake kashe wayar ganin wata Number ma ta sake kira mai sunan Hajara.
Yana kokarin mayardar wayar aljihunsa aka turo kofar dakin aka shigo, wata dattijitowa ce da ba zata gasa 50+ ba, ko tantama babu yasan yar'uwar Halima ce tun da ya aika direba a can gidansu a fada musu ta suma ya kawo ta asibitin kuma wani nata ya zo ya zauna da ita.
“Sallamu alaikum”
Matar ta fada da katon Hijabinta, sai ya amsa mata yana binta da kallo.
“Ke ce?”
“Yayar mahaifiyar Halimatu”
“Alright, ga wayarta aje mata Allah ya sauwake”
Ya fada yana mika mata wayar, ita kuma ta karba tana masa godiya.
“An gode Allah ya saka da alheri ya kara sutura”
“Amin, an kai shi ne?”
“Eh an kai shi gidansa na gaskiya tun dazun”
“Ok”
Juyawa yai ya fice, sai da ya biya ya samu Doc Nura a Office dinsa yana duba wasu marar lafiya, tsaye yai har sai da ya gama.
“Doc zata kai yaushe kamin ta farka?”
“Zata dauki lokaci, tun har bata farka na da aka kawo ta nan, kuma a gida ma kace ai kun saka mata ruwa ko”
“Yes a can din ma bata farka ba”
“Hakan na nufi zuciyarta ba kamar tawa take ba, gaskiya akwai damuwa sosai a zuciyata, irin wannan bugawan zuciyan wani lokacin ya kan so da ajali, kara ma naka idan rai ya bace yana nunawa duk da shi ma mai hadarin ne, amman irin nata yafi naka hadari domin irinta za a cigaba da bata mata ran ne, ba tare da an san tana da wannan ba, idan kuma zuciyarta ta cigaba da buga kamar haka zata iya mutuwa a take, kuma ina tunanin bata shan magani ko?”
“Ban sani ba gaskiya”
Ya amsa zuciyarsa na kara cika da tausayinta.
“To ya kamata a tambaye ta, ko kuma a ga likitanta, yanzu dole sai ta farka zamu iya yin wasu gwaje gwajen, amman jinin zuciyarta yana gudu da karfi fiye da kima wanda hakan matsala ne babba gaskiya, har yanzu da take sume zuciyarta na bugawa fiye da yadda ake son tana bugawa”
“Babu wani abu da zaka iya yi mata Doc i trust you”
“Yeah dole ne sai mun san irin gwaje gwajen da akai mata, kuma tana karkashin shan magani ko a a? Kamin yanzu ya zuciyarta so dole sai ta farka ko kuma idan kasan likitan da ke dubata zaka iya hada ni da shi”
“Ban sani ba, ban san komai akan hakan ba, dole sai ta farka ko kuma wani daga danginta ya fada”
“Yanzu dai best medicine shine a daina bata mata rai ko barinta da damuwa, duk maganin da za a bata zai taimaka mata ne kawai abun yai kasa, amman ba zai iya wakar da ita ba, matukar ba ta daina damuwa ko kuma a daina bata mata rai ba”
“Thank you”
Shine abunda ya fada ya juya zuciyarsa cike da tunani kala kala ya fice daga office din. Harabar asibitin ya fito ya nufi gurin da ya aje motarsa ya shiga yai mata key, ba gida ya jufa kai tsaye ba, family house din su Halimatu ya nufa a gurin yai musu gaisuwa ya kuma shiga har cikin gidan yai ma mahaifiyarta da yan'uwanta gaisuwa. Ko da ya fito unguwar ana Sallah magariba a hanya ya tsaya yai sallah sannan ya karasa gidan Hajiyarsa jikinsa duk a sanyaye, mutuwar mahaifin Halimatu ya tuna masa da mutuwar nasa mahaifin da kuma matarsa da yarsa, kuma ta tuna masa cewar Hajiya da Siyama ne kawai suka rage masa. A falon Hajiya ya zauna tasa aka kawo masa abincin amman ya kasa kallon abincin ma balle ya ci. Ita kanta mutuwar mahaifin Halimatu ya tuna mata da mutuwar mijinta mutum mai dattako da taimako.
Haka yai zaune ya zubawa katon tv ido duk da hankalinsa ba a can yake ba.
“Allah yai muka albarka Ahmad kai da Siyama, ya yalwantar zuri'ar Muhammadu ta karkashinku”
“Amin Hajiya”
Ya fada yana dauke kansa daga kallon tv ya kalleta.
“Ina tunanin aika abincin a gidansu What do you think?”
“Hakan na da kyau, a yanzu mai taimaka musu suke nema, Allah dai yai masa rahama”
“Amin, dazun da safe nake ta tunani a raina cewar ya kamata na samu mahaifinta da maganar mutumen nan mai bibiyarta, domin ina tunanin iyayenta ba su sani ba, a gidansu ma bana tunanin akwai wanda ya sani, a tare muka je meeting dazun ina son nai mata maganar ganin mahaifinta, amman duk sai naji ina jin nauyi na kasa yi mata magana, ashe duk lokacin ma ya rasu”
“Allah be kaddarar ganawarku bane, amman wannan yarinyar tana cikin taskon rayuwa, a halin da take ciki kuma wani ya fada mata, Wallahi ta bani tausayi sosai, tana bukatar farinciki ko yaya ne a yanzu”
Be yi kasa a guiwa ba ya labartawa Hajiya abunda Doc Nura ya fada masa.
“Irin wannan mahaifiyar da ace tana da kudi sai ta dauke ta ta kai ta can wata kasar ta huta ta wannan kunci har sai ta samu sauki ta dawo, Allah sarki rayuwa kenan Allah ya yaye mata”
“Amin”
Ya amsa yana sauke ajiyar zuciya.
HALIMATU POV.
Ba zan iya fadar awannin da na dauka a sume ba, dan dai ba a mutuwa a dawo na nace mutuwa nai na dawo, domin komai na dakin ganinsa nake fari tas, ina jin yawun bakina ya kafe, hayaniyar mutanen uku da ke tsaye kaina ma jinta nake kamar wani yare, ina jin suna taba jikin suna soka min abu suna danna zuciyata can kuma suka daga idona, na kusan minti goma shabiyar a haka sannan idanuwana suka fara gani daidai, sai dai jikin babu kuzari ko kadan yawun bakin ma har a yanzu babu su, numfashin ma ina jin kamar baya isata.
“Sannu”
Likitan ya fada, sai na gyada masa kai, ina kallonsa ya sake yi min wata allurar a cikin ruwan dake shiga cikin jikina. Bayan fitar likitocin na fara kokarin tuna abunda ya kawo ni dakin, a take kaina ya saka hawaye suka samu haya, a hankali na juya kaina sai nai arba da inna Lami, hakan ya tabbatar min da mahaifi na rasa kenan, domin da Mama na rasa da Inna Lami ba zata iya zuwa nan ba saboda kukan rashin yar'uwarta uwa daya uba daya.
“Sannu Halimatu Allah ya baki lafiya”
Unkura nai na tashi amman na kasa sai hawaye nake jikin nawa har lokacin babu kuzari.
“Lafiya kalau na fita na bar Baba, miya same shi?”
“Ai baya bata da kadan Halimatu, ciwon ciki ne ya taso masa sai amai ko kamin ayi wani abu yace garinku”
“Da gaske Uba na rasa”
Na fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. Ban tana jin irin abunda na ji a yau ba, kamar nai hauka nake ji, kamar nai ihu na dawo da shi, ashe haka yaran da suka rasa iyayensu suke ji? Ashe haka mairaici yake da ciwo, ga ni kenan da nai aure har na haifi yara, ina ga kanena da basu yi auren ba, a take tausayinsu ya kara rufe min zuciya.
Na dade ina kukan duk yadda Inna rai rarashina sai na ji kamar tana kara kura wutar kukan ne, misalin karfe daya aka bani tea na sha sai lemun hausa da aka yanka min, a daren ban sake runtsawa ba har safe.
Duk yadda likitan ya so na sauna har nan da kwana biyu ban nuna masa amincewa ta ba, a dole ya sallame ni bayan ya bani shawarar na sake dawowa nan da kwana biyu domin a duba lafiyata. Ya fada min halin da zuciyata take ciki da kuma irin treatment din nake bukata.
Misalin goma muka baro asibiti tare da Inna, da wasu yan'uwanmu da suka zo dubamu, kamin mu isa gida Mama ta fado min rai, sai duk tsoro ya kamani kar na zo na rasa ta ita tun da tana da hawan jini, tun a napep din nai ta kokarin tsayar da hawayena amman abun ya gagara ashe hawayen mutuwa su suke yin kansu, ina ta ganin kamar idan na isa gida zan yi arba da Baba ne a inda ya saba zama, sautin muryarsa yana ta dawo min a kunne, yadda yake dariya da duk wani hali nasa na kirki zuciyata tana ta janyo min shi. Ban kara tsinkewa ba sai da nai arba da yan karbar gaisuwar a kofar gidanmu, lallai mutuwa babu wanda ba shi da tambonki, a lokacin dana shiga cikin gidan sai kukan kowa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 38 Chapter of 55